Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yazam duk sanda yazo sai su maidashi tamkar wani tauraro mai fitowa a daren sha biyar.
      Cike da yaƙe madam Chioma ke basu amsa da cewar wani uzirin gaggawa ya sakashi tafiya, amma wani satin zai tsaya yay gaisuwa da kowa.

      Da ƙyar ta samu kanta daga wajensu, gashi rabin hankalinta duk yana ga Yoohan da Rich keta faman kira yaƙi ɗaga waya. Daga ƙarshe ma wayar bata shiga.
     Tun shigowar motocinsu ƙaton harabar gidan suka fahimci Yoohan ba gida ya zo ba, dan babu ko mai kama da motar da ya shigo acikin jerin mitocin dake gidan. Sai da suka gama fita sannan Madam Chioma ta ƙwalama maigadi kira cikin ƙaraji. Jikinsa na ɓari ya ƙaraso gareta cikin cika umarni.
            Kafinma takai ga jefa masa tambaya Miracle ta rigata. Mai gadi yay saurin basu amsa da cewar Yoohan baizo gida ba. Gaba ɗayansu hankalinsu sake tashi yayi, kowa ya fiddo waya suka shiga nemansa..........😒

🙄😏Mufa an ishemu kamar wani ɗan gwal🤕😤.

_____________________________
                
          Koda Yoohan yabar gidan wani ma'aikata ya nufa, duk da kuwa da ƙyar yake jan motar saboda nauyin jiki dana zuciya da rashin baccin ya haddasa masa.
        Yana tsaida motar a inda ta dace ya ɗan kife kansa a sitiyarin motar na wasu sakkani, zuciyarsa ce keta faman masa kai kawo akan abinda yake shirin aikatawa. wani ɓangaren na ƙarfafasa akan dai-dai, wani kuma na raunana masa niyyar tasa. A haka dai ya kwashe mintuna har biyu kafin kiran daya shigo masa waya ya maidashi cikin hankalinsa. Ɗagowa yay a hankali yana yamutsa fuska, ganin mai kiran nashine ya sakashi ɗagawa tana gab da tsinkewa.
          “Na shigo” ya faɗa kawai cikin harshen nasara. Bansan amsar da aka bashiba. ya dai yanke kiran tare da buɗe motar ya fita.
       Wani matashin saurayi da zasu iyayin sa'anni ya fito daga cikin ginin ma'aikatar fuskarsa ɗauke da murmushi. Kallo ɗaya zakai masa ka shaida shiɗin musulmine, dan yana sanye cikin shadda bara sol dataji ɗinkin tazarce, ga ƙaton tambarin salla a goshinsa ya kuma murza baƙar dara mai taushi.
           Tunda ya tunkaro Yoohan ɗin kallonsa yake ta ƙasa ido cike da nazari. amma ba kowa zai fahimci yana kallon nasaba musamman idan akai dubi da yanda yay wata tsayuwar basarwa yana busar iskar dake kaɗawa ta hantsi mai gauraye da ɗumin rana.
         “Ina fatan dai baƙo nane?”. Saurayin yay maganar fuskarsa ɗauke da fara'a duk da kuwa tun daga nesa ya gama shaida Yoohan ɗin ba musulmi bane.
     Duk da Yoohan yana mu'amulat da musulmai batun yanzuba, a mabanbanta ƙasashe da yarurruka kuma, baya iya sakin jiki da su. Dan shi kullum yana cikin yin taka tsantsanne karsu cutar da shi kamar yanda aka ɗorasa a hakan tun ƙuruciya. Ya dai yarda zai ƙyautatama mai buƙatar taimakonsa ko a wane irin yare yake ko addini, zai kuma gudanar da aikinsa da gaskiya ga kowa. Amma bai aminci da yayi dogon aminci da musulmin ba.
      Sai dai kuma gashi yau a karan farko na tarihin rayuwarsa matsashin saurayi ya burgesa, harma da shigar kamalar dake a jikinsa. Duk da babu ɗigon fara'a kota sisin kwabo tattare da shai sai ya jinjina kansa cikin lumshe ido yana mai miƙama saurayin hannu.
        Saurayin ya sake faɗaɗa fuskarsa da murmushi yana faɗin, “Ina godiya ƙwarai da amsa wannan gayyata tawa da banyi zaton zata karɓu ba. Sunana Hamza Ibrahim khalil, manager mai aiki a wannan kamfani namu mai albarka”. Yanda matashi Hamza yay magana da harshen ingilishi haka Yoohan dake binsa da kallo kwarjininsa na sake cika masa ido shima ya mayar masa da murtani cikin harshen nasaran. “Dr Yoohan Goshpower”. Ya faɗa a hankali kamar bayason maganar, sai dai hakan bai hana voice ɗinsa mai amo fita da ƙyau ba. “Ina sake godiya da amsar gayyata ta a karo na biyu Doctor”.
       “Karka damu” Yoohan ya faɗa a taƙaice. Hamza Ibrahim da kansa yayma Yoohan jagora har cikin office ɗinsa dake a haɗe masha ALLAH, dan babban kamfanine dake fidda kayan masarufi masu ingaci da lafiya ga jikin al'umma.
    Sai da Yoohan ya zauna kafin Hamza Ibrahim ya kawo masa lemo, ya tsiyaya a cup tare da ajiye masa gabansa a kan table ɗin. Godiya Yoohan ɗin ya masa. Hamza Ibrahim ya sake yin murmushi yana gyaɗa kansa tare da yima kansa mazauni shima.
     Sun sake gaisawa a karo na biyu. Yoohan ya sake bin ba'asin kiran da ya samu daga garesu. Babu wani ɓoye-ɓoye Hamza Ibrahim yay masa bayani cikin nutsuwarsa, tare da miƙa masa envelope yana faɗin, “Wannan itace takardar da suka aiko da ita a baka, abinda yasa ban badata kai tsaye taje garekaba saboda gudun ha'incin mutane, zata iya yuwu akai takardar amma taƙi isa gareka. Shiyyasa na buƙaci dama nazo ni gareka da kaina na kawo maka. Sai ma kace min zakazo da kanka.
       Yoohan daya gama duba takardar ya ɗan ɗago kansa yana kallon Manager, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya haɗiye abinsa a rai yana ƙoƙarin maida takardar cikin envelope ɗin.
         Duk da Hamza yayi mamaki da ganin Yoohan ɗin a matsayin wanda yaketa faman hidimtawa bayin ALLAH haka ya haɗiye mamakinsa, dan yayi imani da UBANGIJI na fidda rayayye a cikin matacce, kuma ana samun mutanen kirki a cikin kafiranma, wanda wasu musulman mu sukan gaza gyara zukatansu su zama haka duk da addininmu ya koyar damu komai. cikin hikima irinta masu ilimin addini dana zamani yace, “Yallaɓai ina fatan dai zaka amsa wannan gayyatar? Dan suma mutanene masu karamci da mutunci kamar kai, na tabbata alkairinkane kuma yake sake girmamarsu shiyyasa suka shirya wannan liyafar a gareka domin nuna girmamawarsu a kanka”.
      Karan farko a rayuwar Yoohan da kalaman hikima sukai masa daɗi a rai, har yay wani ɗan motsi da laɓɓansa mai kama da murmushi amma ba murmushin bane ba. Idanunsa ya ɗan lumshe na wasu sakanni yana nazari. Ba zuwan bane matsalarsa, ciwonsane damuwarsa. Bayason kowacce kalar hayani, ba kuma ya buƙatar shiga cikin kowanne irin mutane gudun ƙuntatama wani. To amma kuma maganar Manager tai tasiri a ransa harma da tunaninsa.
     Buɗe idanunsa yay a hankali ya ɗan gyaɗa kansa, “Babu damuwa zanje ɗin, sai daifa ka shirya ayi tafiyar tare da kai”. “Ni kuma Doctor?”. Manager ya faɗa yana ɗan waro idanu. “Indai kace bazakajeba nima kam zan fasa, dan saboda kaine dama zanje. Banyi musu komai dan su damu da sanina ba, sannan wanna shine karo na farko da aka buƙaci yimin karamcin da bai shafi aiki na ba ko yarena ko addinina ba. Shiyyasa nakeson na halarta ko zai shiga tarihin farko da ƙarshe na rayuwata”.
         Manager ya gyaɗa kai a ransa yana faɗin ‘daga ganin wannan a Christians ɗinma inaga ɗan ɗariƙar Catholic ne, ALLAH yasa ina ɗaya daga mutanen da zasu jagoranci duhunsa ya samu haske’ a zahiri kuma sai yay murmushi da faɗin, “Babu damuwa, indai kana buƙatata a tawagar masu rakkiya bazan ƙi ba”.
    Hannu Yoohan ya miƙa masa tare da yin godiya, kafin ya miƙe alamar zai wuce dan yasan hankalin families ɗinsa nacan a tashe da rashin ganinsa.
     Har mota Manager yay masa rakkiya yana ƙara masa godiya sosai, dan yana cikin mutanen da ayanzu company ɗin ke jin daɗin shigowarsu cikin manyan Customers.

★★★

         Lokacin da Yoohan ya iso gidansu ya iske kowa a birkice, dan har papa ya baro church yayo gida. Harma yana shirin kiran police station yay report.
     Tun a harabar gidan ya fuskanci akwai abinda ke faruwa a gidan, dan yaga baƙin motoci da yake ƙyautata zaton na Uncles nashi ne. Sannan yanda yaga Guards ɗinsa da sauran securitys ɗin gidan na sauke manya-manyan ajiyar zuciya yasan da walaki. Amma kowa bai tankamawa ba ya nufi ƙaton ƙofar falon nasu na glass da yaja manya kuɗaɗe masu nauyi koda ba'a faɗaba.

      Wani ihun farin ciki Miracle ta kurma dan itace ta fara ganinsa, kafin ta kwaso a guje tazo zata ɗane masa jiki. Sai dai yanda ya wani uban tsumewa ya sakata jan birki a gabansa ta kama hannunsa kawai ta ƙanƙame a ƙirjinta. A take sauran yaran gidan da baƙin ƴammata da samari yaran Uncles ɗinsa suma duk suka taso kansa. Basubi takan tsumewar tasaba sukam duk suka rungumesa.
     Da ƙyar madam Chioma ta samu suka sakesa, itama ta matsa ta rungume abinta tsam yanda takeso hawaye na gangaro mata akan fuska. Hannunsa yasa ya ɗan buga bayanta kaɗan tare da ɗagota yana mamakin hawayen na miye? Batare da yace komaiba ya ciro handkherchief a aljihunsa ya share mata hawayen.
          Ƙarasowar su Papa da Uncles nashi uku yasa madam Chioma matsawa suma duk suka rungumesa, hakama matansu. Shikam dai kansa sake ɗaurewa ya keyi, dan haka ya tambayesu wai ko lafiya?.
     Basu bashi amsaba sai da Madam Chioma data kama hannunsa ta kaisa har saman kujera, Victoria ta kawo masa ruwa dan kowa yasan yafi ƙaunarsa sama da kayan zaƙi. Bai musaba ya amsa yasha kusan fin rabi, sannan ya sake binsu da kallo da sake tambayar yaya akayi wai?.
       Gebrail ne ya sanar masa da komai. Hakan ya saka Yoohan ɗin dafe kansa dake sara masa kaɗan-kaɗan yana ɗan lumshe idanu. Shi abin nasuma takaici ya bashi sosai. Amma sai baice komaiba. Sanin bazai ceɗinba yasa babu wanda ya damu da jiran sai yace ɗin. Saima ringuɗa da sukai Dining domin yin breakfast ɗin da suka kasa yi tun ɗazun.
        Shi dai Yoohan duk a takure yake matuƙa, amma sanin baƙar masifar Uncle Zamani yasa shi haƙura ya zauna akai breakfast ɗin da shi, wanda shi sam ma baici wani abin kirki ba. Bayan sun kammala sukai sama shida sa'anninsa su uku, sai Rich daya dawo daga nemansa. Amma duk masifar da yay masa akan ɗaukar mota ya fita shi kaɗai a wannan halin da yake ciki sai bai kula Richard ɗinba. Shima bayan gama masa masifar sai ya watsar dashi ya biyema su Osen kawai da suka baje a falon Yoohan ɗin suna kwasar dariya da hirarsu ta shaƙiyanci akan ƴammata.
      A haka Solomon ya shigo da kwalaben barasar da sukai Order, sai kofuna da ƙanƙara. bayansa cikin ma'aikatan gidanne ɗauke da tray da aka shiryo gasashen naman kaji a cikinsa wanda zasuyi amfani dashi wajan shan barasan.
     Sai da suka jera musu komai yanda ya dace kafin su fice su barsu. Miƙewa Yoohan yay zai shige bedroom dan ya rage kayansa. Da sauri Godwin yace, “Mr-x ina zuwa?”. (Dan haka duk abokansa ke kiransa da shi, Rich kawai yafi kiransa da Doctor) Yamutsa fuska Yoohan yay yana hararsa, dan dama abokin bugawarsa ne, kawai dai dan yau baya cikin good mood ne. “Ina zuwa” ya bashi amsa a taƙaice yana shigewa.
           “Wai mike damun Boss ɗinka ne?”. Joseph ya faɗa yana kallon Richard.  Cikin damuwa Rich yace, “Matsalarsa ce dai ta rashin barci ta motsa, nayi-nayi yasha barasa ko nai masa allura yaƙi”.
         Godwin ne yace, “Shegen taurin kan Mr-X ai ba ƙarewa yakeba, ni wlhy sonake wataran na samu wata na biyata tai disvirgin ɗin gayen nan kozai ware yaji daɗin rayuwarsa. Duniya ai sai da jin daɗi, amma shi yabi ya wani ƙanƙame kansa kamar wanda bai wayeba ko ba'a turai yay rayuwa ba. Minene a giya? Dama da shanta kawai nishaɗine, kuma tunda munada aikin yinmu sai fa lokaci- lokaci muke shanta, ba kuma mai cutarwa ba.......”
     Katsesa Joseph yayi da faɗin, “Kaga G. Ka barsa, Mr-x tsarinsa kenan shi da ra'ayinsa, koka manta tun muna secondary shi dama komai nasa da ƙa'ida ya keyi. so ni banga abin damuwa da har zaku shiga masa rayuwa da yawaba, kubarsa ya tsara ma kansa yanda yake buƙatar ya rayu Ok?”.
           Richard yace, “Hakane Joseph, amma idan ka lura shima fa bawai jin daɗinne baya buƙata ba, kawai shi dai ya ɗauki burin duniyane ya ɗaura akan aikin nan namu, a tunaninsa duk abinda zai sha zai iya shagaltar da shi akan aikinsa, sannan mata ma zasu iya takura masa su hanashi yin rayuwarsa da ƙyau, kunsan mutum namu ɗan hutune, ko mace bata faɗa masa son jiki ba”.
     Dariya suka kwashe dashi gaba ɗaya suna mai haɗa kofunan da suka zubama barasa a ciki alamar chssss.
       Hakan yayi dai-dai da fitowar Yoohan daga ɗaki, ya canja kayansa zuwa wando da riga duk blue na kamfanin adidas. Duk da hayaniyar tasu bai sonta haka ya zauna a cikinsu dan gaba ɗayansu childhood Friends ɗinsa ne, kuma ƴan uwansa na jini dan duk ƴaƴan ƙannen papa ne, sai Osen ne kawai ɗan aboki shima kuma iyayen nasu sun zama kamar ƴan uwa, sai kuma Richard shi kuma abokinsa. Amma tare sukai secondary school dukansu, hasalima duk ajinsu guda.
     Osen ne ya miƙa masa cup duk da yasan ba sha zaiba. Aiko Yoohan ɗin ya yamutse fuska da girgiza masa kai tamkar mai ƙyanƙyamin giyar ma. Dariya suka sanya masa suna zuba masa shaƙiyancin da suka saba, tare da labarin daɗin da ƴammatansu ke jiyar dasu harma da karuwai dan dukansu ji suke da ƴan kuɗaɗe a aljihu. iyayensu kuma sun tara, sanna suma ɗin gwasaken kansune sosai. Shiyyasa suke zuba tsiyarsu a garin Abuja da Lagos kamar babu gobe.
         Duk abinda sukeyi saboda Yoohan yaji haushine yay budurwa, dan har maganar ƴammatansa dake bala'in sonsa suke kawowa harda Miracle, tare da koɗa ƙyawunta dama na sauran ƴammatan da Yoohan ɗin shi yake nuna kullum basa gabansa.
         Joseph yace, “Mr-x daga yau ka fara taka tsantsan da G-boy, dan ya shirya yanda za'a maka fyaɗe, kaga sai kasan zaman da zakai da shi”.
    Mangare ƙeyar Joseph Godwin yayi yana faɗin, “Munafiki, halan giyan ya fara kai maka karo zaka haɗani da shi”. Dariya suka kece da ita duka. Yoohan dake harar Godwin ɗin yace, “Barma wani kare kanka naji sanda kake faɗa ai, an faɗa maka ni irinka ne da baida damuwa saita kwana da mata. Please, try and change your habit kaima”.
     Nanma dariya suka sanya, dan sunsan kam G-boy shege ne akan mata, duk yanda zai yaudareki ya biya buƙatarsa ya sani. Rich yace, “Calm dawn my Doctor, duk randa ya aikata maka haka zuwa zakai kawai ka tona masa asiri wajen babien sa, dama gata da shegen kishi kamar taci wuta a cikinta.......”
        Osen dake ƙoƙarin yagar nama yace, “Ashe ka ganota, nifa haushi take bala'in bani, amma G-Boy sam baya ganin laifin hakan da take masa, da kayi magana saiya nuna cewar son da take masa ne”.
       Ajiyar zuciya Yoohan da warin giyar ya fara hawar masa kai ya saki, ya miƙe a hankali ya ɗauki basket ɗin da aka zubo musu kwalaban giyan ya nufi hanyar fita. Da sauri suka shiga kwala masa kira akan ya kawo musu abinsu, amma baiko juyoba ya fice yama kullesu ta baya ya sauka ƙasa. Canma iske su Papa yay suna ɗora tasu suna hira da dariya harda su Momy suma sha suke. Sosai ransa ya sake sosuwa, sai kace ba yanzu papan ya gama wa'azi a church ba. Tsaki yay ciki-ciki ya wucesu batare da ya tanka musu ba yana ƙwalama Solomon kira.
       Da gudu ya shigo kuwa, ya miƙama masa basket ɗin kawai babu bayanin komai ya fice a falon. Garden ya nufa. Sai dai kuma yana shiga ya hango su Miracle a cikin swimming pool suna wanka. Cike da farin ciki duk suka zuba masa idanu, kowacce kwaɗayinta a kansa na fitowa fili saman fuskarta. sai dai kuma tuni ya juya yana jan wani tsakin takaici. Wannan taron yasa sam bayason zama gidan ranar lahadi, yanzu haka zuwa anjima gidan sake cika zaiyi da wasu baƙin kuma. Solomon ya bama key ɗin ƙofar sashensa daya kulle su Rich, yace yaje ya buɗesu, shi kuma ya fice gidan a ƙafa duk da kuwa rana ta fara ɗagawa kuma akwai ɗan zafi............✍

Amin afuwa jiya ciwon kai ya hanani sukuni na kasa typing ɗin🤦🏻.

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


No. 23

................Tun sakkowar Yoohan daga sashensa Momy tai saurin ajiye kofinta na barasa, dan Yoohan ya daɗe da hanata shan giya, kuma ta masa alƙawarin dainawa. Sai dai wani lokacin damuwar da take ciki kansa tasha abinta musamman da daddare idan zata kwanta barci. duk da dama wani mai yawa take sha ba. Binsa tai da wani shegen kallo tamkar idanunta zasu faɗi ƙasa, yayinda fuskarta ma ta nuna shauƙi sosai fiye da yanda suke zaune. Yunƙurawa tai zata tashi amiyarta madam Monecca tai saurin riƙe mata hannu tana girgiza mata kai cikin hikima. Duk da bataso hakanba saita koma ta zauna tana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciyar da harsu Papa da fira ya ɗaukema hankali basusan da wucewar Yoohan ɗinba suka juyi suna kallonta.
          “Lafiya Darling?” papa ya faɗa cike da kulawa a gareta. Murmushi yaƙe ta masa da cewar “Babu komai, bara naɗan rage kayana dai sun fara min nauyi”. Murmushi yay mata da aika mata kiss daga inda yake. Ta miƙe tana fadin, “Thanks Honey”.
       Rakata da idanu yay cike da so da ƙauna harta haye sama sashen bedrooms ɗinsu. Sai da ta wuce da kusan mintina goma kafin Madam Monecca ta miƙe itama tana neman excuse ɗin zuwa toilet. Duk da kowa yasan dama amintarsu tafi zuwa ɗaya da madam Chioma babu wanda yay zargin komai a sauran matan. Sai ma maida hankalinsu ga hirar mazajen su da sukayi kawai.

        A bakin gado Madam Monecca ta iske Momy zaune ta dafe kanta. Ta ƙarasa kusa da ita ta zauna, cikin harshen nasara take tambayarta damuwarta?.
         Ɗagowa Madam Chioma tai idanunta cike da hawaye tana kallon ƙawarta, tace, “Monecca! Ina cikin damuwa sosai akan Yoohan, gaba ɗaya ya sake canjamin, ɗan kusancin da nake murnar ya ƙara shiga tsakaninmu a yanzu neman hanyar kakkkaɓar da shima ya keyi. Rungumarsa ma yanzu bayason yaga nayi, sai kiga ya kama ɗacin rai. Nifa na gaji da ɓoye-ɓoyen nan, dan gashi Honey harya fara tunanin wai yay masa maganar aure.…..”
       “Aure!?” Monecca ta faɗa cikin tashin hankali.
       “Ki bari kawai, jiya da yay maganar naji kamar na bindige shegen nan nama huta da wahalansa, Monecca zan fitoma Yoohan a mutum kawai da buƙatata, duk da kuwa nasan shegen taurin kansa”.
        Cikin sauri Madam Monecca tace, “Karkiyi haka, dan zaki samu babbar matsala. kidai bari muyi tunani akai. Wai ita Mira bazata koma gidansu ba ne. sai naga kamar itace ke ɗauke masa hankali?”.
        Cikin dariyar da Madam Chioma batai niyyar yiba tace, “Miracle fa? An gaya miki kalloma ta ishesa ne a gidan nan. Dama fa Zamani ne keta son ganin Yoohan ɗin ya aureta. kuma ni na gama fahimtar shima akwai tasa manufar akan hakan, shi kuma Yoohan ɗin duk da ƙyan Miracle ɗin bata gabansa shiyyasa nima zamanta a gidan bai taɓa damunaba”.
     Ɗan taɓe baki Monecca tayi tana hararar Madam Chioma a kaikaice. a ranta kuwa rayawa take duk rintsi saita bi hanyar mallakar Yoohan ɗin, dan itama wani Masifaffen sonsa take, tana dannewa ne a gaban ƙawar tata kawai. Sun tattauna sosai ta yanda suke ganin ya dace a samu Yoohan ɗin a hannu. Kafin su fito wajen sauran ƴan uwansu a cigaba da hira.

      Haka gidan ya cigaba da karɓar baƙi har dare, dan yau ranace ta ziyara a garesu, musamman ma gidan papa daya kasance babban mutum a wajensu.
     Yoohan bai dawo gidanba sai yamma lis, ya samu giyar dasu Osen suka sha ta ɗan sakesu, harma sun fito daga sashensa Solomon ya shiga ya gyara. Duk suna harabar gidan zaune dan wasu abokan nasu sun ƙaru saboda jin Yoohan ɗin na gari, shima sai kawai ya zauna a wajensu duk da ba firar yakeba sosai.

______________________________
                *_SAUDIA_*

     Duk da Adawiya na ƙoƙarin ɓoye halayenta hakan bai hanata sakin layi a wasunl lokutan, dan babu abinda ke sakata takaici da ƙunar zuciya kamar yanda Nu'aymah taƙi nuna damuwarta akan duk abinda take mata. Gaba ɗaya Nu'aymahr ma ta maida hankalinta ga ibada ne kamar yanda ta ɗauro niyya tun daga gida.
     Tayi mugun yin watsi da shirmen Adawiyar dan ta gama karantarta tsaf akan lamarin nata, to dama tasan tun suna secondary ma Adawiya tasha haɗata faɗa da ƙawayensu, ta kuma koma ta noƙe ta nuna ba ita tayiba. Amma sai bata taɓa nuna mata ta gane komaiba akan hakan, dan duk sanda taje ta sanarma Umm Adawiya ta mata kaza sai Umm ta lallasheta da nasiha da nuna mata muhimmancin haƙuri da ɗan uwa. Hakanne ke daƙile Nu'aymah daga ramuwa ga Adawiyar gashi har hakan ya zame mata jiki.
         A wannan tsukun kuma data fahimci Adawiya ta canja sabon salon halaye sai itama ta canja takunta a kanta tana binta da gashi cikin ruwan sanyi, a ranta tana zargin kenan dama Adawiya na son Yah Ab komi?. A duk sanda tai wannan tunanin takanyi ƙoƙarin ganin ta ƙaryata zuciyarta, dan bata taɓa ganin alamar hakan ba ga Adawiya a dacan baya. A ganinta yanzu dai daɗin aurene yasa take ganin tafita kusanci da Abdallahn shiyyasa take shirya yaƙarta a kansa.

       Yau ma kamar kullum Nu'aymah na ɗan yin barcin rana a falo, dan da daddare tafi maida hankalinta ga ibada ne, Abdallah ya shigo gidan. Adawiya ta wuce makaranta. daga hajjo sai Nu'aymah. Da tare suke da Hajjon a falo zaune suna ɗan hira sai barci ya kwasheta, itama hajjon saita nufi ɗaki ta kwanta danta huta.
         Kafe Nu'aymah da idanu Abdallah yayi ko ƙyaftawa ba yayi, ya ƙaraso inda take yay tsaye kanta yana cigaba da kallonta tamkar mai nazarin wani abu. Cikin barci Nu'aymah taji alamar tsayuwar mutum a kanta. A ɗan firgice ta buɗe idanu saboda barcin nata baiyi nisaba sosai. Ganin Yah Ab tsaye a kanta ya sakata sake zabura tana binsa da kallon tuhuma itama. Sai kuma ta kumbura baki tana ɗauke kanta cike da takaicinsa.
        Fuskarsa a haɗe ya zauna a kujerar da take kwance, hakan ya saka Nu'aymah saurin miƙewa sosai tana faɗin, “Yah Ab minene haka wai?”.
        “K kika cancanci wannan tambayar ai?”. Ya faɗa shima yana miƙewa yasha gabanta fuskarsa a haɗe, ya cigaba da faɗin, “K harkin isa ki dinga wulaƙantani akan wani banza can Nu'aymah? Kinzo inda nake amma sai wani basar dani kikeyi”.
       Cikin rashin fahimta take kallonsa, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta raɓashi zata wuce. Sake shan gabanta yayi yana mazurai, “Nabaki izinin tafiya ne?”.
     Idanunta cike da ƙwalla tace, “To idan na zauna mizan maka? Kodan kaga nazo na zauna a gidanka kakeson ƙuntata rayuwata?”. Hannu ya ɗaga tamkar zai ƙwaɗa mata mari sai kuma ya fasa ya dunƙulesa yana taune lip ɗinsa jikinsa na tsuma. Yace, “Uban wanene Ameer?”.
           Cike da takaici Nu'aymah ta kallesa ta watsar, kamar karta bashi amsa sai kuma mamakin abin nasa

1 Comments On SARAN BOYE
avatar
maryam-8-1

1 year ago

Reply

Amazing book

Please Login or Register in order to submit comment