Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kallo, sannan ta kalleshi cikin mamaki 'Wai duk daga jiya zuwa yau kayi wannan?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

"Amma ai ka wahalar da kanka da yawa, wannan uban rubutun haka? Shikenan Sai mu kai Cafe a buga?"

Duk da yau baya son yin Magana, amma yaji daɗin yadda ta yaba ƙoƙarin sa.
Dan haka ya ce "Eh, da ina da babbar waya ko system, da a ciki zan mana sai ayi printing, kowa a bashi wanda zai yi presenting"

Fadila ta ce "System ɗina na mota, bari in ɗauko sai in fara typing ɗin, kar aikin yayi maka yawa" ƙarara yake ganin tausayawa a idonta.

"Muje in rakaki" Suka tashi suka jera zuwa in da motarta take, ta buɗe ta ɗauko system ɗin sannan suka dawo aji.
Ya nemi wuri ya zauna, ta buɗe system ɗin ta kunna, hotonta ya bayyana a kan lock screen, ta saka password sai ga wani ya bayyana a wallpaper ɗin ta, ba ƙaramin tafiya da Yazeed hotunan suka yi ba.

Amra ƙawar Fadila a baya, banda yanzu da ta daina shiga sabgar ta, saboda Amran na da wasu halaye da ba su yi mata ba, ta ƙaraso in da su Yazid suke zaune, suka gaisa sama-sama da Fadila. Sannan ta kalli Yazeed ta ce "Yaya Yazid dan Allah wurinka na zo, 'yan group ɗin mu zaka ɗan taimaka mana a kan presentation ɗin da zamuyi"

"A yanzu dai aikin namu yake yi, kuna iya jira zuwa ya gama" Fadila ta bata amsa.

"Bafa da ke nake ba" Amra ta mayar mata da martani.

Yazeed ya ce "Afuwan Amra, bari in kammala namu, sai in zo"

Guntun tsaki Fadila tayi, ta cigaba da operating system ɗin.
Janyo System ɗin gabansa yayi, dan a ganinsa bata sauri a typing ɗin, tunda ya zuba yatsunsa a kan keyboard ɗin nan yake sarrafasu cikin gwanancewa kamar wani inji. Fadila ta ƙureshi da ido, shi kusan komai ya iya, ana batun Mutane gifted bata taɓa gazagata hakan ba, sai a kan Yazeed.

Ji tayi kamar ta tambayeshi a ina ya koyi computer, amma ta basar.

Lokacin sallar azahar yayi, Yazeed ya ce "Zai je yayi sallah, idan ya dawo zai cigaba.
Ta tashi ta bashi wuri, ya tafi salla, ita ma tashi tayi ta bar System ɗin a wurin saboda careless, ta tafi yin salla da cin abinci.
Bayan ya dawo ya tarar da komai yadda ta barshi, ya zauna ya tattara mata litattafanta, minimising yayi, ya zubawa kyakywar fuskarta da ke kan screen ɗin system ɗin ido, yana jin yadda wani abu ke sake fuzgarsa game da ita.
"Ina sonki Fadila" ya furta yana cigaba da ƙarewa screen ɗin kallo.


"Malam Yazeed wai haryanzu baka gama ba?" Ya ji murayar Amra a kunnensa.

Yazeed ya kalli Amra ya ce "Ku mini haƙuri, na kusa gama namu, idan na gama zan zo in sha Allah"

"To shikenan" ta amsa masa tana ƙoƙarin barin wurin, Fadila ta shigo hannunta da leda, ta ƙaraso ta zauna, tana kallon screen ɗin system ɗin.

"Ka kusa gamawa ne?"

"Eh, saura kaɗan, so nake in yi in gama, wancan group ɗin suna jirana".

Fadila ta yamuatsa fuska ta ce "Kaga kayi mana abinmu a nutse Please, ba suna da waya ba suje suyi mana, ko su tafi Library"

Yazida ya ce "A'a ba'ayi haka ba, zasu ga ban kyauta musu ba, kuma wulaƙanci babu daɗi"

Taɓe baki tayi ta miƙa masa leda ɗaya gabansa.

Ya kalli ledar ya ce "Meye wannan?"

"Abinci" ta bashi amsa.

"Alhamdilillah na gode, amma na ƙoshi"

Cikin tsiwa ta ce "Saboda na zuba wani abu a ciki?"

Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Idan ma kin zuba wani abu a ciki da ina jin yunwa ba ruwana cimyewa zan yi"

"Wannan shi ne karo na biyu na baka Abinci ka ƙi ci, meye dalili?".

Yazeed ya ce "Nifa yau azumi nake"

"Dama ana azumi ranar talata?"

"Eh mana, azumin Annabi dawud, yau kayi gobe ka sha ruwa"

Tsuke fuska tayi ta ce "Sannu waliyyi, kamar fa raina mini hankali kawai kake yi, ba wanda zai iya irin wannan azumin"

"Inji wa? Gwauraye na yin irin wannan azumin, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ne ya bawa samari shawarar yawan yin azumi idan... Sai kuma yayi shiru.

Gaba ɗaya Fadila bata gane in da zancen Yazeed ya dosa ba.

"Kaga ni ban taɓa ji ba, ka dubo wata ƙaryara dai kayi"

Ɗan tsuke fuska yayi, ya saka idanunsa a nata, "Ni ne nake ƙaryar?"

Tsiwa ta so yi, amma sai ta kasa jikinta yayi sanyi, idanun Yazid suka yi tasiri a kanta, wanda sai da idanunta suka yi nauyi, ta janye idanunta tana ɗan tura baki.
Ɗauke idonsa yayi shima, yana jin daɗin yadda yake yi mata kwarjini wasu lokutan, har ta kasa magana.
Kusan mintuna goma, yana typing, ya ƙi taɓa ledar Abincin.

Can ta kuma kallonsa ta ce"Wai ba zaka ɗau Abincin nan ko ruwan ka sha ba?"

"Wai ina ruwanki dani ne, nace miki azumi nake"

"Wane irin azumi ne da za'ace wani azumin samari, ba azumin tsofaffi kawai ake ba?"

Sosai Yazid yake dariya, wata amsa ya so ya bata, amma yaga amsar tayi nauyi da yawa, dan haka ya ƙyaleta ya cigaba da dariya.

Ganin yadda yake dariya sosai, haƙoransa suka bayyana ya sanya ta ce "Wallahi ba azumi kake yi ba" ta faɗa cike da tsiwa.

"Subhanallah, ya aka yi kika san ba azumi nake ba? Shikenan ba azumi nake ba ba zan ci ba"

Haushi ne Yakamata, ta miƙe tsaye ta fara jan system ɗinta.

Ya kalleta ya ce "Ya dai?"

"Bani System ɗina tafiya zan yi" riƙewa yayi yana murmushi ya ce "Sorry yi haƙuri, zan ci" yayi maganar wani irin farinciki yana ratsa shi, kamar a mafarki yake ganin faruwar al'amarin, wai Fadila ce take jin haushi dan be karɓi abin hannunta ba.

"Kar ma kaci, bani tafiya zan yi"

"Yi haƙuri in ƙarasa, sai muje Cafe a cire, nima sonake na gama da wuri, idan lecturer nan bai zo ba, zanje wurin sir Kankiya, mun haɗu a masallaci ya ce idan na gama lectures in je Office ɗinsa"

Ɗan saroro tayi, ta kalleshi ta ce "Me kayi masa?"

"Nima ban sani ba, kawai dai ya ce inje"

"Yi sauri ka ƙarasa muje"

"Muje ina?"

"Wurinsa" ta bashi amsa.

"Ai bece muje tare ba"

Fadila ta ce "Ni dai yi sauri ka gama"

Ita kanta har mamakin kanta take yi, yadda yau ta saki jiki da Yazeed, ita gaba ɗaya a rayuwarta bayan 'yan gidansu sai Yusra, sukaɗai ne mutanen da suke bata nishaɗi, dan ita ba shiga harkar mutane take ba, amma Yazid mutum ne mai matuƙar barkwanci, duk haushinsa da kake ji, sai ta fuskanci in ka zauna tare da shi zai baka dariya, sai dai shima ba kowa yake shiga harkarsa ba, balle ka gane tsananin sauƙin kansa, gashi baya fushi abinsa, ga rashin girman kai.

Gaba ɗaya ya manta da su Amra da ke jiransa, ya kammala typing ya kalleta ya ce "to muje Cafe a cire, sai a rabawa 'yan group"

"Sai fa kaci Abincin nan"

Ya ɗan waro ido "In karya azumin nawa?"

"Ai ba azumi kake yi ba" tayi maganar tana sake tsareshi da ido.

Ta saka shi a gaba, ya ciro pack ɗin Abincin, soyayyar doya ce da miya sai uban nama fal a cikin miyar, sai ruwa da lemo.

Ruwan yai bisimillah ya fara sha. Fadila ta ce "Kana malami kana ƙarya, yanzu azumin kenan?"

"Niba malami bane, ɗalibi ne, kuma aike kika karya mini Azumin"

"Wata ƙaryar again" tayi maganar tana hararasa.

Bece mata komai ba, ya fara cin doyar da ƙamshin miyar kawai ya sanya yawun bakinsa tsinkewa, Fadila ta juya masa baya tana danna waya, yayin da shi kuma gaba ɗaya ya kasa sakewa, Yazeed yana da matuƙar gudun zuciya da abin da zai sa a masa gori wata rana, ya ci Abincin nan ne kawai dan yana son ganin yayi abin da zai sa Fadila taji daɗi, ba wai dan yunwar da ta addabi cikinsa ba.

Ya kammala ya dinga yi mata Addu'a, har sai da ta haɗe rai, saboda godiyar tayi yawa.
Sai da suka fara zuwa Cafe, suka ciro aikin, sannan Fadila ta ce suje wurin Sir Kankiya.
Sai dai da suka je, suka tarar baya nan, suka zauna zaman jiran Kankiya, Yazid ya cewa Fadila ta tafi kawai zai jira shi, amma taƙi, saboda ba ta san me zai cewa Yazid ba.
Ƙarshe Fadila ta gaji da zaman, tayi masa sallama ta tafi, a kan Cewar duk yadda suka yi da shi ya gaya mata. Yazid ji yake kamar yayi tsalle dan murna, saboda kulawar da Fadila ta nuna masa yau, zuciyarsa bata taɓa kamuwa da tsananin son abin da yake kasancewa da shi ba kamar Fadila.





Alhaji Ahmad ya dawo gida, kusan ƙarfe biyar na yamma, sai dai daga yadda suka gaisa da Baba, ya lura kamar akwai damuwa a tare da shi. Alhaji Ahmad yayi parking, tare da kallon sa ya ce "Malam Hassan, lafiya naga kamar kana cikin damuwa?"

Baba ya risuna ya ce "Amina ce haryanzu bata dawo daga Makaranta ba, gashi ban san makarantar tasu ba balle in bi bayanta, nayi wauta yakamata ace tun tuni na san makarantar ta su"

Daddy ya ce "Subhanallah, kwantar da hankalika, bari in je makarantar da kaina"

Baba ya ce "A'a ranka ya daɗe, da ka kwatanta mini ni sai inje in duba"

"Haba Malam Hassan, Amina ai 'ya ta ce, idan Fadila ce zan wakilta wani ya nemota ne? Bari inje" yayi reverse ya ja motar ya ya nufi makarantar su Amina.

Alhaji Ahmad kai tsaye cikin makarantar ya shiga, ofishin director ya shiga, suka gaisa, Daddy yake tambayarsa yaji shiru haryanzu Amina bata koma gida ba.

Director yayi murmushi ya ce "Mun tsaresu ne, lesson ake tayi musu, lallai muna son wannan karon branch ɗin Kano, muci comptetions ɗin wannan shekarar, kuma Alhamdilillah Amina akwai basira, duk da ɗazu na zagaya ajin nasu, taƙi mayar da hankali wai ita ta gaji gida zata tafi"

Daddy yayi murmushi ya ce "Dole ta gaji, tun safe fa, kuma gashi in Allah ya kaimu next week, za kuyi resuming makaranta, kaga ita gaba ɗaya bata huta ba kenan"

"Haka ne, amma da anyi an gama shikenan, kuma idan Allah yasa tayi nasara, zaku yi alfahari da hakan, tana da ƙwazo sosai"

"Gaskiya ne, yanzu dai a ƙyaleta, tun da tace ta gaji ba ganewa zata yi ba, a turota mu tafi gida"

Director yayi murmushi ya ce "Dama yanzu za a tashe su su tafi, kuma dan wannan ranka ya daɗe ai da ko waya kayi, da kaina ma sai in dawo da ita gida ba sai ka zo ba"

"Ba komai, a turo ta mu tafi"
Suka fito daga Office ɗin tare da Alhaji Ahmad.

Tunda aka sanarwa da Amina Babanta ya zo ɗaukarta, ita zatonta Baba ne, ta san a rina, yadda tayi yammar nan, dole hankalinsa ya tashi ya biyo bayanta.
Sai jefa ƙafa kawai take, idanunta sunyi fuci-fuci sun yi jawur, jakar ma yadda ta saƙalata da gani ta mata nauyi.
Mamaki ne yakamata ganin Daddy a harabar makarantar.

Murmushi yayi mata ya ce "Sannu, sai kace wadda ake bawa training ɗin sojoji, duk kin yi wujiga-wujiga".

Aikuwa kamar ƙiris take jira.

Kamar za tayi kuka ta ce "Ni ba zan ƙara zuwa lesson ɗin nan ba, duk anfi wahalar da ni, gashi na gaji ga yunwa nake ji, bayana sai ciwo yake da cikina" tayi maganar a wahale, ƙwallar haushi na taruwa a idonta.

Alhaji Ahmad yayi murmushi ya ce "Eh gaskiya kam basu kyauta miki ba, ace mutum yana jin yunwa, kuma ga mutum rago Sarkin kuka, ace an hana shi tafiya gida dole a sa mutum ya gaji ai, har ya fara kuka" ya ƙarasa maganar yana murmushi.

Amina ta gane tsokanarta ya ke yi, sai kawai ita ma tayi murmushin, sannan ta ce "Ya aka yi ka san makarantar mu?"

"Tunani nayi, zuciyata ta bani nan ce makarantar" ɗan shiru tayi tana tunanin ya za ayi haka ya yiwu.

Buɗe mata gaban motar yayi ya ce ta shiga.

"Wai gaban motar zan shiga?"

"A'a tayar motar zaki hau". Ya faɗa tare da zagayawa mazaunin direba.

Ƙarewa motar kallo take, irinta kusan uku ne a gidan, Alhaji Ahmad ne kawai yake hawansu, baya hawa ƙananun motoci sai manya manya, ko nauyi basa masa wurin tuƙawa. Tayi maganar a zuciyarta.
Sai da tayi bismillah sannan ta hau motar, wani irin sanyi tare da ƙamshi suka ratsa hancinta, abinka da wanda yake a gajiye, ta sake kashingiɗewa a jikin seat ɗin motar.
Ya sawa motar lock tare da rufe glasses ɗin, ya ƙaro sanyin A.C ya fara jan motar.

"Tun da nake ban taɓa hawa mota me daɗin wannan ba, ko ta Khalil ba ta kai wannan daɗi ba".

"Allah ko?" Ya faɗa yana murmushi.

"Wallahi kuwa, kamar in bacci, to wai motar bata da nauyi ne, naga tayi girma da yawa kuma kana tuƙata a haka"

"Ko in sauka in baki wuri ki gwada kiji"

"A' a rufamini Asiri, ina zan iya"

Sai kuma tana ɗan yamutsa fuska ta riƙe cikinta.

Ya kalleta cikin kulawa ya ce "Ya dai?"

"Cikina ne yake ciwo"

"Yunwa kike ji, daga yau idan zaki zo lesson, ki dinga zuwa da Abinci, zan bawa babanki kuɗi, ya dinga baki kina sayen Abinci"

A ɗan tsorace ta ce "Taɓ salon ya ce roƙonka nayi, ni bana roƙo, kuma daga yau ba zan sake zuwa wannan lesson ɗin ba, na gaji ai nasara ta Allah ce, ba wannan izayar ce zata sa in ci ba" tayi maganar ranta a ɓace.

Alhaji Ahmad ya ce "Baki san abin da yake tattare da yin nasararki ba, kiyi haƙuri nasara sai an wahala take samuwa, sannan idan mun je gida, za kiyi wa Maman Fadila bayanin abin da ya kai littafinki ɗakin aikin mijinta"

Zaro Amina tayi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, a can na bar shi kenan? Na shiga uku me zance mata?"

"I don't know" ya faɗa yana ɗage kafaɗa.

"Na shiga uku ni Amina, Daddy kai ka jawo mini, baka gayamata kai kace in kai maka Abinci ba, shikenan wataƙila ta koreni karatuna shikenan, idan kuma tayi mini Afuwa kuma ta zageni ni da Baba" kan ta kai ƙarshen maganar, kuka ya ƙwace mata.

"Ke kuka baya baki wahala ne? Da wasa nake miki na karɓi littafin, na gaya mata ni na saki aiki a ɗakin, littafin yana wurina, meyasa kika ruɗe haka?"

Ajiyar zuciya Amina tayi, tana godewa Allah da ya ƙwaceta, da yau ta san tijarar da zata sha ba ta da iyaka.

Tausayin ta ne ya kama shi, da alama ita ma zata sha gwagwarmayar rayuwa kan ta cinma nasara, ya ɗan lumshe idanunsa ya ce "Allah ya rangwanta miki" ya furta a hankali ba tare da Amina ta ji ba.

A ƙofar gida yayi parking ya kalli Amina ya ce "Sauka ki shiga, idan kuma in shiga dake ne, idan ta ganki ki mata bayanin abin da ya kai ki motar mijinta kuma shikenan".

"A'a yi haƙuri bari in sauka, Na gode Allah ya saka da alkhairi".

Bai amsa mata ba, sai binta da yake da kallo.

Baba na ganin Amina ya tareta, yana tambayar ba'asin meye ya faru ta daɗe haka?
Amina tayi masa bayani, tare da gaya masa Alhaji Ahmad ne ya ɗaukota.

"To ki dai kula Amina, hanklina ya tashi sosai"

"To Baba ka cigaba da yi mini Addu'a"

"Aminatu Addu'a kullum cikinta muke ai"


A falo ta tarar da Hajiya Zainab da Khalil, ta durƙusa ta gaishe su, Khalil ya amsa Hajiya Zainab kuwa ko kallonta ba tayi ba, Amina da ta juya baya a hankali ta ce "kanki ki ka yiwa da baki amsa ba'


Khalil ji yake kamar ya janyo dare, dan yaje ya ga Hafsa, sai wata fara'a yake ta mussaman.
Alhaji Ahmad yayi sallama a falon, suka amsa masa gaba ɗaya, ya kalli Khalil ya ce "Kai saukar yaushe?"

Khalil ya amsa da "Ɗazun nan Daddy"

"Masha Allah, ya aikin?"

"Aiki Alhamdilillah Daddy"

"Masha Allah, Ina Fadila ne?"

Mummy ta ce "Ta dawo tana ɗaki tana baccin gajiya"


Ya jinjina kai ya wuce part ɗinsa.
Fadila kuwa bayan littafinta ta juya, tana kallon rubutun da Yazid yayi, sai mamaki take yadda aka yi ya iya kwaikwayon rubutunta, Yazid yana da abubuwan ban al'ajabi.
Tunowa tayi da maganarsa wai Azumin samari yake yi, kawai tayi murmushi ta rufe littafin.



Khalil miƙewa ya yi, ya bar Falon saboda an fara kiran sallar magariba, yaje masallaci ya dawo, ya shirya cikin wasu haɗaɗɗun ƙananan kaya, ya feshe jikinsa da turare, ya ɗauki kayan siyayyar da ya yiwa Hafsa, ya ɗau motarsa ya fice.
Ta wurin da take zaman suya ya fara bi, yaje ya tarar da ita tana ta fama da hayaƙi, ga masu siya sun zagayeta.

"Ke ungo nan bani ta naira ɗari ki riƙe canjin" yayi magana yana bata dubu ɗaya, sam bata san Khalil ya zo wurin ba sai muryarsa da ta ji.

Murmushi tayi tana kallonsa sanann ta ce "Gaskiya ni wannan zuwan be mini ba, kai kayi kwalliya ni kalleni cikin hayaƙi, kuma baka gaya mini zaka zo ba ba zan kula ka ba gaskiya"

Dariya yayi ya tsuguna a kusa da ita "Ni ko a yaya na ganki ƙara kyau kike yi, kawo abun fifitar in fifita miki, sallami waɗan nan"

"A'a ka bari kawai, kar kayi ƙaurin hayaƙi"

Karɓe abun fifitar yayi, yana ffifita mata wuta, ita kuma tana sallamar masu saya. Suna yi suna hira cike da nishaɗi da jin daɗi. Khalil ya saka ta raba sauran sadaka, ya ce ya saya, ba dan ta so ba Khalil ya tayata suka kwashe kayan, ya rufe motarsa suka hau ɗan sahu tare suka tafi gidansu Hafsa, tare da ledar da yayi mata.

Ya zauna a ƙofar gida, ya jirata ta shiga gida tayi kwalliya sama-sama ta fito. Sosai suke hira da Khalil, yana bata labarin wurin aiki.

Can ya nisa ya ce "Babyna yaushe zan turo su Daddy ne? Na gaji da zaman Abuja ba mata"

"To ni me zance?"

"Ban gane me zaki ce ba? Zan sanarwa da Daddy insha Allah zuwa next months zan turo, ginina saura kaɗan, shiyasa zan bari sai na kammala sai in turo" ɗan shiru tayi, sannan tayi ajiyar zuciya.

"Ya kika yi shiru, ko ba kya sona?".

Murmushi tayi ta ce "Ina sonka Sosai, in ba kai ba sai maliya" tayi maganar cikin dariya.

"Wayyo daɗi, dagaske Hafsa?"

"Da gaske nake mana"

"Kar ki saka in tattaro mutane a ɗaura mana aure yanzu"

Hafsa ta ce "Sai kace auren sadaka"

"Ai sai yafi albaraka, yakamata mu fara shirin biki ma"

"Ka san wani abu, yanzu kaje gida ka huta, kaga yau ka dawo"

"A taƙaice dai korata kike yi?"

"Ya za ayi in koreka, ni kaina ban gaji da ganinka ba, kaga motarka tana can, ga sanyi ko so kake kayi mura? Kaje gida ka huta kaji nawan"

"Yau ɗin nan jina nake wani na musamman, tattali da kulawa ta zahiri daga abar ƙaunata"

"Ni kaina mamakin kaina nake yi, ka kawo sauyi da farinciki a rayuwata, na gode Allah da ya sa baka yi zuciya ka rabu dani ba"

"Baby Hafsat, duk wanda yaji halin da kika shiga, dole zai tausaya miki, Hafsa ina sonki, zan ɓoye sirrinki zan miki adalci in sha Allah in kula da ke, dan Allah ki aureni kar ki canza ra'ayinki a kaina"

"Zuciyata na gazgata duk kan kalaman da kayi mini, kuma ina sa ran ba zaka bani kunya ba, ina sonka Mu'azzam"

"Kar ki sa in suma dan daɗi mana" tashi tsaye tayi tana dariya, "muje in raka ka titi"

"A'a gari da sanyi, koma gida ki huta, idan naje gida zamu yi waya"

"Allah ya kai mini kai gida lafiya"

"Naga idan ban yi da gaske ba, yau a a soron Mama zan kwana" ya bata ledar siyayarta ya tafi.


Jinsa yake kamar wani sabon ango, cike da nishaɗi da jin daɗi ya nufi gida.

Kai tsaye cikin gida ya nufa, domin ya ci Abincin dare.


Sai dai yana shiga falon ya tarar da Mummy a tsaye tana huci, tamkar wuta.

"Mummy lafiya kuwa?" Ya faɗa yana binta da kallo.

"Ban sani ba, daga gidan uban wa kake?"

Khalil ya ce "Mummy ban gane....

"Nace daga gidan uban wa kake?"

"Wurin Abdul"

"Sai naci........... Kai da Abdul ɗin, ni zaka tozarta Khalil? Saboda tsiya da abin kunya? Uban me kake a gaban kaskon mai awara?"

Ƙuuuuuuu cikinsa ya bada wani irin sauti gumi ya shiga tsatstsafowa daga goshinsa.

Cikin dakiya ya ce "Mai awara kuma?"

A hasale ta ce "A'a Ubanka"




Ayshercool
08081012143.
GABA DA GABANTA

            BY

AISHA ADAM (AYSHERCOOL/JAKADIYAR AREWA)

Page 30-31

*Zuwa ga masau sanya mini litattafaina a shafukansu ba da izini na ba, na barku da Allah, Allah ya saka mini, ina wahala kuna ci da gumina*

*Albishirinku masoya, littafin Dare da duhu, da ya samu kyakkyawan rubutu daga gamayyar marubuta uku, AYSHERCOOL, ZEE KUMURYA DA KUMA NIMCYLUV Ya kammala a document, ga mai buƙata ya tuntuɓi wannan lambar dan mallakar naku a kan kuɗi ₦500 kacal*

Cike da matsanancin tashin hankali, Khalil ya ce "Dan Allah Mumy waye ya gaya miki?"

"Au tuhumata ma kake yi? To ubanka ne ya gaya mini"

"Mummy walla..

"Zan taka ka ka mini rantsuwa, mutumin banza da na wofi sakarai, dama ina ankare da take taken ka, na zuba maka idanu in ga in da ka saka gaba, Hajiya Salma da Turai sun je duba shago, suka ganoka a gaban kaskon awara, suna kallonka kuka hau napep, saboda kalen tsiya kuka tafi, har wurin suka je suka tambayar mini, aka ce kana zuwa wurinta wai sonta kake, wallahi Khalil ka bani kunya, kamar bani na haifeka, ko ka manta matsayin ubanka a ƙasar nan? Babu 'yar wanda zaka kalla a manyan attajiran ƙasar nan a hanaka, amma saboda lalacewa da rashin sanin darajar kai, saboda tsiya, bama 'yar masu abinci a restaurant ba, mai soya awara a titi, ashe ita ce gayyara tsiyar da kazo da ita nan kana ci ran nan ko, an maka barbaɗe a ciki ka ci, idan takensu sammako ni a tafe na kwana, ni Zainab ban durƙusa na haifi ɗan da zai kawo mini jinin matsiyat ba, daga kai har ita zan yi maganinku, zan tsananta bincike a kan yarinyar".

Kamar Khalil zai ɗora hannu a ka cikin mariraicewa ya ce "Mummy, dan girman Allah kar ki yiwa Hafsa komai, ba ta da laifi ni na kai kana nace ina so"

"Zaka rufen baki ko saina falla maka mari, sakarai sususu, dalla ɓace daga gabana ka bar mini falo, zan ga uban da ya tsaya mata har ta liƙe maka"

"Dan Allah Mummy ni ki hukunta ni, marainiya ce fa"

"Khalil ni nake faɗa kana faɗa? Zan kwarara maka ashar fita ka bar mini falo" ta ƙarasa maganar a fusace tana nuna masa hanyar fita. A sanyaye Khalil ya fice, yana jin yadda wani abu ya tokare masa ƙirji saboda tsananin damuwa da ɓacin rai.

Amina ta sha jinin jikinta, ta tsorata da irin ƙyamar da take yiwa talaka, ta rasa me talaka yayi mata tayi masa wannan tsanar haka, ɗanta na cikinta ta saka a gaba, ta ƙare masa cin mutunci saboda ya nuna yana son 'yar talaka, ƙiyyyar ta wuce misali.
Fadila kuwa tana tare da Mummy aka kirata a waya aka sanar mata da anga Khalil, tare da mai awara, dan haka bata ji tausayin abin da Mummy ta yiwa Khalil ba musamman idan ta tuna yadda ya watsa mata ƙasa a ido, a kan soyayyar da Yusra take nuna masa.

Khalil kuwa wani irin gumi ne ya dinga tsatsatfo masa, saboda azanar tashin hankali, dama ya san a rina, amma yaso ace shi da kansa ya lallaɓata ya sanar da ita, amma wannan algunguman matan suka ɓata masa komai. A gaskiya yana son Hafsa, sai dai ya san babu yadda za ayi ya samu goyon bayan Daddy, muddin ba Mummy ce ta amince ba.
Ya tashi zaune yayi shiru, yana cigaba da tunani, wannan shi ake kira da ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa, ya gama gwagwarmayar samo soyayyar Hafsa da ƙyar, a lokacin da ya ke ƙoƙarin ya miƙa hannu ya kamota kuma, Mummy na ƙoƙarin shiga tsakani.

Hafsa kuwa cike da murna ta dinga bubbuɗa kayan da Khalil ya saya mata, turaruka da kayan kwalliya, sai kuma kwalin sabuwar waya mai tsadar gaske.
Ta dinga murna tana jujjuya wayar nan, tana yiwa Allah godiya ashe ita ma zata yi ta'amalli da kayan zamanin nan.

Vibrating ɗin wayarsa ce ya dawo shi daga tunanin da yake yi, ya kai idanunsa kan screen ɗin wayar yaga beauty. Ji yayi kamar kar ya ɗaga, amma ya miƙa hannu ya ɗauka cikin dakiya ya ce "Baby"

"Sweetheart, na gode sosai da sosai, Allah ya saka maka da alkhairi, waya na gani sabuwa dal har da layuka guda biyu, Allah ya ƙara maka lafiyar neman halal, Allah yaja kwanan mahaifanka, ya biya musu buƙatunsu na alkhairi ya kare su a duka in da suke,

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment