Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin ka baro gida.Cin amana
ne
idan ka dauki wannan Allon Sihiri,Amana,cika
alkawari da fadin gaskiya sune guzurin da
mahaifinka ya baka,kuma idan har ka koyayesu
zaka
sami nasarar abinda ka fito nema.Koda gama
aiyana
hakan sai ya juya ya fice daga cikin tantin.Yana
fitowa ya dubi gabasa da yamma,kudu da arewa
amma bai hango Akisatul Sauwara na kuma baiji
motsin taba.Al'amarin d yayi matukar bashi
mamaki
kenan domin baiga dalilin dazai sa tayi
gangancin
barin Allon Sihirin ta ba a fili haka.Nan dai
Yarima
Lubainu ya nufi gabar wannan korama yaje ya
wanke
fuskarsa ya kuskure bakinsa.Ashe duk wannan
abu
dake faruwa Sarauniya Akisatul Sauwara na labe
a
cikin wata duhuwa kuma tana kallon duk abinda
Yarima Lubainu keyi.Ta buya ne domin ta jarraba
amanarsa ta gani shin zai iya rike amanar.A jiya
da
daddare ta jarraba hakurinsa kuma ya haye
jarrabar
tunda har gari ya waye bai kusanceta ba duk da
cewa ya dimauce da ganin tsananin kyawun
siffarta
kuma ya kamu da matukar sha'awarta.Bisa
mamaki
sai sarauniya Akisatul Sauwara taga cewar
Yarima
Lubainu bai dauke Allonta na sihiri ba yayi
kokarin
guduwa.Maimakon hakan ma sai taga cewar
hankalinsa ya tashi bisa rashin ganinta domin
sa'adda ya wanke fuskarsa da bakinsa a cikin
wannan korama sai ya kasa komawa cikin tantin
ya
rinka kai kawo a harabar wajen yana leke leke a
kowacce kusurwa yana kwalla mata kira amma
yaji
bata amsa ba.Al'amarin dayai matukar
dugunzuma
hankalinsa kenan domin yana tsoro kada ya tafi
nemanta kuma azo a sace wannan Allon
Sihirin.Kuma yana tsoron kada ya dauki Allon
Sihirin
zargi ya shiga tsakaninsa da Sarauniya Akisatul
Sauwara.Lokacin da Akisatul Sauwara taga halin
da
Yarima Lubainu ya shiga sai tayi murmushi ta
juya
da baya ta nausa cikin daji.Sai da taje tayi
farauta ta
harbo wani tsuntsu sannan ta dawo.Tana isowa
bakin tantin ta iske shi a zaune yayi tagumi cikin
alamun tsananin damuwa.Koda ya hangota saiya
mike zumbur!da sauri ya tareta yana mai cewa
haba
ranki ya dade yaya zaki tafii cikin daji batare da
kin
sanar daniba.ALLON SIHIRI
Littafi na daya(2)
Part D
Koda ya hangota sai ya mike zumbur!
Da sauri ya
tareta yana mai cewa,haba ranki ya dade,yaa
zaki
tafi cikin daji ba tare da kin sanar dani ba?
Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Akisatul
Sauwara tayi
murmushi tace,komai akwai dalilin faruwarsa.Ka
bari
mu nutsu tukunna zan yi maka bayanin komai a
saukake.
Nan take Akisatul Sauwara ta dora ruwa a
tukunya ta kunna wuta.A takaice dai ta fara
kokarin
fisge wannan tsunstu data harbo.
Koda Lubainu yayi yunkurin taimaka mata sai ta
ki don haka sai
ya
zuba mata idanu har izuwa lokacin data kammala
gasa tsunsun sannan tayi masa tayi suka zauna
suka kama cin nama tsuntsun.
Tsawon yandakiku
suna cin naman dayansu baice uffan ba a lokacin
da
dajin yayi tsit ba a jin sautin komai face na iskar
dake kadawa.
Kawai sai Lubainu ya katse shirun ya
dubeta yace,yake wannan sarauniya mai
daraja,idan
baza ki damu ba inason ki gaya min dalilin
dayasa
kike sakin jiki dani a cikin wannan tafiya alhalin
ban
kasance muharraminki ba ko kuma amintaccenki?
Koda jin wannan batu sai sarauniya Akisatul
Sauwara ta
kyalkyale da daria sannan tace,tabbas
kayi mini tambayoyi masu amfani kuma dama ai
nayi alqawarin baka amsoshinsu a yanzu dana
sami
nutsuwa.
Da farko dai dalilin dayasa na yarda muka
kwana tare a cikin daki ina so ne na jarraba
hakurinka shin zaka kasance mai tsare
mutuncina bisa
alqawarin dake tsakaninmu na taimakon juna a
cikin wannan tafiya?
Tabbas ka kiyaye wannan
jarrabawa ka hayeta.
Dalili na biyu kuma wanda yasa
na tafi na barka a cikin tanti kana barci shine
domin
na jarraba amanarka na gani shin zaka sace
Allon
Sihiri na ne ka gudu?
Sai gashi kayi matukar bani mamaki tunda baka
sace Allon
Sihirin ba alhalin
kuma gashi na fito dashi fili karara daga cikin
kwalbar da babu wani mahaluki daya isa ya fiddo
shi.
Tabbas ka cika mutum mai amana yanzu abu
daya ya rage nayi maka jarraba akansa,kuma da
sannu zamu kai ga wannan matsayi.
Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a
zancenta sai
Yarima
Lubainu yayi shiru kawai yana mai kura mata
idanu.
Daga can kuma sai ya mike tsaye ya shiga
cikin tantin ya shiga cikin tantin ya shiga hada
kayayyakinsa yana zuba su acikin jakar
guzurinsa.
Itama Sarauniya Akisatul Sauwara ta mike tsaye
ta bishi izuwa
cikin tantin ta shiga
kimtsa na ta kayan.
Har suka gama kimtsa komai
basuce da junansu kala ba.
Nan take suka hau
dawakansu suka nausa cikin daji suna masu
cigaba
da tafiya.Sai da suka shafe sa'a hudu da rabi
suna
tafiya ba tare da sun yada zango ba sannan
Yarima Lubainu ya
matso kusa da Sarauniya Akisatul
Sauwara,da yake dama itace akan gaba tana yi
musu jagora a cikin tafiyar ya dubeta
yace,waishin
tafiyar kwana nawa zamuyi ne mu riski Birnin da
muka nufa?
Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya
Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,ni kuwa
dadina dakai
kenan ka cika zumudi da gaggawa.
Ai idan
kayi
hakuri idanunka zasu nuna maka.Koda gama
fadin
hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi shiru
bata
kara cewa uffan ba har suka sake shafe sa'a
hudu
suna tafiya.
A sannan ne dare ya riskesu suka yada zango a
bakin wani
katon dutse.
Anan suka kwana
washe gari suka sake yin shiri suka ci gaba da
tafiya.Saida suka shafe kwana bakwai cur basu
riski
wani gari ba kuma basu hadu da wani mugun
abu
ba,kawai dai suna ratsawa ne ta cikin mugayen
dazuzzuka.Duk inda suka hadu da wadansu
mugayen dabbobi
ko kwaruka saidai kaga sun yi
musu kwaf! daya.Kai ko mugayen Aljanu ne suka
hadu dasu saidai kaga Aljanun sun gudu sunyi ta
kansu don sun san cewa WUTSIYAR RAKUMI
TAYI
NESA DA KASA! Kuma RUWA BA SA'AN
KWANDO
BANE.
A ranar kwana na bakwai ne da rana tsaka
Yarima Lubainu ya
hango wani babban gari a
gabansu wanda kawatuwarsa ta ninka ta birnin
Rauhul Bagadar sau uku wato birnin sarauniya
Akisatul Sauwara.Tun daga nesa Yarima Lubainu
ya
wangame baki kamar dan kauye yana kallon gine
ginen birnin cikin al'ajabi.Koda Sarauniya Akisatul
sauwara ta
lura da halin da yake ciki sai ta bushe da
dariya tace,haba ya kai Lubainu kada ka bani
kunya
mana,ai baka ga komai ba ma sai mun shiga
cikin
birnin tukunna.
Koda jin wannan Batu sai Yarima
Lubainu ya sake cika da mamaki yace,waishin
yanzu
kina nufin wannan birnin da zamu shiga shine
Birnin Kimras
inda sarki Darmanu yake mulki inda zamu
samu barin Allon Sihiri na biyu?Akisatul Sauwara
ta
jinjina kai tace kwarai kuwa amma abinda nakeso
dakai shine ka nutsu kada kayi komai da kanka
sai
abinda kaga nayi ko wanda na umarce ka dakayi
saboda Sarki Darmanu ba karamin 2shaidanin
Mutum bane.A
yanzu haka maganar nan da mukeyi nasan
yana kallonmu kuma yana jinmu,kuma zai iya yin
wani abu domin ya cutar damu,don bani da
tabbacin
cewar zai bamu hadin ka bisa bukatar da muka
zo
masa da ita.
Tabbas Sarki Darmanu ya fini karfin
Sihirin tsafi,amma fa a bangaren jarumtaka da
iya yaki KARE
JINI BIRI JINI mukeyi.
Sau tara muna
fafatawa ni dashi ba tare da wani yayi nasara a
tsakaninmu ba amma fa muna matukar jin jiki.
Bisa
sa'a ne kawai na samu na tsira daga sharrin
tsafinsa
saboda tsarin dana samu tun daga
kakannina.
Lokacin da Sarauniya Akisatul Sauwara tazo
daidai nan a
zancenta suna daf da shiga cikin
birnin ne,
Kwatsam!sai suka ga wani mutum Tsoho
tukuf ya fito dafa cikin gona goye da kara a
bayansa,shima zai shiga cikin birnin.Cikin Ladabi
Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu
suka
gaishe da tsohon.Kawai sai tsohon ya kare musu
kallo ya lura
cewa baki ne don haka saiya dubesu
yace,yaku wadannann matasa hakika ku baki ne
a
garin nan ko?
Akisatul Sauwara tace,Baba zancenka
dutse ne.Tsohon ya dubi Sarauniya Akisatul
Sauwara cikin yanayi
mai nuna tausayi yace,Yarinya bisa yanayinku da
gani kun fito
daga babban gida kuma kun sami
tarbiya mai kyau,saboda haka zan taimakeku don
kada ku fada cikin tarkon maketacin
sarkinmu.Ina
mai sanar daku cewa bisa al'adar wannan mugun
sarki namu duk bakon daya shigo garin nan
kamashi ake yi a kwace duk abinda ya mallaka a
kaishi
kurkuku a kulle ko kuma ayi masa dukan kawo
wuka sai idan yana da sauran shan ruwa a
duniya
sannan zai tsira da rayuwarsa.
Yanzu zan taimake ku
zna bi daku ta barauniyar hanya inda babu wanda
zai
ganku harmu isa gidana inda zaku kwana,in yaso
indan gari ya
waje sai ku saje da 'yan gari ku
aiwatar da abinda ya kawoku.Tsohon na gama
fadin
hakan kuma sai ya dubi Yarima Lubainu
yace,idan
sarki ya kyallara ido yaga wannan kyakkyawar
'yar
uwar taka saiya rabaka da ita har abada.
Koda jin
haka sai Yarima Lubainu ya gyada kai yana mai
jinjina
al'amarin ba tare da yace kala ba.
Nan dai
tsoho ya wuce gaba suka bishi a baya yana mai
bin
wata barauniyar hanya wacce tabi bayan birnin.
Su kuma suka ci gaba da jan limzamin
dawakansu a
hankali suna yin tafiyar san'da suna waige waige
cikin rashin yarda da kwanciyar hankali.Lokacin
da suka yi 'yar
doguwar tafiya ya zamana cewa tsohon
yana gabansu da tazara ta a kalla taku goma sha
biyar sai Yarima Lubainu ya dubi Sarauniya
Akisatul
Sauwara yayi mata magana cikin karamar murya
yace,nifa ban yarda da wannan tsohon ba,domin
zai
iya zama dan leken asirin Sarki Darmanu ne aka
turoshi ya
yaudare mu ya cutar damu.
Koda jin
wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara taji
zuciyarta ta buga da karfin gaske,take tsoro ya
baibayeta kuma taji ta gamsu da tunanin da
Yarima
Lubainu yayi,don haka sai kawai taja linzamin
dokinta ta tsaya cak!shima Yarima Lubainu sai
ya tsaida nasa
dokin suka kurawa tsohon idanu kawai
yayin da yake ci gaba da tafiya.Koda tsohon yaji
sautin sauwun dawakansu Lubainu ya dauke a
bayansa sai shima ya tsaya cak ya juyo da sauri
cikin alamun mamaki ya dubi su Lubainu yace
'ya'yana lafiya kuwa kuka tsaya a baya haka
kuka daina tafiya?
Caraf sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta
dubi tsohon ta daka masa tsawa tace,kai tsohon
banza!bakin mayaudari na gane ko kai
waye.Maza
ka bayyana surarka ta gaskiya domin mu
tattauna
bisa abinda ya kawomu birninka.Lokacin da
tsohon
yaji wannan batu na sarauniya Akisatul Sauwara
saiya bushe
da mahaukaciyar dariya cikin karfin
murya mai nuna cewa lallai ba muryarsa bace ta
tsoho.Daga can kuma sai yayi girgiza nan take
ya
rikide ya zama sarki Darmanu cikin gagarumar
shigar yaki.
Sarki Darmanu ya kasance katon mutum
mai kirar sadaukai,gashi dogo zankalele kuma
gashi kakkaura
mai murdadden jiki gami da tarin kwanji
da
jijiyoyi.
KALLO DAYA mutum zai masa ya gane cewar
ya cika sadauki mai TARWATSA MAZA.
Wadansu
bakaken kayan yaki ne a jikinsa na karfe.
Rigar dai
Farmaran ce mai budadden hannu,sai dogon
wando da
dogayen takalma duka na bakin karfe.
A hannunsa na hagu kuwa wata katuwar garkuwa
ce
wadda akayi ta da zallan dutsen lu'u lu'u mai
nauyin
gaske wacce sai kato goma sun taru suke iya
rabata
da kasa amma shi ji yake kamar takarda ya
rike.
Bayan anyi kallon kallon na tsawon dakika goma
tsakanin sarki Darmanu dasu sarauniya Akisatul
Sauwara sai Sarki Darmanu ya sake bushewa da
dariyar mugunta karo na biyu sannan ya dubi
sarauniya Akisatul Sauwara yace,ke tsohuwar
abokiyar gaba kiyi sani cewa tun kafin ku baro
birnin ki naga
duk abinda ya faru tsakaninki da
Yarima Lubainu dan sarki Sailur har izuwa
sa'adda
kuka taho izuwa nan birnina domin na baku barin
Allon Sihirin dake hannuna.
Tabbas dake dashi kuma
sami tabin hankali har da kuke tunanin zan
karbeku
hannun bibbiyu na yarda da bukatarku.
Kisa sani cewa na dade ina jiran irin wannan
rana wacce
zakuyi gangancin dauko barin Allon Sihirinki ki
taho
har izuwa birnina domin tuni nayi bincike na
gano
yadda zan iya fidda Allon daga cikin kwalbar
dakika
adanashi.Kin ga kenan yanzu na sami tsuntsu
daga
sama gasasshe tunda kin kawo kanki.Yanzu zan
hallaku na
dauke Allon Sihirin daga jikinki naje na
biya tawa bukatar dashi.
Koda gama fadin hakan sai
Sarki Darmanu yai wuf ya daka tsalle a sama
kamar
an cilloshi daga cikin baka ya kawowa Akisatul
Sauwara da Lubainu mugun sara a sama da duk
su
biyun a lokaci guda.Cikin bakin zafin nama duk
su biyun suka
kaucewa saran suka fado kasa daga kan
dawakansu,ai kuwa sai takobin sarki Darmanu ta
tsarge dawakan biyu tamkar an yanka tsakiyar
tuffa.
Take dawakan suka zube kasa matattu.Cikin
sauri da dimauta su Lubainu suka mike tsaye
zumbur suna masu zare nasu takubban.Sarauniya
Akisatul
Sauwara tayi sauri ta tofawa takobinta da
takobin Lubainu wani dalasimin tsafi sai
takubban
nasu suka kara kaifi,girma da nauyi.Koda ganin
haka
sai Sarki Darmanu ya rugo da gudu izuwa kansu
suka runtsume da azababben Yaki.
Shegen kaya Uban mayaudara Sarki Darmanu.
6 hrs ยท PublicALLON SIHIRI
Littafi na biyu(2)
Part E
Sannan su dauke mu mu ci gaba da tunkarar
gidan
Boka Darbusa.Yanzu ga dawakai nan guda biyu
dana
tanadar muku sai ku hau mu kara gaba.Ba tare
da
gardamar komai ba kuwa Lubainu da sarauniya
Akisatul Sauwara suka hau wadannan dawakai
suka
bi bayan Sarki Darmanu suka fice daga cikin
birnin
gaba daya.Nan dai suka nausa cikin daji suka yi
ta
tafiya ba sassauci har suka shafe sa'a goma sha
biyu ba tare da sun hadu da wani mugun abu
ba.Duk wata muguwar dabba idan ta hangosu
daga
nesa sak kaga ta ratsa ta sauya hanya,haka ma
mugayen aljanu.Yan fashi kuwa da zarar sun
hango
Sarki Darmanu tare dasu Lubainu sai kaga sunyi
ta
kansu saboda sun san cewa Bakin Rijiya ba
wajen
wasan yaro bane.Adaidai wannan lokaci ne
magriba
ta riskesu kuma a sannan ne suka shigo farkon
dajin
da wadannan tsuntsaye na sarki Darmanu
suke.Da
shigarsu cikin dajin sai Sarki Darmanu ya daga
kansa sama yana mai karanta wadansu dalasimai
na
tsafi.Faruwar hakan keda wuya sai Lubainu da
Sarauniya Akisatul Sauwara suka ji wata irin iska
mai karfin daga sama ta fara kadawa.Kwatsam
sai ga
wadansu jibga jibgan tsuntsaye guda uku sun
bayyana suna masu saukowa kasa.Duk su ukun a
gaban sarki Darmanu suka sauka suna masu
dukar
da kawunansu alamar cewa sun kwashi
gaisuwa.Nan
take sarki Darmanu ya shafa kawunan wadannan
tsuntsaye yayi magana dasu a cikin yaren
tsafi.Faruwar hakan ke da wuya sai tsuntsayen
suka
bude fukafukansu suka sake tashi sama suka
luluka
a cikin gajimare har suka bace bat tamkar basu
taba
wanzuwa ba.A sannan ne Sarki Darmanu ya dubi
Yarima Lubainu da Sarauniya Akisatul Sauwara
yace,anan zamu yada zango mu dan huta nan da
cikar kamar sa'a uku wadannan tsuntsaye zasu
dawo su daukemu mu ci gaba da tafiya.Nan take
suka kafa tanti suka fidda abincinsu na guzuri
suka
kama ci suna hira.kafin Yarima Lubainu yayi wani
abu da hannunsa tuni Sarauniya Akisatul
Sauwara ta
miko masa,ya zamana cewa tana kyautata
masa,bata son taga ya yi wani abu na wahala da
kansa face ta taimaka masa.Bayan sun gama cin
abincin ne Akisatul Sauwara ya mike tsaye ta
dubesu tace,tana son ta zagaya bayan wata
katuwar
bishiya dake can gabansu tayi bawali.Tana gama
fadin hakan sai ta juya ta nufi inda wannan
bishiyar
take.Tana isa kuwa ta zagaya bayan bishiyar ta
bace
musu da gani.A wannan lokaci ne Sarki Darmanu
ya
dubi Lubainu cikin murmushi yace,na fuskanci
cewar
Akisatul Sauwara ta kamu da matukar
sonka.Koda
jin haka sai mamaki ya kama Lubainu ya dubeshi
yace,wacce irin magana kake yi haka?Ai wannan
bayani naka daidai yake da tatsuniya a cikin
kunne
na,domin babu yadda za'a yi sarauniya Akisatul
Sauwara ta so ni saboda kwararan dalilai guda
uku.Dalili na farko shine a rayuwarta bata tabayin
soyayya ba don babu wani 'da namiji daya taba
burgeta.Dalili na biyu shine ta san cewa ni ba
cikakken namiji bane,kaga kuwa bazata so ta
auri
wanda baya haihuwa ba tazo ta rasa magaji.Dalili
na
uku shine ta fini kyau,ta fini mulki,kuma kasan su
mata sun fi son su auri wanda yafi su
komai.Koda
Yarima yazo nan a zancensa sai Sarki Darmanu
ya
bushe da dariya sannan dubi Lubainu cikin
nustuwa
yace,Lubainu kai saurayi ne matashi wanda har
yanzu yake daukar darasi a cikin karatun
duniya,sabanin magidancin mutum kamata wanda
yake da matan aure ashirin da hudu.Babu irin
soyayyar daban yi ba a rayuwata,dukkanin
alamomin
SO da KAUNA sun bayyana akan fuskar
Sarauniya
Akisatul Sauwara a gareka da kuma alamomin
kauna
a zahiri.Idan ma baka yarda da abinda nake gaya
maka ba yanzu nan gaba zaka gani a lokacin da
Kura takai bango.Ka bar ganin cewar tasan kana
da
mata a gida mai jiran ka koma gareta.Hakan ba
zai
hana taso ka ba saboda shi SO bashi da hijabi
kuma babu abinda yake iya tareshi idan har ya
yunkuro.Har Lubainu ya bude baki zaice wani
abu
sai ga Sarauniya Akisatul Sauwara ta dawo,don
haka
sai yai shiru baice komai ba yana ta nazarin
abinda
Sarki Darmanu ya gaya masa.Haka dai Akisatul
Sauwara tazo ta zauna tare dasu aka ci gaba da
hira,inda Akisatul Sauwara ta dubi Sarki Darmanu
tace,yanzu kai a ganinka ta yaya zamu jewa
boka
Darbusa?Shin zamuje masa ne cikin lumana da
nasiha ko kuwa zamuje masa ne ta tsiya tsiya?
Koda
jin wannan tambaya sai Sarki Darmanu yayi
murmushi cikin ajiyar zuciya sannan yace,ni ta
yaya
kuka zo mini keda Lubainu?Sarauniya Akisatul
Sauwara tace ai kai baka bari mun iso fadarka ba
tun a daji ka taremu kana mai badda kama kazo
mana a siffar tsoho don ka yaudaremu ka cutar
damu.Dajin haka sai Sarki Darmanu yayi dariya
kuma ya hade fuska yace,to kiyi zaton yaudara
da
tarkon tuggu ninki wanda nayi muku daga Boka
Darbusa tunda kin san cewa ya ninka ni sau dari
A
komai.Koda jin wannan batu sai hankalin
Sarauniya
Akisatul Sauwara dana Yarima Lubainu ya tashi
domin sun fuskanci cewar hadarin dake gabansu
na
fuskantar Boka Darbusa ba kadan bane.Kodai su
sha
wahala ko kuma su rasa rayuwarsu gaba
daya.Haka
dai suka ci gaba da hira har lokaci ya cika sai ga
wadannan manyan tsuntsaye guda uku na Sarki
Darmanu sun dawo suna masu saukowa kasa
daga
can kololuwar sama.Cikin gaggawa su ukun suka
mike tsaye suka hada nasu i nasu
su,kowannensu
ya hau kan tsuntsu guda.Sarki Darmanu ne akan
gaba,Sarauniya Akisatul Sauwara a tsakiya
sannan
Yarima Lubainu.Lokaci guda tsuntsayen uku suka
bude fuka fukansu suka tashi sama suka luluka
izuwa can sama suna masu giftwa ta gaban
Rana
wacce ke shirin faduwa ta zama ja jawur.Abin
gwanin ban sha'awa ga dukkan halittar da take
kallo
daga kasan Turba.Kamar yadda Sarki Darmanu
ya
fada haka al'amarin ya kasance wato saida suka
shafe kwana
hudu da yini daya suna tafiya a sararin samaniya
bisa
wadannan manyan tsuntsaye sannan suka hango
gidan boka
Darbusa a nesa kadan dasu.ALLON SIHIRI
Littafi na biyu(2)
Part F
Sannan suka hango Gidan Boka Darbusa a nesa
kadan dasu.Babban abinda ya baiwa Lubainu da
Sarauniya Akisatul Sauwara a cikin wannan tafiya
shine a tsawon duk kwanakin da akayi ko sau
daya
tsuntsayen dake dauke dasu basu gajiya ba,kuma
ba
a sauko kasa an yada zango ba.Haka kuma duk
su
ukun babu wanda wata bukata ta kamashi ta
bawali
ko bayan gari saidai kawai idan sun gaji da zama
akan tsuntsayen su kwanta suyita sharar barci
abinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da
fargabar
komai ba.Da yammaci ne sakaliya suka hango
wannan gida na Boka Darbusa wanda saidai a
kirashi da aljannar duniya saboda ginuwarsa da
kawatuwarsa.Tunda Yarima Lubainu yazo duniya
ko
a bakin masana tarihi bai taba jin labarin gida
mai
kyan na Boka Darbusa ba.Saidai babban abin
takaice shine a tsakiyar dokar daji aka zo aka
gina
wannan gida wanda aka bata miliyoyin dinare
wajen
ginashi.Kai da gani kasan cewa in ba rikakken
Boka
ba wanda ya cika hatsabibin gaske babu wanda
zai
iya gina irin wannan gida a dokar daji haka ya
zauna
a cikinsa.Da saukar tsuntsayen uku kusa da kofar
gidan da tazarar kamar taku ashirin sai kawai
suka
ga an bude kofar gidan wacce ta kasance
katuwar
gaske.Kofar na budewa sai sukaga wadansu
kyawawan kuyangi su goma sha biyu sun fito
daga
cikin gidan a jere a layi.Shida a hannun dama
ragowar shidan a hannun hagu.Dukkaninsu suna
dauke da wani dan karamin kwando wanda akayi
shi
da karfen jauhar.Kowanne gwando an cikashi da
wani irin jan fure mai tsananin kamshi.Gaba
dayan
wadannan kuyangin suna sanye ne da dogayen
riguna masu launin kore wadanda akayi su da
Miski.Babbar cikin kuyangin ce kadai take da riga
kala dabam mai ruwan kwai wacce akayi mata
dinki
mai siffar dawisu.Tsananin kyawun wannan
kuyanga
gami da kyawun shigar datayi dole ne ya rudi
kowanne lafiyayyen 'da namiji.Cikin tafiyar
kasaita
da karairaya tamkar macijin gona haka wannan
kuyanga da sauran yan uwanta suka iso daf da
su
sarki Darmanu suka risina sukayi gaisuwa gami
da
yimusu barkda da zuwa.A sannan ne shugabar
kuyangin ta dago kai ta dubi su Lubainu tace lale
marhaban da manyan baki na musamma,lallai
mai
girma Darbusa yana farin ciki da zuwanku kuma
yace nayi muku jagora izuwa cikin fadarsa.Koda
jin
wannan batu sai Sarki Darmanu,Sarauniya
Akisatul
Sauwara da Yarima Lubainu suka sauki daha kan
wadannan tsuntsayen.Suna sauka sai tsuntsayen
suka sake bude fuka fukansu suka tashi
sama.Kafin
kiftwar ido sun kule a cikin sararin
samaniya.Koda
ganin haka sai mamaki ya kama Lubainu da
Akisatul
Sauwara suke a cikin zuciyarsu,Wai shin su
wadannan tsuntsaue wane iri nesu?Gashi sunyi
tafiyar kwanda hudu da yini daya basu yada
zango
ba,kuma da saukarsu yanzun nan sun sake tashi
sama ko hutawa basuyi ba bare su nemi ruwan
sha
ko abinci.Anya kuwa wadannan tsuntsaye ba
sihirtattu bane?.Amsar da suka kasa baiwa
kansu
kenan.Ba tare da fargabar komai ba kuwa su
Sarki
Darmanu suka bi wannan shugabar kuyangin a
baya
suka nufi cikin gidan.Su kuwa sauran kuyangin
tuni
suna kan gaba suna zubar da wannan Jan fure
mai
kamshi a kasa su Lubainu na bi ta kansa.Da
shigarsu cikin gidan sai duk su ukun suka kama
kalle kalle da waige waige domin sun zama
cikakkun
yan kauye duk da cewar dukkaninsu sarakai ne
masu tarin abin duniya.Ba komai ne yasa suka
zama yan kauye ba face ganin kayan kawar da
idanunsu basu taba gani ba da abubuwan al'ajibi
wanda ko a mafarki da hasashe basu taba zaton
wanzuwarsu ba.A cikin wannan gida ne suka ga
wani katon Lambu wanda girmansa yafi na wani
dan
karamin garin kuma kyawawan bishiyoyin dake
cikinsa da furanni tamkar halittarsu akayi a ciki
ba
shukasu akayi ba sai kayi zaton idan kayi musu
magana zasu amsa.Barewa,tsuntsaye da kwaron
nan mai suna malan buda mana littafi kuwa gasu
nan birjik a cikin Lambun kala kala,launi launi
bazasu kirgu ba.Kai idan mutum yana kallon
wadannan Lambu da abubuwan dake cikinsa sai
ya
manta da duk wani bakin cikin duniya kuma sai
yaji
kamar shine sarkin duniyar gaba daya saboda
farin
ciki.Saida akayi tafiya dasu kusan ta rabin sa'a
sannan aka iso dasu fadar Boka
Darbusa.Wangamemiyar fada ce wadda girmanta
yakai a sanya gidan sarautar Sarauniya Akisatul
Sauwara guda uku a ciki.Wannan karon sai da su
Lubainu suka rinka yin tuntube suna faduwa kasa
saboda kalle kalle da waige waige bisa ganin
kayan
kawar da yafi wanda suka gani a baya,amma
kuma
duk wannan kawa sai ta zama ta banza domin
kuwa
ba karamar razana da firgita sukayi ba
sakamakon
ganin irin fadawan da suke cikin fadar.Babu
bil'adama ko guda daya a cikin dubbun fadawan
Boka Darbusa face wadansu irin halittu wadanda
mutum bazai iya tantancewa ba yace Aljanu ne
ko
Dodonni.Wasun su rabin jikinsu na mutum ne rabi
na Aljan,wasu rabi dabbobi,rabi dodanni,wasu
kuwa
rabinsu na Aljan ne da wuta.Sun ksance manya
manya,girda girda saidai a kwatanta girmansu da
siffofin maridai ko mutanen farko.Dukkaninsu
suna
da matukar muni,kwarjini da ban tsoro,kuma suna
dauke da mugayen makaman yaki iri iri
barkatai.Wani kalar makamin ma ko a tarihi
mutum
bai taba kin irinsa ba.Wadannan dakaru sun cika
fadar gaba dayanta sai yar siririyar hanua suka
bari
a tsakiyar fadar wacce fadinta bai wuce kamu
uku
ba,kuma itace hanyar dazata kai mutum har
izuwa
inda karagar mulkin Boka Darbusa take.Koda
Boka
Darbusa ya kyallara ido yaga kuyanginsa sun
shigo
cikin fadar tare dasu Sarki Darmanu sai ya mike
tsaye daga kan karagar cikin tsananin farin ciki
ya
bushe da mahaukaciyar dariya yayita dariyar
kamar
wanda aka bashi komai na duniya.Al'amarin daya
kara razana
su Yarima Lubainu kenan sukaji a jikinsu cewar
lallai
Boka Darbusa yaudarsu yayi daya turo aka
karbesu
hannu biyu,lallai yunkurin cutar dasu zaiyi
yanzu.Bayan Boka Darbusa yayi dariyar mugunta
har
ta ishe shi sai ya murtuke fuskarsa a lokacin da
wadannan kyawawan kuyangi goma sha biyu
suka
rikide suka zama aljanun haske rike da zabga
zabgan takubba kuma suka yiwa su Yarima
Lubainu
kawanya.Koda ganin haka sai Sarki
Darmanu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima
Lubainu ma suka zare takubbansu suka jingina
da
bayansu su ukun suna jiran suga ta inda za a
kawo
musu hari.Koda gani haka sai Boka Darbusa ya
sake
bushewa da dariyar mugunta karo na biyu sannan
ya dubi su Yarima Lubainu yace,kunyi hauka
kuma
kunyi babban kuskure harda kuke yin tunanin
cewa
zakuzi wajena neman Allon Sihiri na kuma na
baku
alhalin yau sama da shekara bakwai kenan ina
son
ku kawo kanku nan fadata kun ki.Ai abinda kuka
fada gaskiya ne cewar kowa a gidansa sarki
ne.Ina
mai tabbatar muku da cewa tunda har kuka shigo
nan cikin fadata to tabbas babu dayanku dazai
fita
daga nan a raye,kuma shi kun shigo dauke da
Allunan Sihiri guda biyu.Ku sani cewa tuni nayi
bincike na gano hanyar dazan iya cire Allunan
Sihirinku daga cikin kwalaben Sihirin da kuka
sasu.Ina cirosu zan hada su da nawa.Hakan na
faruwa shike na na zama SARKIN DUNIYAr nan
gaba
daya.Duk wata halitta dake bisa doron kasa
walau
mutum ko aljan,dabba,tsunstu ko kwaro sai ya
dawo
karkashin mulkina da ikona.Yanzu zan barku da
wadannan Aljanun haske da suka yi muku
kawanya
na ga iyakar shirin ku dakuke dashi don karbar
Allon Sihirina.Koda gama fadin haka sai Boka
Darbusa ya yiwa Aljanun izinin su hallaka su
Darmanu.Nan take kuwa Aljanun suka afka musu
aka ruguntsume da azababben yaki ya zamana
cewa
Aljanun suna kai musu sara da suka cikin
tsananin
zafin nama dabasu taba gani ba.Duk sa'adda
takobin Aljanun ta hadu da tasu saidai kaga
tarwatsin wuta na tashi kuma takobin Lubainu
data
Akisatul Sauwara suka rinka dakushewa,ta Sarki
Darmanu ce kawai batayi komai ba.Haka kuma
duk
sa'adda su Lubainu suka sami nasarar sara ko
sukar jikin Aljanun saidai suji kamar iska suka
soka.Bugu da kari da kyar su Lubainu suke iya
tare
harin Aljanun saboda karfin saransu,jinsa suke
kamar katon dutse ake bugawa a kan takubbansu
wanda sai kato arba"in sun tare zasu iya
daukarsa.A
duk sa'adda takobin Aljanun ta shafi jikinsu
Lubainu
koda kuwa dan lakatarsu tayi saidai kaji sun
kwalla
ihi saboda tsananin zafi da zogon da suka ji,a
lokacin da jini je tsartuwa gami da feshi daga
jikin
nasu.Koda Boka Darbusa yaga yana samun
wannan
gagarumar nasara saiya cigaba da kyalkyalewa
da
dariyar mugunta saboda ya tabbatar da cewar
hakansa ya kusa cimma ruwa.Al'amarin su
Yarima
Lubainu kuwa suna wannan yaki ne cikin nadama
da
takaici domin sun gane cewa lallau tsautsayi ne
yasa
suka biyo Boka Darbusa har gidansa domin
karbar
Allon Sihiri.Banda Tsautsayi kuma zasu iya cewa
Ajali ne ya kirasu,domin sun san cewa babu wata
dabara dazasu iya yi a yanzu su ceci rayuwarsu
daga hannun wadannan Aljanu na haske.
SHIN SU YARIMA LUBAINU ZASU KUBUTA DAGA
HANNUN WADANNAN MUGAYEN ALJANU NA
BOKA
DARBUSA HAR SU KARFI ALLON SIHIRIN
HANNUNSA?
IDAN HAR HAKAN TA KASANCE YAUSHE NE
ZASU
ISA KOGON BAHAR IMFAL YARIMA LUBAINU YA
SAMO MAGANIN DA YA FITO NEMA?
YAYA SOYAYYAR SARAUNIYA AKISATUL
SAUWARA
DA YARIMA LUBAINU ZATA KASANCE?SHIN
ZATA
BAYYANA MASA SIRRIN ZUCIYARTA NE KUMA
YAYA
ZAI KARBI TAYIN NATA?
A WANE HALI YAZARINA TAKE YANZU A CAN
BIRNIN
ZAMRAL BISA BAKIN CIKIN RABUWA DA
MASOYINTA
YARIMA LUBAINU?
INA LABARIN YARIMA MANGUL DA MAHAIFINSA
SARKI ALKAS WADANDA SUKA KOMA CAN
BIRNINSU A CIKIN BAKIN CIKI NA SABANI?
SHIN YARIMA MANGUL ZAI CIRE SON YAZARINA
DAGA CIKIN ZUCIYARSA GABA DAYA A
MATSAYINSA
NA WANDA YA ZAMO MASAKI MAI HANNU
DAYA?
WANE MATAKI ZAI DAUKA AKAN MAHAIFINSA
SARKI
ALKASA WANDA YACE YA CIRESHI DAGA
SAHUN
'YA'YANSA?SHIN YANA TUNANIN DAUKAR
FANSA NE
AKAN YARIMA LUBAINU KO KUWA YA RUNGUMI
KADDARA?
YAUSHE NE YARIMA LUBAINU ZAI DAWO
BIRNIN
ZAMRAL HAR YA SAKE SADUWA DA
MASOYIYARSA
YAZARINA 'YAR BABBAN ATTAJIRI NA
NAHIYAR?
Mu hadu a littafin ALLON SIHIRI 3(kashi Na Uku)
don
jin ci gaban wannan kayataccen Kasaitaccen
Labari.
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku

1 Comments On ALLON SIHIRI 1 TO 9
avatar
abdulazeez

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment