Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Duk wainar da ake toyawa bata saniba dan barci takeyi. Baifi mintuna biyarba sai gashi ya fito.  Yanzunma bai kalli sashen da kowa yake ba ya nufi inda motar da zasu tafi take, sauran motocin uku da ɗalibansu zasu shiga da ƴan agaji kuma duk suna a harabar massallaci.
     Suna kallo motar ta fice batare da ko mutum ɗaya ya iya cemasa a dawo lafiya ba, shima kuma bai nuna ya damu da hakan ko jiran cewar tasu ba.

      Umm ce ta fara sulalewa ta koma ciki, kafin sauran suma su fara zare jiki ɗai-ɗai suna shigewa sashensu. Addah dai bayan Umm tabi tana share hawayen da ke sakko mata batare data farga da fitowarsu a cikin idanunta ba.

_____________
*_ABUJA_*

        Tunda labarin kama Nu'aymah ya isa kunne Papa farin ciki ya mamayesa shi da Madam Chioma, breakfast da suke shirin zamanyi ma su kasawa sukayi, sai kai kawo sukeyi zuciyoyinsu fes kamar an basu rabin duniya.
    Dolene yasa a koyama yarinyar hausawan nan hankali, dan shi a rayuwarsa idan da abinda yafi tsana a rayuwarsa to ƴan yankinta ne. Ya tsani yarenta fiye da mutuwarsa, a cewarsa babu abinda suka iya sai haihuwa, ƴaƴan nasu kuma babu tarbiyya sam, daga ƴan bangar siyasa sai masu bara. Sam mutanen da yankinsu basu masaba, inda ace zai iya zama shugaba, sai ya shafe yankin ko tarihinsu baza'a sake aji ba. (hummm Papa, a ringa sara dai ana duban bakin gatari).
           Abinda papa ya keta faman rayawa a ransa kenan yana murmushi. Waya ya sake ɗagawa yay magana da d.p.o ɗin akan yanzunan a bama guards ɗin Nu'aymah su taho masa da ita Abuja. Shi kuma d.p.o ya turo da accaunt Number ɗinsa yanzu zaiji alert.
        Cike da farin ciki d.p.o ya amsama papa. Babu ko tunanin komai a ransa ya aika da accaunt details nashi, ya kumayi zaman shirya takardar ƙarya akan laifin da bashi Nu'aymah ta aikataba.

(Humm! Ya ALLAH ka shiryemu ka shiryi shuwagabannin mu da jami'anmu. Ka tsame bara gurbin cikinmu, idan masu shiryuwane ka shiryesu. Idan bazasu shiryuba UBANGIJI kafimu sanin miya dace dasu, mun barka dasu😭🙏🏻).

________________
*_LAGOS_*

         Fitowarsa kenan daga ɗakin theatre a matuƙar gajiye. yanda yake tafiya kawai zai baka wannan amsar. Tare yake da likitoci uku da suka tayasa aikin, sai Nurses suma guda uku. Dai-dai sun ƙaraso ƙofar wani office nurse ɗin dake a gefen damarsa ta miƙa masa tasar hannunta ya jefa hand gloves ɗin daya cire daga hannunsa ya jefa a ciki, hannu ya ɗaga musu kawai alamar su dakata anan ya tura ƙofar ya shige.
       Basu damu ba, dan kowa yasan Dr Yoohan haka yake, mutum ne mai ƙoƙari akan aikinsa da himma, ga tausayi sosai musamman ga marasa ƙarfi. Bashi da yawan magana, sannan baida fara'a. Wanda bai fahimcesa ba zaita ɗauka kamar kullum shi cikin ƙuncin rayuwa yake, kokuma girman kaine bisa ga ɗaukakar da ALLAH ya basa. Idan kuma ka fahimcesa zaka gane cewa haka halayyarsa take, shi kawai aikinne a gabansa ba shiririta da shashanci ba. Akance likitoci mafiya yawansu sunada son mata, sai dai ga Dr Yoohan sam ba haka baneba. Duk yanda matan ke binsa da soyayya shi bama su ishesa kalloba, shi fa a rayuwarsa damuwarsa kawai shine aikinsa, sai ko family ɗinsa da taimakon marasa ƙarfi. Idan ya shiga cikin musulmi bazaka taɓa cewa shi ba musulmin bane, musamman daya ajiye ƙasunba da yanda yake gudanar da al'amuransa sak halayyar musulman ƙwarai. Sai dai fa idan kaci karoda sarƙar Cross a wuyansa da akoda yaushe baya fashin sakawa ne zaka gane daga ina ya fito. ALLAH ya ɗaukakashi a duniya a dalilin ƙwaƙwalwar aikin likitanci daya azurtashi da ita, likitane shi da kota wane fanni zai iya gunar da aikinsa akan mara lafiya, sai dai abinda ba'a rasaba kam, dan UBANGIJI shine mai komai da kowa.

         Office ne daya amsa sunansa office. Bakajin komai sai sassanyan ƙamshin turarensa dana ac. Wanda ke zaune a rikunin kujeru uku dake can gefen office ɗin yana aiki ya miƙe yana masa barka da fitowa cike da kukawa.
     Kansa ya ɗaga masa fuska a yamutse na alamar gajiya. kafin ya ƙarasa ga kujerar zamansa yaja wani file dake a jiye ya fara singing.
      Tasowa Richard yay da sauri garesa yana murmushi, ya ajiye files ɗin hannunsa gaban Dr Yoohan ɗin yana faɗin, “Doctor akwai mutane biyu da zaka ganifa yanzun kafin ka tafi hutun awa uku da rabi, idan lokaci ya cika zaka sake shiga theatre room, na mutane biyu da suka rage suma”. Da sauri Yoohan ya ɗago yana kallon Richard fuska a marairaice kamar zai fasa kuka. Richard yay saurin haɗiye dariyar dake neman kufce masa dan yasan shima da gaske Yoohan ɗin ya kai iyakar gajiya, amma sai ya fiske yace, “Da gaske nake Yoohan, gama files nasu na kammala dubawa”.
          “Rich.. Please, wlhy na gaji, sai dai kai ka dubasu” ya faɗa yana sauke numfashi da miƙewa ya nufi wata ƙofa.
      Murmushi Richard yayi yana binsa da kallo harya shige. Ya ɗan girgiza kansa da kwasar files ɗin ya fice daga office ɗin zuwa nashi shima.
         ALLAH ne ya haɗashi da Yoohan tun a secondary school, a farkon haɗuwarsu sam basa shiri, dan abokan faɗan junane a aji. Ba komai yasa rashin jituwa tsakaninsu ba sai kasancewar su duka sunada matuƙar ƙoƙari, kafin Yoohan yazo school ɗin shike ɗaukar na ɗaya a ajinsu, amma Yoohan na zuwa ya amshe wannan matsayin. Kafin zuwan Yoohan ɗin kuma kowa sonsa da girmamasa yake a ajin, hasalima shine Monitor, ƴammatan ajin ji suke tamkar su haɗiyesa kuma. Amma Yoohan na zuwa nanma komai ya canja, kan ƴan ajin ya rabu biyu, wasu na ɓangaren Yoohan wasu Richard. Dan haka aka zama abokan dabin juna, duk da sam Yoohan baya kula duk haukarsu. Rashin kulawar Yoohan ɗin tasa a koda yaushe shi da tawagarsa suke ɗauka Yoohan matsoracine, dan babu wanda ya taɓa ganin faɗansa. Sai fa wataran da suka kaishi bango yayma Rich dukan mutuwa, da ƙyar aka karɓesa a hannunsa dan Yoohan akwai zuciyar tsiya. Tun daga wannan duka da Yoohan ya masa suka koma abokan juna, tun sauran ɗalibai na ƙalubalantar abotar tasu har suka fahimci ta gaskiyace suma sukabi. Shi da Yoohan duk burinsu ɗaya ne akan karatu, dan haka haɗewarsu waje guda ta ƙara musu himma da ƙwazo. Koda suka kammala secondary kuma cikin amincin ALLAH iyayensu suka amince musu tafiya karatu tare. A gaba ɗaya rayuwarsu tare ta gudana, sai daga bayane Yoohan daya cigaba da wasu kwasakwasai (Courses) ne suka ɗan rabu, danshi ya amshi aikin da aka bashine a ƙasar London bayan zamowarsu cikakkun likitoci, saɓanin Yoohan daya ƙi amincewa.
     Daga baya Yoohan ya kuma samun ɗaukaka fiye da tashi, danshi ya ƙara faɗaɗa wasu karance-karancen daya bashi damar iya duba marasa lafiya ta kowane fanni, aikinsa ya zam zai iya yinsa a kowacce ƙasa kuma.
       Bayan shekara ɗaya da fara wannan gwagwarmayar Yoohan ya fahimci bazai iya shi kaɗaiba sai da taimakon Richard, dan haka yaje ya dabaibayesa da daɗin baki har saida ya amince suka sake curewa waje guda suke gudanar da aikin a tare. Yanzu haka shekararsu ta biyu kenan da fara aiki, suna ɗaya daga cikin manyan matasan likitoci da duniya ke alfahari dasu bama ƙasarsu ko yankin Africa kawai ba.
    A yanzu haka dai shi Richard ana shirin aurensa ma da wata baturiya, shiko Yoohan yaƙi motsawa sam, a cewarsa shi bama zaiyi aure yanzuba sai nan da wasu shekarun daya tsara.

           Ɗakine madaidaici dake ɗauke da kayan ɗaki complete, shima sai ƙamshi yakeyi kamar ba'a cikin asibiti ba. Kansa tsaye toilet ya nufa yana faman lullumshe idanu dan barci yake matuƙar ji. Tunda ya iso Lagos a daren jiya bai hutaba, dan ya iske patients da yawa da sukai booking ɗin ganinsa. Tun a jiyan yay dauriyar zaman duba files ɗinsu, waɗanda yasan akwai mafita ya rubuta musu Doctors ɗin da zasuje su gani ya turama Rich. Waɗanda kuma yasan sai shine zai duba ya sanar da Richard ya sanar musu time ɗin da zasu gansa ta hanyar text messeges.
       A safiyar yau tun ƙarfe huɗu na asuba ya baro gida, tunda yazo kuma aiki yake bai hutaba. Bayan ya gama duba adadin daya ƙayyade ya shiga theatre akan matsaloli daban-daban kuma, yanzunma ba ya gama baneba, yanada loacin hutawa ne na awa uku da rabi kafin ya koma ɗakin theatre ya ƙarasama mutane biyu dake a ƙasa kamar yanda Rich ya faɗa. Bayan ya kammala dasu zai ƙara hutun awanni uku jirginsa ya ɗaga zuwa ƙasar Kenya inda wasu patients ɗin ke jiransa canma.
            Bayan wasu mintuna ya fito daga toilet ɗin sanye da rigar wanka Blue, sai hular wanka data kare gashinsa daga jiƙewa, da alama dai baya buƙatar jiƙawar. A bakin gadon ya zauna yana mai furzar da iskar daya cika bakinsa da ita, yajawo wayarsa dake a drowar gefen gadon a jiye ya cireta a silent. Dan ya sakata a silent ɗinne tun lokacin dazai shiga theatre room. Solomon ya kira, sai akai rashin sa'a ya samu wayarsa a busy.
        Kume fuska ya sakeyi alamar baiso hakanba, ya ajiye wayar. ɗayar ya ɗauka itama ya cireta a plane mode daya sakata. Kamar jira ake ya cire ɗin sai ga kira ya shigo, kafin ya amsa kuma akai knocking ƙofar. Rasa wanne zai farayi yayi. Ɗaga wayar? Kokuwa buɗe ƙofar?.
       “Yoohan!” ya tsinkayi muryar Richard na kiransa. Duk da yayi tunanin akan maganar patients ɗin da Rich ɗin yay maganar zai dubane hakan bai hanashi tashi ya buɗe masa ƙofaba, sai dai ya sake haɗe fuska alamar da gaske ya gaji baison takura.
      Yana buɗe ƙofar yace, “Rich plea.....”
          Saurin katsesa Richard yay da faɗin, “Yi haƙuri ba wancan maganar bane, akwai damuwa Yoohan, matar da kaima aiki a kano yanzun nan Doctor Sa'ad ke sanar min an samu matsala”.
       “What?!” ya faɗa hankali tashe. Shima Richard da hankalin nasa ke a tashe ya shiga jinjina masa kai. Juyawa cikin ɗakin yay da sauri, yama manta da wata gajiyarsa. Wayarsa ya ɗauka domin neman Dr Sa'ad. Ganin ashe shinema ya kirasa ɗazun lokacin da Richard ke knocking ya sakashi kiransa. Bugu ɗaya kuwa Dr Sa'ad ɗin ya ɗaga.
       Ko gaisuwa basuyi zaman yiba Dr Sa'ad ya shiga masa bayanin dukan abinda ya faru, da halin da matar ke a ciki yanzun.
        Hannunsa dafe da kansa cikin tsagwaron damuwa yace,  “Dr Sa'ad ta yaya hakan ta faru? Ince duk yanda ya kamata a bata kulawa na sanar muku. Miyasa kuke da sakaci akan rayukan mutane!!?” ya ƙare maganar da ɗan kaushin murya.
        Dr Sa'ad da maganar Dr Yoohan tai masa zafi ya buɗe baki zaiyi magana cikin ƙoƙarin danne fushinsa, amma sai Yoohan ɗin ya kuma dakatar dashi ta hanyar faɗin, “Bana buƙatar jin komai please, zan turo maka hanyar da zakubi wajen fara bata taimako yanzun, nima ina hanyar tahowa”.
       “Okay Sir” Dr Sa'ad ya amsa masa daga can cikin wata irin murya mai cike da ɗaci da takaici. Yaro ƙarami dashi yana juyasu dan kawai ALLAH ya basa baiwar da tafi tasu, tabbas idan ba kawar da Dr Yoohan sukaiba a duniya rayukansu da hanyar cin abinsu na a cikin garari.
      (Ni dai nace Humm).

      Shi Yoohan baima saurari amsawar Dr Sa'ad ɗinba, dan tuni yayi wurgi da wayar saman gado cike da takaicin likitoci irin Dr Sa'ad, da a kullum basu da kishin ƙasarsu da jama'arsu, burinsu sudai kuɗi kawai da taƙama da aikinsu. Da hanzarinsa ya fito ainhin Office ɗin yana faɗin, “Rich Please ka bincika min idan akwai jirgi mai tafiya kano daga nan zuwa mintuna talatin”.
       Da sauri Richard ya fita daga office ɗin zuwa nasa, dan yabar wayarsa a canne. Shi kuma Dr Yoohan yaja Laptop ɗinsa dake saman tebirin daga tsaye ya shiga dannata da sauri sauri cikin ƙwarewa. A haka Solomon ya shigo ya samesa, batare daya tsayaba yay saurin shigewa bedroom ɗin domin fidda masa kayan da zai saka dan Richard ya sanar masa halin da ake ciki, kuma shi Dr Sa'ad ya fara samu a waya kafin Richard ma.
         Dr Yoohan na kammala tura abinda zai aikama Dr Sa'ad ya nufi ɗakin shima. bai wani damu da tsayawa duba kayan da Solomon ya ajiye masanba ya ɗauka ya fara ƙoƙarin sakawa, shi kuma Solomon ya fito ya bashi waje.
        Shirin yake ransa duk a jagule da takaici, yana kammalawa ya fito jacket ɗin suit ɗinsa a hannu, necktie ɗinma haka. Gashinsa kansa yau sama-sama ya samu gyara. Haka yake shi, a kullum matsalar al'umma itace tashin hankalinsa da damuwarsa. Da kaga damuwa a idanunsa to patient ɗinsa na cikin matsala ne. Baiko kalli inda Solomon ke tsaye da jikkarsa a hannuba ya nufi hanyar fita fuskarnan babu alamar wasa.
      Kusan cin karo sukai da Richard dake ƙoƙarin shigowa ya sanar masa an samu jirgi, kuma cikin amincin ALLAH zai tashi nan da mintuna goma sha bakwai ne, da ƙyar akama samu ticket ɗin guda biyu. A yanda Dr Yoohan yasan garin Lagos da yammaci irin haka yasan kafin su isa airport ma lokacin tashin jirgin ma ya wuce, dan haka ya yanke shawarar su tafi a Ambulance kawai zasufi samun hanya da sauri.
       Rich kansa yayi na'am da wannan tunanin na Yoohan, dan haka yama yanke shawarar kaisu da kansa ko Yoohan ɗin zai kuma samun nutsuwa.............✍

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*

       *_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*

_______________________________

15

.................Kaɗan ya rage su makara a hanyar zuwa airport, ALLAH dai ya taimakesu suka isa gab. Sai da Richard ya ga tashin jirgin sannan ya bar Airport ɗin yana mai kiran Dr Sa'ad ya sanar masa ga Dr Yoohan nan ya taho su kwantar da hankalinsu.
      Duk da Dr Sa'ad baiso hakanba sai ya amsa masa harda addu'ar isowarsu lafiya. A ƙasan ransa kam ji yake kamar zuciyarsa zata babbake da wuta dan takaici da tsanar Dr Yoohan ɗin da bai taɓa tare masa komai a duniyaba bayan nusar dashi ya san kansa kawai.
     Yana sauke wayar daga kunnensa kiran Madam Chioma na shigowa. Ɗagawa yay da hanzarinsa, dan yasan dai bai wuce ta kira Number Yoohan ɗin bata shigaba ko bai ɗagaba. Ya gaidata cikin girmamawa kamar yanda ya saba, kafin ya ɗora da faɗin, “Mom lafiya dai ko?”. Daga can tace, “Eh Richard, lafiya, amma na kira abokinka sau uku bai ɗagaba, nayi zaton ko yana akan aikine idan ya kammala zai kirani, sai dai har yanzu banga kiransaba. Na kuma nemesa yanzu da kaina wayarsa bai tafiya. Shine nace ko lafiya?”.
       Murmushi yay yana ƙara jinjina ƙaunar wannan uwa da ɗa a zuciyarsa. Cike da kulawa yay mata bayani yanda zata fahimta, sai dai yanda tai azamar katsesa jin ya ambaci kano sai abin ya nema firgitashi. Kafin ya samu damar tambayarta dalili harta yanke kiran.

*_ABUJA_*

       Hankalin Madam Chioma a tashe tai kiran Guards ɗin Yoohan dake shirin tahowa da Nu'aymah Abuja. Cikin azalzala ta sanar musu karsu taho su ajiye Nu'aymah a police station ɗin maza su nufi airport su tarbi Yoohan gashi nan ya taho da ga Lagos. Tai mugun basu gargaɗi akan inhar wani abu mara ƙyau suka bari ya faru da Yoohan ɗin yau to su tabbatar a bakin aikinsu kenan, bayan horo mai tsanani da zasu fuskanta kuma.
              Sanin Madam Chioma zata aikata fiye da abinda ta faɗa inhar akan Yoohan ne ya saka guards ɗin Yoohan bin dukkan umarninta. Har an fito da Nu'aymah da ko harara babu wanda yay mata a station ɗin, hasalima tana a office ɗin d.p.o tunda aka kawota suka sanarma d.p.o halin da ake ciki game da umarnin mahaifiyar uban gidansu.
       Babu musu ya amince da ajiye Nu'aymah har suje su dawo, su kuma suka shiga motocinsu suka bar station ɗin zuwa airport ɗakko Dr Yoohan da suka san nanda mintuna ƙalilan ne jirginsu zai sauka.

      Murmushi Nu'aymah tayi tana mai buɗe tafin hannunta ta kalli ƴar takardar da baba malam ya saka mata lokacin daya kamo hannunta. Takardar ta sake buɗewa ta karanta addu'ar dake ciki tana murmushi, wata irin ƙaunar mahaifinta da tausayinsa na ratsata a zuciya da ɓargo. A yau ta ƙarajin ƙwarin gwiwa akan shirin mahaifin nata. Wanda daga ita sai shi sai ALLAH daya hallicesu sukasan da shirin. Amma ko Umm yaja mata gargaɗi mai ƙarfi akan karta bari ta sani, bakomai yasashi yin hakanba sai wani dalilinsa da itama yace ba yanzu zai sanar mataba sai nan gaba.

 ______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

______________________★
 
          Gaba ɗaya Yoohan ji yake kamarma jirgin baya wani sauri, duk bayan mintuna sai ya kalli agogon hannunsa yayi ƙaramin tsaki da Solomon ne kawai ke jinsa, yay masifar ƙosawa yaga sun sauka. A yanda hankalinsa ke a tashe har sai da Solomon yaji tausayinsa ya kamasa. Yana mamakin yanda Dr Yoohan sam babu wani ƙyashi ko ƙabilanci a ransa, game da aikinsa bai taɓa banbanta kai ɗan wane addini bane ko kai ɗan wane yankine. Kansa tsaye yake ƙoƙarin sa, shiyyasa a kullum ALLAH ke sake ɗaukaka darajarsa, dan kullum bayin ALLAH cikin masa addu'oi suke a zahiri da baɗinin zuciya.
          Duk da burinsa nason jirgin yay saurin sauka ahakan bai hanashi fita cikin nutsuwa ba lokacin da jirgin ya taɓa ƙasa. Yanda yake tafiya kawai ya isa abin kallo ga mutane. Duk da fuskarsa kullum a cinkushe take hakan bai hana ya ɗauki hankalin masu kallonsa daga maza har mata ba.
         “Welcome sir”. Yaji an faɗa Lokacin da suke isowa wajen masu taxi shi da Solomon dake a bayansa. Kamar zai share sai kuma dai ya juya. A bazata idanunsa suka sauka akan guards ɗinsa waɗanda baiyi zato ko tsammanin ganiba.
     Da sauri suka ƙaraso gabansa zuciyarsu na dukan ɗari-ɗari ganin kallon da yake musu na tsagwaron mamaki da tuhuma, cike da girmamawa suka shiga gaishesa ɗaya bayan ɗaya, kafin su ɗora da masa bayanin Mom ce tace suzo su tarbesa.
      Duk da akwai magana a bakinsa game da ganin nasu a kano sai ya share bai yiba. Ya nufi inda ɗaya daga cikinsu ya buɗe masa mota ya shiga.
       Sai da suka fito da ga airport ɗin gaba ɗaya suka hau kan titi sannan ya jefama driver da Solomon ke kusa da shi tambaya a bazata.
     Cikin harshen nasara yace, “Miya kawoku kano?”. Cikin faɗuwar gaba driver ya kallesa ta madubi. Sam bama kallonsu yake ba, hankalinsa nakan waya yana dannawa. Cikin ɗan rawan baki na rashin gaskiya driver ya bashi amsa da faɗin, “Sir M... Madam ce ta aikomu”. “Yin me?”.Yoohan ya faɗa da ɗago fararen idanunsa ya zubama drivern cike da nazari. Sosai kallon ya firgitashi, dan anyi sa'a lokacin da Yoohan ɗin ya ɗago idanu yayi dai-dai da ɗagowar driver shima ya kallesa.
     Saurin riƙe sitiyarin yayi jin zai ƙwace masa, dan har motar sai da tayi ɗan tangaɗi kaɗan. “I am sorry sir” driver ya faɗa da sauri ƙirjinsa na dukan tara-tara ganin yana neman zubar dasu a ƙasa. Shiru Yoohan bai tanka ba, hasalima ya ɗauke kansa tamkar baiga wani abu daya faru ba. Sai ma ya ɗauka waya yay kiran Dr Sa'ad da kai hannu saman kunnensa ya gyara Bluetooth ɗinsa na fama dake a maƙale.

       Solomon da duk ya fahinci akwai wani abu dangane da zuwan ƴan uwanasa kanon ya haɗiye yawu da ƙyar shima yana satar kallon madubin, ganin hankalin Yoohan ɗin baya garesu sai yay saurin maidawa ga drivern. Ƙyaftama juna idanu sukai, alamar dai sun saba da yaran. Solomon ya ɗan gyaɗa kansa yana gyara zama.
     A haka suka isa asibitin batare da kowa ya sake magana ba. Tun kafin a buɗe masa shi harma ya buɗe ya fice abinsa. Da yake yau zuwan bazatane Dr Sa'ad kawai ya san zaizo sai Dr Aysha, sauran Doctors ɗin basu fito sun tarbesa ba kamar yanda suka saba.
    Sai dai tun shigowar motocinsa wasu daga ma'aikatan asibitin suka fahimci shine. Yayin da gefe guda kuma da ya zama abin kallo ga mutane. Musamman ma yanda yake tafiya Guards ɗinsa na take masa baya. Waɗanda suka sanshi nata faɗin, “Dr Yoohan yay zuwan bazata, yaukam za'asha masifa musamman akan ma'aikatan dakeda sakaci akan aikinsu.
     Duk da ya fahimci yanda wasu a cikin ma'aikatan ke ta guje-gujen sanarma iyayen gidansu zuwansa basuko ishesa kalloba. dan abinda ya kawosa shine kawai a gabansa ba su da shirmensu ba.

     Tunda su Solomon sukaga shigewarsa sai yaja hannun ɗaya daga cikin Guards ɗin suka fito, sauran kuwa na tsaye ƙiƙam tamkar an dasasu gadin duniya🙄😏, sai zazzare idanu suke sun hana masu kai kawo ta wajen sukuni. Ba marasa lafiya da ƴan uwansu kawaiba, hatta ma'aikatan asibitin a takure suke. Masu sanya da aikinsu duka sun dage saboda jin zuwan Dr Yoohan. (ALLAH ya ƙyauta. Bazakaji tsoron UBANGIJIN daya halicceka ya baka amanar wannan aikin a ranka ba sai wani shasha mutum irinka, ba kuma komai ke kawo tsoronsa ba sai gudun karka rasa aikinka🤦🏻, ya salam. Musulmai ina muka ajiye gaskiyar tamu? Ina muka ajiye koyarwar addinin namu? Ina muka ajiye tausayi dajin ƙan da aka san mumini da shi?. Ku dubafa Dr Yoohan ba musulmi bane, baɗan yankinku bane, ba yarenku bane?

1 Comments On SARAN BOYE
avatar
maryam-8-1

1 year ago

Reply

Amazing book

Please Login or Register in order to submit comment