Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da suka shafe sa'a hudu da rabi
suna
tafiya ba tare da sun yada zango ba sannan
Yarima
Lubainu ya matso kusa da Sarauniya Akisatul
Sauwara,da yake dama itace akan gaba tana yi
musu jagora a cikin tafiyar ya dubeta
yace,waishin
tafiyar kwana nawa zamuyi ne mu riski Birnin da
muka nufa?Koda jin wannan tambaya sai
Sarauniya
Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,ni kuwa
dadina
dakai kenan ka cika zumudi da gaggawa.Ai idan
kayi
hakuri idanunka zasu nuna maka.Koda gama
fadin
hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi shiru
bata
kara cewa uffan ba har suka sake shafe sa'a
hudu
suna tafiya.A sannan ne dare ya riskesu suka
yada
zango a bakin wani katon dutse.Anan suka
kwana
kashe gari suka sake yin shiri suka ci gaba da
tafiya.Saida suka shafe kwana bakwai cur basu
riski
wani gari ba kuma basu hadu da wani mugun
abu
ba,kawai dai suna ratsawa ne ta cikin mugayen
dazuzzuka.Duk inda suka hadu da wadansu
mugayen dabbobi ko kwaruka saidai kaga sun yi
musu kwaf! daya.Kai ko mugayen Aljanu ne suka
hadu dasu saidai kaga Aljanun sun gudu sunyi ta
kansu don sun san cewa WUTSIYAR RAKUMI
TAYI
NESA DA KASA!Kuma RUWA BA SA'AN KWANDO
BANE.A ranar kwana na bakwai ne da rana tsaka
Yarima Lubainu ya hango wani babban gari a
gabansu wanda kawatuwarsa ta ninka ta birnin
Rauhul Bagadar sau uku wato birnin sarauniya
Akisatul Sauwara.Tun daga nesa Yarima Lubainu
ya
wangame baki kamar dan kauye yana kallon gine
ginen birnin cikin al'ajabi.Koda Sarauniya Akisatul
sauwara ta lura da halin da yake ciki sai ta
bushe da
dariya tace,haba ya kai Lubainu kada ka bani
kunya
mana,ai baka ga komai ba ma sai mun shiga
cikin
birnin tukunna.Koda jin wannan Batu sai Yarima
Lubainu ya sake cika da mamaki yace,waishin
yanzu
kina nufin wannan birnin da zamu shiga shine
Birnin
Kimras inda sarki Darmanu yake mulki inda zamu
samu barin Allon Sihiri na biyu?Akisatul Sauwara
ta
jinjina kai tace kwarai kuwa amma abinda nakeso
dakai shine ka nutsu kada kayi komai da kanka
sai
abinda kaga nayi ko wanda na umarce ka dakayi
saboda Sarki Darmanu ba karamin shaidanin
Mutum
bane.A yanzu haka maganar nan da mukeyi
nasan
yana kallonmu kuma yana jinmu,kuma zai iya yin
wani abu domin ya cutar damu,don bani da
tabbacin
cewar zai bamu hadin ka bisa bukatar da muka
zo
masa da ita.Tabbas Sarki Darmanu ya fini karfin
Sihirin tsafi,amma fa a bangaren jarumtaka da
iya
yaki KARE JINI BIRI JINI mukeyi.Sau tara muna
fafatawa ni dashi ba tare da wani yayi nasara a
tsakaninmu ba amma fa muna matukar jin
jiki.Bisa
sa'a ne kawai na samu na tsira daga sharrin
tsafinsa
sabodatsarin dana samu tun daga
kakannina.Lokacin da Sarauniya Akisatul Sauwara
tazo daidai nan a zancenta suna daf da shiga
cikin
birnin ne,Kwatsam!sai suka ga wani mutum
Tsoho
tukuf ya fito dafa cikin gona goye da kara a
bayansa,shima zai shiga cikin birini.Cikin Ladabi
Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu
suka
gaishe da tsohon.Kawai sai tsohon ya kare musu
kallo ya lura cewa baki ne don haka saiya
dubesu
yace,yaku wadannann matasa hakika ku baki ne
a
garin nan ko?Akisatul Sauwara tace,Baba
zancenka
dutse ne.Tsohon ya dubi Sarauniya Akisatul
Sauwara cikin yanayi
mai nuna tausayi yace,Yarinya bisa yanayinku da
gani kun fito daga babban gida kuma kun sami
tarbiya mai kyau,saboda haka zan taimakeku don
kada ku fada cikin tarkon maketacin
sarkinmu.Ina
mai sanar daku cewa bisa al'adar wannan mugun
sarki namu duk bakon daya shigo garin nan
kamashi
ake yi a kwace duk abinda ya mallaka a kaishi
kurkuku a kulle ko kuma ayi masa dukan kawo
wuka sai idan yana da sauran shan ruwa a
duniya
sannan zai tsira da rayuwarsa.Yanzu zan taimake
ku
ba bi daku ta barauniyar hanya inda babu wanda
zai
ganku harmu isa gidana inda zaku kwana,in yaso
indan gari ya waje sai ku saje da 'yan gari ku
aiwatar da abinda ya kawoku.Tsohon na gama
fadin
hakan kuma sai ya dubi Yarima Lubainu
yace,idan
sarki ya kyallara ido yaga wannan kyakkyawar
'yar
uwar taka saiya rabaka da ita har abada.Koda jin
haka sai Yarima Lubainu ya gyada kai yana mai
jinjina al'amarin ba tare da yace kala ba.Nan dai
tsoho ya wuce gaba suka bishi a baya yana mai
bin
wata barauniyar hanya wacce tabi bayan
birnin.Su
kuma suka ci gaba da jan limzamin dawakansu a
hankali suna yin tafiyar san'da suna waige waige
cikin rashin yarda da kwanciyar hankali.Lokacin
da
suka yi 'yar doguwar tafiya ya zamana cewa
tsohon
yana gabansu da tazara ta a kalla taku goma sha
biyar sai Yarima Lubainu ya dubi Sarauniya
Akisatul
Sauwara yayi mata magana cikin karamar murya
yace,nifa ban yarda da wannan tsohon ba,domin
zai
iya zama dan leken asirin Sarki Darmanu ne aka
turoshi ya yaudare mu ya cutar damu.Koda jin
wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara taji
zuciyarta ta buga da karfin gaske,take tsoro ya
baibayeta kuma taji ta gamsu da tunanin da
Yarima
Lubainu yayi,don haka sai kawai taja linzamin
dokinta ta tsaya cak!shima Yarima Lubainu sai
ya
tsaida nasa dokin suka kurawa tsohon idanu
kawai
yayin da yake ci gaba da tafiya.Koda tsohon yaji
sautin sauwun dawakansu Lubainu ya dauke a
bayansa sai shima ya tsaya cak ya juyo da sauri
cikin alamun mamaki ya dubi su Lubainu yace
'ya'yana lafiya kuwa kuka tsaya a baya haka
kuka
daina tafiya?Caraf sai Sarauniya Akisatul
Sauwara ta
dubi tsohon ta daka masa tsawa tace,kai tsohon
banza!bakin mayaudari na gane ko kai
waye.Maza
ka bayyana surarka ta gaskiya domin mu
tattauna
bisa abinda ya kawomu birninka.Lokacin da
tsohon
yaji wannan batu na sarauniya Akisatul Sauwara
saiya bushe da mahaukaciyar dariya cikin karfin
murya mai nuna cewa lallai ba muryarsa bace ta
tsoho.Daga can kuma sai yayi girgiza na take ya
rikide ya zama sarki Darmanu cikin gagarumar
shigar yaki.Sarki Darmanu ya kasance katon
mutum
mai kirar sadaukai,gashi dogo zankalele kuma
gashi
kakkaura mai murdadden jiki gami da tarin kwanji
da
jijiyoyi.KALLO DAYA mutum zai masa ya gane
cewar
ya cika sadauki mai TARWATSA MAZA.Wadansu
bakaken kayan yaki ne a jikinsa na karfe.Rigar
dai
Farmaran ce mai budadden hannu,sai dogon
wando
da dogayen takalma duka na bakin karfe.A
hannunsa na hagu kuwa wata katuwar garkuwa
ce
wadda akayi ta da zallan dutsen lu'u lu'u mai
nauyin
gaske wacce sai kato goma sun taru suke iya
rabata
da kasa amma shi ji yake kamar takarda ya
rike.Bayan anyi kallon kallon na tsawon dakika
goma
tsakanin sarki Darmanu dasu sarauniya Akisatul
Sauwara sai Sarki Darmanu ya sake bushewa da
dariyar mugunta karo na biyu sannan ya dubi
sarauniya Akisatul Sauwara yace,ke tsohuwar
abokiyar gaba kiyi sani cewa tun kafin ku baro
birnin ki naga duk abinda ya faru tsakaninki da
Yarima Lubainu dan sarki Sailur har izuwa
sa'adda
kuka taho izuwa nan birnina domin na baku barin
Allon Sihirin dake hannuna.Tabbas dake dashi
kuma
sami tabin hankali har da kuke tunanin zan
karbeku
hannun bibbiyu na yarda da bukatarku.Kisa sani
cewa na dade ina jiran irin wannan rana wacce
zakuyi gangancin dauko barin Allon Sihirinki ki
taho
har izuwa birnina domin tuni nayi bincike na
gano
yadda zan iya fidda Allon daga cikin kwalbar
dakika
adanashi.Kin ga kenan yanzu na sami tsuntsu
daga
sama gasasshe tunda kin kawo kanki.Yanzu zan
hallaku na dauke Allon Sihirin daga jikinki naje na
biya tawa bukatar dashi.Koda gama fadin hakan
sai
Sarki Darmanu yai wuf ya daka tsalle a sama
kamar
an cilloshi daga cikin baka ya kawowa Akisatul
Sauwara da Lubainu mugun sara a sama da duk
su
biyun a lokaci guda.Cikin bakin zafin nama duk
su
biyun suka kaucewa saran suk fado kasa daga
kan
dawakansu,ai kuwa sai takobin sarki Darmanu ta
tsarge dawakan biyu tamkar an yanka tsakiyar
tuffa.Take dawakan suka zube kasa
matattu.Cikin
sauri da dimauta su Lubainu suka mike tsaye
zumbur suna masu zare nasu takubban.Sarauniya
Akisatul Sauwara tayi sauri ta tofawa takobinta
da
takobin Lubainu wani dalasimin tsafi sai
takubban
nasu suka kara kaifi,girma da nauyi.Koda ganin
haka
sai Sarki Darmanu ya rugo da gudu izuwa kansu
suka ruguntsume da azababben Yaki.
(Shegen kaya Uban mayaudara) ,ya
zama cewa yana kai musu sara da suka cikin
bakin
zafin nama da jarumtaka ta ban al'ajabi.Duk da
tsananin jarumtaka irin ta Lubainu data
Sarauniya
Akisatul sai gashi sun raina kansu domin basa
iya
maida martani saidai kokarin kare kansu daga
mugayen hare haren da yake kai musu.Al'amarin
dayai matukar firgita Sarauniya Akisatul Sauwara
ke
nan,kuma ya bata matukar mamaki domin ada
can
ta san cewa karfin damtsenta da iya yakinta yazo
iri
daya sak dana Sarki Darmanu,amma sai gashi
yanzu
labari ya sha bambam.Koda Sarki Darmanu yaga
ya
fisu zafin nama da jarumtaka sai ya kara zage
dantse a kansu ya ci gaba da kuntatasu yana
mai
sauya salon fada,wato ya hada da kai musu
naushi
da hannu da kafa.Faruwar hakan keda wuya sai
ya
fara samun lagonsu.Nan da nan ya hada musu
jini
da majina.Idan ya naushe su a ciki sai cikinsu ya
kulle sunyi ihu sun kife kasa.Idan kuma a fuska
ya
naushe su sai kaga har sama sukeyi suna
fadowa
kasa a galabaice.Maimakon yasa takobinsa yayi
musu kisan gilla sai ya rinka yankarsu a sassan
jikinsu jini na tsartuwa da feshi suna ihu da
kururuwa sakamakon tsananin zafi da zogin da
suke
ji har saida suka sami sama da raunika biyar a
jikinsu.A sannan ne suka zube kasa wanwar suna
numfashi sama sama kamar zasu mutu suka
kasa
koda mikewa tsaye.Koda Sarki Darmanu yaga ya
sami wannan gagarumar nasara sai ya tsaya cak!
a
kansu yana mai kyalkyala dariyar mugunta da
farinciki.Daga can kuma sai ya nufi kan
Sarauniya
Akisatul Sauwara da nufin ya lalube jikinta ya
dauke
wannan Allon Sihirin nata.Kwatsam!ba zato ba
tsammani sai yaji Yarima Lubainu ya gabza masa
mahaukacin naushi a fuska.Saboda karfin
naushin
saida yai tsalle sama da baya yaje ya gwaru da
wata
bishiya ya fado kasa a matukar galabaice a
lokacin
da hancinsa da bakinsa ke yoyon jini.Kafin Sarki
Darmanu ya yunkura ya mike tsaye tuni Lubainu
ya
dako tsalle a sama ya doki cikinsa da guiwar
kafarsa ta dama.Take wani gudan jini yai fitar
burgu
dagacikin bakin Darmanu kawai sai ya koma
kasa
ya baje sumamme.Da kyar da jan ciki Yarima
Lubainu ya karasa inda Sarauniya Akisatul
Sauwara
ke kwance ya rinka yagar rigar jikinsa yana daure
sassan jikinta inda ta sami raunika don tsaida
zubar
jini.In ba don yayi hakan ba cikin gaggawa da
tabbas zata iya rasa rayuwarta.Bayan ya gama
ceton
rayuwarsa sai ya fara kokarin daddaure nasa
raunikan sannan ya sake jan ciki ya koma inda
Sarki
Darmanu ke kwance ya cire dukkan gurayen
tsafin
dake jikinsa ya mai dasu nasa jikin,kuma ya
dauke
takobin sarki Darmanu ya koma can inda Akisatul
Sauwara ke kwance ya taimaka mata ta mike
zaune
ya jingina bayanta a bayan wata bishiya.Faruwar
hakan ke da wuya sai Sarki Darmanu ya farfado
daga dogon suman da yayi.Koda ya bude
idanunsa
yaga babu takobinsa a kusa dashi kuma ya shafa
jikinsa yaji duk babu guraye da layunsa na
tsafi,sai
ya takarkare ya kwarara uban ihu na bakin ciki
da
takaici,amma sai Yarima Lubainu ya tari
numfashinsa yana ma daka masa tsawa
yace,yakai
wannan sarki kayi sani cewa a halin yanzu duk
tasirin tsafinka yana hannuna tunda na mallaki
takobinka da dukkan gurayenka na tsafi.Abinda
nake
so dakai shine ka bamu hadin kai yanzu mu tafi
izuwa fadarka ka kirawo likitocinka suyi mana
magani a raunikan dake jikinmu,sannan kuma ka
bamu hadin kai bisa abinda muka zo nema.Idan
kaki
bin umarnina koka nemi ka shammace mu kayi
mana wani tuggun zan fille maka kai da
takobinka
sannan mu shiga har cikin fadar taka mu bincike
ko
ina da ina har mu gani inda ka boye Allon Sihirin
naka mu daukeshi mu kara gaba.Lokacin da
Yarima
yazo nan a zancensa sai kwallar bakin ciki ta
ciko a
idanun Sarki Darmanu.Bisa dole ba don son
ransa
ba ya mike tsaye ya wuce gaba,shi kuma Yarima
Lubainu sai ya goya Sarauniya Akisatul Sauwara
a
bayansa saboda ba zata iya takawa ba da
kafafunta
suka bi bayan Sarki Darmanu don shiga cikin
Birnin
Kimrasa.Maimakon Sarki Darmanu yabi hanyar
kwarai ta zuwa gidan sarautar tasa sai yabi
wannan
barauniyar hanya saboda kada asirinsa ya tonu
jama'ar gari su gane cewa yau fa AN CI SHI DA
SHI.'Yar gajeriyar tafiya sukayi sai gasu sun bullo
a
wata kofa dake can bayan gidan sarautar.In
banda
Sarki Darmanu babu wani mahaluki wanda yake
bi ta
cikin wannan kofa.Shima yana amfani da kofar
ne
kawai idan zai gabatar da al'amuransa na
sirri.Tun
daga nesa Sarki Darmanu yayi kamar dawo ne
cikin
nasarar samo abokan gabarsa,domin yana tafiya
ne
cikin tunkaho da izza kamar yadda ya saba a duk
sa'adda ya dawo daga rangadi.Nan dai ya wuce
kai
tsaye ta cikin wannan koda ta gaban dakarun
dake
gadi.Duk da cewa dakarun sun fahimci abinda ke
faruwa sai da suka yi mamakin abu daya.Ba wani
abu suka yi mamaki ba face ganin takobin sarki
Darmanu a hannun bakon dazo dashi.Ita dai
wannan
takobi ta Sarki Darmanu ta kasance
sihirtacciya,kuma itace sirrin dukkan karfinsa na
damtse dana sihiri.Ma'ana karfin damtsensa na
zahiri bai kai wanda takobin ke kara masa ba.A
duniya babu abinda Sarki Darmanu ke so sama
da
wannan takobi,kuma babu abinda daya dogara
dashi
sai ita ita.Ganin raunika a jikin Yarima Lubainu
da
Sarauniya Akisatul Sauwara ne yasa hankalon
masu
gadin ya kwanta suka ratsa suka basu hanya
suka
wuce.Koda suka fara tafiya a cikin wannan gidan
sarautar sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta tsaida
Lubainu tace,ya kai Lubainu ka sani cewa kowa
Prince Auwal Auwzab Auwzab
a
gidansa sarki ne,baka tunanin cewa wannan
mutumin bazai iya yaudararmu yanzu a cikin
gidan
nan nasa ya cutar da mu?Koda jin wannan batu
sai Lubainu yayi murmushi yace ki kwantar da
hankalinki yake Akisatul Sauwara ai mun gama
dashi tunda kema kin tabbatar dacewar wannan
takobi itace tasirinsa,ai babu abinda zai iya yi
mana.Sarauniya Akisatul Sauwara tayi ajiyar
numfashi tace hakane amma ka rike takobin
hannu biyu komai rintsi kada ka bari ta subuce
maka.ALLON SIHIRI
Littafi na biyu(2)
Part B
Koda ganin abinda ya faru gareshi sai sarauniya
Akisatul Sauwara ta sake bushewa da dariya a
karo
na biyu.Lokaci guda kuma ta hade fuska tace,ya
kai Lubainu
kamar yadda na gaya maka da farko babu
wani mahaluki walau mutum ko aljan wanda ya
isa
ya dauki wannan Allon Sihiri daga cikin wannan
kwalba face ni.
Koda gama fadin hakan sai Sarauniya
Akisatul Sauwara taje gaban wannan kwalba ta
shafeta da hannunta na hagu.
Take kwalbar ta rabe gida biyu kamar an yanke
lemon bawo.
Kawai sai ta
sa hannunta ta dauko Allon ta dorashi akan tafin
hannunta ta yafito Lubainu da hannu tace
dashi,zo
kaga irin abinda aka rubuta a jikin Allo.Cikin sauri
Lubainu yazo daf da iya ya tsaya ya kurawa
Allon
idanun.
Ai kuwa sai yaga Rubutun a rabe yake gida
biyu.Kuma bazai
taba karantuwa ba a haka face an
jona daya barin Allon na biyu.Kawai sai yayi
ajiyar
numfashin ya dubi Akisatul Sauwara cikin alamun
karayar zuciya yace,
Ai wannan Allon dake hannunki
bashi da wani amfani idan ba'a samo daya Allon
bana biyu.Koda jin haka Sai Akisatul Sauwara
tayi murmushi
tace to ina tabbatar maka da cewa idan
ma an samo Allon na biyu an hada da nawan
rubutun dake jikinsu ba zai karantu ba sai an
hada
dana ukun.Koda gama fadin hakan sai ta mayar
da
Allon cikin wannan kwalbar.
Take kwalbar ta koma
ta manne tamkar bata taba rabewa ba
biyu.Akisatul
Sauwara ta dauke kwalbar ta juya ta fice daga
cikin
wannan gida Lubainu yabita da sauri.
Nan dai suka
yita bin sako sako da lungu lungu har suka dawo
inda turakarta take.Anan ne ta tsaye cak shima
Lubainu sai ya tsaya.
Akisatul Sauwara ta juyo tana mai yi masa wani
kallo mai
dauke da murmushi da
ayar tambaya(?) tace,ai anan zamu rabu ka koma
izuwa masaukinka ka sake hutawa,
amma ina
gayyatarka da yamma a can filin motsa jini na
bayan
turakata domin mu dan motsa gabban jikinmu in
yaso gobe da safe muyi haramar tafiya.
Tana gama fadin hakan ta kunna kai izuwa cikin
turakarta
kuyangi na gyara mata hanya.
Yarima Lubainu ya
juya ya nufi hanyar da zata mayar dashi
masaukinsa
zuciyarsa cike da tunanin wannan kallo wanda
Sarauniya Akisatul Sauwara tayi masa wanda ya
kasa gano ko na mene ne tsakanin SO da tausayi
ko kuma
KAUNA.
Kamar yadda Sarauniya Akisatul
Sauwara ta fada haka al'amarin ya kasance wato
da
yammaci ta tura aka zo dashi izuwa filin motsa
jini
dake bayan turakarta.
Yana isowa wajen sai ya iske
sarauniya Akisatul Sauwara a tsaye cikin shigar
yaki
rike da takobi.
Yana isowa sai shima aka miko masa sulke
takobi da garkuwa.
Ba tare da gardamar komai
ba ya karba ya sanya sulken amma sai yaki
karbar
garkuwar saboda yaga itama Sarauniya Akisatul
Sauwara ta dubi Lubainu tace ina mai
shawartarka
daka dauki garkuwar nan ka rike domin zan iya
baka mamaki.
Lubainu yayi murmushi yace,ai ni dai ke
baki rike garkuwa ba a matsayinki na 'ya mace
nima
ba zan rike ba.
Akisatul Sauwara tace,shi ke nan
muje zuwa mu gani mahaukaci ya hau kura.
Kafin
Yarima Lubainu ya budi baki kara cewa wani abu
tuni Akisatul Sauwara ta zare takobinta ta daka
tsalle ta kawo
masa wawan sara a kafada.
In ba don
Lubainu ya daka tsalle gefe daya ba cikin
tsananin
zafin nama da tuni ta tsargeshi gida biyu.
Nan fa
suka kacame da azababben yaki ta rinka kai
masa
mugayen hare hare da wani irin azababben zafin
nama da karfin gaske wanda yai mutukar bashi
mamaki tun da
yake haduwa da mazaje bai taba
haduwa da mai kamar jarumtakarta ba.
Bisa dole
shima ya zage damtse yaci gaba da kare hare
haren
nata amma sai yaga duk da haka tana neman
kuntatashi,don ta fara turashi jikin bango tana
hanashi yin kyakkyawan motsi yadda ko yay yayi
sakaki zata
iya gamawa dashi.
Nan fa shima ya fara
maida martani,ai kuwa sai yakin nasu ya zama
abin
tsoro abin tashin hankali,hatta kuyangi,borori da
dakarun dake tsaitsaye a zagayen filin saida
hankalinsu ya dugunzuma ainun bisa ganin irin
azababben yakin dasu sarauniya ke yi.
Saida suka dauki dogon lokaci a haka dayansu
bai sami
nasarar
koda shafar jikin abokin gwaminsa ba.
Al'amarin
dayai mutukar girgiza Yarima Lubainu shine ko
alamar gajiya babu a tare da sarauniya alhalin
shi
kuwa ya fara haki
Koda ya fuskanci cewa lallai zaiji
kunya idan baiyi da gaske ba,sai ya sauya salon
fadan ya hada
dakai naushi da bugu.Ai kuwa sai ya
shammaci Akisatul Sauwara ya doki kafafunta da
kafarsa guda tayi sama tana mai katantanwa
amma
tana fadowa kasa sai ta dafa kasa da hannunta
guda
tayi sama kamar sifirin ta doki kirjinsa da
kafarta.Saboda karfin dukan saida Lubainu yayi
tsalle
sama da baya ya fado kasa,amma shima sai yayi
wuf ya mike tsaye Zumbur.
Yana mai gyara tsayuwa
a lokacin da Akisatul Sauwara ta duro kasa bisa
kafafuwanta.Kawai sai ta dubeshi tayi murmushi
tace,tabbas yanzu bani da wata fargana a cikin
tafiyar da zanyi
tare dakai domin na gamsu cewar
kai jarumi ne na kwarai.
Koda jin wannan batu sai
ran Lubainu ya baci daya fahimci cewar sunyi
wannan gumurzu ne don kawai taga iyakar
jarumtakarsa.
Amma sai ya boye fushin nasa bai
nuna mata ba.
A wannan lokaci duk sun jike Sharkaf da gumi
don haka sai ta
shawarce shi akan yaje yayi
wanka ya hutu,amma bazasu sake haduwa ba sai
gobe da safe yayin wannan tafiya.
Nan take kuwa
Yarima Lubainu ya cire sulken dake jikinsa ya
bayar
gami da takobin hannunsa ya tafi yana waigen
sarauniya yana yi mata wani irin kallo wanda
itama ta fada
cikin wasi wasi domin ta kasa tantance
irinsa.Kallo ne mai kama dana jin haushi ko na
gajiya?
Nan dai itama ta juya ta nufi hanyar da zata
kaita turakarta.
Kafin Alfijir ya keto tuni sarauniya
Akisatul Sauwara ta gama yi musu shirin
tafiya,kuma
bata bukaci rakiyar dakarunta ko kuyanginta
ba.Su biyu rak
suka fice daga birnin Rauhul Bagadar
bayan ta baiwa tsohuwa Dulaiba jiran gari.ALLON SIHIRI
Littfina na biyu(2)
Part C
Nan fa Lubainu da Akisatul Sauwara suka
sakarwa
dawakansu linzami suka nausa cikin daji sukayi
ta
tafiya ba sassauci.Saida suka yini suna tafiya
basu
yada zango ba,idan suka ji yunwa ko kishirwa sai
dai su bude jakar guzurinsu su kama cin abincin
ko
kuma su daga battar ruwansu su sha.Tsawon
wannan lokaci dayansu bai ce uffan ba,babu
wanda
yayiwa wani magana.Daf da faduwar rana ne
dawakansu suka fara nuna alamar sarewa domin
suna bukatar ruwan sha.A sannan ne Akisatul
Sauwara ta dubu Yarima Lubainu tace,yakamata
mu
yada zango inba haka ba kuwa dawakanmu zasu
sare.Lubainu yayi murmushi yace,ai tun dazu
nake
son na sanar dake hakan amma sai na kasa don
kada kice na gaza.Koda jin haka sai Sarauniya
Akisatul Sauwara ta kyalkyale da dariya tace,ai
tun
kafin ma mu bari birnina ka sare tunda ka bari
mukayi kunnen doki a gasar yakin da mukayi ni
da
kai.Lubainu ya girgiza kai yace aa bamuyi
kunnen
doki ba tunda nine na fara kai ki kasa kafin ke ki
kaini.Akisatul Sauwara ta sake yin murmushi a
karo
na biyu tayi shiru bata kara cewa komai ba.Cikin
sa'a kuwa sai suka hango wata fadama a can
gabansu nesa kadan kuma a kusa da fadamar
akwai
duwatsu da dogayen bishiyoyi.Cikin murna suka
karasa bakin koramar suka sauka.Dawakansu
suka
kama shan ruwa suna cin ciyawar dake bakin
koramar.Kawai sai Akisatul Sauwara ta kwance
jakar
guzurinta ta dauko tanti ta shiga aikin
kafashi.
Al'amarin dayai mutukar baiwa Yarima
Lubainu Mamaki kenan,ya mike da sauri ya kama
ma ta aikin yana mai cewa,haba ranki ya dade
saboda me bazaki umarceni dana kafa tantin ba?
Ai
mulki ba wasa bane dole ne na baki girmanki a
wannan fannin.Sa'adda Sarauniya Akisatul
Sauwara
taji wannan batu sai tai murmushi tace,kamar
yadda
nake mai mulki kaima ai mai mulki ne tunda ka
kasance dan sarki.Lubainu yayi murmushi yace,ai
dan sarki ba sarki bane,don haka yanzu kin bani
tazara mai yawa.Darajarki da daukakarki a duniya
ta
ninka tawa sau goma.Akisatul Sauwara tayi 'yar
guntuwar dariya tace,abinda ka fada gaskiya ne
amma ai duk sarkin daya baro birninsa ba sarki
bane tunda idan ya hadu da wanda bai sanshi ba
zai
iya wulakantashi ya wuce abinsa.
Ni yanzu na ajiye
karagar mulkina a gefe daya na dauki kaina
daidai
da kowanne talaka har sai bayan bukatarka ta
biya
mun koma kasata.Koda jin wannan batu sai jikin
Yarima Lubainu yayi sanyi yace,yake wannan
sarauniya mai daraja,yanzu kina nufin kice bakya
tsoron irin tsananin tashin hankalin dake cikin
wannan tafiya tawa har kike tunanin zaki ci gaba
da
bina har izuwa lokacin da burina zai cika?
Ki tuna fa
cewa yanzu akan mataki na farko muke kawai.A
kalla nan gaba akwai sauran matakai bakwai
zuwa
goma a gabanmu tunda sai mun nemo barin
Allon
Sihiri na biyu dana uku,sannan mu tafi neman
abokan tafiyarmu mutum uku.Yayin da Sarauniya
Akisatul Sauwara taji wannan batu sai tayi
murmushi
tace,ai rai ba abakin komai yake ba indai akwai
biyan bukata,kuma matsoraci har abada bazai
zama
gwani ba.Yayin da Yarima Lubainu yaji wannan
batu
sai ya cika da mamaki gami da wasi wasi.
Abinda ya
bashi mamaki shine aka wane dalili sarauniya
Akisatul Sauwara ta siyar da rayuwarta don ganin
bukatarsa ta biya?
Abinda zuciyarsa keyi masa wasi
wasi kuwa shine,anya kuwa sarauniya Akisatul
Sauwara bata da wata manufa ta binsa wannan
tafiya?.
A zahiri dai bai ga wani abu dazata amfana
dashi ba kuma bata gaya masa da bakinta
ba.Nan
dai Yarima Lubainu ya taimakawa Sarauniya
Akisatul
Sauwara suka karasa kafa tantin kuma ya
kwance
jakartaya debo kayan shimfidarta ya gyara mata
inda zata kwana.Bayan ya gama kintsa komai a
daidai lokacin da magriba ta kunno kai sai suka
fara
jiyo kukan dabbobin daji dana manyan tsuntsaye
masu shawagi a sama.Koda jin haka sai
Sarauniya
Akisatul Sauwara ta fito daga cikin tantin da
sauri ta
tofa wadansu dalasiman tsafi gabas da
yamma,kudu
da arewa da kuma sama da kasa,sanna ta dawo
cikin tantin ta dubi Yarima Lubainu wanda ke
shirin
biyota izuwa wajen tantin don tabbatar da cewar
babu wani mugun kwaro ko raminsa.Cikin
mamaki
Lubainu ya dubi Akisatul Sauwara yace,mene ne
naga kin fita da sauri daga cikin tantin nan kuma
kin
dawo da sauri?Koda jin wannan tambya sai
Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace
naje
na samar mana da tsaro ne a waje.Ko dabba ko
mutum ko aljan bai isa yazo nan ba ya cutar da
mu,don haka ka saki jikinka kayi barci mai
dadi.Koda gama fadin haka sai Sarauniya
Akisatul
Sauwara ta nufi inda shimfidarta take ta fara
kokarin
cire tufafin jikinta domin tasa rigar bacci.Cikin
hanzari Yarima Lubainu ya juya ya fice daga
cikin
dakin.Da yake a wannan lokaci wata irin iska mai
sanyi ta fara kadawa,sai Yarima Lubainu yaje ya
samo itatuwa ya kunna wuta ya zauna a gaban
wutar yana jin dumi.A daidai wannan lokaci ne
yaji
yunwa ta kamashi.Don haka sai ya bude jakar
guzurinsa ya fiddo da abinci ya kama
ci.Kwatsam!ba
zato ba tsammani sai yaji takun sawu a
bayansa.Cikin zafin nama Lubainu ya zare
takobinsa
ya mike tsaye zumbur!Koda yai arba da abinda
ya
tunkaroshi sai yai sauri ya sunkui da kansa kas a
lokacin da jikinsa ya kama tsuma.Ba wani abu ya
gani ba face sarauniya Akisatul Sauwara sanye
da
wata doguwar Rigar fara mai shara shara wacce
ta
bayyana komai na surar jikinta.Ganin tsananin
kyawun surar jikin nata ne yasa jikinsa ya kama
kyarma kuma zuciyarsa ta kama bugawa da sauri
da
sauri kuma da karfi.Tunda Yarima Lubainu ya
taso a
rayuwarsa bai taba ganin 'ya mace haka ba a
rayuwarsa sai wannan karon,don haka sai ya
danne
zuciyarsa da karfin tsiya,duk da cewa bashi da
cikakkiyar lafiyar da zaiji
wani abu sai zuciyarsa ta rinka harbawa.Ita kuwa
sarauniya Akisatul Sauwara tazo masa ne a cikin
wannan siffa don ta jarraba iyakar hakurinsa duk
da
cewar shine mutum na farko da ya taba ganinta
a
hakan.Kai tsaye ta matso daf dashi ta dubeshi
cikin
murmushi mai rikirkita kwakwalwa da hankali
tace,shin na baka tsoro ne bisa jin sautin tafiya
ta?
Ba tare da ya dago kai ba ya dubeta sai yayi
yake
sannan yace,ai dole ne naji tsoro tunda ban taba
zaton zanji wani motsi ba a baya.Koda jin haka
sai
Ta bushe da dariya sannan ta kama hannunsa
suka
zauna tare a gaban wutar suka ci gaba dajin
dumin
tare.Koda Lubainu yaga taki sakin hannunsa sai
ya
mike tsaye yace ina zuwa.Kawai sai ya zagaya
bayan tantin yayi kamar yana bawali ne sannan
ya
dawo ya sake zama a kusa da ita suna fuskantar
gabas,amma wannan lokaci bai yarda sun zauna
daf
da daf ba sai daya zamana cewa akwai tazarar
taku
uku a tsakaninsu.Tsawon 'yan dakiku dayansu bai
ce uffan ba sannan Lubainu yayi ajiyar numfashi
ya
dubeta yace,ranki ya dade ya kamata kije ki
kwanta
kiyi barci tunda dare ya soma kuma akwai gajiyar
tafiya a tare dake.Wai shin ma mene ne dalilin
dayasa kika fito ne alhalin gashi kinyi shirin
bacci?
Lokacin da Akisatul Sauwara taji wannan
tambaya
sai tayi murmushi tace,ya kai Lubainu kayi sani
cewa a rayuwata tun daga kuruciyata har izuwa
girmana ban taba kwanciya ba ni kadai a cikin
turakata face tare da kuyangina.Yau gashi zan
kwana ni kadai a cikin tanti kuma a cikin
daji.Tabbas
ko na kwanta barci ba zai zo min ba face ina jin
numfashin dan Adam a kusa da ni.Bisa wannan
dalili
ne na kasa barci har na fito wajenKa.Abinda
nake so
dakai yanzu shine kazo mu koma cikin tantin nan
mu kwana muyi barci.Koda jin wannan batu sai
Idanun Yarima Lubainu suka zazzaro ya dubeta
cikin
alamun tsananin firgici da tsoro yace gaskiya
bazan
iya barci ba a kusa dake.Ranki ya dade kiyi sani
cewa babu wani 'da namiji dazai ganki a cikin
wannan yanayi bai rude ba ya kamu da
sha'awarki
da sonki.Ni a matsayina da saurayin da bai taba
sanin 'ya mace ba kuma wanda yake nisantarku
dole
ne naji tsoron taraiya dake.Koda Lubainu yazo
nan a
zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta
kyalkyale da dariya sannan tace,kamar yadda
baka
taba sanin 'ya mace ba nima ban taba sanin wani
'da namiji ba,don haka na baka amanar kaina.Ina
mai tuna maka cewa samun yin barcina yana
gareka.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya
Akisatul Sauwara ta mike tsaye ta shige cikin
tantin
taje ta kwanta akan shimfidarta kanta na kallon
saman tantin ta fada kogin tunani.Shi kuwa
Yarima
Lubainu dake a zaune a wajen gaban wuta sai ya
mike tsaye ya kama kai kawo cikin tsananin
damuwa da wasi wasi.Daga can sai ya shiga
cikin
tantin yayi shimfida a gefe daya nesa da ina
Akisatul
Sauwara ke kwance ya kwanta.
Yana kwanciya sai
zuciyarsa ta tafi izuwa tunanin irin
gwagwarmayar
dayayi a baya.Yana cikin wannan tunani ne kuwa
barci ya saceshi har yana munshari bai sani
ba,kuma bai sake farkawa ba saida gari ya waye
rana ta kwalle.Yarima Lubainu na bude idanunsa
sai
ya hango shimfidar Sarauniya Akisatul Sauwara
wayam babu kowa akai.Koda yayi arba da abinda
ke
kan shimfidar sai zuciyarsa ta buda da kafi ya
kamu
da tsananin mamaki.Ba wani abu ya gani ba
akan
shimfidar face Allon Sihirin nan na Sarauniya
Akisatul Sauwara.Allon ne tsurarsa akan
shimfidar
wato an cireshi daga cikin kwalbar data
lullubeshi.Har Yarima Lubainu ya yunkura zaije
ya
dauki Allon Sihirin sai wata zuciyar ta daka masa
tsawa tace,shin ka manta ne da guzurin da
mahaifinka ya baka

1 Comments On ALLON SIHIRI 1 TO 9
avatar
abdulazeez

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment