Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaye tana binsa da wani shegen kallo na fusata, dan ko kaɗan batai tunanin shiɗinne yasa a kawota nan wajenba, saboda sam bata wani gane guards ɗinsa ba, hasalima ta manta da shi da abinda ya faru tsakaninsun.
     Nunashi tai da ɗan yatsa babu alamar koda tsoro tattare da ita, “Kai ne dama kasa a kawoni nan wajen?” tai maganar fuskarta ɗauke da murmushin takaici, sai kuma ta haɗe fuska da maida dubanta ga d.p.o. “Yallaɓai ai bani na cancanci zuwa nanba wannan mai suffar ƴan damben ne, dan haka nima yanzu na kawo ƙararsa”.
      Kafin d.p.o yace wani abu ta fisge hannunta daga na ƴar sandar ta fice a office ɗin da ɗan sauri duk da tana ɗingishi. Saurin bin bayanta d.p.o da ƴan sandan da ke office ɗin sukai, yayinda Yoohan ya lumshe idanu da saka glasess ɗinsa da ganinta ya hanashi sakawa ɗazun shima yabi bayansu.
     Isowar su d.p.o yayi dai-dai da furucin Nu'aymah dake tsaye gaban ƴan sandan dake wajen kanta  . “Yallaɓai na kawo ƙara”.
      A tare suka kalleta, ɗaya a cikinsu yace, “ƙarar wa? A kanmi kuma?”. Juyawa tai inda su d.p.o ke tsaye cike da al'ajabi da mamakinta, dai-dai kuwa da fitowar Dr Yoohan daga lungun da office ɗin d.p.o yake ta nunasa da faɗin, “Ƙarar wannan mai siffar ƴan damben na kawo”............✍

😂Wagga ɗiya kina da tsaurin ido aradu😚🚶🏻.
      
         
Barka da juma'a😘😍🤗.

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


*_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*

*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
   *_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
    *_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
       *_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.

*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
     *_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
   *_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

__________________________________
No. 17

.............Tsitt wajen yayi, dan kuwa kowa ya kasa koda tari dan al'ajabi wannan ƴar budurwa. Dalilai biyu suka hana kowa magana a tsakanin ƴan sandan da Guards ɗin Yoohan, sai kallon Nu'aymah da sukeyi.
        Ƴan sandan ganin d.p.o ya fito da kansa yasa duk sukai tsit domin girmamawa a garesa. Guards ɗin Yoohan ɗin kuwa sanin ransa a ɓace yake da sune ya hanasu cewa komai suma duk da zukatansu zafi suke tamkar ana haɗa wuta a cikinsu. Ji suke da Yoohan ɗin zai basu wata dama akan Nu'aymah da wlhy ko buzunta bazasu bari ba saboda walmakalufatun da zasuyi mata.
         Buɗe baki Nu'aymah tayi zata sake magana wanda batayi zato ko tsammanin ganiba taga ya shigo cikin station ɗin. Idanunsa a kanta suka fara sauka, kafin ya maida kan ƴan sandan da sauran mutanen da abinda Nu'aymah tayi ya sakasu tsayuwar sojan badakkare suga yanda wasan zai ƙare.
       Sallama ya sake maimaitawa kafin ya bisu da sannu. D.p.o da bai amsa ko ɗaya a cikiba ya maida dubansa ga Yoohan dake jira su bashi hanya ya fice, dan ko kallon inda Nu'aymah take baiyiba balle ya nuna ya fahimci danshi takeyi ɗin. Kafin yace wani abu Barrister Atiku lauyan baba malam da shima ke kallon Nu'aymah yace, “Nu'aymah lafiya kuwa?”.
       Fuska ta ɓata kamar zatai kuka, tace, “Uncle nima ƙarar wanda ya sa a kawoni nan ɗin zan shigar”. Sosai ya fiddo idanunsa waje na mamakinta, sai kuma yay saurin juyawa ya kalli ƴan sandan dake a kan kantar. “Officer idan bazaku damuba dan ALLAH inason ganin d.p.o ne, sunana Barrister Atiku Salis tofa”.
       Kallon inda D.p.o ke tsaye suna magana da Yoohan sukai, kafin ɗaya a cikinsu yace, “To Barrister zaka iya faɗar mike tafe da kai sai a faɗa masa”. Ɗan murmushi Barrister Atiku yayi irin na kamilan mutane. Sai kuma ya kalli Nu'aymah da gaba ɗaya hankalinta na akan Yoohan, dan batason ya sulale ya fice bata saniba.
       “Ba wani abu ya kawoniba, dama akan yarinyarnan ne” yay maganar yana nuna Nu'aymah ɗin.
        Ɗaya a cikinsune yace, “Indai a kantane kakeson ganin Oga to ai an sallameta ma, ganinta da kai anan tsaye wai ta kawo ƙara ne”.
      Da mamaki Barrister yake sake kallon Nu'aymah. Kafin yace wani abu d.p.o da suka gama magana da Dr Yoohan ya juyo garesu yana tambayar lafiya?. Cikin ƴan sandan wani ya sake cewa, “Oga wannan shine nake faɗa maka na gani zaune tun ɗazun a waje, harma nake sanar maka kamar ban yarda da shiba. To ashe lauya ne, yazone akan batunta”. ya ƙare maganar da nuna masa Nu'aymah da ganin Yoohan zai fita ya sakata raba hankalinta biyu. Batare da Barrister ya ankaraba tayi caraf tabar wajen tabi bayansa.
       
      Ganin zasu tsere matane ya sakata saurin zuwa tasha gaban Yoohan da guards ɗinsa ke biye da shi fuska a murtuke da haushin kuɓutar Nu'aymah daga hannunsu.
        A wani irin zafafe guards ɗin sukayo kanta kamar zasu cita ɗanya. Babu ko ɗar tattare da Nu'aymah ta zuba masu harara tana faɗin, “Dalla kukuma ku bani hanya marasa lokacin kansu, ba daku nakeyiba da oganku zanyi dan shine dai-dai da ni ba marasa aikiyi irinku ba”. Ta ƙare maganar da musu alamar su matsa a kanta da hannu tana wani tsume fuska da cije baki.
        Lokaci guda duk suka sake kumbura da haushinta, sai dai kallon da Yoohan ɗin yay musu ya hanasu kowanne irin motsi suka zuba mata ido cike da tsagwaron takaici da tsana..
         Yoohan dake ƙare mata kallo ta cikin google ɗinsa ya wani juya idanun tare da lumshesu a lokaci guda, so yake kawai yaga iya gudun ruwanta yau dai.
         Fahimtar da Nu'aymah tai bayajin hausa a karon farko tai masa magana da turanci. “Ɗan dambe ban gama da kaiba ai, dan kaima na kawo ƙararka kuma na rantse har kotu sai munje”.
           Koda wasa Dr Yoohan bai tunanin jin turanci a bakin Nu'aymah ba, turancinma mai ƙyau irin haka. Amma sai ya fiske a zahiri ya shanye mamakinsa a rai, ya koma mamakin tsaurin ido da rashin tsoron yarinyar.........
          Tsawa Solomon da yazo wuya ya sake daka mata yana nufosu a fusace da nufin yima Nu'aymah dukan mutuwa kozata dawo hankalinta, inma oga zai kashesane ya kashesa ɗin. Jikinsa har wani irin rawa yake.
      Saurin ɗaga masa hannu Yoohan ɗin yayi alamar ya dakata. Nu'aymah dake cike da haushin rashin yin maganar Yoohan ta kalli Solomon ɗin sheƙeƙe tana nunasa da yatsa, “Kai wlhy idan baka shiga hankalinka ba saika koma garinku da tsagen yarabawan farkon ƙarni, dan wlhy agaban d.p.o ɗin can zansa a maka tsatstsargiya a kumatu tunda taurin kaine da kai mtsooww”....
         Duk yanda Barrister dake a bayansu yaso daurewa da lamarin yarinyar ya kasa daurewa, da ƙyar ya iya danne dariyarsa. Shi ba komaine ya burgesa da itaba sai yanda take masifarma cikin nutsuwa, babu wani rawan kai tattare da ita da zaisa kaimata fassarar bata da tarbiyya. Tsiwarce kawai a bakinta irin ta yaran nan ƴan gata da wahalar duniyarma basusan taba sai abinda baza'a rasaba. Yana mamakin yanda ta iya tsiwa, musamman idan yay dubi da irin gidan data fito. Dan shi kansa shaidane su baba malam tsaye suke a kan ƴaƴansu fiye da tunani, sannan ada da gaisuwa kawai ke haɗashi da Nu'aymah bai taɓa kawowa a ransa tana magana mai tsayibama balle akai ga wannan tsiwar.
     Gyaran murya ya ɗanyi, hakanne ya saka Nu'aymah dake zubama Solomon harara ta ɗauke idonta ta maida ga Barrister.
     “Kin sanshi ne?”. ɗaya daga cikin ƴan sandan da suka biyo Barrister ɗin zasuyima Nu'aymah rakkiya gida kamar yanda Yoohan ya sharɗanta ya tambayeta yana nuna mata Barrister Atikun.
          Kanta ta ɗaga masa tana harar Yoohan dake shirin barin gurin, a bazata ta tsinkayi muryarsa mai amo da nutsuwa ya furta, “Silly girl” A hankali.
        Jitai kamar ya jefeta da dutse a ƙirji ko ya mata wani ƙatoton zagi, ‘ita wannan mutumin zai kira da Silly girl?’ ta yunƙura zatai magana Barrister da shima yaji abinda Yoohan ɗin ya faɗa yay saurin dakatar da ita yana danne dariyarsa. “Kinga ƙyalesa kinji, taho mutafi a maidake gida, kinga na kira Malam na sanar masa an gama komai gani zan maidake, kuma shima ya tabbatar min suna a hanyar baro katsina”. Kamar zatayi kuka ta kallesa, dan rashin barinta tai ƙarar Yoohan yafi komai tokare mata zuciya, a ranta ta raya ‘In kere na yawo zabo na yawo wataran ai za'a haɗu, indai nice wlhy kasa a ranka mun ƙulla kenan’. Da haka tabi bayan Barrister tana zubama motocin Dr Yoohan da suka bar wajen harara tamkar sunsan tanayi.
    
★★★★

         Koda suka iso anguwar Barrister bai ƙarasa gidanba, dan dama haka suka tsara da baba malam, to saima akai sa'a ƴan sandan sun shirya maida Nu'aymah gidan da kansu. Suna gama fakin Abban Abdallah da fitowarsu kenan daga massallaci sallar la'asar yayi kiciɓus dasu Nu'aymahr. Da mamaki ya ƙaraso ga ƴan sandan.
     Yayinda suma cike da girmamawa suka nufesa. Kamar ɗazun sun gaishesa da mutuntawa. Kafin cikin nutsuwa ɗaya daga cikinsu ya fara magana. “Malam ayi haƙuri dan ALLAH a mana afuwa, munzo mu gyara kuskuren da mukayi ɗazun akan tafiya da wannan yarinya. Gata mun dawo da ita, dan bata da laifin komai ashe rashin fahimtace aka samu”.
       Ajiyar zuciya Abbah su Abdallah yayi yana mai jero addu'ar godiya ga ALLAH cikin ransa, tun ɗazun da aka tafi da Nu'aymah hankalin kowa ba'a kwance yakeba a gidan, sun kira baba malam yafi sau ashirin dan su bashi haƙuri ya janye sharaɗin daya gindaya musu subi Nu'aymah amma yamaƙi ɗaga wayar. Gudun kar abin ya zafafa kuma sun kasa gayama Hajjo da tunda ta farka a barcinta wajen sha biyu take faman saka yara su kira mata Nu'aymah tai mata kitso, dan itace ke mata duk sati. Idan kuma tanajin ƴan rashin arziƙi tace bazata mataba sai ta biya. Bawai kuɗi take nufin ta bataba, furar hajjon ta ƙa'ida mai daɗin tsiya da kowa ke ƙulafuci a gidan takeso ta bata mai yawa. Dan kullum Hajjo saita zaɓi wanda ta gadama a gidan take bama furar🤣.
      Sai dai duk wanda ya fita bayan wasu mintuna sai ya koma ya sanarma hajjon Nu'aymah barci take. tun bata damu ba harta fara faɗan wane irin barcine haka Nu'aymahn keyi kamar wacce bata da mafaɗi a gidan. Daga ƙarshe ta mike da nufin zuwa ta tasota da kanta bayan sallar azhar sai ga Abba Musbahu ALLAH ya kawo gidan. Shine yay mata dabarar hanata yace bara ya aika a duba kidai Nu'aymah bata jin daɗine kokuma batama gidan.
     Da wannan dabarar ya wagarar da ita da hirar mahaifinsu har akai sallar la'asar, ALLAH ya taimakesu sun fito kenan da nufin shirya yanda zasubi bayan Nu'aymah koda baba malam ɗin zaiyi fushi kuma sai gata ta dawoma.
       Godiya yayma ƴan sandan, ya kama hannun Nu'aymah da haushin Yoohan bai bartaba har yanzu suka shige Abba Musbahu biye da su. Su Muhammad da suka fito zasu islamiyya ne suka fara cin karo dasu, aiko cike da ihun murna suka shiga faɗin Aymah ta dawo! Aymah ta dawo!.
         Hayaniyarsu ce ta fiddo ƴan gidan har Hajjo da taji abun banbaraƙau. Umm ce kawai bata fitoba dukda kuwa tanajinsu daga sashenta, ranta kuma cike yake da zumuɗin son ganin halin da ƴarta take ciki. Amma saita danne ta cigaba da azkar ɗinta na yamma.
       Rungumeta iyayen mata sukaitayi, musamman ma Addah da harda ƴan ƙwallarta tana dudduba jikin Nu'aymahr. Ganin ras babu ko ƙwarzane sai yunwa da takeji da kuma fushin fuskarta saita sake rungumeta tana godema UBANGIJI daya dawo musu da ita lafiya.
       Cike da mamaki Hajjo tace, “Wai mi ake ɓoyemin ne halan? Zainabun gidan ubanwa taje da har ake wannan gayar tarbar tata?”. Shiru wajen yayi kowa ya kasa bata amsa. A take takaici ya kumeta ta kwanto bakin zaninta ta fara matsar ƙwalla da juyawa zata bar wajan. Cikin sauri Abbansu Abdallah ya riƙeta yana faɗin, “Yi haƙuri Innah, bafa wani abu baneba, dama wata ƴar matsalace ta faru, to ashema Nu'aymahn bata da laifin komai an samu rashin fahimtane kawai”.
       “Gidanku Lurwanu. nace kaci gidanku! Yanzu nan ni zaku maida shashasha, tun ɗazun nake cigiyar Zainabu a gidannan amma anamin yawo da hankali, ni dama naji a jikina badai lafiyaba, yarinyar da bata iya awa biyu bata shigo sashenaba indai tana a gidanan ace wuni zur banga giccintaba kuma lafiya sumul”.
       “To kiyi haƙuri inna anyi kuskure, amma za'a gyara insha ALLAH”.
      “Ya zanyi na haƙura, amma a faɗamin yanda akai to”.
    Babu musu sukai mata bayanin komai a gaban kowa, suka kuma ɗora da bayanin ƴan sandan da suka dawo da Nu'aymah ɗin. Ajiyar zuciya kowa ya shiga saukewa a wajen da nuna jin daɗin Nu'aymah ba wani laifi tayiba. Daga haka kowa ya kama sabgar gabansa, Addah kuma ta kama hannun Nu'aymah dake yatsine fuska saboda mararta da kamar jira take ta dawo ta fara tsunkula mata.
    Umm na zaune tana azkar suka shigo, dukda taji sanyin ganin Nu'aymah lafiya lau saita ɗaure fuska ta ɗauke kanta. Addah batabi takantaba ta shige da Nu'aymah toilet, ruwa mai zafi ta haɗa mata tace tai wanka ta gasa jikinta sosai. Nu'aymah dake murmushi cike dajin ƙaunar Addah ta gyaɗa mata kai.

       Zama Addah tayi a bakin gado tana kallon Umm data ɗauke kai, ƙaramar dariya tai ta tsokana da son ganin Umm ɗin ta manta da komai itama tace, “Wlhy ki gama ɗaure-ɗauren fuskarki nasan ranki fes, ni wlhy yanda kike wani ture Nu'aymah har mamaki kike bani”.
      Hararta Umm tai ta sake ɗauke kanta. Addah ta kwashe da dariya a karo na biyu tana faɗin, “Oho dai, duk abinda da dai zakiyi munsan mune zuciyar taki”.
      Ƙin tankawa Umm tayi, dukda kuwa abinda Addah ta faɗa ɗin shine gaskiya. Tana kawaicine kawai akan nu'aymah dan kar aga rashin kunyarta akan ƴar fari, ƴar farinma wadda ta ɗauki tsahon shekaru bata samu ba. Amma kam Nu'aymah itace cikar dukkanin farin cikinta, itace kuma dukkanin hauhawar damuwarta. Shiyyasa take jigatuwa a gidan, dan inma lagontane maƙiya sun gane akan Nu'aymah shiyyasa suke jigata rayuwar yarinyar ta hanyar SARAN ƁOYE.

____________________________
             *_SAUDIA_*

     Ta jima tana kai kawon jiran fitowar tasa amma bai fitoba. Daga ƙarshe sai ta fahimci da alama yau bama zai fita yabar gidanba kenan. Zama tai shiru tana ƙullawa da kwancewa a cikin ranta. Ta kusan sake shafe mintuna talatin tana wannan nazari da ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwarta da ƙuruciya ke ɗawainiya da ita. Daga ƙarshe ta miƙe bisa yarda da shawarar da zuciyarta ta ɗorata akai.
      Ɗakin nasa ta nufa tai knocking, ta kusa tsayuwar mintuna biyar baiyi ko tariba daga ciki, sai da ya gama shan ƙamshinsa sannan ya bata iznin shigowa. Mamaki yay bala'in kama Adawiya ganinsa kwance a saman gado yana danne-danne a laptop, tsabar wulaƙanci ashema yana jinta ba kamar yanda tai tunanin ko wanka yakeba.
      Amma sai ta danne zafin da taji bisa koyarwar Maman Aaida, da kuma son da take masa da akoda yaushe yake hanata ganin laifinsa. Gefen gadon ta zauna murya a sanyaye tace, “Sannu da aiki Yah Ab, nifa na zata koma bakajin daɗine naga yau baka fitaba”.
      Sai da yaja wasu sakkani kafin yace mata “Sannunki kema” a taƙaice. Duk da hakan bai mataba saita daure bata karayaba, ta sake cewa “Yah Ab wlhy kewar Aymah nakeji dasu Amal, dan ALLAH ka bani aron wayarka na kirasu muɗan gaisa”.
    Sunan Nu'aymah data sanyane ya sakashi ɗaga ido ya kalleta a karan farko, saita narke fuska harda tara ƙwalla a cikin idonta. Karan farko da tun zuwansu ta bashi tausayi, dan shiɗin shaidane bisa shaƙuwarta da Nu'aymah. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana girgiza mata kai. “Ni bazaki kira kowa da wayataba”.
    Hawayen da take maƙalewa suka silalo mata saman kumatu, ta haye gadon sosai kusa da shi, “Yah Ab dan ALLAH ka taimakeni, wlhy ina kewarsu musamman Nu'aymah. Ni tunda nake ban taɓa sati bama tare ba wlhy. Amma yanzu gashi har ana neman ƙulla shekara, wata takwasfa kenan ana shirin shiga na tara. Yah Ab miyasa wai kuke son rabani da itane? Kumata uziri akan laifin ta dan ALLAH, nasan tayi kuskure amma ajizancine. Yah Ab dan ALLAH kabar fushi da ita haka nan ka yafe mata”.
     Kallon Adawiya yayi cikin ido, kafin ya ɗauke yana jan ƙaramin tsaki. “Ni na taɓa gaya miki fushi nake da Nu'aymah?”.
      Saurin haɗiye yawu tayi jin zata saki layi, tace, “A'a baka taɓa faɗaba, to amma yanda ko maganarta bakayi, baka kiranta ai dole zan fassara haka. Yah Ab inhar zaka yafema Nu'aymah namaka alƙawarin saina sake farauto maka soyayyarka a ranta. Ko wanene shegen Ameer ɗin nan saita barsa da izinin ALLAH. Kaga tunda Yusrah bata tare ba ita saika lallaɓa su baba malam a warware aurenku a ɗaura maka da Nu'aymah. ALLAH koni da muka tare zan iya haƙura na barmata tunda dama akwai wanda nakeso”.
      Duk da bai ɗago ya kalletaba maganganunta da alama sun fara tasiri a ransa. dan kuwa cak ya tsaya daga latsa lap-top ɗin yana saurarenta kawai. Kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa ya kalleta. “Miya hanaki zuwa makaranta yau?”. ya jeho mata tambayar bisa ƙoƙarin kauda wancan zancen na farko.
    Baki ta tunzura masa gaba tana matso hawaye, “Banajin daɗi, kuma kewar su Nu'aymah na damuna. Ni wlhy idanma ba tare da itaba karatunma jakanta zantayi harsai an maidani gida ko an kawota nan munyi tare”.
        Karan farko a tarihin zamansu ya sakar mata murmushin da rabon data gansa tunkam a maida auransa kanta. Ya kai hannu ya lakace mata hanci yana faɗin, “A kawota nan ku hautsinamin kai da rashinjin ku”. Wani daɗine ya lulluɓe Adawiya, ta ƙyalƙyale da dariya tana gyara zama da fadin. “Wlhy Yah Ab harma ka tunamin wani abu, akwai wata tsiya da muke tafkama Hajjo ni da Aymah har yanzu bata taɓa saniba”.
     Tashi yay zaune sosai ya zuba mata idanu alamar bata duka hankalinsa yana saurare. Aiko hakan ya kuma tsundumata a kogin farin ciki ta shiga bashi labarin rashinjin da sukema Hajjo dama na makaranta. Tun yana iya murmushi kawai harya ware yanata kwasar dariya. Dan rabin iya shegen nasu duk Nu'aymah ce oganniyar yinsa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ware yana magana da bata labarin Shima abinda Nu'aymah kan masa wataran. Ya shiga buɗo mata videos kala-kala nata ita da Nu'aymah suna rashin ji batare da tasan wanene yake ɗauka yana tura masaba.

Hummm ashe kan Adawiya na ja🤔🤥🚶🏻.

_________________________________

            Tunda suka bar police station ɗin waya yake da Rich.. Ya sanar masa cewar ya gama masa booking jirgin tafiya Kenya, hakama wanda zai biyo daga nan kano ya dawo Lagos ɗin.
       Magana yayma driver da ke shirin ɗaukar hanyar Abuja akan suje airport. Duk da sunji wayar da yakeyi shi da Solomon da har yanzu haushin Nu'aymah bai barsaba shima, sai dai hakan bai musu daɗi ba. Dan sunso ace Abujar za'a koma ko hakan ya taimakesu wajen Madam Chioma da Papa da sukasan sunacan suna jiran isowarsu da Nu'aymah.
         Suna isa Airport ɗin ya sallamesu akan su tafi kada suyi dare a hanya, su kuma shi da Solomon zasuyi zaman rabin awa na jiran jirgi.

     Jiki a sanyaye sukai musu sallana da addu'ar a dawo lafiya suka fito daga airport ɗin. Yoohan da duk yake a galabaice da gajiya da yunwa ya ƙoƙarin kiran papa suyi magana dan baya buƙatar kuma wani abu makamancin hakan ya sake tasowa. Sannan ya lura da tsoron dake a fuskokin Guards ɗin nasa harma Solomon dake a tare da shi. Irin kuma wannan tsoron suka baro d.p.o da shi shima.
     Duk da yanda papan ke masa wayar cike da ɗoki ga Yoohan ba haka bane. Sama-sama yake bashi amsar duk tambayar da yay masa wadda gaba ɗayanta akan lafiyarsace.
     Sai da ya bari papan ya kammala kafin yay masa magana ta nutsuwa akan case ɗin Nu'aymah, ya kuma nuna fushinsa sosai akan matakin da papan yaso ɗauka akan ƙaramar yarinyar da ko hankali bata gama mallaka ba.
         Daga can sai papan ya danne nasan haushin ɓata masa shiri da Yoohan ɗin yayi akan Nu'aymah ya koma lallashinsa dan baya ƙaunar fushin ɗan nasa kamar yanda Madam Chioma ta tsana itama. Ya jima yana lallashinsa dan har lokacin da jirginsu ya gama shirin ɗaukar masu tafiya sannan sukai sallama. Wayarce ma ta ɗauke hankalin Dr Yoohan daga uwar yunwar dake cin hanjinsa da gajiya..............✍



Ku ƙara haƙuri dani fa dai dan ALLAH 🙏🏻.


_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
  
                
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun

1 Comments On SARAN BOYE
avatar
maryam-8-1

1 year ago

Reply

Amazing book

Please Login or Register in order to submit comment