Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana da wani sabon rainin wayon saceki akayi?. To idan saceki akayi uban wanene ya rubuta saƙwannin da kika barmana? Wanene kuma ya sacekin? Wanda naga ya ajiyeki yanzu shima wanene?. Duk sai ki bamu waɗanan amsoshin muna saurarenki?”.
       Kai Nu'aymah ta shiga girgizawa tana hawaye. “Wlhy Abbah bansan komaiba akai. Bansan su wanene ba? Bansan wanene wanda ya ajiyeninba nima? Sannan ban ajiye saƙon komaiba ga kowa wlhy”.
       “Nu'aymah!!!”. A tsananin tsawace baba malam ya kira sunanta. Sai da hantar cikin kowa ta kaɗa da tsawarsa. Itama tai baya ƙasa wanwar jikinta na ɓari na tsabagen tsorata. Dan bata taɓa ganin fushin mahaifinta irin hakaba duk da tasan yanada zuciya.
           Nufarta yay tamkar wani mayunwacin zaki, sai famar huci yakeyi jikinsa na tsuma.
      Da sauri Abban Abdallah da Abba Mustapha suka sha gabansa yana gab da isa ga Nu'aymahn. Kareta sukayi yanda bazai ko iya ganinta ba balle ya taɓata.
         Sake ɓaci ransa yay, ya kallesu da jajayen idanunsa da ƙwalla suka taru a ciki. kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya juya zai zagayesu ya damƙeta.
      Caraf aka riƙe masa hannu. Dan haka ya tsaya cak batare da ya shiryaba. Hajjo data fito yanzun nan saboda tsawarsa da taji ta kalli hannunsa data riƙe da tana sake tamke fuska batare da tayi magana ba.
        A take dukkanin jikinsa yay sanyi laƙwas, sai wata irin zufa data shiga tsatstsafo masa a goshi. Sun kai kusan mintuna biyar a haka ana kallon kallo tsakanin duka ƴan gidanma. yayinda Umm tunda Baba malam ya shigo ta sulale ta koma ciki tana hawaye.
         Da idanu Hajjo tai masa magana da yaren da tun yana yaro ya haddace sa, kafin ta saki hannunsa a hankali ta nufi Nu'aymah dake durƙushe ƙasa tana kuka har yanzun. su Abbah zagaye da ita suma har yanzun suna bata kariya daga baba malam. Kamata hajjo tai ta miƙar da ita ta rungumeta a jikinta. Nu'aymah ta ƙanƙame Hajjo sosai tana jan numfashi da ƙyar. A hankali kuma sai idanunta suka fara lumshewa, kafin kowa ya farga tama sume.
         Hajjo da taji ta mata nauyi tai ƙoƙarin ɗagota amma ta kasa. Gabantane ya faɗi tace, “Kai Mustapha zoku duba yarinyarnan kamarma bata da rai”.
      Ai kafinma ta rufe baki sun kama Nu'aymah da hanzari. Yaraf tai baya jikin Abban Adawiya alamar dai da gaske bata numfashin. Sake tashi hankalin kowa yayi, duk sauranma suka matso suna ambaton Innalillahi....
      Ɗaukarta Abban su Adawiya yay ya nufi sashen Hajjo sauran biye da shi. Yana kwantar da ita bisa kujera Ahmad na miƙo ruwa daya ciro a fridge. Amsa Abban su Abdallah yay ya zuba a hannu sannan ya shafama Nu'aymah a fuska. Ko motsi bataiba balle ai tunanin farfaɗowar ta. Sake tashi hankalinsu yayi. Ahmad da Malam ƙarami suka durƙusa da saurin kama ƙafafunta suna murzawa, suma su Abba hannayen Nu'aymah suketa faman murzawa. Amma abin tashin hankali ko motsi bataiba har lokacin.
          A yanzu kam kowa ya fara tunanin ciwon Nu'aymahr ne ya motsa, dan haka Abba Musbahu da bai jima da shigowa gidanba yay saurin faɗin, “Inaga a kira Doctor ɗinta, kamarfa ciwontane ya motsa”.
        Cikin kuka Hajjo tace, “Kirashi Musbahu, dan ALLAH ka kirashi da sauri. Innalillahi......... Zainabu karki mutu ki barmu kinji”. Kukan Hajjo ba ƙaramin sake ɗaga hankalinsu yayiba, matan ma sai faman share hawaye sukeyi.

        Duk abinda ke faruwa akan idanun Baba malam ne dake tsaye a jikin daga ƙofar falon Hajjo yana kallonsu. Kallo ɗaya zakai masa ka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali. Nu'aymah zuciyarsa ce, yana dannewa ne kawai, amma bazai yuwu ya bari son da yake mata ya hanashi hukuntata akan kuskurenta ba, dan yasan icce tun yana ɗanye ake tanƙwarashi, idan ya bushe karyewa yakeyi.

      Sun cigaba da ƙoƙarin ganin ta farfaɗo kafin Doctor ya iso, sai dai fa ko motsi babu wani sashe na jikinta dake nuna alamar zaiyi ma...........✍
     

Tashin hankali😪, kumuje zuwa.


_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
*_Typing📲_*

No. 8

...................Doctor na isowa aka maida Nu'aymah bedroom ɗin Hajjo. duk fita sukai suka bashi waje yay aikinsa yanda ya kamata. Sai Abubakar da aka bari kawai dan ya taimaka masa da wani abun idan ya buƙata.
        Sunyi jigum-jigum a falon Hajjo, kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa wadda ALLAH kaɗai yasan minene a cikinta.

       Juyawa baba malam yay a hankali ya fice daga sashen. Sashensu ya nufa dan sai yanzune hankalinsa ya kai ga rashin ganin Umm tare da su. Babu kowa a falon, ya nufi bedroom ɗinta canma babu kowa. Fitowa yay ya nufi nasa ɗakin ko tana can. Sai dai kuma nanma babu kowa. A ɗan ruɗe ya dawo ɗakin Muh'd. Muhammad ɗin kawai ya samu yana canja Uniform ɗin islamiyya dan yanzun suka taso. Baima gansaba, sai da yace, “Muhammad ina Umm ɗinku?”
     Jiyowa Muhammad yay da sauri, fuskarsa da ɗan damuwa yace, “Abba nima ban gantaba, na shiga ko ina bata nan kuma yunwa nakeji”.
       Shigowa sosai Baba malam yay cikin ɗakin idonsa akan Muhammad ɗin. “Yunwa kuma Muhammad? Bakaci abinciba ka fita ne?”.
       “Abba lokacin nasha fura wajen Hajjo na ƙoshi, yanzu kuma zanci”.
     Kama Hannunsa Baba malam yay suka fita kitchen da tsammanin zaiga Umm a can. Sai dai kuma mai aikinta kawai suka samu tana gyaran kayan miya. Cike da girmamawa ta gaida Baba Malam ɗin. Amsawa yay yana cirar tuffah dake cikin fruit tray ɗin da suke sakawa. Ƙarasawa yay wajen fanfo zai wanke Saude tai saurin faɗin, “Baba malam kawo a wanke”. Baiyi musu ba ya miƙa mata tuffa ɗin guda biyu daya ɗauka. Sake bin kitchen ɗin yay da kallo kafin yace, “Ina Jannat ɗin take na ganki ke kaɗai kina aiki?”.
       Saude data wanko apple ta ɗaura a ƙaramin filet tace, “Nima na shigo ban gantaba, dama naje can ƙasan layine na sayo mata daddawa data bada. To nadawo kuma na duba kamar ta fita, shine nace bara na gyara ko kayan miya kafin ta dawo”. Shiru Baba malam yayi gabansa na faɗuwa. Amma sai ya danne ya kalli Muhammad dake saurarensu. Filet ɗin tuffa ɗin ya miƙa masa yana faɗin, “Karɓa wannan kaje kaci muje salla mu dawo saika zauna cin abincin”.
         Kai Muhammad ya ɗaga masa da amsar filet ɗin. Yaron nagaba yana biye da shi har suka fice. Sake komawa yay ɗakin Umm ɗin dai zuciyarsa na bala'in harbawa. Tsaye ya isketa gaban Wadrobe tana fiddo kaya da alama wanka tayo. Ya sauke ajiyar zuciya da faɗin ‘Alhmdllh’ a fili. Hakanne yasata juyowa da sauri dan bataji shigowarsa ba. Kamar zatai magana sai kuma tai shiru tana kallonsa kawai.
       “Naje massallaci”. ya faɗa a taƙaice yana juyawa ya fita daga ɗakin. Binsa da kallo Umm tayi harya ɓace mata sannan ta ɗauke kanta hawaye na ziraro mata.

★★★★

        A ɓangaren Hajjo Doctor ya bama Nu'aymah dukkan taimakon daya dace kamar yanda ya saba a duk lokacin da ciwon nata ya motsa. Sai dai yau ta jima bata farfaɗo ba. Dan sai da sukaje sukai sallar magriba suka dawo sannan ya ƙarasa ƴan dabarunsa cikin amincin ALLAH ta farfaɗo.
         Godiya yayma UBANGIJI tare da fita ya sanar musu ta farfaɗo. Dan yau ana idar da salla gaba ɗayansu suka baro massallaci, baba malam ne kawai yay zamansa. Matanma suna idar da sallar duk nan suka sake dawowa harda yaransu da dawowarsu islamiyya sukaji komai.

      Bayan Doctor ya kammala komai ya buƙaci tattaunawa da su Abbah. Da ƙyar suka samu Baba malam ya baro massallaci yazo.
        Doctor ya gyara zamansa cikin girmamawa a garesu yace, “Gaskiya wannan karon jikin Nu'aymah yayi tsamari. Kunsan matsalarta ba'aso abu yana firgitata da tsanani. tsawa da duhu suna gaba-gaba wajen girmama ciwonta da ƙarfafa shi”.
        Hajjo ce tai saurin faɗin,  “Hakane likita, duk munsan wannan, kuma ana ƙoƙarin kiyayewa. Yau ɗinma kuskure aka samu kasan ajizanci na ɗan adam. Yanzu minene mafita?”.
           “To Hajjo ALLAH ya kiyaye gaba, amma kam yau abin yaso yin tsamari sosai a gareta, dan yanzu haka zancen da nake muku sam bata cikin hayyacinta, fatanmu dai ta dawo hayyacinta lafiya batare data manta komaiba ma bayan ta farka”.
       Da matsanancin tsoro suke kallonsa, sai dai kowa ya kasa magana. Da sauri yace, “Bamu da tabbacin hakan, komai na ALLAH ne, mucigaba da mata addu'a insha ALLAHU zata farko cikin ƙoshin lafiya. Dama inada shawara ne, dan tun kwanaki naso zuwa da zancen sai nai tafiya kuma, yau kwanana shidda kenan da dawowa ma, zan kuma iya komawa a koda yaushe dan na samu gurbin ƙaro karatu a ƙasar Australia ne”.
        A tare sukace, Masha ALLAH, ALLAH ya sanya albarka ya bada ikon karanto abu mai amfani”.
      “Amin ya rabbi, nagode sosai”.
      Abbah Musbahu yace, “Muna surarenka. Wane shawarace da kai?”.
        “Dama akwai wani likita babba kuma ƙwararre, dan kam ALLAH ya hore masa baiwa ta fannoni da dama inhar a ɓangaren likitancine. To wani abokina ya tabbatar min har masu irin ciwon Nu'aymah yana basu taimako. Matsalar ɗaya ce, shine ganinsa. Ganinsa nada matuƙar wahala dan yana aikine a Nigeria da wajen Nigeria. Ko a yau zai iya shigowa kano ya duba marasa lafiya ya fice, zuwa dare kuma kaji bama ya ƙasar gaba ɗaya”.
            “To ai mu Doctor ko biyansa ya kama muyi sai muyi dan yazo ya duba ta”. Cewar Abban Abdallah.
        “Ai anan gizo ke saƙar Malam. Dan ko nawa za'a biyashi bazaizo gida duba mara lafiya ba. Dolene sai dai mutum yaje yay tanadin ganinsa kamar kowa, zai baka date ɗin da zaka gansa idan har ciwonka yakai shi zai dubaka, idan kuma yaga akwai mafita zai haɗaka da wani likitan da zakaje ka gani. Date ɗin da za'a rubuta maka kuma dole a sannan ne zaka gansa babu alfarma. Kwanaki yaron president ya samu wata babbar matsalar da sai shine ake fatan ya dubasa ko za'a dace. Har jirgi aka aika ya ɗakkosa daga wata ƙasar dan kawai yazo ya dubashi amma yace suje su sai kati subi layi kamar yanda kowa keyi shi bazaije ba. Kuma dole hakan akayi”.
      Babu wanda bai jinjina wannan al'amari ba a cikinsu, sukai shiru kowa na tunanin mafita kuma. Ganin haka Ahmad yace, “To Doctor idan babu damuwa ai muma sai kai mana hanya mubi hanyar data dace ɗin na ganin nasa kawai, ko'a ina yake mu zamu bisa insha ALLAH. Fatanmu dai a dace”.
        “Hakan shine dai-dai. Ga Number ɗaya daga ma'aikatansa zan baku sai ku nemesa, insha ALLAH zai muku ƙarin bayanima fiye da nawa ma, ga kuma ta abokina ma duk zan haɗa muku shima likitane zaku iya neman taimakonsa koda ni na wuce ne”.
      Rubutawa yay ya miƙama Hajjo dake a kusa da shi, ita kuma saita miƙama Baba malan da tun shigowarsa baiyi ko tari ba. Bai musaba ya amsa ya ajiye gefensa da nufin idan ya tashi sai ya ɗauka yaje ya adana. Doctor ya tattare file ɗin bayanan ciwon Nu'aymah waje guda ya sake miƙama Hajjo yana faɗin, “Da wannan zaku gansa dole, dan ƙa'idarsa sai yaga bayanan ciwon mutum na baya inhar ya taɓa ganin likita akan hakan”.
     Nanma godiya suka sake masa. Hajjo ta sake miƙama baba malam. Amsa yay ya saka Numbers ɗin da aka bashi a cikin file ɗin ya ajiye.
     Kasancewar lokacin sallar isha'i yayi duk sai suka fice har Doctor. Bayan an idar da salla Doctor ya sake dawowa tare dasu Ahmad ya shiga ya ƙara duba Nu'aymah. Sai da ya sake tabbatar da komai ya zauna sannan ya fito yay musu sallama akan insha ALLAH da sassafe zai dawo yaga jikin nata. Idan kuma sunga da wata matsala komai dare su kirashi.
     Sun masa fatan alkairi da godiya ya tafi.

_★__★_

      Baba malam bai shigo gidan ba sai kusan goma saura, dan ya tsaya sunyi karatu ne. Sashen Hajjo ya fara shiga ya duba Nu'aymahn. Har sannan barci take, dan haka ya ɗauka file ɗin nata ya fice da shi zuwa sashensu.
      Duk abinda Umm take masa bata fasaba. Yanda kuma bai mata magana akan Nu'aymahr ba itama batace da shi ƙala ba har suka kwanta.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________
WASHE GARI
_______________

          Alhmdllh Nu'aymah ta tashi jikinta da sauƙi, kuma kamar yanda kowa yay fata bata manta da komai ba kamar yanda Doctor yayta jin tsoro. Hajjo ce ta taimaka mata tayi wanka. Yusrah ta kawo mata abinci tama zauna da kanta ta ringa bata. Ta ɗanci babu laifi, dan Yusrah lallaɓata ta dingayi ita da Hajjo.
     Kamar yanda kowa na gidan yazo ya dubata da safen haka Baba Malam da Umm ma sukazo suka dubatan. Sunji nutsuwa sosai a zukatansu ganin jikin nata Alhmdllh. Sai dai kowansu bai nunaba a fuska, sunma haɗe mata gabas da yamma.
    Hakan ba ƙaramin sake ɗaga hankalin Nu'aymah yay ba, harta kasa haƙuri ta shiga tambayar Yusrah ko wani abu ya faru bayan barinta gida ne? Dan ita tayi zaton idan ta dawo zataga kowa na murnar dawowar tata. Amma saita samu saɓanin hakan, sai ma kalaman baba malam na jiya keta mata kaikawo a cikin rai.
    Ƙasa Yusrah tayi da kanta hawaye na cika mata idanu, haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Nu'aymah ɗin mai tsanani. “Yusrah dan ALLAH kimin bayani mana? Ina Yah Ab da Adawiya duk bamma gansu ba”. Nu'aymah tai maganar cikin sanyin murya na alamun rashin jin daɗin jiki.
     Saurin miƙewa Yusrah tayi ta juya mata baya zata bar ɗakin. Nu'aymah ta riƙe hannunta itama da sauri. Hannu Yusrah tasa ta goge hawayen dake rige-rigen sakko mata a kumatu batare data juya ta kalli Nu'aymah ba.
     Dai-dai nan Hajjo ta shigo tare da Doctor da yazo sake zuwa ganin jikin nata.
         “Kai lafiyarku?”.
Hajjo ta faɗa ganin Nu'aymah da Yusrah duk suna hawaye.
         “Ba komai Hajjo”. Yusrah ta bama Hajjo amsa tana zare hannunta daga cikin na Nu'aymah. Kamar hajjo zata sake magana sai kuma tayi shiru suka bama Doctor damar duba Nu'aymahn. Yaji daɗin ganin jikin nata normal, sai dai yanason mata allura yana tsoron rikicinta da zasu kwasa. Nu'aymah ta mugun tsanar allura a rayuwarta, indai akace za'ai mata allura to lallai an taro match kuwa. Dan sai kowa yaji a gidan harma makwafta.
     Kallon hajjo yay murya ƙasa-ƙasa yace, “Hajjo ko za'a kira mana su Ahmad ne kusa. Allura zan mata kinsan kuma sai ansha yaƙi”.
       Sosai hajjo ta waro idanu waje. Taɗan kalli Nu'aymah data kwanta idonta na kallon fanka dake juyawa a hankali. Sake kallon Doctor tayi, itama a hankali tace, “bara dai a dubamin cikin iyayen nasu tunda duk basu fita ba”.
    Kansa ya ɗaga mata ya tashi ya fita falon dan ya haɗa allurar. Itama Hajjo biyosa tayi.

      Kusan mintuna biyar da fitar tasu duk suka dawo harda Baba malam dake cikin shirin fita. Batare da yayi maganaba ya kama Nu'aymah da kansa ya tayar zaune. Kallonsa take cike da so da ƙaunar mahaifin nata. Amma yanda yay kicin-kicin da fuska sai yake ƙara tsoratata. Ganin yanda ya jata jikinsa ya rungumene ya saka ƙirjinta bugawa. Dan tun tana yarinya inhar taga ya mata irin wannan rungumar to lallai allura za'a mata. Saurin ɗagowa tai ta kalli Doctor daya ɓoye hannunsa a baya. Jikinta ne ya fara tsuma, zatai magana Baba malam ya balla mata hararar da ta sakata maida kanta jikinsa ta kwantar.
      Rikici sosai akasha kafin Doctor ya mata allurar, ba ita kanta ba har baba malam da hajjo masu riƙetan saida ta tarama gajiya. Doctor kam har ƴar zufar wahala yakeyi a goshi, a ransa yana sake jinjina daru irin na Nu'aymah.
        Tunda baba malam ya maidata ya kwantar ajiyar zuciya kawai taketa faman saukewa hawaye na zirarar mata da gudu. Hajjo ta zauna inda baba malam ya tashi ta ɗago kan Nu'aymah ta aza bisa ƙafarta tana shafa mata dogon gashinta.
       Sauran magungunanta Doctor ya ajiye yayma hajjo sallama suka fice shi da Baba malam.
        Hajjo ta jima tana lallashin Nu'aymah kafin ta samu tayi shiru barci ya saceta. Amma har cikin barcin tsabar rikicinta ajiyar zuciya taketa faman saukewa a jajjere. Haka dai hajjo ta lallaɓa ta kwantar da ita da gyara mata kwanciya ta tashi ta fice.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________
______________
DUBAI
________

              Amarya Adawiya da ango Abdallah sun isa ƙasar dubai lafiya, sai dai gaba ɗaya ya canja tsarin daya shiryama kansa da Nu'aymah. Ya dai kama musu babban hotel kuma a ɗaki ɗaya. A randa suka isan kuma ya sace wayar Adawiya ya ɓoye batare data saniba.
     Ita dai duk abinda yake mata bai ɓata mata rai, haɗe fuska da ƙin mata magana tunda suka taho baisa taji haushinsaba balle sonsa ya ragu mata a zuciya. Saima ƙaruwa da ya sakeyi tanajin kamar ta haɗiyesa.
     Gadon ya bata ta kwanta shi kuma yasa bargo a ƙasa yay kwanciyarsa. Da asuba ya rigata tashi, yay wankansa yay shiri tsaf. Sai da ya kammala komai sannan ya tadata. Mamaki ya kamata matuƙa ganinsa cikin shirin fita, sai dai kuma babu fuskar tambayarsa.
       Murya a shaƙe yace, “Duk abinda kike buƙata ki kira zasu kawo miki”. Daga haka bai sake tofa komaiba yay ficewarsa daga ɗakin yaja mata ƙofar. Ta jima zaune a wajen tamkar wata gunki har gari yay haske sosai kafin ta sakko jiki a sanyaye taje tayo alwala. Duk da hakan da yay mata babu daɗi sai bataji haushinsaba. Haushin Nu'aymah nema ya kamata, dan a ganinta zaman dataine cikin zuciyarsa yasa baya ganin kowa da gashin mutunci sai ita. Aiko ta ɗauki alwashin sai ya manta wata banza Nu'aymah a zuciyar tasa har abada balle kuma wata Yusrah da tasan bata a gabansa.

“Hajiya Adawiya, ke dai kike kiɗanki kike kuma rawarki🤣😏”.

               Haka ta yini ita kaɗai, daga kallo sai cin abinci da kwanciya. Gashi ta nema wayarta ta rasa, sai kawai tunaninta ya bata kota barta a gidane kokuma ta yaddata a jirgi Yah Abdallah ya ɗauke mata. Ta barsa akan idan ya dawo zata tambayesa.
         Abdallah bai dawo hotel ɗinba sai kusan 11 na dare, harkokin kasuwancinsa ya yini yi hankalinsa kwance. Baiyi zaton iske Adawiya ido biyu ba. Amma a mamakinsa sai ya sameta zaune dirshen tana kallo. Sannu da zuwan data masa kawai ya amsa ya ɗauke kansa. Ya ɗauka kayan barci ya nufi bathroom. Tana nan zaune ya fito tsaf da shi. Nanma bata ishesa ko kalloba ya zauna a ɗaya daga rukunin kujerun ɗakin yay kira a kawo masa tea. Babu jimawa akai knocking ƙofar. Adawiya ta miƙe jiki na ɓari zataje ta buɗe ya ɗaga mata hannu. Da kansa ya tashi yaje ya amso ya dawo yay zaman sha bayan ya kunna laptop.
       Sunja tsahon lokaci zaune, Adawiya nata faman kallonsa kamar ta samu television, shiko aikinsa yakeyi tamkarma ya manta da ita a cikin ɗakin.
      “Uhhm Yah Ab dan ALLAH ko kaga wayata?”. Cak ya tsaya daga aikin da yake yana sake tsuke fuska batare da ya kalleta ba. Ba komai ya jawo hakanba sai Yah Ab datai kiransa da shi. Dan Nu'aymah itace ta fara kiransa da suna har kowama ya ɗauka. itace kuma ke kiransa hakan a koda yaushe. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya girgiza mata kansa kawai ya cigaba da abinda yakeyi.

★★★★

        Haka suka cigaba da tafiya a kwanakin da duk suka gabata na barinsu ƙasarsu. Adawiya duk a takure take, dan Abdallah kullum da sassafe yake fita, bazai dawoba kuma sai sha ɗaya. amma soyayya ta rufe mata idanu ta kasa jin zafin hakan da yake mata.
     Shiko gaba ɗaya ya ɗauketa yasa a kwandon shara ya maida hankalinsa ga kasuwancinsa kawai, dan a maimakon kwana goma da ya shirya yi a ƙasar ya maidashi kwana shida zasu wuce.

         Tun a randa Nu'aymah ta dawo gida yay mafarkin hakan da daddare, aiko tunda asuba yay kiran Number Ahmad. Cike da farin ciki Ahmad ɗin ya sanar masa komai, dan dama shima yana da shirin kiran nasa, so yake kawai jikin Nu'aymah aga yanda zai kasance a washe garin.
            Karan farko da tun faruwar al'amarin nan Abdallah yay sassanyan murmushi hawayen farin ciki na cika masa ido. Jiyake tamkar an tsundumasa aljanna yau. Yana katse kiran ya kira Momy itama. A lokacin dawowarta kenan daga sashen hajjo taje ta duba Nu'aymah itama.

        Bayan sun gaisa cike da so da ƙaunar juna irin ta ɗa da uwa, ya tambayi lafiyar kowa a gidan sannan cike da zumuɗi yace, “Momy ashe Nu'aymah ta dawo?”.
       Jimm tayi kamar bazata amsa masaba, sai kuma tace, “Uhmm! ta dawo jiya”.
        “Kai Alhmdllhi Momy, yanzu zanje na saya mana tickets kuwa mu dawo, in ALLAH ya yarda wannan karon bazan sake ta sake kuɓuce minba Momy, a yau ɗin nan ina durowa koda magriba ne

1 Comments On SARAN BOYE
avatar
maryam-8-1

1 year ago

Reply

Amazing book

Please Login or Register in order to submit comment