Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can cikin gidan ma, gurin iyalansu, sai a aiko taje a aiketa, ko a sata wani aiki mai wahala, duk dan a cuzguna mata a ɓata mata rai, abin duniya ya haɗu yayi mata yawa, gashi ba ta da waya balle ta kira Baba ta sanar da shi halin da take ciki, gashi su kawu sun matsa a kan lallai ko yana nan ko ba ya nan, sai sun siyar da gonarsa sun mata Aure.
Abin da yake ƙara mata damuwa shi ne, bayan aikin gadin nan, da ɗan gurin da suke zaune a cikin gidan nan, to da Allah suka dogara da Wannan gona kuma guda ɗaya tal, siyar da ita na nufin tozarta Mahaifin Amina ne.

"Amina, wai ke sai kin ɗorawa kan ki wata rashin lafiyar saboda wannan tunanin da kike, sannan hankalinki zai kwanta?"

Cikin damuwa Amina ta ce "Ba haka bane Inno? Tunanin ne yake zuwa ko ban shirya ba".

"Yo dama wani tunani ne zai tsaya jiran sai kin shirya? Na san ba zai wuce tunanin boko ba".

Amina ta girgiza kai ta ce "Inno ni na haƙura da karatun boko ma, ni yanzu auren nan nake tunani bana son Auren nan sam, sai kuma gonar Baba da zasu sayar, dan Allah Inno ki saka baki, su ƙyale mana gonarmu"

Buɗe baki Inno ta yi ta ce "Ni kaza! Rufamini asiri, kin san ko mahaifinki ba ya jayayya da maganar kawu Bala, balle ni 'yar karo da aka auro".

"To ko ni inje in same shi, in masa maganar?, bamu fa da Komai sai gonar nan, kuma ni wallahi ba zan yadda ayi mini wannan auren ba".

"Ke ki rufawa kanki asiri, kin ga Amina kiyi haƙuri ki runugumi Auren nan, tun kafin su yi miki wani sharrin, kin san kawu Bala da kaidi kamar mace"

"Aikuwa a aurawa wata ba dai ni ba, dan Wallahi da raina da lafiyata ba zan auri Wannan mutumin ba, mara imani wanda bai san darajar Aure ba, mata nawa ya mayar zaurawa, ya auri mace ya saketa ita da 'ya'yanta banda 'ya'yan da ke gidansa, duk kaka sai ya saki mata ya auri wasu haka kurum a kashe mini rayuwa".

"Rigimar ki tayi yawa Amina, ke ba a gaya miki gaskiya ki bi, amma ki rubutawa babanki wasiƙa a kai tasha, gara ya zo garin nan a san abun yi, ya san halin da ake ciki".

Amina ta yi murmushi ta ce "Ashe dai bokona na da muhimmanci Inno, amma ai baba bai iya karatu ba, wa zai karanta masa, ni nafi son muyi magana da shi a waya"

"To a ina zaki samo tarhon?"

Amina ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Ashirun gidan Jimmale kamar yana da waya".

"A'a ni kin san bana san alaƙa da wannan matar, yanzu sai kiji ƙananun maganganu".

Amina ta ce "to idan na tuna wata mafitar na gaya miki".

Inno ta ce "To shikenan".

************
Sai haki take ta rasa wace kwanciyar za ta yi, domin ta ji daɗi, komai ba ya mata daɗi, Hafsa na zaune a gefenta, tana ta jera mata sannu, tana yi mata fifita.

Cikin Muryar marasa lafiya Mama ta ce "Hafsa, ki tashi ki dafa ƙullin awarar can, kar yayi tsami".

Cikin damuwa Hafsa ta ce "Mama ba zan iya zuwa gurin suyar awarar nan ba, alhalin kina cikin yanayi na ciwo, ni yanzu hankalina ya koma kan yadda zan samo kuɗi mu tafi Asibiti".

"Haba Hafsa, jikina fa da sauƙi kece kike sanyawa kan ki damuwa, amma da sauƙi Alhamdilillah".

Cikin halayarta ta miskilanci Hafsa ta ce "Wannan nishin ma da kike duk cikin sauƙin ne? Kin ji yadda ki ke numfarfashi kuwa? Na san fa kina jin jiki sosai, ni dama ciwon ya dawo kaina in ga kina walwalar ki da lafiyarki".

"Auzubillah, haba Hafsa, sai kace wata mara imani, ni aka ce miki zan iya jurara ganinki cikin ciwo ne? Ki mini Addu'a kawai, Allah ya bani lafiya, kije gurin sana'arki, ko ba yawa ki samo wani abun, mu sai sabulun wanki". Da ƙyar Mama ta takura Hafsa, ta tashi ta fara kiciniyar haɗa kayan sana'ar, ba dan ranta yana so ba.

*****
Duk yadda ya so zuwa Makaranta da wuri, Allah bai yi ba, dan be samu ba sai da ya makara, yana zuwa tuni hall ya cika an fara gabatar da darasi.
Baya son zama a can baya, saboda baya ƙaunar zafi ko kaɗan. Wani space ya hango, dan haka cikin hanzari ya nufi gurin yana ƙoƙarin ɗosanawa ya zauna, tare da ciro wata 'yar jotter da ga aljihunsa.

"Kai meye haka a kusa dani zaka zauna dan ba ka da hankali?".

Cikin magiya ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri, ba kusa da ke zam zauna ba, gani na yi da sauran guri, dan Allah ki bari in zauna".

"Wallahi ba ka isa ba, kut haka kurum Wallahi ba za a kashe ni da warin hammata ba, ka nemi wani wurin". Ganin ta fara ɗaga murya har an fara kallonsu, ya sanya shi cire takalminsa a ƙasa ya zauna a kai.

"Kai ba gurin zama ne ka zauna a ƙasa?"Cewar malamin da ke darasi a lokacin.
"Malam bana son zaman baya ne, kuma na makara"

"Ba ka gudun ka ɓata kayan ka?".

"Ba komai, na karkaɗe".

Malamin yayi murmushi ya ce "kun ga irin wannan ustazan, da basu ɗau duniya da zafi ba, su ne ƙwarin aji they make it in life".

Fadila ta kalli uwar hular kan gayen nan, tashi ka fiye naci ce a kansa, saboda tsabar tsufa har zaren hular ya fara tashi, babu datti a jikinta, sai azabar tsufa, ya takure ƙafafunsa da suka yi busu-busu da ƙura, ya zauna akan takalmansa. Kamar kullum wata dariya Fadila ta kuma yi, tana cigaba da ƙare masa kallo ta ce "wai su ƙwarin aji manya" yana jinta, sai dai ko ɗagowa bai yi ba ya kalleta ba, ya cigaba da 'yan rubuce rubucen sa, duk da ba ya jin daɗin abin da yarinyar take masa.

Malamin ya cigaba da gudanar da darasinsa, sai da ya kusa kammalawa sannan ya bada damar tambaya, aikuwa ɗan ustazun nan ya ɗaga hannu, malamin ya bashi dama ya miƙe, ya fara tambayarsa sai dai da harshen turanci yake yi, kuma da alama turancin bai zauna a bakinsa ba, dan sai fama yake ya tattara yayi bayani yadda malamin zai fahimta.

Fadila ta ce "Wai turanci ya ga ta kansa, kai kuwa kayi da hausa mana tunda turancin baka iya ba" iya na kusa da su wanda suka ji mai ta ce, suka kwashe da dariya, wanda hakan ya sanya jikinsa yayi sanyi.
Malamin ya ce ya cigaba da tambayar, dan tambaya ce mai matuƙar mahimmanci, wadda za'a ƙaru da ita sosai, ya girgiza kai ya ce wa malamin ya gama tambayar.
  Aikuwa malamin ya dinga fashin baƙin tambayar nan, dan iliminne mai zaman kansa a cikin tambayar.

A ka kammala lectures, kowa ya fita sabgar gabansa, masu neman Abinci su siya da sauransu.
Fadila na tsaye a jikin motar ta ustaz ya zo wucewa, tana ganinsa ta tuna yadda ya dinga kokawa da turanci ɗazu a aji, aikuwa ta sake bushewa da dariya, yana jinta amma ya sake sunkuyar da kansa ƙasa ya wuce ba tare da ya ko ɗaga kai ya kalli in da take ba.

**********
Amina ta dawo daga siyan itace, ta shigo sashinsu taji kawu Bala yana yiwa Inno bayani, wai ranar juma'a Malam Rabi'u zai turo magabatansa, su kuma sun sanya gonar Baba a kasuwa, malam Rabi'u yace zai siyi gonar.
Jiki a sanyaye Amina ta ƙarasa ta ajiye itacen, ya mai da dubansa kan Amina ya ce "Au to faɗuwa ta zo daidai da zama, iyayen mijinki zasu kawo kuɗi ranar juma'a in Allah ya kaimu, kuma zai sai gonar mahaifinki ya siya ya bamu kuɗin mu yi miki kayan ɗaki".

"Amma baffa idan ka siyar da gonar baba, mai zamu dinga nomawa?".

"Rufen baki, mara kunya, ko shi Hassan ɗin ubanki bai isa in magana ya ce zai yi jayayya ba, ke kin je 'yan kwangilar yahudawa sun hure miki kunne har zan faɗa ki mayar ko? To na yanke hukunci na gama"
Shiru Amina tayi, zuciyarta na wani irin raɗaɗi, har ga Allah bata son a salwantar da 'yar gonar nan ta su, ga uwa uba wannan Auren da bata ƙaunarsa sam.

Bayan tafiyar Kawu Bala, Inno ta ce "Amina yanzu meye abin yi, ta yaya zamu samu mahaifinki balle a sanar masa da halin da a ke ciki?".

Amina ta ce "'Nima ban sani ba"

Inno ta ce "Ni dai bana son a sayar da gonar nan, kuma da idan sun sayar wata uwar arzikin zasu saya miki na kayan ɗakin da sauƙi, amma na san abin da Allah ya nufe su zasu saya miki, sauran su riƙe abun su".

Ita dai Amina ba tace komai ba, saboda takaici ya hanata Magana sam.

**********

Abun duniya ya isheta, duk yadda Ummanta ke nuna jikinta da sauƙi, amma ita hankalinta dai yafi kwanciya da ace sunje Asibiti an duba umman nata sosai, sai dai idan har suka ce za suyi jigilar zuwa Asibiti a dubata, to zasu shiga cikin jarinsu sosai, duk da haka ba yadda Hafsa ba tayi ba, a kan Umman ta amince su tafi Asibiti Allah ya kawo wata hanyar, amma Umman taƙi haka Hafsa ta ƙyaleta.
Hafa na zaune a bakin rariya, tana wankin waken awara, Umma ta kalleta ta ce "Yanzu Hafsa har yanzu shiru ko ba kowa?"

Sarai Hafsa ta gane abin da Umma ke nufi, amma tayi shiru taƙi amsawa.

"Nifa wannan miskilancin naki ne yake ƙular da ni, da ke fa nake Magana".

"Umma to me zance, kema fa kin san ba kowa ɗin".

"Ko a gurin sana'ar taki baki haɗu da kowa ba?"

"Umma kefa kike cewa in tsare mutuncina, ni da na fita sana'a ina ni ina kule kulen maza?".

"Ba haka nake nufi ba Hafsa, daidai gwargwado kina samun masu sonki, amma kin ƙi ki tsaida hankalinki, kuma ko wannan rashin fara'ar taki da haɗe rai, ya isa ya hana samarin kulaki".

Hafsa ta ce "Aikuwa su sha zamansu, dan ni ba su ne a gabana ba".

"Au haka ma zaki ce? Ai shikenan idan dangin ubanki suka kuma waiwayoki kya shiga hankalinki ai".

"Ai ba su da wani iko da ni, dan haka ba su da damar da zasu ɗaga mana hankali, har yanzu ban manta da wahalar da muka sha a hannunsu ba".

"Ki manta ɗin dai shine yafi alkhairi, dan akwai gaɓar da dole a neme su a rayuwarki, mussaman a gurin Aure, dan kin san dai ni ba zan aurar da ke ba ko?".

Shiru Hafsa tayi, dan ko zancen Mutanen nan ba ta ƙaunar ayi sam.

***********
"Daddy" ta faɗa da ƙarfi tana rungume shi, kamar wata 'yar yarinya.

"Fadila ke dai ba kya girma ko? Don't you know, that you are now a big girl?" Mutumin yayi Maganar yana murmushi.

Tura baki Fadila tayi ta ce "Daddy wannan karon ka daɗe da yawa, kuma mu kayi waya da kai jiya baka gaya mini zaka dawo ba".

"Eh dama nace bari in yi surprising ɗin ku ne kawai"

"Kamar yadda Yaya Khalil yayi mana kenan, sai ganinsa kawai muka yi a gida".

"Eh munyi waya, ya gaya mini yazo, na so in biya in ganshi ma, amma Allah bai nufa ba, ya school ɗin, dama Mum ɗinku tace mini kin fara zuwa".

"School gata nan so boring and frustrated".

"Da haka duk muka yi karatun, kawai ki maida hankali kiyi abin da ya kai ki, abin da duk baki gane ba, idan da wanda ya fiki ganewa ki zauna ya koya miki".

"Taɓ, salon a rainani ace mini daƙiƙiya, i better Google what ever i dont understand".

"But is not as accurate as what someone will guide and teach you, anyway i wil find someone to be assisting you at home after school" Cewar Alhaji Ahmad.

"A nice idea Daddy, thank you ina Mummy?"

"Nima ita nake jira, tana sashinta go and have some rest" Fadila ta miƙe tare da yasar da jakarta a nan falo ta wuce.

Hajara ce ta shigo tana kwashe kayan da Fadila ta zubar a falon, ta risuna ta gaida Alhaji Ahmad, hannu ya ɗaga mata tare da faɗin sannu kawai.

Hajiya Zainab ta fito cikin gayu, ta zauna kusa da maigidan nata tana ta kwarkwasa, kamar Amarya.

Fadila ce ta kuma fitowa ranta a ɓace, ta tarar da Hajara na gyaraa falo, cikin faɗa ta fara yiwa Hajara magana "Wace ta gyara mini ɗakina a cikinku?"

Hajara ta ce "Asabe ce"

"Wai wasu irin banzaye ne ku? Kira mini ita, yarinya sai daƙiƙancin tsiya, kira min ita".

Alhaji Ahmad ya ce "Yaya, mai ya faru ne?".

"Daddy na gaji da halin maids ɗin nan, sai ka yi ta maimaita musu abu ɗaya amma basa ganewa".

Mummy ta ce "Wallahi ni kaina ina mamakin rashin tunanin na yaran nan, kai ta maimaita magana basa ganewa".

Asabe ce ta ƙaraso ta ce "Gani".

"Eh gaki na ganki, wai jahilar ina ce ke? In ta maimaita magana ba kya ganewa, na gaya miki kar ki sake maimaita mini bedsheet, da na tashi a cire shi a wanke, na bar underwear a toilet, kin wanke banɗaki kawai amma baki wanke mini ba, ni kike jira inje School in dawo in wanke? Idan naki ne zaki bar su baki wanke ba? Ko da yake ku dama ƙazanta a jininku take".

Asabe ta duƙa ta ce "dan Allah ki yi haƙuri, Hajiya ce ta samu aiki, ayyukan sun yi yawa yau saboda dawowar Alhaji".

"Shut up I don't care malama, aikina na sani dana saki kiyi mini, idan ba zaki yi ba you can park your load and go back to your useless village, 'yar ƙauye mara ganewa kawai"

Tun ɗazu Hajiya Zainab suna falon, suna jin yadda 'yar su ke wannan zazzaga amma ba su tofa ba, sai yanzu Alhaji Ahmad ya ce "Easy Daughter, ai ta baki uzurinta, ke ki je kiyi mata aikin, and ke kuma 1ki daina yiwa mutane shouting haka ba daɗi".

"Daddy ni kaina ba jin daɗin shouting ɗin nan nake ba, suke sani Wallahi".

Haka Asabe ta wuce sashin Fadila ranta a matuƙar ɓace, da jin zafin cin zarafin da Fadila tayi mata.

Da sassafe, bayan kammala ayyukan gidan, iyalan na kan dining suna cin abinci.
Hajara ta tarar da Asabe tana ta haɗa kaya.
"Asabe wannan kayan da kike haɗawa fa?".

Asabe ta ce "Ƙauyenmu zan koma".

"Saboda me?"

"Ba zan iya jure zama ana cigaba da ci mini mutunci ba, na haƙura da aikin na nemi wani gurin".

"Haba Asabe, yanzu kan ki samu wani gidan aikin fa?".

"Allah ba zai hana ni ba, na gaji da cin mutuncin nan".

Hajara ta ce "Na shiga uku ni Hajara, Asabe idan kika tafi aiki da jarabar mutan gidan nan kashe ni zai a gidan nan".

"Allah ya baki yadda zaki, amma ni ba zan iya ba na gaji, zan iya wankawa yarinyar nan mari".

Asabe ta fito falo da kayanta, ta kuma gaishe da su, Alhaji Ahmad ne ma ya ɗan saki jiki ya amsa.

Asabe ta ce "Dama ina so zanje gida ne, ance mahaifiyata babu lafiya, zan je jinyarta bani da tabaccin zan dawo".

Mummy ta ce "To ki gaida gida"

Fadila ta ce "Allah raka taki gona" Asabe jiki a sanyaye ta miƙe, Alhaji Ahmad ya kirata, ya sa hannu a aljijunsa, ya ɗauko kuɗi masu yawa zai miƙawa Asabe.

Mummy ta yi caraf ta ce "Na meye kuma zaka bata wannan uban kuɗi haka? Naga an biyata kuɗin aikinta, wannan kuma na menene?".

Daddy ya ce "Ai wannan watan ya kai a biyasu, tun da  jibi in Allah ya kaimu zai mutu, kuma ai tayi aikin watan, gara a biyata kuɗin aikinta, kuma a bata na siyan magani, ai ko bakomai an moreta a gidan nan" ba dan Mummy ta so ba, ya bawa Asabe kuɗi kusan dubu sittin ya sallameta.

Hajara kuwa zullumi ta shiga da taradaddi, ta san duk wata wahala da ɗawainiyar gidan nan kanta zata dawo ita kaɗai, ga mutanen gidan da shegen sa aiki su kuma ga son jiki, in an bar 'yar aiki ta huta to fa dare ne yayi, suna su biyun ma da ya suka ƙare, balle yanzu sai ita kaɗai.

*********

"Yawwa Hanne, yau da Yamma Malam Rabi'u zai kawo kuɗin Auren Amina, duk da ina samun labarin yadda kike zigata take masa rashin mutunci, bata saurarsa to ki sani duk wani ƙulle ƙullenki da makircinki ba zai hana Auren nan ba".

Inno ta ce "Ni wani ƙulle ƙulle zan akan auren nan, ni da nake 'yar karere?" Tayi maganar cikin ladabi kuma a sanyaye.

Kawu Bala ya ce "Oho miki dai, kuma anwa gonar Hassan kuɗi, dubu ɗari uku, zai kawo kuɗin gonar da na Auren, sati biyu kawai za'a saka ba wata bidi'a za a tsaya yi ba".

Amina dake ta ƙoƙarin tuƙa tuwo ta zabura ta ce "Gonar baban ce dubu ɗari uku? Wallahi kawu cutarku zai yi gonar nan tafi haka".

"Zaki rufe mini baki ko sai na zo na danna kanki a murhun nan? Fitsararriya mara kunya ina Magana kin tsoma baki, naga uban da ya isa ya hana a siyar da gonar nan ayi auren nan" Amina ta sunkuyar da kai, ranta na mata ƙuna, Shikenan duk wata kadara da Baba ya mallaka an kaɗar da ita.

Albarkacin Asabe, ya sanya Alhaji Ahmad ya biya sauran ma'aikatan da ke gidansa kuɗaɗen albashinsu, duk da watan bai mutu ba. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa ma'aikatan ba, dan idan baya nan sai sabon wata ya kwan bakwai, matar gidan ba ta biyasu haƙƙoƙinsu ba.
Baba Hassan ji yake ina ma tun kan a rufe jarrabawar su Amina, aka biya albashin nan, da ko duka kuɗin ya kama zai bada albashin nasa ta biya jarrabawar.
Da yamma Baba Hassan ya nemi izini, ya tafi tasha in da su Saminu ke lodin can garin su Baba Hassan, Saminu ɗan garinsu ne, shi yake bawa duk wani saƙo da yake kai wa su Amina.
Kamar yadda ya saba yi, ya ɗan yi siyayyar kayan Abinci, da sabulun wanka da wanki da su man shafawa, ya ɗora kuɗin kashewa ya kaiwa Saminu tasha ya ce ya kai wa su Amina, ace musu yana nan tafe yazo ya gansu da ya samu lokaci.

Amina ta yi murna da ganin Saminu, dan har satar hanya tayi, da ƙafafuwanta ta tafi babbar tasha ta garinsu, tana neman Saminu amma baya nan. Sai gashi katsam ya kawo musu aike daga wurin Baba Hassan.

Bayan gama gaisawa da Inno da Amina, Amina ta gyara zama ta ce "Dan Allah ka kira mana Baba a waya, ina son Magana da shi".

Saminu ya ce "Sai dai wayar tawa babu kuɗi sosai, amma bari in jarraba kiransa a waya". Saminu ya kira wayar Baba Hassan, amma shiru ba ta shiga.

Saminu ya ce "Amina wayar ba ta shiga, idan da wani saƙo ne ki bani in kai masa".

Shiru Amina ta yi, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin zafi.

Inno ce ta ce "Hmm, ka sanar masa 'yan uwansa za su aurar da Amina ga Malam Rabi'u Jarmai, kuma zasu sayar da gonarsa su yi mata kayan ɗaki".

Saminu ya kalli Amina ya ce "Wace irin magana ce haka? Ina laifin su jira ya dawo? Kuma kamar ba su san halin Rabi'u Jarmai ba, karatun nata fa"

Inno ta ce "Kaga kar ka tunzurata, Aure ba laifi bane gallafirin da take a titi da sunan boko sam bai yi ba, amma wanda zasu haɗata da shi ɗin ne ba mutumin kirki ba ne"

Saminu ya jinjina kai ya kalli Amina da hawaye suka wanke mata fuska ya girgiza kai ya ce "Kiyi haƙuri Amina, insha Allah zan sanar wa da Baba Hassan ɗin, ki daina kuka".

Amina ta jinjina kai, tana ji a jikinta idan har Baba ya samu labari, wataƙila ya iya taimaka mata ta samu sassauci.

Su kayi sallama da Saminu ya tashi ya tafi.

Tun da Saminu ya tafi, jikin Amina yayi sanyi, tana tunanin ya Baba zai ji idan yaji ana shirin katse cikar burinsa a kanta, da kuma salwantar da 'yar gonar da ta rage ya mallaka.

Bayan tafiyar Saminu, Inno ta shirya ta fita, saura Amina kaɗai a gidan.

"Assalamu alaikum, wai ana sallama da Amina" cewar wani yaro da ya afko ba sallama.

Amina ta ce "Kai kar ka sake shigo mana gida ba sallama, kuma ka koma kace masa ba zan zo ba, ya san in da dare yayi masa"

Amina ta shige ɗaki abin ta, tamkar ba da ita ake sallama ba, sai da yayi kusan aike huɗu amma mirsisi ta ƙi fita. Allah ya taimaketa Inno ba ta nan, balle ta tursasata sai ta fita.

Amina na nan zaune, tana sake duba litattafanta na makarantar boko tana hawaye, ta ƙallafa ranta a kan karatu, ta ɗakko littafin da ake shigar mata da makinta na haddar Alqur'ani a makarantar boko. Ta haɗa kai da gwiwa ta din ga kuka, tana tunanin meye mafita, dan ko a ƙafa a ka ɗaura mata Malam Rabi'u Jarmai, sai ta gutsure ƙafar ta huta, amma ta yaya zata iya daƙile wannan Auren? Tana cikin kukan wani tunani ya faɗo mata, cikin hanzari ta miƙe tsaye. Sai dai murayar da ta jiyo ana kwaɗa sallama ce ta sanya gabanta ya faɗi, ta dafe ƙiji tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"!

Domin gyara sharhi ko shawara
08081012143

GABA DA GABANTA

Page 5

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Litatafaina na AƘIDATA DA RUƊIN ƘURUCIYA duk na kuɗi ne Please.

Ta taga Amina ta leƙa, sarai ta ɗau Muryar su waye, kasa amsa sallamar ta yi dan bata san da wani idon zata kallesu ba.

Yadda suke kwaɗa sallamar ba ƙaƙƙautawa ne ya sanyata amsawa, tare da fitowa daga cikinu ɗakin.

Kallo ɗaya ta yi musu gabanta ya faɗi, dan bata san da wacce suka zo ba, 'ya'yan Malam Rabi'u jarmai ne, wanda ƙawayen ta ne, sai dai su duk sun yi Aure, har da mai yara biyu, Iklima da Shema'u.

Amina ta ɓoye damuwarta ta ce "Shema'au sannunku da zuwa, ku shigo".

Iklima ta ce "Ji munafuka, mu shigo ina, algunguma ki rasa wanda zaki aura a garin nan dan rashin ta ido sai mahaifinmu, Wallahi kin ji kunya Amina".

Shema'u ta karɓa da "Ai zuwa mu ka yi mu ja miki kunne, Wallahi baki isa kiyi kishi da iyayenmu ba, gidanmu kamar kabari ne, Wallahi kika shiga azaba da wahala sai sun koreki da ƙafafuwan ki, gara tun wuri ki san abin yi".

Jiki a sanyaye Amina ta ce "Shema'u ku yi haƙuri, ni kai na ba son Auren nan nake ba Wallahi, kuma har yanzu ban ji a jikina zan iya Auren mahaifinku ba....

"Ba wani nan rufe mana baki, kwaɗayi ne ya sanya zaki auri baban mu ba wani abu ba".

Amina ta ce "Wallahi ba haka bane, ku tambaya ku ji Wallahi ni ba son mahaifinku nake ba".

"Yi mana shiru munafuka, har akwai yarinyar da ta isa ta ce ba ta son babanmu, zaki aure shi dan kwaɗayi,  an yi kwantai a gari an ƙare a hanyar boko, ba abin da bokon ta amfana miki, kin gama gantalinki za a liƙawa babanmu, Wallahi ki ka aure shi ƙannenmu sai sun illata ki".

Amina ta ce "Naga ina ta lallaɓa ku kun kasa ganewa, to bari in fito muku a yadda kuke so, ni bana son mahaifinku shine ya nace mini sai ya aure ni, sai wani ihun kwaɗayi kuke yi, meye a gidan naku kuɗin baban naku da ba ci ake ba, tuwo safe rana dare, miyar gidanku kamar ruwan tsarki, kullum a wahala kuke, ya auri wannan ya saki waccan, insha Allah babu abin da zai sa in Auri babanku iyayenku ma fama suke, ta kan su suke yi".

Shema'u ta ce "Kutt, baban namu kike gayawa haka?".

"An gaya masa ɗin, yayi zuciya ya daina mayar da 'ya'yan mutane dan yana da kuɗi".

"Gara namu uban an san aure yake yi yana saki, wayasan me naki uban yake aikatawa a birni".

"Bakomai tun da ba'a san me yake ba, naku uban kuwa kowa ya san me yake yi, me ake da mutumin da bai san martaba da darajar Aure ba" ganin Amina ta fisu baki ya sanya suka fita suna ƙananun maganganu.

Amina ta koma ɗaki tayi shiruu, tana tunanin mafita, tabbas ta san idan ta auri Malam Rabi'u kashinta ya bushe, dan a gidan nan babu kalar yaran da babu dan wasu daga manyan 'ya'yansa yayyen su Shema'u 'yan daba ne, ga uwar gidansa ita ce babbar masifaffiya, gidansa tuwo kwano uku zuwa biyar ake tuƙawa, idan ranar girkin ki ce ke zaki tuƙa wannan tuwo, sai a kwan uku ana cinsa.
"Kai ba zai yiwu ba, Wallahi ba zan yadda in auri wannan mutumin ba".

"Ke Amina, au zama ki ka yi

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment