Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sumame
kimanin
su arba'in sanye da jajayen tufafi sun dako tsalle
a
sama sun kewayeshi.Su duka sai suka zare
takubbansu suka ja tunga cikin shirin afka
masa.Tunda Barde Ruhaisu yazo duniya bai taba
ganin ZARATAN DAKARU masu kwarjini da kirar
SADAUKAI ba irin wadannan.Nan take jikinsa ya
bashi cewa yau fa ya gamu da gamonsa,amma
da
yake shima jarumi ne mai DAKAKKIYAR ZUCIYA
ko
kadan baiji tsoron yayi kokarin ceton kansa
ba.Abinda ya aiyana aransa shine ko ba komai
sai
yayi iya bakin kokarinsa yaga cewa bai mutu shi
kadai ba.A kalla yana son ya sami nasarar kashe
koda mutum goma ne daga cikin wadannan
zaratan
jarumai da suka kawo masa MAMAYAR
BAZATO.Lokacin da dakarun suka ga Ruhaisu ya
gyara tsayuwarsa yana dafe kufen takobinsa ba
tare
daya nuna alamun tsoro ba ko tunanin
guduwa,sai
su ma suka sha jinin jikinsu,suka fahimci cewa
lallai
shima JAN IDO ne,kuma zai iya yin barna kafin a
gama dashi.Hakan ne yasa dakarun basuyi saurin
afka masa ba suka tsaya daga baya baya suna
nazarinsa tukunna.Shi dai wannan wuri inda
DAKARUN SUMAMEN suka ritsa Ruhaisu wajen
gari
ne sosai a tsakiyar daji inda babu gida gaba ko
baya,kuma babu wani mahaluki dazai tsaya a
wajen
tsawon dakika goma batare daya firgita ba
saboda
waje ne mai yanayi na ban tsoro.Akwai dogayen
bishiyoyi masu duhuwoyi gami da manyan
tsaunika
wanda dole ne baza a rasa mugayen dabbobin
daji
ba akansu.Ko yaushe wajen tsit yake tamkar
babu
wata halitta mai rai a wajen,kai da gani kasan
cewa
ba za'a rasa mugayen MUTANEN BOYE ba a
wajen.Ana cikin wannan hali ne sai tsulum
dakarun
sumamen sukaga wani Badakaren a cikin shigar
bakaken kaya rike da takobi ya duro tsakiyarsu
daga
can sama daga kan wata doguwar bishiya ya
tsaya
daf da Ruhaisu suka hada baya alamar ce
Ruhaisu
ya kawowa dauki.Koda ganin haka sai shugaban
dakarun sumamen yabaiwa sauran yan uwansa
inkiya suka afkawa su Ruhaisu.Nanfa aka
ruguntsume da azababben masifaffen yaki mai
matukar tayar da hankali da muni.Ana fara yin
wannan gumurzu ne kowa ya san cewa KARO DA
KARO sai RAGO!Kamar yadda dakarun sumamen
suke da KARFIN DAMTSE da iya yaki,zafin nama
da
bakin naci,haka Ruhaisu ma da mai bakaken
kayan
nan suke dashi,don haka saida aka shafe sa'a
biyu
da rabi ana dauki ba dadi,in banda karar haduwar
takubba gami da sautin naushin jiki babu abinda
kunne yakeji.Gashi dai an kasa koda lakutar jikin
mutum daya a GUMURZUN bare a fitar masa da
JINI
mai yawa,amma kuma ana naushin juna yadda
yakamata kuma ana shanye naushin sai kace
jikin
kowa bana jini da tsoka bane.Duk wanda ka duba
saidai kaga hancinsa da bakinsa na yoyon
jini.Koda
shugaban sakarun sumamen yaga an bata
wannan
lokaci mai tsawo haka ba tare da sun sami wata
nasara ba saiya fusata ainun ya bayar da wata
inkiya.Take dakarun sumamen suka ja da baya su
duka alokaci guda suka zaro wadansu adduna
guda
dai dai wato ya zamana cewa kowannasu na rike
da
makamai biyu a jikinsa ga TAKOBI ga kuma
ADDA.Koda ganin haka sai wannan badakare mai
bakaken tufafi yai wuf ya zaro wadansu Wukake
guda
biyu a cikin jikinsa ya mikawa Ruhaisu guda ya
karba,suma suka dubi juna sukayi wata inkiya iri
daya.Koda Ruhaisu yaga sunyi inkiya iri daya shi
da
wannan badakare mai bakaken kaya sai
zuciyarsa ta
buga da karfi kuma tsoro ya shigeshi.Ba komai
ne
yasa masa wannan tsoro ba face ya gane cewa
ba
wani bane wannan badakare mai bakaken kaya
face
SARKI SAILUR.Take Ruhaisu ya tambayi kansa a
cikin zuciyarsa yace,saboda ne sarki yake siyar
da
rayuwarsa don ceton tawa rayuwar?Ai wannan ba
karamin ganganci bane a matsayinsa na sarki
yayi
haka kuma idan wani abu ya sameshi nima na
shiga
wani bala'in.Yana cikin wannan tunani ne
dakarun
sumamen suka sake afko musu aka sake
ruguntsumewa da sabon masifaffen yaki a karo
na
biyu wanda yafi na farko tashin hankali da bala'i
domin wannan karon wani irin sabon salon yaki
dakarun sukazo dashi ya zamana cewa sun hada
da
tsalle tsalle da kwance kwance suna yawo a
saman
su Ruhaisu da kasansu suna kai musu hari ta ko
ina.Faruwar hakan keda wuya kuwa sai suka fara
ruda sarki Sailur da Ruhaisu nan take suka sami
nasarar yankar kowannansu sau uku uku,jini yai
tsartuwa daga jikinsu suka kurma ihu sakamakon
tsananin zafi da zogin da suka ji.Nan take jiri ya
kwashi Ruhaisu ya durkushe kasa yana mai cake
takobinsa cikin kasa don kare kansa daga
faduwa.Koda ganin haka sai shugaban dakarun
sumamen ya dako tsalle sama cikin shammace
da
zafin nama ya daga makaman nasa biyu sama da
nufin ya fille masa kai.Koda Sarki Sailur yaga
abinda
ke shirin afkuwa gashi yana yaki da sauran
dakarun
sumamen shi kadai ya hanasu kusantar Ruhaisu
sai
ya daka tsalle sama yayi wata irin katantanwa da
kafafunsa a tsakiya dakarun sumamen ya
tarwatsa
su kuma ya kare saran da shugaban dakarun
sumamen ya kawowa Ruhaisu a gadon
bayansa.Taka takobin da Addar suka datsa
bayan
sarki Sailur jini yai feshi a lokacin da sarki sailur
ya
kurma uban ihu kuma ya fadi kasa tim a
sume.Koda
Ruhaisu yaga abinda ya faru ga Sarki sai ya
kurma
ihun daya ninka na sarki Sailur sau goma kamar
MAHAUKACIN ZAKI ya faso gari.Take gaba
dayan
dakarun sumamen suka firgita suka ja da
baya.Shi
kuwa Ruhaisu zuciyarsa ce ta kekashe ga barin
jin
dukkan tsoro da kasala saboda tafarfasa data
kamayi kamar zata kone saboda fishi bisa ganin
halin da sarki ya shiga,kawai sai gani akayi
Ruhaisu
ya daka tsalle sama tamkar daga cikin BAKA aka
harboshi ya sare kan shugaban na
su kuma ya soka masa wuka a tsakiyar kirjinsa
ta
fullo ta gadon bayansa.Take gangar jikin
shugaban
dakarun sumamen ta sulale kasa matacciya.Shi
kansa Jarumi Ruhaisu yayi matukar mamakin
yadda
akayiyayi wannan gagarumar BAJINTA da
JARUMTAKA.Koda sauran dakarun sumamen
suka
ga yadda Ruhaisu yayi da abin dogaronsu,wato
shugaban nasu sai suka firgice suka zubar da
makamansu suka cika wandunansu da iska.Kafin
kace wani abu babu dayansu a kusa.A sannan ne
Ruhaisu ya fashe da kuka ya fara dinke raunikan
dake gadon bayansarki sailur cikin razana da
dimauta yana ta fama rusa kuka domin a lokacin
ma
gani yake kamar tuni sarki ya dade da
mutuwa.Bayan ya gama dinke masa raunikan ne
yaga har a sannan jini bai daina zuba daga cikin
raunikan,al'amarin daya dugunzuma hankalinsa
kenan ya ruga da gudu izuwa cikin daji ya samo
wadansu saiwoyin bishiyoyi yazo ya dakesu ya
shafe
raunin dasu.A sannan ne jinin ya daina zuba,har
izuwa wannan lokaci Ruhaisu bai daina kuka ba
saboda ko kadan babu alamar numfashi akan
kirjin
sarki Sailur,kuma babu inda yake motsi a
jikinsa.A
daidai wannan lokaci ne Ruhaisu ya fara sakar
zuci
wata zuciyar tace dashi menene amfanin
rayuwarka
a duniya tunda ka rasa wannan BABBAN MASOYI
wanda baka da kamarsa a duniya.Ai gwara kaima
ka
kashe kanka tunda idan ma ka dauki gawarsa ka
kaita cikin gari babu yadda za'ayi ka tsira daga
zargin cewa kaine ka kasheshi.Koda gama aiyana
hakan sai Ruhaisu ya sake fashewa da
matsanancin
kuka na bakin ciki har izuwa lokaci mai dan
tsawo.Daga can kuma saiya daga takobinsa
sama
da nufin ya cakata a cikinsa ya kashe
kansa.Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga
sarki
sailur yayi wuf ya taso zaune ya rike hannunsa
kuma
ya budi baki da kyar cikin matukar karfin hali
yace,dakai ka mutu gwara ni na mutu kai ka rayu
saboda indai ban samu haihuwa ba kai nakeso ka
gajeni.Har yau har gobe wannan shine babban
BURIN ZUCIYATA.Koda sarki Sailur yazo nan a
zancensa sai Ruhaisu ya rungumeshi cikin
tsananin
farin ciki bisa ganin cewa bai mutu ba.Kafin sarki
Sailur ya sake budar baki yace da Ruhaisu wani
abu
sai Ruhaisu yayi wuf ya goyashi a bayansa ya
falfala
da azababben gudu izuwa hanyar dazata kaisu
cikin
gari.Nanfa ya rinka yin wani irin gudu na ban
al'ajabi
yana gifta bishiyoyi tamkar giftawar tauraruwa
mai
wutsiya.Cikin kankanin lokaci suka iso cikin gari
suka karasa fada,tun a kofar gidan sarautar
Ruhaisu
ya kwallawa likitan sarki Sailur kira don haka
kafin
su karasa turakar sarki sailur tuni anje an kirawo
likitan ya karaso da gudu izuwa cikin
turakar.Nandai
Likitan ya shiga aikinsa ya baiwa sarki sailur
wadansu magunguna wajen kala uku yasha kuma
ya
shafa wani maganin akan rauninsa.Faruwar
hakan
keda wuya sai barci ya sace sarki.Saida sarki
Sailur
ya shafe sati uku a kwance yana jinyar wannan
rauni
na gadon bayansa sannan ya warke
sumul,tamkar
bai taba samun wani rauni ba ma.Sa'ar dayayi
itace
saran da akayi masa bai taba kashi ba,tsokar
nama
ce kawai ta dare.Wannan shine takaitaccen
tarihin
Barde Ruhaisu.
¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤
BAYAN SARKI SAILUR da Barde Ruhaisu sun dan
jima a tsaye rungume da junansu suna kuka sai
sarki sailur ya janye jikinsa daga cikin na Ruhaisu
ya
dubeshi a nutse yace,yakai dana kayi sani cewa
ba
komai nake so kayi mini ba face ka yiwa
surukata
Yazarina rakiya izuwa tafiya neman mijinta
dan'uwanka Yarima Lubainu.Ka sani cewa tuni
mun
gama shirya komai ni da mahaifinta Abu Yazarina
saboda haka a cikin wannan dare nake so kayi
wannan tafiya kuma zan hada ka da wadansu
amintattun zakwakuran dakaru nawa kamar
mutum
dari kacal wadanda zasu taimaka maka.Ina son
kuyi
bad-da-kama a cikin daren yau zaku bar garin
nan
domin a samu cikakken sirri.Koda Sarki Sailur
yazo
nan a zancensa sai farinciki ya lullube barde
Ruhaisu ya dubi sarki sailur fuskarsa cike da
annuri
yace,yakai Abbana kayi sani cewa a iya tsawon
rayuwata ban taba jin farin ciki ba a raina irin na
yau
saboda yaune ranar farko daka taba neman wata
alfarma a wajena.Tun daga kuruciyata kawo
izuwa
girmana bantaba saka maka ba da abin alherin
daka
ke yi mini tsawon shekaru,amma yau gashi ka
bani
damar dazan iya kwatantawa.Na rantse da
darajar
kauna da soyayyar dake tsakaninmu dakai zan
sallama rayuwata don kare ta surukarka,kuma
duk
inda dan'uwa na Yarima Lubainu yake a cikin
duniya
sai na damka Yazarina a hannunsa cikin koshin
lafiya kuma a raye.Koda jin wannan batu sai farin
ciki ya sake baibaye sarki sailur ya rungume
barde
Ruhaisu a karo na biyu yace,ina alfahari dakai
yakai
yayan Lubainu,kuma nasan cewa saika cika
wannan
aiki dana baka bisa amana.Ni yanzu babbar
masifar
dazan fuskanta itace ta kewarka a yayin daka yi
wannan tafiya.Ka tuna cewa tun daga ranar dana
daukoka a gidan sarautar Birnin Darnis kawo
izuwa
yau bamu taba rabuwa daidai da rana daya
ba,yanzu
gashi zakayi wannan tafiya mai mugun hadari
wacce
bansan ranar dawowarka ba.Koda sarki sailur
yazo
nan a zancensa sai ya sake kankame barde
Ruhaisu
a kirjinsa ya fashe da matsanancin
kuka.Al'amarin
daya karya zuciyar barde Ruhaisu kenan,shima ya
fara yin sabon kukan.Tabbas irin son da sarki
Sailur
yake yiwa Barde Ruhaisu har yafi wanda yake
yiwa
Yarima Lubainu duk da ya san cewa barde
Ruhaisu
ba dansa bane na cikinsa,'da ne na TSUNTUWA
wanda ma baisan asalinsa ba.Tsananun tausayin
barde Ruhaisu da yakeyi be yasa yake kaunarsa
fiye
da Yarima Lubainu.Sarki Sailur bai taba fifitashi
ba
kan Ruhaisu,kuma kowanne taro sarki zai tura
wakilci bai taba tura Yarima Lubainu ba saidai ya
tura barde Ruhaisu.Kai saida takai cewa Yarima
Lubainu ya fara
nuna kishinsa a fili akan Barde Ruhaisu saboda
ganin yadda sarki ke fifitashi akansa.Daga ranar
da
sarki sailur ya baiwa Yarima Lubainu labarin
haduwarsu tun yana dan shekara goma kawo
izuwa
girmansa shike nan sai Yarima Lubainu ya
kaunaci
barde Ruhaisu fiye da yadda ma sarki ke
sonsa,kuma suka zamo manyan abokai yan'uwa
kuma aminan da basa son rabuwa.A ranar da
Yarima Lubainu zaiyi wannan tafiya saida suka
shafe
rabin sa'a cif a tsaye rungume da junansu suna
kuka na bakin cikin rabuwa,da kyar suka saki
juna
Yarima Lubainu ya tafi,domin a cikin zukatansu ji
suke kamar dama can sun kasance yan'uwan
juna
na jini.Bayan bardw Ruhaisu da sarki Sailur sun
dan
sake jimawa a kankame da juna sai Ruhaisu ya
janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna
yana mai share hawayensa yace,yakai Abbana
kayi
sani cewa akwai bukatar naje na kammala
dukkan
shirye shiryena yanzu tunda bani da isasshen
lokaci
kuma nayi bankwana da matata.Sarki sailur ya
gyada kai a lokacin da hawaye ya subuto masa
yace
wannan gaskiya ne,kuma ka nema mini gafara a
wajen surukata matar taka tunda na rabata dakai
a
lokacin datafi koyaushe kewarka.Na sani cewa
bata
da burin dayafi ta haihu kana nan ku raini abinda
kuka haifa tare domin babu takaicin dayafi na
rabuwa da IYAYE tun mutum yana karami.Gashi
kai
ka rabu da iyayenka a lokacin ma baka sansu
ba,amma na sani kuma naji a jikina cewa tarihi
bazai maimaita kansa akanka ba,lallai kai zaka
dawo
gida a raye cikin koshin lafiya tun kafin 'danka ko
'yarka tayi wayo.Koda jin haka sai fuskar Barde
Ruhaisu ta fadada da murmushi ya yiwa sarki
Sailur
godiya sannan ya juya da sauri ya fice daga cikin
turakar ba tare daya yarda ya sake waigowa
ba.Take
Barde Ruhaisu ya nufi izuwa gidansa.
2 mins · PublicALLON SIHIRI
Littafi na Hudu (4)
Part D
DA ISAR BARDE RUHAISU gidansa sai ya iske
matarsa ZASMIN tsaye a falo dauke da tsohon
juna
biyu tana kai kawo cikin alamun damuwa.koda ta
hango shigowar Barde Ruhaisu sai ta taho
gareshi
fuskarsa cike da annuri suka rungume,amma
yayin
data janye jikinta daga nasa taga idanunsa sunyi
jajir alamar cewa yasha kuka sai zuciyarta ta
buga
da karfi ta dubeshi cikin alamun tsananin tashi
hankali tace,gaya min gaskiya yakai mijina yau
kuma menene ya faru a fada?Lallai ba ka taba
dawowa gida a cikin irin wannan yanayin ba.Shin
wani makusancinka ne ya mutu ko kuwa wani
abu
ne ya sami sarki?Tabbas yadda na sanka da
DAKAKKIYAR ZUCIYA in ba wadannan abubuwa
ba
babu abinda zai saka kuka.Koda jin wannan
tambaya
sai Barde Ruhaisu ya suri Zasmin ya dagata
sama
yana mai rungumeta a kirjinsa yayi juyi da ita don
haka bata san sa'adda ta kama kyalkyala dariya
ba.A hankali Ruhaisu yaje ya shimfide Zasmin
akan
gado ya kama wasa da gashin kanta suna kallon
juna cikin murmushi.A sannan ne ya kwashe
labarin
dukkan abinda ya faru tsakaninsa da sarki Sailur
ya
zayyane mata.Koda gama bata wannan labari sai
yaga ta kyalkyale da dariya,amma kuma hawaye
na
zuba a cikin idanunta.Al'amarin dayai matukar
bashi
mamaki kenan kuma ya kadu,cikin mamaki
yace,yake matata ina dalilin wannan dariya taki
gami
da kuka a lokaci guda.?Sa'adda Zasmin taji
wannan
tambaya sai ta nutsu ta dubeshi da kyau tace,ya
kai
mijina abin begena dare da rana,kayi sani cewa
ba
komai ne ya sakani wannan kuka ba face yau ne
ranar farko da zan fara rabuwa dakai tun daga
lokacin aurenmu.Alhinin rabuwar tamu ne kawai
ya
sakani kuka,amma ina ji a jikina cewa tabbas
zaka
dawo gareni.Abinda ya sani nake yin wannan
dariya
kuwa ba komai bane face tsananin tayaka
farincikin
samun damar dazaka iya sakawa sarki kadan
daga
cikin irin abubuwan alherin dayayi maka.Kash!In
badon ina dauke da wannan TSOHON CIKI ba da
lallai tare dani za'ayi wannan tafiya,sabida inason
na
haife maka danka a lokacin da kake cikin
GWAGWARMAYA ko shima dan naka ya sami
tabarraki irin naka.Koda Zasmin tazo nan a
jawabinta sai farin ciki ya lullube Ruhaisu ya
rungumeta ya kama sumbatarta yana sa mata
albarka.Nan take Zasmin ta mike tsaye da kanta
ta
fara debo kayan Ruhaisu tana zuba su cikin jakar
guzuri don kammala shirye shiryen
tafiya.Al'amarin
daya kara bashi mamaki kenan,kuma yaji ya
kamu
da tsananin sonta fiye da koyaushe.Cikin
kankanin
lokaci ta gama shirya masa dukkan kayansa
sannan
suka yi bankwana ya saba jakarsa a kafadarsa
bayan
yayi shigar bad-da-kama irin ta fatake sannan ya
koma can kofar gidan sarautar.A wannan lokaco
tuni
Sarki Sailur ya gama shirya komai,domin a samu
cikakken shiri dangane da wannan tafiya Tasu
Ruhaisu saida aka sauya masu gadin kafor gidan
sarautar gaba daya a cikin daren aka zuba
wadanda
ya tabbatar da cewa masoyansa ne na gani
kasheni,kuma ya gargadesu akan cewa duk
abinda
suka gani ko sukaji a wannan dare su barshi a
cikin
zukatansu kada su kuskura su sanar da wani.D
isowar Barde Ruhaisu bakin kofar gidan sarautar
sai
ya iske sarki Sailur tsaye a gaban wadansu
dakaru
guda dari suna bisa kan dawakai dauke da hajoji
da
makaman yaki alamar cewa su fatake ne.Tun
daga
nesa Barde Ruhaisu ya fara nazarin fuskokin
wadannan dakaru,koda ya shaidasu sai ya kamu
da
tsananin farinciki da mamaki.Ba komai ne ya
haddasa hakan ba face ganin cewa gaba daya
sa'anninsa ne kuma manyan abokansa wadanda
ya
aminta dasu a cikin dakarun yakin kasar.Koda
sarki
Sailur ya hango tahowar Barde Ruhaisu sai ya
tafi
gareshi cikin murna yace,yakai dana an gama
shirin
komai dama kai kadai ake jira saboda haka sai
kayi
haramar tafiya.Koda jin haka sai Ruhaisu ya
kama
hannayen sarki guda biyu ya sumbacesu kawai
sai
ya sake rungume junansu suka dan jima a
kankame
da juna.Al'amarin daya karya zukatan sauran
dakarin
kenan suka kamu da tausayinsu saboda sunsan
irin
shakuwar dake tsakaninsu.Nandai Barde Ruhaisu
da
Sarki Sailur suka rabu bisa dole sunayin kwallah
badon suna so ba,aka kawowa Barde Ruhaisu
wani
farin INGARMAN DOKI wanda ya fita dabam da
dukkan dawakan abokan nasa ya kama ya
hau.Take
ya kada linzamin dokinsa ya fice daga cikin
gidan
sarautar ba tare daya yarda ya sake waigowa
ba.Ai
kuwa sai sauran dakarun guda dari suka rufa
masa
baya da sauri shi kuwa sarki Sailur sai ya bisu da
kallo kawai,bai bar wajen ba har saida suka kule
ya
zamana cewa ko kurarsu baya iya
hangowa,sannan
ya juya ya koma izuwa cikin gidan sarautar yana
mai
zubar da hawaye.
¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤
A CAN BIRNIN Sarki Alkasu kuwa tun da aka
gama
wannan gasa ta neman Auren YAZARINA
tsakanin
YARIMA LUBAINU da YARIMA MANGUL suka
dawo
gida sai sarki Alkas ya sanya hijabi tsakaninsa da
Yarima Mangul.Suna dawowa gida yayi masa
korar
kare daga fada kuma ya gaya masa cewa idan ya
sake sa kafarsa a cikin harabar gidan sarautarsa
zai
yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan
kurkuku.Koda jin wannan batu sai mamaki da
bakin
ciki ya turnuke Yarima Mangul ya dubi dungulmin
hannunsa a lokacin da hawaye yake zubo masa
sannan ya dubi Sarki Alkas yace saboda mezaka
kyamaceni alokacin dana fi bukatarka?Ka dubi
yadda
na zamo musaki ka tuna cewa nine fa kadai
danka
guda wanda zai gaji karagarka?Ka tuno da irin
tsananin son daka keyi min saboda me yau zaka
bari zuciyarka ta rinjayi soyayyar danka?Kafin
Yarima Mangul ya gama rufe bakinsa tuni sarki
Alkas ya daka masa tsawa a lokacin da shima
hawaye ya zubo masa ya dubeshi yace,karka
sake
kirana da matsayin ubanka domin tuni nasaka
TAKOBI na datse wannan
alaka dake tsakaninmu kamar yadda ka datse
wacce
ke tsakanina da Abokaina kuma manyan
masoyana
sarki Sailur da Attajiri Abu Yazarina.Ka sani cewa
ka
jefa wadannan masoya nawa a cikin bakin cikin
da
har abada babu abinda zai gusar dashi tunda ka
rana Yarima Lubainu da lafiyarsa ka sanya masa
cutar da bata da magani kuma a sanadiyyar
hakan
yayi rabuwar doke da masoyiyar tasa rabuwar da
ba
lallai bane su sake saduwa ba.Kaga keknan ka
raba
iyaye da 'ya'yansu kuma ka raba MASOYA.Ka
sain
cewa a yau idan na rasaka a gobe daya daga
cikin
matana zata iya sake haifa mini wani dan,amma
aminaina daka rabamu dasu bazan taba samu
kamarsu ba.Yarima ka cuceni cutar da har abada
ba
zan iya yafe maka ba.Koda jin wannan batu sai
Yarima Mangul ya zube kasa a gaban sarki Alkas
ya
fashe da kuka kuma ya kama tuba yana rokon
gafara.Maimakon sarki Alkas yaji tausayinsa sai
ya
dubi wadansu dakarunsa su shida dake tsaye a
gefe
daya yace dasu su kama Yarima Mangul su fitar
dashi daga cikin gidan sarautar kuma a kulle
kofar
gidan.Nan take kuwa dakarun suka kama Yarima
Mangul Suka fitar dashi daga cikin gidan
Sarautar da
karfin tsiya yana kuka da ihu gami da turjewa
kuma
yana kwallawa sarki Alkas kira mma sarki Alkas
ko
waigowa baiyi ba bare ya dubesi ya tausaya
masa.Ana fitowa da Yarima Mangul daga cikin
gidan
sarautar sai akayi wurgi dashi a wulakance
tamkar
bai kasance dan sarki ba,aka janyo kofar gidan
sarautar aka kulleta bam,aka zuba mata
sakatu.Cikin
tsananin bakin ciki da takaici Yarima Mangul ya
mike tsaye yana kuma.Nan taje yaji ya tsani
sarki
Alkas yadda ya tsani mutuwarsa.Kawai sai ya
takarkare ya bushe da dariyar mugunta iska ta
dauki
sautin dariyarsa takai har izuwa kunnen sarki
Alkas
gami da muryarsa yana mai cewa yakai Abbana
ka
saurari ranar da zan dawo gidan nan nine zan
zama
sanadin AJALINKA kuma saina hau kan
KARAGARKA.Koda jin wannan batu sai bakin ciki
ya
turnuke sarki Alkas zuciyarsa ta kama
tafarfasa.Har
ya zare takobinsa da nufin ya juya da baya da
gudu
yaje ya kashe Yarima Mangul sai zuciyarsa ta
daka
masa tsawa tace dashi so kake kabarwa kanka
abin
gori a wannan masarauta?Ka kyale Yarima da
Halinsa ai duniya makarantace zata koya masa
darasi.Daga wannan rana Yarima Mangul ya bar
cikin birninsu gaba daya ya koma daji da zama
saboda bakin ciki.A sanadinyyar haka ne ya hada
kai da 'yan TAWAYE gami da 'YAN FASHI suka
fara
shirye shiryen yadda zasu kawar da mulkin sarki
Alkas ya dane KARAGAR MULKINSA,amma
kullum
idan ya dubi iya yawansu da iyakar makaman
dasuka tanada sai takaici ya kamashi saboda
yasan
cewa ko kasa daya cikin kaso goma na shirin
sarki
Alkas basu kai ba don haka dole ne ya cigaba da
hakurin jiran lokaci.A haka dai Yarima Mangul ya
cigaba da jagorantar wannan runduna ta yan
fashi da
tawaye suka rinka kai harin SUMAME izuwa
kauyukan dake sauran kasashen ketare suna
kwaso
mata,dukiya da kudi suna kamo bayi da karfin
tsiya
suna basu horon yaki domin kara yawan
dakarunsu
kuma suna siyan mugayen makaman yaki suna
tarasu.Ana cikin wannan hali ne wata rana
Yarima
Mangul na zaune a cikin sansaninsu yana shan
giya
ga mata a gabansa suna ta fama tika rawa anayi
musu kida saiga wani DAN LEKEN ASIRINSA ya
rugo
da gudu bisa kan doki.Da isowarsa kusa da
Yarima
Mangul sai ya tsaida dokinsa ya sauko kasa ya
fadi
a gaban Yarima Mangul yace ya shugabana ga
wani
AYARI can na BAKIN FATAKE kimanin su dari da
doriya dauke da HAJAH mai tarin yawan gaske
sun
nufi hanyar dazata kaisu Birnin SARAUNIYA
AKISATUL SAUWARA.Koda jin wannan batu sai
Yarima Mangul yayi jifa da kwalbar giyar dake
hannunsa ya mike tsaye zumbur cikin tsananin
farin
ciki yace,tabbas yau zamuyi babbar farauta mai
inganci.Maza a kawo mini dokina da kayan
yakina.Dakaru dubu daya kacal nakeson suyi min
rakiya.Nan take kuwa cikin gaggawa aka kawowa
Yarima Mangul kayan yakinsa ya sanya sannan
ya
hau dokinsa ya zabureshi da gudu dakaru dubu
suka rufa masa baya."Ashe wannan AYARI na
fatake
ba wasu bane face su Barde Ruhaisu wadanda
suka
fito neman Yarima Lubainu a cikin shiga ta bad-
da-
kama domin a sada Yazarina da Mijinta Yarima
Lubainu.
kuyi hakuri yau Ansamu delay din post hakan
yafarune sbd bansamu time bahALLON SIHIRI
Littafi na Hudu (4)
Part E
TUNDA WANNAN Ayari nasu Barde Ruhaisu suka
baro birnin Zamrul sukayi ta ratsa
dazuzzuka,kauyaka da kananan Birane basu
fuskanci
matsalar komai ba har tsawon kwana tara.Kuma
a
duk tsawon wadannnan kwanaki Barde Ruhaisu
bai
taba yarda ya gusa ba daga kusa da Yazarina ba
wacce koyaushe fukskarta a rufe take cikin
mayafi
idanunta kadai ake gani,kuma shigar datayi
mutum
bazai iya gane cewa ba macece ko namiji.Ko
dare
ne yayi har tayi bacci Barde Ruhaisu yana tsaye
a
kusa da ita kuma ya saka Dakaru sun kewaye
yankin
wajen da take.Kai ko wani kyakkyawan motsi
yaji a
kusa da wajen da suke sai ya duba ya tabbatar
da
cewar babu abu wanda zai kawo mata
barazana.A
tsawon wadannan kwanaki da suka shafe suna
tafiya
ko sannu babu wanda ya yiwa wania tsakanin
Barde
Ruhaisu da Yazarina ma'ana basuyi magana da
junansu ba.A ranar kwana na taran ne da
yammaci
sakaliya suka yada zango a bakin wata korama
domin su dan huta kuma dawakansu su sha
ruwa.Bayan an tsaya kowa ya sauka daga kan
Dokinsa,dakaru sun kewaye wajen don tabbatar
da
tsaro,Yazarina ta zauna a gefe daya ta bude
jakar
guzurinta ta dauko nama yana ci,shi kuma barde
Ruhaisu yana tsaye a bayanta ya zare takobinsa
yana wasata akan dutse sai kawai suka jiyo
sukuwar
dawakaia daga yamma,gabas,kudu da
Arewa.Sannan
kuma sai suka jiyo kururuwar mazaje mai ban
tsoro
amma saboda su Ruhaisu sun kasance ZARATAN
JARUMAI masu dakakkiyar zuciya ko gezau
basuyi
ba,kawai sai sukayi sauri suka zaro wadansu
manyan garkuwoyi daga kan dawakansu saboda
tsoron kada a fara kawo musu hari da harbin
kibiya.Take kowannen badakare yacake
garkuwarsa
a gabansa sannan ya zare takobinsa,kowa ya
tsaya
a inda yake ba tare da wata razana ba.Yazarina
ce
kadai ta firgita a lokacin data hango wadansu
dakarun sumame su da yawa sun durfafosu a
guje
bisa dawakai rike da makamai tsirara suna ihu da
kururuwa.Har ta yunkura zata mike tsaye a
dimauce
sai Barde Ruhaisu yayi wuf ya kamo hannunta ya
zaunar da ita kasa.A karon farko ya dubeta
yace,ki
gafarceni ya shugabata idan kika matsa daga
nan
koda taku daya ne halaka zakiyi.Abinda nakeso
dake
shine komai RINTSI DA TSANANI kada ki gusa
daga
kusa dani,koda kuwa kinga an karar da dukkan
dakaruna saura ni kadai jal na rage a raye!Lallai
ki
kiyaye wannan umarni dana baki muuddin kina
son
ki sake saduwa da masoyinki dan'uwana Yarima
Lubainu.Koda Yazarina taji wannan batu sai ta
gyada
kai tana nuna masa alamun cewa lallai zata
kiyaye
wannan umarni nasa.Koda jin haka sai Ruhaisu
yai
sauri ya rufe fuskarsa da rawani suma sauan
dakarun nasa sai sukayi koyi dashi.Abinda ya
daurewa Ruhaisu kai shine har dakarun sumamen
suka iso daf dasu ya zamana cewa tazarar dake
tsakaninsu bata wuce taku ashirin ba amma basu
harbo musu kibiyoyi ba.Da isowar dakarun
sumamen sai sukayiwa su Ruhaisu KAWANYA
suka
yi cirko cirko bisa dawakansu.A sannan ne
shugaban dakarun sumamen wanda dashi da
dukkan yaran nasa sun rufe fuskokinsu sai ya
sauko
daga kan dokin sa ya karewa fataken kallo
tsaf,sannan ya bushe da dariyar mugunta,lokaci
guda kuma ya turbune fuskarsa ya dubesu
yace,ni
da yarana mu dubu daya ne da daya,ku kuwa
bakufi
ku dari ba,abin kunya ne mu yakeku ta hanyar
farar
harbo muku kibiyoyi.To waishin kuma menene
amfanin rufe fuskokinmu damu daku mukayi?Ai
kawai kowa ya bude fuskarsa muyi GABA DA
GABA
fada da buya ai tsoro ne.Koda gama fadin hakan
sai
shugaban dakarun sumamen ya kwaye rawanin
dake
kan fuskarsa su Barde Ruhaisu sukayi arba
dashi.Ba
wani bane face Yarima Mangul dan sarki Alkas!!!
Hannunsa na dama na rike da zabgegiyar
takobi,ya
saki daya dungumin hannun nasa.Koda Barde
Ruhaisu yayi arba da Yarima Mangul sai shida
dukkan dakarunsa suka kamu da tsananin
mamaki
gami da tsananin tsoro.Koda ganin haka sai
barde
Ruhaisu ya kwaye fuskarsa shima ya mike ya
matso
gaba kadan ya dubi Yarima Mangul yace,sau tari
Jarumi yakan rufe fuskarsa saboda wata
BABBAR
HUJJA da manufa saboda haka mu bazamu bude
fuskokinmu ba saidai mu gwabza daku a
hakan.Kafin sannan kuma muna son mu san
dalilin
dayasa kuka kawo mana wannan hari na
MAMAYAR
BAZATO.Koda jin wannan batu sai Yarima
Mangul ya
bushe da dariyar mugunta sannan yace,ai shi dan
fashi bashi da wata hujja takai hari face don ya
kashe rayuka kuma ya kwashe dukiya.Koda yake
nasan ka san ko ni waye tunda ni fitacce ne a
wannan nahiya kuma ada ni ba dan fashi
bane,amma
a yanzu ni UNGULU ne dakan ZABO!Har yanzu
ina
nan akan matsayina na Yarima Mangul dan Sarki
Alkas mai jiran Gado.Yakai wannan jarumi ka
sani
cewa zan iya yi muku adalci guda daya kai da
dukkan jama'arka naki kasheku na karbe
dukiyarku,amma sai idan zaku bude fuskokinku
naga
ko ku su waye?Koda jin wannan batu sai Barde
Ruhaisu ya tari numfashin Yarima Mangul yana
mai
daka masa tsawa yace,ba zamu taba bude
fuskokinmu ba don cika umarninka kuma kaidin
nan
baka isa ka iya kashemu ba ko ka karbe
dukiyarmu.Ina mai shawartarka daka janye
jama'arka
ku bar wannan wuri idan ba haka ba kuwa sai
kayi
nadamar kawo mana wannan hari.Idan ka
kuskura
ma sai na sake guntule maka daya lafiyayyan
hannun naka!!Koda jin wannan batu sai Yarima
Mangul ya fusata ainun ya zare takobinsa kuma
ya
daka tsalle daga inda yake ya dira a gaban Barde
Ruhaisu ya kawo masa wawan sara aka.Cikin
bakin
zafin nama barde Ruhaisu ya kare saran.Nanfa
suka
ruguntsume da azababben yaki,ya zamana cewa
suna kaiwa Junansu SARA DA SUKA cikin
tsananin
bakin zafin nama,juriya da bajinta,sauran dakarun
kuwa na kowanne bangare sai suka zuba ido
suka
zama yan kallo tunda ba'a basu umarnin suyi yaki
ba.
WAYE ZAI SAMU NASARA A WANNAN
AZABABBEN
YAKI DA AKE KWABSAWA TSAKANIN YARIMA
MANGUL DA BARDE RUHAISU?
INA LABARIN YARIMA LUBAINU DA BAKON
JARUMI
DASU SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA DAKE
CIKIN
GIDAN BOKA DARBUSA?
SHIN YARIMA LUBAINU ZAI CIKAWA ALJANA
BADI'ATUL SARIRA ALKAWARIN DAYA DAUKAR
MATA NA KWANCETA DAGA DAURIN DA BOKA
DARBUSA YAYI MATA ITA KUMA TA TAIMAKA
MASA?
WANE NE BAKON JARUMI DA TARIHINSA?
YAUSHE BAKON JARUMIN ZAI SAMU NASARAR
YADA ADDININSA NA MUSULUNCI A NAHIYAR?
SHIN YARIMA LUBAINU YANA SAMU LAFIYA
DAGA
LALURAR DA YAKE CIKI?
YAUSHE YAZARINA ZATA SADU DA MASOYINTA
YARIMA LUBAINU?
WAYE ZAI MALLAKI ALLON SIHIRI A TSAKANIN
DUMBIN JAMA'AR DA SUKE NEMANSA?
WANE IRIN MUGUN TANADI SU SARAUNIYA
AKISATUL SAUWARA ZASU YIWA BAKON
JARUMI?.
Mu hadu a littafin ALLON SIHIRI littafi na Biyar
(ALLON SIHIRI-5)don jin cigaban wannan
kayataccen,kasaitaccen labari.
1 hr · PublicTARWATSA MAZA-1 TYPE E »««
Nidai a iya yawon da nayi bantaba shiga daji
mai kwarjini da ban tsoro ba, tamkar dajin
shajaril maurud. Ba komai ne yabawa dajin
kwarjiniba, face wasu irin dogayen bishi yoyi
gami da

1 Comments On ALLON SIHIRI 1 TO 9
avatar
abdulazeez

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment