Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na daina cin abincin gidanne kawai ya sata cewa ta ƙoshi. Sai da ta shanye tsaf taci rabin biscuit ɗin sannan taje ta sake yo brush tazo tai kwanciyarta.

★★★★

        A ɓangaren madam Chioma kam ta fitane da wani irin jin zafi da takaicin Aymah, dan ita duk a tunaninta da biyu tayi abinda tayi. Batasan ita Nu'aymah ko tarin farko da tayi, tayine kawai dan neman tsokana bawai danta kawo wani abu a ranta game da zaman nasu ba, tunda tasan sudai basu ɗauki taɓa jikin juna komaiba musamman ma ita dake a matsayin mahaifiyarsa. Ko kallon Victoria da Abraham dake rigima akan camara batai ba ta shigewarta ɗakinta ta banko ƙofa. Zama tai kan sofa zuciyarta tamkar zata tarwatse dan tsanar Aymah. Waya ta ɗauka kamar zata kira ƙawarta sai kuma ta fasa, a ganinta gara ta bari su haɗu a church jibi lahadi zasufi yin maganar yanda ya kamata ai.
      Hular gashin dake a kanta ta tuge ta ajiye, cirkuɗaɗɗen ainahin nata dake guntu ya bayyana. Fitowa ta sakeyi daga ɗakin zuwa sashen Papa. Baya falo, dan haka ta nufi bedroom ɗinsa kai tsaye. Saurin tura hoton hannunsa da lighter da zai ƙonashi yayi ƙarƙashin gado dan yazata cikin yaransa ne wani ya shigo masa. Amma ganin matarsa ne sai ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai dai hakan baisashi sake ɗakko hotonba duk da itama tasan wani abu akan hoton.
     Ita sam bama ta lura da abinda yayi ba, ta zauna a bakin gadon kusa da shi tana hawaye. Duk rikicewa yayi, ya shiga jera mata tambayaoyi da rungumota jikinsa. Bata iya bashi amsaba sai da tai kukanta ta more sannan ta labarta masa abinda ya faru. Murmushi yayi dan shi baiga wani abin fushi ba anan, a fili kam sai yace, “Uhm-uhm Darling cool down, ke mima ya kaiki sashensu yanzu? Kin sanfa yanzu yana da mata, duk kulawar da kike tunanin baya samu yanzu akwai mai masa”. Ɗan turesa tai ta tashi zaune sosai. Ya ƙyalƙyale da dariya yana riƙo hannunta, “Ah son ƴaƴa yamiki yawa Madam, karfa kice zaki ringa irin halin su mama akan matar John Please, dan indai kina nuna mata ƙi bazamuci nasara akan burinmu ba zaki rusa mana aiki”.
           “Honey yarinyar nan bata da kunya, ciwon da kaga Mira taji fa itace ta saka mata ƙafa ta faɗi saboda ta mata tsaki”. Idanu papa ya zaro waje sosai da faɗin, “Da gaske?”. “Na rantse maka kuwa Honey, abinda yasa nai shiru banyi maganaba saboda itama Miracle ɗin shegiyan kanta ne, danni tama isheni a gidan nan, ya kamata ta koma gidansu hakanan tunda ta kammala karatun ai”.
       Da sauri Papa yace, “No baza'ayi hakaba Darling, kawai dai zan mata gargaɗi karta sake shiga rayuwar matar John, inba hakaba kuwa shine da kansa zai koreta a gidan nan tunda tasan halinsa”. Wani shegen kallo Madam Chioma kema Papa mai cike da tuhuma. Amma sai ya basar kamar bai ganta ba. “Humm” ta faɗa tana haɗiye abinda ke a ranta. a ganinta inma hakanne ai zata saka idanu ta tabbatar. “Naji, yanzu dai inason kaima John magana, dolene idan yana garin nan ya ringa fita church bawai dole sai Sunday ba. Idan bamuyi hakaba yarinyar nan zata iya sakashi ya fara salla. Gara mu saka masa ido sosai itama kanta duk Sunday ya sata tana binmu tunda akwai addu'oin da ake masa, tunda kuma yanada mata kaima kasan a ƙa'ida dole saita ringa kasancewa a wajen”.
        “Eh maganarki gaskiyane kam, zan zauna da shi sai muyi magana”.
      Kanta ta jinjina masa alamar gamsuwa. Daga haka suka cigaba da hirarsu har ya manta da batun ƙona hoto ma.

*******

      A ranar gaba ɗaya Nu'aymah wasan ɓuya ta dingayi da Yoohan, gaba ɗaya taƙi yarda su haɗu har yamma duk da dai ya daɗe bai tashi a barci bane, sai gab da azhur ya tashi, yana yin wanka kuma yay shirin massallaci ya fita. A lokacinne ya isketa a falo tana kallo. Amma tanajin motsinsa ta tashi da gudu ta shige ɗakinta harda mirza key. Shi dariya ma ta bashi a lokacin, amma sai ya gimtse baiyiba yay ficewarsa dan ya kusa makara.

          Sai bayan sallar la'asar ya dawo massallaci ne ya ritsata ta fito zataje garden. Karo sukayi a bakin ƙofa, tai baya da sauri tana tura baki gaba da dafe goshinta. Uffan baice mata ba, sai idanu daya kafeta da shi. Dan doguwar rigar atamfar jikinta ta mata ɗas, daka ganta kaga cikkakkiyar bahaushiya ƴar arewaci.
        Jin yaƙi cemata sannu ta sake tura bakin tana tara hawayen ƙarya, ita a lallai dole taji zafin bigewar da tayi. Raɓashi tayi zata wuce yay azamar riƙo hannunta ya dawo da ita gabansa. “Kin gama gudun?”. Ya faɗa a hankali kamar bayaso. Yanda yay maganar muryarsa a sanyaye ne yasa kallonsa da sauri, kallon ido cikin ido sukaima juna, ya ɗan lumshe nasa dake da ja a ciki, gashi sun ɗan kumbure ya sake buɗewa a kanta.
      Samun kanta tai da faɗin, “Baka da lafiya?”. Kansa ya ɗan jinjina mata da yamutse fuska, kafin yace, “Kaina ke min ciwo”. Ya bata amsa yana sakin hannunta dake cikin nashi.
     A bazata yaji tace, “Dama likitoci na rashin lafiya?”. Tai maganar da waro idanunta manya waje sosai. A karan farko ya saki murmushi yana ƙoƙarin raɓata zai wuce, sai da ya shige falon sosai sannan yace, “Shi likita ba mutum bane?”.
         Harta buɗe baki zatayi magana sai ta fasa saboda hango Papa na sakkowa daga sama waya a kunnensa. Sai dai kuma idanunsa na kansu da ga ita har Yoohan ɗin. Juyawa tai ta fice abinta.

_______★★★★________

  *_KANO TA DABO_*

        Kamar yanda baba malam yayma Umm bayani akan ƴar aiki da Aymah ta buƙata daga nan, itama Hajjo ya sameta da zancen, Ɗari bisa ɗari hajjo ta bada goyon baya, sai dai tace ya kamata a tuntunɓi Yoohan idan ya amince, idan bai aminceba a haƙura kawai, a hankali zata saba da waɗanda ƙadadara ta kaita zama da su. Harma suna mata fatan cin riba akan hakan.
       Duk da baba malam ya riga da yayi magana da Yoohan akan maganar tun kwana biyu daya wuce sai ya amsama hajjo da cewar insha ALLAH a yau zai tuntuɓi Yoohan ɗin, yanda sukayi kuma zataji. A ransa kuwa da biyu yaƙi faɗa mata gaskiyar yanda al'amarin zai kasance. Ba komai ya jawo hakaba sai laɓe daya fahimci anai musu shi da Umm kwana biyun nan, inuwarnan daya gani a ranar da za'a kai Aymah Abuja. Sai kuma ya sake ganinta randa yakema Umm bayani akan wayar da sukayi da Nu'aymah. Sai dai yayi shiru da bakinsa ko Umm ɗin bai sanarmawa ba. Sai Yoohan da shima yay masa zancen ganin mutum a randa akai maganar cikin nan na Aymah,  dan randa Nu'aymah tai masa maganar mai aiki daga nan kano ya kira baba malam sunyi doguwar waya.
      A yanzu haka fatansa ALLAH yasa maganar da sukayi da hajjo an laɓe musu ɗin. Dan duk mai aikata musu SARAN ƁOYEN zaiso ace koma wace ƴar aiki za'a turama Nu'aymah ya samu dangantakar da zai ringa samin bayanai akan Aymah.
      Baba malam ya jima a wajen Hajjo da tunanin ko zai sake ganin inuwar mai laɓen nan. sai dai harya ƙaraci zamansa da kallon windows babu ko ƙyallin mutum balle wata inuwa. Hakan ya bashi mamaki amma sai ya share dan baya buƙatar hajjo ta fahimci komai tun yanzun, sai sun kammala ɗana tarkunansu tsaf sannan.

         Washe gari baba Malam ya sake samun Hajjo da maganar cewar Yoohan ya amince da maganar mai aikin. Fuskar Hajjo faɗaɗe da murmushi tace, “To to Alhmdllhi, madalla da ɗan albarka Yahya. Kaga bara na shiga nan gidan Iyami da kaina sai na mata bayanin a samo mai hankali ba yarinya irin Zainabu ba. Dan bazai yuwu a irin wannan zaman a haɗa ƙuruciya da ƙuruciya ba. Sai dai wadda taɗan tasa idan taga ba dai-dai ba ta nusar da ita”.
       “Eh gaskiya ne inna, hakan yayi kam. Dan mamana halinta kam sai ita, inba mai ɗorata a hanyar aka samoba sai aita samun matsala dan har yanzun hankali bawai ya gama isarta bane”.
          “Ai karka damu ɗan malam, wlhy duk abinda kaga Zainabu nayi nima nayisa, babu abinda ta bari na ƙuruciyata. Malam yasha fama dani bana wasa ba. Amma kaga ina fara haihuwa duk saina rage nawa. Garama Zainabu ai a shekarun da akai mata aure ta tasa fiye dani. Tunda ni ina sha uku aka aurama babanku ni, itako sha bakwai fa harda wasu watanni”.
          Baba malam dai kansa a ƙasa yanata ƙoƙarin haɗiye dariyarsa. Dan shima kafin mahaifinsu ya rasu ya taɓa bashi labarin ƙiriniyar da Hajjon tayi a gidansa. Da yake shi haka yake, duk randa ƴan labarin nasa ya motsa sai ya zaunar dasu yayta basu tarihin gwagwarmayar da yayi ta rayuwa harma da ƙuruciyarsu. Wannan ɗabi'ar ta mahaifinsu tana ɗaya daga cikin abinda basa iya mantawa a rayuwarsu su duka.

        Kamar yanda Hajjo tai alƙawari da yamma kuwa sai ta shiga gidan su Hamisu wajen mahaifiyarsa Iyami. Sosai Iyami ta dinga haba-haba da hajjo duk da kuwa kasancewar su maƙwafta. Amma da yake ba ɗabi'ar shige-shigence da suba inba da ƙwaƙwaran dalili ba, sai yazam duk randa akaga juna kamar baƙi.
       Bayan sun gaisa hajjo tasha ruwan da Iyami ta kawo mata duk da ba ƙishin take jiba, sai dai a cewarta ruwan zuminci yafi zuma garɗi. “Yauwa Iyami nasan kinata mamakin ganina da maraicen nan. To dama ba wani abune ya sani fitarnan ba ta gabannin magriba sai takwarata ƴar jikalleta Zainabu da aka kai Abuja”.
        Iyami dake murmushi tace,  “Oh ALLAH sarki Nu'aymah amarya zaki cemin, inadai fatan suna nan lafiya ko?”.
          “Ah lafiya lau suke sai alkairi kam. Mijin ne dama ya kira wai a nema mata mai aiki daga nan, shine nace to bara nazo da kaina wajenki ƙila ta hanyarki a samo wata mai hankali. Danni ƴan aikin gidan nan namu yanzu tsoro al'amarinsu ke bani wlhy Iyami. Kuma kinsan duk deluwa ce dama take kawo manasu gashi ALLAH yay mata rasuwa”.
        “To hajjo babu damuwa. Tunda har kika zaɓeni nikuwa insha ALLAH zan samoma Nu'aymah mai aiki ƴar gaske wadda baza'ayi kuka da ita ba. Duk da dai yanzu kinsa al'amarin mutanen namune sai dai addu'a. Baka fiya ganin abinda ke cikin zuciyar mutum ba a fuskarsa. Sai dai muce ALLAH ya datar damu”.
        “To amin dai Iyami. Lamarin bani adama kam na wannan rikitaccen zamani sai godiyar ALLAH kawai. Yanzu dai sai a bincika mana ɗin daga nan zuwa kwana biyu. Amma sai a samo mana ƴar babba ko tunda kinga ba'a haɗa Zainabu da sha katafi irinta ba. Wadda dai idan tayi ba daidaiba za'a tsawatama yaro a kuma ɗorasa akan hanyar data dace”.
       “Eh gaskiya kam hajjo, aiko indaima hakane bari zuwa anjima idan cikin su Hamisu wani ya ya shigo sai na saka su kira min Uwaliya idan zatayi, ƴar wajen yafendona ce acan wudil, mijinne ya tafi da ita can kudu da yake ɗansanda ne ya gama wajigo rayuwarta shine fa ya turota da takardar saki har uku. Shekara biyu kenan wani auren ya gagara abu kamar na magani”.
       Hajjo daba cika son irin waɗannan ƙananun maganar tayiba ta miƙe tana faɗin, “Ai ɗan adam sai ki barsa kawai Iyami, ALLAH dai ya ƙyauta ya shiryrmu mu da halinmu”.
       “Amin dai to”.
Iyami ta faɗa badan taso firar ta tsaya iya haka ba. Daga haka hajjo tai mata sallama ta dawo gidan dan anata haramar fara kiraye-kirayen sallar magriba ma.

_________★★★★_________

*_SUNDAY MORNING_*

         Washe gari ta kama Sunday. Gaba ɗaya ahalin gidan sun tashi ne da shirin tafiya church kamar yanda suka saba. Papa ya riga kowa fita shida bodyguard ɗinsa. Aymah da batasan hidimar da sukeyi ba tana tsaka da mopping a falo akai knocking ƙofa. Batare da ta damu da sanin wanene ba ta nufi ƙofar zata buɗe. Dan akwai hijjab ƙarami a saman kayan barcin jikinta.
       Momy ce cikin shiga ta alfarma, anci uban kwalliya kamar zataje gasar ƙyau. Abraham biye da ita shima cikin gayunsa. Kamar zata shareta karta gaisheta sai kuma tace, “Good Morning”. Bata saurari amsarta ba tai gaba abinta. Haka kawai itadai Madam Chioma batai mataba, badan mahaifiyar Yoohan bace ba da lallai zamansu a waje ɗaya zai iya haifar da matsaloli, dan a rayuwarta ta tsani wulaƙanci koda a wajen babba ne.
        Da harara Momy ta raka bayan Aymah data koma kan aikinta batare da ta sake bi takansu ba. Ɗakin Yoohan kai tsaye ta nufa Abraham biye da ita. Sai dai koda ta tura ƙofar suka shiga sai taga wayam. Jikin ƙofar toilet taje nanma babu wani motsi, ta tura ƙofar ta leƙa babu kowa a ciki, amma dai da alama anyi amfani da shi babu jimawa. Tunanin ko yana ɗakin motsa jikinsa ne ya sata fitowa ta nufi can. Lokacin Aymah tana dining tana aikinta ko kallonsu batayi ba. Canma babu Yoohan, babuma alamar yau ya shigo wajen dan komai tsaf yake.
        “K ina my son?”.
   Nu'aymah taji muryar Momy a bazata. Ɗago dara-daran idanunta dake saka tsigar jikin Momy tayi tana kallonta. A yanayin halin ko-inkula tace, “Nima ban gansa ba tunda na tashi”. Daga haka ta ɗauki botikin ruwan mopping ɗinta ta nufi ɗakin Yoohan ɗin danta gyara tunda taji baya a ciki.
       Cike da takaici Madam Chioma ta bita da harara, kafin taja hannun Abraham su fice. Fita tai harabar gidan, dan sauranma duk sun fita harma sun shishshiga motoci.
       Guards ɗin Yoohan ɗin ta shiga tambaya ko sunga fitarsa?. Solomon ya bata amsa da cewar ya fita tun ɗazun ma, sunce zasu bisa yace baya buƙata. Ranta a ɓace tace, “Baku da hankali, sau nawa nake jaddada muku kubar barinsa yana fita shi kaɗai?. Da wace motama ya fita tunda naga duk ga motocinsa?”.
       Kan Solomon a ƙasa yace, “Sorry maa. Babu yanda banyiba koni kaɗaima na bisa amma yaki, a mashin ya fita kuma”.
        Wani shegen ihu ta buga tana ambaton “Jesus!!. Da wannan uban iskan safiyan kuka barshi ya fita a mashin dan ku kidahumai ne? idan Asthma ɗinsa ya tashi fa?”. Duk yanda sukaso ta fahimci ba laifinsu bane sam taƙi. Ihunta sai da yasa harsu Gebrail da suka shiga cikin mota duk suka fito. Nu'aymah kanta dake can sama sai da ta jiyo, hakan yasata buɗe Window ɗin bedroom ɗin Yoohan tana leƙosu. Ba ƙaramin dariya madam Chioma ta bataba yanda taketa faman tsalle da bala'i harta yadda takalman gayun nata saboda jarabar da takema guards ɗin Yoohan. Dariya sosai Aymah tasha harda hawaye, a ranta tana sake jinjina hauka da rashin kangado irin na waɗannan mutanen. Danma batasan akan mi madam Chioma ke bala'in bane😂.

         Jin gidan yayi tsitt bayan gama bala'in madam Chioma da wucewarsu  sai tunanin maganar hoto ta dawo mata a cikin rai. Tabbas wannan shine lokacin da take da shi akan hakan tunda taga duk sun fice kamar maigadi ne kawai aka bari. Sai dai bata sani ba ko hadda duk masu aikin gidan. Sannan kuma bataga Miracle ba ma a amasu tafiyar.
     Ɗakinta ta koma tai wanka a gurguje. Shiryawa tai cikin doguwar rigar jallabiya blue. A falo ta zauna danta karya saboda yunwa dake cinta. Jiya tayi barci da wuri bataci abinci ba, duk da ma har yanzun ta kasa sakin jiki da abincin gidan sam. Ta gwammace zaman cin kayan ƙwalam ɗin da Yoohan ya ajiye. Aiko dukta kusan ganin ƙarshensu batare da ya sani ba.
       Yanzun ma madara ta haɗa da kauri tai zaman shan Cornflakes hankalinta kwance. Tana sha tana tunanin hanyar shiga sashen papa ɗakko hoton nan, a gefen zuciyarta kam cike da fargabar ALLAH yasa bai ƙona ɗin ba. Wannan tunanin ne ya saka cornflakes ɗin fita mata a rai ma. Ta ture bowl ɗin gefe tana miƙewa. Bedroom ɗinta ta koma ta leƙa harabar gidan ta Window, sai da ta tabbatar babu motsin kowa sai maigadi kawai sannan ta rufe glass ɗin a hankali.
         A falon gidanma bataga motsin kowa ba, hakama sama ko ina shiru ƙofofin bedrooms ɗin duk a rufe. Duk da haka batayi gangancin yin komai kai tsaye ba. Ta sauka downstairs ɗin ta shiga kitchen kamar zata ɗakko wani abu. Babu kowa a kitchen ɗin tabbacin da Blessing aka tafi. Ƙofar da zata kaika bayan gidan ta buɗe ta kitchen ta fito, nanma shiru babu kowa. Ta sake dawowa cikin jin daɗi ta haye upstairs ɗin. Ɗakin da take da tabbacin nasu Miracle ne ta nufa, tunkan ta ƙarasa jikin ƙofar sosai tajiyo minsharin Miracle dake barci. A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta leƙa kanta. Kan gado ta hangota a cikin bargo, ga kafarta data sha ɗaurin bandage taɗan leƙo, key ɗin ƙofar dake ta ciki ta zaro a hankali, sannan taja ƙofar ta kulle mira ta waje.
      Lumshe idanu tayi a hankali tana karanto addu'oin neman nasara. Daga haka ta nufi sashen papa da addu'ar ALLAH yasa a buɗe yake. Cikin sa'a kuwa tana tura ƙofar sai gashi ta buɗe. Nannauyan numfashi ta sauke da turawa gaba ɗaya ta shiga corridor ɗin. Ƙofar falon ma ta sameta buɗe, nanma ta shige cike da ɗoki.
      Koda wasa batai tunanin tsayawa a falon ba, dan tasan yanda papa ya nuna muhimmancin hoton nan bazai yarda ya ajiyesa anan ba sai dai bedroom. Bedroom ɗinma dai a buɗen ta samesa. Da alama ma ko gyara bai samu ba dan gadon duk a curkuɗe yake. Bata damu da wannan ba. Ta fara buɗe-buɗen bedside drawer farko tana ɗaɗɗaga abubuwan ciki. A duka biyun bata sami hotonba. Dan haka tabar nan ta juya kan Wadrobe ɗin kaya. Sai dai koda ta buɗe ma sai ta rasa da ina ya kamata ta fara?.  Sunan ALLAH ta shiga ambata tana ɗaɗɗaga duk abinda taci karo da shi. Amma babu alamar wannan hoto. Harta sare da tunanin kodai ya ƙona. Sai idanunta suka sauka kan wani ɗan kanta dake can gefe da tarin littatafai da takardu. Nanma zuwa tai tanata ɗagawa ɗaya bayan ɗaya sai dai babu anan ma.
      Kanta ta dafe hawaye na ciko mata idanu dan takaici, tabbas yanzu kam tama yarda ya riga da ya ƙona kenan?.  Zuciyarta ce ta ayyana mata ƙasan gado. Saurin nufar gadon tayi. sai dai tana ɗora hannunta a kai tajiyo dariyar Papa a falo yana faɗin, “Kai! Kai kai gaskiya kamin bazata Andrew, da alama ka matsu da kayan nan kam gaskiya”. Dariya wanda ya kira Andrew taji yayi shima, cikin harshen turancin yake faɗin, “Mr Goshpower bazaka ganeba ne, kuɗi masu nauyi ne na hango mana shiyyasa zuciyata ta kasa zama waje guda duk da nasan kana church a irin wannan lokacin”.
        Wata shegiyar dariya Papa ya kece da ita yana nufar hanyar bedroom ɗinsa, “Ai kai indai akan kuɗine zakama iya saka kanka a kowane kalar haɗari, shiyyasa kaga bana wasa da al'amarinka”. Ya ƙare maganar yana ƙarasa tura ƙofar bedroom ɗin da Aymah ke a ciki ya shi🙆🏻............✍

  Hannuna ya firgita ya gaza aikinsa😱🙆🏻.

        

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[6/12, 12:23 PM] Oum Siyama: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 51

____________

_*HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION._*

_Ina mata masu son ingattun kayan kamshi: Na kece raini? Kayan mata masu sa kishiya k’wafa? Bikin dangin miji ba za’a baki yankan albasa ba da wankin tumatir? To matso kusa domin HAJARA COLLECTION ta kawo muku kayayyaki na gyara ciki da wajen mace, Wanda suka kunshi:_

_Khumrahs: Sudaniyya, Chadian, Dufr, Fara da brown, Kai harda masu flavours... _

_Akwai turaren wuta irin su sandal, Hawi, Alut, Gab gab da sauran su.._

_Akwai turaren tsugunno dana jiki original gangariya tafiyayye dan gaske_

_Hajara collection ta kawo muku air fresheners, Mopping sprays da turaren wanki..._

_Akwai herbal organic soap wato sabulun gyaran jiki na maida tsohuwa yarinya.._

_Sannan Hajia hajara collection tana gyaran jiki.. Tana kuma siyarwa da kayan gyaran jiki na dilke set, Fata tai luwai luwai kamar ta jarirai.._

_Akwai special bridal spa wato gyaran jikin Amarya... Duk Amarya mai son tadinga kamshi har bayan shudewar bikinta to ta nemi hajara collection.._

_Akwai duk wasu nau’in kayayyakin turare masu kamsasa unguwa baki d’aya, Ki mopping tiles suyi sati suna kamshi, Kayan Haj hajara collection akwai inganci sosai._

_Akwai page dinta a favebook mai suna *GIDAN KAMSHI* ga mai son zuwa ya duba hajarta, Ko kuma ya tuntubeta a number wayarta kamar haka: 09032069304_

_Adireshi: KANO NIGERIA, MARIRI dake Kan titin MAIDUGURI RD. KANO STATE.._

_TANA BADA KAYANTA AKAN FARASHIN SARI KO SAYA DAYA DAYA, SANNAN TANA TURA KAYANTA A KOINA AFADIN NIGERIA_

_AVAILABLE IN WHOLESALE/RETAILS. Nationwide deliveries. 100% tested and trusted...!!!_

_Kyau, inganci, Rahusa... Sai kayan HAJARA COLLECTION....!_

_idan anje siya ace daga zafafa biyar.. Akwai special package da Za’a hada maka masu kamshi🥰😍🧚🏻‍♂️_

_____________

No. 51

............Tun fara jin dariyar Papa Aymah ta rintse idanunta da ƙarfi, ko ɗar bataji a rantaba na tsoro. Sai dai bata fatan ya ganta a ɗakin. Harta yunƙura zata ɗaga katifar da zaton ba shigowa zaiyiba sai taji sautin takowarsa. Da sauri ta saki tana waige-waigen ina ya dace ta shiga ta ɓuya. ‘Toilet ’ zuciyarta ta bata amsa a taƙaice. Da gudu ta nufi toilet ɗin dai-dai da murɗa handle ɗin ƙofar bedroom ɗin da papa yayi. Yana shigowa tana turo ƙofar bathroom ɗin.
       Da sauri ya kalli ƙofar toilet ɗin danjin ta ɗanyi ƙara alamar rufewa. Yay tsaiy yana kallonta zuciyarsa fal mamaki. Shi dai yasan baiyi tsammanin ganin kowa a ɗakinsa ba. Musamman daya san duk ahalin gidan ya barsu a church ne. Shima harya fara lecture sai ga baƙonsa mai muhimmanci Andrew yazo. Dole ya baroma Uncle Mike shikuma yazo yaji da baƙon nasa dan yafi lecture ɗin da zaiyi a church ɗin muhimmanci.
       Duk da yasan babu kowa ɗin dai, sai ya sami kansa dason tabbatarwa. Dan haka ya nufi toilet ɗin yana zancen zuci.
       ‘Ya ALLAH!’. Nu'aymah ta faɗa a zuciyarta tana rumtse ido da ƙarfi jin kuma ya nufo toilet ɗin. Da sauri ta koma ta jikin bayan ƙofar, yanda idanma ya buɗe bazai gantaba sai dai idan shigowa yay ya rufe.
     Ƙofar kuwa ya tura ya leƙa kansa yana bin ko ina da kallo. Baiga alamar akwai wani motsi ba saboda numfashi Aymah ta ɗauke gaba ɗaya. Yay guntun tsaki ya jawo ƙofar ya rufe ransa na raya masa abarda ya shace a daren jiya bata gama sakinsaba kawai.
        Yana maida ƙofar ya rufe Aymah ta saki wani nannauyan numfashi, hannunta toshe da bakinta, idanunta kam har sun kaɗa sunyi jajur dan wahala. Da sauri ta matsa tana leƙensa ta kafar makulli. Ta zaro idanu waje da saurin sake toshe bakinta jin zatai suɓutar baki saboda ganin Papa daya danna wani ɗan abu

1 Comments On SARAN BOYE
avatar
maryam-8-1

1 year ago

Reply

Amazing book

Please Login or Register in order to submit comment