Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hawaye suka zubo mata, ta miƙa masa wata babbar jaka, ta ajiye a gabansa, sannan ta kalleshi ta ce "Khalil, jiya na maka text, ka turo mini kuɗi, ka bani ninkin abin da na nema, na nemi kuɗin nan ne dan mayar da asarar da aka yi mini, na kayan sana'ata, Khalil daga rana mai kamar irin ta yau, ka sa a zuciyarka baka taɓa saɓnin wata mai kama da ni bama, balle tuna mun yi soyayya.
Jiya mahaifiyarka ta zo ita da wasu, sun yi mini kashedin babu ni babu kai.
Tabbas sun yi gaskiya, zaren ba kalar yadin bane, ni da kai bamu dace ba, kyautatawarka a garrni ta ruɗeni na fara sonka, ba tare da na kalli banbancin matsayinmu ba.
Ga shi nan duk wani abu daka bani, na tataro na dawo maka da su, zoben nan ne kawai ba zan iya dawo maka da shi ba, saboda kana cikin mutane masu muhimmanci da suka shigo rayuwata, na san ba zan taɓa iya mantawa da kai ba, Na gode Khalil Allah ya haɗa kowa da rabonsa" ta ƙarasa maganar tana zubar da hawaye, ta juya ta shiga cikin soron.
Cikin zafin nama Khalil ya bita, ya riƙota ya juyo da ita tana fuskantar sa.

Kamar zai fashe da kuka ya ce "Haba Hafsa, ina duk alƙawarin da kika yi mini na kasancewa da ni, duk ƙalibalen da ka iya tasowa kuwa, dan Allah karki ce zaki rabu da ni ba, dan Allah kar ki mini haka, in dai Mummy ce zan yi mata bayani, zata fuskance ni kuma, dan Allah Hafsa, muna son junanmu karki yanke wannan hukuncin"

"Bakin Alƙalami ya riga ya bushe Khalil, idan na ce bana sonka nayi maka ƙarya, amma duk wani abu da za ayi iyaye ba sa so ba zai taɓa yin albarka ba, banga alamar Mummy zata fahimceka har ta bari muyi aure ba, dan Allah Khalil kar ka sake shigowa rayuwata, Allah ya haɗa kowa da rabonsa"
Ta zame hannunta daga cikin nasa da ya riƙe, ta shige cikin gidan tana kuka.

Contact me for the VIP group
AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA

BY

AISHA ADAM AYSHERCOOL



PAGE 38

Wani abu me mai nauyi ya tokarewa Khalil ƙirji, bai taɓa tunanin Mummy zata aikata abin da ta aikata ba, na zuwa ta ci mutuncin Hafsa a gaban mutane.
Tamkar wanda aka zare wa lakar jiki, haka ya ja jikinsa ya buɗe motar, ya shiga ya zauna, ya kifa kansa a kan sitiyarin motar, ya rasa abin da yake masa daɗi, ya rasa ta ina zai ɓullowa wannan lamarin, gab ɗaya komai ya cakuɗe masa, ya shafe a ƙalla mintuna Ashirin a cikin motar ya kasa ko da kunna motar, balle ya ja. Ganin bashi da wata mafita a cikin wannan tsayuwar da yake yi, ya sanya ya kunna motar, ya fara tuƙi, sai dai jin jikinsa yake tamkar an zare masa dukkan wata laka dake jikinsa, da wani dishi dishi yake gani, da ƙyar yake iya jan motar, ya nufi gidansu Abdul.
Shagon Abdul a rufe yake, alama Abdul ɗin baya nan, Khalil ba shi da kuzarin da zai kira Abdul, dan haka ya cigaba da zama a cikin motar ta sa yana kuma tuno maganganun da Hafsa tayi masa.
Bai san iya adadin lokacin da ya kwashe a zaune a cikin motar nan ba, knocking ɗin glass ɗin motar da aka yi ne ya sanya shi dawowa play, har ya sauke glashin motar, Abdul ne a tsaye yana kallon Khalil "Ya aka yi baka kirani a waya ba, ka zauna a mota kana bacci?"
Khalil baice komai ba, ya buɗe motar ya fito, Abdul ya wuce ya buɗe ƙofar shagon, Khalil ya shiga ya nemi wuri ya kwanta, ba tare da ya ce wa Abdul komai ba.

Abdul ma bai takura shi sai yaji meke damunsa ba, ya ƙyaleshi.

Fadila kuwa sai yamma suka gama shirin komai, suka zauna yin kwalliya, har su Hajiya Turai sun zo, Daddy maa da wuri ya dawo gida, sai dai Fadila ba taji daɗin rashin Khalil a wurin ba, ta yank Cake suka yi hotuna, zuwa magariba kowa ya watse.

Hafsa kuwa bayan shigarta gida wani sabon kukan ta zauna tana cigaba da yi, Sai da Mama ta ga kukan ya yi yawa sannan ta sameta a ɗaki ta ce "Hafsa, wannan kukan da kike fa babu in da zai kai ki, kiyi haƙuri, kiyi Addu'a Allah ya zaɓa miki mafi alkhairi, ko kin auri Khalil tunda mahaifiyarsa ba ta ƙaunarki, ba zakiji daɗin zama da shi ba, kiyi haƙuri Allah ya musanya miki da mafi alkhairi"

Hafsa ba ta cewa Mama komai ba, dan ita kaɗai ta san me take ji a ranta, a kan rabuwarta da Khalil, ta sani rabuwarsu ba yana nufin rayuwarta ta zo ƙarshe bane, amma samun wanda zai maye mata gurbin Khalil abunne mai wahala, ita ta riga ta gama yadda ba ta da sa'a a rayuwata, duk wani abin alkhairi da zai tunkarota, sai ya lalace.

Can Mama ta nisa ta ce "Yanzu wace sana'ar kike ganin zamu koma yi? Bana son ki cigaba da fitar nan tunda na fauskanci babu alkhairi a hakan, kowa ya tashi sai ya sameki a can ya yi miki wulaƙanci a cikin mutane, yanzu dai bari zuwa jibi in Allah ya kaimu idan kin yi tunanin wani abun da zamu yi sai ki mini magana,tun da muna da Abinci.
Jinjina kai kawai Hafsa tayi, ba tare da ta iya cewa komai ba.

Har Khalil ya gama zamansa a ɗakin Abdul, bai cewa Abdul ɗin komai ba, sai bayan sallar magariba, sannan ya yi wa Abdul Sallama ya tafi gida.

Ko da ya fito zai tafi gida, zuciyarsa ji yake kamar ya sake komawa gidansu Hafsaz ko zata sakko ta saurareshi, amma yadda yaga hawayen nan a idonta cikin damuwa ya ƙara tabattar masa da gaske take, ta bar shi.
Haka ya shiga motarsa ya tafi gida.

Ita kanta Fadila rashin walwalar Khalil ya fara damunta, kwata kwata ya daina shigowa cikin gidan, ko ba komai ko su haɗu suyi faɗa yana ɗebe mata kewa.
Ta kalli Mummy da ke zaune tana cin cake, su Hajara kuma na gyara falon,.

"Mummy, wai dan Allah haka za'a zubawa Yaya Khalil ido? Kinga fa ya daina shigowa cikin gidan nan sam, ko ma bashi da lafiya ne?"

Mummy ta ce "Lafiyarsa ƙalau, duk a kan na raba shi da waccan yarinyar ne, yake fushi da wannan iskancin, na ɗau matakin ƙarshe da nake ganin ya dace, in shi ba zai rabu da ita ba, su dolensu su rabu da shi, idan har suna da zuciya"

"Amma Mummy wane matakin kika ɗauka"

Mummy ta yi murmushi ta ce "Ke ina ruwanki, ba dai nace miki na ɗau mataki ba"

Fadila na shirin yi magana sai ga Khalil ya shigo falon, gaba ɗaya ya rame duk yayi wani iri.

Fadila ta ce "Yauwa brother, na je ɗakinka babu adadi ina nemanka, yau birthday na duk an yi hotuna babu kai".

Be kula Fadila ba ya ƙarasa in da Mummy ta ke, ya kalleta ya ce "Mummy, ban taɓa zaton zaki mini abin da kika yi ba, dan kawai na ce ina son 'yar talaka ba, yanzu Mummy meye laifin yarinyar da za'a wulaƙanta ta haka? Me tayi ita?"

"Au Yanz zuwa kayi ka titsiyeni ko ka tuhumeni a kan wannan shegiyar yarinyar? To ka kyauta daidia nake da kai, zan ga ni da kai waye ya haifi wani"

Kamar Khalil zai fashe da kuka ya ce "Mummy ba haka bane, Mummy da girmanki da mutuncinki yarinya ce fa ƙarama Hafsa, 'yar cikinki kuma sirikarki"

Miƙewa Mummy ta yi ta ce "Zan tsinke ka da mari, ni zaka zo ka tsayaa kaina kana gaya mini maganar banza, ka kiyayeni Khalil, wallahi ka cigaba da bibiyar yarinyar nan, zan maka abin da tunaninka bai taɓa kawo wa zan maka ba, kuma idan ta cigaba da bibiyarka, wallahi saina ƙasƙanta ta na tozartata fiye da abin da nayi mata yanzu, idan yaso ka nemi wata uwar ka canza ni"

Khalil ya girgiza kai ya ce "A'a Mummy, ke uwata ce, ba yadda za ayi in iya canzaki, ko in fifita wata a kanki, Mummy ina nuna miki illar abin da kika aikata ne, ita ma 'ya ce, uwa ce ta haifeta ya tata uwar zata ji da wannan abin da kika yi mata? Haba Mummy"
"Lallai Khalil, wuyanka ya riƙa ya isa yanka, ka nuna mini ka kawo ƙarfi, gara da na farga na miƙe tsaye, kan kwaso mini wadda zata dinga juyaka, idan kaga na bari kayi aure, to matar da na zaɓa maka ce, tun da naga baka da hankali"
Idonsa fal hawaye ya ce " Shikenan Mummy, kin yi nasara kin rabani da Hafsa, shikenan Mummy"

"Kar ma ta rabu da kai, da ta cigaba da bibiyarka dai, da taga ƙaryar talauci, sakarai kawai"

Ta wuce fuuuuuu ya bar falon.

Khalil ya zauna ya dafe kansa, yana girgiza kan yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa.

Fadila ta zauna a kusa da Khalil ta ce "Brother, wai me Mummyn tayi maka ne?"

Ya ɗago idanuna da suka yi jawurr, jijiyoyin kansa duk suka mimmiƙe suka kumbura, ya kalli Fadila ya ce "Yanzu fisabilillahi Fadila ya dace ace Mummy taje da ƙawayenta, sun ci mutuncin yarinyar mutane a gaban al'umma, suka watsar mata da kaya a cikin ƙasa, ita meye laifinta?"

Fadila ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Haka ne, gaskiya Mummy bata kyauta ba, amma kaima Yaya Khalil meye kaika, duk matan duniya ka nacewa wata mai awara, ai koma menene kaine ka janyo mata, tunda Mummy ta nuna bata so ai saika haƙura"

Kalaman Fadila ƙara masa ɓacin rai suke, dan haka ya tashi, ya bar falon zuciyarsa babu daɗi.
Sosai Amina taji tausayin Khalil ya kamata, mussaman ita wadda ake ce anje an ci mutuncin ta a gaban mutane. tana mamakin baƙar zuciya irin ta Hajiya Zainab, babu tausayi ko Allah a ranta, gani take kamar ita ta yiwa kanta arziki ba Allah ne ya bata ba.

Fadila ɗan taɓe baki tayi, ta tashi ta bar falon, duk da Khalil ɗin ya bata tausayi, amma a ganinta matakin da Mummy ta ɗauka yayi daidai, dan Khalil yana da taurin kai wasu lokutan.

Amina wasu lokutan mantawa ma take da wayar da Daddy ya bata, saboda bata son ta ɗauke mata hankali da ga kan karatunta sam.

Da Asubar fari Khalil ya shirya kayansa, ya ɗauki motarsa ba tare da ya yiwa kowa sallama ba, ya fice daga gidan.
Abdul yana zaune yana azkar, bayan idara da sallar asba, yana jiran gari yayi haske yayi wanka, ya ga wayar Khalil.
Yasa hannu ya ɗaga wayar yana faɗin "Lafiya kake mini wannan kiran haka da sassafe?"

"Ina ƙofar gidan ku, airport nake son ka kaini, jirgin Bakwai da rabi zanbi in koma Abuja"

Mamakine ya kama Abdul, dan ba suyi wannan zancen da Khalil ba jiya, ya miƙe, ya saka hula ya ɗau wayarsa ya fita, aikuwa yaga motar Khalil.

Ya rufe shagon nasa, sannan ya nufi wurin da motar Khalil ɗin take.

Ya buɗe motar ya shiga, ya kalli Yadda fuskar Khalil duk ta kumbura, ga idanunsa mu duk sun kumbura sun yi ja, kamar wanda bai yi bacci ba.

"Wai Khalil meke damunka ne? Meyasa zaka koma yau bayan kace mini sai next week zaka koma?"

"Abdul, Hafsa ta rabu dani, ba zata aureni ba" ya faɗa tamkar zai fashe da kuka.

Abdul ya ce "Subhanallah, saboda me?"

Cikin damuwa Khalil ya ce "Abdul, could you imagine Mummy da kanta iya da ƙawayenta wai suka je suka yiwa Hafsa warning a kaina, suka watsar da kayan sana'arta a gaban mutane? Abdul waye ni ɗin ne? Me aka yi aka yi ni? Yanzu ya dace abin da Mummy tayi, girmanta ne yin hakan?"

Abdul ya ce "A'a Khalil, yi haƙuri, Mummy uwa ce kar ɓacin rai ya sanya ka faɗi wata maganar a kanta"

"Haba Abdul, ka duba lamarin nan dan Allah, yanzu dama da yaya na samu kan yarinyar nan, maimakon idan ma rabuwar ce, a bari mu rabu ta daɗin rai, in mata bayani mu rabu cikin mutunci, amma anje an ci mutuncinta, meye laifinta? Har Abada ba zata taɓa ganin mutuncin Mummy ba, na rasa dalilin da yasa Mummy ke biyewa wannan ƙawayen nata suna zigata tana abubuwan da basu dace ba, idan nayi yinƙurin gayamata Gaskiya, ta ƙare mini zagi ta nuna mini haryanzu bani da hankali, amma ka duba wannan lamari meye na Hafsa a ciki?"

"Haka ne Khalil, bai kamata Mummy ta aikata hakan ba, amma hakan ba shi yake nufin ka faɗi abin da kake so a kanta ba, kayi haƙuri ka cigaba da yi mata addu'ar Allah ya ganar ita. Ita kuma Hafsa idan rabonka ce, Allah ya daidaita lamarin, ya tabbatar muku da alkhairi, idan kuma ba alkhairi bace, Allah ya haɗa kowa da rabonsa.

Khalil ya sauke wata ajiyar zuciya ya ce "Baka san wani abu ba, cewa fa tayi wai bani ba zaɓar macen da nake so na aura, ita zata zaɓa mini, kuma wallahi na san duk wannan matan ne suka kitsa mata ta hau ta zauna, Mummy tana valueing maganar ƙawayenta fiye da kima"

Abdul ya ce "Kayi haƙuri abokina, ka cigaba da yi mata Addu'a"

Khalil ya ce "Shikenan, muje airport, kai sai ka dawo da motar, idan ka samu lokaci ka mayar musu da motar can gida"

"To shikenan, Allah ya tsare" Khalil ya ja motar suka tafi.

Kamar kullum, yau ma Amina ta kammala shirinta na makaranta, cikin gogaggun uniform ɗinta, ta saɓa jakarta a bayanta, ta fita wurin Baba, ta tsaya suka gaisa da Baba, Baba ya ce "Uwata, kuɗin makarantar da nake baki ba sa isarki ne?"

Cikin rashin fahimta Amina ta ce "A'a Baba me ka gani?"

"Alhaji Ahmad ne ya bani kuɗi, kusan dubu goma, wai idan zaki tafi makaranta, in dinga baki isasshen kuɗi, saboda ba kya tafiya da Abinci, yunwa na damunki a makaranta"

Amina ta mariraice Fuska ta ce "Wallahi Baba ban ce masa wani abu aba, ranar da na wuni a makaranta ne a wurin lesson, yazo ya ɗaukeni na ce ba zan sake zuwa lesson ba, mun wuni a makaranta ina jin yunwa, amma wallahi Baba ni bance masa komai ba"

Baba yayi ajiyar zuciya ya ce "To Uwata, ba zan fasa yi miki nasiha ba, ki iya kankina duk in da kika tsinci rayuwa, kar ki sakankance da mutumin nan ki jamana wata matsala a gidan nan"

Amina ta ce "To Baba in sha Allah"

"To ni yanzu wannan kuɗin zan baki dubu uku, idan sun ƙare sai ki kuma yi mini magana in baki wasu, amma bance kiyi ta kashe-kashen banza ba"

"A'a Baba, dubu biyu ta isheni duka watan nan, ka sayawa Inno kayan shayi a aika mata, ita ma ta dinga cin mai daɗi kamar yadda muke ci a nan"

Baba yayi murmushi ya ce "Uwata kenan, ke dai ki karɓa, ni na san abin da zan yi"

Amina ta miƙe daga tsugunon da tayi, ta ce "Baba, bari in tafi, bani yadda ka saba bani, idan na dawo sai muyi maganar kar na makara"

Baba ya saka hannu a aljihunsa, ya cirowa Amina naira ɗari uku ya bata, ta saka hannu biyu ta karɓa, tayi masa sallama ta fita.

Tana ta sauri ta ƙarasa titi, ana ta wucewa da yaran masu kuɗi a cikin motoci zuwa makaranta, ba tsammani taji an kira sunanta.
Ɗan tsawa tayi ta waiwaya, Bilal ta gani cikin suit baƙaƙe.

Ya ƙaraso in da take yana faɗin "Amina, makaranta zaki tafi ne?"

Amina ta ce "Eh, ina kwana?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ɗan jirani in shiga gida in ɗauko mota, in kai ki mana"

Amina ta ce "A'a sauri nake, ka bari na gode"

"Haba Amina, dan Allah ki tsaya in kai ki"

"A'a ka bari wallahi na gode"

Bilal ya ce "Gaskiya ban ji daɗi ba, to muje in rakaki titi"

"A'a karka damu dan Allah, zan ƙarasa"

Bilal bai saurreta ba, ya cigaba da binta, suna tafiya tare, gaba ɗaya hankalin Amina baya kan Bilal, sai surutu yake mata, ba tare da tana amsa masa ba.

Sun ƙarasa titi tana jiran mota, ba tsammani sai ga motar Daddy ta zo wucewa, lokacin da ta fito daga gida ko tashi baiyi ba, amma har ya shirya ya fito, sai da ya zo daidai in da suke, sanan ya ɗan ja motar a hankali, yayi musu horn, dan Amina ta san ya ganta, sannan ya ja motar da sauri ya bar wurin.

Sai da cikin Amina yayi ƙara, ba ta san hukuncin da Daddy zai yi mata ba, saboda yayi mata gargadi a kan Bilal.

Sai da Bilal ya tabattar da ta hau mota, ya biya kuɗin, sannan ya juya ya koma.

Yau Fadila ita da kanta taje wurin zaman Yazid, sai kallonta yake yana murmushi, ta miƙa masa wata 'yar ƙaramar jaka ta ce "Gashi nan, kayan birthday ne, na kawo maka"

"Ohh ni Yazid, har da ni a cikin kayan, to Allah ya sanya abin da kika bani ɗin na iya ci"

"Idan ma baka iya ba saika koya"

Ya ce "To shikenan, zauna muyi wata Magana"

Fadila ta nemi wuri ta zauna, ya ɗan dubeta ya ce "Da kika ƙara shekara a duniya, kuma kika kama hanyar komawa ga ubangijinki, wace Addu'ar ki ka yi?"

Fadila ta ɗan taɓe baki ta ce "Wace Addu'ar kuma?"

"Au ke baki Addu'a ba, sai iyayi"

"Ba wani iyayi, family and friends sun yi wishing ɗina, that's all"

Yazid ya ce "No, yakamata ki roƙi Allah gafara, ki yiwa kanki kyakkyawan fata a cikin abin da ya rage miki a rayuwarki, kiyi Addu'a a kan karatunki, da kuma fatan Allah ya kawo miki abokin rayuwa na gari, wanda yake sonki"

Ta ɗan kalleshi ta ce "Waye abokin rayuwar?"

"Miji mana, na gari mai sonki saboda Allah, ko da kuwa Kankiya ne"

Haɗe rai ta yi, ta ce "Wai sau nawa zan gaya maka, kar ka sake haɗani da mutumin nan, bana son irin haka na gaya maka"

Yazid ya ce "Ikon Allah, to ke haka ake yi? Ba Addu'a nayi miki ba, ai idan kana neman azaɓin Allah, barwa Allah komak ka ke, baka zaɓe-zaɓe"

"Over my death body in auri wanan mutumin mara tunani"

Da sauri Yazid ya ce "Subhanallah, Ukty malaminki ne fa"

Ai tamkar da kankiyan take magana, ta ce "And so what? Ko na rasa mijin Aure ni ba ajinsa ba ce, yana rayuwa kamar wani bagidaje da bai san meya ke yi ba, a haka zan so shin?"

Jikin Yazid yayi sanyi, Kankiya ma kenan, da ya na ɗaukar wanka, ina ga shi, da kayan sawarsa ma ba su fi a ƙirgasu ba.

Har tayi shiru ta cigaba da mita, "Allah na tuba, ko a ƙafata a ka ɗaura mini shi ba sai na kwance shi na yar ba, kai mini wata Addu'ar banda Wannan, ni waima waye ya ce maka zan yi Aure ne? Da in yi Aure da kar in yi duk normal ne"

Yazid yayi murmushi ya ce "A hakan da kike?"

Ta ɗan kalleshi da mamaki ta ce "Kamar yaya a hakan da nake?"

Ɗan taune lips ɗinsa na ƙasa ya yi ya ce "Bar zancen, amma kina buƙatar abokin rayuwa na gari, ai kin kai girman da kin zama mutum 'yar yarinya"

"Haka nace maka?"

"Ko baki faɗa ba yanayinki ya nuna Besty, anyway mu bar wannan maganar, Allah ya baki miji nagari, ko da Yazid ne"

Da wani irin sauri ta kalli Yazid, tare da yamutsa fuska kamar wadda ya gayawa saƙon mutuwa ta ce "What? Wane Yazid ɗin?" Tayi maganar babu alamar wasa a tare da ita.

"Kai bari kaji in gaya maka, tun wuri ka mayar da hankalinka, am still the Fadila you know, kawai naga rashin dacewar wulaƙancin da nake maka ne, ya sanya nake kulaka, kan ka yiwa kanka fatan zama mijina, Yakamata ka san waceceni, ba sa'arka ba ce ni, we are just friends, tun da abin da kake tunani kenan, friendship ɗin ma is over now, Fadila ba matar ire-iren mutane kamar baka ce".

Yazid yayi shiru, bai taɓa zaton Fadila zata yi masa haka, ta bishi da wanan kausasan kalaman ba, tun ma bai kai ga furta cewar yana sonta ba, matuƙa kalamanta sun tsaya masa a zuciyarsa.

Ita kuwa tana gama yanka masa wannan maganganun, ta tashi ta bar wurin da yake.

Ya bita da idanuwa, yana jin zafi a ransa.

Ko da yake maganganun Fadila suna bisa turba, ita ba sa'ar aurensa ba ce, matsayinsa da nata ba ɗaya bane ba, amma idan aka duba matakan addini, yana da duk wani qualities da za a aureshi domin su.
Shiru yayi yana jin yadda duniyar ta yi masa zafi, yana ji a ransa dama bai yi mata wannan maganar ba, da wataƙila sun cigaba da gaisawa.

Gaba ɗaya Ajin ta bari, ta tafi department ɗin su Yusra, tana zuwa ta tarar da malami a ajinsu Yusra, dan haka ta jira sai da suka kammala lectures, malamin ya fita, sannan ita kuma ta shiga ajin.

Yusra ta kalli Fadila da ɗan mamaki a fuskarta ta ce "Girl ya dai? Na ganki rai a ɓace".

Fadila ta zauna tana ɗan hura hanci.

"Ke wai meye ne?" Yusra ta faɗa tana sake tattara hankalinta a kan Fadila.

"Kin san wani abin takaici da raini?"

"A'a sai kin faɗa"

"Yazid fa sona yake" ta faɗa cike da takaici.

"Au da da nake gaya miki baki yadda ba? Me yayi miki ne?"

"Wai Allah ya bani miji nagari ko shine"

Yusra ta kwashe da dariya ta ce "Gaskiya Fadila baki da wayo, ke ce baki da tunani wasu lokutan, idan ba sonki yake ba mai zai saka yayi ta bibiyarki har ya dinga taimaka miki, yayi ta miki abubuwan da zai burgeki" Fadila ta ɗan yi shiru ta ce "Lalli bani da hankali, kawai na ɗauki alaƙarmu ne a friendship, ni mai yasa mazan nan suka rainani, amma Yazid tsaurin idonsa ya kai in da ya kai, ina shi ina mace kamar ni?"

"Kar ki cika baki malama, tun da ya fara bijirowa a mafarkanki da kika gaya mini, akwai alamar cigaba da tarayyarku ka iya sanyawa ki fara son shi, saboda gayen yana da kirki sosai"

"Ashe kuwa da Mummy ta kwaɗani ta cinye, kin san a tashin hankalin da Yaya Khalil yake dan ya ce yana son mai awara, hmm naga wautar Yaya Khalil"

Yusra ta ce "Ikon Allah, shi kuwa Yaya Khalil meya yi masa zafi?"

"Oho masa, duk yadda suke da Mummy,tayi masa fata fata, ko cikin gida ba ya iya shigowa, ba kiga ko jiya bai shigo wurin birthday na ba. Ina gama alhakinki ne"

"A'a kar ki ce haka Fadila, Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi"

"Amin dai, da nazo na gaya miki maganar nan har naji sanyi, ni wallahi tausayi yake bani ma, Kankiya ya sako shi a gaba da yawa a kaina, ni kuma bana son a lalata masa karatunsa saboda ni, amma shi ma Kankiya tara sh nake, idan ya kaini bango sai ya rasa aikinsa wallahi"

"A'a Fadila ki bi a hankali dai"

"Ai a hankalin nake bi, ke kin san da ba a hankalin nake bi ba, Kankiyan shi da koyarwa a jami'ar nan har Abada, banda ke babu wanda ya san abin da ke tsakanina da shi, sai Yazid, shi kuma wannan ko ban gaya masa abu ba, ganowa yake kamar aljani"

Yusra ta ce "Do you know one Funny thing? Kin iya faɗar sunansa wallahi, har wata madda kike Yaziiiid"

Tsaki Fadila tayi ta ce "Ke bana son wulaƙanci, bana son duk wani abu zai sake haɗani da shi, kowa yayi rayuwarsa kawai".

Yusra ta ce "Shikenan, tunda kin huce yanzu a kan yadda kika zo mini"

"Bari kawai ya ƙular da ni ne, da wani shegen takalminsa irin na danƙon nan, sai uban saka jallabiya kamar limamin harami"

Yusra ta kwashe da dariya ta ce A'a kar ki zafafa dai"

Fadila ta kai kusan twenty minutes tare da Yusra, sannan ta koma department ɗin su.

Da idanun Yazid ta fara cin karo, kallo ɗaya zaka yi masa, ka gane jikinsa yayu sanyi, guntun tsaki tayi ta wuce wurin zamanta.

Ƙarfe biyu daidai, aka tashi daga makaranta, Amina tayi sallama da 'yan ajinsu, ta fito gate.
Wata uwar mota ta gani a bakin gate ɗin makarantar ta su a tsaye, da wasu 'yan sanda biyu a jikin motar.
Bata kawo tunanin komai a ranta ba, ta cigaba da tafiya. Ji tayi kamar ana binta a baya, ta waiwaya taga 'yan Sandan sun biyota.
Gabanta ne ya faɗi , tana sake dubwa taga wa suke bi.

Ɗaya ɗan sandan ya ce "Amina ko?"

Idanuwa waje Amina take binsu da kallo, tana tunanin meye haɗinta da 'yan sanda suka biyota makaranta.

"You Are under Arrest!!!"

AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA
            BY

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment