Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki,kuma nayi
maka
alkawari cewar zan taimaka maka da raina da
jikina da
dukiyata har izuwa lokacin da bukatarka zata
biya.Ina so ka gama dukkan shirye shiryenka a
yau
din nan amma zan shiga nawa shirin kuma yanzu
zamuje dakin da wannan Allon Sihiri yake na
daukoshi in yaso gobe da sassafe a lokacin da
alfijir
ya keto zamu bar garin nan mu durfafi BIRNIN
KIMRAS domin
mu gana da SARKI DARMASU mu
sanar dashi bukatarmu ta barin wannan Allon
Sihiri
dake hannunsa.Kayi sani cewa bana tunanin
cewa
Sarki Darmasu zai amince ya bamu wannan barin
Allo dake hannunsa domin yau shekara kusan
bakwai kenan muna yaki a tsakanin kasashenmu
akan mallakar
Allon Sihirin amma abun ya gagari
kowanne bangare.Idan har kaga ya amince da
fito
da Allon Sihirin dake hannunsa saidai idan shima
yana da wata bukatar dabam.Babban abinda
yake
bani tsoro shine kamar yadda nake da tsaro akan
nawa Allon Sihirin haka shima Sarki Darmasu
yake da tsaro
akan nasa,kuma bazamu iya rabashi da
Allon ba da karfin damtse kona yaki da
tsafi.Sa'adda
Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta
sai
hankalin Yarima Lubainu ya dugunzuma ya rasa
abinda yake masa dadi,kawai sai ya dubi
sarauniya
Akisatul Sauwara yace,nikam bani da wani zabi
wanda yafi na
jarrabata sa'ata kawai don haka babu
gudu babu ja da baya a cikin wannan tafiya.Koda
jin
haka sai fuskar sarauniya Akisatul Sauwara ta
fadada
da murmushi tace biyoni muje.Tana gama fadin
hakan ta juya ta fice daga cikin turakar shi kuma
saiya bita da
sauri a baya.
SHIN YARIMA LUBAINU ZAI SAMI NASARAR
SAMO
ABINDA YA FITO NEMA?
A WANNE HALI YARIMA MANGUL DA
MAHAIFINSA
SUKE CIKI?
INA LABARIN MATAR YARIMA LUBAINU
(YAZARINA) DA
MAHAIFINSA?
ME ZAI FARU TSAKANIN SARKI DARMASU NA
BIRNIN KIMRAS DASU SARAUNIYA AKISATUL
SAUWARA ITA DA YARIMA LUBAINU YAYIN DA
SUKA
JE GARESHI DON KARBAR BARIN ALLON
SIHIRIN
HANNUNSA?
SHIN ZAI AMINTA YA BASU WANNAN BARIN
ALLON
SIHIRIN?
Mu hadu a ALLON SIHIRI 2 don jin cigaban
wannan
kasaitaccen labari.
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__ALLON SIHIRI
Littafi na biyu(2)
Part A
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
Sarauniya Akisatul Sauwara ta durfafi wani
bangare
daban na cikin gidan sarautar tayi ta kutsawa ta
cikin wani surkuki mai lunguna da yawa har saida
suka yi tafiya mai tsawo sannan suka iso kofar
wani
gida.Koda masu gadin gidan suka hango
Sarauniya
Akisatul Sauwara tare da Yarima Lubainu sun
tunkaro inda suke sai sukayi sauri suka bude
kofar
gidan tun kafin su iso.Suna isowa kuwa masu
gadin
suka risina suka gaida sarauniya.Ita kuwa ko
kallonsu batayi ba ta kunna kai cikin gidan
Lubainu
na take mata baya.Babu komai a cikin wannan
daki
face kayna tarihi iri iri na kasar musamman
abinda
ya danganci kayan yaki kamar
takubba,masu,Garkuwa da sauransu,kai harda
kayan
kyale kyale dana kawa kala kala.Nanfa Yarima
Lubainu ya zama dan kauye ya kama kalle kalle
da
waige waige.Saida suka iso tsakiyar gidan suka
iske
kwalbar sihiri wacce aka dorata akan wani
zagayayyen tubalin gini.A cikin wannan kwalba
ne
aka sanya Allon Sihiri.Nan take Lubainu yayi arba
da
wannan Allon Sihiri,ya dubi kwalbar da kyau yaga
babu wata kofa ko huda a jikinta wacce za'a iya
zura
hannu a ciki a dauko Allon.Da isowarsu gaban
kwalbar sihirin sai sarauniya Akisatul Sauwara ta
dubi Lubainu tace,kayi iya kokarinka da duk
abinda
kake takama dashi wajen fasa wannan kwalba
don
dauko wannan Allon sihirin mu ga abinda zai
faru.Ai
kuwa kafin ta gama rufe bakinta tuni Yarima
Lubainu
ya dauko wani katon barandami ya sari wannan
kwalbar sihirin da dukkan karfinsa.Maimakon
kwalbar ta dare ko ta tarwatse sai shi
barandamin ya
karye bal,ya rabe gida biyu.In banda tarwatsin
wuta
daya tashi akan Gilashin babu abida ya
sameshi.Al'amarin dayai mutukar girziza Yarima
Lubainu kenan yaja da baya a dan tsorace.Ita
kuwa
sarauniya Akisatul sauwara sai ya bushe da
dariya
ta sake duban Yarima Lubainu tace to ai saika
jarraba Karfin sihirin tsafinka mu gani.Lubainu bai
karaya ba sai ya matsa dafda kwalbar sihirin ya
shiga karanta wadansu dalasimai na tsafi yana
shafar kwalbar da tafin hannunsa.Kwatsam sai
yaji
wata irin iska mai karfi ta sureshi ta baya ta
gwarashi
a jikin bangi ya fado kasa a galabaice.
Koda ganin abinda ya faru gareshi sai sarauniya
Akisatul Sauwara ta sake bushewa da dariya a
karo
na biyu.Lokaci guda kuma ta hade fuska tace,ya
kai
Lubainu kamar yadda na gaya maka da farko
babu
wani mahaluki walau mutum ko aljan wanda ya
isa
ya dauki wannan Allon Sihiri daga cikin wannan
kwalba face ni.Koda gama fadin hakan sai
Sarauniya
Akisatul Sauwara taje gaban wannan kwalba ta
shafeta da hannunta na hagu.Take kwalbar ta
rabe
gida biyu kamar an yanke lemon bawo.Kawai sai
ta
sa hannunta ta dauko Allon ta dorashi akan tafin
hannunta ta yafito Lubainu da hannu tace
dashi,zo
kaga irin abinda aka rubuta a jikin Allo.Cikin sauri
Lubainu yazo daf da iya ya tsaya ya kurawa
Allon
idanun.Ai kuwa sai yaga Rubutun a rabe yake
gida
biyu.Kuma bazai taba karantuwa ba a haka face
an
jona daya barin Allon na biyu.Kawai sai yayi
ajiyar
numfashin ya dubi Akisatul Sauwara cikin alamun
karayar zuciya yace,Ai wannan Allon dake
hannunki
bashi da wani amfani idan ba'a samo daya Allon
bana biyu.Koda jin haka Sai Akisatul Sauwara
tayi
murmushi tace to ina tabbatar maka da cewa
idan
ma an samo Allon na biyu an hada da nawan
rubutun dake jikinsu ba zai karantu ba sai an
hada
dana ukun.Koda gama fadin hakan sai ta mayar
da
Allon cikin wannan kwalbar.Take kwalbar ta
koma ta
manne tamkar bata taba rabewa ba biyu.Akisatul
Sauwara ta dauke kwalbar ta juya ta fice daga
cikin
wannan gida Lubainu yabita da sauri.Nan dai
suka
yita bin sako sako da lungu lungu har suka dawo
inda turakarta take.Anan ne ta tsaye cak shima
Lubainu sai ya tsaya.Akisatul Sauwara ta juyo
tana
mai yi masa wani kallo mai dauke da murmushi
da
ayar tambaya(?) tace,ai anan zamu rabu ka koma
izuwa masaukinka ka sake hutawa,amma ina
gayyatarka da yamma a can filin motsa jini na
bayan
turakata domin mu dan motsa gabban jikinmu in
yaso gobe da safe muyi haramar tafiya.Tana
gama
fadin hakan ta kunna kai izuwa cikin turakarta
kuyangi na gyara mata hanya.Yarima Lubainu ya
juya ya nufi hanyar da zata mayar dashi
masaukinsa
zuciyarsa cike da tunanin wannan kallo wanda
Sarauniya Akisatul Sauwara tayi masa wanda ya
kasa gano ko na mene ne tsakanin SO da tausayi
ko
kuma KAUNA.Kamar yadda Sarauniya Akisatul
Sauwara ta fada haka al'amarin ya kasance wato
da
yammaci ta tura aka zo dashi izuwa filin motsa
jini
dake bayan turakarta.Yana isowa wajen sai ya
iske
sarauniya Akisatul Sauwara a tsaye cikin shigar
yaki
rike da takobi.Yana isowa sai shima aka miko
masa
sulke takobi da garkuwa.Ba tare da gardamar
komai
ba ya karba ya sanya sulken amma sai yaki
karbar
garkuwar saboda yaga itama Sarauniya Akisatul
Sauwara ta dubi Lubainu tace ina mai
shawartarka
daka dauki garkuwar nan ka rike domin zan iya
baka
mamaki.Lubainu yayi murmushi yace,ai ni dai ke
baki rike garkuwa ba a matsayinki na 'ya mace
nima
ba zan rike ba.Akisatul Sauwara tace,shi ke nan
muje zuwa mu gani mahaukaci ya hau kura.Kafin
Yarima Lubainu ya budi baki kara cewa wani abu
tuni Akisatul Sauwara ta zare takobinta ta daka
tsalle
ta kawo masa wawan sara a kafada.In ba don
Lubainu ya daka tsalle gefe daya ba cikin
tsananin
zafin nama da tuni ta tsargeshi gida biyu.Nan fa
suka kacame da azababben yaki ta rinka kai
masa
mugayen hare hare da wani irin azababben zafin
nama da karfin gaske wanda yai mutukar bashi
mamaki tun da yake haduwa da mazaje bai taba
haduwa da mai kamar jarumtakarta ba.Bisa dole
shima ya zage damtse yaci gaba da kare hare
haren
nata amma sai yaga duk da haka tana neman
kuntatashi,don ta fara turashi jikin bango tana
hanashi yin kyakkyawan motsi yadda ko yay yayi
sakaki zata iya gamawa dashi.Nan fa shima ya
fara
maida martani,ai kuwa sai yakin nasu ya zama
abin
tsoro abin tashin hankali,hatta kuyangi,borori da
dakarun dake tsaitsaye a zagayen filin saida
hankalinsu ya dugunzuma ainun bisa ganin irin
azababben yakin dasu sarauniya ke yi.Saida suka
dauki dogon lokaci a haka dayansu bai sami
nasarar
koda shafar jikin abokin gwaminsa ba.Al'amarin
dayai mutukar girgiza Yarima Lubainu shine ko
alamar gajiya babu a tare da sarauniya alhalin
shi
kuwa ya fara haki.Koda ya fuskanci cewa lallai
zaiji
kunya idan baiyi da gaske ba,sai ya sauya salon
fadan ya hada dakai naushi da bugu.Ai kuwa sai
ya
shammaci Akisatul Sauwara ya doki kafafunta da
kafarsa guda tayi sama tana mai katantanwa
amma
tana fadowa kasa sai ta dafa kasa da hannunta
guda
tayi sama kamar sifirin ta doki kirjinsa da
kafarta.Saboda karfin dukan saida Lubainu yayi
tsalle
sama da baya ya fado kasa,amma shima sai yayi
wuf ya mike tsaye Zumbur.Yana mai gyara
tsayuwa
a lokacin da Akisatul Sauwara ta duro kasa bisa
kafafuwanta.Kawai sai ta dubeshi tayi murmushi
tace,tabbas yanzu bani da wata fargana a cikin
tafiyar da zanyi tare dakai domin na gamsu
cewar
kai jarumi ne na kwarai.Koda jin wannan batu sai
ran Lubainu ya baci daya fahimci cewar sunyi
wannan gumurzu ne don kawai taga iyakar
jarumtakarsa.Amma sai ya boye fushin nasa bai
nuna mata ba.A wannan lokaci duk sun jike
Sharkaf
da gumi don haka sai ta shawarce shi akan yaje
yayi
wanka ya hutu,amma bazasu sake haduwa ba sai
gobe da safe yayin wannan tafiya.Nan take kuwa
Yarima Lubainu ya cire sulken dake jikinsa ya
bayar
gami da takobin hannunsa ya tafi yana waigen
sarauniya yana yi mata wani irin kallo wanda
itama
ta fada cikin wasi wasi domin ta kasa tantance
irinsa.Kallo ne mai kama dana jin haushi ko na
gajiya?Nan dai itama ta juya ta nufi hanyar da
zata
kaita turakarta.Kafin Alfijir ya keto tuni sarauniya
Akisatul Sauwara ta gama yi musu shirin
tafiya,kuma
bata bukaci rakiyar dakarunta ko kuyanginta
ba.Su biyu rak suka fice daga birnin Rauhul
Bagadar bayan ta baiwa tsohuwa Dulaiba jiran
gari. Prince Auwal Auwzab
Nan fa Lubainu da Akisatul Sauwara suka
sakarwa
dawakansu linzami suka nausa cikin daji sukayi
ta
tafiya ba sassauci.Saida suka yini suna tafiya
basu
yada zango ba,idan suka ji yunwa ko kishirwa sai
dai su bude jakar guzurinsu su kama cin abincin
ko
kuma su daga battar ruwansu su sha.Tsawon
wannan lokaci dayansu bai ce uffan ba,babu
wanda
yayiwa wani magana.Daf da faduwar rana ne
dawakansu suka fara nuna alamar sarewa domin
suna bukatar ruwan sha.A sannan ne Akisatul
Sauwara ta dubu Yarima Lubainu tace,yakamata
mu
yada zango inba haka ba kuwa dawakanmu zasu
sare.Lubainu yayi murmushi yace,ai tun dazu
nake
son na sanar dake hakan amma sai na kasa don
kada kice na gaza.Koda jin haka sai Sarauniya
Akisatul Sauwara ta kyalkyale da dariya tace,ai
tun
kafin ma mu bari birnina ka sare tunda ka bari
mukayi kunnen doki a gasar yakin da mukayi ni
da
kai.Lubainu ya girgiza kai yace aa bamuyi
kunnen
doki ba tunda nine na fara kai ki kasa kafin ke ki
kaini.Akisatul Sauwara ta sake yin murmushi a
karo
na biyu tayi shiru bata kara cewa komai ba.Cikin
sa'a kuwa sai suka hango wata fadama a can
gabansu nesa kadan kuma a kusa da fadamar
akwai
duwatsu da dogayen bishiyoyi.Cikin murna suka
karasa bakin koramar suka sauka.Dawakansu
suka
kama shan ruwa suna cin ciyawar dake bakin
koramar.Kawai sai Akisatul Sauwara ta kwance
jakar
guzurinta ta dauko tanti ta shiga aikin
kafashi.Al'amarin dayai mutukar baiwa Yarima
Lubainu Mamaki kenan,ya mike da sauri ya kama
ma ta aikin yana mai cewa,haba ranki ya dade
saboda me bazaki umarceni dana kafa tantin ba?
Ai
mulki ba wasa bane dole ne na baki girmanki a
wannan fannin.Sa'adda Sarauniya Akisatul
Sauwara
taji wannan batu sai tai murmushi tace,kamar
yadda
nake mai mulki kaima ai mai mulki ne tunda ka
kasance dan sarki.Lubainu yayi murmushi yace,ai
dan sarki ba sarki bane,don haka yanzu kin bani
tazara mai yawa.Darajarki da daukakarki a duniya
ta
ninka tawa sau goma.Akisatul Sauwara tayi 'yar
guntuwar dariya tace,abinda ka fada gaskiya ne
amma ai duk sarkin daya baro birninsa ba sarki
bane tunda idan ya hadu da wanda bai sanshi ba
zai
iya wulakantashi ya wuce abinsa.Ni yanzu na
ajiye
karagar mulkina a gefe daya na dauki kaina
daidai
da kowanne talaka har sai bayan bukatarka ta
biya
mun koma kasata.Koda jin wannan batu sai jikin
Yarima Lubainu yayi sanyi yace,yake wannan
sarauniya mai daraja,yanzu kina nufin kice bakya
tsoron irin tsananin tashin hankalin dake cikin
wannan tafiya tawa har kike tunanin zaki ci gaba
da
bina har izuwa lokacin da burina zai cika?Ki tuna
fa
cewa yanzu akan mataki na farko muke kawai.A
kalla nan gaba akwai sauran matakai bakwai
zuwa
goma a gabanmu tunda sai mun nemo barin
Allon
Sihiri na biyu dana uku,sannan mu tafi neman
abokan tafiyarmu mutum uku.Yayin da Sarauniya
Akisatul Sauwara taji wannan batu sai tayi
murmushi
tace,ai rai ba abakin komai yake ba indai akwai
biyan bukata,kuma matsoraci har abada bazai
zama
gwani ba.Yayin da Yarima Lubainu yaji wannan
batu
sai ya cika da mamaki gami da wasi wasi.Abida
ya
bashi mamaki shine aka wane dalili sarauniya
Akisatul Sauwara ta siyar da rayuwarta don ganin
bukatarsa ta biya?Abinda zuciyarsa keyi masa
wasi
wasi kuwa shine,anya kuwa sarauniya Akisatul
Sauwara bata da wata manufa ta binsa wannan
tafiya?A zahiri dai bai ga wani abu dazata
amfana
dashi ba kuma bata gaya masa da bakinta
ba.Nan
dai Yarima Lubainu ya taimakawa Sarauniya
Akisatul
Sauwara suka karasa kafa tantin kuma ya
kwance
jakartaya debo kayan shimfidarta ya gyara mata
inda zata kwana.Bayan ya gama kintsa komai a
daidai lokacin da magriba ta kunno kai sai suka
fara
jiyo kukan dabbobin daji dana manyan tsuntsaye
masu shawagi a sama.Koda jin haka sai
Sarauniya
Akisatul Sauwara ta fito daga cikin tantin da
sauri ta
tofa wadansu dalasiman tsafi gabas da
yamma,kudu
da arewa da kuma sama da kasa,sanna ta dawo
cikin tantin ta dubi Yarima Lubainu wanda ke
shirin
biyota izuwa wajen tantin don tabbatar da cewar
babu wani mugun kwaro ko raminsa.Cikin
mamaki
Lubainu ya dubi Akisatul Sauwara yace,mene ne
naga kin fita da sauri daga cikin tantin nan kuma
kin
dawo da sauri?Koda jin wannan tambya sai
Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace
naje
na samar mana da tsaro ne a waje.Ko dabba ko
mutum ko aljan bai isa yazo nan ba ya cutar da
mu,don haka ka saki jikinka kayi barci mai
dadi.Koda gama fadin haka sai Sarauniya
Akisatul
Sauwara ta nufi inda shimfidarta take ta fara
kokarin
cire tufafin jikinta domin tasa rigar bacci.Cikin
hanzari Yarima Lubainu ya juya ya fice daga
cikin
dakin.Da yake a wannan lokaci wata irin iska mai
sanyi ta fara kadawa,sai Yarima Lubainu yaje ya
samo itatuwa ya kunna wuta ya zauna a gaban
wutar yana jin dumi.A daidai wannan lokaci ne
yaji
yunwa ta kamashi.Don haka sai ya bude jakar
guzurinsa ya fiddo da abinci ya kama
ci.Kwatsam!ba
zato ba tsammani sai yaji takun sawu a
bayansa.Cikin zafin nama Lubainu ya zare
takobinsa
ya mike tsaye zumbur!Koda yai arba da abinda
ya
tunkaroshi sai yai sauri ya sunkui da kansa kas a
lokacin da jikinsa ya kama tsuma.Ba wani abu ya
gani ba face sarauniya Akisatul Sauwara sanye
da
wata doguwar Rigar fara mai shara shara wacce
ta
bayyana komai na surar jikinta.Ganin tsananin
kyawun surar jikin nata ne yasa jikinsa ya kama
kyarma kuma zuciyarsa ta kama bugawa da sauri
da
sauri kuma da karfi.Tunda Yarima Lubainu ya
taso a
rayuwarsa bai taba ganin 'ya mace haka ba a
rayuwarsa sai wannan karon,don haka sai ya
danne
zuciyarsa da karfin tsiya,duk da cewa bashi da
cikakkiyar lafiyar da zaiji
wani abu sai zuciyarsa ta rinka harbawa.Ita kuwa
sarauniya Akisatul Sauwara tazo masa ne a cikin
wannan siffa don ta jarraba iyakar hakurinsa duk
da
cewar shine mutum na farko da ya taba ganinta
a
hakan.Kai tsaye ta matso daf dashi ta dubeshi
cikin
murmushi mai rikirkita kwakwalwa da hankali
tace,shin na baka tsoro ne bisa jin sautin tafiya
ta?
Ba tare da ya dago kai ba ya dubeta sai yayi
yake
sannan yace,ai dole ne naji tsoro tunda ban taba
zaton zanji wani motsi ba a baya.Koda jin haka
sai
Ta bushe da dariya sannan ta kama hannunsa
suka
zauna tare a gaban wutar suka ci gaba dajin
dumin
tare.Koda Lubainu yaga taki sakin hannunsa sai
ya
mike tsaye yace ina zuwa.Kawai sai ya zagaya
bayan tantin yayi kamar yana bawali ne sannan
ya
dawo ya sake zama a kusa da ita suna fuskantar
gabas,amma wannan lokaci bai yarda sun zauna
daf
da daf ba sai daya zamana cewa akwai tazarar
taku
uku a tsakaninsu.Tsawon 'yan dakiku dayansu bai
ce uffan ba sannan Lubainu yayi ajiyar numfashi
ya
dubeta yace,ranki ya dade ya kamata kije ki
kwanta
kiyi barci tunda dare ya soma kuma akwai gajiyar
tafiya a tare dake.Wai shin ma mene ne dalilin
dayasa kika fito ne alhalin gashi kinyi shirin
bacci?
Lokacin da Akisatul Sauwara taji wannan
tambaya
sai tayi murmushi tace,ya kai Lubainu kayi sani
cewa a rayuwata tun daga kuruciyata har izuwa
girmana ban taba kwanciya ba ni kadai a cikin
turakata face tare da kuyangina.Yau gashi zan
kwana ni kadai a cikin tanti kuma a cikin
daji.Tabbas
ko na kwanta barci ba zai zo min ba face ina jin
numfashin dan Adam a kusa da ni.Bisa wannan
dalili
ne na kasa barci har na fito wajenKa.Abinda
nake so
dakai yanzu shine kazo mu koma cikin tantin nan
mu kwana muyi barci.Koda jin wannan batu sai
Idanun Yarima Lubainu suka zazzaro ya dubeta
cikin
alamun tsananin firgici da tsoro yace gaskiya
bazan
iya barci ba a kusa dake.Ranki ya dade kiyi sani
cewa babu wani 'da namiji dazai ganki a cikin
wannan yanayi bai rude ba ya kamu da
sha'awarki
da sonki.Ni a matsayina da saurayin da bai taba
sanin 'ya mace ba kuma wanda yake nisantarku
dole
ne naji tsoron taraiya dake.Koda Lubainu yazo
nan a
zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta
kyalkyale da dariya sannan tace,kamar yadda
baka
taba sanin 'ya mace ba nima ban taba sanin wani
'da namiji ba,don haka na baka amanar kaina.Ina
mai tuna maka cewa samun yin barcina yana
gareka.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya
Akisatul Sauwara ta mike tsaye ta shige cikin
tantin
taje ta kwanta akan shimfidarta kanta na kallon
saman tantin ta fada kogin tunani.Shi kuwa
Yarima
Lubainu dake a zaune a wajen gaban wuta sai ya
mike tsaye ya kama kai kawo cikin tsananin
damuwa da wasi wasi.Daga can sai ya shiga
cikin
tantin yayi shimfida a gefe daya nesa da ina
Akisatul
Sauwara ke kwance ya kwanta.Yana kwanciya
sai
zuciyarsa ta tafi izuwa tunanin irin
gwagwarmayar
dayayi a baya.Yana cikin wannan tunani ne kuwa
barci ya saceshi har yana munshari bai sani
ba,kuma bai sake farkawa ba saida gari ya waye
rana ta kwalle.Yarima Lubainu na bude idanunsa
sai
ya hango shimfidar Sarauniya Akisatul Sauwara
wayam babu kowa akai.Koda yayi arba da abinda
ke
kan shimfidar sai zuciyarsa ta buda da kafi ya
kamu
da tsananin mamaki.Ba wani abu ya gani ba
akan
shimfidar face Allon Sihirin nan na Sarauniya
Akisatul Sauwara.Allon ne tsurarsa akan
shimfidar
wato an cireshi daga cikin kwalbar data
lullubeshi.Har Yarima Lubainu ya yunkura zaije
ya
dauki Allon Sihirin sai wata zuciyar ta daka masa
tsawa tace,shin ka manta ne da guzurin da
mahaifinka ya baka kafin ka baro gida.Cin amana
ne
idan ka dauki wannan Allon Sihiri,Amana,cika
alkawari da fadin gaskiya sune guzurin da
mahaifinka ya baka,kuma idan har ka koyayesu
zaka
sami nasarar abinda ka fito nema.Koda gama
aiyana
hakan sai ya juya ya fice daga cikin tantin.Yana
fitowa ya dubi gabasa da yamma,kudu da arewa
amma bai hango Akisatul Sauwara na kuma baiji
motsin taba.Al'amarin d yayi matukar bashi
mamaki
kenan domin baiga dalilin dazai sa tayi
gangancin
barin Allon Sihirin ta ba a fili haka.Nan dai
Yarima
Lubainu ya nufi gabar wannan korama yaje ya
wanke
fuskarsa ya kuskure bakinsa.Ashe duk wannan
abu
dake faruwa Sarauniya Akisatul Sauwara na labe
a
cikin wata duhuwa kuma tana kallon duk abinda
Yarima Lubainu keyi.Ta buya ne domin ta jarraba
amanarsa ta gani shin zai iya rike amanar.A jiya
da
daddare ta jarraba hakurinsa kuma ya haye
jarrabar
tunda har gari ya waye bai kusanceta ba duk da
cewa ya dimauce da ganin tsananin kyawun
siffarta
kuma ya kamu da matukar sha'awarta.Bisa
mamaki
sai sarauniya Akisatul Sauwara taga cewar
Yarima
Lubainu bai dauke Allonta na sihiri ba yayi
kokarin
guduwa.Maimakon hakan ma sai taga cewar
hankalinsa ya tashi bisa rashin ganinta domin
sa'adda ya wanke fuskarsa da bakinsa a cikin
wannan korama sai ya kasa komawa cikin tantin
ya
rinka kai kawo a harabar wajen yana leke leke a
kowacce kusurwa yana kwalla mata kira amma
yaji
bata amsa ba.Al'amarin dayai matukar
dugunzuma
hankalinsa kenan domin yana tsoro kada ya tafi
nemanta kuma azo a sace wannan Allon
Sihirin.Kuma yana tsoron kada ya dauki Allon
Sihirin
zargi ya shiga tsakaninsa da Sarauniya Akisatul
Sauwara.Lokacin da Akisatul Sauwara taga halin
da
Yarima Lubainu ya shiga sai tayi murmushi ta
juya
da baya ta nausa cikin daji.Sai da taje tayi
farauta ta
harbo wani tsuntsu sannan ta dawo.Tana isowa
bakin tantin ta iske shi a zaune yayi tagumi cikin
alamun tsananin damuwa.Koda ya hangota saiya
mike zumbur!da sauri ya tareta yana mai cewa
haba
ranki ya dade yaya zaki tafii cikin daji batare da
kin
sanar daniba.
Koda ya hangota sai ya mike zumbur!Da sauri ya
tareta yana mai cewa,haba ranki ya dade,yaya
zaki
tafi cikin daji ba tare da kin sanar dani ba?Koda
jin
wannan tambaya sai Sarauniya Akisatul Sauwara
tayi
murmushi tace,komai akwai dalilin faruwarsa.Ka
bari
mu nutsu tukunna zan yi maka bayanin komai a
saukake.Nan take Akisatul Sauwara ta dora ruwa
a
tukunya ta kunna wuta.A takaice dai ta fara
kokarin
fisge wannan tsunstu data harbo.Koda Lubainu
yayi
yunkurin taimaka mata sai ta ki don haka sai ya
zuba mata idanu har izuwa lokacin data kammala
gasa tsunsun sannan tayi masa tayi suka zauna
suka kama cin nama tsuntsun.Tsawon yandakiku
suna cin naman dayansu baice uffan ba a lokacin
da
dajin yayi tsit ba a jin sautin komai face na iskar
dake kadawa.Kawai sai Lubainu ya katse shirun
ya
dubeta yace,yake wannan sarauniya mai
daraja,idan
baza ki damu ba inason ki gaya min dalilin
dayasa
kike sakin jiki dani a cikin wannan tafiya alhalin
ban
kasance muharraminki ba ko kuma amintaccenki?
Koda jin wannan batu sai sarauniya Akisatul
Sauwara ta kyalkyale da daria sannan
tace,tabbas
kayi mini tambayoyi masu amfani kuma dama ai
nayi alqawarin baka amsoshinsu a yanzu dana
sami
nutsuwa.Da farko dai dalilin dayasa na yarda
muka
kwana tare a cikin daki ina so ne na jarraba
hakurinka shin zaka kasance mai tsare
mutuncina
bisa alqawarin dake tsakaninmu na taimakon
juma a
cikin wannan tafiya?Tabbas ka kiyaye wannan
jarrabawa ka hayeta.Dalili na biyu kuma wanda
yasa
na tafi na barka a cikin tanti kana barci shine
domin
na jarraba amanarka na gani shin zaka sace
Allon
Sihiri na ne ka gudu?Sai gashi kayi matukar bani
mamaki tunda baka sace Allon Sihirin ba alhalin
kuma gashi na fito dashi fili karara daga cikin
kwalbar da babu wani mahaluki daya isa ya fiddo
shi.Tabbas ka cika mutum mai amana yanzu abu
daya ya rage nayi maka jarraba akansa,kuma da
sannu zamu kai ga wannan matsayi.Koda
Sarauniya
Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai Yarima
Lubainu yayi shiru kawai yana mai kura mata
idanu.Daga can kuma sai ya mike tsaye ya shiga
cikin tantin ya shiga cikin tantin ya shiga hada
kayayyakinsa yana zuba su acikin jakar
guzurinsa.Itama Sarauniya Akisatul Sauwara sai
mike tsaye ta bishi izuwa cikin tantin ta shiga
kimtsa na ta kayan.Har suka gama kimtsa komai
basuce da junansu kala ba.Nan take suka hau
dawakansu suka nausa cikin daji suna masu
cigaba
da tafiya.Sai

1 Comments On ALLON SIHIRI 1 TO 9
avatar
abdulazeez

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment