Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in ya ki yi.
     Sallah bata yiwuwa sai da alwala.

  ALWALA:
Ubangiji Madaukakin Sarki yana cewa:
"يأيها الذين ءامنوا إذا قمتم إلى الصلوة فاغسلوا وجوهكم وأيديكم إلى المرافق وامسحوا برءوسكم وأرجلكم إلى الكعبين وإن كنتم جنبا فاطهروا وإن كنتم مرضى أو على سفر أو جاء أحد منكم من الغائط أو لامستم النساء فلم تجدوا ماء فتيمموا صعيدا طيبا فامسحوا بوجوهكم وأيديكم منه ما يريد الله ليجعل عليكم من خرج ولكن يريد ليطهركم وليتم نعمته عليكم لعلكم تشكرون" المائدة: 6.
"Ya ayyuhal lazina aamanuu izaa kumtum ilas salati fagsilu wujuuhakum wa’aydiyakum ilal maraafiki wamsahuu biru’uusakum wa’arjulakum ilal ka’abayni wa’in kuntum junuban faddahharuu wa’in kuntum marda au alaa safarin au ja’a ahadun minkum minal ga’idi au laa mastumun nisa’a falam tajidu ma'ana fatayammamu sa’idan dayyiban famsahuu biwujuuhikum wa’aydiykum minhu maa yuridul Laahu liyaj’ala alaykum min harajin walakin yuridu liyudahhirakum waliyutimma ni’imatahu alaykum la’allakum tashkuruun”. Alma’ida: 6.
         “Yanzu zamuje kaga yanda ake alwala kafin salla”. Baba malam ya faɗa yana miƙewa. Gaba ɗaya suka biyosa ƙofar toilet ɗin dake cikin falon. Yayinda Yoohan da baba malam suka kasance daga ciki.
       *YADDA AKE YIN ALWALA SHINE:*
      1-Da farko yin niyya a zuci sannan ka ce: “Bismillahi” sannan ka wanke tafukanka na dama da na hagu kowanne sau uku(3).
     2-Sannan ka debo ruwa ka kurkure bakinka ka zubar da ruwan sau uku(3).
     3-Sannan ka debo ruwa ka shaka a hanci ka fatar shi ma sau uku(3).
      4-Sannan ka debo ruwa ka wanke fuskarka gaba dayanta sau uku(3), a lura cewa wanke fuska yana farawa ne tun daga farkon goshinka har izuwa karkashin haba wato kusa da makoshi a tsayinta kenan, a fadi kuma tun daga gefen kunnen dama zuwa gefen kunnen hagu.
     5-Sannan a wanke hannu tun daga tafuka har zuwa gwiwar hannu na dama da na hagu shima uku(3).
      6-Sannan a ɗebo ruwa a yi shafar kai wato a tafin hannu a shafo tun daga farkon goshi har a kai ƙeya sannan a sake dawowa farkon goshi.
       7-Sannan shafar fatar kunnuwa na dama da na hagu.
     8-Sannan a wanke kafafu na dama da na hagu tun daga tafin kafa har izuwa gwiwar kafa.

          *ADDU’A BAYAN KARE ALWALA:*
"أشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له وأشهد أن محمدا عبده ورسوله" رواه مسلم.
"سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك" رواه الطبراني.
“Ashhadu an Laa ilaha illal Lahu wahdahu laa sharika lahu wa’ashhadu anna Muhammadan abduhu warasuluhu”. Muslim ne ya rawaito.
        Ko kuma ka ce;
“Subhanakal Lahumma wabihamdika Ashhadu an Laa ilaha illa anta astagfiruka wa’atubu ilaika”. Dabarani ne ya rawaito.

       “Wannan itace alwala Yahya. Da ita ake gabatar da bautar ALLAH, idan babu ita babu salla. Akwai abubuwan da suke warwareta, amma zamu ajiyesu zuwa nan gaba a neman ilimi zaka sansu. A yanzu muna tsinkayar jiran shigar lokacin azhar ne, dan a ƙa'ida ko wanne wuni musulmai na gabatar da salla sau biyar ne. Akwai nafiloli da mutum kan ƙara dasu domin samun kusanci ga UBANGIJI. Amma da waɗan nan biyar dazan lissafa maka sune wajubabbu. Wanda ya barsu ko yayi sakaci dasu, haƙiƙa bai cika cikakken musulmi ba.
       *SALLOLI  WAJIBABBU:*
Ya zo a hadisin Dalhatu bin Ubaydullah cewa:
"أن أعرابيا قال: يا رسول الله ماذا فرض الله عليَّ من الصلاة؟ قال: «خمس صلوات في اليوم والليلة.. الحديث…
Ma'ana: "Cewa wani Balarabe ya ce: Ya Ma'aikin ALLAH me UBANGIJI (SWT) ya wajabta a garemu na daga sallah? Sai ANNABI (SAW) ya ce: Salloli biyar a cikin (kowane) wuni da dare".
       Salloli wajibabbu guda biyar sune: 1-Asubah, 2-Azzahar,  3-La'asar,  4-Magriba,  5-Isha'i.
  
       *LOKATAN  SALLAH  DA ADADINSU:*

ASUBAH: Sallah ce da ake yin ta raka'a biyu, Lokacin yin ta kuma shine bayan bullowar alfijir na gaskiya. Sannan ana yin karatunta a bayyane, Fatiha da sura a kowacce raka'a sannan a yi tahiya ayi sallama.

AZZAHAR: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacin yin ta yana farawa idan rana ta bar tsakiyar sama ta karkata zuwa mafadarta. Sannan ana yin karatunta a asirce, Fatiha da sura a raka'o'in biyun farko, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka'o'in biyun karshe, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.
Amma a ranar Juma'a sallar Azzahar tana zamowa sallar Juma'a a inda take komawa raka'a biyu kuma ana yin karatunta a bayyane, bayan liman ya kare khuduba.

LA'ASAR: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacinta na farawa daga inda inuwar abu tayi daidai da tsayinsa. Sannan ana yin karatunta a asirce, Fatiha da sura a raka'o'in biyun farko, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka'o'in biyun karshe, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.

MAGRIBA: Sallah ce da ake yin ta raka'a uku, lokacin yin ta shine idan rana ta fadi a mafadarta (a nan Najeriya fuskar yamma). Sannan ana yin karatun raka'o'i biyun farko a Fatiha da sura amma a bayyane, sai a zauna a yi tahiya sannan a mike a yi raka'a daya ta karshe a karanta Fatiha kawai a asirce, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.

ISHA'I: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacinta yana farawa ne idan shafaki ya buya (wato dan jaja-jajan nan na bayan faduwar rana idan gari ya fara duhu). Sannan ana yin karatunta raka'o'in biyun farko Fatiha da sura a bayyane, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka'o'in biyun karshe a asirce, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.

*KIRAN SALLAH:*

الله أكبر الله أكبر
أشهد أن لاإله إلا الله
أشهد أن لاإله إلا الله
أشهد أن محمد رسول الله
أشهد أن محمد رسول الله
حى على الصلاة
حى على الصلاة
حى على الفلاح
حى على الفلاح
الله أكبر  الله أكبر
لا إله إلا الله
Allahu Akbar,
Allahu Akbar,
Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah,
Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah,
Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah,
Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah,
Hayya alas-Salat,
Hayya alas-Salat,
Hayya alal-falah,
Hayya alal-falah,
Allahu Akbar
Allahu Akbar
La’ilah aillall-lah.
Wannan shi ne lafazin kiran sallah. An so ga wanda ya ji kiran ana kiran sallah ya maimaita abin da mai kiran sallar yake fada shi ma, sai a wajen fadin "HAYYA ALAL SALAT" da kuma fadin "HAYYA ALAL FALAH" a madadin ka maimaita su idan mai kiran sallah ya fade su, sai ka ce "LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH".

*YADDA AKE YIN SALLAH:*
- Da farko sai ka fiskanci alkibla (Saitin inda Ka’aba take, anan arewacin Najeriya ana cewa Gabas domin nan ne saitin inda Ka’aba take daga nan) sai a yi ikama, ga yadda lafazinta yake:
        Allahu Akbar, Allahu Akbar, Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah, Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah. Hayya alas-Salati. Hayya alal-falahi. Kad-kamatis-salatu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilah aillall-lahu.
       Sai ka daga hannuwanka daidai kafadunka ko daidai kunnuwanka sai ka yi Kabbara wato ka ce: “Allahu Akbar”.
       -Sai ka dora hannunka na dama akan hannunka na hagu a kirjinka (kabalu), ko kuma ka sake su (sadalu), duk wanda ka yi daidai ne.
      -Sai ka karanta karatun bude sallah a asirce ake yinta ita ce:
“Subhankal Lahumma wabihamdika watabaraka ismuka wata’ala jadduka wala’ilaha gairuka”
        ko kuma ka ce: “Allahumma ba’id baini wabaina hadayaya kama ba’adta bainal mashriki wal magribi, Allahumma nakkini min hadayaya kama yunakkal saubul abyadi minad danasi, Allahumma agsilni bil ma’i wassalji wal baradi”.
        -Sannan a karanta Fatiha zuwa karshenta.
      -Sannan a karanta abinda ya sauwaka na daga Alkur’ani sura ko wani sashi na sura daga Alkur’ni.
       -Sai ayi kabbara “Allahu Akbar” ayi ruku’u, a cikin ruku’u ana iya karanta: “Subhana Rabbiyal Azim Wabihamdihi” ko a karanta “Subbuhun Kuddusun Rabbul Mala’ikati Warruhu” gwargwadon abinda ya sauwaka.
      -Sai a dago daga ruku’u ana fadar "Sami'al Lahu Liman Hamidahu" idan an dago an tsaya kafin a tafi sujjada sai a ce: “Allahumma Rabbana walakal hamdu” ko ka ce “Rabbana walakal hamdu”
        -Sai kuma ayi kabbara “Allahu Akbar” a yi sujjada ana fadin “Subhana Rabbiyal A’ala wabihamdihi” a cikin sujjada gwargwadon abin da ya sauwaka a (a lura cewa sujjada ana yinta akan gabobi guda bakwai, goshi tare da hanci, tafuka biyu, guiwoyi biyu da kuma kafafu biyu).
       -Sai ayi kabbara “Allahu Akbar” a dago daga sujjada a zauna akan kafar hagu ko duwawun hagu, a dora tafuka akan cinyoyi ana fadin “Rabbigfirli” ko kuma “Allahumma Igfirli”.
     -Sannan ayi kabbara “Allahu Akbar” a koma sujjada ta biyu ana fadin “Subhana Rabbiyal A’ala wabihamdihi” a cikin sujjadar gwargwadon abin da ya sauwaka.
-Sannan a yi kabbara “Allahu Akbar” a dago daga sujjada ta biyu, yayin mikewa zuwa raka’a ta biyu (idan an zauna dan kadan kafin mikewa raka’a ta biyu ba laifi, ana kiran wannan dan zama kadan “jalsatul istirahati”).
   Sai a sake kawo raka’a kamar yadda aka yi wannan ta farko, amma idan an dago daga sujjada ta biyu a raka’a ta biyu sai a zauna kamar irin zaman da aka yi na dagowa daga sujjada ta farko a dora hannaye akan cinyoyi, sannan hannun dama ayi nuni da dan yatsa manuniya a yi karatun tahiya a wannan zama, karatun tahiya shine:
       “Attahiyatu Lillah, Azzakiyatu Lillah, Addayyibatus Salawatu Lillah, Assalamu alaika ayyuhan Nabiyu Warahmatullahi Wabarakatuhu, Assalamu Alaina wa’ala ibadil Lahis Salihina, Ash’hadu an La’ilaha illal Lahu Wa’ash’hadu anna Muhammadan Abduhu warasuluhu”.
      Haka ya zo a (Muwadda Malik, lafazin Umar bn Khaddab).
  Idan sallar mai raka’a biyu ce, kamar sallar Asubah sai ka cikasa karatun tahiyar anan da salati Ibrahimi. Shi ne kamar haka:
      “Allahumma salli ala Muhammadu wa’ala aali Muhammad kama sallayta ala Ibrahim wa’ala aali Ibrahim innaka Hamidun Majid, Wabarik ala Muhammad wa’ala aali Muhammad kama barakta ala Ibrahim waala aali Ibrahim Innaka Hamidun Majid”.
       Sai kayi sallama, ka ce “Assalamu Alaikum Warahmatullah”. Ko kuma ka yi sallamar bangaren damanka da kuma hagunka.
       Idan kuma sallar mai raka’a uku ce kamar Magariba ko raka’a hudu kamar Azahar da La’asar da Isha’i, idan kayi kashi na farko na karatun tahiya sai ka tashi ka cikasa ragowar raka’ar da ta rage ko daya ko biyun (a lura cewa a ragowar raka’ar da ta rage bayan biyun farko Fatiha kadai za’a karanta ban da sura ko wani sashi na sura) sai ka sake zama na tahiya a karo na biyu ka cikasa tahiyar har zuwa sashi na biyu na salati Ibrahimi sannan ka yi sallama ka ce “Assalamu Alaikum Warahmatullah” Ko kuma ka yi sallamar bangaren damanka da kuma hagunka.

        *BAYANIN SHARADAN SALLAH
Sharadan sallah sune:-*
1.Musulunci. (ba ta inganta ga wanda ba Musulmi ba).
       2.Hankali (ba ta inganta ga mara hankali).
     3.Tsarkin dauda: Shine tsarkake jiki da tufa da bugire na mai sallah tun daga farawa har kammalawa.
    4.Tsarkin Hadasi: Shine duk abin da ke warware alwala, shima tun daga fara sallah har zuwa kammalawa. Ana bukatar wadannan tsarki a cikin kowace irin sallah ma’abociyar raku’i da kuma sujjada kai har ma wanin nan nata.
        5.Shigar lokacin sallah.
6.Niyya.
     7.Sitirce al’aurar namiji tana kamawa ne daga cibiya har zuwa gwiwa. Ita kuwa mace baki dayan jikinta al’aurane ga ajnabinta sai dai fuskarta da tafukan hannuwanta.
     8.Fuskartar Alkibla; Sai dai in a halin rincabewar yaki ko nafila a tafiyar da ya halatta ayi kasaru kuma mutum ya zamo mahayi ne kan abin hawa.
     Wanda ya yi sallah yana kallon watan alkibla ba yana mai mantawa ko rashin sani har sai da ya yi sallama, to ya saketa har abada, sai dai malamai sun yi sabani a cikin wannan hukunci, haka hukuncin ya ke idan ya zamo bai yi sani da alkiblar ba ko ya ganganta yin sallar ba a alkiblar ba.

       “Yahya musulinci yana da ƙa'idoji da tsare-tsare ga komai na rayuwa musamman ma ibada. Wannan kaɗanne daga ciki nake tsakuro maka a yanzu, kafin kayi ninƙaya cikin taskar ilimi ka fahimci manufata. Inaga yanzu mataki na gaba da zamuje domin gabatowar Azhar shine karantar fatiha daga littafin ALLAH, wato Al-qur'ani. Sauran abinda zai biyo baya zamu bisa daki-daki mu tsara yanda zaka samu karantarsu. Dan zamu sake komawa baya muyi cikakken bayani akan tsarki a muhimmancin sa. Ina fatan kana fahimtar duk abinda mukeyi”.
         Cikin raunin murya da sanyin gaɓoɓi Yoohan ya amsa da, “Ina fahimtar komai Uncle, ina kuma cikin ɗunbin farin ciki da kasancewata cikin wannan addini dake cike da tarin hikimomi da ƙa'idoji ababen birgewa da ƙayatarwa. Tabbas tun a yinin farko na fara cin karo da ni'imomin musulinci, ina fata da addu'ar cigaba da karo dasu har ƙarhen numfashina. A yau ina jina tamkar wani sabon hallita, tamkar ba Yoohan Goshpower ba, lallai babu abinda ya kai addinin musulinci nutsuwa da kwanciyar hankali. Ya ALLAH na gode maka da wannan ni'ima taka, ina roƙon ka cigaba da tabbatar da ita a gareni batare data yanke ba koda a sakan guda ne na rayuwata”.
      Cike da farin ciki su Baba malam suka amsa masa. Handkherchief Yoohan yasa ya ɗauke hawayen da suka ciko masa idanu. Kafin ya durƙusa har ƙasa yana godiya gasu baba malam da suka zamewa rayuwarsu sandar jagora wajen jawosa daga DUHU zuwa HASKE.
      Saurin ɗagosa baba malam yay ya runmesa. “Yahya bamu bane ALLAH ne, mu kawai mun kasance ne daga cikin ƙaddararka ta alkairi, ALLAH yayi maka albarka, ya share hawayenka, ya yaye maka damuwarka, ya karɓi tubanka, ya shafe zunubanka damu baki ɗaya”.
      A tare suka sake amsawa da amin.

__________★★★★__________

                A hotel kam hankalin su Solomon a matuƙar tashe yake da rashin ganin Yoohan. Gaba ɗaya sun tada hankalin ma'aikatan hotel ɗin da barazanarsu. Saboda maigadi ya tabbatar shi baiga fitar Yoohan ba. Hakama wanda yake a reception yace baiga fitarsa ba. Ga kuma motocinsu duk suna ajiye alamar Yoohan bai fitaba a fahimtarsu.
        Ganin ƙaramar magana na neman zama babba Solomon ya kira papa ya sanar masa halin da ake ciki. Cikin matsanancin tashin hankali papa yace su kira layin Yoohan ɗin mana.
         “Sir! Duk wayoyinsa na nan cikin ɗakin, shiyyasama muka fahimci bada kansa ya fitaba kenan”. Solomon da jikinsa har tsuma yake ya bama papa amsa murya na rawa. Wata wawiyar tsawa papa ya sake daka masa daga can, tare da sakin wani irin ihu tamkar zai fasa gidan.
       “Solo!!!!!! Inhar yarona ya shiga wani hali na rantse muku da ALLAH duk sai na kasheku da hannuna, na baku awa biyar kacal akan nemansa. Idan har kuka bari na iso kano kuyi kuka da kanku!!....”
    Ƙit ya yanke wayar batare da ya bari Solo yay ko ƙwaƙwaran numfashi ba.

        Sosai hankalin Solomon ya sake ƙololuwar tashi, hakama na sauran ƴan uwansa. Dan sunsan wanene Pastor Goshpower, sun san kuma abinda zai iyayi, musamman ma akan Yoohan da duk duniya bai haɗa sonshi dana kowa ba.
       Suna cikin tashin hankali da tararrabin mafita sai ga ƴan sanda kusan mota uku sun iso hotel ɗin bisa jagorancin D.p.o Emanuel.
     Su masu hotel babban tashin hankalinsu kar sunansu ya ɓaci. suko su Solomon sune sukasan babban tashin hankalin da zai iya samunsu da su kansu masu hotel ɗin indai har ta tabbata anyi kidnapping ɗin Yoohan a hotel ɗin ne, kamar yanda kowa yake tunani da hasashe.............✍

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.



No. 30

................Lokacinda su Solomon ke acan cikin tashin hankalin tsoron cikar lokacin da papa ya basu akan sanin inda Yoohan yake, shi yana nan suna shirin tafiya massallacin juma'a shi da su baba malam.
      Kowa ya kalli baba malam ɗin a yau zai fahimci yana cike da tsantsar farin ciki. A cikin nishaɗin daya shiga da shi cikin gidan nasa ya sake fitowa shi da Umm data taimaka masa yay shirin massallaci.
    Ƴar tsokanar da ya kema Umm yasa Nu'aymah dake zaune a falon tana gyaran fruit ɗin da Umm ta sakata ɗagowa tana kallonsu. Cikin washe baki tace, “Abbah yau dai kana cikin farin ciki ALLAH, naga tun safe fuskarka sai annuri takeyi”.
      Da ga Umm har baba malam dariya sukayi, ya matsa kusa da ita tare da kai hannu ya shafa kanta. “Tabbas yau ina cikin farin ciki mamana, saboda wannan farin cikin yau har ƙyauta ta musamman na shirya miki ke da Muhammad, dan haka kafin na dawo ki shirya faɗa mini abinda kike so”.
         Sosai farin ciki ya sake kamata. Ta shiga jera masa godiya da addu'ar fatan dawowa lafiya. Daga shi har Umm amsa mata suke cike da kulawa. Kowannensu najinta a ransa sosai, dan daga Umm har Baba malam ba ƙaramin so sukema Nu'aymah ba. Suna dannewane kawai saboda ƙarfafama kansu tarbiyarta. Ga ɗunbin tausayinta dake mamaye da ruhinsu game da matsalarta. Dan har yau da muke ɗin nan baba malam bai gajiya ba wajen cigaba da neman likitan nan, yana kuma gayama UBANGIJI da neman taimakonsa a kowane daƙiƙa.

     Bayan Umm tama baba malam rakkiya ta dawo. A inda tabar Nu'aymah nan ta sake isketa tana ƙalular gyara fruit ɗin.
      “Nikam naga takaina da wannan hali naki Nu'aymah! Mutum yayta abu sanyi-sanyi tamkar bazai ƙaresa ba. Yanzu maimakon ki zauna kiyi aikin nan a kitchen shine kika taho nan kuma dan salon neman ɓata guri?”.
       Baki ta tura gaba tana ɓata fuska, “Yoni Umm idanfa na zauna a kitchen wlhy Rabi damuna zatayi da surutun ta, kin sani dai ko redio haka ta ganta ta ƙyale akan zanc........”
      Bammm!. Umm ta make mata baki, hakanne ya hanata ƙarasa faɗa. Da sauri ta saki wuƙar hannun nata hawaye na taruwa mata a ido. Umm dake hararta tace, “Saunawa zan faɗa miki karna sake jin wannan maganar banzan a bakinki Nu'aymah? Rabi bata girmeki ba? K wai yaushe ne zaki bar tsiwa da rashin kunya? Itaɗin sa'arki ce?”.
       “Kiyi haƙuri Umm bazan sakeba ALLAH ”.
      “Kima sake mana, mara wayau kawai”. Umm ta faɗa tana hararta da barin wajen. Harta kusa ƙofar sashen baba malam ta juyo. “Kiyi ki tashi a wajen nan kuma kafin na fito, ga man-shanu can a kitchen ki ɗauka ki kaima Addah, kuma idan kinje ki zauna shiririta karki dawo ki ƙarasa aikin dana sakaki kinji ko”.
        Sake ɓata fuska Nu'aymah tayi hawaye na zirara mata. Sai dai batace komaiba har Umm ta shige ciki. Dan zuciyar gadon tazo mata wuya.
     
       Duk yanda Umm tace tayi haka tayi, sai dai data shiga kitchen Rabi tasha harara, dan a ganinta saboda itane Umm ta Mammangare ta. oho ita batama san tanaiba, dan aikinta takeyi koda ta shigo bama ta kalli inda Nu'aymahn takeba tunda tasan basa doguwar magana lafiya sai sunyi faɗa.
       Manshanun ta ɗauka zuwa sashen Addah. Sai da tai sallama kusan sau uku kafin a amsa mata ciki-ciki. Bata damuba ta shige tana ɗaure fuska dan har yanzu akwai haushin faɗan Umm tare da ita. Kubrah kawai ta iske zaune a falon, tunkan ta ƙaraso ciki take jefo mata harara.
       Jitai kamar ta juya dan haushi, amma sai ta daure ta ƙarasa da faɗin, “Aunty Kubrah Umm ce ta aikoni wajen Addah?”.
     Banza tai mata tamkar bata jitaba, har Nu'aymah ta fara yanke shawarar juyawa sai ga Hajarah ta fito daga ɗakinsu hannunta ɗauke da Al-qur'ani.
       “A'a Aymah ce a wajen namu?”.
Ajiyar zuciya Nu'aymah tayi da maida kallonta gareta. Fuskarta da ɗan damuwa tace, “Aunty Hajarah Umm ce ta aikoni wajen Addah. Amma ina tambayar Aunty Kubrah tamin banz.....”
           Kafin ta ƙarasa taji saukar duka a bakinta, Kubrah da tai dukan ta nunata da yatsa cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “K dan uwarki ni sa'arki ce ko?”.
       “Kai haba Aunty Kubrah daga tambaya, yanzu dan ALLAH mita miki zaki dakar mata baki? Minene abin laifi anan to?”. Hajarah ce mai maganar dai-dai tana ƙarasowa inda suke ta kama hannun Nu'aymah dake hawaye, dama bakin bai gama mata zafiba akan dukan da Umm tai masa yanzu. Ga kuma Kubrah ta ƙara mata wani.
    Cikin masifa Kubrah ta kalli Hajarah, “Kozaki rama mata ne?”.
     “Bazan rama mata ba, amma ALLAH zai saka mata. Tunda duk wanda ya zalinci wani ALLAH na kallonsa. Nu'aymah jeki Addahn na ɗakinta kinji ko”.
      Kai Nu'aymah ta ɗagama Hajarah tana share hawayenta. Batare datace komaiba ta nufi ɗakin Addah zuciyarta na mamakin yanda Aunty Kubrah kejin zafinta a ƴan kwanakin nan, duk da dai dama ita babu wani shaƙuwa sosai tsakaninta da ita tun da can. Sai dai bata taɓa nuna mata banzan hali irin na wannan karonba. Tana gab da shiga ta tsinkayo muryar Kubrah na faɗin, “Ƴar iskar yarinya ki taka a sannu dan a tafin hannuna kike wlhy, inba hakaba saina tona asirin iskancinki a gaban kowa yasani a gidan nan”.
     Sosai gaban Nu'aymah yay bala'in faɗuwa, dan tasan inhar Kubrah ta faɗi abinda ta gani tsakaninta da Yoohan ranar tata ta ƙare. Da ƙyar ta iya haɗiye kukan daya taho mata.
        Da mamaki Hajarah ta kalli Kubrah, “Haba Aunty Kubrah wace irin maganace haka? Wai nikam minene ya haɗaki da Nu'aymah mai zafi a kwanakin nan dan ALLAH?”.
      “Ki shaƙeni in faɗa miki mana”. Kubrahn ta faɗa a harzuƙe.
      “ALLAH ya baki haƙuri”. Hajarah ta faɗa tana barmata wajen ranta fal tunane-tunane kala-kala akan ƴar tsamar yayar tata da Nu'aymah data gaza fahimtar tushenta a kwanakin nan sam.

       Sai da Nu'aymah tai sallama Addah ta bata izinin shiga sannan ta shiga ɗakin. Tsaye ta isketa tana ninke abin salla alamar sallar ta idar. Ganin Nu'aymah na sharar hawaye yasa fara'ar fuskar Addah gushewa lokaci guda. “Lafiya Nu'aymah? mi akai miki?”.
       “Babu komai Addah, Umm ce tace na kawo miki wannan”.
    Sam Addah bata yarda da maganar Nu'aymah ba, dan haka tai shiru tana cigaba da kallonta kawai batare data amshi man-shanun ba. “Nu'aymah bana son shirme, faɗamin gaskiya mi akai miki?”.
      “Addah wlhy aunty Kubrah ce ta dakar mata baki dan hawai tacemin ta tambayeta kina ina ta mata banza”. Hajarah dake shigowa ɗakin ta bama Addah amsa.
      Cikin ɓacin rai Addah tace, “Kubrah?!”.
       “Eh wlhy Addah, ni bama dukan ya ɓatan rai ba, bakiji yanda take faɗama Nu'aymahr maganar banza ba. A kwanakin nan dama na kula tana matsama yarinyar nan a gidan nan, haka ɗazun a islamiyyar asuba dan kawai Nu'aymah ta fiddo Fahad ɗin maman Sadiya daga aji saboda suna faɗa da wani yaro wlhy bakiga abinda tai mataba. Alhalin baikamata taima Nu'aymahn maganaba tunda yaran duk ƴan ajintane, ta fita sanin halin kowa a cikinsu”.
      Kama hannun Nu'aymah Addah tayi suka fito ranta a ɓace. Hakan yasa Hajarah biyo bayansu da sauri itama.
         “Kubrah!!”. Addah ta ƙwala mata kira ganin bata a falon.
    Da sauri ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da plate ɗin abinci.
     “Ubanmi Nu'aymah tai miki kika daketa?!”.
        Sake tsuke fuska Kubrah tayi, ta kalli Nu'aymah data duƙar da kai tana hawaye har yanzun. Wani ɗan murmushin mugunta tayi kafin ta kalli Addahn. “Addah catai na daketa?”.
       “Ni na faɗa ba ita ta faɗaba, tunda a gabana akai komai”. Hajarah ta bata amsa kafin Addah tai magana.
      “Mtsooow!! Munafuka kawai. Addah ni ban daketa haka kawaiba, rashin kunya zataimin shiyyasa........”
     “To amma shine zaki ce mata ƴar iska, kuma sirrinta a tafin hannunki yake. Idan kinso zaki tona mata asiri agaban kowa”.
       “Wlhy Hajarah zan sauya miki kamanni, wai ni sa'ar wasanki ce?”.

         “Kai!! Ya isheni haka, banason rashin mutunci. Bazan ɗauki wannan wawancinba kunji na faɗa muku. Shin kuɗin yaran goye ne da kullum baku da wani buri sai na samin

1 Comments On SARAN BOYE
avatar
maryam-8-1

1 year ago

Reply

Amazing book

Please Login or Register in order to submit comment