Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya
dubi Dazyan yayi masa zancen kurame.A Sannan
ne
Sarki Darmanu da sarauniya Akisatul Sauwara
suka
taho garesu da sauri domin suji abinda bakon
jarumin zaice.Dazyan yayi gyaran murya sannan
yace,yakai wannan dan sarki kayi sani cewa
shugabana yace inda zaka yi imani da
UBANGIJIN
MUSULUNCI ka karbi addininmu zaka iya samu
lafiyarka a rana guda a cikin dakika guda daya
ma jal
ka yankewa kanwa duk wahalar dake gabanka.To
amma ya fuskanci cewa zuciyarka da ta
wadannan
Abokan Gaba tana da rauni akan yin imani da
ubangijin musulunci saboda kun yarda da Addinin
iyayenku da kakanninku,kuma kuna gani kamar
addinin naku shine addinin gaskiya,saboda kuga
zahiri kuma ku gamsu cewar addinin musulunci
shine na gaskiya mafin inganci da daraja akan
naku,shugabana ya amince zai ci gaba dayin
wannan tafiya tare daku amma duk inda akaje zai
barku ku jarraba kafin sihirinku da na damtsenku
wajen ganin cewa kun kawar da kowacce irin
masifa
da aka riska sai bayan kun kasa sannan shi ya
kawar da masifar da taimakon ubangijin
musulunci,amma fa sai idan kun dauki alkawarin
cewar bayan anzo karshen tafiyar zakuyi imani
da
addinin musulunci,idan kuma baku yarda ba da
wannan sharadi ba,to zai cigaba da binku kawai
a
cikin wannan tafiya ya zaman dan kallo ba tare
daya
taimaka muku da komai ba.Koda Dazyan yazo
nan a
jawabinsa sai hankali Sarki Darmanu dana
Sarauniya
Akisatul Sauwara ya dugunzuma ainun fiye da ko
yaushe suka rasa abinda yake musu dadi a
duniya,shi kuwa Yarima Lubainu sai farin ciki ya
lullubeshi ya dubi bakon jarumin cikin murmushi
yace tabbas ni na yarda da wannan sharadi
naka.Koda jin hakan sai Bakon Jarumin yayi
maganar kurame ga Dazyan shi kuma Dazyan sai
ya
dubi Yarima Lubainu yace mai gidana yana
murna
dajin bayaninka.Dazyan ya juya ya dubi Sarki
Darmanu da Sarauniya Akisatul Sauwara
yace,maigidana yace ki kuma fa menene
ra'ayinku?
Cikin rawar murya da tuntuben harshe Sarauniya
Akisatul Sauwara tace babu matsala muma mun
amince da sharadin maigidanka to amma yanzu
yaza ayi akan batun ALLON SIHIRIN Boka
Darbusa
wanda mukazo nema a cikin gidansa?
pls Like nd comments
15 hrs · PublicALLON SIHIRI
Littafi na uku (3)
Part C
Batun ALLON SIHIRIN Boka Darbusa wanda
mukazo
nema yanzu a cikin gidansa.Koda jin wannan
tambaya sai Bakon Jarumin ya dubi Dazyan ya
sake
yi masa zancen kurame da hannu.Dazyan ya dubi
sarauniya Akisatul Sauwara yace maigidana yace
yanzu zamu bazama neman wannan ALLON
SIHIRI a
cikin wannan gida,amma ku ukun ne zaku fara
neman ALLON SIHIRIN da karfinku sihirinku,idan
kuka kasa sai mu roki ubangijinmu ya nuna mana
inda yake mu daukeshi da izininsa mu baku.Koda
gama fadin hakan sai Yarima Lubainu ya dubi su
Sarauniya Akisatul Sauwara yace to kunji yanzu
dai
shawara ta rage ga mai shiga rijiya.Sarauniya
Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu suka dubi
junansu sukayi murmushi kuma suka budi baki
cikin
hadin murya suka ce muma mun amince da
hakan.Nan take Sarauniya Akisatul Sauwara,Sarki
Darmanu da Yarima Lubainu suka sake kunna kai
izuwa cikin gidan Boka Darbusa kowannensu na
karanta dalasiman tsafinsa a cikin ransa.Shi
kuwa
Bakon Jarumi da Bawansa Dazyan sai suka bisu
a
baya kawai suna kallonsu kuma suna neman
tsarin
Allah daga dukkan mugun abun dake cikin
gidan.Abu dai kamar wasa saida su sarauniya
Akisatul Sauwara suka shiga duk wani sako,lungu
da
dukkan dakunan dake gidan kuma suka caje
komai
da ko ina a cikin gidan amma har suka gaji likis
ko
alamar ALLON SIHIRI basu gani ba.Daga karshe
ne
suka ga wani daki mai katuwar bakar kofar karfe
a
kulle wanda ya rage basu shiga ba.Ita kanta
kofar
wannan daki ta isa abar tsoro domin anyi tane da
mulmulallen karfe mai kaurin gaske,sannan akwai
hoton KWARANGWAL din kan BIL'ADAMA da
kafafuwansa a jikinta alamar cewa wannan
daki,daki
ne me mugun hadari wanda mutum zai iya rasa
rayuwarsa a ciki.Koda sukayi arba da kofar
wannan
daki sai sarauniya Akisatul Sauwara,Yarima
Lubainu
da sarki Darmanu suka dubi junansu sukayi cirko
cirko suna kallon kofar.Kawai sai Sarki Darmanu
ya
dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace ai sai fara
jarraba taki sa'ar mu gani.Ba tare da wata
gardama
ba kuwa sarauniya Akisatul Sauwara ta kama
kofar
taja da nufin ta budeta amma sai ta kasa kawai
sai ta
fara karanta wadansu dalasiman tsafi tana
tofawa a
kofar.Maimakon kofar ta bude sai wata irin iska
mai
karfin gaske ta fito daga cikin kofar ta doki kirjin
Sarauniya Akisatul Sauwara tayi sama da ita da
karfi,bayanta ya gwaru da jikin bango ta fado
kasa a
galabaice.Koda ganin abinda ya faru sai hankalin
Sarki Darmanu ya tashi jikinsa ya kama tsuma ya
dubi Yarima Lubainu yace saura kai.Yarima
Lubainu
ya numfasa yace shin ka mantane kai abinda
Sarauniya Akisatul Sauwara ta kasa yi nima
bazan
iya ba.Koda jin haka sai Sarki Darmanu ua ciza
lebe
sannan ya dunkule hannayensa biyu yayi nuni
dasu
izuwa ga kofar yana mai rintse idanu.Faruwar
hakan
keda wuya sai iska mai karfi ta fito daga cikin
hannayensa ta rinka duka kofar dakin tana
jijjigata
kamar zata burma ciki amma sai hakan ya
gagara.Maimakon ma kofar ta bude sai ta maido
masa da iskar hannun nasa ta sureshi sama ta
rinka
katantanwa dashi a sama ya rinka ihu yana
neman
hallaka.Koda ganin haka sai Bakon Jarumin ya
daka
tsalle sama ya riko rigar Sarki Darmanu.Take
iskar
tsafin ta dauke dif sarki Darmanu ya fado kasa
tim.Shi kuwa Bakon Jarumin sai ya diga a kasa
bisa
kafafunsa cikin koshin lafiya.Sarki Darmanu kuwa
saida hancinsa da bakinsa suka kama yoyon
jini.Bakon Jarumin ya dubi Dazyan yayi masa
zance
da hannu sannan Dazyan ya dubi sarauniya
Akisatul
Sauwara da Sarki Darmanu yace shugabana yace
zai
bude muku wannan kofa da izinin ubangijinsa
wato
ubangijin musulunci.Koda jin haka sai Sarauniya
Akisatul Sauwara ta dubi Yarima Lubainu da
Sarki
Darmanu tayi musu kallon ko menene ra'ayinsu?
Duk
su biyun sai suka sunkui da kawunansu
kas.Faruwar
hakan keda wuya sai Sarauniya Akisatul Sauwara
ta
dubi Bakon Jarumi tace mun baka dama.Dajin
haka
sai Bakon Jarumin ya tunkari kofar dakin kai
tsaye
ba tare da shakkar komai ba,da isarsa bakin kofar
sai ya dungureta da dan yatsansa guda
daya.Take
kofar ta bude a hankali tamkar yaro ne karami
wanda
baifi shekara hudu ba ya turata ta bude din.Saida
kofar ta gama wangamewa gaba dayanta sannan
su
Yarima Lubainu suka matso kusa da Bakon
Jarumin
suna leka cikin dakin jikinsu na tsuma saboda
tsoro
da fargabar ko wata masiface zata taso,amma
sai
suka ji shiri kamar maye ya ci shirwa.Koda ganin
cewa su Yarima Lubainu sun kasa shiga dakin sai
Bakon Jarumin ya juyo ya dubi Dazyan yayi masa
inkiya.Take Dazyan ya rugo ya bishi a baya,suka
kunna kai izuwa cikin dakin su biyu,ba tare da
fargabar komai ba.Duk da haka sai su Yarima
Lubainu suka kasa shiga dakinDaki ne babba mai
girman gaske tamkar wata karamar unguwa.Babu
komai a cikin dakin face durowa da tebura a jere
a
layi,layi kuma sahu sahu reras,iyakar ganin
idanun
mutum babu iyaka.Akan teburan da durowoyin
kwalabe ne birjik.Cike da RUWAN SIHIRI kala
kala.A
cikin durowoyin kuwa kayan TSATSUBA ne iri iri
kamar kahonni,Layu,Guraye,Kawunan Tsuntsaye
da
sauran sassan jikin dabbobi dana dan Adam dana
Aljanu.Shi kansa bakon jarumin daya shigo cikin
wannan daki saida ya cika da mamakin irin
abubuwan dake cikinsa da yadda akayi aka iya
tarasa.Koda Ya ga sun dan jima a ciki amma su
Sarauniya Akisatul Sauwara sun kasa biyosu
izuwa
ciki sai ya dubi Dazyan yayi masa maganar
kurame.Take Dazyan ya juya da baya ya ruga
waje
yace da su Yarima Lubainu maigidana yace ku
cire
tsoron komai a cikin ranku ku shiga ciki saboda
kune kuka san abinda kukazo nema,kuma akwai
rubuce rubucen sihiri da yawa a cikin dakin a
jikin
abubuwa da yawa wadanda ba zamu iya
karantasu
ba mu fahimta.
Koda jin haka sai Sarki Darmanu yayi wuf ya
wuce
gaba ya shige cikin dakin.Koda Ganin haka sai
Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu
ma
suka bi bayansa da sauri.Shima dan wada
Dazyan
sai ya bisu da sauri sukaje suka riski bakon
jarumin
a tsaye a cikin tsakiyar daki.Da isarsu Dazyan ya
dubesu yace maigidana yace ya baku damar ku
dudduba ko za kuga abinda kukazo nema.Koda
jin
haka sai duk su ukun suka rarrabu suka rinka
bude
durowoyi suna duba kan tebura.Saida suka shafe
sama da sa'a daya da rabi suna neman ALLON
SIHIRIN Boka Darbusa amma basu ganshi
ba.Al'amarin dayai matukar dugunzuma
hankalinsu
kenan suka rasa abinda yake musu dadi a
duniya.Koda Bakon Jarumi yaga yadda hankalinsu
ya tashi sai mamaki ya turnukeshi yace a
ransa"Hakika iska na yawo da mai kayam kara!
Yanzu fa saboda kwadayin abin duniya ne yasa
wadannan mutane idanunsu suka rufe akan
neman
wannan ALLON SIHIRI?A cikinsu ma babu wanda
yafi
cancanta a taimakawa sama da Yarima
Lubainu,domin shine wanda aka zalunta kuma
ake
neman salwantar da rayuwarsa".Koda gama
Aiyana
hakan a cikin ransa sai bakon Jarumi ya tafa
hannayensa sau uku.Koda jin sautin tafin sai
Yarima
Lubainu,Sarki Darmanu da Sarauniya Akisatul
Sauwara suka tsaya cak ga barin binciken da
sukeyi
suka dawo inda yake tsaye.Da zuwansa sai dan
wada Dazyan ya dubesu yace,maigidana yace
tunda
dai kun kasa gano inda wannan ALLON SIHIRIN
yake
to shi zai bincikoshi da yardar ubangijinsa.Cikin
alamun karayar zuciya Akisatul Sauwara tace
shike
nan mun amince ya dauko ALLON SIHIRI.Koda
jin
haka sai Bakon Jarumin ya nufi inda jerin
durowoyin
suke.Har yabi layi na farko domin ya fara
bincikawa
sai ya tsaya cak,ya kirga layi na tara ya shiga
yana
kirgasu saida yazo kan durowa ta tara sannan ya
tsaya cak ya dubeta da kyau.Babu kofa a jikin
durowar kuma a rife take ruf.Babu alamar akwai
wani
abu a jikinta inda za'a iya budewa har aga abinda
ke
cikinta.Kawai sai ya daga hannunsa ya doki
tsakiyar
durowar take ta wargaje,ai kuwa sai ga ALLON
SIHIRI
kaso na uku a cikinta.Koda Yarima Lubainu,Sarki
Darmanu da sarauniya Akisatul Sauwara sukayi
arba
da wannan ALLON SIHIRI sai suka cika da
tsananin
mamaki.Kawai sai Sarki Darmanu da Sarauniya
Akisatul Sauwara suka yunkura cikin bakin zafina
nama duk su biyun a lokaci guda suka kaiwa
ALLON
SIHIRIN cafka,kowannansu na kokarin yariga
dayan
dauka,amma sai bakon jarumin yayi caraf ya
rigasu
dauka ya dubesu cikin murmushi yace,ai dama
nasan cewa sai hakan ta faru a tsakaninku.Da
zancen kurame yayi wannan bayani kuma Dazyan
ne
yayi musu jawabin.Bakon jarumin ya cigaba da
cewa
Kunga wannan ALLON SIHIRI dakuke gani duk
wanda
ya hada gudu uku a cikinsu bai isa ya iya rikeshi
ba
a hannunsa daidai da tsawon dakika goma
ba,amma
idan kuma shakkar hakan ku kawo ragowar bari
biyun dake hannunku kuga zahiri.Koda jin wannan
batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki
Darmanu suka kama muzurai suna duru duru
suka
kasa miko Allunan Sihirin nasu.Koda ganin haka
sai
Bakon Jarumi yayi murmushi kawai sai ya ajiye
ALLON SIHIRIN Boka Darbusa a tsakiyar dakin ya
koma gefe daya zura musu idanu.Nanfa
Sarauniya
Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu suka kama
Kallon juna kuma suna kallon wannan ALLON
SIHIRI.Nan take kowannensu ya zaro nasa Allon
Sihirin kuma lokaci guda sai kowannensu ya daka
tsalla ya kaiwa Allon Sihirin Boka Darbusa
cafka.Ai
kuwa sai hannayensu suka cafki Allon Sihiri a
lokaci
guda.Nan fa suka mike tsaye a tare suka kama
naushin juna kowannensu na kokarin ya kwace
Allunan biyu ya hade da nasa.Gashi dai
kowannensu
yana dakuwa domin naushin junansu sukeyi a
fuska
da ciki amma saboda naci sunki yarda su saki
ALLON SIHIRIN.Shi kuwa Yarima Lubainu dama
ya
koma gefe daya ya zuba musu idanu kawai yana
jiran yaga yadda karshen al'amarin zai
kasance.Bakon Jarumin da dan wada Dazyan
kuwa
sai suka kara matsawa can gefe daya suka
zauna
akan wata doguwar kujera suna morewa
idanunsu
da kallon fadan da akeyi.Sarauniya Akisatul
Sauwara
da Sarki Darmanu na cikin kwarmazuwa sai
kawai
suka ga wata irin GUGUWA ta shigo cikin
daki.Nan
take ta suri komai na cikin dakin har da Sarki
Darmanu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima
Lubainu tayi sama dasu ta rinka gwara kansu a
jikin
bango.Amma bakon Jarumi da dan wada Dazyan
kuwa ko kusa dasu wannan guguwa batazo ba
kuma
suma suka ki suyi wani motsi suka cigaba da
zuba
idanu kawai.Cikin yan dakiku kadan su Yarima
Lubainu suka jigata suka fita daga
hayyacinsu.Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki
Darmanu basu san Sa'adda suka saki duka
Allunan
Sihirin uku ba suka fado kasa.Faruwar hakan
keda
wuya sai Allunan Sihirin suka hade waje guda
suka
manne da juna tamkar ba'a taba rabasu ba suka
zama babban Allo guda daya.Faruwar hakan
keda
wuya sai wannan guguwa ta rikide ta zama
wadansu
irin SAMUDAWAN BAKAKEN ALJANU dauke da
muggan MAKAMAN YAKI.Nan fa samudawan
bakaken aljanun suka ruguntsume da masifaffen
azababben yaki a tsakaninsu,ya zamana cewa
kowannensu na kokarin ya dauki ALLON SIHIRI
ya
gudu dashi amma duk wanda hannunsa yaki kan
ALLON SIHIRI sai kaga an dankara masa SARA
ko
SUKA ko kaga an mangareshi ya fadi can gefe
daya
sumamme,ko kallonsa babu mai yi saidai ma
acigaba da tattakeshi a kokarin gwagwarmayar
daukar ALLON SIHIRIN.Tunda aka watsar dasu
Sarauniya Akisatul Sauwara gefe daya a
galabaice
suka kasa mikewa tsaye suka cigaba da zama
dirshen a kasa suna kallon wadannan Aljanu
kawai
suna ganin masifaffan yakin da ake yi tsakanin
wadannan samudawan bakaken aljanun.Su kansu
sun san cewa basu isa su iya tarar wadannan
aljanu
da yaki ba bare su iya karbar wan
Nan ALLON SIHIRI daga hannunsu.Saida aka
shafe
sama da sa'a biyu da rabi ana yin wannnan
azababben yaki ya zamana cewa da yawa daga
cikin
aljanun sun zama nakasassu wasu ba
hannaye,wasu
ba kafafu,wasu ma an datse rabin jikinsu,amma
saboda taurin rai irin na aljanu basu fasa cigaba
da
kokarin daukar ALLON SIHIRIN BA.Koda bakon
jarumi yaga ana ta bata lokaci amma an rasa
wanda
zamo GWARZON JARUMIN da zai iya daukar
ALLON
SIHIRIN sai kawai ya mike tsaye zumbur daga
inda
yake tsaye yana mai kwalla KABBARA ya falfalo
da
gudu izuwa inda akeyin wannan gumurzun
yako.Da
karfin tsiya ya ratsa ta tsakiyar samudawan
bakaken
aljanun yana bankesu suna zubewa kasa tamkar
yana sassabe a gona.Koda yazo tsakiyar aljanun
sai
ya sake saka tsalle sama izuwa inda Aljanun
sukayi
tsiri sama wani kan wani domin sukai izuwa kan
wani Gansamemen Aljani mafi tsawo,kauri da
Kirar
SADAUKANTAKA wanda shi ne ya sami nasarar
cafe
ALLON SIHIRIN ya bude fuka fukansa yai sama
da
niyyar ya gudu,amma sai wadansu daga cikin
aljanun suka ruko kafafun nasa suna janyoshi
kasa
don ya fado,amma sai suka kasa saboda
tsananin
karfin damtsensa.A haka sadaukin Aljanin ya
cigaba
da fuffuka yana kai yakushi SARA DA SUKA da
faratan kafafuwansa.Lokacin da bakon jarumin ya
daka tsalle a sama tamkar an harboshi daha
cikin
baka sai da ya iso inda basamuden sadaukin
aljanin
yake,yana isowa daidai fuskarsa sai ya takarkare
ya
zabga masa wawan naushi a fuska.Saboda karfin
naushin take karan hancin aljanin ya karye ya
kurma
uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da
yaji.Nan take ya dimauce bai san sa'adda ya
saki
ALLON SIHIRIN ba.Caraf sai bakon jarumin ya
cafe
Allon Sihirin da hannu daya alhalin su kansu
samudawan aljanun basa iya daga Allon Sihirin
da
hannu daya saboda tsananin nauyinsa.Koda
Aljanun
suka ga wannan bil'adama ya karbe ALLON
SIHIRIN
sai sukayi caa!a kansa suka yanyameshi suna
masu
kai masa sara da suka ta ko ina domin su
hallakashi.Ai kuwa sai ya tarwatsa su a lokacin
da
ya sake kwalla Kabbara ya zare takobinsa cikin
bakin zafin nama ya shiga kare kansa gami da
maida martani.Wohoho!wanda Allah ya kare yafi
gaban Magauta!Duk da tsananin yawa na
wadannan
samudawan bakaken aljanu da tsananin karfin
damtsensu da mugayen makamansu sai gashi
bakon jarumi ya zame musu ALAKAKAI,Sai gashi
yayi musu mummunar barnar datafi wacce
sukayiwa
kansu,domin kuwa duk aljanin da yayiwa duka
daya
tofa idan ya baje a kasa wanwar da kyar ma
yake iya
numfashi wasu ma kamar sun zama gawa.Kai!da
bala'i yakai bala'i sai gashi aljanun suna cika
wandunansu da iska suna ficewa daga cikin
dakin
da gudu.Kafin a jima duk sun tarwatse sun fice
daga
cikin dakinsu duka sun bar bakon jarumin shi
kadai
a tsaye rike da ALLON SIHIRIN a lokacin da dakin
yayi tsit tamkar babu wani mutum daya mai rai a
cikinsa.Yarima Lubainu,Sarauniya Akisatul
Sauwara
kuwa saboda tsananin mamaki bisa ganin irin
gagarumar jarumtakar da bakon jarumin yayi sai
suka kura masa idanu kawao suka kasa budar
baki
suce wani abu,kai mikewa ma tsaye sai ya
gagaresu.Koda ganin haka sai bakon jarumin ya
dubi dan wada Dazyan yayi masa wata inkiya,shi
kuma sai ya dubi Sarauniyar Akisatul Sauwara da
Sarki Darmanu da Yarima Lubainu
yace,Maigidana
yace bazai baiwa dayanku wannan Allon Sihiri ba
face an zauna an tattauna kuma koda ma ya
baiwa
dayanku shi bazai sami damar karantashi ba bare
har ya cika burinsa saboda masu farautar Allon
Sihirin suna da yawa kuma sunfi ku karfin damtse
dana Sihiri.Wadannan Bakaken Samudawan
Aljanu
da sukazo yanzu maigidana ya fatattakesu Yaran
Boka Darbusa ne anan gaba kuma akwai sauran
Manyan MATSAFAN DUNIYA da MANYAN
JARUMAI
dazasu fito farautar wannan ALLON SIHIRI.Kuma
shi
kanshi Boka Darbusa ba hakura zaiyi ba zai
cigaba
da kokarin karbarsa ne.Yanzu sai kowa yaje ya
nemi
dakin da zai kwanta a cikin wannna fada domin
ya
huta tunda dare yayi in yaso gobe da safe mu
tattauna akan abinda muke ganin cewar shi ya
kamata ayi.Gama fadin hakan keda wuya sai
Bakon
Jarumin ya juya domin ya fice daga cikin
wannan
daki,amma sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi
wuf,ta mike tsaye kuma tayi gyaran murya
tace,yakai
wannan JARUMIN JARUMAI kayi sani cewa mu
muna
cikin tsoro da fargaba don haka bazamu iya
sakin
jikinmu ba har mu kwanta a cikin wannnan fada
ta
Boka Darbusa mu iya kwana a cikinta saboda a
ko
yaushe zai iya kawo mana ZIYARAR BAZATO ya
cutar damu.Koda jin wannan jawabi sai Bakon
Jarumin yaji kamar ya bushe da dariya amma sai
ya
dake ya dubi dan wada Dazyan yayi masa zancen
kurame.Nan take Dazyan ya dubi Sarauniya
Akisatul
Sauwara yace,ashe bakuyi mamakin yadda
shugaban
ya iya yakar Boka Darbusa ba da dukkan
Aljanunsa?
Shin bakuyi mamakin yadda ya gano inda Allon
Sihirinsa yake ba ya daukoshi kuma har ya hana
wasu saceshi?To ku sani cewa zamanku anan
cikin
wannnan gida tare da shugabana shine kadai
abinda
zai baku kariya amma da zarar kun fita daga nan
to
fa komai zai iya faruwa a gareku,kuma abune
mayuwaci dayanku ya iya tsira da rayuwarsa
bare
har ya sami damar cika burinsa.Koda gama fadin
hakan sai Bakon Jarumin ya saba ALLON SIHIRI
a
hammatarsa ya juya ya fice daga cikin wannan
daki
Dazyan na biye dashi.Koda ganin haka ai
Sarauniya
Akisatul Sauwara,Yarima Lubainu da Sarki
Darmanu
suka bishi da sauri cikin alamun tsoro suna ta
waige
waige,gani suke kamar ma a koda yaushe Boka
Darbusa ko wakilinsa zasu iya kawo musu hari a
ko
yaushe. kuyi hakuri dangane da jinkirin post yauALLON SIHIRI
Littafi na Uku (3)
Part D
LOKACIN da Bakom Jarumi ya fita daga cikin
wannan daki na kayan sihirin Bokab Darbusa sai
ya
tunkari inda turakarsa ta barci take,kai tsaye sai
kace
dama can yasan kowanne lungu da sako na
gidan.Da isowarsa kofar turakar sai ya tsaya cak
sannan ya juyo baya.Take yayi arba dasu
sarauniya
Akisatul Sauwara suna biye dashi.Cikin matukar
mamaki ya dubesu sannan ya dubi Dazyan sukayi
magana kamar yadda suka sabaDazyan ya dubi
su
Sarauniya Akisatul Sauwara yace shugabana
yace na
gaya muku ba zai taba yiyuwa ba ya kwana da
dayanku a cikin daki guda ba,shi kadai zai
kwanta a
cikin wannan turaka tare da ALLON SIHIRI,don
haka
ya zama wajibi kowannenku ma yaje ya nemi
inda
zai sa hakarkarinsa.Kuma yace lallai ku kwantar
da
hankalinku tamkar tsumma a randa,yayi muku
alkawarin cewar babu abinda zai taba lafiyar
jikinku
koda kuwa kwarzane guda da izinin
ubangijinsa.Koda gama fadin hakan sai Bakon
Jarumi ya shige cikin turakar ya janyo kofar ya
rufeta ruf ya bar Dazyan tsaye sororo a kofar
dakin
tare dasu Sarauniya Akisatul Sauwara,suma sunyi
cirko cirko suna mamakin bakon jarumin.Abinda
ya
fara fado musu arai shine."Menene dalilin dayasa
bakon Jarumin bazai iya kwana tare dasu ba a
cikin
daki guda?Kuma menene dalilin dayasa duk a
tsawon wannan lokaci bai yarda anga fuskarsa
ba?
To waishin ma shi Namije ne ko Mace?Lallai
akwai
bukatar su tantance hakan domin su san hanyar
dazasu bi su rabashi da ALLON SIHIRI.Sarauniya
Akisatul Sauwara ta dubi dan wada Dazyan tace
ashe maigidan naka ma bai yarda da kai ba
tunda ya
kasa kwana tare dakai a cikin daki guda?Koda jin
wannnan batu sai Dazyan ya takarkare ya bushe
da
dariya lokaci guda kuma yace yake wannan
sarauniya kiyi sani cewa ni kaina bansan ko waye
maigidana ba,ban san matsayinsa ba ko
asalinsa,hasalima haduwata dashi bata wuce ta
shekara uku ba,kuma a tsawon wannan lokaci
ban
taba ganin fuskarsa ba,kuma ban taba jin
muryarsa
ba bare kuda kuka hadu dashi a yau din
nan.Shawarar da zan baku kawai itace,ku yarda
da
duk abinda kukaji ya fada,kuyi imani dashi,in ba
haka ba kuwa karshenku shine NADAMA gami da
yin MUMMUNAN KARSHE!Nidai yanzu zanje na
nemi
inda zan kwanta saboda na gaji likis kuma nima
barci nakeji.Amma maigidana yace na shaidawa
miki
ke Sarauniya Akisatul Sauwara cewa lallai kema
ki
ware dakinki ke kadai domin a ka'idar addininmu
haramun ne kiyi cudanya da mutanen da basu
kasance muharramanki ba.Koda gama fadin haka
sai
dan wada Dazyan ya hango wani karamin daki
dake
can gefe daya wanda kofarsa ke bude
wanwar,kawai
sai ya tafi izuwa cikin dakin ya kunna kai
ciki.Koda
ganin haka sai Sarki Darmanu ya bishi da
sauri.Ita
kuwa Sarauniya Akisatul Sauwara sai ta tsaya ta
kama duru duru ta rasa dakin dazata shiga.Daga
can
kuma sai ta nufi wani babban daki wanda
kofarsa ke
rufe.Da isarta sai tasa hannunta ta murda
kofar,bisa
mamaki sai taga kofar ta bude da
kanta.Sarauniya
Akisatul Sauwara ta kunna kai izuwa cikin
daki.Tana
shiga sai kanta ya daure tamau ta kamu da
tsananin
mamaki,ba don komai ba sai saboda ganin irin
kayan kawar dake cikin dakin.A tsakiyar dakin an
ajiye wani lumtsumen gado mai girman gaske
wanda
aka cikashi da kayan taushi na alfarma.Sannan
kuma akwai kofar kewaye a cikin dakin.Sarauniya
Akisatul Sauwara ta leka cikin kewayen shima
taga
an kawatashi da bahon wanka na zinare.Kawai
sai ta
koma falon tayi tsalle ta fada kan wannan
luntsumemen gado cikin jin dadin huce
gajiya.Amma
kuma har a sannan raunikan jikinta basu daina yi
mata dan zogi da radadi ba.Nan take Sarauniya
Akisatul Sauwara ta fada kogin tunani.
¤P¤H¤Y¤S¤I¤C¤I¤S¤T¤
AL'AMARIN Yarima Lubainu kuwa,bayan yaga
kowa
ya shige cikin daki an tafi an barshi shi kadai a
tsaye sai ya kama yawo a cikin gidan yana
neman
dakin dazai shiga ya kwanta shi kadai.Ba don
komai
yake son ya sami inda zai kwanta ba shi kadai
sai
saboda ya sami damar dazai zauna yayi tunani
da
nazari ya yankewa kansa shawarar da zata
fissheshi.Da yake wannan fada ta Boka Darbusa
tana
da tsananin girma tamkar gari guda,kuma gashi
anyi
gine gine da yawa a cikinta na kawa,sai Yarima
Lubainu ya rude ya rasa ma bangaren dazai
shiga
domin da yayi yunkurin shiga wani dakin saiya
hango wani wurin wanda ya fishi kyau da
kawa.Yana
cikin wannan kai kawo ne ya shigo wani bangare
dabam na musamman wanda aka killaceshi a
wuri
mai ban al'ajabi.Shi dai wannan wuri ya kasance
tamkar lambu kuma an kewayeshi da katangar
zinare,sannan an zuba shuke shuke na 'ya'yan
itatuwa na marmari kala kala ga kuma tsuntsaye
masu kyau ababan sha'awa kuma kofar wannna
lamby a bude take.Har Yarima Lubainu ya gifta
kofar
zai wuce gaba sai ya jiyo shesshekar kuka cikin
muryar MACE!Al'amarin dayai matukar bashi
mamaki kenan,domin a zatonsa bandashi dasu
bakon jarumi babu sauran wani mahaluki a cikin
wannan gida.Yarima Lubainu ya dawo da baya ya
tura babbar kofar kambun ya kunna kai ciki.Yana
shia sai ya kame,idanunsa suka zazzaro
sakamakon
abinda yayi arba dashi.Ba komai ne abinda yayi
arba
dashi din ba face wata zabgegiyar kyakkyawar
Budurwar ALJANA a daddaure cikin wata
murtukekiyar sarkar tsafi waccce ta kanannade
hannayenta,kafafuwanta da sauran sassan
jikinta,kuma sarkar an zagayata ne a jikin wata
dirkar tsafi mai tsananin kaurin gaske wacce fiye
da
rabinta ya nutse a cikin karkashin kasa.Abin daya
daurewa Yarima Lubainu kai dangane da wannan
Aljana shine ko a bakin masana labarai bai taba
jin
cewar akwai halitta mai siffarta ba.Rabin jikinta
na
bil'adama ne,daga kasan cibiyarta zuwa
kanta.Daga
gwiwar kafafunta zuwa tafin
kafafunta kuwa na Aljanu ne.Kash!in badon
wannan
ratsin siffa ta Aljana ba dake jikinta da Yarima
Lubainu zai iya cewa duk duniya babu wata 'YA
MACCE mai kyan wannan budurwa ba.Koda
Yarima
Lubainu ya hada idanu da wannan budurwa yaga
idanunta sunyi sharkaf da hawayemkuma gata a
daure cikin sarka,sai nan take yaji ya kamu da
tsananin tausayinta.Amma da ya tuna cewa nan
fa
gidan Boka Darbusa ne babu mamaki ma wani
tuggun ne aka shirya musu aka ajiye wannan
Aljana
domin su fada tarkon wahala,sai kawai ya juya
da
nufin ya fice daga cikin lambun,kawai sai yaji
aljanar
ta budi baki cikin murya mai zaki da bai taba jin
irinta ba kuma mai tsananin taushin gaske
tace,haba
yakai Yarima Lubainu,ya ya kai daka kasance
mai
tausayi da jin kai zaka tafi ka barni a cikin
wannan
hali?Ka sani cewa shekara uku kenan wannan
azzalumin Boka Darbusa na tsare dani anan,ina
jiran
ranar da zakuzo ku koreshi daga cikin wannan
fada
ku ceceni.Koda jin wannan batu sai mamaki ya
sake turnuke Yarima Lubainu ya dubi Aljanar
cikin
alamun rashin yarda yace,wace ce ke kuma ya
akayi
kika sanni har kika san cewa zamu zo wannan
fada
mu kori Boka Darbusa?Sa'adda aljanar taji
wadannan
tambayoyi guda biyu ko uku sai hawaye ya zubo
mata,tace ni sunana BADI'ATUL SARIRA,Kuma
nice
'ya guda daya jal a wajen mahaifina Sarkin
Bokayen
Aljanu na duniya kaf,wato ZARHASU IBINI
SAMBILA.A cikin wannan duniya kaf in banda
Boka
Darbusa babu wani mahaluki daya kai mahaifina
karfin sihirin tsafi da kuma tarin sirrikansa.Loka
cin
da mahaifina da Boka Darbusa suka gano cewa
karfinsu yazo daya a sirrin tsafi sai suka zamo
manyan ABOKAN GABA ya zamana cewa
kowannensu na kokarin ya hallaka dayan ya
rabashi
da dukkan sirrikan tsafinsa.Asalin wannan ALLON
SIHIRI da kuka daukoshi a dakin tsafin Boka
Darbusa
a hannun mahaifina yake,daga baya ne bayan
Boka
Darbusa ya samu nasarar kashe shi ya
daukeshi.Ba
komai ne yasa Boka Darbusa yaki kasheni ba ya
daureni anan face cewa koya hada ragowar bari
biyun na ALLON SIHIRI dana Mahaifina bazai iya
cika
burinsa ba face nidin nan na karanta masa
wadansu
dalasiman tsafi dake jikinsa na fassara masa su
yadda zai fahimta,saboda yaren a akayi rubutun
dashi a jikin Allon Sihirin mahaifina ni kadai ce na
iya shi a duk fadin duniya,saboda mahaifina ne
ya
kirkireshi kuma tun ina yarinya karama ya koya
minshi.Ina mai rokonka daka taimakeni ka
kwanceni
daga cikin wannan sarka yanzu in dai kayi min
haka
ni kuma nayi maka alkawarin cewa zan iya raba
bakon jarumi da wannan ALLON SIHIRI,a cikin
dakika
daya jal,sannan na daukeka na kaika KOGIN
BAHAR
IMFAL a cikin abinda baikai rabin sa'a ba mu
shiga
cikin karkashin kogin na tsinko maka dan itaciyar
dazaka sha ka warke daga cutar da YARIMA
MANGUL ya sanya maka ka dawo cikakken da
namiji
ka koma ga matarka,babbar masoyiyarka
YAZARINA
ku fara sabuwar rayuwar aure cikin farin
ciki.Ladan
wannan aiki nawa kawai shine ka bar min
wannan
ALLON SIHIRI.Koda Aljanar tazo nan a jawabinta
sai
hankalin Yarima Lubainu ya dugunzuma ainun ya
rasa irin amsar da zai bata.Abinda ya fado masa
a
rai shine,shin zai iya yarda da wannan Aljanr
kuwa?
To ai idan ma ya yarda da ita kamar yaci amanar
su
Sarauniya Akisatul Sauwara ne!
WACE IRIN SHAWARA YARIMA LUBAINU ZAI
YANKE
AKAN WANNAN DAMA DA YA SAMU?
MAI ZAI FARU TSAKANIN SU SARAUNIYA
AKISATUL
SAUWARA DA BAKON JARUMI IDAN GARI YA
WAYE?
WANE HALI BOKA DARBUSA YAKE CIKI BAYAN
YA
FALFALA DA GUDU IZUWA CIKIN DAJI BAYAN
SUN
FAFATA AZABABBEN YAKI SHI DA BAKON
JARUMI
DON YA TSIRA DA RAYUWARSA?
WANENE BAKON JARUMIN DAYA BAYYANA?
YAUSHE YARIMA YAKE CIKA BURINSA NA
SAMUN
LAFIYA DAGA LALURAR DA YAKE CIKI?
WAISHIN INA LABARIN YARIMA MANGUL?
WAYE ZAI MALLAKI ALLON SIHIRI.
Mu hadu a littafi na hudu(ALLON SIHIRI-4)don jin
cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari.
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also

1 Comments On ALLON SIHIRI 1 TO 9
avatar
abdulazeez

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment