Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Malami yana bayani, ki dinga rubuta abin da kike fahimta a game da darasin, idan kika koma gida sai ki faɗaɗa bincike, sai ki haɗa ki tsinci abin da zaki tsinta ki haɗa, amma idan ki ka ce handout zaki haddace baki fuskanci darasin ba, zaki iya samun idea escape ma a wurin exams. Dan haka idan ana lectures a daina yiwa malamai tsiwa ana korar mutum daga aji, wani abin idan har aka yi baka nan ya riga ya wuceka kenan"
Murguɗa masa baki tayi, jin statement ɗin sa na ƙarshe, tare da cewa "Ina ruwanka da an koreni, bana son sa ido, ban littafina".

"Zan baki littafinki, amma kan in baki duba wannan, sai in ƙara yi miki bayani, zaki ga yafi sauƙi a kan wanda kike yi" kallon rubutun nasa tayi, har da wani larabci a ciki.

"Kaga nifa bana gane larabci" tai maganar tana wani basarwa.

Aikuwa Yazeed kamar an kunna fanfo, ya dinga zuba yana mata bayani tana saurarensa, babban abinda ya sanya shi farinciki, bai wuce saurarensa da take yi ba.

Sai da ya gama, tayi ajiyar zuciya, dan idan ta ce ba ta gane me yayi mata bayani ba tayi ƙarya, dan duk abin nan da ake, haddacewa kawai take ba ganewa ta yi ba.

"Na fahimta, Na gode sosai".

"Never mind ranki ya daɗe, bari inje masallaci"
Ta jinjina masa kai, bayan tafiyarsa, ta ɗau jakarta ita ma tayi waje ta nufi gida.


Khalil an fara yi masa way da ga wurin aiki, a kan lallai ana buƙatar sa, ji yake kamar ya ce Ya fasa komawa, saboda yadda yake jin Hafsa a zuciyarsa, ji yake kamar ba zai iya tafiya ya daɗe bai ganta ba.

Ana gobe zai koma, ya je gidansu Abdul ya yi masa sallama, suka sake tattaunawa a kan yadda Khalil zai ɓullowa Hafsa, suka yi sallama Khalil ya tafi wurinta.

Wannan karon ba Mutane sosai a wurin nata, dan da alama ta kusa tashi ne ma.
Yana yin sallama a wurin, ta haɗe rai tare da amsawa ta ɗauke kai.

"Ina wuni tun da ke baki iya gaisuwa ba".

"To ai nima bance ka gaishe ni ba".

Khalil ya numfasa ya ce "shikenan, ba faɗa na zo muyi ba, sallama na zo muyi zan koma wurin aiki insha Allah".

Hafsa ta ce "To ni ina ruwana da zaka tafi?".

"Amma dai at least ai kya yi mini A dawo lafiya ko?".

Hafsa ta ce "To Allah ya kiyaye hanya"

"Ameen Hafsat, ya jikin Mamana?"

"Wace maman taka?".

"Mamanmu mana, mamanki ai mamana ce ko abin ba kara ne?".

"Jikin Mama da sauƙi".

Khalil ya ce "Masha Allah, Alhamdilillah, amma sauƙi na bahaushe ko kuma ta warke?"

"Da sauƙi sosai" Hafsa ta bashi amsa a lokacin da hankalinta ya koma kan wata coustomer.

Khalil ya sa hannu ya ɗau wayarta mai madannai, wadda ta sha jiki da yawa, lambarsa ya sa a wayar, ya kira lambarta ta fito a tasa, ya ajiye mata wayar.
Ya yi gyaran murya, wanda ya sanya ta waiwayo. Ya ce "Ko zamu je in duba Maman ne?"
Ta ɗan waro idanunta ta ce "Saboda me? Ince ga wa ya zo dubata?".

"Coustomer ɗinki, mai takura miki, kuma wanda yake fatan ya Aureki. Duk da ban gaya miki dalilin da ya sanya na nace ina ta bibiyarki ba, Hafsa ina sonki ne, kuma Wallahi da gaske nake, ni Aurenki zan yi, ina kishin ganinki a wurin nan kina wannan aikin"

Ai tuni ɗan annurin yau da ya gani a fuskarta, saboda zancen Mama da ya yi, ya gushe daga fuskarta, ta haɗe rai sosai da sosai tayi shiru taƙi magana.

"Hafsa maganata ce ta ɓata miki rai?"

"Dan Allah ka rabu dani, kar ka sake zuwa in da nake, ni ban fito sana'ata dan wani ya tausaya mini ba, ba ruwanka da sana'ata, kuma kar ka sake zuwa wurin nan, idan ba haka ba zan iya dena zuwa ni, in bar maka wurin".
A ɗan rikice Khalil ya ce "Amma Hafsa...

"Malam bana son jin wata magana, ka ƙyaleni" tayi maganar a hasale.

Haka Khalil ya tashi ya baro wurinta, jiki a sanyaye, yana mamakin halayen Hafsa, wace irin Yarinya ce haka, dan ance ana sonki ki birkice ki kama masifa?.

A sanyaye haka ya koma gida, yana tunanin mafita, amma dole ya san abin yi, da zuciyarsa ba zata iya haƙuri da Yarinyar nan ba.

Da ya koma gida, a Falo ya tarar da Mummy, da Fadila suna kallo, suna hira, Amina nata gyara dining, in da suka ci Abinci suka bar wurin.

Fadila na ta bawa Mummy labarin Yazeed, yadda ya iya larabci amma bai iya turanci ba hadda cewa "Mummy kin gan shi kuwa, kayan da yake sakawa? Amma sai ƙwaƙwalwa kuma baya iya turanci a baki".
Mummy ta taɓe baki ta ce "Wasu lokutan dama haka ne, yaran nan marasa galihu da suke tashi a wahala, suna da ƙoƙari, sai dai na banza ne, dan ko sun gama karatun ba aiki suke samu ba, sai da su zama masinja a manyan ofisoshi".

Amina da ke aiki a ranta ta ce "Ji mata da mugun baki, wato ɗan talaka ba zai huta ba, iyayenmu su yi muku bauta, muma muyi muku da 'ya'yanku, insha Allah ta Allah ba taku ba'

"Khalil lafiyarka kuwa, ka zo ka zaun kayi shiru haka?".

"Mummy bakomai".

"Ya fa bakomai? Ga yanayinka duk ya canza".

"Mummy wata Yarinya ce" sai kuma yayi shiru.

"Mai Yarinyar ta yi?" Mummy ta tambaya cike da zaƙuwar son jin ƙarshen zancen.

"Mummy Bakomai" ya faɗa cikin damuwa.

"A'a ka fara magana kace bakomai, ko dai ka fara Soyayya ne?".

"Eh to, Yarinyar ce dai haryanzu ban samu shawo kanta ba".

Mummy tayi murmushi ta ce "Ikon Allah, dama akwai lokacin da zaka samu macen da tayi maka, sarkin kushe kushe? A ina take kuma 'yar waye? Ina fatan ba gidan tsiya zaka je ka ɗauko mana sirika ba?"
Gaban Khalil ne ya faɗi, be bawa Mummy amsa ba ya miƙe, ya ce "Idan komai ya daidaita za muyi maganar".

Fadila kuwa wani takaici ne ya mamayeta, da tausayin Yusra da take ji, gaba ɗaya haushin Khalil ya kamata, ta tashi ta bar falon ita ma.


Haka Khalil ya kwana yana tunanin dalilin da ya sanya, Hafsa ta canza fuska dan kawai ya ce yana sonta, shi dai ya san ba muni ne da shi ba, dan ƙarewa ma mata ne suke rushing a kansa, bai taɓa tunanin Soyayya zata iya kai shi wurin mai awara ba, dan da shi a yadda yake tsara rayuwarsa, macen da ta kammala degree ma yake so, very matured lady, haka yayi bacci rabi da rabi.

Washegari tun sassafe, Fadila da Mummy zasu je unguwa, dan haka suka raka Khalil airport, su kuma suka wuce in da zasu.

Hajara ma shiri tayi, ta tafi kasuwa saboda akwai kayan da babu, mai zuwa kasuwar sayowar kuma Hajiya Zainab ta koreshi.

Amina taje wurin Baba suka sha hira, daga nan ta koma cikin gidan, tana ɗan ƙara dudduba abin da za tayi.
Ta dawo babu daɗewa aka fara bubbuga ƙofar falo. Amina ta je ta buɗe ƙofar falon, wasu mata ta gani su huɗu, sai yara su ku san biyar.
Amina ta ce "Sannunku da zuwa"

Suka amsa mata da yauwa, ta basu wuri suka shiga falo, suka zazzauna.

Ɗaya daga cikin matan ta ce "Ahmad ɗin yana nan ne?" Amina ta ɗan yi jimm, tana tunanin wanene Ahmad.

Matar ta ce "Me gidan"
Amina ta ce "Au, ai ba ya gari bai dawo ba, sai da ki kai magana naga kuna kama, 'yan uwansa ne ku?".

Matar ta yi murmushi ta ce "Eh ƙannensa ne da iyayensa".

Amina ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Allah sarki, sannunku da zuwa gashi duk ba sa nan, sannunku" nan da nan Amina ta tafi kitchen, ta dinga jido ruwa da lemuka a fridge, tana kawo musu, ta koma ta haɗo musu fruit a ƙaton faranti, ta zo ta zube musu, cikin hanzari ta koma kitchen, ta ɗora girki, ta sake dawowa falo tana musu sannu da zuwa.

Ɗayar ta kalli Amina ta ce "Amma dai ke baƙuwa ce a gidan nan ko?".

Amina ta ce "Eh baƙuwa ce, aiki nake yi ban cika wata biyu bama".

"Allah sarki yarinyar kirki, Allah ya yi miki Albarka. Mun zo duba wani ɗan uwa ne da aka kwantar a Asibiti, muka ce bari dai mu biyo mu duba Ahmadu, tun da shi ya watsar da mu mu bari muzo".

Amina ta ce "Allah sarki, ai kuwa kun kyauta zumunci ai Akwai daɗi". Nan da nan kamar sun san juna tun tuni, Suka saba da Amina, abinka da wanda ya ce maka ungo.
Ta shirya musu lafiyayyen girki, yaji uban nama, ta kawo ta ajiye musu, aikuwa suka zage, suka ci Abincin nan, suka yi sallar azahar, Amina ta ware musu A.C ta kunna musu kallo.

Hajara ce tayi sallama, daga kasuwa ta dawo wujiga wujiga. Sai dai tana ganin matan da ke Falon tai turus, ta gaishe su, suka amsa mata, Amina ta tashi ta tayata ɗaukar kayan da tazo da su zuwa kitchen. Suna zuwa kitchen Hajara ta kalli Amina ta ce "Amina, waye ya saki bawa baƙin nan hidima haka, har da girki?"

Amina ta ce "Ban gane ba"

"To ki shirya hukuncinki a wurin matar gidan nan, Allah ya sa ƙarshen zamanki a gidan nan bai zo ba, dan wannan mutanen arziƙin ruwan pure water suke samu idan sun zo, shi yasa suka daina zuwa".

Amina ta ce "Amma Hajara 'yan uwan mai gidan ne fa". Amina ta faɗa cikin damuwa.

"Ke ki ka san 'yan uwan mai gidan ne, amma ki shirya karɓar mummunan hukuncin da zaki fuskanta a wurin!!!.


IDAN BA A COMMENT ZAN DAI NA TYPING TABBAS, KO YA KOMA PAID, IN ƁATA LOKACI INA TYPING, KU BINI DA THANKS😏😏😏

GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143

P13

Gaba ɗaya jikin Amina ya yi sanyi, jin abin da Hajara ta gaya mata, mussaman batun korar nan da ta ambata, jiki a sanyaye ta ce "Amma Hajara ai baƙon ka annabinka, ka yi baƙi 'yan uwan mai gida ka wulaƙanta su?".

"Na gaya miki kefa ki ka san wannan, ita ba ruwanta, kawai ki saurari kwandon bala'in da zata zo ta sauke miki a ka, kiyi fatan ya tsaya a iya tijarar da zata miki"

Jikin Amina yayi sanyi, amma babu yadda zata yi, tun da har ta riga ta musu kyakywar tarba, kuma ita ba taga aibun abin da ta aikata ba. Jiki ba ƙwari ta fito falon, ta tarar sun fara haramar tafiya.
Amina ta ɓoye damuwarta ta ce "Ya naga kun fara shirin tafiya? Ba zaku jira su dawo bane?".

"A'a kar yamma ta yi mana, gara muje mu tari motar garinmu".

"Au dama ba a garin nan ku ke ba?"

Ƙaramar cikinsu ta ce "A'a, mu daga jigawa muka zo" suna tsaka da maganar, Hajiya Zainab ta turo ƙofar falon,  Fadila na bayanta. Tana shigowa ta yi turus ganin mutane a falon, ta bi su ɗaya bayan ɗaya da kallo, ta sauke idanunta a kan farantan da ke falon, alamar an ci an sha, dan har da taunannun ƙasusuwa, da ragowar kabeji a cikin farantan, ta sauke idanunta a kan Amina, da tayi tsuru-tsuru kamar ta yiwa sarki ƙarya.
Cikin takunta na isa da taƙama ta ƙarasa shigowa falon, tana cigaba da yi musu kallon ƙasƙanci.

Ɗaya daga cikinsu ta ce mata "Sannu da zuwa"
Sai da ta sha ƙamshi sannan ta ce "Yauwa" tayi gaba ta nufi sashinta, Fadila ta bita ba tare da ko gaida su ba.

"Hmm mai hali baya fasa halinsa, ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta, Ahmad dai ɗan uwanmu ne, ko anƙi ba za a taɓa canzawa tuwo suna ba"

Amina ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri".

"Babu komai, ke dai mun gode sosai da karamcin da kika mana, dan rabon da mu zo gidan nan a kalle mu da mutunci har mun manta, mu mun tafi sai an jima". To muje in rakaku. Amina ta bisu Suka fita tare,  na ta sake basu haƙuri, ta rakasu har haraba, sannan ta dawo ta kwashe kwanukan da suka ɓata, ta gyara falon tsaf, ta shirya wa su Hajiya Zainab na su Abincin a kan dining, ta koma kitchen ta yi wanke-wanke, tana ta tsumayin jin kiran Hajiya Zainab amma shiru, ba tace mata komai ba.

La'asar liƙis, Bayan an idar da sallar La'asar, Khalil ya kasa jurewa, ya ɗau wayarsa ya fara lalubar lambar Hafsa.
Hafsa kuwa ta kammala haɗa kayanta na fita wurin sana'a, ta tsaya yin sallar la'asar.
Wayarta ce ta fara ringing, har ta katse ba a ɗaga ba, aka sake kiran wayar, Mama ta gaza haƙuri ta ɗaga ta ce "Salla take" ta katse wayar.

Da Hafsat ta idar sa salla, ba ta bi ta kan waye ya kirata ba, ta cigaba da shirin fitarta, tana daf da fita aka kuma kiran wayar a karo na uku. Ba tunanin komai ta ɗaga tare da yin sallama "Assalamu alaikum warahmtullah".

Khalil ya yi wata ajiyar zuciya sannan ya amsa ya ce "Babyna ya kike?".

Sarai ta ɗau muryarsa, amma ta haɗe rai ta ce "Wake magana?".

"Khalil ne".

"Wane Khalil ɗin" ta faɗa tana yatsuna fuska.

"Khalil coustomern ki, kuma masoyin ki" ɗif ta kashe wayar, tare da wani guntun tsaki, ta ja kayanta ta bar gidan.

Hajiya Zainab ce ta fito cikin taƙama, fuskarta babu annuri ta kalli Hajara, da ke ta kiwa tana komowa a falon ta ce "Ke kina gidan nan ki ka bari aka saukar mini wannan mutanen a gida? Uban waye ya bada izinin aikata hakan"

Jiki na rawa Hajara ta ce "Wallahi Hajiya bani bace ba, ba laifi na bane, ni bama na gida na je kasuwa sayayya, Amina ce"

Hajiya Zainab ta wani hura hanci, tana huci ta ce "Tana ina?"

"Tana wurin Babanta"

"Wuce ki kira mini ita, daga ita har shi ɗin"

Hajara ta ce "To" ta bar falon jiki na rawa ta nufi harabar gidan.

Amina na zaune tana karatu, suna hira da Baba jefi jefi.

Hajara ta ƙaraso ta ce "Wai kuje in ji matar gidan" cikin Amina ne yayi wata tsuwwa, saboda tashin hankali.

Baba ya kalli Amina ya ce "Uwata, lafiya kuwa? Ina fatan ba wani laifin kika aikata ba?"

Amina ta girgiza kai ta ce "Ban yi laifin komai ba Baba"

Baba ya ce "To Allah ya sa, tashi muje muji".

Amina ta tashi suka bi bayan Hajara, ko da suka shiga falon, kallo ɗaya Amina ta yiwa Hajiya Zainab, ta san babu mutunci, babu afuwa a tare da fuskarta.

Baba ne ya gurfana a gaban Hajiya Zainab, hakan ya sa Amina ma ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta gurfana ɗin.

"Waye ya baki iznin ki ɗau Abincina ki girka ki bawa wannan wahalallun mutanen?" Tai maganar cikin isa tana tsare Amina da idanu.

Amina ta ce "Ba kowa".

"Abincin naki ne, ko kuma da izinin wa ki ka yi hakan?"

Amina ta ce "Wallahi ni ban san ba a bawa baƙo Abinci a gidan nan ba, naga idan wasu suka zo ana basu, kuma ce mini suka yi daga nesa suke, 'yan uwan maigidan ne, shi yasa na basu Abinci".

"Kin taɓa ganin ire-iren wannan mutanen a gidan nan da zaki basu abinci na?, har ki kwashe mini kaya a fridge ki ba su? Talakan ubanki ne ya saya ya ajiye, da zaki ɗebar mini kaya kiyi gwaninta da su?" Damm! Ƙirjin Amina ya buga da ƙarfi, talakan ubanki ta maimaita abin a zuciyarta.

Baba ya ce "Dan Allah, dan Annabi kiyi haƙuri, laifina ne da ban gaya mata dokar ki ba, amma dan Allah kiyi haƙuri ba zata sake ba".

"In yi haƙuri ko kar in yi bai shafeni ba, zaka biya kuɗin abin da ta salwantar a albashinka, kuma wannan shi ne na farko kuma na ƙarshe, idan ta sake makamancin laifin nan, sai ta bar mini gida, ta koma ƙauyen da fito, ta je can ta cigaba da hauka da jahilicin da ta zo da su"
Wata irin ƙunar rai ce ta kama Amina, jikinta har rawa yake saboda baƙi ciki, da ɓacin rai, da gari banza ne wani ya hɗata da Baba ya ci mutuncin ta, da sai in da ƙarfinta ya ƙare, amma yanzu babu damar magana.

Baba ya ce "Ba damuwa Hajiya, insha Allah ba zata sake ba" ya kalli Amina ya ce "Uwata ki bata haƙuri"
Amina kamar zata fashe, haka ta risuna ta ce "Allah ya baki haƙuri, ba Baba ne ya sai Abinci ba, insha Allah ba zan sake aikata haka ba".

Hajiya Zainab ta ce "Kima sake, kiga ƙarshen rashin mutunci" Baba dai ya kwantar da kai, ya cigab da bawa Hajiya Zainab haƙuri.

Sai da ta sallame su sannan suka tashi, Baba ya ja Amina waje, ya kalleta ya ce "Uwata, yanzu har kin manta da nasihar da na miki a kan zamanki a gidan nan? So kike sai kin yi dalilin rasa damarki ko?".

Amina ta ce "A'a Baba, ban san dokar gidan ba ce ba saukar baƙi, amma insha Allah ba zan sake ba".

Baba ya ce "To ki kiyaye, ki daina shiga abin da babu ruwanki, ko kuma aikata abin da ba a saka ki ba, kin ji ko?".

"To Baba insha Allah ba zan sake ba"

"Yauwa uwata, Allah yayi miki Albarka, maza koma ciki abinki" Amina ta juya ta koma, ranar na mata ƙuna, yadda aka ƙasƙanta mahaifinta a gabanta, a kan laifin da ita ta aikata ba shi ba.
Haka ta koma ɗakinta sukuku, ta zauna baƙin ciki ya isheta, ta tuna yadda Baba ya gurfana a gaban matar da ya girmeta nesa ba kusa ba, ba ta kalli furfurar kansa ba, ta dinga zazzaga masifa, da Amina tana da burin idan ta samu ta cigaba da makaranta, amma taga kamar abin ba mai yiwuwa bane, saboda gaba ɗaya zaman gidan ya fara sire mata.

Sai wajen ƙarfe tara na dare, sannan Hafsa ta dawo daga wurin sana'arta, ta tarar Mama ta dafa mata ruwan wanka, ga kuma girkin dare ta yi, ta zauna ta ci Abinci, tayi sallar isha'i sannan ta shiga ta yi wanka da ruwa mai zafi sosai, kasancewar dul zafi duk sanyi Hafsa ba ta wanka da ruwan sanyi, saboda tana jin daɗin zuba ruwan ɗumi ko mai ɗan zafi a jikinta.
Ko da Hafsa ta fito daga wanka, mai ta nema ta shafa, tana yi suna hira da Mama, wayarta ta fara ringing, ta kai hannu ta duba, taga lambar Khalil, wanda sai a yanzu taga missed calls huɗu ya yi mata tana wanka, katse kiran ta yi, tare da kashe wayar gaba ɗaya.
Mama tana kallonta ba tace mata komai ba, sai da ta bari Hafsa ta gama shirinta tsaf tana ƙoƙarin jan bargo. "Hafsa" Mama ta kira sunanta.
"Na'am Mama".

"Waye ya ke kiranki a waya?".

"Mama ba kowa"

"Ba na miki magana ne dan muyi jayayya ko ki mini musu ba, amsa kawai nake buƙata daga gareki" Mama tayi maganar babu alamar wasa a tare da ita.

Hafsa ta ce "Mama kawai fa..

"Kar ki mini ƙarya Hafsa, namiji ne yake kiranki waye?".

"Mama, ba komai fa tsakanina da shi, kawai zuwa yake ya sai awara a wurina".

"Ina jinki sai kuma aka yi yaya?".

"Cewa ya yi yana sona" Hafsa ta ƙarasa maganar kamar wadda tai saɓo.

"Shi ne kuma ki ke wulaƙanta shi, har ya kira ki katse wayar? Anya Hafsa rayuwa zata cigaba a haka? Bai kamata kowa ya nuna yana sonki ki koreshi ba, ki bashi dama mana, na ɗaga wayar kina banɗaki, ya gaisheni, naji alamun nutsuwa a tare da yaron. Amina ina buƙatar in ga aurenki kan bar duniya, kina gani yau ina da lafiya gobe babu, ina son in ganki a hannu na gari kan in mutu Hafsa".

Cikin matsananciyar damuwa Hafsa ta ce "Mama dan Allah ki daina irin wannan maganar, kin san fa komai Mama, mai zai sa in yi wani ganganci,gara kawai mu cigaba da rayuwarmu ni da ke a haka".

"Hafsa, duk abin da ya wuce, to ka bar shi a baya kawai, karki waiwaya kan abin da ta wuce idan har ba na Alkhairi bane, ki sa ka magogi ki goge abin da ya shuɗe ki fuskanci rayuwarki, zama haka ba zai yiwu ba, ke macece zamanki a bakin hanya kina wannan sana'ar dan babu yadda zan yi ne, zamanki a ɗakin ki shi ne rufin asirinmu gaba ɗaya".

Hafsa ta kwaɓe fuska za ta yi kuka ta ce "Ni dai dan Mama...
Mama ba ta bari ta ƙarasa ba, ta ɗaga mata hannu ta ce "Ya isa, tun da ke dai ba a baki shawara, ki je kiyi abin da kike ganin daidai da ke ne"

"Mama dan Allah kiyi haƙuri, ba nayi ne dan in ɓata miki rai ba".

"Rabu dani ni" Mama ta faɗa a ƙufule. Haka Hafsa ta kwanta cike da damuwa, ta shiga tuno irin hali da yanayin ƙaddarori, da suka haɗu da su na rayuwa ita da Mama.

Saura kwanaki uku a fara exams, akwai teses ɗin da Yazeed ya yi missing, lokacin da bai zo ba ba shi da lafiya, wasu malaman sun karɓi uzurinsa sun yi masa, wasu kuwa sai wahalar da shi suke yi.
Ɗaya daga cikin malaman da ke wahalar da Yazeed, saboda ya rasa Attendance ɗinsa, kuma ya ce wanda bai yi Attendance ɗinsa na ƙarshe ba, ya sa a ransa ya faɗi jarrabawarsa. Sannan ya fito da wani littafi ya ce lallai kowa sai ya saya, littafin naira dubu biyu ne, kusan sati biyu kenan ana sayar da littafin.
Kwatsam, saura kwanaki uku jarrabawa, ɗalibai na ta fama da karatu, ya shigo ajin, ya ce zai yi musu lecturer, kuma da wannan littafin zai yi amfani, duk wanda ba shi da littafin ya tashi ya fita, ko kayi Attendance idan baka da littafin nan, to baka da exams ɗin sa, ko da kuwa ka cinye duka. Idan kuwa baka da Attendance, amma ko baka da Attendance, muddin kana da wannan littafin to ka haye exams ɗin sa.
Idonta ne ya sauka a kan Yazeed, da ya yi shiru, ko motsawa bai yi ba, balle a sa ran ya fito da nasa littafin, A kunyace tsirarun waɗanda ba su da littafin, suke tashi suna fita daga ajin, malamin yana ta musu bala'i cikin tozarci.
Fadila ce ta miƙe tsaye, ta nufi hanyar fita, ta ajiyewa Yazeed littafinta ita kuma ta wuce zata fice.

"Hey Madam zo nan" sautin muryar malamain ta daki dodon kunnuwanta, cak ta tsaya sannan ta waiwayo fuskarta babu alamar wasa, cike da izzarta ta kalli malamin, tana sauraren mai ze ce.
"Ina littafinki?" Ya tambayeta yana tsareta da ido.
"Bani da shi sir, ban samu na saya ba" ta faɗa ba tare da wata shakka ko damuwa ba.
"Shi kuma wancan littafin da ki ka ajiye masa fa" ta yi mamakin yadda aka yi ya ga ta ajiyewa Yazeed littafi.
"Ba nawa ba ne, na sa ne ya ara mini".

"Ƙarya ki ke yi, Malam fito nan"
Yazeed ya fito jiki a sanyaye, yana jinjina irin ƙasƙancin da za a masa a gaban mutane. Ga ajin yayi shiru an maida ido kan su.
Lecturer ya kalli Yazeed ya ce "Littafinka ne ko nata?" Yazeed zai yi magana, Fadila ta ce "Sir ba fa ƙarya nake maka ba, littafinsa ne ba nawa ba"
Yazeed baya son ya faɗi wani abin da zai janyowa Fadila matsala, ko cin mutunci, hakan ya sanya ya kasa magana.
Lecturer ya karɓi littafin daga hannun Yazeed, sai dai yana buɗewa ya ga sunan Yazeed da Admission number ɗinsa.
Shi kansa Yazeed bai san ya aka yi ta rubuta ba, Ya miƙawa Yazeed littafin sannan ya kalli Fadila ya ce "Kina nufin baki sai littafin ba?"

"Eh na saya, amma nayi karatu na manta shi a aji, na dawo ban ganshi ba".

Malamin ya ce "Ok, ku koma ku zauna, amma ki sake sayan wani".
Yatsina baki ta yi, suka koma wurin zamansu.

Har malamin ya yi ya kammala karatun, Yazeed yana kallon Fadila lokaci lokaci, yana jinjina abin da ta yi masa, ba dan tayi hakan ba da ya fuskanci tozarci da ƙasƙanci a gaban 'yan aji.

Bayan fitar malamin, Yazeed yana son yiwa Fadila magana, amma 'yan aji sun saka ido, suna son ganin Action ɗin da su Fadila za suyi, amma Fadila ta haɗe fuska tamau, wani na kawo raini zata balbale shi da masifa da tsiwa.
Yazeed ma basarwa yayi, amma ƙasan zuciyarsa so yake ya yi mata magana.
Class rep ne ya shigo da takaddu a hannunsa, na wata test da suka yi.
Ya fara rarrabawa kowa test ɗin, sai dai abin da ya ƙara bawa Yazeed mamaki, bai wuce yadda aka miƙo masa takadda ba, ya karɓa yana dubawa, wannan dai ba rubutunsa ba ne, dan lokacin da aka yi

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment