Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lalle.

"Ina wuni" ta faɗa a taƙaice.
Maimakon ya amsa mata sai ya shiga ɗaukarta hoto a wayarsa. Haɗe rai ta yi ta ce "Ka bari bana so".

"Tom na bari, kin yi mamakin ganina ko kya ce na fiye naci, ba laifina bane, laifin zuciyata ne". Hafsa ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta.

"Kin yi shiru, ashe biki kuke babu labari. Nayi mamaki da mama tace mini bikin ƙawarki ne, ashe kina da ƙawaye?".

Abinda ba ta taɓa yi masa ba tayi, murmushi wanda sai da dimples ɗinta da bai taɓa sanin tana da su ba suka lotsa.

A hankali ya furta masha Allah beautiful.

"Ina da ƙawaye mana, kana mini kallon bani da kirkin da zan yi ƙawaye ko? Babbar ƙawata ce tun muna yara muka tashi tare shiyasa na zo bikinta".

"Ashe ma bikin namu ne, duk da ba a gayyaceni ba muje, a bani wurin zama da Abinci daga Abuja nake ko gida banje ba Wallahi" ɗan zaro ido tayi dama ga idanun nata tubarkallah.

"Me yasa baka je ka huta ba?".

"Ganinki nake son yi" ta jinjina kai, ta shiga gaba ya bita a baya, wurin taron yayi kyau da tsari, ta sama masa wurin zama, tasa aka kawo masa Abinci da abubuwan sha.

"Shikenan ko kana buƙatar wani abun?".

"Eh ke nake buƙata a kusa da ni, ki zauna idan kika tafi ban san kowa ba, kar ace na zo gayyar soɗi. Ta ɗan murmusa kaɗan ta samu wuri ta zauna.

Ba kunya Khalil ya fara cin Abincin nan, duk da hakan ba ɗabi'arsa bace, cin kowane irin Abinci, kuma a gaban mutane, amma so yake Hafsa ta sake da shi, dan haka ya zage yana ziri.

"Allah ya nuna mana ranar bikinmu, muna kan high table kamar wannan couples ɗin, wane irin kaya zamu saka?"
Shiru tayi masa tare da ɗan taɓe baki.

"Hafsa meyasa ba kaya sona ne?" Yayi Maganar da dukkan nutsuwarsa.
Ta ɗauke kai tamkar ba ta ji abin da yace ba.

Ya kalli agogon hannunsa ya ce "Tashi muje in mayar da ke gida, tara saura yanzu".

"Dama jira nake ka gama, yanzu zan tafi nima".

"Na gama muje" ba tare da ko sallama ta tsaya ta yiwa Amaryar ba suka fito ita da Khalil.

Suna zuwa inda motarsa take ta ce "To ka gaida gida".

"Me kike nufi?"

"Zan hau Napep in tafi gida"

Khalil ya ce "Ke kin isa ma? Dan Allah kar muyi haka da ke" da ƙyar Khalil ya lallaɓata, ta amince ta shiga motarsa.

Suna cikin tafiya ta ce "Ina Yaya Abdul?"

"Yana nan, ko wurinsa ban je ba, sai Allah ya kaimu gobe, ya batun case ɗin nan kuwa, ina fatan dai bai kuma dawowa ba?"

"Eh bai sake ba"

"Ai ba dan Mama ba, da sai na sa an rufe mini shi Wallahi, in ga ƙaryar iskanci, amma naji ya ce "Shi ɗan uwanki ne ko?"

Shiru tayi ba tayi magana ba, Khalil ya kalleta ya ce "Ya naji kin yi shiru?".

Kawai sai ta fashe da kuka, irin kukan nan me taɓa zuciya da bayyanar da tsantsar damuwa da ma'abocin yinsa ke ciki.

Da sauri ya yi parking ɗin motar, ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri, ban san maganata zata ɓata miki rai ba, kiyi mini afuwa"

Sake rushewa tayi da kuka, tamkar zata shiɗe, wanda hakan ya sake ɗaga wa Khalil hankali, bai san lokacin da ya kai hannu ya ɗago fuskarta cikin damuwa ba "Dan Allah kiyi haƙuri" yayi Maganar a hankali yana share mata hawayen dake ta zubowa ba ƙaƙƙautawa daga cikin idonta.
Duk rarrashin da ya yi mata, bata yi shiru ba, sai da tayi mai isarta, sannan ta kalli Khalil ta ce "Mu tafi dare yana yi".

"Ai ba zan iya tuƙin ba, kin sani a zullumi, ina son sanin dalilin wannan kukan naki, da kuma dalilin da yasa ba kya sona, Hafsat ban miki bane ko ina da wani aibu".

Ta kashingiɗa da jikin seat, a hankali ta ce "Baka da wani aibu, hasali ma a karamcinka duk da halin ko in kula da nake yi maka, bai hana ka taimake ni ba, Amma meye amfanin fara son ka bayan a gaba na san zan iya samun tangarɗa a aikata hakan?"

"Wace irin tangarɗa? Ina sonki Hafsa"

Ɗago kai tayi ta kalli Khalil cikin rauni "Ina ganin hakan a idonka, amma... Sai kuma tayi shiru hawaye na zubowa daga idanunta.

"Akwai ƙaddarar da zata iya zame mana shamaki, bana son in fara sonka, wani abu yazo ya kawo mana tangarɗa, ka san wacece ni ka guje ni".

Khalil ya haɗa hannayensa ya ce "Dan Allah Hafsa, ni ba ruwana da wata ƙaddara in dai bata haramta mana aure ba a shari'a, Ina sonki, amma wace ƙaddara ce haka da kike tunanin zata zame mana shamaki da cikar burinmu, tunda ai kina sona ko?"



MASU BUƘATA DAGA FARKO, AKWAI A AREWABOOKS KO MANHAJAR WATPAD.
AYSHERCOOL
08081012143
https://arewabooks.com/chapter?id=638e2c023cc3212f4202c4d8


GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143

P17

Shiru Hafsa tayi, ba tayi magana ba.

Khalil ya ce "Yau Allah ya haɗani da gamona ni Ibrahim, Baby magana nake Please answer me" yayi Maganar yana kuma marairaicewa.

Kwaɓe fuska tayi kamar za tayi kuka "Ni ka ƙyaleni ko in yi kuka Subhanallah, ba ƙaramin narka zuciyar Khalil Hafsa tayi ba, saboda a rayuwarsa yana son shagwaɓaɓɓiyar mace.

"Kar ki yi kuka Please" yayi Maganar yana kwaiwayonta.

"Ni ba haka nake magana ba"

"To ya kike yi?" Yayi Maganar yana kallon in da take.

"Kaga muyi sauri, kar Mama taga na daɗe ta hanani zuwa na gobe in Allah ya kaimu".

"Allah ya sa ta hanaki zuwa" ya faɗa yana kunna motar.

"Allah ya sa ta hanani zuwa ko?" Ta maimaita tana leƙa fuskarsa.

"Eh mana, gaba ɗaya ma ni kishi ne ya ke damuna, duk an gama ganinki, ga mayafinma ba wani babba ba"

Kallon kanta tayi da mayafin, ta sake jan mayafin tana rufe jikinta.

"Me zaki rufe bayan an gama ganin komai?"

"Me aka gani?".

"Kyakywar surarki mana, shiyasa duk naji haushi ai" haɗe rai tayi, tana sake gyara zamanta.

Haka Khalil ya yi ta janta da hira, ga mamakin Khalil ashe Hafsa na magana sosai, duk a hirar tasu ma, idan ba ta ga dama ba, shiru take taƙi tanka masa, amma yau ta ɗan sake da shi.
Har ƙofar gida ya kaita, sannan ya kalleta ya ce "Babyna, yau zan kwana cikin farinciki, duk da ban samu amsar tambayar da nayi miki ba, amma naji daɗin kulani da kika yi, Ina sonki Hafsa" Hafsa ta ɗaga ido ta kalli Khalil, haka nan taji tana tausayinsa, tabbas ya nuna mata so, ko ga wannan sintirin da yake yi a kanta.

"Sai da safe, ka samu kaje gida ka huta, Allah ya kiyaye hanya".

"Ameen my love" ya furta a hankali, ta buɗe motar ta fita ta nufi gida, har ta shige gida, yana tsaye yana kallonta, sannan ya ja mota ya bar wurin.

Sai ƙarfe goma Sa'annan Khalil ya isa gida, Mummy ce ta rage ba ta kwanta ba, taji ana knocking ƙofar Falon taje ta buɗe, mamaki ne ya cikata da ta ga Khalil.
"Kai, saukar yaushe?".

"Yanzu Mummy".

"A wannan daren? Baka samu Flight ɗin yamma ba ne?".

Ya shiga cikin falon yana faɗin, a mota fa na dawo.

"What, mota kuma? Amma baka da hankali, da wani abu ya faru fa, yadda gari babu tsaro?".

"Ai ba abinda ya faru Mummy, baki bacci ba ashe?".

"Eh ban kwanta ba tukuna, bari in taso masu aikin can, su girka maka wani abun ka samu ka ci".

"No bana jin yunwa, a ƙoshe nake, na shigo ne ma kawai dan kusan na dawo, naga motar Daddy a waje yana gari ne?".

"Eh yana nan kusan sati guda kenan yana gari".

"Masha Allah, shikenan sai da safe"

"To Allah ya kaimu lafiya" ya fice daga falon ya nufi sashinsa.

Mama ta lura da yadda Hafsa ke murmushi lokaci lokaci, amma ba taji ta ce mata komai ba.

"Nace Khalil ya biki wurin bikin ne?".

Hafsa taji tambayar a bazata. "Eh yaje mun gaisa"

"Yazo nan nemanki ai, nace masa kina wurin biki" Hafsa tayi shiru tana cigaba da tuna yadda suka kasance yau, haka nan take jin nishaɗi itama a ranta, Khalil ya damu da ita sosai.

Bayan ta kwanta, ta shiga cikin abin rufarta, ta ɗau wayarta ta turawa Khalil saƙo kamar haka
   _*Ya kaje gida? Na gode sosai. Hafsat*_

Khalil yana ƙoƙarin saka wayarsa a silent ya kwanta, saƙon Hafsa ya shigo wayarsa, jujjuya saƙonya dinga yi yana murmushi. 'insha Allah sai kin zama tawa Hafsa'.

Ya yi mata reply da

*"Na koma lafiya, amma ai kamata yayi ki kirani kiji, mura fa ta kamani saboda sanyi na daɗe a waje"*_

Ta yi masa reply da "Subhanallah, Allah ya baka lafiya, Asuba ta gari".

Kissing ɗin screen ɗin wayar ya yi, ya kwanta, tare da ƙanƙame wayar a ƙirjinsa. Ya ƙudurce a ransa washegari zai jewa Abdul da labari me daɗi a kan Hafsa na daf da fara soyayya da shi.

Fadila har fargabar kwanciya bacci take, saboda babu wani abu da yake zuwa mafarkinta, Kamar yadda Sheikh Yazeed yake zuwa, abun har mamaki yake bata, gashi ta rasa wanda zata gayawa, kawai ta yanke shawarar washegari za taje gidansu Yusra ta bata labari, ko da wata shawara da zata iya bata.

Ba ƙaramin farinciki Alhaji Ahmad ya yi ba, da ganin Khalil, dan a wata shida sau ɗaya suka haɗu, tun bayan fara aikin Khalil, Alhaji Ahmad mutum ne mai son iyalinsa da kyautata musu, duk abin da suke so shi yake musu, baya son duk wani abu da zai taɓa masa su.
Yau gaba ɗaya sun haɗu a kan dining, suna karyawa, sai hira suke cikin nishaɗi da jin daɗi, tamkar basu da wata damuwa a rayuwarsu.
Amina ta kallesu sai taji sun burgeta, ita kuwa gidansu duk sun rarrabu, dan nemwa kansu mafita, sun baro Inno ita kaɗai a ƙauye cikin jarabar su Kawu Lawan, nan Baba yana gadi ita kuma tana aikatau, duk dan samun abin da zasu rufawa juna asiri.

"Ya Ubangiji Allah ka wadatamu, ka wadatamu da halal ka nesanta mu da haram, Allah ka sake haɗa kanmu a wuri guda cikin farinciki, Allah yasa sanadin karatu nan nawa, ya kawo canji a rayuwarmu" tayi Addu'ar a zuciyarta.

Haka ta jira suka kammala, ta kwashe kayan da suka ci Abincin, ta gyara wurin kamar ba ayi Komai a wurin ba.
Suka kuma komawa falo suka baje, suna ta hira da iyayen nasu. Daga bisani Alhaji Ahmad yayi musu sallama ya koma ɗakinsa, dan gabatar da wasu ayyuka.

Khalil ya yi shiru yana kallon hotunan da ya yiwa Hafsa jiya, duk da bata so ya yi mata hotunan, amma tayi kyau matuƙa, Kamar a saceta a gudu.
Mummy ce ta fizge wayar ta ce "Bani nan in ga abin da kake kallo haka ko ƙwsƙwaran motsi baka yi"

Mummy ta zubawa hoton Hafsa ido, ta kalli Khalil ta ce "Ita kuma wannan fa?"

Khalil ya yi shiru bai ce komai ba.

"Ko ita ce wadda kake so ɗin?".

Jin abin da Mummy ta ce, ya sanya Fadila tashi da sauri, ta karɓi wayar.

Ta kalli hoton Hafsa kwaɓe baki ta ce "Taɓ dan Allah kalleta ga kumatunta da ido kamar wata Philippines, ko ɗan murmushi babu a fuskarta gaskiya ka faɗo".

"Bani wayata dan ubanki, ta fi ki kyan gani dai".

"Wallahi na fita kyau, Dan Allah Bro dame wannan tafi Yusrana, amma ka watsa mini ƙasa a ido".

Haɗe rai Khalil yayi ya ce "zan tattakaki Wallahi".

Mummy ta ce "Kar kuyi mini faɗa ni, ita wannan ɗin a ina take? Kuma 'yar wanene?". Gaban Khalil ne yayi mummunar faɗuwa, shi kansa sai yanzu ya sake ankarewa akwai damuwa a soyayyar su. Miƙewa yayi ya kalli Mummy ya ce "We will talk later" yana gama maganar ya fice.

Fadila ta ce "Mummy, ke sai ki bari ya auri wannan mummunar?".

"Ke Fadila, kina taya Yusra kishi dai, amma ai ba ta da muni, ba laifi".

"Wallahi Mummy ba ta da wani kyau, kalleta fa wata 'yar lukuta da ita, ko fara'a babu a fuskarta Wallahi Mummy kar ki bari ya kwaso mana 'yar wahala".

"Barni da shi tukuna na ga iya gudun ruwansa".

Fadila ta miƙe ta ce "Mummy, a round 11 zan je wurin Yusra".

"Ok sai kin dawo"

Khalil kuwa bayan ya fita daga falon, ɗakinsa ya wuce, ya shirya don zuwa wurin Abdul su tattauna, a kan yadda suka yi da Hafsat a daren jiya.
Yana tafe a mota yana saƙe-saƙen yadda zai ɓullowa lamarin, amma shi babbar damuwarsa a yanzu shi ne ya tabattar da soyayyarsa a wurin Hafsat.

Fadila na gaban mudubi, tana shiri dan zuwa gidansu Yusra, wayarta ta fara ringing, ta janyo wayar da ke kan mudubi, ta ɗaga ta sakata a speaker, ta ajiye ta cigaba da abin da take yi.

"Assalamu alaikum warahmtullah" aka yi sallama daga cikin wayar.

"Wa'alaikum salam" ta amsa tare da yin shiru dan jin wanda ya kirata.

"Fadila Dutse ya kike?".

"Wake magana?".

"Ai kya amsa gaisuwar tawa da fari ko"

"Idan baka da abun yi ni ina da shi koma waye".

"Kankiya ne" ita gaba ɗaya ta manta da waye ma wani Kankiya, banda yanzu da ya kirata, maganganun Yazeed ne suka dawo mata, da ya gaya cewar sonta kankiya yake yi. Tsuke fuska tayi ta ce "Ina jinka"

"Ya kike ya hutun, hope kina jin daɗin hutun?"

"Sir ya aka yi ne, kace jarrabawata akwai matsala zaka kirani, kuma ka kirani kana tambayata wasu abubuwa daban"

"Eh, saboda ba saboda jarrabawa na kiraki a wannan karon ba, saboda inji lafiyarki ne"

"But you have no Business with that"

"Who told you so, nafi kowa buƙatar son sanin lafiyarki".

"Sir sai anjima, am busy now" ta katse kiran ta ajiye tana huci, tare da harar wayar.

Nan da nan ta kammala shirinta, ta ɗau mota ta nufi gidan su Yusra.

A ƙofar gidan su Abdul, Khalil yayi parking ɗin motar, kan ya fito sai da ya fara kiran Hafsa a waya, dan yaji ya take, a wannan karon yadda take amsa masa wayar ba ƙaramin daɗi yake masa ba.
"Ina kwana" bayan ta amsa salamarsa ta gaishe shi.

"Yau wace rana an gaishe ni" yayi maganar yana murmushi.

"Mhmm shi ne abin da ta iya cewa kawai".

"Kin tashi lafiya ya mamana?".

"Mama lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya mutan gidan? Ya jikin naka?"

"Kowa lafiya ƙalau, amma meya same ni?".

"Kace mini kana mura mana"

"Lallai kin fara damuwa dani, mura na warware Alhamdilillah, ina fatan kina lafiya ba wata matsala?"

"Ƙalau nake Alhamdilillah".

"To Masha Allah, zan shigo anjima insha Allah, da ƙarfe nawa zan zo?" Khalil yayi Maganar yana shafa sumar kansa.

"Idan an yi sallar isha'i, lokacin ne na dawo gida"

"To shikenan dear, me zan taho miki da shi?".

"Bakomai" ta bashi amsa.

"A'a nifa bana son haka, dan Allah ki gaya mini" yayi Maganar cikin shagwaɓa.

Dariya ya bawa Hafsa, "Wai shagwaɓa kake yi, gaskiya Mama na fama".

Dariyar shima yayi ya ce "Ai kuma kece yanzu zaki dinga faman, duk shagwaɓata ai ban kai ki ba, haka fa kike cewa malam ka rabu dani kar ka sake zuwa in da nake" ya yi yana kwaiwayonta in zata yi masa tsiwa.

Rufe fuska tayi kamar yana gabanta "Am sorry, kayi haƙuri na san na gaggaya maka maganganu marasa daɗi, ba halina bane bana son kowa ya matsi ratuwata ne" ta ƙarasa maganar a sanyaye.

"Na fahimta, kar ki damu sai na zo ki gaishe mini da Mama"

"Zata ji insha Allah" ya katse kiran, sannan ya fito daga motar.

" 'yar yarinya da wa kike wayane haka kike ta wannan fara'a?" Mama tayi maganar bayan ta shigo cikin ɗaki, Hafsa na kan katifa tana ta murmushi, shiru tayi tana ɗan mazewa ba ta zaci Mama na jiyo ta ba.

"Ya kika yi shiru, ko Khalil ne?" Hafsa ta gyaɗa mata kai.
Mama ta zauna a gefen katifar tana faɗin "Yauwa ko ke fa? Ki dinga sakar masa fuska, shi har abada wanda yace yana sonka ya gama yi maka komai"
A raunane Hafsa ta kalli Mama ta ce "Amma Mama...

"Shhh na san mai zaki ce Hafsa, ki kwantar da hankalinki, in dai da gaske Khalil yake sonki, na san ba zai gujeki dan ƙaddararki ba, nayi farinciki da shigowar wanda yake saki walwala rayuwarki, duk da halinki na miskilanci da taurin kai".

"Mama taurin kai kuma?".

"Eh taurin kai mana, ke baki san yadda kike da taurin kai ba, ai sai dai Allah ya shirya mink mini ke".

Hafsa kam shiru tayi tana tunani, tabbas ta fara jin Khalil a zuciyarta, dan ma tuntuni basar da shi take, amma Khalil ya haɗu ta kowane ɓangare amma tana tsoron tayi zurfi a sonsa ya san ko ita wacece, ya zo ya rabu da ita, kamar yadda ya faru da ita a baya.

"Girl, kince mini akwai Magana, kuma tun da kika zo kin yi shiru, yakamata muyi magana"
Fadila ta ɗan yi shiru tana kallon Yusra, sannan ta ce "Ai ke rainin hankali ne ya miki yawa, ina tsoron in gaya miki ki raina mini hankali"
Dariya Yusra tayi ta ce "Idan ma na raina miki hankali, ai mun saba kema kina mini, ina jinki".

"Zan gaya miki damuwata, idan kika gayan ba daɗi zan zage ki ne tsaf in tashi in tafi gida".

"Nima ina da bakin ramawa ai".

Fadila ta labartawa Yusra abin da ake ciki, game da mafarkin da take yawan yi a game da Yazeed, da kuma abin da Yazeed ya gaya mata a game da Kankiya.
Yusra ta ce "To sai me dan kina yawan mafarkinsa, kin sa shi a ranki ne, kuma kuna yawan haɗuwa a school shikenan".

Fadila ta ɗanyi tsaki ta ce "Ke ba kya gane abubuwa, ba fa Normal mafarki nake kawai in ganshi ba" Kan Fadila ta gama maganar, Yusra ta tuntsire da dariya.

"Ke nifa bana son iskanci, gayen nan ya taimakeni lokacin exams, duk da yadda na raina masa hankali, Wallahi idan ya zo kusa dani bana iya cewa komai, sai dai jikina yayita rawa, jikina yayi wani iri, inji kamar zan yi kuka, wasu hawaye su cika mini ido".
Me Yusra za tayi banda dariya, harda hawaye, dan sai da Fadila ta fara ƙuluwa, can Yusra ta ce "Ba faɗa da malam ba daren, yarinya ƙila zuwa yayi yai tsayuwar dare a kanki, saboda iskancin da kike masa, sai ki shiga hankalinki ai"

"Ban gane me kike nufi ba ai"

"Wataƙila Addu'a yayi miki yarinya, waye ya gaya miki ana ja da malamai?".

"Ke ni ki bani shawara kawai"

"To ni wace shawara zan baki? Tun da dai bani nake haɗaku a mafarkin ba, you need each other maybe shima yana mafarkin da ke, kin sashi a ranki ne kawai".

"Wai ya za ayi in sa shi a raina, a kan me zan a shi a raina? Ni shishsigin da yake mini ma haushi yake bani, dan dai kawai yana taimaka mini sosai ne".

Yusra ta ce "To ni yanzu me zance miki, idan ba damuwa ki kayi da shi ba, yawan mafarkinsa da kike alamane da yake nuna ruhinku na tare da juna, kuma jikinki na gaya miki yana buƙatar Aure, kuma ɗan ustazu yake so" tayi maganar tana dariya.
Haɗe rai Fadila tayi ta ce "Laifina ne da na zo wurinki"

"To idan ba haka ba, duk mazan duniya da wanda kike gani yau da kullum ba wanda kike gani sai shi, na fassara miki abin da kike buƙata kina jin haushi na. Meke saka miki rawar jiki dan kuna tare? Idan baki wasa ba, wataran sai dai kiga kin rungumeshi. Zahiri ki zata mafarki ne, shi zuciyarki da gangar jikinki ke buƙata"
Tsaki Fadila tayi, ta tashi ta ɗau jakarta ta ce "Sai kiyi da wata dan ubanki".

"Ubana ya gode matar Ustaz".

"Allah ya isa shegiya, kije dan kanki, Allah ya tsareni haɗa jiki da wannan yarom".

"Zaki ga yaro, Amma dai kin san ba ƙazami bane"
Banza Fadila tayi mata ta nufi hanyar fita.
Yusra ta ce "Amaryar Ustaz ko Kankiya, ranar Saturday ki aiko a karɓar miki chocolate cake zan yi" Ko waiwayowa Fadila ba tayi ba, ta yiwa maman su Yusra sallama ta fice.

Khalil ma cike da farinciki ya je wurin Abdul, sun sha hira sosai, yayin da Abdul ya ƙara bashi shawarwari tare da bashi ƙarfin gwiwa a kan yadda zai cigaba da neman Soyayar Hafsat.

Bayan sallar isha'i, Khalil ya sha kwalliya cikin cofee ɗin yadi mai laushi, ya sanya hula tare da feshe jikinsa da turare. Ya ɗau hanya ya nufi gidansu Hafsa.

A kan dandamalin ƙofar gidansu tayi musu shimfiɗa, ta kalleshi tana murmushi ta ce "Kayi kyau sosai"

"Ko baki faɗa ba ai ni mai kyau ne"

"To ai sai ka bari a faɗa, na ma janye ba kai kyau ba" Khalil yayi dariya ya ce "Daga baya kenan, ina Mama"

"Mama na ciki tana gaisheka" Hafsa ta kawo masa ruwa a Jug, suna hira yana sha, rabon da Khalil ya sha ruwan borehole har ya manta, sai dai ya sha na roba, amma ya sai gashi zaune yana ɗaɗɗakar ruwan borehole.
  Sosai ya dinga jan Hafsa da hira, yau kam ta biye masa sosai, ita kanta ta san ta samu farincikin da ta daɗe ba tayi ba.
"Hafsa kina sona?" Ya jefo mata tambayar. Gaba daya annurin fuskarta ya ɗauke, tayi shiru ba ta ce komai ba.
"Hafsa meyasa kike gudun amsa mini tambayar nan ne?".
"Saboda ƙaddarata"
"Mecece ƙaddarar taki gaya mini, zan fahimceki".
Ta share hawayen da suka fara zubo mata ta ce "Zan gaya maka idan ka sake dawowa, amsarka bayan jin mecece ƙaddarata ita zata amsa maka tambayar da kake mini na idan ina sonka"
"Ki gaya mini yanzu ko zan samu nutsuwa mana".
"A'a dare ya fara yi kuma ga sanyi, zan gaya maka insha Allah"
"Shikenan, jeki ki gayawa Mama zan shigo in gaisheta" Hafsa ta tashi ta tafi, shi kuna ya buɗe jug ɗin ruwan, ya zubar da sauran, ya ƙulle kuɗi a leda ya saka mata, dan ya san idan ya ce zai bata ba zata karɓa ba.

Ya shiga suka gaisa da Mama, Bayan ya fito Hafsa ta biyo shi da wata leda babba, ta bashi. Ya sa hannu ya karɓa ya ce "Ni kome kika bani karɓa zan yi, ni ba irinki bane"
"To ni ɗin ya nake?"
"Kin fini sani ai, ranar ai a kan 500 kika kusa yi mini tijara"
Murmushi Hafsa tayi ta ce "Baka da mantuwa ko?"
"Ina zan manta, sai da safe" yayi mata sallama sannan ya tafi gida, aikuwa a hanya Hafsa ta dinga kiransa a waya, ya san a kan kuɗin nan ne, dan haka yaƙi ɗagawa. Gaba ɗaya zuciyarsa ta tafi a kan son sanin ƙaddarar da ke cikin rayuwar Hafsa.

Da yaje gida a falo ya shigo da ledar, jin ledar da zafi tun lokacin da Hafsa ta bashi, ya san cewa abin ci ne a ciki.
Ya sa Amina ta kawo masa plate da cokali, Mummy sai binsa take da kallo, tana tambayarsa daga ina yake.
"Wurin Abdul" ya bata amsa.
Ya zazzage ledar, Awara ce fal, da miyar jajjage ga kabeji da cucumber fal a gefe. Murmushi yayi ya juye a kan plate ɗin, ya sa cokali ya fara ci"

"Me kake ci haka ne?" Mummy tayi maganar tana leƙa plate ɗin.

"Mummy awara ce fa" ya faɗa yana cigaba da ci.

Yamutsa fuska ta yi ta ce "Awara Khalil? Kaima ka fara irin wannan cimar yunwar? Meye haɗinka da wata awara?"

Khalil ya ce "Mummy amma naga Abinci ce itama, ta burgeni ne shi ne na saya".

"Duk Abincin da yake gidan nan ka rasa me zai burgeka sai awara? Me akayi a ka wata awara, wannan ƙazantar da ake sayarwa a bakin hanya, wato shi dai Abdul ɗin nan dole sai ya maida kai irinsa, shike koya maka duk wani halin ƙauyanci da shirme, yanzu idan cikin ka yayi ciwo fa?"

"Mummy ba Abdul ne ya sani saya ba, ni na saya da kuɗina fa".

"Tun da kake a gidan nan ka taɓa ganin an sa kuɗi an sai wanna abar? Saboda kalan yunwa da nemawa kai masifa shine kaje ka saya kana sawa a cikinka, baka san da yadda aka yi ta ba, ke zoki ɗauke wannan a bar kuje ku cinye ta" tayi maganar cikin tsawa tana kallon Amina.

Mamaki ne ya kama Amina, duk a kan awarar ake wannan tashin hankalin, wato idan ma abun mutuwa ne su suci su mutu kar ɗanta ya ci. Khalil yana ji yana gani, Amina ta ɗauke awarar kitchen ta kai awarar ta ce "Aikuwa ba zamu ci ba, shi ɗin ne zai cinye a barsa, wannan matar lamarin nata ya wuce tunani" Khalil yayi fushi ya bar Falon, dan ba ƙaramin daɗi awarar tayi masa ba, dan da gani ta musamman ce Hafsa tayi masa.
Ta ƙofar corridor Amina tabi, taje ta ƙwanƙwasawa Khalil ƙofa. Kamar ya share sai kuma ya buɗe.

Amina ta miƙa masa plate ta ce "Ga awararka nan na

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment