Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwaɓewa, to ta isa ma tayi wani yinƙuri na furta wani mummunan abu a kan maigida meye hujjarta?'

A fili ta ce "Allah ma ya ƙara, ni tsorona Allah ya sa ba lalubeta yake yi ba, ita matar gida tana can gantali kamar 'yar akuya kullum tana tafe kamar iska"

Ɓangaren Hafsa kuwa, ta rame tayi duhu, gaba ɗaya ta daina walwala, waccan rayuwar tata ta baya ta sake dawo mata sabuwa fil, cike da sabon salo mai ɗauke da ciwo irin na soyayya.
Tun daga koke koken nan da tayi, take fama da ciwon kai, tayi ta ƙoƙarin kawar da tunani da damuwa da Khalil, amma abu ya gagara tun tana ɓoyewa kar Mama ta gane, har abu ya zo ya zarce mata da zaɓi mai zafin gaske.
A hakan Mama ta gane, saboda ganin yawan kwanciyar da Hafsa take yi, ga rashin cin Abinci.

Cikin dare Mama ta tashi, domin yin sallar dare, ama ta dinga jin sheshsheƙar kukan Hafsa, ta miƙa hannu zata yaye abin rufar Hafsa, amma taji jikinta zafi rau.

"Hafsa meye haka? Meke damunki ne?"

"Mama bakomai"

"Kamar yaya babu komai, ji yadda jikinki yayi zafi, Hafsa kin ɗora kanki damuwa kina nema ki hallaka kanki, Hafsa ƙaddara ba zata samu bawa yayi tawakkali ba?"

Hafsa ta ja jikinta da ƙyar ta zauna, ta ce "Mama ba laifina bane ba, kawai rashin lafiya nake yi"

"Haba Hafsa, nifa na haifeki ba ke kika haifeni ba, na sani kin shaƙu da Khalil haryanzu kina son sa, amma ki cigaba da Addua, Allah ya kawo miki mafita, bana jin daɗin ganinki a wannan yanayin ko Abincin kirki ba kya ci, kuma ni baki gaya mini baki da lafiya ba" Hafsa dai tayi shiru, ba tace komai ba.

"Tashi ki lallaɓa kiyo alwala, ki zo ko raka'a biyu kiyi, kiyi Addua Allah ya bamu mafita gaba ɗaya, ina da guntuwar gasara sai in dama miki kunu ki sha, sai in baki paracetamol"

Cikin yanayi na jin jiki Hafsa ta ce "A'a Mama, dare yayi sosai, bari in sallar kawai"

"A'a ba komai, bari in dama miki, yunƙura ki tashi"

Hafsa ta yunƙura za ta tashi, ama jiri ya kwasheta ta koma luuuuu zata faɗi.
Duk da Mama bata da cikakkiyar lafiya, haka ta yunƙura ta rungumo Hafsa, suka kusa faɗuwa.

Cike da damuwa Mama ta ce "Hafsa har jikin naki ya kai haka?"

"A'a Mama, jiri ne kawai ya ɗan ɗebe ni"

Mama ta kama Hafsa ta zauna, sannan ta ce "Kinga zauna, bari in je in dama miki kunun, in baki maganin, zuwa in Allah ya kaimu sai mu tafi Asibiti".

Hafsa ba ta ce komai ba, sai lumshe idanunta da ta yi, tana sake jin jikinta babu daɗi.

Bayan sallar isha'i Amina tana ƙoƙarin buɗe jakarta ta ciro litattafanta, ta ci karo da tarin kayan ciye-ciye na biscuit da chocolate, da wani turare da kwalinsa kawai abin kallo ne, jan kwali ne kwalbar turaren ma ja ce, mai matuƙar ɗaukar hankali.
Ta fesa turaren a hannunta ta sansana, wani irin sassanyan ƙamshi ne da turaren mai kwantar da hankali. Ko ba a gaya mata ba ta san turare ne mai tsada sosai.
Murmushi Amina ta yi, tana sake jujjuya turaren da kallon tarkacen kayan ciye-ciyen.
Wani murmushi Amina tayi, wanda ita kaɗai ta barwa kanta sanin ma'anar murmushin.

Fadila kuwa a ɗakinta ta ci Abinci ita kaɗai, tayi wanka tana saka kayan bacci tana shafa mai, ta kalli turarukan wurin Yazid, ta zuba musu ido tana kallonsu tamkar Yazid ɗin take gani a wurin, tunani ta shiga yi a kan barkwancinsa, da yadda yake ta nuna mata kulawa daga fara shirin su zuwa yanzu, mutum ne mai haƙurin gaske da kawaici, ta tuno yanayin da ya shiga a lokacin da ta gaya masa tafi ƙarfin sa, har aka tashi jikinsa babu wani kuzari. Guntun tsaki tayi a fili tana tunanin sai me dan tayi masa warning a kan ya fita daga harkarta, ai ya san ruwa ba sa'an kwando bane, kuma kamar yadda Yusra ta gaya mata, sanyin halin Yazid da kyautatawarsa zata iya sawa ta fara son shi ba tare da shirya hakan ba, gara ma tun wuri ta raba gari da shi.

Wayarta ce ta kawo haske, ta kalli in da wayar take taga message ne ya shigo, ta ɗaga wayar ta duba sai taga missed calls biyar, duk na Kankiya saboda wayar na silent bata san ya kira ba.  Ta duba saƙon ta ga roƙonta yake  wai yana son ta bashi dama ya zo gidansu.
Dire wayar tai tana harar wayar tamkar ita ta turo mata saƙon, "Zan ɗau mataki a kanka, idan ya so ka yiwa Yazid ɗin abin da ka ga dama ku ta shafa" tayi maganar tana ƙoƙarin kauda wani abu mai kama da tausayi a ranta game da Yazid.

Mummy ce ta faɗo ɗakin Fadila babu ko sallama fuskarta cike da damuwa.
Fadila ta kalleta ta ce "Mummy ya dai?"

"Kin yi waya da Khalil ne?"

"Mummy wane Khalil kuma, wayar me zan yi da shi bayan yana gidan nan"

Mummy ta ce "Khalil baya gidan nan, sai yanzu na farga, tun safe banga gilmawarasa ba, na duba babu motarsa, naje in tambayi wancan shashashan tsohon when last Khalil ya fita, amma na tarar baya nan, sai direban babanku ne ke buɗe gate ɗina, wai ya nemi iznin babnku ya tafi ƙauye, shi kuma bai san lokacin da Khalil ɗin ya bar gidan nan ba"

Fadila cikin mamaki ta ce "Ikon Allah, to Mummy ki kira wayarsa mana"

"Na kira taƙi shiga sam, gaba ɗaya hankalina ya ɗaga"

"Ko ya koma wurin aiki ne?" Fadila ta sake tambaya.

"To wa ya sani ne? Kuma sai ya koma wurin aiki bai mini sallama ba, yaya hakan zai yiwu, kar inje a sace mini ɗa a banza, sai sa na gaya wa babanku, ya samar muku da security, yawonmu haka a gari is not safe, duba sa matsayin da ya riƙe a ƙasar nan, amma ya ce mini no need, ai ga irnta nan"

Fadila ta ɗanyi shiru sannan ta ce "Mummy, bana tunanin sace Yaya Khalil aka yi, wataƙila ya tafi wani wurin ne dan huce haushin abinda kika yi wa yarinyar da yake so"

Cikin mamaki Hajiya Zainab ta ce "Kuma haka ne ko? Yanzu sai Khalil ya bar gidan nan ya tafi wani wurin ba tare da na sani ba saboda haka? Aikuwa idan haka ne da ya ci ubansa, sai na nuna masa nice uwarsa kuma dole ya bini"

"Mummy kibi a hankali, kar garin neman gira a rasa ido"

"Rabu dani da wata ido da gira, zan cigaba da bincikawa muddin na tabbatar haka ne idan bai yi wasa ba saina ci mutuncinsa".

"Amma me Daddy ya ce?"

"Rabu dani da Daddyn nan na ku, nayi masa Magana amma bai mayar da abin serious ba, wai Khalil ba yaro ne ƙarami ba, duk in da yaje zai dawo kar in damu kaina"

"Mummy, gaskiya Daddy ya faɗa, ki kwantar da hankalinki zuwa Allah ya kaimu da safe mu ga yadda hali zai yi"

Jinjina kai Mummy ta yi ta bar ɗakin Fadila, gaba ɗaya ta rasa nutsuwarta saboda rashin sanin halin da Khalil yake ciki, da kuma a ina yake, ta ɗora alhakin duk wannan abun a kan Hafsa, wadda take can tana fama da kanta.

Da safe wajen ƙarfe tara na safe, Mama ta shirya ta dafawa Hafsa ruwan wanka, da ƙyar Hafsa ta rarrafa tayi wanka, kasa cin Abincin ma ta yi, Mama ta taimaka mata, ta shirya suka tafi Asibiti.
Tashin farko teses kawai sun yi na dubu biyu aka rubutawa Hafsa, aka yi mata likita ya tabbatar da jininta ya hau, ga malaria mai zafi da ulcer.
Mama ba tayi mamaki ba jin Hafsa tana da hawan jini, likitan ya ɗan nazarci fuskar Hafsa sannan ya ce "Ƙanwata meke damunki a 'yan shekarunki kika kamu da hawan jini, jininki ya hau fiye da yadda za a iya cewa ko zafin zazzaɓin ne ya sanya jinin ya hau"
Hafsa ta sunkuyar da kanta, tana muza yatsunta na hannu.

"Magana fa nake" ya sake maganar yana ɗan dukan teburin gabansa.

Hawaye ne ya taru a idon Hafsa, Mama ta ce "Likita rabu da ita kawai, duk saboda ta rabu da wani saurayinta, shi ne ta saka kanta a uku, nayi nasihar nayi rarrashin amma ta saka abin a ranta"

Likitan ya ce "Mahaifiyarta ce ke ko yayarta?"

Mama ta ce " 'ya ta ce"

Likitan ya ce "Ba abune mai sauƙi ba Hajiya, musamman ga mu mutanen wannan zamani, muna bawa soyayya muhimmanci sosai da sosai, dole zata shiga damuwa, saboda abun ba sauƙi amma kiyi haƙuri ki cigaba da Addu'a ko kina son Mama ta rasaki at your young age, ko ki kamu da ciwon zuciya?" Hafsa ta ce "A'a"

"Tukuna ma, gaya mini sunansa, sannan maiyasa ya yaudareki?"

"Ba yaudarata yayi ba"

"Ok na gane, kin san kowane bawa, akwai rubutacciyar ƙaddararsa, kiyi haƙuri, ga magunguna nan da ruwa, zan riƙe ki a Asibitin nan tsawon kwanaki biyu, sai naga jikinki yayi kyau, jininki kuma ya sauka"

Mama ta yiwa likitan godiya, da jin daɗin yadda ya nuna damuwarsa ga Hafsa, ta riƙe Hafsa suka fita ma'aikatan jinya suka basu gado, Mama taje ta biya kuɗin, da kuma sayo magunguna.

"Baban Fadila nifa ban gane manufarka ba, yaya zan gaya maka ban san in da yaro yake ba, amma ko a jikinka"

"To yaya zan miki ni? Khalil dai ba yaro bane ba ƙarami, da hankalinsa kuma ke da bakinki kika gaya mini abin da kika yi masa, dan haka yayi wani wurin ne, dan yaje ya ji da tension ɗin da kika saka masa"

Cikin ɓacin rai ta ce "Kana nufin saboda na rabashi da 'yar matsiyata shi ya sanya zai bar gida ban san in da ya tafi ba? To wallahi ko zai mutu ba zai kawo mini jinin tsiya a matsayin sirika ba, zai ga yadda zan yi da shi, bai isa ba wallahi"

Daddy ya ce "Dan haka sai ki daina tayar mini da hankali a kansa, matsla ce da kika kunnota ke zaki maganinta"

"Au haka ma zaka ce?"

"To me zance ni?"

"Zaka ga me zaka cex" ta bar falon Daddy Fuuu ranta a ɓace.

Amina har ta tafi makaranta Baba bai dawo ba, bata san ya aka yi ya tafi ƙauye ba sanarwa ba, bai gaya mata zai tafi ba suka haɗu da Safe tayi masa sallama zata makaranta, amma bai gaya mata cewar za shi ƙauye ba, sai da ta dawo daga makaranta.
Tayi ta ƙoƙarin kiran wayarsa, amma wayar bata shiga, sai ta shiga damuwa tana fatan Allah ya sanya komai lafiya.

Haka ta dawo daga makaranta tana sa ran ganin Baba, amma ta dawo ta tarar bai dawo ba.

Sai wajen la'asar sannan Baba ya dawo, Amina ma bata san ya dawo ba, kawai ta fito da niyyar ta duba ko ya dawo ta tarar da shi yana salla.
Murna ta dinga yi tana godewa Allah, da ya sanaya yana lafiya.

Ta jira ya idar da sallar, yayi Adduoinsa sannan ya kalleta ya ce "Uwata ya makaranta?"

"Lafiya lau Baba, amma baka gaya mini zaka tafi ƙauye ba, sai da na dawo nake ji jiya"

Baba ya ce "Eh, tafiyar ce ba ta shiri ba, nayi ta ƙoƙarin ma in kira wayarki in haɗaki da babarki, amma wayar taƙi shigowa"

Amina ta ɗan ɓata fuska ta ce "Kash, nima nayi ta ƙoƙarin kiranka amma ba ta shiga, Baba dan Allah ka saiwa Inno waya, in dinga jin muryarta"

Baba yayi murmushi ya ce "ai na bayar a saya mata, har layi na bawa Saminu nace ya sai mata mai ɗan kyau wadda zata iya gane kanta"

Amina tayi murmushi ta ce "Yauwa Baba, yaya ka baro su, ya kowa da kowa"

Baba ya ce "Duk suna lafiya suna gaisheki, Sa'a an saka bikinta. Mun yi magana da Alhaji Ahmad, yayi mini maganar zuwanki birnin tarayya a kan harkar karatunki, da fari dai na ɗan yi jayayya amma daga baya ya mini bayani na amince, ina fatan zaki kula da kanki Amina, ki riƙe mutuncinki, ki tuna ke ba 'yar kowa bace, ki kula da tarbiyyar da muka baki"

Washe baki Amina ta yi ta ce "Baba, ka amince inje ɗin?"

"Eh uwata, na amince ina miki fatan alkhairi, sannan ya ce mini zaki gida kiga gida kuma kiyi musu sallama, saboda doguwar tafiya zaki yi"

Hawayen farinciki suka cika idanun Amina, ta kalli Baba ta ce "In Allah ya yarda ba zan baka kunya ba Baba, zan kula da kaina, ka mini Addu'ar samun nasara"

"Addu'a ai kullum cikinta nake, Allah ya yi miki albarka, ga kayayyaki can babarki ta haɗo wai in kawo miki"

Cikin murna Amina ta nufi wurin kayan da Baba ya nuna mata, ta ɗau ledar Vivan, tana jin yadda take jin kewar Inno a ranta.

Har zata fita daga ɗakin Baba ya ce "Yauwa na haɗu da wannan malamin naku na makarantar boko, na manta sunansa, ya cc in gaisheki"

"Laa Malam Sunusi?"

"Eh shi"

"Allah sarki, ina amsawa, yauwa Baba a kawo Abinci ne, ko in dafa maka wani abun?"

"A'a ba sai an kawo ba, nan da kika ganni a ƙoshe nake"

Amina tayi murmushi ta juya ta bar ɗakin Baba.

A falon gidan ta tarar da Hajiya Zainab tana kaiwa tana komowa a falon, da waya a hannuta kamar ka taɓata ta fashe sai cika take tana batsewa.
Tana ganin Amina da leda ta ce "Ke!" Amina ta tsaya tare da kallon in da Hajiya Zainab take.

Cikin kaushin murya ta ce "Daga ina kike?"

"Naje wurin Baba ne ya dawo" Amina ta bata amsa.

"Maza kije ki kira mini shi, dama shi nake jira" tayi maganar tana hura hanci.
Sai da Amina ta ɗan tsaya tana kallon Hajiya Zainab, tana son gano dalilin da ya sanya take son ta kira mata Baba.

"Ba zaki je bane kika tsaya kina kallona haka?"

Amina ta ajiye ledar hannunta, ta juya ta fita, tun daga nesa Baba ya hangota ta nufo shi, fuskarta a haɗe, tsayaqa6 yayi yana jiran ƙarasowarta.

"Uwata lafiya naga kin dawo?"

"Matar gidan ce ta ce na kiraka"

Baba ya ce "To, Allah ya sa ba wani laifin ki ka yi ba, ko ni nayi ba"

"Nima ban san meye ya sa take nemanka ba"

"To muje, koma meye sai na ji"

Suka rankaya suka nufi falon.

Suka shiga Baba yayi sallama, amma Hajiya Zainab tayi biris tana ta wani kumbura wuya kamar kasa. Ta ƙarewa Baba kallo a wulaƙance, irin kallon yake ƙonawa Amina rai.

"Jiya da yaushe ka bar bakin gate ɗin nan?" Ta jefowa Baba tambayar.

Cikin girmamawa ya ce "Sai goma na safe ranki ya daɗe?"

"Kenan kana nan Khalil ya fita?"

"Eh, nina buɗe masa ƙofa, bayan sallar Asuba ya ɗau mota, na buɗe masa ƙofa ya fita".

"Wane irin mutum ne kai da zaka buɗe masa ƙofa ya fita bayan sallar Asuba, ina ya ce maka zai tafi?"

"A'a Hajiya, bai gaya mini ba, ko gaisawa ba muyi ba ya fita"

Wani uban tsaki ta ja, sannan ta ce "Kai dai banga amfaninka a zaman gadin nan ba, tayaya yaro zai fita bayan sallar Asuba, amma ka kasa tambayar ina zai tafi"
Ikon Allah Amina ta tsaya tana kallo, aikin Baba buɗewa da rufewa to meye huruminsa na sanin in da wani zai je a gidan?

"Yaya dai meke faruwa ne?" Suka jiyo muryar Alhaji Ahmad, da ya fito yana ta zuba ƙamshi cikin wani vowel baƙi.

Ya kalli Baba Hassan da ke tsaye fuskarsa cikin damuwa, ya risunar da kai kamar mai neman gafara.

"Malam Hassan, ka dawo ashe?"

Baba ya ce "Eh na dawo ranka ya daɗe"

Baba ya Kalli Mummy ya ce "Meke faruwa ne?"

"Ka jiye mini wannan rainin hankalin mana, wai Khalil ya fita daga gidan bayan sallar Asuba amma ya kasa tambayarsa ina za shi ko ya sanar mana, ni na gaji da sokoncin wannan mutumin"

"Sokonci kuma?" Amina ta tambaya rai a ɓace.

Nunata Hajiya Zainab tayi ta ce "Idan ina magana kina saka mini baki, sai na ɗauke ki da mari, da ubanki nake magana, na faɗa sokwanci, sam bai san aikinsa ba, nace maka ka sallame shi ka samo mana masu gadi na hukuma, wannan ko wani abun ne zai faru ba sai dai ya same mu ba, ba uwar da zai iya tsinana mana ba"

Ga mamakin Amina ta sai ta ji Alhaji Ahmad ya ce "My dear kiyi haƙuri, ki bi komai a hankali, sanin in da Khalil za shi ba alhakinsa bane ba, kuma yana iya ƙoƙarinsa, bai kamata ace kina tada jijiyoyin wuya haka ba"

"Ba dole in tada jijiyoyin wuya ba, ka bar wannan mutumin a shiritarsa ɗana ya bar gida, gaskiya Allah amfana aikin da yayi haka, ya koma in da ya fito, na gaji".

Baba ya risuna ya ce "Dan Allah Hajiya kiyi haƙuri, in Allah ya yadda hakan ba zata sake faruwa ba"

Amina ta zata Alhaji Ahmad zai ɗau wani mataki, amma ya ɓige da lallaɓa Hajiya Zainab a kan tayi haƙuri.

Wani mugun kallo Amina ta yiwa Alhaji Ahmad, idanunta suka cika da hawaye ta ɗau ledarta ta wurin Baba kawai ta bar falon, saboda yadda zuciyarta ke mata zafi zata iya zagin Hajiya Zainab.

Alhaji Ahmad ya lura da yadda Amina ta ɗau zafi, amma ba damar yayi wani yinƙuri a lokacin, haka ya dinga rarrashin Hajiya Zainab, ya ce Baba ya koma bakin aikinsa.

Baba kansa ba ya jin daɗin yadda Hajiya Zainab ke masa a wasu lokutan, amma ba yadda ya iya idan ya bar aiki makomar karatun Amina da kuma iyalinsa baki ɗaya yake tunani.
Kan ya ƙarasa wurin gate ɗin, aka fara horn.
Ya ƙarasa da sauri jikinsa na tsuma, ko Fadila ce ta dawo, kar ya yi wani laifin ya kuma jawa kansa wani cin mutuncin.

Yana buɗewa yaga motar Khalil, ɗan tsayawa Baba yayi, yana kallon motar.

Abdul yaje yayi parking ɗin motar ya fito ya nufo Baba, Baban ma nufarsa yayi ya ce "Malam Abdul, ya na ganka kai kaɗai ina Khalil ɗin?"

Abdul ya ce "Ai Khalil ya koma wurin aiki ne, ya aikin Baba Hassan?"

Baba ya ce "Alhamdilillah"

"Mutanen gidan kuwa suna nan?"

Baba ya ce "Eh ka shiga suna ciki"

Abdul ya nufi cikin gidan.

A falon ya tarar da Hajiya Zainab, tare da Daddy, yana ta aikin rarashinta a kan rashin sanin in da Khalil yake.

Abdul ya shiga da sallama, Daddy ne kawai ya iya amsa masa.
Ita Mummy ma sai yanzu ta tuna da Abdul, ƙila ya san in da Khalil ya tafi, amma ko ya sani ma ita bata da lambarsa balle ta kirashi ta tambaye shi, ko da yake ta san wataƙila Khalil ɗin ɗin yazo nema shima dan da ya san in da yake, ba zai biyo shi gida ba.

Har ƙasa Abdul ya durƙusa ya gaishe su.
Daddy ya amsa masa cikin sakin fusak Daddy ya amsa, ita kuwa Hajiya Mummy ba ta bi ta kan gaisuwarta sa ba.

Abdul ya ce "Dama motar Khalil ce na dawo da ita gida"

"Motar Khalil kuma? Ina shi Khalil ɗin ya kex Mummy ta faɗa tana zazzaro wa Abdul ido.

Mamakine ya kama Abdul, ganin da alama ba su san ina Khalil ɗin ya tafi ba.

"Mummy, wajen ƙarfe shida ya sameni a gida, ya ce in kai shi airport zai koma Abuja, sai in dawo da motarsa gida, naje wurin aiki ne shi ya sa ban dawo da ita ba".

"Amma kai baka da mutunci, har ya haɗa baki da kai ya tattara kayansa ya koma aiki, ban san in da yake baka gaya mana ba sai yanzu, kasa hankalinmu duk ya tashi bamu san ina yake ba".

"Wallahi Mummy ni ban san bai gaya muku ba, kawai...

"Dalla rufe mini baki, ai duk wata ƙulla-ƙullar rashin gaskiya kaine kake bashi shawara, na san wataƙila kaine kake hure masa kunne, yaje ya gano wata 'yar talakawa ya maƙale wai ita yake so"
Abdul ya sunkuyar da kai yayi shiru ya gaza cewa komai.
Daddy ya kalli Abdul ya ce "My son, tashi ka tafi Allah yayi maka albarka, ka gaida maman naka"

Abdul ya ce "To Daddy sai anjima"

Sai da Abdul ya fita, sanan Daddy ya ce "Zainab wai meke damunki ne? Dan kawai ɗanki ya miki laifi sai ki dinga bin wanda ba su ji ba ba su gani ba da miyagun maganganu da cin mutunci?"

"Au haka kace? Suwaye ma mutanen wa na yiwa ƙarya wancan sakaran tsohon da bai san aiinsa ba ko wannan yaron mai kama da maye ya liƙewa ɗana ya ƙi rabuwa da shi duk wata harkar ƙasƙanci shi ne yake nuna masa"

Ran Daddy ya ɓaci, ya miƙe ya ce "Sai kiyi abin da kika ga dama ki ki cigaba kar ki fasa, idan kika kaini bango kin fi kowa sanin halina"
Bayansa tabi da harara, ta tashi tai nata wuri.

Fadila kuwa tun da taje makaranta, ba ta ga Yazid ba sai lokacin lectures kawai, da an yi yake ficewa daga ajin sai lokacin wata lectures ɗin, kuma ko da wasa bai yadda ya kalli in da zai ga Fadila ba, balle a samu kuskure ko ido su haɗa.
Ita ma tayi nata ƙoƙari, wurin ganin ba ta ko nuna ta san da zamansa a ajin ba, ta cigaba da harkokint.
Sai dai yin hakan taji ta takura kanta sosai da sosai, ko ba komai Yazid mutumin kirki ne, kuma ya taimaketa sosai a first semester, wanda garin taimakon nata ne har ya rasa wasu marks ɗin, amma hakan bai hana shi zama overaller ba!

Bayan Daddy ya dawo daga sallar isha'i, ya tarar da Amina tana shirya Abincin dare, fuskarta babu walwala sam, idanunta duk sun ƙanƙance da alama tayi kuka.
Dining ɗin ya ƙarasa yana murmushi "Meenali me aka dafa ne yau?"

Banza ta yi masa ta cigaba da abin da take yi.

"Ba kya jina ne?"

"To ni me zance" ta faɗa bata ko kallon inda yake.

"Amma magana fa nake miki"

Idanunta da suka cika da hawaye ta ɗago tana kallonsa.

"Ka zama mai kulawa da mutuntawa a gareni, ka ɗauki lamurana da muhimmanci amma a gabanka matarka take ciwa mahaifina mutunci, idan nayi magana ka ji haushina, ka san yadda nake ji a duk lokacin da iyalinka suka ci zarafin mahaifina a gabana? Kawai dan muna talakawa? Mu muka yiwa kanmu? Duk lalacewar uba uba ne, balle babu lalacewa a iyaye, ni kar ka sake nuna mini wata kulawa, babban abin da za a mini a rayuwata shi ne a girmama mahaifina ya fi mini duk wani tattali da kulawa" ikon Allah Alhaji Ahmad ya tsaya yana kallo, tuni idanunta suka yi jawur hawaye ya wanke mata fuska, ta bar falon ta bar shi a tsaye.

AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA

BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL



PAGE 41


Alhaji Ahmad ya shafi gemunsa, bai zaci Amina zata iya tsayawa ta yi masa tsiwa haka ba, amma ta wani fannin da gaskiyarta, ba bu wanda zai jure a dinga cin mutuncin iyayensa haka kurum, dan kawai talaka ne, amma ai ba shi yayi mata laifin ba.

Amina kuwa ɗaki ta koma, ta zubar da hawaye sosai tayi kuak, ba zata iya ƙirga adadin yadda aka sakata kuka ba a gidan nan, iya cin mutuncin da ake mata baya damunta a kan wanda ake yiwa Baba.

Komawa aiki ya gagari Khalil, daga masallaci sai gida, sai yaji yunwa zata kassara shi, sannan yake order Abinci ya ɗan ci kaɗan.
Haka nan yaji yana son ya kunna wayar, yayi trying layin Hafsa.
Da saƙonnin Mummy ya fara cin karo rututu, a kan ina ya tafi, bai sanar da ita ba?

Message ɗaya ya iya yi mata reply ya ce 'ina wurin aiki'

Ya lalubo lambar Hafsa, ya fara kira, cikin ikon Allah ya ji wayar ta shiga, tashi yayi zaune ya gyara zamansa, yana jiran ya jibta ɗaga wayar, amma har wayar ta kaste bata ɗaga ba.
Ya kira ya kai sau biyar, amma bata ɗaga ba.

Message ya tura mata kamar haka "Dan Allah Hafsa, ba dan ni ba ko sau ɗaya ki ɗaga wayata mana, magana nake so muyi" yana tura nata ya ajiye wayar ya dafe kansa. Mintuna kaɗan ya ji kira ya shigo wayarsa, da sauri ya miƙa hannu ya ɗauko wayar, a zatonsa Hafsa ce amma ya ga sunan Mummy, ya ɗaga wayar ya kai kunnensa tare da yin sallama.

"Sannu Khalil, wato saboda mace ka zama ɗan kanka ko? Ka shirya ka koma aiki ban sani ba, saboda bani da amfani a wurinka, sai kawai ka aiko mini da motarka ko?"

"Ba haka bane Mummy, bana jin daɗi ne, kuma na riga nayi booking ɗin jirgi shiyasa na san at that time babu lallai kin tashi"

"Ai dole kaji babu daɗi, tunda na rabaka da waccan yarinyar mana, laila majnun baban soyayya, da ni kake zancen Khalil" ta katse wayarta.

A saɓule ya ajiye wayar ya cigaba da riƙe kansa.

Fadila kuwa zaune take a

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

1 year ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment