Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iskanciba. Na rantse da ALLAH Umm ba laifina baneba, sai da naita roƙonsa karyayi banaso, amma shi mugune sai da yayi. Gashi na kasa tafiya, wajen kamar zai fita, ciwo yake min, gashi inajin fitsari inajin tsoron yi Um........”
       Harga ALLAH dariya ta bama Umm, amma sai ta danne abinta tai saurin faɗin, “To ya isa zubaina sarkin magana. Wai nikam yaushene ranar hankalinki Nu'aymah?. Kai ALLAH na gode maka ni Firdausi. Yanzu shi mijin naki yana ina kike zubamin zance haka?”.
      Baki ta kumbura na haushin ba'a barta takai ƙarshen labariba tace, “Yanacan ɗaki bai tashi ba. Ni kuma ina toilet asuba fa tayi anan”. Ta ƙare maganar hawaye na silalo mata.
     Ajiyar zuciya kawai Umm ta sauke hawayen farin ciki itama na silalo mata. Koba komai dai ta fahimci yarinyarta takai mutincinta gidan aurenta. ALLAH ya ƙara wanketa a garesu ga ƙazafin da akai mata. Hawayenta ta share. Tace, “Ki shiga ruwan zafi kinji ko, ki daure duk zafinsa ya ratsaki sosai zakiji daɗi”.
       “Umm wlhy jiya daya sakani kamar zan mutu. Dan ALLAH ki faɗamin wani maganin sai nace ya sayo min zansha. Amma dan ALLAH kice Abbana ya kirashi ya kawoni gida yau”.
      “To naji, yanzu ki ƙara shiga ruwan zafin bazakiji zafin kamar na farkoba kinji ƴar albarkana”.
      Cikin jin daɗin sunan ƴar albarka da Umm ta kirata tace, “To Ummuna. In kiraki video call ki ganni, ƙila zakifi ƙarajin tausayina ma”. Da sauri Umm tace, “A'a jekiyi abinda na sakaki, kije kiyi salla lokaci na shigewa”.
        Fuska ta ƙwaɓe zatai wani sabon kukan, zatai magana Yoohan da shirunta ya sakashi a damuwa ya taso da ƙyar ya biyota yay azamar zare wayar daga hannunta dan yaji maganar video call da taima Umm, sai dai baisan amsar data bataba da ga can.
       Zabura tayi dan batasan da shigowar tasa ba. Shi kuma ya zaune a step din yana dafe kansa da faɗin, “Acshh!! Kaina”. Miƙewa ta nemayi duk da ganin yanayinsa ya bata tsoro, yay saurin damƙo hannunta ya maidata ya zaunar. Hannunsa dake akan goshinsa ya cire yana dubanta da idanunsa dake jajur. “Zeeynab baki da hankali wa kika kira? Ba dai Uncle ba?”.
          Tana cika kumatu da iska tace, “Ni ban kira Abba ba, Ummna na kira na faɗa mata abinda kaimin. Nace tasa Abbah yasa ka maidani gida”.
   Tuni ya manta da maganar ciwon kai, ya waro idanu waje yana faɗin, “Kin kasheni Zeeynab. Kika faɗa matafa kika ce?”.
        “To wa yace kayi? Gobe ma ka ƙara kaga idan bankira harda Hajjo da Abbana da Addah duk na faɗa musu ba ALLAH. Kai harma Ananah sai tasan halinka”.
      Gaba ɗaya kunya ta lulluɓe Yoohan, ji yake tamkar yana a gaban Umm. cike da ƙarfin hali yace, “Yarinyar nan ALLAH har yanzu kanki da motsi, dole na sake maidaki wajen su Dr Liam”.
     Umm da duk take saurarensu da ga can ta yanke wayar tana dariya. Dama ta tsayane ta sake gaskata zancen Nu'aymah. Wayar ta ajiye tana faɗin, “Yaron nan kaga takanka indai Nu'aymah ce. Bayan motsin ciwo dake a kanta akwai ma na hali wlhy. Ni harma ka bani tausayi”.....
       “Waye ya bada tausayi?”. Cewar baba malam dake shigowa ɗakin. Dan dawowarsa kenan gidan. Juyowa tai tana cigaba da dariyarta. Ya zauna a bakin gadon ya riƙo hannunta. “Jannat da alama dai kina cikin farin ciki, zoki ɗan sammini nima muyi tare”. Sosai take ƙara faɗaɗa dariyarta. Ta shiga bashi labarin kiran da Nu'aymah tai mata da drama ɗin data gama ji tsakaninta da Yoohan a ƙarshe. Shi kansa baba malam sai da ya dara.
      “Ai Jannat lamarin mamana sai ita. Yarinya tamkar goyon kaka. Amma koba komai ni hakan yamin daɗi tunda munji cewar dai sharri dai akai mata kamar yanda zukatanmu ke faɗa mana. Wannan shine amfanin ka bama yaro tarbiyya akan duk abinda ya shafesa ya sanar maka. ALLAH yay musu albarka su duka. Ya azurtasu da zuriya masu albarka da alkairi. Wadda zata zama maijin ƙai a garesu damu baki ɗaya”.
       “Amin ya rabbi. Sai dai kuma naji muryar mijin nata kamar wanda baida lafiya ma. Dan da ƙyar yake magana”.
        Ɗan jimmm baba malam yay yana sauke numfashi. Yace, “To inaga dai bara na sanarma yaron nan abokinsa shi sai ya nema wanda zaije ya duba halin da suke cikin, dan yanzu ni idan na kirashi a kunya zan sake sakashi tunda mamana ta ɓallo masa aikin data iya na wauta”.
     Dariya Umm tayi shima yana tayata. A take ya kira Richard dan yanzu yana da Number sa. Sai dai bata shiga ba. hakan na nufin Rich baya Nigeria kenan kokuma wayar a kashe. ya barsa akan zuwa anjima zai sake gwadawa kawai.

          A nan Austria kam Yoohan da ƙyar ya iya taimakama Aymah ta sake shiga cikin ruwan zafi. Sai dai yau batai rakin jiyaba. Hawayene dai kam tanata abunta. Baiyi maganaba dan shima takansa yakeyi, da alama ma yafita jin jiki yanzun. Tana ganin ya shiga wajen wanka tai alwala ta fice daga bayin tana ɗingishi. Yau ko jiransa ya jasu salla batayiba. Tana idarwa yana fitowa. Komawa tai kan gado ta kwanta.
      Bazai iya salla a tsayeba saboda jiri yake gani ga ciwon kai. Hakan ya sakashi yinta a zaune, yana idarwa shima gadon ya koma ya sake kwanciya. Wayar landline ya ɗauka da nufin kiran yima Aymah order ɗin breakfast saboda shan maganinta sai yaga wayarsa na haske. Hotel ɗin ya fara kira, kafin ya ɗauka wayar tasa dan silent take dama. Richard ya gani, cike da mamaki ya amsa kiran dan alamu sun nuna Rich ɗin yana a cikin Austria tunda da Number ƙasan ya kirashi.
         Ko gaisawa basuyi ba Richard ya fara jera masa tambaya a rikice saboda jin muryarsa, cikin son kwantar masa da hankali Yoohan yace, “Ciwon kai ne kawaifa. Dama kana Austria?”.
       “Jiya da dare na iso, yanzu dai idan ba damuwa bara nazo ɗakin naku na dubaka hankalina zaifi kwanciya”. Murmushi kawai Yoohan yayi da faɗin “Okay”. Daga haka ya ajiye wayar ya juya yana kallon Nu'aymah data juya masa baya. Ta naɗe a cikin bargo alamar sanyi takeji. Maida idanunsa yay ya lumshe tunda yasan akwai kaya jikinta.

        Kusan a tare Richard da ma'aikaciyar hotel ɗin suka iso. Rich ya amshi abinci kawai sannan ya danna door bell. Miƙewa Yoohan yayi da ƙyar hannunsa dafe da kansa. Ya gyarama Aymah ɗan kwalin kanta daya zame sannan ya nufi ƙofar ya buɗe. Saurin riƙesa Rich yayi ganin yanda yake layi, duk ya rikice masa da faɗan yaya zai zauna da ciwo irin haka baije asibitiba?. Amma yana faɗin wai ciwon kai ne kawai. Murmushin ƙarfin hali kawai Yoohan yay masa shi dai, ya zaunar da shi a kujera yana sake jera masa sannu.
       Kansa ya ɗaga masa yana magana cike da ƙarfin hali. “Shine zaka shigo baka sanar min ba?”.
       Rich da damuwa duk ta baibayesa yace, “Manta da batun shigowata faɗamin mike damunka Please X-man”.
      “Kai dai ka cika ruɗiya. Ciwon kai ne kawai da zazzaɓi”.
     Hararsa Rich yayi da faɗin, “Shine bazakaje asibiti ba? Ina madam?”.
      Da idanu ya nuna masa gadon da cewa, “Gata can, itama bata da lafiyar”.
       “Oh GOD. Miya faru haka?”.
Murmushi kawai Yoohan yayi baice komaiba. Hakan yasa shima Rich ɗin bai sake magana ba ya miƙe ya fita yana faɗin, “Ina zuwa Please”.
       “Okay” Yoohan ya faɗa da jingina jikin kujerar ya lumshe idanunsa. Yanason tashi yaje ya tada Nu'aymah data fara barci taci abinci amma jiri da yake gani ya hanashi motsawa. Har tsahon mintuna sha biyar Richard ya dawo da kayan magani. Sannu ya sake yima Yoohan ɗin sannan ya zauna yay allurai a cikin drip. Yana gamawa ya dubi Yoohan.
       “Ya kamata ka koma kan gado sai a saka drip ɗin”. Idanu Yoohan ya buɗe da ƙyar, batare da yayi magana ba yay ƙoƙarin tashi tsaye. Taimaka masa Rich yayi har kan gadon. Aymah nata barcinta batasan hidimar da sukeyi ba ita dai.
       Ɗaura masa ruwan yayi, sai da ya tabbatar ya fara shiga jikinsa sannan yace, “Ita kuma yaya zamuyi da ita?”. Isaka Yoohan ya ɗan furzar idanunsa a lumshe yace, “Inaga ita barta kawai, dan allura ya kamata ai mata kuma bazata tsaya ayi da arziƙi ba. Dan bata ƙaunar allura sam”.
      “Okay, idan ka tashi kayi mata. Sai dai akwai alluran a wajenka ko sai an siyo?”.
       “Sai an siyo”.
Ya bashi amsa a yanayin barcin daya fara fisgarsa. Sai kuma ya faɗama Rich ɗin sunan allurar da yake buƙata.
        Idanu Richard ya ɗan waro waje jin allurar da Yoohan ɗin ya faɗa. Cike da neman magana ya shuri ƙafar Yoohan ɗin yana faɗin, “Shegen sama, ashe kasan tsiyar daka aikata”.
       Shi dai Yoohan baice masa komaiba dan barcin ya fara masa Nauyi, Richard ya fice cike dajin daɗin ɗan uwansa ya zama babban mutum yau.
     
        Yanayin rashin jin daɗin jikin ya sakata kasa barci yanda ya kamata, ta buɗe idanunta a hankali kansa. Barci yake sosai yanzun. Ganin kamar ana ƙara masa ruwa ya sakata tashi aɗan zabure. Cike da ruɗewa ta kai hannunta ta ɗora a bisa kansa. Har yanzu kan nasa bai gama hucewa ba da zafi. Sosai damuwa da tausayinsa suka bayyana ƙarara a fuskarta. A fili tace, ‘Bawon ALLAH, ashe shima bashi da lafiya, shiyyasa ɗazun yaketa magana da ƙyar. Ɗan balarabe ALLAH na zata duk muguntar da kaimin ce ta sakaka komawa kalar tausayi ai’. Ta ƙare maganar da ɗora kanta bisa ƙirjinsa hawayena cika mata idanu ganin an saka masa allura a jiki. Dan itafa ba'a taɓa mata ƙarin ruwa cikin hankalinta dan bazata yardaba. Inhar yazam za'a ƙara mata ruwa to lallai sai an bata maganin barci ko an mata allurar barci saboda tsabar ƙiyayyar dake a tsakaninta da allura.
        Ta daɗe jikinsa kwance kafin ta tashi ta zauna, tagumi tayi hannu bibbiyu ta zuba masa idanu kaikace television ta samu. Ta shafe kusan mintuna talatin a haka kafin ta miƙe saboda fitsari da takeji. bayan ta fito kuma idonta ya sauka kan abincin. Yunwa takeji bana wasaba, dan haka ta zauna ta faraci dan ta fahimci natane dama. Tanaci tana kallonsa harta kammala dan kaɗan ma taci saboda rashin daɗin bakinta, cike da son ƙarfafa kanta da rashin daɗin da jikinta ke mata ya sakata ɗaukar magungunanta tasha kamar yanda taga yana bata kullum. Kasancewar barcin da suke sakata idan tasha ya sa ta ƙara ɓingirewa barcin a wajen.

★★★★

        A hankali Yoohan ya buɗe idanunsa saboda kaɗawar alarm alamar lokacin sallar zuhur yayi. Hakan kuma yay dai-dai da farkawar Aymah dake can kan sofa itama. Sai dai har Yoohan ya miƙe zaune ita ɗin bata tashinba tana kwancenta. Inda take ya kalla yana sake lumshe idanu da buɗewa. Sosai ciwon kan nasa yay ƙasa. Zazzaɓin ma kuwa duka ya sauka. Ya zare drip ɗin da kaɗan ya rage ya ƙare. Fuskarsa a yamutse na alamun wanda ya tashi a barci ya sauke ƙafafunsa ƙasa yana ambaton Alhmdllhi a cikin ransa. Sai da yay kusan minti uku a zaune sannan ya miƙe zuwa inda Nu'aymah ke kwance.
        Da sauri ta maida idanunta ta rufe, shikam batare da yasan idanunta biyu ba ya ɗora hannunsa saman kanta. Alhmdllh ya faɗa jin babu zafi. Ya taɓa wuyanta ma nanma sanyi ƙalau. Maganganun data sha ya dudduba yaga tashasu dai-dai, hakan ya sakashi miƙewa ya nufi bayi zuciyarsa sakayau da farinciki da nishaɗi. Jinsa yake tamkar wani sabon mutum a duniyar mutane. Aymah na ganin ya shige ta tashi zaune fuskarta a curkuɗe kamar zatai kuka. Gaba ɗaya jitake tama rasa abinda ke mata daɗi a duniya. Babu abinda tafi buƙata kamar ta ganta a gaban Umm ɗinta. Ta haɗiye ƙwallar daya cika mata idanu tare da zabga uban tagumi.
       A haka Yoohan ya fito ya sameta. Kallo ɗaya tai masa tai azamar maida kanta ƙasa saboda ganinsa da ga shi sai boxer da ƙaramin towel a hannu. Direct yayo kanta yana faɗin, “Kin tashi?”. Kunya ta hanata masa magana, sai kai kawai ta kaɗa masa. Bai damuba dan ya fahimci kunyarsa takeji. Ya zauna a hannun kujerar yana cigaba da goge wuyansa idanunsa a kanta. “Mike miki ciwo yanzun?”.
     Murya na rawa tace, “Komai ma”.
A ransa yace, ‘Abin nemafa ya samu ga iya madam hajjaju malamar tsiwa da shagwaba'. A fili kam sai yace, “Oh so sorry Mrs Yoohan. Jekiyi wanka sai na duba wajen na gani”.
     Da sauri ta ɗago tana hararar sa kai kace idanun faɗowa zasuyi ƙasa. Gashi dama sun kumburo saboda kukan data sha sannan akwai ja a cikinsu. Da sauri ya kauda kansa gefe gudun kar dariya ta kufce masa ya ƙara laifi. Miƙewa tai tabar wajen tana ƙunƙunin da baisan mitake faɗaba a ciki saboda hausa takeyi. Ya ɗan lumshe idanu ya sake maidasu kanta. Sosai yanda take tafiya da ɗingishi ya ƙara masa tausayinta da ƙaunarta a cikin zuciya. Tana gama shigewa ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe..............✍




Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 63

............Ganin lokacin salla zai wuce ya sakashi mata knocking dan taƙi fitowa. “Sorry baby fito muyi salla kinga munata makara. Na yarda idan mun idar ki hukuntani koda bulalane ok”.
         Fitowa tayi, dan itama batason lokacin sallar ya wuce, dama ta sake  shiga ruwan zafi ne dan tanajin daɗinsa sosai. Ƙin yarda ta kalli inda yake tayi. Taje ta saka doguwar riga, shi kuma ya saka musu abin salla. Suna raka'a ta biyu Richard ya shigo ɗakin bayan yayi knocking yaji shiru. A zatonsa ko jikin nasu ne shiyyasa ya shigo abinsa. A hankali ya ajiye kayan hannunsa idanunsa a kansu. Tsigar jikinsa sai tashi take. Haka ya zauna yanata kallonsu tamkar ya samu television har suka idar. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da Yoohan ya zubo masa harara. Da yare yace, “Shine bazaka jira a baka izinin shigowa ba zaka wani faɗoma mutane ɗaki?”. Jikin Richard duk a sanyaye yake, shiyyasa yace, “I'm sorry” kawai yana furzar da iska. Kauda kai Yoohan yayi ya maida ga Aymah dake jinsu sai dai ko ɗago kai batayiba dan itama shigowar Rich ɗin ta bata haushi. Dan tarbiyyarta ta koya mata shiga waje da sallama da kuma jiran bada dama. Yoohan ya fahimci shigowar Rich ta bata haushi. Dan aɗan zamansu ya fara fahimtar wasu daga halayenta. A hankali yace, “Kiyi haƙuri. Sai kin taimakeni wajen ceto rayuwar ɗan uwana da ga duhu zuwa haske”.
      Karan farko ta ɗago kai ta ɗan kallesa. sai kuma tai ajiyar zuciya da maida dubanta inda Rich yake zaune. Sai dai ba kallonsu yakeba yanzun. “Good Afternoon”. Ta faɗa da dasashshiyar muryarta datasha kuka.
     Miƙewa Yoohan yayi yana faɗin, “Ana gaisheka”.
        Buɗe idanu Rich yayi yana kallonta, ya amsa cike da kulawa da tambayarta ƙarfin jiki. A taƙaice tace, Am better now”.
         “Thanks God”. Ya faɗa shima yana miƙewa.  Fita yay ƴar barandar nan ya zauna, yayinda Yoohan kuma ya zauna inda ya tashi yana kiranta. Batare data tankaba ta miƙe ta nufesa. Gefensa ya nuna mata yana binta da kallo. Ita dai taƙi kallonsa sam. Abincin da Rich ya kawo musu ya buɗe. Gasashshen naman kaza ne da yasa akayisa na musamman domin Nu'aymah, sai haɗin salad da sauran tarkacen abincin Austrian daba gama haddace sunayensu tai ba itakam. Kamo hannunta yay ya matso da ita sosai jikinsa yana magana cike da lallashi.
      “Ki daure kici wannan bakinki zaiyi daɗi sosai. Kuma zaki samu sauƙi insha ALLAH. Dan abincine da ya dace da buƙatar irin yanayin da kike ciki ok”.
       Idanunta cike da ƙwalla tace, “Toni bakina fa babu daɗi ALLAH”.
       “Eh idan kikaci wannan zai miki daɗi, idan kuma kinason na miki allura tom, ina dasu buhu-buhu a ɗakin nan. Ohya buɗe bakin”. Hawayen da take maƙalewa ne suka silalo, jin zancen allura ya sakata buɗe baki ya saka mata. Share mata ya shigayi yana faɗin, “Kefa yanzun babban mace ne, kin girmi harkar yara. Kona tayaki ci ne?”.
     Da sauri ta ɗaga masa kanta alamar eh.
    Yace, “Okay to dinga bani da kanki muyi maza mu mucinye kinga Rich yana jirana”. Babu musu ta dinga bashi shima yana bata. sai ko gashi sun cinye kazar tas harma suka ƙara da wani abun. Yana son ɗaukar allurar da Richard ɗin ya kawo amma bayason ɗaga mata hankali. Hakan ya sakashi ɗaukar ledar yabar wajen. Bata fahimci mizaiyi ba shiyyasa bata maida hankali kansa ba. Sai tattare kayan da sukaci abincin take.
       Batare data san mi yayoba yazo ya sake zama kusa da ita. Kallonsa tayi sau ɗaya ta janye idonta tana tura baki. “Ba kace jiranka akeba”.
        Wuyansa ya shafo yana gyaɗa mata kai. “Magani zansha sannan. Ɗakko min gasu can”. Kamar zata fasa masa kuka ta miƙe inda ledan maganin yake. Batason yin tafiya saboda zafin da takeji. Da kallo ya bita harta ɗakko ta juyo sannan ya janye idonsa.
         Ledar data miƙo masa ya haɗa d hannunta gaba ɗaya ya jawota saman cinyarsa. kafin ta sami damar yin magana ya manne bakinsa da nata tare da saita allurar dake ɓoye cikin ɗayan hannunsa a inda ya dace. Tanajin shigar allurar ta nema fisge jikinta daya fara rawa dan abin yazo mata a bazata. Ya rumtse idanunsa da sauri saboda wani shegen mintsini datake masa a hannunsa. Allurar ya zare tare da bakinsa yana faɗin, “Ouch!!. sweet girl Zaki fasamin fata”.
        Lafewa tai a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere da shashshekar kuka mara sauti. Ga hawaye na zirara. Goshinta ya sumbata yana ɗan murmushi. Am sorry bazan ƙaraba huyim?”.
      Ita dai bata tankaba. Tanata hawayenta ne. Cigaba yay da shafa bayanta har sai da ta daina kukan sannan ya sauketa a kujerar, a gabanta ya durƙusa hannunta cikin nasa. Ya share mata hawayen da ɗayan hannun, a ransa yana dariyar rakinta akan allura. Sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa yanda ya kamata sannan ya duƙo ya sumbaci kumatunta da bakinta. “Bara inje inazuwa. Insha ALLAH wajen zai daina zafi kinji”.
      Batace komaiba. Amma yasan tana jinsa. Ya sake sumbatar laɓɓanta sannan ya miƙe. da kallo tabi bayansa harya fice ƴar barandar nan. Sai ta maida idanun ta lumshe duk da ba barci takejiba kuwa.

       ★★★

  “Sai yanzu kagama lallashin?”
       Richard da ke danna lap-top ya faɗa cike da tsokana.
           Hararsa Yoohan yayi, yaɗan sosa tsakkiyar kansa da cewa, “Ka samin ido da yawa fa”.
     Dariya Richard yayi kawai. Sai kuma ya juyo masa da fuskar lap-top ɗin yana sauke numfashi. “Brother lamarin zancen cikin nan fa akwai rikitarwa. Kasan gaba ɗaya Doctors ɗinan gaskiyar abinda suka gani suka faɗa? A iya bincikena babu wanda ya haɗa kai da su wajen bada result ɗin ƙarya, aikinsu sukayi a gaske”.
         Yoohan dake kallonsa yana ɗan taunar lip ɗinsa na ƙasa ya lumshe idanunsa da buɗewa a kansa. Da ɗan yanayin ruɗani yace, “Amma to miyasa sukaga haka? Yarinyar nan fa She's virgin wlhy”.
       “Really?”.
“Kasan bazan faɗa maka abinda ba haka yakeba Rich. Amma lallai akwai abinda ke ɓoye da bamu sani ba. Minene sauran bayanin?”.
         Iska Rich ya furzar yana matso da kujerarsa kusa da Yoohan, ya gyara zaman lap-top ɗin. “Nabi diddigin duk abinda abin recording ɗin nan ya naɗa na mai aikinku. Ga su nan zaka iya samun lokaci ka saurara. Nata tunanin ta hanyar dazan samu wayarta, shine da mukai magana da kai kace nasa Blessing. A randa mukai maganar kuwa washe gari nasaka Blessing ta sato mana wayar har gidan Uncle ɗin madam ɗinka. Waɗanan sune gaba ɗaya Contacts ɗin wayarta. Na kuma bibiyesu dukansu da duk wayoyin da tayi da masu Numbers ɗin. Abinda na gano na farko shine kakar madam ɗinka kamar tana kan sani ta aiko yarinyar nan wajenku. Sai dai dalilinta nayin hakanne sam ban saniba gaskiya. Nabi duk hanyoyin dazan iya fahimtar wani abu ban samu dama ba”.
       Kai kawai Yoohan da ke saurarensa da kallonsa yake kaɗawa.
        Rich ya cigaba da faɗin, “Wannan itace Number datafi kira. Sannan da itanema mukafi samun bayanai. Sai dai matsalar da hausa language suke magana. Inaga dole sai madam ta taimaka mana. Wannan shine ainahin sunan da akai register ɗin layin da shi. *_Rabi'atu Halidu dauda_* kuma yanda alama ta nuna mana mai Number tana a cikin gidansu madam ɗinka. Sai dai bamu saniba ko anan take rayuwa, ko zuwa kawai takeyi”.
         “Gaskiyarka, dolene sai da taimakon Zeeynab zamu san wasu abubuwan kam. Tunda ita dai duk wanda ke cikin gidan ko shiga da fita ta sani”. Yoohan yayi maganar hankalinsa akan lap-top ɗin.
          “Tabbas wannan shine mafita, kuma itace hanya mai sauƙi. Dan inhar wannan Rabi ɗin tana a cikin gidan to itace first suspect ɗinmu, dan inhar aka samu nasarar kamata zamu iya samun bayanai masu yawa a wajenta”.
        “Okay ina zuwa” Yoohan ya faɗa yana mikewa. Ɗakin ya koma. Sai dai daga bakin ƙofar ya tsaya yay kiran Nu'aymah da ke zaune yanzun ta kunna television tana kallo. Babu musu ta taso inda yake dan bataga fuskar wasa tattare da shi ba. Kafin ta ƙaraso ya juya ya fito, hakan yasa itama biyo bayansa har wajen. Ya gyara mata kujerar kusa da shi ta zauna.
        Wayar da Richard ke dannawa ya ajiye ya ɗan kallesu, sai dai baice komaiba. Itama dai Aymah bata kallesa ba. Coffee ɗin da suke sha Yoohan ya nuna mata alamar ko tanaso?. Kanta ta girgiza masa.
      Yace, “Okay, Please wani aiki zaki mana dama Sweet girl”. Kallonsa ta ɗanyi, sai kuma ta maida kanta ta duƙar. Shi dai Rich na jinsu amma bai saka baki ba. Sai ma latsa waya daya cigaba da yi yana turama Juliet ɗinsa text message.
          Lap-top ɗin Yoohan ya tura mata gabanta yana nuna mata Number Rabi da sunanta. “Kinsan wannan Number da sunan?”. Ɗan tsirama lap-top ɗin idanu Aymah tayi tana gyara glass ɗinta. Tai wani ɗan murmushi a bazata tana ɗagowa ta kalli Yoohan da shima ita yake kallo. “Sunan dai kam irin na mai aikinmu ne, sai dai ban riƙe Number ɗinta ba. Amma bara mu kira Umm sai ta turo mana”.
          Da ga Yoohan har Richard sunyi na'am da hakan. Yoohan ya mikama Aymah wayarsa alamar ta kira Umm ɗin. Number Umm ta saka tai dailing. Sai dai harta tsinke bata ɗagaba. Sake kira tayi, nanma har sun fidda ran zata ɗaga sai sukaji an daga. Zazzaƙar muryar Muhammad tai sallama. hakanne ya saka Aymah yin murmushi mai faɗi da cewa, “Uhm

1 Comments On SARAN BOYE
avatar
maryam-8-1

1 year ago

Reply

Amazing book

Please Login or Register in order to submit comment