Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kar ka damu Baba insha Allah zan kawo maka ita lafiya".

"To shikenan Saminu, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi"

************

Yau Juma'a dan haka wankan hijjabi ta yi, pink tun daga sama har ƙasa, ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, ta shigo tana rataye da jakarta pink, hannunta riƙe da robar ruwa da mukullin motarta, bai san yadda aka yi ya shagala da kallonta ba, tayi kyau ƙarshe, ga wani irin sassanyan ƙamshi da take yi. Sai dai ta yi missing ɗin lectures ɗin farko da aka yi, dan suna takun saƙa da malamin, dan haka yau ba ta yi attending darasin sa ba, kuma darasin da yayi da lissafi a ciki, kuma ko da kai aka yi lissafin a ajin, abu ne mawuyaci mutum ya fahimta saboda yayi tsauri da yawa.

"Kai lafiya kar ka cinye ni dalla" tayi masa maganar cikin tsawa.

Sunkuyar da kansa ya yi daga kallonta, ya koma kallon wani wurin daban.

Class rep ne yayi dariya ya ce "Kai Fadila wannan tsawar haka?"

"To ya sani a gaba da kallo, sai na faɗi tukuna aikin banza".

Dariya ƙawayenta suka din ga yi, wata wadda ake cewa Amra ta ce "Kyau ki ka yi masa ko ustaz?"

Tsaki Fadila ta ja ta ce kwaji da shi.

Babu jimawa wani lecturer ya shigo, wanda ya basu class work ya ce su yi da waya, nan ya dinga yi musu mita ya ce "Ace gaba ɗaya ajin nan babu wanda ya fahimci tambayar da na yi sai mutum ɗaya, ina sane nace ku duba waya, dan na san idan har baku fahimci tambayar ba, babu yadda za ayi ku samo amsar. Waye Yazeed Hashim Shareef?".

"Sir" ya faɗa tare da ɗaga hannunsa sama.

Gaba ɗaya idanun mutan ajin suka dawo kansa.

"Wow, dama na gaya muku ustazan nan sune ƙwarin ajin, Malam Yazeed fito ka mana bayanin yadda ka fuskanci tambayar da na yi, har ka samu damar amsawa"

Yazeed ya fita gaban aji, ya ce "Sir zan iya yi da Hausa?".

"Yi da duk yaren da kafi iyawa"

Yazeed na haɗa ido da Fadeela ta ƙunshe baki tana sinne dariya, ta ɗan ɗaga murya ta ce "Sir gara yayi mana da hausar dai, da turancin nan bama ganewa"

Malamin bai kawo komai a ransa ba, ya yin da 'yan ajin suka gane me Fadila take nufi da faɗar hakan, su kai ta yi masa dariya.
Tun a nan ya rasa karsashin da zai yi bayanin, duk ya ji jikinsa yayi sanyi, amma ya daure ya aro jarumta, ya daidaita nutsuwarsa, cikin kamalarsa ta zance da iya sarrafa harshe, yayi bayanin yadda ya fuskanci tambayar da yadda ya bi amsa tambayar.

Malamin da kansa ya tafawa Yazeed ya ce "Weldone Ustaz, you are genius man, ka burgeni ƙwarai mutane masu sharp brain irinka ba su da yawa, Allah ya ƙara basira"

Yazeed ya ce "Thank you sir".

Malamin ya ce "Gaskiya duk ajin nan babu wanda ya amsa daidai sai Malam Yazeed, dan haka kowa yaje ya sake faɗaɗa bincike a kan bayanin da yayi, zan yi test a kansa, idan kuma kuna buƙata ku tuntuɓe shi yayi muku bayani sosai".

"Gaskiya mu dai Sir kai mana bayanin da kan ka" cewar Fadila.

"Meye baki gane ba a bayanin da yayi?".

"Ni ban gane komai ba" ta faɗa cike da rainin hankali.

"Well, zaki iya zuwa ki same shi ya yi miki bayani".

"A'a Sir gaskiya gara ka yi mana da kanka".

"Ba zan ba" ya bata amsa.

Tura baki tayi cike tsiwa da harare-harare.

"Leave my class" malamin ya faɗa yana nuna mata hanyar fita.

Kamar kullum, ta saɓi jakarta ta fice, tana fita ya kalli 'yan ajin ya ce "A ciro takarda, kowa ya rubuta attendence, attendance 30 marks, test 10 marks.

Takardar attendence ta fara zagawa, har ta zo kan Yazeed, ya kalli takardar attendance ya kalli wurin zaman Fadila, ya rubuta sunansa sannan ya rubuta Fadila Ahmad Musa.

Bayan kammala lectures, malamin ya ƙirga ɗaliban ajin, ya ga mutum ɗaya ya hau kai, aikuwa ransa ya ɓaci, ya ce "Waye ya rubutawa wani attendance? Kowaye ya faɗa kafin in binciko shi da kaina".

Yazeed ya miƙe tsaye cikin jin kunya ya ce "Ni ne Sir".

"Wa ka rubutawa?" Yayi shiru.

Malamin ya kalli Attendance ɗin ya ɗago ya kalli Yazeed ya ce "Yazeed Hashim Sharif, Faidla Ahmad Musa, da kai da ita kun rasa wannan 30mrks ɗin".

Tana ƙarasawa ƙaramar tashar garinsu, ta tarar an fara lodi, kasancewar fuskarta sanye da niƙabi ne, babu wanda ya gane wacece, ta samu wuri ta shimfiɗa ɗankwalinta ta yi sallar asuba, daga nan ta shiga motar da za ta kai ta babbar tashar ƙaramar hukumar su.
Gari da sauran duhu, haka suka ɗauko hanyar barin ƙauyensu, babu abin da Amina take a zuciyarta sai Addu'a, da fatan Allah ya kaita lafiya ba tare da kowa ya ganta ba.

Ƙarfe bakwai suka isa babbar tasha, ta shiga tambayar direbobin nan Saminu, tare da yi musu kwatancen sa, wasu suka ce ba su gane shi ba, wasu kuma suka ce sun gane shi, amma ya kwan biyu bai shigo tashar ba, ganin gari na cigaba da haske, ya sanya ta fara tsoron kar a biyo sawunta, dan haka ta shiga motar da ake lodin Kano!.

Haka tayi ta rarraba ido, kamar agola a rabon gado, tana kallon hanya, tare da mamakin manyan gine gine da tituna da ababan more rayuwa da suke shimfiɗe a maraya, yayin da ƙauyuka ko oho, banda yau da Allah ya sa ta fito maraya ta gani da idanunta, da sai ta ce ƙaryane a garin Kano babu irin wannan manyan ababan more rayuwar, duba da yadda rayuwar karkara take da wahala, saboda rashin isar da ayyuka yadda yakamata har karkarkara.

Sai da suka yi kusan tafiyar awanni biyu cir a mota, sannan suka iso babbar tashar mota ta kabuga da ke cikin ƙwaryar birnin Kano.

Ware idanunta tayi a kan manyan motocin da ke shiga suna fita a cikin tashar, wadda ta sha banban da tashar su ta ƙauye, sai a yanzu ta gane tayi wauta, ta ina zata fara neman Inda Baba yake? Ga Saminu ya ce mata yana Ikko, amma yau zai ƙaraso, to idan ya ƙaraso ina za shi? Nan Kano ko can gida? Gaba ɗaya ta rasa abin yi, ga jikinta babu daɗi, cikinta sai hautsunawa yake, saboda yunwa da kuma doguwar tafiyar da suka yi ta mota wadda ba ta saba ba. Ta samu can wani wuri a ƙarƙashin wata bishiya, ta rungume kayanta tayi zamanta tana kalle kalle.

Saminu kuwa cikin dare suka sauka, dan haka washegari da safe baccinsa ya kwanta ya sha hankali kwance saboda gajiyar tafiya. Sai wajen sha biyu saura ya tashi yayi wanka kasancewar juma'a ce, ya shirya dan ya fara biyawa ta gidansu Amina, ya sanar mata da saƙon Baba sannan ya ce ta shirya su haɗu a tasha washegari da safe, ba tare da sanin a ranar za a ɗaurawa Aminan Aure ba.

Ko da yaje gidansu Amina, sahsensu ya nufa ya tsaya a bakin ƙofa yayi salama, aka amsa masa tare da bashi izinin shiga. Sai dai yana shiga yayi tozali da Inno a zaune, idanunta sun yi jawur sun kumbura, sai ajiyar zuciya take yi, ga mata duk a zazzaune a kusa da ita.

Saminu ya ce "Subhanallah, babar Amina lafiya kuwa? Aminan ce ta rasu ko kuwa mai ya faru?".

Aikuwa Inno ta sake fashewa da kuka,maƙwabciyar su Inno ce ta iya cewa "Ka san yau za'a ɗaurawa Amina aure, har kafi anje an yi an gama komai yau ɗaurin Aure, an wayi gari an nemeta an rasa".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, an nemeta an rasa kamar yaya? Ba sai wani satin ɗaurin Auren ba?".

"A'a an dawo da shi yau, sai wayar gari aka yi babu Amina babu dalilinta a garin nan".

Saminu ya girgiza kai ya ce "Ta ina zan fara gayawa mahaifinta wannan mummunan labarin haka? Kunga illar Auren dole kenan".

"Wallahi Hanne ba ki isa ba, duk in da yarinyar nan ta shiga garin nan kin sani, Wallahi sai kin nemota dan ba zaki mayar da mu ƙananan mutane ba, yau ɗaurin Aurenta ace an nemeta an rasa, duk mun zagaye garin nan kowa yace bai ganta ba" Kawu Bala kenan, har wani irin yawu ne yake tsartuwa daga bakinsa, saboda azabar masifa da jaraba.

Inno kuwa ta sake fashewa da kuka, ita ba batun Auren ne ya dameta ba sanin in da Amina ta tafi ne ga bata da lafiya shi ne babban damuwata.

"Wallahi yau duk in da yarinyar nan take sai an nemota, ko gawarta aka tsinto a gidan Jarmai za a mata sutura, Wallahi Hanne ko ki fito da Amina, ko in je har birni in ɗauko miki 'yan doka su kama ki. Kuma bari kiji in gaya miki ko kuna so ko ba kwa so, ko tana nan ko bata nan sai an ɗaura mata Aure dan ubanta Hassan".

Saminu ya ce "Haba Baba Bala, a fara mayar da hankali wurin gano in da Amina ta shiga mana, wannan faɗan ai duk ba shi ne abun yi ba".

Aikuwa ya dawo da idonsa kan Saminu "Au munafuki Algungumi, ashe kana nan, bana raba ɗaya biyu da haɗin bakinka yarinyar nan ta gudu, dan na lura da take takenka, ance har tasha take zuwa wurinka".

"Me za ta je tasha ta yi mini, iyakacina da iyalan Malam Hassan saƙo ne su bani in kai masa ko ya bani in kawo musu, kaga tafiyata ba zaka ɓata mini suna ba, Babar Amina Allah ya bayyana ta" dag haka Saminu ya fice, yana jinjina lamarin mugunta na 'yan uwan mahaifin Amina, su b ta ɓatan yarinyar suke ba, ta yadda za a ɗaura kar sunan su ya ɓaci suke yi.

Malam Rabi'u Jarmai ne ya zo har gidansu Amina yana bala'i a kan idan har ba a ga Amina ba, a dawo masa da kuɗinsa, idan an ganta a san abun yi.

Kawu Bala ya dinga ba shi haƙuri ya ce "Haba Jarmai, ka kwantar da hankalinka za a ganta duk in da ta shiga, idan ma ba a ganta ba, za a ɗaura muku aure a haka, duk in da ta shiga da Aurenka a kanta idan ya so ds ta dawo sai a daƙumota a kaita gidanka".

Jaramai ya ce "Amma ka raina mini hankali, tana nan baku kula ba ta gudu saboda kun mayar da ni mahaukaci, sai a aura mini gaibu, ni ba zan yadda da wannan sagegeduwar ba, na baku daga nan zuwa ranar Lahadi, idan an ganta to idan ba a ganta ba, ku san yadda za kuyi ku sallame ni".

"Ke Fadila, jarida zazzafa" cewar Amra da ta samu Fadila a Cafeteria.

Fadila ta ce "Jaridar me fa?".

"Bayan fitar ki daga class, Mutumin nan ya ce ayi Attendance, 30mrks duk wanda baya nan babu shi a 30mrks ɗin nan, ba kawai sai gayen nan yayi miki ba"

"Wane gayen?".

"Wannan Zaidu yake ko Yazeed, wanda aka ce shi ya ci class work, aikuwa ya gano shi ya ce da ke da shi ba ku da 30mrks ɗin nan".

Fadila ta ja tsaki ta ce "To uban waye ya sashi yayi mini? Allah ya ƙara"

"Kai mutuniyar baki da dama, Allah ya ƙara ma zaki ce?".

"Idan ba Allah ya ƙara ba me zance? Ni muje class ɗin ma in ƙare masa ta tas kar ya sake mini shishshigi a lamurana".

Aikuwa Amra ta dinga zigata, suka nufi aji, suka tarar da shi yana wurin zamansa, yana motsa bakinsa a hankali da alama karatu yake yi.

"Kai wurinka na zo" Fadila ta yi maganar tana tsare shi da manyan idanunta.

Ya ɗago kai ya kalleta, ba tare da ya ce komai ba.

"Uban waye ya saka ka yi mini Attendance? Na ce maka ina buƙata ne? Ai ni malamin nan ya gama mini komai da kaima ya soke naka Attendance ɗin, uban shishshigi kawai" lumshe idanunsa yayi a hankali, ba tare da ya ɗago ba, balle ta sa ran zai tanka mata.

"Da kai nake magana fa"

"Wai ni?" Yayi Maganar yana kallonta.

"Au duk maganar da nake, baka ma san da kai nake ba saboda ka raina mini hankali?".

"Yi haƙuri" ya faɗa a taƙaice.

"Aikin banza kawai" ɗan murmushin gefen baki yayi, tare da kau da kansa gefe, dan tuni idanun sauran 'yan ajin ya dawo kansu.

Class rep ya ce "Haba babbar yarinya, duk ajin nan babu wanda ya tuna da ke ya yi miki Attendance sai shi, amma sai taimako ya zama faɗa?".

"Kaga saurara mini babu ruwanka da ni, ai ba da kai nake ba, na gaya masa ina buƙatar taimakonsa ne? Ya ji da tsummar rayuwarsa kan yayi tunanin shiga rayuwata ya taimaka mini".

"Dalla class rep ka daina shiga sabgar yarinyar nan, gaba ɗaya ba ta da kunya Wallahi" cewar wani matashi shima mai ji da kansa, wanda suke kira da Babson.

"Lokacin da aka raba kunyar ni ba a haifeni ba, idan an raba kana nan zaka iya ɗebar mini a taka".

Babson ya ce "Ni kike gayawa haka?".

"Na gaya maka ɗin waye kai? Banza useless"

Ganin Babson ya miƙe ya hayayyaƙowa Fadila, kuma bakin Fadila ya ƙi mutuwa, sai cigaba da tunzura Babson take.

Yazeed ya miƙe ya riƙe Babson ya ce "Ɗan uwana dan Allah kayi haƙuri ka ƙyaleta. Fadila ba mutuncinki bane ki dinga rigima da mutane mussaman maza, muryarki al'aura ce, sai ɗagata ki ke yi...

"Dalla yi mini shiru, ji yadda kake ambatar Sunana kamar kai ka raɗa mini, idan ba ka kiyayi shiga sabgata ba saina kwarfeka na bi ta kanka a gaban mutane"

Dariya jama'ar wurin suka fara, tana fama da kayan rama, kamar a busheta ta faɗi, amma ta kalli zabgegen namiji kamar Yazeed ta ce zata kwarfe shi.

Babson ya ce "Dan Allah ku ƙyaleni in tattaka wuyan yarinyar nan, in kawo ƙarshen fitsararta".

"Sai dai kayi ka kaɗai, ƙazami mai warin hammata kawai" ba dan Yazeed yana riƙe da Babson ba, da ba abin da zai hana ya yiwa Fadila mahangurɓa.

Baba sai kiran wayar Saminu yake, a kan batun tahowar su tare da Amina, Saminu ya tabattar masa da cewar Amina ta ɓata an nemeta an rasa.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" shi ne abin da Baba Hassan ya dinga maimaitawa, tare da dana sanin rashin zuwansa ƙauye akan lokaci, take ya fara dana sanin zaɓar aikin nan a kan zuwa ƙauye wurin tilon 'yar sa.
Gaba ɗaya Baba ya rasa abin yi, jikinsa banda rawa babu abin da yake, banɗaki ya fara zagawa yayi gudawar fargaba, sannan ya ɗauro alwala ya zo ya tada salla ya kaiwa Allah kukansa, sannan yayi tunanin mafita. Baba Hassan mutum ne mai matuƙar tawakalli, dan haka ba lallai ka karanto damuwar da yake ciki a halin yanzu.

"Baiwar Allah, ke tun safe na ga mota ta sauke ki, amma kin zo nan kin duƙunƙune a nan, lafiya kuwa?".

Amina da ke jin jiki ta kalli mutumin ta ce "Dan Allah a tashar nan kake?"

"Eh a nan nake".

"Dan Allah ka san wani Saminu, ɗan garin Shanono, direba ne shima"

Yayi shiru sannan yayi ajiyar zuciya ya ce "Gaskiya ban san shi ba, amma ke ina zaki je?"

"Wurin Babana na zo, kuma Saminun ne kawai ya san in da Baban yake".

"Idan ba zaki damu ba muje in baki masauki mana"

"Nace maka ina buƙatar masauki ne? Ka bari na gode kawai".

Amina na nan zaune ta ji ana cewa wani Sarkin tasha, miƙewa ta yi tabi bayan Sarkin tashar, zuwa wani Office da ya shiga, ba tare da ya san tana bin sa ba.

Yana ƙoƙarin zama ya ga Amina a tsaye a bakin ƙofar ofishin, ta zuba masa ido.

"Lafiya kuwa?".

"Dan Allah yayana tambaya nake"

"To Allah ya sa lafiya, ya sa kuma na sani"

"Dan Allah ka san Saminu direba, yana zuwa daga Shanono?".

"Ahh na san Saminu wani dogo baƙi, yana jan mota KIA?"

"Eh shi, dan Allah idan kana da lambar wayarsa ka kira mini shi"

"Eh ina da ita, amma ta sayarwa ce"

"To nawa ce?" Amina ta faɗa da mamaki.

"Eh, amma ba da kuɗi ba, ƙofar ofishin nan kawai zamu rufe, mintuna kaɗan sai in baki wayar ma kyauta".

Amina ta kalleshi tsaf tayi ajiyar zuciya, kawai ta juya ta bar wurin, tana tunanin wannan wane irin abu ne haka? Babu wanda zai iya yi maka alfarma a birni, sai ya nemi mutuncinka?.
"Da in koma gida a mini wannan Auren, gara in cigaba da yawo a nan" ta faɗa a fili. Ta koma in da ta bar kayanta ta yi alwala tayi sallar Azahar

Tana nan zaune, sai ga wanda ya fara yi mata magana da farko ya dawo wurinta, ya ce "Ke, na gane Saminun da kike nufi, ke 'yar uwassa ce?".

Amina ta jinjina masa kai, alamar eh.

"Ok bari in kira miki shi a waya" ya kira wayar Saminu ya bawa Amina.

"Saminu gani a tashar Kano, dan Allah ka gaya mini ina zan bi inje wurin Baba?".

"Amina, dama nan kika tafi, kin sa ana ta nemanki a gida?".

"Dan Allah ni dai ka taimaka mini, kuma kar ka gaya musu in da nake dan Allah".

"Shikenan, kwantar da hankalinki, kin ganni a hanya na kusa shigowa 1 21Kano, idan na shigo zan kai ki in da yake".

"Yawwa na gode sosai, Allah ya kawo ka lafiya"

Ta miƙawa mutumin wayarsa, tare da yi masa godiya, ta zauna tana jiran zuwan Saminu.
Mutumin nan ya zauna ya dinga yiwa Amina surutu, amma ko uhmm ba ta ce masa.

Sai bayan la'asar Sannan Saminu ya iso, wata irin ajiyar zuciya Amina ta dinga saukewa tana murmushi.

"Yi haƙuri Amina na barki kina jira, Amina wannan ramar da kika yi fa?"

Maimakon ta bashi amsa sai ta hau kuka, Saminu ya ce "Yi haƙuri, share hawayenki, nayi miki laifi nima dan ban gayawa Mahaifinki da wuri ba, kuma da na gaya masa dama cewa yayi in kai masa ke. Muje maza in kai ki"

Mutumin da ya kirawa Amina Saminu ya ce "To Amina ba sallama?" Shiru ta yi masa tana cigaba da share hawaye.

Saminu ya ɗaukar mata kayanta, ya sa a motarsa ta shiga, ya je ya sayo mata gurasa da nama da lemo ya bata, ta riƙe a hannunta amma ta kasa ci. Suna tafe yana bata labarin yadda gidansu ya hargitse, ita duk tausayin Inno ne yafi damunta.

Ko da suka shiga cikin unguwar tudun Yola, rukunin gidajen da Baba Hassan yake gadi, Amina ta saki baki, tana ganin gidaje tamkar a ɗauka a ci.

Da Saminu yayi parking ya ce mata sun zo, nan mamaki ya ƙara baibayeta, gate ɗin gidan ma kawai abin kallo ne.

Saminu ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin, amma ya ji shiru, ya tura ƙofar suka shiga, lokacin Baba Hassan na fitowa daga ɗakinsa na gadi, a guje Amina ta ruga da gudu ta nufi in da Baba yake ta riƙe hannunsa ta fashe da kuka.

Baba kasa Magana yayi, sai kallon Amina yake yana murmushi, shi dai a duniya ba abin da ya rage masa da yake ƙauna kamar Amina.

Saminu ya ƙaraso yayi masa bayanin komai, Baba Hassan ya dinga yi masa godiya, sannan ya ce dan Allah idan ya koma garinsu, ya haɗa shi da Inno a waya yayi mata bayani, amma bayan ita kar ya gayawa kowa abin da ya faru. Saminu ya tabbatar masa da zai yi hakan, daga nan suka yi sallama ya tafi.

Baba ya zauna Amina ta gaya masa duk abin da ya faru a ƙauye, ya jinjina kai shi kuma ya gaya mata yadda suka yi da Alhaji Ahmad.
Amina ta dinga murna jin batun cigaba da makaranta. Amma Baba ya ja mata kunne a kan yanayin mutanen gidan da halayarsu, A ƙuruciya ta Amina gani tayi ai dan wannan ai mai sauƙi ne.

Baba ya dinga jadadda mata "Sai kin yi haƙuri, rayuwar birni da ta karkara ba ɗaya bace, su mutane ne masu ƙyamar talaka ki iya kan ki, kiyi musu aikinsu su biya miki kuɗin Makaranta".

Amina sai murna take, ashe da rabon burinta zai cika a rayuwa.

Baba ya ce "Muje in gabatar da ke a wurin su".

Amina ta bi bayan Baba da kayanta a bagco, tana ta kalle-kalle, kamar zata faɗi.

Ya yin da Baba ke ta Addu'a Allah ya sa Amina ta shigo a sa'a, ta samu ta kammla makarantar Sakandire ɗin ta.

Ayshercool
08081012143

GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

P7

Tuni Amina ta manta da zazzaɓin da take fama da shi, dama na fargaba da damuwa ne, ita wancan Auren da ta baro ya fi komai yi mata daɗi, ga kuma wannan abin farinciki da ta zo ta riska, ba ta taɓa zaton abubuwa za su zo da sauƙi haka ba.
Har sun kai bakin ƙofar da zasu shiga cikin falon gidan, Baba ya tsaya ya kalli Amina ya ce "Uwata ina sake jadadda miki, sai kin yi haƙuri kin kauda kan ki, ki kwantar da hankalinki duk abin da suka ce ki yi, babu musu haka wanda suka ce ki bari, banda shishshigi ki zauna kiyi haƙuri mu samu ki kammala makarantar ki lafiya ƙalau".

Amina ta yi murmushi ta ce "Insha Allah Baba ba zan baka kunya ba, zan yi duk abin da kace" ya jinjina kai sanan ya tura ƙofar ya shiga da sallama.

Alhaji Ahmad ne kawai ya amsa, Hajiya Zainab kuwa na zaune, Fadila na kwance a kan cinyarta, tana kallon T.V.

Baba na gaba Amina na biye da shi, suka ƙarasa cikin falon, Amina ta zube har ƙasa ta gaida Alhaji Ahmad, ya amsa mata cikin mutuntawa.

Ta kalli Hajiya Zainab ita ma ta gaisheta, sai da ta yi mata kallon sama da ƙasa sannan ta ɗauke kanta ta amsa da ƙyar.

Alhaji Ahmad ya ce "wannan ce yarinyar taka?".

Baba ya ce "Eh ranka ya daɗe"

Alhaji Ahmad ya kalli Mummy ya ce "Madam, ga yarinyar da na yi miki magana ɗazu, 'yar wurin Malam Hassan, dan haka sai ku haɗata da masu aikinku ku nuna mata aikin da zata ringa yi. Sannan yanzu ana hutun makaranta ne, amma da zarar an koma Makaranta za'a kai ta makaranta insha Allah".

Baba ya ce "Na gode Ubangiji Allah ya ƙara Arziƙi".

Amina ma ta ce "Na gode Allah ya saka da alkhairi".

"Ba komai, ki nutsu ki mayar da hankali kiyi karatu da kyau kin ji ko?".

"Tom insha Allah na gode sosai".

Duk wannan abun Mummy da Fadila basu tofa ba, Baba Hassan ya gama godiyar sa ya tashi ya koma bakin gate in da yake aikinsa.

Amina na zaune tana jiran a bata masauki, amma babu wanda ya kuma kulata, sai ma cigaba da hirarsu da suka yi.

Kusan mintuna arba'in tana zaune, ga yunwa tana ji, gurasarta na cikin kayanta, tana so ta keɓe ta samu ta ci, amma ba wanda ya kuma saurararta.

Ba tsammani ta ji muryar Fadila tana kiran "Hajara"

Amina a ranta ta ce "Ji wata murya kamar aljana".

Hajara ta ƙaraso falon hannunta riƙe da duster, ta ce "Gani".

"Dan Allah kai yarinyar nan can wurinku, ta zo ta sanya mutane a gaba da kallo".

Sai yanzu Mama ta ce "Ki kaita ɗakin da Asabe ta bari, da safe zan mata orientation"

Hajara ta ce "to" ta kalli in da Amina take, yarinya ɗanya sharaf, tubarkallah baƙa ce mai kyau da ita, sai dai kayan jikinta zai tabattar maka da akwai rangwamen gata.

Hajara ta yi matamurmushi ta ce "Ta so muje ciki".

Amina ta ce "To bari in ɗakko takalmana a bakin ƙofa, kar wani ya samin".

Wani irin kallo Fadila ta yiwa Amina, jin abinda tace, Daddy kuwa murmushi kawai yayi.

Amina ta ɗakko takalmanta silifas ɗan madina mai zanen yatsu.

Hajara ta ɗaukar mata jakarta suka shiga ciki, Hajara ta buɗe wata ƙofa suka shiga wani falon.

Amina ta ce "Kai, sanyi sosai, naga lokacin bazara ne, amma sanyi sosai nan"

Hajara ta ce "Na'ura ce take sanyaya ɗakin ai"

Amina ta ce "Ok ita ce A.C air condition?" Hajara ta kalli Amina jin ta yi turanci ta ce "Eh ita ce".

Ta kai Amina ɗakin da Asabe ta bari, ɗan madaidaici ne da ƙatuwar katifa, akwai mudubi da banɗaki a cikin ɗakin.

Hajara ta ce "Ga ɗakin ki nan"

Amina ta zaro ido ta ce "Wannan duk ni kaɗai? Amma tare zamu dinga kwana a ɗakin ko?"

"A'a kowa da ɗakinsa, ga banɗaki nan bari in kawo miki sallaya ko zaki salla, bari in je kitchen in samo miki Abinci"

"To Na gode" bayan fitar Hajara, Amina ta dinga kallon ɗakin, ta leƙa banɗakin tas da shi.

'Allah sarki Inno, da na san haka zan samu komai a wadace da mun taho tare, wannan aljannar duniya haka?"

Ta shiga banɗakin, ta dinga taɓe- taɓe, Dan Amina akwai rawar kai wasu lokutan, hakan ne ya sanya take iya wasu abubuwan.

Ta yi alwala, ta yi sallar magariba, ta janyo kayanta tana ƙoƙarin ɗauko

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment