Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk fitar kibiya da tashin kabbara haka wadannan dakaru suka rinqa zubowa qasa kamar kiyashi Suma suna mayar da martani da dalamisan sihirinsu Amma sunqi tasiri daqyar suka samu suka sauka akaci gaba da gwabza bata kashi tsayin lkc sannan sukayi nasarar kaisu qass.




Bayan qarewar wannan mayaqan aljanu sai mutanen birninsu Jawal suka rinqa yanke jiki suna faduwa wani irin baqin hayaqi yana fita ta jikin duk wata qofar gashi dake jikinsu ciki kuwa harda Yarimah Isham tsayin lkc sannan suka samu suka fara farfadowa sannan suka dunguma sukayi cikin gdan sarautar inda Isham yayi musu jagora inda ya killace Gimbiya Samrah suka shiga.
Wani abin tashin hankali suna shiga suka isketa gawa, tashin hankalin da Najmah ta shiga baya faduwa ta rungume yar tata tayi tanata kuka shikenan ta rasa Samrah a lkcn da take matuqar buqatarta, a sanyaye Nurain ya dagota jikinsa ya rungumeta yace “Allah bazai karbi rayuwar Samrah ba face yakasance mafi sani ga dalilinsa ki qaddara zamu sake samun wata samrah din.
Sake narkewa tayi a jikinsa tace “haqiqa nasani kashemin yata akayi amma komai ya farune da sanin Allah shine zai sakamin Kuma ya mayar min da mafi alkhairi" daga haka suka dauki gawarta sukayi Mata sutura suka binneta a wani bangare na gidan sarautar Jawl.




Daganan suka dunguma dakin maita inda aka gwabza yaqin mazan fama tsakanin Nurain da Aljani Lamarud ya mayar gurin da yake ta'annatinsa har daga qarshe Nurain yayi nasarar kashe Lamarud ya sare kansa ya rataye a jikin dirka inda gangar jikin ta zama jini tayi tsiri ta tashi sama daganan Kuma ta zama hayaqi ta qone, daganan dakin da gunkin Harsan yake suka nufa inda suka isheshi ya tumurmushe ya zama gari al'ummar birnin Jawl suka cika da tsananin ta'ajibi.
Bayannan Kuma gidan kurkuku suka nufa suka rinqa fito da daurarrun da aka dauresu bisa zalumci aka rinqa musulumtar dasu sannan aka mayar dasu gdajensu, bayan an gama danan aka Kuma dunguma aka koma fada anan aka yanki filin masallaci aka saka tubalin gini, washegari Nurain da yan majalissar masarauta suka nada Yarimah Isham a matsayin sarkin masarautar Jawl inda anan ne naquda ta kama Najmah mahaifiyar Isham itace ta karbi haihuwar ta sake haihuwar yarta mace, hohoho ga inda asalin kyawun yake kyawun yarinyar ya nunka na Samrah sau uku take sukayi Mata huduba da Muhsinah sunso daukar hanyar komawa gida inda Isham ya dage saidai su bari ayi bikinsa da Nurayyah wadda itama ta musulumta sakamakon wannan ambaliyar ruwa data cinye tsibirinsu mahaifiyarta Juhaira ta mutu ita Kuma Isham ya sake tsintota.




Hakance ta kasance bayan biki suka dauki hanyar garinsu dauke da sabuwar jaririyarsu sunyi tafiyar kwanaki arba'in da biyar sannan suka isa suka tarar da Muftee yabar qasarsu wai yatafi yaqin daukaka musulumci, Basu wani tashi hankalinsu ba sukayi masa fatan alkhairi kasancewar Gurail Uzair ya umarcesu dasu hqr da yawo haka tunda masarautar Jawl ta karbi musulumci Kuma Muftahu ya tafi yada musulumci to Muslumci zai yadu zai fantsama duniya duniya zata kasu kashi biyu duk da haka Muslumci zai mulki duniya.
Mahaifiyar Nurain aljana Badiyyah ita tazo akayi nadin sarautar Nurain a matsayin sarkin Faris sannan akaci gaba da gudanar da abubuwa na shagalin bikin sarauta,

*BAYAN SHEKARU ASHIRIN*


Musulumci ya zama shine addinin da duniya take alfahari dashi a wannan lkcn ya kasance daular Muslumci tana alfahari da masarautar Fazbar saboda ta kasance masarautar data sadaukar da komai nata domin kafuwar Muslumci, a lkcn ne Kuma Mufta ya waiwayo gda bayan ya zagaye duniya da manyan daulolin kafirci ya rugujesu sun koma na Muslumci addinin Muslumci ya zama shine addini me qarfin fada aji a duniya.
Lkcn daya iso masarautar babu Wanda ya ganeshi Amma qirar sadaukantarsa ta yanayin zubin halittar Sarki Nurain da yake dashi yasa suka kasa dakatar dashi har saida yakai ga isa cikin gidan sarautar Gimbiya Najmah tanata bawa Gimbiya Yazidah horon harbi yazo ya tsaya a bayansu yana kallonsu, kamar ance da Najmah ta juya taganshi ta zuba masa ido ya kwance nadin dayayiwa fuskarsa ta matsa gabansa da sauri ta riqo hannunsa tana murmushi tace “tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya halicci mutym biyu masu kama daya tabbas Nurain ne ya sake dawowa a matsayin dan Nurain Ubangiji ya qarawa jinin gamayyar jinsi martaba a idon duniya tabbas gamayyar halitta gaskiya ce tafi halitta daya kyawun gani da karsashin jarumta, muje gida na baka abinsha kaji dana..."
Sarki Nurain ne ya hadasu duka ukun ya rungume yace “nifa waye zaibani abinsha yake matata" dariya sukayi tare suka dunguma suka nufi bangarensu"


_Alhmdllh alhmdllh Alhmdllh_

_Nan ne ya zama qarshen wannan lbr badon nagaji dashi ba saidon wasu dalilai da zasu sani tafiya hutu na wata guda, insha Allahu kafin na tafi zanyi qoqarin kammalawa da_ *_WANI QANGI_* _shima kamar yanda muka gama wannan Allah yabamu ikon gama na gaba lfy,_
_Sai Allah ya sake hadamu a cikin_ *_GIDAN UNCLE RETURN_* wanda _zaizo da sabon salon hikima na rubutu daya bambamta da salon da muke amfani dashi yanzu kada ku manta cigaban _ *_GIDAN UNCLE_* _yananan tafe nanda wani dan lkc,_




_Mu'assalam taku a kullum_
# *UMMUH HAIRAN*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment