Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan ƙyaƙyƙyawar zuciyar haka irin tasu baba malam. Yayinda wasu kuma suka ɗauki ɗammarar shigowa cikin tawagar a dama dasu da iya abinda ALLAH ya hore musu suma. Komai ya ƙaytar, dan ya tafi cikin nutsuwa, sarki ya bama waɗanan yara ƙyaututtuka, hakama Gwamna daya turo wakilinsa dan shi bai samu damar zuwaba ya dai bada tashi ƙyautar ga waɗannan angwaye da amare.
          Su Nu'aymah ansha kaikawo, dan kuwa sunyi tiɓis kamar sune amarorin. Bayan an tashi daga walimar da ƙyar suka rarrafa masaukinsu suna maida numfashin wahala. Su dai su Umm sunbi mazansu sun koma gida kamar yanda sukazo tare. Su Nu'aymah d Hajjo kuwa suna nan sai sunga ƙwal uwar daka.

________________________
 
           Bayan sallar isha'i baba malam ya tattara ƴan uwansa su duka uku a falonsa. A tare sukaci abincin dare, tare da tattauna yanda walima ta tafi cikin aminci da farin ciki babu wata matsala. Sunyi godiya ga UBANGIJI da ya zamemusu garkuwa, sannan baba malam dake tsaye akan komai.
     Ɗan murmushi kawai yayi batare da yace dasu komai akan hakanba. Kafin cikin nutsuwa ya nuna musu leda ruwan ƙasa da aka kawo ɗazun kafin walima tare da kayan abinci. Kasancewar bai samu zama dasu ba ɗazun sai bai sanar dasu komaiba ya bari sai sun dawo gida suyi maganar a tsanake sannan su duba abinda ke a ciki.
     Abba Musbahu da ya kasance ƙarami shi baba malam ya mikama ledan yana faɗin, “Musbahu buɗe muga minene a ciki, dan shi manager ɗin kamfanin da aka kawo kayan ta hanyarsu yace dukkan bayanan da muke bukata zamu samu anan. Amma mu kwantar da hankalinmu wanda ya bada ɗin baiyi da wata manufa ba, kuma shi yayine badan musan wanene shi ba, idanma muna tsoron wani abune to duk abinda mukaga be kwanta mana a raiba ko wata matsala ta biyo baya to mu nemesa shi, zai kaimu ga mai saƙon idan buƙatar hakan ta taso”.
      A tare sukace masha ALLAH, ALLAH ya sakanka masa da alkairi, ya biyasa da sakamakon abinda yafi wanda yayi. Shima ALLAH ya faranta masa fiye da yanda ya farantama mabukata.
      “Amin". baba malam ya amsa musu, yayinda Abba Musbahu ya fiddo abinda ke naɗe cikin leda mai ƙyalƙyali. Buɗe ledar yayi sai ga madaidaicin kwali ya bayyana. ya buɗe kwalin shima. Sun sami envelope guda biyu, ta farko check na kuɗi da suka basu mamaki fiye da zato. Dan a irin wannan halin da ake ciki mai bada ƙyautar irin waɗanan kuɗi masu yawa haka ai dole a jinjina masa. Sai zungureriyar wasiƙa, wadda bayanan cikinta ke magana akan su bada sunan yara talatin na gidan marayun da suka ƙare sakandire, ya ɗauki nauyin karatunsu na jami'a harsu ƙare, maza 15, mata 15. sai sunan kuma wasu ashirin din, maza 10 mata 10 sukuma waɗanda suka kare karatun zai nema musu aiki. Daga ƙarshe yace yana roƙonsu alfarmar sakashi cikin jerin mutane da zasu dinga hidima ga wannan gidan marayu gwargwadon ƙarfinsa.
         dukansu ajiyar zuciya suka shiga saukewa na mamaki da al'ajabin wannan mai saƙo. Kafin su shiga ja masa dogayen addu'oi, daga ƙarshe suka tattauna sosai akan lamarin. Sun yake shawarar faɗama UBANGIJI akan lamarin. Idan alkairine kuma mai wannan ƙudiri bada niyyar cuta musu ya zoba ALLAH yay riƙo da hannayensu gaba ɗaya. Idan kuma da wata manufa tattare da shi ALLAH yay musu maganinsa tunkan ya samu damar shiga jikinsu balle ya cutar da bayin ALLAH.
     Daga haka suka tashi akan zasu mikama UBANGIJI kukansu tsahon kwanaki uku, inda zuciyarsu ta karkata akan al'amarin zasu ɗaukesa a matsayin shine zaɓin da ALLAH yay musu, saisu yanke hukunci akan hakan. zasu cire kuɗaɗen daya rubuta ɗin a maidasu asusun gidan marayun.  bayan an gama ƙurar ɗaurin auren gobe idan ALLAH ya kaimu kuma saisu tantance yaran daya buƙata game da cigaban karatunsu da kuma waɗanda za'a nemarwa aiki.

*_ABUJA_*

               Bayan tafiyar Yoohan da kamar awa biyu sai ga papa da tawagarsa shi kuma ya dawo gida. Dama sunje taron manyan fastocine daya gudana a jihar Lagos, yau kwanansu biyar kenan a can. Ya samu tarba daga iyalansa da ma'aikatan gidansa, inda madam Chioma ke maƙale da shi har sashensa tai masa rakkiya.
       Bayan ya ƙimtsa ya fito sukai zaman yin lunch su duka a dining, sosai suka cika falon da surutu kamar ba abinci suke ciba, kowa na bama papa labarin abinda ya faru da baya gida. A cikin surutun nasu ne Abraham ke faɗama papansu an fasama Brother Yoohan motarsa a kano.
     Cak Papa ya tsaya daga cin abincin yana kallon Abraham ɗin, kafin ya maida kallonsa ga Madam Chioma da a lokaci guda ɓacin rai ya mamaye fuskarta. “Mi naji Abraham na faɗa Darling?”. Kanta ta jinjina masa tana ɗan karta cokalin hannunta akan filet ɗin abincinta, “Hakane Honey, jiya da yaje Kano abin ya faru, dama jira nake ka dawo asan matakin daya dace a ɗauka, shiyyasa bance masa komaiba dan karya ce bayaso ayi komai dan kasan halinsa dai”.
      Ɗan dukan table ɗin papa yayi da ture kofin da aka zuba masa lemo ya faɗi. A tare yaran duk suka zabura dan tsorota. Ya miƙe a fusace yana faɗin, “Miyasa tun a jiyan baki sanar minba, Gebrail ka tattaramin guards ɗin Yoohan gaba ɗayansu yanzun nan”.
            Cike da jin daɗi Gebrail ya amsa ma papa yana miƙewa. Dan shima burinsa a ɗauki matakin dama.

      Cikin mintuna ƙalilan guards ɗin Yoohan suka taru a falon, kallo guda zakai musu ka fahimci hankalinsu a matuƙar tashe yake. Musamman da suka shigo falon suka iske Papa nata kai kawo rai ɓace, kai kace gadin wani abu ya keyi. Sunkai tsayuwar mintuna goma kansu a ƙasa kafin ya kallesu da jajayen idanunsa.
         “Inaga baku da wani amfani game da tsare lafiyar Yoohan, zamu sallameku mu canzaku da waɗanda zasu iya, dan na inhar kune zaku cigaba da kulamin da yaro wataran sai an masa yankan rago kuna kallo baku iya yin komaiba akai”.
     Cikin ƙololuwar tashin hankali suke bashi haƙuri da roƙonsa. Suka ɗora da faɗin, ba laifinsu bane suma, boss ɗin nasune ya hanasu kowanne irin yunƙuri akan yarinyar. Kuma suna isowa sukaima Madam bayanin komai da ya faru....
      Tsawa papa ya daka musu wadda ta sakasu yin shiru lokaci guda. “Idan ya hanaku ɗaukar mataki miyasa bazaku kirani tun a lokacin ku sanar mini ba?! Tunkan ku fara aiki ban sanar muku duk randa kukayi kuskure wani abu ya faru da yarona abakin aikinku ba?”.
        Ka faɗa mana sir. Suka bashi amsa kowanne rai a dagule a tsorace kuma.
     Hannu yasa ya bugi kujerar gabansa, “Oh shine kuma baku tuna wannan dokarba?!!”.
         Madam Chioma dake bayansa ta kama hannunsa ta riƙe cikin nata tana ɗan murzawa alamar lallashi, dan bata buƙatar a sallami guards ɗin, itama suna mata nata aikin ne daban. “Darling relax, kasan halin Yoohan ɗin namu ai, kai musu afuwa su kiyaye gaba kawai. Sai kuma musan abinda ya dace a ayi, idan aikawa za'ayi a kamo mana yarinyar shikenan, dan bana goyon bayan a barta”.
        Iska ya furzar daga bakinsa, ya zare hannunsa daga nata ya zagaya cikin falon sosai ya zauna a kujera. Kwalba dake a saman ƙaramin tray ya ɗauka ya tsiyaya abinda ke a cikinta a kofin glass ɗan ƙarami da shima yake a kan tray ɗin. Gaba ɗaya ya juye a baki yana ya mutsa fuska, kafin ya ajiye kofin ya kallesu ɗaya bayan ɗaya.
        “A ina abin ya faru?”.
“A ƙofar gate ɗin wani orphanage ne sir, kuma muna ƙyautata zaton yarinyar itama ƴar gidan ce, dan ciki boss yasa muka shiga akai treatment ɗin yaron”.
        “Daga nan zuwa safiyar gobe ku tabbatar wannan yarinyar tana nan cikin abuja, inba hakaba a bakin aikinku”.
        A tare suka saki murmushin jin daɗi, dan koba komai suma dama ƙulle suke da yarinyar, da kuma takaicin hanasu ɗaukar mataki da Yoohan yayi jiya. Yanzukan sun sami damar cin ubanta dai-dai gwargwado. Cike da girmamawa da alƙawarin yin abinda papan ya sakasu suka amsa. kafin ya basu izinin barin falon.

      Ko cikakken mintuna ashirin basu ƙaraba a gidan suka ɗakko hanyar kano duk da kuwa a lokacin ƙarfe ɗaya na rana ya gota.

      Tofa, ana wata ga wata kenan😳😳 .

_____________________
*_NU'AYMAH_*

            A ɓangaren su Nu'aymah suma a washe garin wannan ranar bayan sakkowa sallar juma'a a massallacin aka ɗaura auren yara talatin da shida dake a gidan marayu na ƊAN JIBIYA FAMILY. Inda bayan kammala ɗaurin auren aka rakasu da addu'oin fatan alkairi kuma.

         Da yamma su Nu'aymah suka ɗanyi shagalinsu iya mata a sashen matan, suma mazan anguna sukayi nasu a sashensu tare da sauran angunan da ba'a gidan marayun suke ba suma. Bayan sallar la'asar kusan ƙarfe biyar da tai dai-dai da isowar tawagar guards ɗin Yoohan gidan marayun aka kwashi amare gaba ɗayansu aka miƙasu ɗakunan mazansu, bisa rakkiyar iyayensu su baba malam. bayan doguwar nasiha da sukasha daga garesu tamkar yanda mahaifa kema ƴaƴansu idan zasu miƙasu gidan miji.
        Duk wani jan ido da barazanar Guards ɗin Yoohan securitys sun hanasu shiga cikin Orphanage ɗin, acewarsu sai dai su faɗi miya kawosu anan gate, idan sunga da damar barinsu su shiga shikenan, idan sunga babu damar hakan kuma sai dai su juya. Ran guards ɗin ya ɓaci matuƙa, sunji kamar su harbesu kowama ya huta. amma sai suka danne sukai musu bayani akan abinda ya kawosu, tare da tabbatar musu suna tare da ƴan sanda.
      Duk da securitys ɗin gidan marayun sun gane wa ake nufi da kuma miya faru jiya sai suka nuna bama su ganesuba, dan a ganinsu bai kamata su bada damar da za'aci zarafin ƴa ɗaya tilo ga wanda bai taɓa gajiyawa wajen musu hidimaba. Sun kaɗasu dambu taliya sunce basu gane Nu'aymah ba, su bama susan anyi wani abuba.
     Ran guards ɗin yayi ƙololuwar ɓaci, sai dai ɗaukar mataki ya gagaresu, dan suma securitys ɗin gidan marayun bawai kanwar lasa bane. Sun san taɓasu babban bala'ine ga ogan nasu papa balle su ɗin karan kaɗa miya. Dan haka suka bar orphanage ɗin ransu a ɓace, akan zasuje su sake shiri gobe su dawo.
     Hotel suka kama, kafin su kira papa su sanar masa da komai daya faru.

★★★★

         Su Nu'aymah da basusan wainar da ake toyawaba ana kammala miƙa amare baba malam yasa Yah Ahmad ya tattara masa su aka wuce dasu gida badan sunso hakanba. Dan so sukai sukam sai sunyi sati ɗai-ɗai a gidan kafin su koma gida. Sai dai baba malam ya ɓata musu shirinsu.
     Aiko koda suka koma gidan sai suka dinga fushi da kumbure-kumbure. Kayan biki da baba habi ta haɗa musu ma sunƙi kulawa. Babu wanda yabi takansu a gidan, saisu Kubrah ne ma ke musu dariyar tsokana suna sake ƙulal dasu dan duk suna sashen Hajjo ne da suka dawo tare.

____________________

    
         Gaba ɗaya ran guards ɗin Yoohan a ɓace yake, tunda suka iso hotel ɗin da suka kama basu zaunaba, sai faman ƙulle-ƙullen yanda zasu sami Nu'aymah da matakin da zasu ɗauka a kanta sukeyi. Kai kace wata babbar ƴar ta'adda suke bibiya.
      Sun ƙulla yafi sau hamsin suna warwarewa. Suna tsaka da sake ƙullawa saƙo ya iso garesu daga hannun ɗaya daga ma'aikatan hotel ɗin. Number wayace daga wani, ya basu damar su kirashi idan suna buƙatar sanin inda wadda suke nema take.. 
             Da yake burinsu kenan jiki na ɓari suka kira kuwa. Ba'a ɗagaba har sai da ta kusan tsinkewa. Ƙinyin magana akayi. sai da ɗaya daga cikin guards ɗin ya fara magana.
      “Duk da bamusan ko wanene ba, mun maka alƙawarin inhar ka sanar mana inda yarinyar take zamu biyaka da kuɗi masu nauyi, oganmu ma zai maka ƙyauta ta musamman”.
       Batare da an basu amsaba aka yanke wayar. Kallon juna suka shigayi tambayoyi fal ransu. Kafin ɗayansu ya iya furta wani abu sai ga saƙo ya shigo. Da sauri suka buɗe ganin Number da suka kira ɗince. Ba komai bane a saƙon face cikakken address ɗin gidansu Nu'aymah, da sunanta harma da hotonta.
    Daɗine yay mugun kamasu, dan kuwa sun sake tabbatar da itaɗince, dan haka jiki na rawa suka sake kiran wanda ya tura musu ɗin. Yanzun ma dai baiyi maganaba, sai sune suka buƙaci ya turo musu accaunt details nashi ko nata zasu tura masa ladan aikinsa. Ƙitt aka yanke wayar batare da ance komaiba. Mintuna kaɗan kuwa saiga accaunt Number an turo. A take suma sukaima papa massege bayan sun kirashi sun sanar masa komai.
            
     Har a lokacin cike yake da ɓacin ran abinda ya faru, dan yaje yaga yanda akaima motar bugu na fitar hankali, shiyyasa ransa ya sake ɓaci, ya kuma tabbatarma kansa ko ɗiyar uban wacece yarinyar sai ta yabama aya zaƙinta.
           Babu ko tantama ana turo masa accaunt details ɗin ya antayama maishi kuɗi masu tsoka, dan a ganinsa bukatarsa ta biya. Mizaisa yaji ciwon biyan wanda ya taimakesu.

________________________________
*_NU'AYMAH_*

               Yau sama-sama Nu'aymah ta wayi gari, dan ta tashi da ciwon ƙafa alamar zuwan period ɗinta. Ita dama takan fara da ciwon ƙafane, randa yazo kuma zataita amai har saita jigata. Kafin daga bisani ta koma normal sai shegen ƙwaɗayi kamar taci mutum ɗanye.
      Tunda Umm ta shiga tadasu sallar asuba ta lura batajin daɗi, dan maimakon kwance saita isketa zaune ƙasa a bakin gado kan kafet ta kife kanta a kan gadon. Yusrah da Amal nata barcinsu a kan gadon su. Ita ta fara tadawa kafin su Amal, har zata juya ta fita sai kuma ta dakata ta kalli Nu'aymahn data maida kanta ta kife tsakanin ƙafafunta.......
      “Ke kuma lafiya?”. Da ƙyar Nu'aymah ta ɗaga kai ta kalli Umm, sai dai gudun kar ace ta shirya aje asibiti a mata allura sai ta daure tace, “Umm lafiya lau, kawai gajiyace tasa ƙafafuna ciwo”.
      Ɗan ƙura mata idanu Umm tayi na wasu mintuna, kafin ta janye tai ficewarta batare data sake cewa komaiba. Yusrah ce ta ƙaraso wajen Nu'aymah ɗin ta durƙusa. “Baby ƙarya kikaima Umm wlhy, daga gani baki da lafiya”.
    Yamutsa fuska Nu'aymah tayi kaɗan tana maida ƙwallar data cika mata ido. “Ƙafafuna ke ciwo wlhy Yusrah, nasan kuma period ɗinane zaizo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ko anjima”.
         Amal dake fitowa daga bayi tace, “To miyasa kikaƙi faɗar gaskiya?”. Yusrah data harbo jirgin Nu'aymah tai saurin cewa, “Allura”. A tare suka kwashe da dariya ita da Amal. Nu'aymah kuma tai tsaki idonta cike da ƙwalla ta miƙe. Da ɗingishi ta shiga bayi batare data kula dariyar dasu Yusrah ke mataba har yanzun.
 
       Bayan sun idar da salla Yusrah da Amal suka fice taya iyayensu aiki, Nu'aymah kam saita koma saman gado ta kwanta. Babu jimawa barci yay gaba da ita.

     Umm da duk ta gama fahimtarta bata nemeta ba, dan tasan zata gama zagayenta ne tazo ta nemeta. Bayan sun kammala breakfast ita da ƴan aiki ta shirya na baba malam da sauran ƴan uwansa a falonsa da kanta kamar yanda ta saba inhar duk suna gari, dan tare sukecin abincin safe da dare. Na rana ne dai bai zama dole su dukansu suna a gidaba shiyyasa. Garama idan ta kama juma'a ace dan duk basa zuwa ko ina a wannan ranar sai massallaci.
        Sai da taga komai ya mata yanda takeso sannan ta saka turaren wuta ta leƙa bedroom ɗinsa. Yana wanka, sai kawai ta buɗe Wadrobe ɗinsa ta zaɓo masa kayan da zai saka, saboda yau zasuje taron wani wa'azi a jihar katsina. Bayan ta ajiye masa duk abinda tasan zai buƙata ta fita zuwa ɗakin Muhammad danta taimaka masa yayi shirin makaranta shima.

*_08:15am_*

       Kusan takwas da kwata su baba malam suka hallara a falonsa shi da sauran ƴan uwansa domin karyawa. Sun sake gaisawa cikin girmamawa kamar yanda suka sabama kansu. Kafin su zauna su fara karyawa abin cike da birgewa.
     Sunyi nisa da cin abincinsu sukaji sallama. A tare suka amsa idonsu akan ƙofar. Ƙarasawa ciki falon Abbas da yay sallamar yayi. Ya durƙusa har ƙasa ya gaidasu. kafin cikin damuwa yace, “Abba ƴan sandane ke sallama”.
       “Ƴan sanda kuma Abbas? Lafiya dai ko?”. Baba malam dake kallon Abbas babu ko ƙyaftawa ya faɗa.
       “Abba ban saniba wlhy, amma sun nuna wai an turosu su tafi da Nu'aymah ne”.
       Ran Abban Adawiya a ɓace yace, “Wace irin Nu'aymah kuma? Miya haɗata da ƴan sanda banda shashanci irin naka Abbas?”. “Wlhy Abba haka sukace, dan hotonta ma suka nuna”. Miƙewa sukai su duka huɗun, sai dai su uku suka fara fita, kafin baba malam yabi bayansu..............✍

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*

       *_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*

_______________________________

14

.................A tare suka fito harabar gidan, inda suka iske matan gidan da sauran samarin da basu kai ga ficewa sabgoginsu ba duk sun fito suma.
      Suna ƙarasawa ga ƴan sandan Nu'aymah da Amal taje ta kira itama sai gata ta fito tana ɗan ɗingisa ƙafa. Sanye take da siket da riga na atanfa, sai ƙaramin hijjab da Umm ta sabar mata da sakawa a cikin gidan saboda samarin gidan tunda ba muharramanta bane ba.
       Tunda su Baba malam suka fito jikin wasu a cikin police ɗin yayi sanyi ganin dai da gaske an turosune gida mai daraja kamar wannan dan suyi abinda basu da tabbacin faruwarsa tunda ba'a gabansu akaiba. To amma yaya zasuyi, d.p.o ne da kansa ya sakasu zuwa su kama Nu'aymah, ga kuma kuɗaɗe da sukaci har kashi biyu daga Papa da kuma guards ɗin Yoohan na toshiyar baki. (Ya rabbi ka tsaremu cin rashawa da bada ita. Amin🙏🏻😭).
       
     Sun gaisa dasu Abba cikin girmamawa, kafin su sanar musu daga station ɗin da aka turosu da kuma abinda zasuyi. Kusan a tare su Abbah duk suka juya suna kallon Nu'aymah. Baba malam ne kawai kansa a ƙasa yana ɗan murmushi. Batare da yace komaiba ya nufi inda jama'ar gidan ke tsaitsaye suma suna kallonsu hankali a tashe.
       Hannun Nu'aymah ya kama batare da yacema kowa uffanba. Itama kuma babu musu ta bisa har wajen ƴan sandan. Ya miƙama macen hannun Nu'aymah yana faɗin, “Itace wannan?”.
        Kallon hoton dake a waya babban nasu yayi, kafin ya kalli Nu'aymah. “Eh itace ALLAH ya gafarta malam”. Ya faɗa cike da girmamawa ga baba malam. Murmushi baba malam yay musu yana nuna masu Nu'aymah dake kallonsa kamar wata sokuwa. “Gata nan, zaku iya tafiya da ita”. Da sauri Abban su Abdallah ya yunƙuro zaiyi magana baba malam ya ɗaga masa hannu fuska a ɗaure. Cak ya tsaya hankalinsa a ƙololuwar tashe. Hakama su Abban Adawiya hankalin nasu a tashe yake da hukuncin da baba malam ya shirin yankewa. A ganinsu ai basai anje station ba, zasu iya tsayawa su tattauna anan, musamman ma shi Abban Adawiya da yana cikin Orphanage randa abin ya faru. Kuma an sanar masa komai akai.
        Godiya ƴan sanda sukai tare da juyawa da Nu'aymah zasu tafi. Tirjewa tai tana kallon Baba malam daya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garesu tamkar baisan mi akeyiba. Hannunta ta fara ƙoƙarin fisgewa idanunta na cika da ƙwalla. “Abba wlhy bansan mina musu ba”. Tai maganar muryarta na rawa.
     Juyawa baba malam yayi zai bar wajen batare daya kula maganar Nu'aymah ba. Sai da yay taku biyu uku sannan ya tsaya tare da juyawa ya kalli ƴan sanda da Nu'aymah data fisge zata dawo. Cikin tsananin kaushin murya yace, “Idan bazata biku da arziƙiba ku ɗauketa!!”. 
     Tsayawa Nu'aymah tayi cak tana kallon baba malam ɗin. Sai kuma ta kalli inda su Umm suke. Sake dawo da idonta tayi kan ƴan sandan da suma ita suke kallo. kunyar baba malam ce kawai ta hanasu fara cin ƙaniyarta tun anan. Tsaf ta haɗiye kukanta. Ta juya cikin ɗingishi ta nufi ƴan sandan. Basuce mata komaiba suka tasa ƙeyarta gaba suka fita waje inda motarsu take.
      A gaban ƴan anguwa daketa kai kawo aka sakata a motar ƴan sanda. Gaba ɗaya hawayen da Nu'aymah ta fara ɗazun sun ƙame ƙaf. Ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tai shiru. Sai faman cije baki kawai take saboda zugi da ƙafarta ke mata. Har suka isa police station ɗin bata ɗagoba. Sai da ƴar sandar ma ta taɓata sannan ta san sun iso. Ɗago kanta tai a hankali ta kalli station ɗin, sai kuma ta juya ga ƴar sandar dake mata kallon tausayi. Dan ita yanda taga mutanen na hanƙoro akan yarinyar ta zata ma wata tsohuwar macece, ashe yarinyace ƙarama. Itace ta taimaka mata ta fito, ta kama hannunta ganin kamarma ta kasa tsaiwa. A haka suka shiga cikin station ɗin da taimakon ƴar sandar.

 
         “Amma Yaya ka.......” hannu baba malam yay saurin ɗagama Abban su Adawiya dake son masa bayanin ainahin abinda ya faru. Ya kallesa fuskarsa babu wasa, “Banason jin komai akan hakan Mustapha. Kaje ka shirya mu wuce banason yazam mu ake jira”.
     Kai kawai Abban su Adawiya ya kaɗa masa. Kafin ya kalli su Abba Musbahu ya bar wajan jiki a sanyaye. Da sauri su Abban Abdallah suka nufi mota da nufin bin bayan su Nu'aymah, sai kawai a bazata suka tsinkayi muryar Baba malam na faɗin, “Na haramtawa kowa bin bayanta a cikin gidan nan, idan kuma wani ya aikata koda ban saniba zai fuskanci fushina”.
     Cak suka tsaya daga yunƙurin shiga motar, kowannensu goshinsa na tara zufa. Babu wanda ya iya sake cewa komai har Baba malam ya shiga sashensu ya fito cikin shirin fita. Ta gabansu ya wuce zuwa sashen Hajjo data sha maganin mura tun ɗazun ta kwanta.

1 Comments On SARAN BOYE
avatar
maryam-8-1

1 year ago

Reply

Amazing book

Please Login or Register in order to submit comment