Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan, sannan ya zaunar da ita, ya fuskanceta "Am sorry, na tafi ban kuma kiranki ba, bani da lafiya ne, baki ga na rame ba?"

"Na zata ba zaka dawo ba" ta faɗa cikin kuka.

"Baby me zai hana ni dawowa?"

Magana take son yi, amma ta kasa.

Khalil ya gyara zamansa ya ƙara matsawa kusa da ita ya ce "Ya isa haka dan Allah, so kike ki kuma sani a damuwa? Ki daina Please" da ƙyar ya samu ta sassauta kukan da take ta ce "Na zata ka daina sona ba zaka dawo ba, saboda abin da na gaya maka, ko kana ganin ƙarya nake yi".

"Haba Hafsa, Wallahi ba haka bane, labarinki ya tsma zuciyata to the extent tun da na bar wurinki bani da lafiya, sai yau na samu sauƙi. Ina da ƙanwa mace, mai rawar kan tsiya da tsiwa, sai dai idan makamanciyar ƙaddara irin taki ta sameta wani ya muzanta ta yaƙi aurenta, ko ya ce ƙarya ne abin da ya sameta bai mini adalci ba, Saboda na fi kowa sanin halinta, duk rashin jinta, tana da kamae mutuncinta, kwatankwacin yadda kike.
Meyasa zan ƙi dawowa gareki, dan wani abu da kika rasa a sanadin ƙaddara wanda ko ni ɗin ne na karɓe shi, iya na lokaci ɗaya ne, kyawawan ɗabi'unki da halayarki da su zan rayu tsawon rayuwata?.
Matasa da yawa bama yiwa kanmu adalci, wurin zubar da mutunci da ƙimarmu kan mallakar abin da Allah ya halarta mana na aure. Sai dai akwai tsautsayi da ƙaddara, abin da kika gaya mini na yarda ɗari bisa ɗari, kuma ni banji cewar zan iya rabuwa da ke saboda haka ba, ina son ki Hafsa, kuma ni aurenki zan yi, dan Allah ki daina wannan kukan"

"Dan Allah haryanzu kana sona?" Tayi maganar tana kallonsa.

Yayi mata murmushi ya ce "Ina sonki mana, kema kina sona?"

Murmushi take haɗe da hawaye ta ce "Na zata ba zaka dawo ba ka daina sona, shiyasa nayi ta kuka"

"Allah sarki Sweetheart ɗina, ni damuwa ce ta sani rashin lafiya, na kashe wayoyina, amma kina zuciyata am sorry for not hearing from me"

Hannayenta biyu ta haɗa a fuskarta ta cigaba da kuka.

"Babu ya isa haka mana, ki daina kukan nan mana"

"Kukan farinciki nake ka ƙyaleni"

Murmushi yayi ya ce "Dole ki kuka, Allah ya azurta ki da ɗan shawalwalin saurayi kamata, ɗan beauty da ni"

Murmushi tayi, duk da akwai hawaye kwance a fuskarta.

"Yanzu gaya mini, kina sona?"

"Sai nayi shawara" ta faɗa tana dariya, wadda ke ƙara mata kyau.

"Kin ma isa? Sai kin faɗa ai".

"Ina sonka Ibrahimul mu'azzam" ta faɗa tana kauda kanta gefe guda.

"Alhamdilillah, Masha Allah, bana jin ko Daddy da ya raɗa sunan nan, ya taɓa daɗi a bakinsa kamar yadda ya yi a naki bakin, Ibrahimul mu'azzam. Kai amma na sha gwagwarmaya kan in shawo kan wannan Japanese baeb ɗin"

"Nice Japaneese ɗin kuma?"

"Eh mana, My Japanese doll"
murmushi suka yi gaba ɗaya, Khalil ya dinga kwantar mata da hankali, da sake bata tabbacin iya wuya, zai aureta yana tare da soyayarta.
Suka kasance cikin nishaɗin da sai da ya wanke musu zukatansu daga dukkanin damuwowin da suke ciki.

Khalil ya nisa ya ce "Ina ga idan na sake dawowa, zan shigar da ƙarar dangin mahaifinki, in ɗaukar muku lawyer, a ƙwato muku hakkinku.

Hafsa ta girgiza kai ta ce "A'a, ni bana son duk wani abu da zai sake haɗamu da su, mun barwa Allah, wanda ya tara dukiyar ma yau yana ina? Allah ya karɓi abunsa, ni fatana Allah ya bamu mafita kawai"
"Allah sarki babyna, insha Allah very soon zan aureki, mu wuce wurin nan, sonake ai komai da komai a abinda bai wuce 6months ba"

Hafsa ta ce "Kai, yayi wuri da yawa ai".
"Ba wani wuri, amfanin soyayya aure, sai munyi aure za muyi soyayya ta gaske"
"Ni ban isa aure ba" ta faɗa a shagwaɓe.
"To ni na isa, ki bari idan muka yi auren, sai mu gani in dagaske baki isa auren ba" Jin Khalil zai ɓaro magana ya sanya ta ja bakinta ta tsuke.
  Kayan ciye-ciye ya bata, tare da bata saƙon gaisuwar sa zuwa ga Mama, ya yi mata sallama ya tafi.

Ba kowa a falo, sai Daddy yana ta aiki a computer, Amina ta hango hasken lantarki a falo, ta fito falon da nufin ta kashe wutar, ta tarar da Alhaji Ahmad yana ta aiki a kan system.
Komawa tayi kitchen, ta yayyanka fruit ƙanana, ta ha ɗa cofee, ta ɗoro a plate ta fito falon.

"Daddy sannu da aiki"
Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Yauwa sannunki"

Ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin a gabansa ta ce "Ga wannan naga kana ta aiki"

"Masha Allah, na gode sosai kuwa"

"Ba komai" ta juya zata koma ya ce "Yauwa, an kirani daga makarantarku ɗazu, sun ce kije ranar Saturday"

"Ok Allah ya kaimu, zan je insha Allah"

"Good".

"Gobe in Allah ya kaimu ma da wuri zaka fita?"

Daddy ya ce "Eh da wuri zan fita muna seminar ne"

"Ok, to shikenan sai da safe"

Ta juya ta nufi in da ɗakinta yake, ta ci karo da Hajara a tsaye tana binta da kallo.

Shareta Amina tayi ba tare da ta kula Hajara ba, ta wuce ɗakinta tare da faɗin "Kema Allah zai mini maganinki"




RUƊIN ƘURUCIYA

https://arewabooks.com/chapter?id=6220844388e1ec3a041032a8

_*ƘURUCIYA: Ita ce mataki mafi hatsari da kowane ɗan Adam yake tsallakewa kan ya zama babban mutum me cikakken hankali. Sai dai wannan mataki da ɗan Adam ke tsallakewa shekaru ne masu hatsarin gaske, idan ya wuce su lafiya ana saka masa ran samun kyakywar rayuwa zuwa tsufa, idan kuwa aka samu tangarɗa rayuwa ta samu tawaya zuwa tsufa. SHIN KE UWA CE? SHIN KINA CIKIN WANNAN MATAKI NA ƘIRUCIYA HAR YANZU, KO KUWA KAI NAMIJI NE KANA DA 'YAN UWA MATA?  Ya dace ki karanta wannan littafi. Rayuwar matasanmu a makarantun sakandare, hatsarin wasu al'adun bahaushe ga 'ya'yayensu mussaman mata, illar sangarta, Cutar depression, shaye-shayen matasan yara mussaman mata, dama abubuwa da baku yi zato ba, suna nan a cikin wannan littafi, ku garzaya manhajar Arewabooks don mallakar naku, ko ku kira wannan lambar don sayen naku a kan kuɗi ƙalilan 08081012143*_

Ayshercool.
08081012143
Ayshercool
GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

P22-23

Arewabooks Ayshercool7724

Amina ta shige ɗakinta, ta cigaba da saƙa da warwara a cikin ranta, daga bisani ta tashi ta hau gyaran kayanta, dan ba ta jin bacci sam, ita wannan hutun duk ya isheta so take ayi a koma makaranta.
  Kamar yadda Daddy ya gaya mata, ranar asabar ta shirya ta tafi makaranta, taje ta tarar Quiz ne aka yi musu, domin fitar da gwanayen da za'a tafi da su Abuja, wurin yin babban Quiz na ƙasa. Suka gabatar da quiz, da kuma mini exam da aka yi musu, wanda iyayensu suka je, suka karɓar musu results ɗinsu, Amina na ji tana gani, haka ta dawo gida ba a bata result ɗin ta ba, haka ta dawo gida duk ranta babu daɗi.

Khalil jinsa yake tamkar an masa bushara da wani abu na musamman, wata irin Soyayya da shaƙuwa ce suka shiga yi a tsakaninsa da Hafsa, a haka hutunsa ya ƙare, ya koma wurin aiki, cike da kewar Hafsa. Ya labartawa Abdul yadda yayi nasara, Hafsa ta karɓi soyayyarsa, Abdul ya taya shi murna sosai, sai dai a ransa yana tausayawa Khalil gwagwarmayar da zai sha da mahaifiyarsa kan ta amince.

Hutunsu Fadila ya ƙare, ji take tamkar ta ɗora hannu a ka tayi kuka, dan sam bata son stress da takurar makaranta.
Wannan semester da sabuwar mota dal ta koma school. Bayan ta ƙara kusan kwanaki uku a kan hutun nasu. Kwanaki ukun da ba ta zo ba, har an yi wasu lectures ɗin bata nan.

Haka kawai ta fara waige-waige a ajin, ko zata hango Yazid, amma sam ba ta ganshi ba, tana cikin tunanin ko shi ma bai dawo hutun bane, Kankiya ya shigo ajin. Yana shigowa ta haɗe rai, dan ko san ganinsa ba ta yi, tun da ta fara ganin zancen Yazid na daf da zama gaskiya, saboda yadda yake uzzura mata da saƙonni, da kuma kiran waya ba gaira babu dalili.
  Har kankiya yayi lectures ya gama yana satar kallon Fadila, da ba kowa ne ya san yana mata ba, sai ita ɗin da ya addabawa da ido.

Amina na zaune a gaban TV stand, tana gogews, aka turo ƙofar falo haɗi da sallama. Ta ɗaga kai tana amsa sallamar. Hajiya Turai ta gani a tsaye, ta gama ƙarewa Amina kallo daga sama har ƙasa, tana sanye da doguwar riga ta ɗaura ɗankwalin atamfar, kai ba ka ce 'yar aiki ba ce.
Ta ɗan taɓe baki ta ce "Hajiya Zainab na nan ne?"

Amina ta ɗan kalleta ta ce "Eh tana nan, ki zauna yanzu zata fito".

Hajiya Turai za tayi magana, sai ga Hajiya Zainab ta fito cikin shiri, da alama fita za tayi.

"Hajiya Turai, har kin ƙaraso?".

"Eh, yanzu na shigo ashe ma kin shirya"

"Wallahi kuwa, ai na san ba kya son jira, bari muyi mu tafi" ta mayar da hankalinta kan Amina ta ce "Ki kula mini da gida da kyau, ki kammala girki da wuri, bana son Fadila ta dawo ba a gama girki ba".

"To insha Allah" Amina ta faɗa cikin girmamawa.

"Wai ni kuwa Zainab, haka kika bar Yarinyar nan tana miki yawo a gida, ga mijinki ga ɗanki, ba zata dinga saka hijjabi ba, naga wancan zuwan da muka yi da hijjabi a jikinta, tafa fara girma kalli ƙirjinta a cike fam, kalli ƙugunta"

Amina a ranta ta ce "Ji 'yar bala'i har ta ga ƙirjina, ta rasa in da zata kalla sai nan, wannan ai iskanci ne, tubarkallah".

Mummy tayi wata dariyar ƙeta ta ce "lallai Turai kin manta wacece Zainab ne, Ai Alhaji Ahmad na riga na zame masa teku, na sha kansa ba yadda ya iya da ni, gidan nan daga ni sai 'ya'yana, da can bai ƙara aure ba sai yanzu da girma ya kama shi, Khalil kuwa shima ya san bai isa ya kawo mini jinin babu cikin zuriyata ba"
Sukayi dariya tare da yin shewa suka fice. Kwaɓe baki Amina tayi, ta cigaba da aikinta a ranta ta ce "Ko ni me zanci da dattijo ma oho, in banda tsautsayi wa zai auri jinin wannan matar ko ya auri mijinta, bala'inta ya ishi mutum?'
ƙarshe dai Amina ta manta da batun Hajiya Zainab, ta fara tilawarta tana yi tana aikinta.
  Ta kammala goge gogenta, ta miƙe zata bar wurin, tayi ido huɗu da Alhaji Ahmad, da ke tsaye yana kallonta.
Shan jinin jikinta tayi kamar mara gaskiya, ta ɗan diririce, dan sam ba ta zata yana gidan ba.
"Ina kwana" ta furta tana kauda kanta gefe.

Bai amsa mata ba ya ce "Kawon breakfast"

"Ai ban san kana gida ba, an cinye komai sai dai in wani abun zan dafa maka"

"No, haɗo mini coffee kawai, ina da biscuit sai in haɗa" yana gama maganar ya juya ya bar wurin.

Mamaki ne ya kamata, babban mutum kamar wannan ya ce zai karya da biscuit.
Kitchen ta nufa, cikin azama ta fara feraye dankali.
Hajara ta shigo kitchen ɗin ta sameta tana gyara dankali.
"Amina me kuma zaki da dankali?"

"Babansu Fadila ashe yana gida, hajiya ba ta yi mana bayani ba, ba a yi breakfast da shi ba, shi ne nake haɗa masa"
"Yayi" shi ne abin da Hajara ta ce ta bar kitchen ɗin.
Nan da nan Amina, ta dafa tea da dankali, ta haɗa a tray ta tafi kai masa, sai dai ta shiga tunanin ina zata kai masa?. Ta yanke shawarar kai masa kan dining, taje ta ajiye ta cigaba da sabgoginta, sai kuma ta tuna ba yadda za ayi ya san ta kai masa, idan ba gaya masa tayi ba.

Cike da faɗuwar gaba, ta nufi part ɗinsa, ta shiga da sallama, yana zaune a falonsa yana kallon labarai. Bai waiwayo ba ya amsa mata.
Cikin ladabi ta ce "Ga Abincin can a kan dining".

"Kawo min nan" ya faɗa a taƙaice. Amina ta ɗan yamutsa fuska ta koma falo, tana mitar Alhaji Ahmad ya fiye mulki, sai dai shi baya wulaƙanci kamar matarsa da 'ya'yansa, sai dai miskili ne na gaske.

Da sallama ta koma falon, taje gabansa da tray a hannu ta tsaya, ta kalli kan Centre table ya miƙe ƙafafuwansa a kai, ta wuce Kan dining ɗin dake falon, ta ajiye masa. Har ta juya zata fita a hankali ya ce "Nan zaki kawo mini"
Amina ba ta san lokacin da tura baki ba, ta sake ɗauko trayn ta dawo gabansa, ta kalli ƙafafuwansa dake kan Centre table, in da yakamata ace ta ajiye kayan Abincin.
"To a ina zan ajiye?" Tayi maganar tana satar kallonsa, dan ba ƙaramin kwarjini yake da shi ba.
Shareta yayi, ya cigaba da latsa remote ɗinsa.
Ta ajiye a saman carfet, ta juya zata fita "Zo nan" ya faɗa ba tare da ya kalli in da take ba. Ta dawo ta tsaya.
Ya sauke ƙafafuwansa daga kan Centre table ɗin, yayi mata nuni da ido, a kan a nan zata ajiye masa Abincin.
Kamar Amina ta fasa ihu, dan ta ƙulu sosai, haka ta ɗau tray ɗin ta ajiye a kan table.

"Come back in the next 30minutes" ya faɗa yana gyara zamansa.

Amina ta bar falon tana "yau naga tsiya da wasali, da iko da mulkin mulaka'u na masu kuɗi, a haka kamar na Allah ashe shima ya iya tsiya, aikuwa ba zan koma ba" ta leƙa ɗakin Hajara ta ce "Mai gidan nan ya ce kije nan da mintuna talatin"

Hajara ta zare ido, ita a zamanta a gidan nan banda gaisuwa ba abin da yake haɗata da Alhaji Ahmad, ko aiki baya sata, me zai sa ya ce ta je?

"Amina  nayi laifi ne?"

"Nima ban sani ba, ya ce dai kije"

A rikice Hajara ta ce "Na shiga uku Allah ya sa ba korata zai yi ba ni Hajara"

Amina ta koma ɗaki abin ta, yayin da Hajara ta tasa agogo tana lissafin mintuna talatin cikin zullumin rashin sanin dalilin kiran da mai gidan yake mata.
Sai da Hajara tayi Addu'oi sosai sannan ta tunkari sashin Alhaji Ahmad.
Tayi sallama ya amsa mata, ta ƙarasa ta shiga falon, ta zube a ƙasa ta ce "Alhaji gani, Amina ta ce kana kirana".
Da mamaki ya kalli Hajara ya ce "Ni kuma?"

"Eh haka ta ce mini, tun ɗazu ta ce bayan mintuna talatin kana kirana" ya ɗan yi shiru tare da jinjina kai ya kalli Hajara ya ce "Kirawo mini ita" Hajara ta koma ta kirawo Amina, sai dai bata ɗakinta, sai da tai ta dubawa ta ganota a ɗakin Fadila tana gyara mata.
Nan Hajara ta isar mata da saƙon Alhaji Ahmad na kiranta da ya yi. Sai kuma a lokacin ita ma cikinta ya ɗuri ruwa, sumi-sumi tabi bayan Hajara suka koma falon Alhaji Ahmad. Ya kalli Hajara ya ce "zaki iya tafiya"

Sai a lokacin Amina ta ga tayi wauta, ya mayar da hankali ya cigaba da kallon TV, tamkar bai san da wanzuwar Amina a wurin ba.
Amina tun tana sanya ran zai kulata, har ta sare gashi ta gaji da tsayuwa, ya ɗago ya kalleta, yayi mata alama da ta je gabansa. Ba musu ta je in da yayi mata nuni. "In zauna?" Ta faɗa a raunane.

Ya ɗaga manyan idanunsa masu matuƙar haske da kwarjina, ya tsareta da idanunsa ya ce "Na ce ki dawo in the next 30minutes, amma kin turo mini wata, kin kyauta kenan? Ko kuma kin san dalilin kiran?"

Amina ta ɗaga kai ta kalleshi, amma tayi saurin janye idanuwanta ta ce "Dan Allah kayi haƙuri, nima sai da ga baya na ga nayi laifi, kayi haƙuri"

"Kwashe kwanukan nan, kije ki dawo, ko bana falon ki jirani" ta amsa masa da to, ta kwashe kwanukan ta fita sai dai tana zuwa kitchen ta tarar Hajara na tsaye na jiran dawowar ta.

"Amina me ya ce miki? Naga kin daɗe" haɗe rai Amina tayi tana tura baki taƙi kula Hajara, ta lura kwanakin Hajara ta koyi munafunci da sanya ido.
Ko da ta koma Alhaji Ahmad baya falon, dan haka ta zauna a kan carfet tana jiransa, dan bata manta kashedin Hajiya Zainab ba a game da zaman kan kujera ba.

Ta daɗe a zaune, sai ga Alhaji Ahmad ya fito, sanye cikin wani baƙin yadi, ya haska yadin kasancewarsa fari, sai zuba ƙamshi yake yi. Yaje ya buɗe wata drower ya tako in da Amina take, wadda tuni ta miƙe tsaye, ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ranar Sunday in Allah ya kaimu, zani wani ɗaurin Aure haɗeja, ƙarfe shida da rabi zan fita, a ɗan sama mini abin da zan ci kan in tafi"
Kamar mara gaskiya Amina ta sunkuyar da kai ta ce "To, insha Allah"

"Karɓi nan" Ya miƙa mata envelope ɗin hannunsa. Ta ɗago ta kalleshi sannan ta kalli envelope ɗin, amma ta kasa karɓa.

"Karɓi mana" yayi Maganar yana sake miƙa mata.
Jiki a sanyaye ta sa hannu ta karɓa, ganin tambarin makarantarsu a jiki ne, ya sanya hankalinta ya ɗan kwanta.

"Buɗe da sauri, zan fita" jiki na rawa Amina ta fara kokowa da envelope ɗin, tana ganin takarda ta san result ne, aikuwa gabanta ya faɗi, hannunta ya hau rawa.

"Ko ba kiyi abin Arziƙi bane, kika tsorata haka?" Bata san lokacin da ta ɗaga masa kai ba alamar eh.

"To ciro mu gani" ya faɗa yana cigaba da tsareta da ido.

Ta zaro paper, ta shiga dubawa duk grades ɗinta A ne, First position ta gani a jiki. Wani irin farinciki mara misaltuwa ya ziyarci zuciyarta, ta ɗago ta kalli Alhaji Ahmad fuskarta ɗauke da murmushi, ga hawaye a lokaci guda na farinciki da suka zubo mata a kan fuskarta, a kan gwiwarta ta zube ƙasa tana kallonsa.

"Yadda ka faranta mini, ta hanyar maida ni makaranta, Ubangiji Allah ya faranta maka, ya sa ranar alkiyama ka karɓi littafinka a hannun dama" har cikin kansa addu'a da tayi masa ta tsirga masa.
"Ameen ya Allah, Na gode tashi tsaye"
A hankali ta miƙe tana cigaba da share hawayen fuskarta.

"Makarantarku sun kirani, naje na karɓo result ɗin ki, nayi farinciki sosai da yabon da suke miki, na ƙoƙari da jajircewa, sai dai an ce ba kya jin magana haka ne?" Amina ta sunkuyar da kai alamar a'a.

"Ya zaki ce a'a bayan nima kinyi na gani"

"Dan Allah kayi haƙuri na daina, kar ka gayawa Baba"

"Anyway, an sanar da ni cewar kin ci wannan jarrabawar da suka yi muku, 15th December in Allah ya kaimu, zaku je Abuja, wurin baban Quiz na ƙasa da sauran festival da ake yi na makarantu, zasu fara yi muku lessons na mussaman"
Amina ta ɗan yi jimm, da ta san abu ne mawuyaci Baba ya barta taje Abuja, amma ta dake tayi murmushi ta ce "Allah ya kaimu, na gode sosai Allah ya ƙara buɗi yasa ka fi haka, inje in nunawa Baba result ɗin?" Ya jinjina mata kai. Ta juya da sauri ta bar falon.

A harabar gidan ta tarar da Baba da Zakiru direban Alhaji Ahmad, suna hira, da fara'arta ta tunkaresu, ta miƙawa Baba takardar hannunta.
Ya karɓa tare da kallonta ya ce "Uwata menene wannan?"

"Baba sakamakon jarrabawata ne, ka duba ka gani".

"To ai kin san sai dai ki karanto mini".

"Baba ta ɗaya na zo, duk ajinmu na fi kowa maki"

Baba ya faɗaɗa murmushinsa yana faɗin "Alhamdilillah, dama na san uwata ba zata bani kunya ba"
Zakiru ya karɓi result ɗin yan dubawa, ya murmusa ya ce "Baba Hassan lallai wannan 'yar taka ƙwaruwa ce, Allah ya dafa 'yar gidan Babanta"
Amina tayi murmushi ta ce "Amin Malam Zakiru na gode sosai, ka mini alƙawarin cigaba da koya mini karatun addini, amma haryanzu ka ƙi saka lokaci"

Zakiru ya ce "Ba ƙi nayi ba Amina, kinga yanayin aikin namu, wasu lokutan nike kai Alhaji duk in da za shi, idan ba haka ba kuwa gyaran harabar gidan nan kaɗai da aike ta isa ɓata lokaci. Kuma da zarar sun ga muna karatun nan za'a iya tsiro wani abu daban, amma insha Allah zan saka mana lokaci"

"To shikenan, na gode sosai"

Alhaji Ahmad ne ya fito harabar gidan, Zakiru ya nufi in da motarsa take, dan shi zai fita da shi. Baba kuwa ya nufi Alhaji Ahmad, ya cigaba da yi masa Addu'a da godiya.
Alhaji Ahmad ya ce "Ba komai, ai ɗa na kowa ne, naji daɗi sosai kaga zan cigaba da samun ƙwarin gwiwar biyan kuɗin makarantar, tun da tana abin da ake so"
Baba ya ce "Haka ne, Allah Ya ƙara arziƙi"
Ya amsa da Ameen ya nufi mota.

Yau da azahar Fadila ta dawo gida, duk da Sir Kankiya yayi ƙoƙarin ganawa da Fadila a Office ɗinsa, dan har ya tura mata saƙo yana son ganinta a Office ɗin sa, amma ta share tayi tafiyarta, dan zuciyarta raya mata take taje ta tatala masa rashin mutunci, dan ta fara gajiya da takurar  da yake mata.
Haka nan take mamakin meye ya hana Yazid dawowa Makaranta.

Amina tayi farinciki sosai da sakamakon ta na makaranta, ta fara ƙoƙarin cigaba da hora kanta a kan darrussan kimiyya, tun kan a neme su a makaranta, a fara yi musu lesson.
Amina ta rage jin haushin Alhaji Ahmad a kan abin da iyalansa suke mata da kuma shima abin da yayi mata.
Ranar lahadi tun da ta idar da sallar Asubahi bata koma ba, ranar lahadi da su da masu gidan basu fiye tashi da wuri ba, saboda ba wanda yake fita a ranar.
Amina ita kaɗai ce idonta biyu, ta ɗora girki saboda Alhaji Ahmad zai fita.
Kan ƙarfe shida da rabi, Amina ta kammala girkin, har ta tsaftace falo ta kukkuna turaren wuta.
Tana ta sake goge kan dining, sai hamma take, saboda baccin da take ji.

"Sannu da aiki" ta jiyo muryarsa.
da sauri ta waiwaya, ta kalli in da yake tsaye "Ina kwana" ta faɗa tana ɗan lumshe ido. Maimakon ya amsa sai ya kuma maimaita mata "Sannu da aiki".

Ta fuskanci baya son yayi magana a share, dan haka ta ce "Yauwa na gode, ga breakfast ɗin".

Alhaji Ahmad ya ƙarasa ya zauna, ya kalleta ya ce "Afuwan na katse miki bacci" ta ɗan girgiza kai ta ce "Bakomai"
Ya bubbuɗe flask ɗin, yayi mamakin ganin ƙosai da soyayyen dankalin Hausa, da kuma koko.

Kawai sai ta ga murmushi ya mamaye fuskarsa. "Ke kika yi girkin nan?" Haka nan Amina ta tsinci kanta da tura baki, to wa yayi idan ba ita ba, saboda kawai ya raina mata hankali yake tambayarta.

"Hajiya am talking to you"

"Eh nina girka"

Ya jinjina kai, ya zuzzuba ya fara ci, yaji daɗin girkin nan sosai, yana son Abincin gargajiya sosai da sosai, amma sam Hajiya Zainab bata so, gashi na wuraren sayarwa baya masa daɗi sam ko a Lagos haka nan yake maleji ba daɗinsa yake ji ba.

Ya tsare Amina ya hanata tafiya, sai da ya gama, ta kwashe komai, sannan ya tashi zai tafi, Amina ta bi bayansa, har ya shiga mota ya hangota, ya tsaya yana jiran ƙarasowarta, ta miƙa masa wata jaka, be tambayi ta meye ba, ya karɓa ya duba, akwai manyan robar ruwa guda biyu a ciki, sai babban kwalin lemo, sai wata jarka guda ɗaya, ya ɗauko jarkar yana dubawa, fura da Nono a ciki.
Ya kalleta ya ce "Ina kika samu fura?"

"Mamana ce ta aiko mini da ita daga garinmu, na baka ne saboda hanya amma idan ba ka sha shikenan bani".

Yayi murmushin gefen baki ya ce "Bayan wauta ashe kina da hankali, ga ruwa ga lemo ga fura duk an bani kar inji yunwa a hanya, Na gode sosai"

"Bakomai Allah ya sanya Alkhairi"

"Ameen ya Allah" ya zura hannu a aljijunsa ya ɗauko kuɗi ya miƙa mata ya ce "Ungo wannan, kya sayi wani abun na gode sosai" ga mamakinsa sai ta girgiza masa kai alamar ba zata karɓa ba.

"Meyasa ba zaki karɓa ba?"

"Baba zai mini faɗa, kuma yana bani kuɗi shima"

"Ke kuma sai ki gayawa Baban na baki kuɗi?"

Cike da wauta ta ce "Ai ni duk abin da aka yi sai na gaya masa, saboda idan nayi ƙarya yana ganewa"

"Ai yanzu ba zai sani ba, idan ma kika gaya masan, kice ni na baki"

"Ni dai a'a gaskiya, ban taɓa riƙe kuɗi me yawa ba, ba ruwana, kuma dama ai aiki nake kuna biyana meyasa zaka bani kuɗi?"

"Ai nima babanki ne, ki karɓa"

Girgiza kai tayi ta ce "Babansu Fadila ne, ni Baba ne Babana" shi mamaki ma ta bashi, yaran yanzu da son abin duniya, amma ta dage ba zata karɓa ba, baya son cigaba da takura mata, dan haka ya ce "Shikenan, na gayawa Baban idan na baki abu ba kya karɓa" ba ta ce komai ba ta juya sumi-sumi ta koma ciki.

Tana zuwa ɗakinta, ta nemi wuri ta kwanta, dan ta samu

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment