Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

test ɗin ma ba ya nan, gashi nan ya ci 7/10.
Shiru yayi yana sake nazartar rubutun, tabbas na Fadila ne, dan bai manta wanda ta rubuta masa a littafin sa ba.

Yana waigowa ya hangeta ta tashi zata bar ajin, cikin sauri ya tashi ya bi ta ƙofar baya, ya bi bayan Fadila, tana ta sauri ta nufi in da motar ta ke ajiye.

Sauri yake sosai, yana kiran sunanta, tazararsa da ita ba yawa sosai, tana jinsa ta share shi, ta cigaba da sauri.
Sai da taje in da motar take sannan ya cinmata.
Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Ina ta magana kin mini shiru".

"Malam lafiya ta yi maganar kamar bata taɓa ganinsa ba"

"Dama...
"Kaga sauri nake tafiya zan yi"
"Ga littafinki" ya yi maganar yana miƙa mata littafin.
Sai a lokacin ta waiwayo ta kalleshi da fararen idanunta da ke matuƙar narka zuciyar Yazeed.
"Ka riƙe kawai" ta faɗa tana ƙoƙarin ɗauke kanta daga fuskar Yazeed.
"A'a ba za ayi haka ba, Halaccin da ki ka yi mini yanzu ma, Na gode sosai ubangiji Allah ya saka da alkhairi, kuma ga test ma kin yi mini, duk da hatsarin da ke cikin hakan, Na gode sosai ƙanwata".
Ɗagowa tai ta kalli Yazeed "Wacece ƙanwar taka?".
"Fadila mana" ya bata amsa, ta yamutsa fuska ta ce "Ka kiyayeni, ni na maka kama da ƙanwarka, ƙila ma na girmeka tsaurin ido kawai, na ce ka bar littafin, ka bani hanya zan kunna mota in tafi".
Wani irin murmushi Yazeed yake, wanda sai da haƙoransa suka bayyana, wanda ya ƙara masa kyau, daga murmushi ya fara dariya, har da rufa baki, dan ba ƙaramin dariya Fadila ta bashi ba.

"Saboda kina ganin tsayin mu ɗaya, shi ne ki ke cewa kin girmeni, ai ko da ki ke doguwa tubarkallah na fiki tsayi, balle ki kalli wannan tsofaffin idanuwan nawa, ki ce mini wai kin girme ni"

"To sannu tsoho" ta faɗa tana kallonsa.

"Yau ba zaki tsaya karatun ba?".

"Eh"

"To shikenan, Allah ya sauke ki lafiya?"

"Kamar yaya Allah ya sauke ni lafiya, masu ciki fa ake gayawa haka"

Yazeed ya ce "Subhanallah, ba haka nake nufi ba, ina nufin Allah ya kai ki gida lafiya".

"Inyee me ake tattaunawa ne haka besty da besty, yau munga ƙarshen ƙauna, kowa na ƙoƙarin kare ɗan uwansa a kowacce gaɓa da ɗayan yake fuskantar barzana" Cewar Captain da ya ƙaraso yana dafa Yazeed.

Fadila ta haɗe rai ta ce "Nifa bana son sa ido, kar ka kuma ce mini wani bestynsa na gaya maka".

Yazeed ya ce "A'a Nothing like besty in Islam, she's my sister in Islam, ƙanwata ce ta Addinin Musulunci ko Fadila?"

"Kai ka sani" tai maganar tana hararasa.

"Kwa dai ji da shi, muna nan mun kasa mun tsare mun zuba ido, muga yadda ƙarshen wasan zai kaya, kwana biyun nan, kullum sai naga ka lallaɓo jikin motar nan kun keɓe kuna ƙusƙus, idan tai wari zata bazu mu ji ai" daga haka ya juya ya tafi yana murmushi.

"Kaga ustaz ka ke ko Sheikh, ka Matsa zan kunna mota, ni bana son damuwa yanzu ka zo kana suma, ace ni ce".

"Sunan nawa ma baki sani ba, amma kin iya rubutawa a cikin littafi ko? Da kuma test ɗin da kika rubuta mini, ni ina ga zanje in gayawa malamkn nan gaskiya, ni ban yi test ɗinsa ba, ƙanwata ce ta yi mini".

"Sai ka dawo" da haka ta rufe motar, ta kunnata ta ja ta a hankali ta bar wurin.

A hankali Yazeed ya dinga shafa sajensa yana murmushi, shi dai in dai Fadila ta kula shi, yana kasancewa cikin farin ciki mara misaltuwa tsawon wannan wuni.

Khalil ya riƙe wuta, wurin yawan kiran Hafsa a waya, kuma sai ya daidaici tana gida yake kiran, gudun kar Mama ta ɓata rai, sai ta ɗau wayar ta amsa masa ciki ciki. Idan ha ji haka sai ya ce ta bawa Mama ya gaisheta.
Duk wulaƙancin da take masa, baya gajiya da safe da yamma sai ya kirata, bayan saƙonnin Soyayya da yake tura mata, amma ko ɗaya bata kulawa, balle ya sa ran zata amsa saƙonnin nasa. Sai dai kasa jure ganinta yayi, dan haka ya ƙudurce a ransa zai zo ko a ranar ne ya ganta ya juya ya koma, ba tare da yaje gida ba

Tana zaune tana fama da masu sayan awara, ta samu ta sallami da yawa daga cikin masu sayen, katsam ta ɗaga kai, taga fitowar wanda ta fi tsana a rayuwarta. Gabanta ya faɗi dan ba ta san da wacce ya zo ba, dan a kullum idan zasu haɗu ba shi da burin da ya wuce yaci mutuncinta, haka kwanaki ya zo ya sameta har wurin sana'arta a gaban mutane ya ci mutuncinta ba tare da kunya ko shakka ba.
Kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta, ta cigaba da abin da take yi.
"Au haryanzu kina aikin wahalar nan? Ko da yake ba abin mamaki bane ba, tun da ke da uwarki ba ku gaji arziƙi ba, titi dai a nan zaku ƙare"
Hafsa ta sunkuyar da kanta, tana jin wata irin ƙuna a cikin zuciyarta, wanda suka haddasa mata zubar hawaye.
Mai shayin kusa da Hafsa ne ya taso ya ce "Haba Malam, kai wani irin mutum ne mara tunani, kullum sai ka zo cikin mutane kana cin zarafinta, haba malam kamar ba musulmi ba".

A fusace mutumin ya ce "Ba ruwanka da ni malam, ka fita harkata a wannan sabgar, waye ya sa da kai, wannan Yarinyar har wadda za a tausayawa ce, uwatta ta goya mata baya tan zama a kan titi tana tallan kanta, ta ɓige da suyar awara tana karuwanci, ko da yake ai barewa bata gudu ɗanta yai rarrafe, abin da taga uwarta na yi ne" Yadda miyagun matashin suka daki zuciyarta, ba tare da ta shirya ba, ko wani tunanin ba, ta daki kaskon man da ke kan wuta, ya ƙonawa mutumin ƙafa.
Wani irin uban ihu ya saki, nan da nan ƙafa ta yi ja, ya yin da babu alamar nadama a tare da Hafsa.

Salati da salallami mutane suka fara yi da ganin abinda ya faru. Har Hafsa ta yi wannan aika aika ta gama, kuka take yi, mutane suka dinga bashi rashin gaskiya.

"Ba dai ni ki ka yiwa haka ba, to Wallahi zaki gani, zaki ga abin da zan miki, sai kin gwammace kiɗa da karatu da ni ki ke zancen".

Mai shayi ya ce "Ai ni kin mini daidai Hafsa, ɗan iskan banza kawai, bari in aika yaro ya sayo miki man ki, ki ƙarasa ki tashi.
Amina ta girgiza kai ta ce "A'a, gida zan tafi" ta yi maganar tana share hawaye.
Mai shayi ya sai mata mai, ya bata, da ƙyar ta karɓa, ta tattara kayanta ta tafi gida, dan ba zata iya cigaba da zama ba. Da ta je gida ma ba ta bari Mama ta gane ba halin da take ciki ba, Maman ma ba ta bi ta kanta ba, dan ta  fuskanci Hafsa yau tambotsan nata take ji.

Washegari da sassafe, Hafsa na shirin zuwa ta kai markaɗen wake, aka ƙwanƙwasa ƙofar gida. Hafsa na shirin zuwa ta buɗe, Mama ta ce "Ƙarasa bari in leƙa in ga waye"
Mama ta sanya mayafi, ta ƙarasa ƙofar gidan, tana buɗewa sai ga 'yan sanda biyu a tsaye da motarsu a farkon layi.
Gabanta ne ya faɗi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Yallaɓai lafiya kuwa?".

"'yar ki muka zo nema"

"Me 'ya ta tayi muku?"
"Yanzu ba lokacin yaɗa rahotanni bane, idan muka je can kya ji abin da tayi".

Jin Mama shiru ne ya sanya Hafsa ta tashi ta bi bayanta, sai dai tana zuwa soro ta yi turus, ganin 'yan Sanda.
"Mama lafiya kuwa?".

"Kece Hafsa?"

"Eh nice"

"An bamu iznin mu kama ki, dan haka ki zo mu wuce station".

Ayshercool
08081012143

GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143

Page14



"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" shi ne abin da Mama take ta maimaitawa, ya yin da Hafsa tayi tsumu tsumu tana tunanin wani lafin ta yi, da har 'yan sanda za su zo gida kamata?.

Mama ta kalleta cikin tashin hankali da firgici da yaya mamaye fuskarta ta ce "Hafsa me kika aikata haka, da za a zo har gida ana ƙoƙarin kamaki?".

Hafsa ga girgiza kai ta ce "Ni Mama ban yi komai ba, ban taɓa kayan kowa ba ba abin da ya haɗani da wani".

"Ke malama, ba lokacin tattauna wannan maganar ba ne, wuce mu tafi"  Suka ingiza ƙeyar Hafsa, tana kuka tana kiran Mama, a gaban maƙota, wani maƙocinsu Hafsa ya yi ƙoƙarin dakatar da su, ya ji ba'asi amma suka ƙi saurarsa, Mama ta ce su bari ta ɗauko mayafi su tafi tare, nan ma suka ƙi suka ce ta biyo su a baya.
A kiɗime Mama ta shiga gida, ta yafo mayafi, ta rufe gidan hankali tashe ta nufi titi. Tuni Maman ta fara jin haki, saitin zuciyarta ya mata nauyi, alamun hawan jininta zai tashi, kai tsaye station ɗin unguwarsu ta nufa, amma da taje aka ce mata ai ba wannan police station ɗin aka kai Hafsa ba.
Rushewa Mama tayi da kuka, tana tunanin ina aka kai Hafsa, 'ya mace a hannun 'yan sanda, ta kuma bazama ta tari wani abin hawan ta tafi wani division ɗin.

Khalil ji yake tamkar ana hura masa wuta a ƙirjinsa, babban burinsa kawai shi ne ya ganshi a garin Kano, a gaban kaskon wutar suyar awarar Hafsa, ya yi tozali da fuskarta da take sa shi nishaɗi da nustuwa.
Da fari ya jira ya yi booking ɗin jirgi, ya taho bayan kwana biyu, amma ya ji ya kasa jurewa, kawai ya ɗauki motarsa da yake amfani da ita a nan Abuja, ya nufo gida, yana tafe yana murmushi, zuciyarsa cike da muradin tozali da fuskar Hafsat.
  Kusan wuni Mama ta yi tana bulayi, amma ta rasa station ɗin da aka kai Hafsa. Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, kuka kam babu irin wanda ba tayi ba, 'ya mace a hannun 'yan sanda abin da tayar da hankali sosai.
Tana komawa gida maƙota suka fara tambayarta yaya ina Hafsan, cikin kuka ta ce ta rasa station ɗin da aka kai Hafsa, yanzu ma kuma bazama za tayi neman in da aka kaita.
Maƙocinsu mai suna Malam Sani ya ce "A'a Maman Hafsa ba za ai hak ba, bari in ɗauki babur ɗina in je in zazzaga nima, amma ki nemi wuri ki zauna ki huta, tunda dama ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba".
Da ƙyar suka rarrashi Mama, ta haƙura ta zauna, Malam Sani shima ya tafi zagawa stations ɗin da suke nan shiyarsu.
Ko mintuna Arba'in ba ayi ba, Mama ta kasa jurewa, ta sake ɗaukar mayafi, ta cigaba da yawon neman Hafsa.
  Khalil kuwa, a Hotel ya sauka, yayi wanka ya ci Abinci, dan kwana ɗaya zai yi ya koma, baya son Mummy ta tuhume shi dalilin dawowarsa a yanzu, bayan bai daɗe da tafiya ba.

Wajen ƙarfe biyar na yamma, yayi kwalliya ya ɗau motarsa zuwa wurin sana'ar Hafsa, amma ya tarar bata nan.
Ya ɗakko wayarsa ya kirata, wayar ta shiga amma ba a ɗauka ba.
Fitowa yayi daga motar, ya ƙarasa wurin mai shayin dake kusa da wurin da Hafsa ke sana'a, suka gaisa sannan Khalil ya ce "Dan Allah Hafsa fa?".

Mai shayi ya ce "Gaskiya yau ba ta fito ba, kuma ban jin zata zo, da zata zo da tuni ta almajiri ya fara kawo mata kaya".
"Dan Allah ina ne gidansu?"
"Taɓ, yo wannan ina zata saki jiki da wani har a san gidansu, ni dai na so naji ance gidansu a nan wajen makarantar brilliant yake, daga nan sai ka tambaya".

Khalil ya ce "Masha Allah, na gode sosai, Allah ya sa dai tana lafiya".

Har Khalil ya juya zai tafi, wani a cikin rumfar mai shayin ya ce "Ai nifa ina ga rashin fitowar tata yana da nasaba da abin da ta yiwa mutumin shekaranjiya, dama ya ce zata gani, maybe ko tsoro ta ji kar ya mata wani abu".

Cak Khalil ya tsaya, ya waiwayo, ya kalli mutumin da ke maganar, ya ce 'Malam wani abin ne ya haɗata da wani?".

Mai shayi ya ce "Wallahi wani mutumi ne yake yawan zuwa wurin nan, ya yi mata zagin rashin mutunci a gaban Mutane ya tafi, babu wanda ya san abin da ya haɗata da shi, aikuwa shekaranjiya ta watsa masa mai a ƙafa ya ce zata gani, wataƙila shi ya sa yau bata fito ba"
Cikin hanzari Khalil ya ce ya gode, jikinsa na rawa ya koma mota, gidansu Abdul ya fara zuwa, dan ya fishi sanin kan unguwannin.
Yana tsaye a ƙofar shagon Abdul, ya kira shi a waya, Abdul ya ɗaga tare da "Assalamu alaikum".
"Wa'alaikum salam, kana ina ne? Na zo shago baka nan?".
Abdul ya ce "Wane shagon?"
"Shagonka mana, ina Kano fa, dan Allah kana ina akwai matsala ne".
"Subhanallah, Allah yayi mana maganin matsala, fito titi mu haɗu" Khalil ya ajiye wayar, ya ja mota ya koma titi.
A titi ya samu Abdul ya ɗauke shi suka tafi.
Abdul ya ce "Wai ina zamu ne? Tukuna ma me ka dawo yi?, kwata kwata yaushe ka tafi da har ka dawo?".
Khalil ya kwashe komai ya gaya masa, Abdul ya jinjina kai ya ce "Ikon Allah, to Allah ya sa lafiya muje mu nemi gidan" Suka ƙarasa makarantar da aka kwatanta musu, da tambaya da ƙyar suka gano gidan, sai dai suna zuwa suka tarar gidan a rufe. Khalil yayi mamakin ganin gidansu Hafsa, ɗan ƙuƙuta kamar ɗakin tattabaru. Hakan yayi daidai da dawowar Malam Sani daga taya Mama neman Hafsa. Ganin yana ƙoƙarin shiga gidan kusa da na su Hafsa, ya sanya Abdul ya ƙarasa, ya yi masa sallama, Malam Sani ya amasa masa, suka gaisa.
Khalil ma ya ƙaraso, suka gaisa da Malam Sani, Abdul ya ce "Dan Allah munga kaine maƙwabcin wannan gidan, munzo wurin su Hafsa ne, kuma basa nan ga layin ba kowa balle mu tambayi wani".
Malam ya ce "Kunga dawowar nan tawa? Daga neman in da yarinyar take nake Hafsa, tun safe 'yan sanda suka tafi da ita, ba wanda ya san ina suka kaita, mahaifiyarta sai bulayi take tana neman ta, duk station ɗin da taje sai ace bata nan, shine nima na ɗau babur na zaga nima ban dace ba, gashi mu bamu san wani nasu ba, kowani tsayayyen namiji, balle muje tare a cigaba da nemansu, su kaɗai suke zaune a nan"
Khalil ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, me Hafsa ta yi haka har da za a kamata? Yarinyar da babu ruwanta da kowa ya za ai ace tayi laifin da za a kamata?" Nan da nan fuskar Khalil ta sauya, ya harzuƙa matuƙa.
Abdul ya ce "Ka kwantar da hankalinka mana, yanzu ba kumfar baki ce abin yi ba, mota zaka ɗauka muje division ɗin unguwar nan, muje mu ji me zasu ce"
Da ƙyar Khalil ya kwantar da hankalinsa, Abdul ya karɓi tuƙin, suna tafe Khalil sai zufa yake duk da sanyin AC dake motar, ace an kama Hafsa tun safe, amma babu wanda ya san ina ma aka kai ta.
Kallon tausayawa Abdul yake wa Khalil, dan da alama ya faɗa soyayyar yarinyar nan da yawa, babban abinda yake fargaba shi ne yadda mahaifiyar Khalil zata karɓi batun auren Khalil da Hafsat ba.

Abdul na parking, Khalil ya buɗe motar da sauri, kamar zai faɗi ya shiga cikin station ɗin.
Abdul ya ƙarasa kashe motar da hanzari, ya fito ya bi bayan Khalil, dan kar yaje yayi kataɓora.
Khalil ya yi sa'a D.P.O yana nan, aka yi musu iso suka shiga cikin ofishin DPO.
Bayan sun gaisa Khalil ya yi masa bayanin meke tafe da su. DPO ya ce "Gaskiya ba station ɗin nan aka kawota ba".

Khalil ya ce "Ai a shiyyarka take, dan haka ka bincika mana in da aka kai ta"

Abdul ya ce "Haba Khalil, ka bi a hankali mana, ya kake magana a haka?"

"Bar shi yayi mini rashin kunya, yanzu in sa saka mini shi a cell".

Khalil ya ce "Ni zaka dubi kamata kace a sakani a cell, ai ko kisan kai nayi nafi ƙarfin sarƙa Wallahi"

"Shut up Khalil, meye haka wai?" Cewar Abdul da yake zarewa Khalil ido.
"Malam ka daina zare mini ido, kana ji zai raina mini hankali dan yana kan wannan kujerar" da ƙyar Abdul ya sa Khalil ya yi shiru, ya lallami DPO da ƙyar, sannan ya bincika musu in da aka kai Hafsa.



Tuni su Fadila sun fara jarrabawa, kuma ba ƙaramin ganin amfanin abin da Yazeed yake koya mata tayi ba, a sauƙaƙe take karatunta, kuma take rubuta jarrabawar ta cikin nasara.

A gobe ne zasu rubuta jarrabawar course ɗin da ta tsana, saboda bata ganewa, tana matuƙar buƙatar taimakon Yazeed, amma ba zata iya cewa ya koya mata ba, dan a ganinta idan tayi hakan ta faɗo. A haka ta tunkari ajinsu, ranar ba su da jarrabawa, wasu daga cikin ɗalibai ne suka shigo karatu.
Sassanyan ƙamshin turarenta ne ya shiga hancin Yazeed, wand ya saukar masa da wata irin nutsuwa ta mussaman.
Yana zaune cikin ɗalibai, yana musu tutorial, galibinsu mata ne, duk sun kewaye shi, ciki har da wata yarinya Azima, sai nanuƙar Yazeed take, shi kuma yana takure jikinsa, yana matsawa, kallo ɗaya zaka yi masa ka san a takure yake musu koyarwar nan. A hankali ya ɗaga idanunsa ya sauke su a cikin Fadila, da take tsaye tana kallonsa.

"ماذا حدث ىااختي"
Ya faɗa yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi.
A hankali ta janye idanunta, tare da lumshesu, ta nufi wurin da take zama, hakan ya so tafiya da hankalin Yazeed, dan ta ƙasan idonsa ya cigaba da binta da kallo, har taje ta zauna, saboda ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, ta ɗanyi kwalliya yau, sai dai abin da bai masa daɗi ba shi ne yadda ta yi parking ɗin gashinta, ta fito da shi.

Captain ne ya kalli Fadila ya ce 'Babbar yarinya, irin wannan wanka haka kamar zaki gasar sarauniyar kyawawan Nigeria?" Harar captain ta yi ta basar, wani irin kishi ne ya kama Yazeed, amma ya danne ya cigaba da ƙoƙarin cigaba da abin da yake.

"Malam Yazeed wai ya ne, sai gaba muke kana dawowa baya?" Azima ta yi maganar tana ƙoƙarin taɓa shi.

Cikin sauri ya janye jikinsa ya cigaba da koya musu, sai dai lokaci lokaci ya kan ɗaga kai ya kalli Fadila, da sun haɗa ido, sai ta harareshi ba gaira ba dalili.

Gaba ɗaya suka kasa gane kan Yazeed, hankalinsa yana kan Fadila. Haka ya ƙarasa musu ya tashi.
Azima ta ce "Aikin banza, wannan gayen ba shi da zuciya, da yaga yarinyar nan yayi ta rawar kai, tana wulaƙanta shi".
Amra da a baya ƙawar Fadila ce, amma yanzu ƙawancen na su ba sosai ba ta ce "Ke ina ruwanki to, tunda bake yake shigewa ba".

Fadila ta bar ajin, amma motarta na wurin da ta saba ajiyeta, haka Yazeed yai ta dubawa, har ya gano ta, tana zaune a wani wuri ita kaɗai, tana waya.
Ba tsammani taga Yazeed ya zauna kusa da ita, wani irin shocking ta ji a jikinta, gaba ɗaya ta nemi nutsuwarta ta rasa. Bakinta ne ya hau rawa ta kasa cigaba da wayar da take yi, ta waiwayo ta kalli Yazeed, taga ita yake kallo gaba ɗaya jikinta ya ƙara yin sanyi, haka kurum ta ji wasu hawaye da bata san na menene ba suka taru a idonta, ga wani irin mugun kwarjini da yayi mata, wanda da bata taɓa sanin yana da shi, musamman kasancewar kusan kullum da facemask a fuskarsa, yau kuma ya cire, ga sajensa ya ƙara yawa, gashi ya ɗan tsare ta ido.
Yazeed ya yi murmushi ya ce "Gani naga kamar kina son ganina".

Kallonsa tayi ta sake haɗe rai. Kamar ba za tai magana ba ta ce "Ka matsa daga kusa da ni".

"Zan matsa, amma meyasa hannunki yake rawa, ko baki da lafiya ne?"

Ɓoye hannun tayi tana jin yadda jikinta ke cigaba da rawa, ba tare da tasan dalilin hakan ba.

"Fadila" ya kira sunanta.

"Kallonsa ta kuma yi, amma ta ji idanunsa sun yiwa nata nauyi a nata idon"

"Naga kina nema ne ne, shiyasa na biyoki nan".

"Ni ba nemanka nake ba" ta faɗa tana kauda kanta gefe daga kallonsa.

Yazeed ya ce "Ba nemana ki ke ba, amma kika tsaya kina kallona? Shikenan na ji, ɗauko littafin in koya miki, kina son in koya miki abu, amma kin kasa gaya mini, ba ke kika ce in koya miki ba, ni nace zan koya miki, ɗauko mu yi" Kallonsa tayi da mamaki, tana tunanin yadda akai ya san abin da ke ranta.

"Ba mamaki zaki tsaya yi ba, ɗauko muyi abin da yakamata".

"Malam ka Matsa daga kusa da ni" ta faɗa tana haɗe rai.

Yazeed yayi murmushin sa mai ƙayatarwa ya ce "Ko na matsa ba zaki daina jin abinda kike ji ba, kuma hannunki ba zai daina rawa ba, amma gashi na matsa, kawo littafin in ga me kika karanta a kan course ɗin".

Miƙewa tsaye tayi ta ce "Dan Allah malam ni ka ƙyaleni, sai kace dole, ka fita daga harkata kar ka sake zuwa in da nake, bana buƙatar taimakon naka, ni ai bance maka ina son ka koya mini abu ba".

Shima ya miƙe tsaye ya ce "Am sorry, Allah ya baki haƙuri, na yi miki shishshigi, ba zan sake ba insha Allah"

Jakarta ta ɗauka tai gaba, tana cigaba da yadda jikinta ke tsuma kamar wadda tai artabu da aljan.


Cikin ikon Allah su Khalil suka gano in da aka kai Hafsa, tun safen nan ba ta ci komai ba, sai kuka da take yi, kuma taƙi magana, fuskarta duk tayi jawur saboda kuka, an rufeta a ceil.

Su Khalil basu tarar da DPO division ɗin ba, sai yaransa, bayan sun gaisa Aminu ya sanar da su cewar sune wanda suka zo wurin Hafsa.
Ɗansandan ha kallesu ya ce "To mintuna uku kacal zaku yi, dan kotu zamu kaita".
"Wai a kan ta aikata wane laifin?" Khalil ya yi maganar a hargitse.
Abdul yayi saurin dakatar da Khalil ya ce "To Yallaɓai, a bari mu gantan".
Aka fito da Hafsa, idanunta jawur, tana rarraba ido taga Mama, kawai taga Khalil da Abdul, aikuwa tayi sak tana kallonsu, ta ƙaraso gaban teburin ta tsaya tana sunkuyar da kai.
"Hafsat, me kika yi aka kawo ki nan?" Khalil ya yi maganar yana kallonta cikin kulawa.
Fashewa da kuka Hafsat tayi, ta kasa magana.

"Ai na zata faɗa ba, tayi attempting illata mutum, kina mace amma kina abin 'yan daba, ta ƙonawa mutum ƙafa da mai, kuma ta rarumo makami tana nema ta sokawa mutum" cewar wani ɗan sanda mai jajayen idanuwa.

Tsaki Khalil yayi, ya ce "Wanan dalilin ne ya sanya aka kawota nan, wace irin magana ce wannan? Ta yaya zata ɗau makami tace zata illata wani, Yarinyar da ko kuzarin kirki ba ta da shi?"

"Kaga shi mugu fa ba a ido ake ganinsa ba, wanda ya kawo ƙararta ya ce bai yadda da sulhu ba, a kai su kotu a bi masa hakkinsa"

Khalil ya ce "Shi dabban ina ne da zai kai mace kotu ya tsaya a kotu ya ce wai ta ɗau makami zata masa illa? Wace doka ce ma ta bada damar a riƙe mutum tsawon wannan lokaci family ɗinsa ma ba su sani ba, a bani belin ta".

DPO ne ya shigo yana zazzare ido "Yaya, Yaya, meke faruwa nake jin hayaniya haka?"

"Welcome sir, wannan ne ya zo zai mana tsageranci, wai sai an bashi belin wannan 'yar dabar".

"Wallahi ka kuma ce mata 'yar daba, saina ɓata maka rai".

"Kai nutsu, nan station ne, kar kai mana fitsara" Cewar DPO yana zarewa Khalil ido.

Abdul ya ce "Dan Allah Khalil abi komai a sannu".

Khalil ya ce "Wallahi ba zan bi a sannu ba, ya za'a kama yarinya ba bisa ƙa'ida ba, kuma aci zarafinta, sun ajiyeta daga ita sai su a wuri ko danginta basu san in da take ba?"

DPO ya ce "Au rashin kunya zaka mini, kai ku mayar da ita ceil, ba za a bada belin nata ba, sai ta ɗau nauyin maganin wanda ta illata".

Khalil ya ce "Bari in ɓullo muku in da ya dace" kawai ya fita daga cikin station ɗin, kuka Hafsa ta saka, da taga Khalil ya juya ya fita. Abdul ya bi bayansa da sauri.

Mintuna bakwai, DPO ya fito a gigice yana faɗin "Suna ina? Wannan wane irin ɗan tijara ne, maimakon ya tsaya a sasanta sai ya kunno mini wuta daga saman ƙololuwa? Ku kira mini shi mana".
Khalil ne ya shigo ya ce "To zaku bani ita ko kuwa?".
"Za a baka, ai ban sai kai waye

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment