Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Auta kaine?”.
        Daga can yace, “Lah Aunty N dama ke ce?”. Murmushinta ya sake faɗaɗa. Sai da ya gaisheta ta tambayesa ya makaranta sannan tace masa ina Umm?.
      “Umm tana sashen Addah, amma bara na kai mata wayar”.
      Da sauri Yoohan ya girgiza mata kai. Hakan yasa itama saurin cewa, “A'a barta, amma ko zaka iya dubamin Number Rabi ka turo min yanzun?”.
       “Eh zan iya Aunty. Ranarma bani na tura miki Number Gwaggo ba da su aunty Zulfah”.
       “Yes, hakane my sweet Darling. Yanzuma ka turomin Please, amma ka nutsu ka ɗauki Number dai-dai kaji ko”.
        Amsa mata yay da to, sannan ta yanke wayar. Ko mintuna uku kuwa ba'ayi cikakku ba sai ga message ya shigo. Suna buɗewa sukaga Muhammad ɗinne ya turo. Number lap-top ɗin da wadda ya turo suka duba. Sai ko gata tazo iri ɗaya. A tare suka kalli juna. Cike dason jin dalilin zuwan Number wajensu Aymah tace, “Amma miya faru wai?”.
       “Karki damu zan faɗa miki. Saka earpiece ɗin nan ki saurari vn ɗin nan yanzu dai. Munason musan abinda ke ciki”. Babu musu ta amsa earpiece ɗin daya miƙo mata ta saka a kunne. shi kuma ya makala jikin lap-top ɗin yay mata playing na farko.
       Shiru tayi tana mamaki cike da tsoro da al'ajabi, duk da ta daɗe tana zargin rabi na musu SARAN ƁOYE bata kawo abin ya kai har hakaba. Yana karewa ta zare earpiece ɗin daga kunnenta ta riƙe a hannu tana kallon Yoohan da duk suka zuba mata ido.
         Da damuwa tace, *_“Wai tana tambayarta ne yaya zamana yake a gidanku?. shine Uwaliya ta sanar mata ita dai bataga komaiba har yanzun, dan tunda muka shiga gidan na rakata ɗaki bata sake ganina ba har yanzu. Tanama ɗakin bata fitaba._* hakan na nufin kenan ranar farko da mukaje da Uwaliya gidan”.
      Sosai fuskar Yoohan ke a tsuke. Batare daya ce komaiba ya nuna mata ta maida earpiece ɗin. Sake mata playing na gaba tayi. Bayan ta gama saurare shima tai musu bayin, dan akan dai zaman gidanne. Na uku ma haka, har na randa Momy sukai hayaniya da Aymah. Sai randa kuma Gebrail ya shigarma Aymahn ɗaki wanda yay sanadin zuwansu Austria duk ta bama Rabi labari har suna kwasar dariya. Musamman ma Rabi har faɗi take ALLAH yasa Nu'aymah ta mutu acan wajen aikin, dan ta matuƙar tsanarta. Sannan ta godema Gebrail da yaba masa.
       A matuƙar firgice Yoohan yace, “Hasashena yana dai-dai kenan. Gebrail!! Gebrail!”. Yay maganar da dukan tebir ɗin gabansu da ƙarfi yana miƙewa.
        Aymah da dama Gebrail ɗin ta zarga itama ta sauke numfashi da faɗin, “Na Gebrail ba shine important ba Yah Yoohan, tunda ALLAH ya kuɓutar dani. Bakuma sake yarda zanyi ya kuma samun damaba insha ALLAH. Wannan matar da kullum take nane da Umm ɗina tsahon shekaru itace abin duba. Bansan mi take buƙatar ji tattare da niba data addabi Uwaliya da tambaya kullum a kai na harda min fatan na mutu ta tsaneni. Sannan ita kanta Uwaliya kenan dama an kawotane dan ta dinga tattara bayanai akaina tana faɗa musu ko mi?. Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un”.
         Richard ne ya sauke nannauyan numfashi tare da kamo hannun Yoohan da ransa ke a ƙololuwar ɓace ya zaunar. “Cool down X-man. Maganar Madam nakan hanya. Na Gebrail mai sauƙine tunda a kusa da mu ya ke.......”
      A fusace Yoohan ya katsesa da faɗin. “Karku gayamin maganar banza mana Rich!!. Tayama zakuce nasa mai sauƙine shima? Ya shigarmin ɗakin mata sannan kuce mai sauƙi? Kenan raping ɗinta ya keson yi komi? Ni yaron nan zai shigarma ɗakin mata!!.....”
       Ba ƙaramin firgita Aymah tai da yanayin Yoohan ba. Dan tsantsar wutar masifa dake gauraye da kishi ta hanga cikin idanunsa. Gashin jikinsa duk ya mimmiƙe tsabar bala'i. Rich ya fahimci kishin ƴan maza ne ya motsa. Dan haka ya daga kafaɗarsa cikin lallashi yace. “Please ka fahimcemu. Gebrail bai ƙyautaba kam. Amma abinda zaka duba shi namune. Zamu iya hukuntashi a yau ɗin nan idan munso. Itako wannan fatama fa take Madam ta mutu. Kaga lamarin nata ya gawurta kuma akwai ban tsoro a ciki. Dan zata iya bata wani abunda zai halakata ma ba'a saniba........”
       Maganar Richard kam tamkar ta tsikari Nu'aymah ne. ta dubesa zuciyarta nason kawo mata wani tunani da sai yanzunne yazo mata a cikin rai ma ita. amma badai tace komai ba.
      Da ƙyar Richard ya samu Yoohan ya dawo hankalinsa akan zancen Gebrail suka cigaba da tattauna maganar Rabi.
       Ransa a dagule yace, “Wannan matar lallai akwai wanda takema aiki a gidan wannan ba basirarta bace ita kaɗai. Sannan akwai wanda ke laɓema mutane a gidan ta Window, kodai itace ɗin dai, kokuma yazam wanine daban shima”.
        Kallonsa Aymah tayi da sauri domin ƙara tuna abu na biyu. Tace, “Yah Yoohan kana nufin kaima ka taɓa ganin hakan a gidanmu?”.
      Kallonta yay da jinjina mata kai. “Tabbas nagani a randa naje gidanku game da pictures ɗin nan. Naga mutum a jikin Window ɗin Granny. Shinema ya bani haske akan lallai an ƙulla miki ne akan zancen ciki, kokuma akwai wani abu daban dasu Uncle su basu saniba. Amma kema kin taɓa ganine?”.
          “Na taɓa ganin inuwar mutum yafi a ƙirga jikin Windown ɗakina kona falonmu. sai dai ban taɓa kawo komai a raina ba dan bamayi zaton mutumu ɗin bane. Sai a daren da wannan abun zai farune lokacin cikina ya fara ciwo ina ɗagowa naga inuwar, sai kuma aka bar wajen shine dalilin zargin cewa mutumne a wajen”.
        Kallon juna Yoohan da Rich sukayi. Sai kuma duk suka dubi Aymah ɗin. Yoohan ya kamo hannunta cikin nasa da kulawa yace. “To waini abindama ya kamata tun wancan lokacin duk mu sani shine. Tayaya ma kika fara bleeding a waccan ranar?”.
        “Babu wanda ya taɓamin wannan tambayar, nima kuma ban taɓa tunanin bama wani amsarta ba,, duk da abin na'a cikin raina”. Tai maganar hawaye cike da idanunta.
     “Kiyi haƙuri, maybe kowama bai tuna bane, dan ana cikin tashin hankalin ciwonki shiyyasa. Amma na tabbata koda kowa baiso mikiba Uncle da Umm zasuyi tunanin miki ita. Yanzu ki sanar mana yaya abin ya faru?. Maybe mu samu wani evidence ta dalilin jin”.
      Hannu tasa ta ɗauke ƙwallar da suka cika mata idanu, Yoohan na shafa bayanta alamar lallashi. Cikin nutsuwa ta fara basu labarin tun daga fitowarta da gamo da Rabi datai ɗauke da zoɓo zata kai mata. Da shayi data sakata dafa mata har sauran abinda ya biyo baya ta suma. Sai da ta farfaɗo ne takejin sauran abinda ya farun a bakin Yusrah. Dan Umm bata taɓa mata maganarba har yanzu”.
      Matso da ita yay jikinsa ya kwantar da ita a ƙirjinsa yana shafa damtsen hannunta alamar lallashi, dan hawaye takeyi. Shi kansa sai faman sauke ajiyar zuciya yake a jajjere da taune lip ɗinsa na ƙasa. Richard kansa mamakin tsantsar salon makirci yake yi. Da ƙyar ya iya katse shirun nasu shi.
        “Wato idan na fahimta wannan matar itace ta bata abinda ya haifar da matsalarnan ta sha. To amma ni abinda ban ganeba anan, inhar da magani ta saka a cikin lipton ɗin ai dolene Doctors su gani? Su kuma san maganine ya haifar da bleeding ɗin. Amma kuma sai saɓanin hakan ma ya biyo baya kowa result ɗinsa na fita da zancen ciki. Kaina ya kulle gaba ɗaya”.
       Ita kanta Nu'aymah kanta ya kulle ɗin. Yoohan kam baice komaiba dan zuciyarsa a wuya take natuƙa. Ganin yanda har yanzu Nu'aymah ke hawaye ya saka Rich cewa, “Brother kaje da ita ta samu nutsuwa. zuwa dare sai mu ƙarasa magana dan dole na juya Nigeria da wuri. Akwai maganar da nake son nayi da ku kuma zuwa anjima daman”.
      Kai Yoohan ya jinjina masa kawai batare da yace komai ba.

       Bayan wucewar Rich sumbatar kan Aymah Yoohan yayi. A hankali yace, “Is ok. Kukan ya isa haka. Na miki alƙawarin insha ALLAH sai inda ƙarfina ya ƙare wajen amso miki haƙƙinki ga duk ma wanda keda hannu akan wannan al'amarin. Dan haka banason ganin hawayenki masu daraja na zuba akan azzalumai ok?”.
       Kanta ta jinjina masa. Ya miƙe riƙe da ita suka koma cikin ɗakin. A kujera ya zauna ya zaunar da ita saman cinyarsa. Zamewa tai a hankali ta kwanta dan jikin nata bawani ƙarfi yake mataba har yanzun. Ɗankwalin kanta ya zame ya sumbaci sumar kanta daketa ƙamshin gyaran jiya har yanzun. Cikin raɗa-raɗa yace, “Sweet girl!”.
       “Uhyim” ta faɗa kamar wadda barci ke shirin ɗauka.
     Ya tura hannunsa a rigarta yana shafa cikinta. Idanunsa a lumshe yace, “Bani labarinki, ina nufin yanda kika rayuwu a gidanku, da yanda kowama yake rayuwa a gidan”.
      Hannunta ta ɗora akan nasa dake shafa cikinta, sotake ta janye amma yaƙi yarda, sai ma jitai yayi sama da hannun. Ɗan zabura tayi da ɗaga kanta ta dubesa. Idanunsa a lumshe suke, sai dai yana kallonta. Hakan ya sakashi yin ɗan murmushi da ɗaga mata gira ɗaya.
      Tace, “ALLAH saima na fasa”.
Ƙasa yay da hannun nasa yana cigaba da murmushinsa bai dai ce mata komaiba. Itama sai ta saki numfashi a hankali, dan gaba ɗaya wuyar datasha jiyace ke dawo mata a rai. Kaudata tai a zuciyartata ta fara bashi labari tundaga asalin kakansu Malam Hashim ɗan jibiya har kawo yanzun. Yakan mata tambaya akan inda bai fahimtaba tai masa ƙarin bayani. A haka lokacin sallar la'asar tayi suka tashi suka gabatar. Bayan sun idan yace ta shirya suɗan fita tunda yaga jikin nata da sauƙi.
       Cike da ɗoki kuwa ta shirya. Sai da ta kammala yana fesa turare ta dubesa tana kumbura fuska. “Amma dai bada wannan jelan naka zamuba ko?”.
      Turaren ya ajiye yazo gareta, fuskar dai babu walwala. Hancinta yaja da faɗin, Silly girl waye jelana?”.
      “Wannan basamuden Solomon ɗin mana. I don't trust him bansan miyasaba”.
      Da mamaki yake kallonta, furicinta na masa yawo a zuciya. Yaɗan ranƙwafo ya sumbacin laɓɓanta da sukasha lipsgloss sunata walƙiya. “Sweet girl! Kinada rigima da yawa. Miye laifin Solo kuma?”.
    “Oho, nidai kawai I don't like him gaskiya”. Tai maganar da juya masa baya.
        “Alright. let go”.
“Indai da shine fa bazaniba”.
       “Trouble maker badashi ba ne” yay maganar yana raɓata ya wuce.
       Bin bayansa tai tana ƙunƙunin mita. Bai dai juyoba duk da yanajinta. Amma sai da yaɗan murmusa. Haka suka fice abin sha'awa. Yau dai taxi suka shiga bai amshi motar hotel ɗinba dan garau yake jinsa da sabuwar lafiya ma.

*_ABUJA NIGERIA_*

          A rayuwa madam Chioma zata iya cewa bata taɓa gamo da dare mafi tsayo irin na yau ba. Duk uwar giyar data kwankwaɗar ma cikinta a wannan dare baisa ta samu nutsuwar da take buƙata ba. Dan barcin kansa ma gagarar idanunta yayi. Ƙarfe huɗu na asuba na bugawa ta tashi tai wanka ta shirya duk da tana a cikin halin maye. Burinta kawai takwas tayi subar gidan dan jirginsu sai tara dai-dai zai tashi zuwa River state. Tana zaune wajen kallon agogo ta ɓingire barci. Hakan yama Madam Rebecca daɗi. Dan dama ta addabeta akan ta shirya. Sake kwanciyarta tayi tai barci, sai takwas ɗinma ta tashi tai wanka tai shiri. Tara saura kwata ta tada madam Chioma dake barci a kujera.
     Da wani uban ihu ta tashi saboda ganin abinda agogo ya nuna.
    “Hhheeyyyyy!!!! Heyyyy Jesus!!! Rebecca!.....”
     Da sauri Madam Rebecca ta dakatar da ita ta hanyar cemata “Please muje nidai karmu makara”.
      Da yake tafiyar itace mafi girman damuwarta sai tai gaba jiki na rawa dan da gaske barci takeji yanzun. Amma da zaman wannan barcin gara ta ganta a gaban bokanta.
      Aiko sun kusan isa a makare, dan har an fara shiga jirgi. Anan madam Rebecca tabar motarta cikin airport ɗin ta riƙe Madam Chioma dake malangarin suka shiga suma. A cikin jirgin ma barci ta kamayi, koda suka iso kuma cikin mintuna ƙalilan sai da taimakon madam Rebecca ta fita. Taxi suka ɗauka ya kaisu can tashar da zasu hau motar kusa da ƙauyen. Nanma suka samu drop da ƙyar saboda rashin wadatuwar motocin............✍


*_Ga tsoron mutuwa ga son soyayya su o, e zafafa's fan🙄😉😜😂🏃🏃🏃._*

*_BARKA DA JUMA'A😍😍🤗_*


Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 64

............Motar ta ajiyesu a wani ƙauyene dan iya nan kawai zata iya shiga saboda uwar zaizayar ƙasar dake damun ƴan kudancin ƙasarmu duk ta cinye titunan. Ruwa mai uban sanyi na kwatami madam Rebecca ta samu ta sheƙama madam Chioma saboda sunyi-sunyi ta fita a motar ita da drivern madam Chioma da giya ke aiki a kanta taƙi fita.
      Firgigit ta kawo numfashi tana wani bada faɗi tamkar zata make mutum. Duk baya sukaja kam suka bata fili. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta share fuskarta tana hararsu.
     “Rebecca minene haka kuma?”.
Dariya Rebecca tayi tana miƙama yaron data ari roba a wajensa. “Inda ba hakan nai mikiba zaki tashi ne. Lokacin da ya bamu ya kusa cika kuma kinsan halinsa”.
      Zabura kuwa madam Chioma tayi ta wawuro handbag ɗinta tana ambaton Jesus. Haka yasa itama Madam Rebecca ɗaukar tata handbag ɗin suka zagaye zaftarewar ƙasar suka koma kan titi sosai. Suna tafiya suna ƙoƙarin tare mashin dake wucewa. Amma kowanne sai kaga da mutum. Sai da sukai tafiya mai nisan zango sannan suka samu mashin ɗaya. Badan zai ishesuba suka hau, dan madam Rebecca balaifi tanada jiki. Tafi madam Chioma ƙiba. Haka suka shirma cikin jejin da korayen ciyayi suka ƙawata suna nishin matsuwa. Tafiya sukai sosai kafin su isa wani ƙauye again. Anan mai mashin shima ya saukesu dan zasu hau kwale-kwale ne. Ga madam Chioma da tsoron ruwan masifa. Duk sanda sukazo wajen bokan nan a tsorace take. Shiyyasa wani lokacin tafi buƙatar Rebecca tazo mata sai ta biyata kuɗin da duk ta buƙata. Haka suka shiga kwale-kwale tanata faman ƙunshe kanta a cikin cinyoyi. Tafiyar mintuna ashirin ta kaisu gaɓar ruwan. Daga haka kuma suka kwashi ƙafafunsu suka nausa cikin jajenin da bazaka taɓa ɗauka akwai mutum mai numfashi a wajen ba. Amma da yake zukatansu sun bushe ko tsoro basaji. Sun iso ƙauyen da bokan yake a galabaice. Kamar yanda ƙa'idar shiga wajensa take suna isowa ƙofar fadarsa suka cire duka suturar jikinsu. Haka masu tsaron ƙofar suka basu hanya suka shiga tsirara haihuwar uwarsu (😱🤦🏻). Ba wannan ne ya firgitaniba. Dan su nasan komaima iya aikatawa zasuyi. Shigarsu wajen ne ya rikita tunanina da ɗarsa tsoron duniya a raina. Dan kuwa mutanene cike da wajen suna jiran layi kowanne tsirara yake. Abin kaico da takaici da ALLAH wadai harda musulmai a wajen, kai harma Hausawa saika samu ma'abota son duniya da ruguza lahirarsu. Manyan mutane ƴan siyasa da hasashenka bai taɓa baka ganin irinsu a wajenba sai gasu tumɓur suna zazzare idanu a fadar boka. Manyan mata masu neman duniya da gudun kishiya suma gasu nan ba'a magana. Wannan ya ƙara tabbatar min da sutura na rufawa bawa asiri a idanun mutane. Dan da yawan mutane munana ne idan ka gansu tsirara wlhy🙄.
        Sai da suka tsaya gaban wasu ƙartai akai musu wankan ƙa'ida kafin su ƙarasa su hau layi inda sauran suke. Suna nan zaune masu shiga na shiga suna fitowa har layi yaxo kansu suka shiga suma.
      ‘Wa'iyazubillah’. Ɗakin bokan cike yake da gumaka na dodannin tsafinsa ta kowace kusurwa. Suna shiga suka zube sukai sujida a gaban waɗanan gumaka. Kafin su miƙe zuwa wajen bokan dake hakimce a kujera sai kace sarki. Shima sujidar sukai masa sannan suka miƙe tsaye haihuwar tsoffinsu. Shima dai a tsirarar yake dama🤦🏻. Gashi ƙaton gaske mummuna baƙiƙƙirin matsiyacin sheɗani. Kallon madam Chioma yayi ya kece da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan ya haɗe fuska.
      “Yaron da kike tattali da burin mallaka yana neman ƙuɓuce miki ko? Hhhhhhhh!!!!. Ai tun farko kece kikai sakaci. Miyasa kika barsa yay aure?”.
      Kuka ta fashe da shi, “Bangaruta ba laifina baneba. Mijina nane ya cikani da daɗin baki akan ya yarda yaron ya aureta ne dan ya halakata da babanta. Shiyyasa na yarda ni kuma. Tunda nasan ka bani abinda bazai iya taɓa kallon mace da suffar mata ba”.
        “Hhhhhhh!!!!!. Yardarki kuwa ta zamar miki matsala. dan wannan yarinyar daya aura tafi ƙarfinki. A duk inda take tana zagaye da wani haske da ko iya ganinta ni kaina banayi. A yanzu haka bana iya ganin yaron ma kansa a ƙwaryar tsafina saboda kasancewarsu tare. Ke koma basa tare shima bana ganinsa a watannin nan gaba ɗaya.....”
      “Bangaruta ka taimakeni ta tsafemin shi. Na shiga uku shikenan tawa ta ƙare”.
       “Hhhhhhh taki zata ƙarene idan wannan aikin dazan miki yazam bai kamasu ba”.
      Da sauri ta nutsu tana sharar hawaye. Ya kuna ƙyalƙyalewa da muguwar dariyarsa mara daɗin ji. Kamar yanda na faɗa miki tun farko aikinmu dake kansa bazai taɓa barinsa mu'amula da mataba sai ke. dan haka ki kwantar da hankalinki wannan kam tabbatacciyar maganace hakan bazai faruba. Yanzu zakiyi ƙoƙarin rabasa da yarinyarne kawai. gaba ɗaya hankalinsa zai dawo gareki a wannan karon dan bazamuyi masa da wasa ba”.
       “Nagode Bangaruta, sai dai kumafa igiyar nan ta tukunya ta kwance, wannan shine ya girmama tashin hankalina”.
     “Karki damu da kwancewarta, mu ta wajenmu tana nan a ɗaure. Dan bazai taɓa kwanciya da wata maceba sai ke. Cike dajin daɗi ta duƙe gabansa ta sakeyi sujida🤦🏻😭. A take ya haɗa mata duk abinda zatayi akan Yoohan da Nu'aymah. Ta dire masa maƙudan kuɗin daya buƙata sannan suka fito bayan itama Rebecca ta amshi nata aka abinda ya shafeta.
     A ranar suka sake juyiwa cikin River state a matuƙar galabaice. hotel suka kama zasu kwana sai zuwa da safe su koma abuja.

_____________________

     *_VIENNA AUSTRIA_*

     Su Yoohan da basusan wainar da ake toyawa ba sunacan hankalinsu kwance. Dan wani shagon cin ƙwalam da maƙulashe na kalolon chocolate da ice-creem ya kaita. Ko sha zumamu baya faɗama Aymah shan zaƙi ba. Tako dinga lodama cikinta cike da farin ciki. Duk gargaɗin da yake mata akan tabi a sannu saboda duk zaƙin da take danƙara zai tambayetane a wajen period bata sauraresaba.
         Sun daɗe sosai a wajen, kafin su fito da ƙafa kamar yanda ta buƙata wai tanason taga gari da ƙyau. Aiko ta gani ɗin. Dan birnin Vienna ya matuƙar haɗuwa da gine-gine masu ƙayatarwa. Sai da ta fara hakkin gajiya sannan ya tsaida musu keken doki suka shiga ya maidasu masaukinsu.

        Suna isowa wanka Aymah ta shiga. Sai faman complain take wai ƙafafunta na ciwo.  Baice mata komaiba shi dai tunda itace ta ja musu shan wahalar ai. Amma da yake ta fisa baki shine take cewa shine.
    Wanka tayo ta fito tana ɗingisa ƙafa wai ciwo take mata. Da kallo kawai ya bita shi dai, ya ɗan girgiza kansa yana miƙewa da faɗin, Silly girl maganinki kenan ai”.
       Juyowa tai tana hararsa. Sai dai shi baimasan tanayi ba dan tuni ya shige toilet ɗin abinsa. Koda ya fito ya iske har tayi shirin barci. Sai dai bata kwanta ba. Tana kwance a sofa tana kallo. Shirin barcin shima yayi. Yana kammalawa wayarsa tai Ring. Miƙewa tai zata kawo masa sai taga ya nufota. Hakan yasa ta koma ta zauna harya ƙaraso. Yana amsa yaga Rich ne, sai ya maida kallonsa gareta. “Please sa hijjab muje mu ƙarasa maganarnan yana jiranmu”.
      “Okay” ta faɗa tana miƙewa. Ta ɗauki hijjabin sallarta ta saka tare da zura Slippers suka fito harabar hotel ɗin wajen swimming pool ɗin nan da mutane keta shanawarsu tamkar rana. Daga can gefen garden ɗin hotel ɗin suka koma. dan shima dai mutane ne keta hidimarsu. Aymah ta fahimci mutanen nan sam basa banbance dare da rana halan. Dan koda yaushe su dai hidimarsu suke hankali a kwance.
       Zama sukai inda suka iske Richard. Ta gaishesa da ƴar sakewa fiye da ko yaushe. Shima fuskarsa da murmushi ya amsa mata harda tsokanar wai ta ƙwace masa aboki.
      Murmushi tayi kawai batare datace komaiba. Shi dama Yoohan bai saka bakinsa ba, sai dai ya bama Rich ɗin hannu sun gaisa.
      Bayan an kawo musu Coffee ɗin da yay musu order itama Aymah aka kawo mata lipton data buƙata sai suka fara tattaunawa akan yanda zasu ɓulloma lamarin. Suna gamawa da maganar gidansu Aymah Rich ya turama Joseph saƙo akan ya janye masa hankalin Yoohan.
     Haka kuwa akayi, ko mintuna biyu da tura saƙon ba'ayiba kira ya shigo wayar Yoohan. Ɗagawa yay suka gaisa da Joseph batare da ya tashi ba. Sai daga baya kuma ya miƙe saboda magana da Joseph ɗin yace yanason suyi.
           Yana barin wajen Rich ya kalli Aymah data ɗauke kanta daga garesu tana kallon wata mata da yaranta twins da babansu dake gefensu. Sai soyayyarsu suke zubawa da tattalin ƴan yaran nasu. jitai sun bata sha'awa sosai har tana kwatanta kanta da Yoohan ace yaran nasune wai (ƴar baba malam an fara hankali kenan🤣).
      Gyaran murya da Rich yayine ya sakata juyiwa taɗan kallesa. murmushi yayi shima dan haka kawai yay zargin abinda take tunani akan mata da mijin da yaransu.
       “Inason muyi magana Please, sai dai tsakanina da ke ne banason Yoohan ya sani”.
      Cike da mamaki ta tsura masa idanun tana tsuke fuska. Saurin girgiza mata kai yayi yana murmushi. “Am sorry sister akan gidansu ne karki zargi komai”.
      Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye da ɗan shafa gefen wuyanta alamun taji kunya. Shima sai ya ƙara murmusawa dan ta birgesa. Hakan na nufin a duk inda take zata karema ɗan uwansa mutuncinsa. Wayarsa ya miƙa mata tare da miƙewa yabar wajen. Can ya koma inda Yoohan ke zaune yana waya dan ya fahimci shima hankalinsa na kansu.
      Binsa da kallo Nu'aymah tayi. sai kuma ta buɗe video ɗin data gani akan wayar, da alama shi Rich ɗin ke buƙatar ta gani. Ba ƙaramin bugawa ƙirjinta yayi ba, saboda cinkaro da kanta a ranar data shiga ɗakin papa ta ɗakko hoto. Sai dai iya falone. har shigowar Papa da Andrew falon. Shigarsa bedroom ɗin da fitowarsa da sake komawarsa. Harma fitarta da kayan harƙallar papa da suke magana akai shi da Andrew. Cocaine ce da wasu ƙwayoyi, sai abinda ke cikin ɗayar jikkar dai bai buɗeba, hakan yasa batasan minene ba. Hannu tasa ta sharce zufar data tarar mata a goshi. Ta ƙara playing ɗayan video ɗin dake a ƙasan wancan shima. Shi kuma papa ne da wasu mutane yana bada kwangilar a kasheta duk sanda suka dawo Nigeria. Randa aka kashetan kuma a kashe baba malam shima. ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ ta shiga maimaitawa tana kallon inda Yoohan da Rich suke zaune. Ganin Rich nata jan ra'ayinsa ga barin

1 Comments On SARAN BOYE
avatar
maryam-8-1

1 year ago

Reply

Amazing book

Please Login or Register in order to submit comment