Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sarki Urzan da baifishi ba a shekaru yace “kayi sani yakai wannan sarki kamar yanda ka fada mun ratsa Nahiyar nan ne domin cimma wani buri namu, haqiqa hakane" nan ya kwashe komai ya sanarwa da Sarki Urzan hankalinsa yayi qololuwar dugunzuma ya dago yace “idan ka amince ka bani dama nabika domin kafa kalmar Allah inaso na kasance daya daga cikin shahidai wadanda zaa karbi rayukansu a wajen jihadin kafa kalmar Allah"
Da farko Yarimah Nurain yaso yayi turjiya Amma yanda Urzan ya rinqa roqonsa ya sanyashi amincewa a wannan dare Urzan ya Kira Wazirinsa ya damqa masa amanar garinsa shi kuma ya shiga gda, inda Nurain yake kwana kuka yana tuna da ace yana tare da iyalinsa a wannan dare me cike da ni'ima da bazata barsa da kewa ba amma yanzu saidai yayita juyi har ya samu nutsuwa sannan yayi alwala yayi sallah yana kusanta kansa da Allah domin samun rinjaye wajen abokan gaba.
Haka Yarimah Nurain ya wanzu cikin wani yanayi na kewar iyalinsa har zuwa wayewar gari inda sukayi karin kumallo suka dauki hanyar tsibirin Qursum tafiya ce data hada sadaukan gaske shiyasa sukeyinta da karsashi sallah da cin abinci ne kawai yake tsayar dasu a haka suka iso wani daji da ake kira Darul Nar shi wannan daji ya kasance matattarar batoyi da iyalansa idan sukaga dama yanzune zasu sanya masa wuta ta kama ganga ganga ta tinqayin tsiri sama.




Duban Sarki Urzan Yarimah Nurain yayi yace “me ka sani game da wannan dajin da muke tunkara?" Duban dajin Urzan yayi jikin jinjina lamarin dajin yace � ya kasance matattarar batoyi a duk shekara yakanyin watanni tara yanaci da wuta watanni uku shine kawai dajin yake kasancewa a wannan yanayin da muka rinskesa, wannan daji ya kasance yanada tsayi sosai a wajen tafiya wacce idan muka shigeshi zamu dauki tsayin mako biyu a cikinsa Wanda a yanzu zancen da nakeyi maka saura kwanaki goma sha biyu wannan daji ya kama da wuta inda duk wata halitta dake rayuwa a cikinsa takeyin qaura a cikin watanni taran nan harsai wutar ta mutu sannan su dawo akwai hanya guda daya bayan wannan saidai ta kasance tanada tsayi zamu dauki tsayin wata daya da mako daya kafin mu fita daga wancan dajin sabanin wannan da zamu fita cikin sati biyu"





Shiru Nurain yayi tare da dakatar da dakaru ya zaburi dokin da yake Kai ya nufi cikin dajin da mugun gudu kamar walqiya ya rinqa zagaya dajin yana tare da nazartarsa sannan ya juyo ya fito daga dajin ya dawo ya sauka daga dokin ya zauna tare da duban Shugaban fatake Juhair da Sarki Nurain yace “Ta cikin wannan dajin zamu ratsa mu wucce Juhair ka daure mana dajin nan kai kuma Nu'ad ka kasance a bayan dakaru lkcn dana shiga dajin nan naga sawayen wasu manyan halittu, a cikin wannan dajin babu fadan gaba da gaba saidai ruwan kibbau tabbas akwai wasu halittu dake rayuwa a cikin dajin nan bayan batoyi da iyalansa na baku nan da wayewar gari ku gama shirinku har kullum Ina fada muku wata uku ne damu munci watanni biyu, tabbas saura wata uku Gimbiya ta haihu wanda nake fatan duk rintsi da tsanani ya kasance bayan Gimbiya nine na biyu da abinda zata haifamin zai fara arba dashi a duniyarsa"........
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:57 PM - Ummi Tandama: *MM* Haka al'amarin ya kasance a wannan daren duk wani shiri daya kamata ayi Saida akayishi aka gama suna tashi da asuba kari kawai sukayi suka dunguma cikin neman saa da kiyayewar ubangiji suka ratsa wannan daji me hatsarin gaske, haka sukayita tafiya tsayin kwanaki biyu babu wani Abu na cutarwa da sukayi karo dashi.
A daren rana ta uku ne sun yada zango domin yin sallar isha suna tsaka da alwala suka rinqa jiyo wani sauti me amo tare da wani taku me kama da girgizar qasa yana tunkarosu take dukkannin su suka mimmiqe tare da zare makamai sukari rabu biyu wasu suka kalli gaba wasu suka kalli baya, ihun ya daina tashi sai takun sawayen da wani huci da yake qara kusanto su.




Suka qara gyara tsaiwarsu suna masu ambaton sunan Allah a bakunansu haka wannan taku yaci gaba da tunkarosu tsayin rabin saa sannan suka fara hango inuwar wani gungu na wasu manyan dodonni suna nufosu ba dakarun ba hatta Yarimah Nurain saida zuciyarsa ta kadu da ganin girman wadannan dodonni ya hadiye wani yawu me daci lkcn da hucin numfashin dodonnin ya matsosu sosai tazarar dake tsakaninsu batafi ta taku goma ba, ja sukayi suma sukayi turjiya suka tsaya suka daga bakunansu sama suka kece da wata mahaukaciyar dariya data sanya ganyen bishiyoyin dake dajin suka rinqa kadewa suna zubewa wata wuta na tsiri tana tashi sama daga bakunan wadannan miyagun dodonnin.
Sun dauki lkc suna wannan dariya data sabbabawa dakarun Yarimah Nurain zubewa a qasa suna masu toshe kunnuwansu, dariyar ce ta tsaya cik shugaban dodonnin ya matso sosai ya sanya qafa yayo sama da wani itacen bishiya daya karye sakamakon wannan wuta dake fita ta bakinsu, cakar qasa yayi dashi take wata qura me mugun qarfi ta turnuqe dajin, daqyar dakarun Yarimah Nurain suka miqe tsaye suna masu ambaton sunan Allah.




Cikin wani matsanancin al'ajab qurar ta lafa dodonnin suka rinqa toshe kunnuwansu tare da miqar da hannuwansu suka nufo su Yarimah Nurain Suma wadannan dakaru suka rinqa ja da baya tare da saita kibbau suka fara sakar musu harbi, wani qarin tashin hankali babu abinda harbi yake yiwa wadannan dodonni saima kawai susa hanu su shafe kibiyar, abinda ya daga hankalin wannan runduna kenan suka rinqa gwada basira iri iri amma taqi tasiri dodonnin sai barna suke musu su kuma sun kasa ko kartar daya cikinsu.
Haka aka kwana ana wannan gumurzu mayaqan Yarimah Nurain sun fara gajiya ga bacci bayan ketowar alfijir wani dodo yayi nasarar saran Sarki Urzan ya qwallah wata qara tare da sakin kabbara ya sokawa wannan dodo takobi a ramin cibiyarsa, dodon yayi wani gunji ya saki ihu ya fadi qasa yana burburwa sarki Urzan ya fincike takobinsa take ta fito da hanjin cikin wannan dodo ya fadi qasa matacce.




Wannan saa tayiwa dakarun dadi suka rinqa soke dodonnin nan da tokubba a cibiya sunata mutuwa tare dayin kabbara akan kowanne sara, abin tashin hankali shine zubar da dodonnin sukeyi amma kamar qara yawansu akeyi dabara ce ta fadowa Yarimah Nurain ya rinqa karanto wasu addu'o'i yana tofawa dodonnin take suka rinqa zubewa matattu wadanda basu zube ba kuma suka rinqa saran junansu tsayin yini suna yaqar junansu har saida suka qare kaf.
Hamdala Yarimah Nurain yayi suka zube Suma cikin dodonnin suka kama baccin wahala basu farka ba sai dare suka fita cikin jinin dodonnin suka nufi wata idaniyar ruwa suka tsaftace jikinsu sukayi sallolinsu sannan sukaci abinci wadanda aka illata aka basu magani aka dorasu saman wani aljani akaci gaba da tafiya.




A rana ta shidda ce suna tafiya cikin dajin acan gabansu suka rinqa qanin qasa tana tsagewa wasu qananun halittu suna fitowa masu kama da tsutsotsi kafin ka ankara sun yanyame maka jiki suna yanyame mawa mutun jiki zasu fara zuqar jininsa abin babu kyawun gani wani abin tsoron har ido basu bari ba kuma hatta wanda yake sama tsalle sukeyi su cafkeshi nan fa maza suka rinqa zubewa jikinsu kamar an huhhuda hankalin wadanda basukai ga tabawa ba ya tashi cikin tsananin jarumta Yarimah Nurain yayi kukan Kura ya ya zaro takobin muzhar dake rataye a kafadarsa yana mai karanta kalmar shahada take wani farin haske ya gauraye dajin Wanda ya bi wadannan halittu ya narkar dasu suka zama jini cikin qanqanin lkc jinin ya bace bat.




Dakarun da suka zube ne suka rinqa miqewa jikinsu yana salubewa take suka koma asalin fatarsu wannan hujajjiyar fatar ta salube suka rinqa kallon jikkunansu suna tasbihi ga Ubangiji.
Anan ma saida suka huta sannan suka sake nunkawa cikin dajin sukaci gaba da tafiya zuciyar Yarimah Nurain cike da begen matarsa Gimbiya Najmah da tunanin halin da take ciki idan abin ya isheshi sai idanunsa su kada suyi jawur yayita hucci yanacin alwashin cewa duk wanda yakeda hanu wajen rabashi da matarsa idan ya kamashi dakansa zai bawa Najmah takobi ta sare kansa koma wanene.
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:57 PM - Ummi Tandama: *MM* Lamarin Najmah kuwa lkcn data farka daga wannan dogon baccin ta tashi a firgice tare da salati take ta diro daga gadon tana qarewa dakin kallo, wani kusurwa kusurwa ne da dakin gefe wani teburi ne dauke da wani dan qaramin gunki sai wani qaramin kurtu dake bude wani turiri na tashi a cikinsa, jan qafarta tayi da sauri ta matsa ga wannan kurtu ta leqa tare dayin Bismillah take fuskar Yarimah Nurain ta bayyana a cikin wannan kurtun yana nade da rawani mamaki ne ya cikata ta qara matsawa tana me sake leqa wannan kurtu.
Ga mamakinta sai taga ya tsugunna a daidai wani dutse ya dage wani qaramin dutsi saiga ruwa ya bayyana ya sanya hannunsa ya ware rawanin fuskarsa ya debo ruwan yana alwala dashi bayan ya gama ya sake maida nadinsa, ya koma ya tayar da sallah mamaki ya cika Najmah ta juya da sauri da nufin fita daga dakin da take ciki tana fadin.
“Na kasance Ina alfahari da samunka a matsayin miji uban dan da zan haifa aljannata Kuma duniyata gani gareka mijina, ina nake me hakan yake nufi? Ina ka boyemin?"




Ta saba idan suna cikin nishadi wannan yan baitocin take rera masa shikuma duk inda yake zai nufota yana fadin “komai nisa zanzo gareki matata na bayyana gaba gareki Ina mai qanqan dakai nasan bazaki barni na tozarta ba" jin ta rera baitin har sau uku bai amsa ba yasata bude idonta abin mamaki kawai saita ganta a wata duniyar matsafa, tayi baya da sauri tana mai furta “Subhanallahi" ji tayi an kece da dariya ta bayanta dariyar data gigita nutsuwarta ta durqushe qasa da sauri cikinta yana hautsinawa, ta dauki lkc a durqushe kafin sautin muryar ya tsaya daidai lkcn da juyawar cikinta ta lafa ta bude idonta da sauri kawai sai taga wata kyakkyawar budurwa tsaye gabanta tanayi mata murmushi,
Tsoronta ne ya nunku ta miqe da sauri tana fadin “wacece ke me kike nufi dani yake wannan mushrika Ina kika kaimin mijina?" Dariya Nurayyah ta kumayi tace “yake wannan Gimbiya kiyi sani ni nice me nasara cikin mutum sama da dari dake farautarki naje har gurin mijinki na satoki a gabansa batare daya iya komai ba tabbas na cancanci a jinjina min"
Numfashi Nurayyah ta sauke tace “sunana Nurayyah ya ga Matsafiya Juhaira wadda ta gaji tsafi a gurin mahaifiyarta, tabbas inada dalilai biyu qwarara da suka sanyani dagewa kaida fata wajen ganin na satoki na kawoki fadar mahaifiyata a yayin da mahaifiyata take da dalili biyu itama,




Dalilina na farko shine muradin cikar burina na mallakar mijinki a matsayin nawa Wanda bazai taba cikaba harsai na saceki na shiga jikin ganganr cikinki yayi tarayya dani a zuwan kece, tabbas alqaluman tsafi sun nuna hakan itace nasara ta, dalili na biyu na daukar fansa akan kashemin haskena da kikayi a duniya aka, aka daina kallo a matsayin sarauniyar kyawawan duniya aka koma kallonki har ya kasance duk wani isasshe a duniya burinsa mallakarki tabbas ina baqin ciki da wannan abin wannan dalilin yasa naci alwashin daidaita rayuwarki bayan burina ya cika,
Dalilan mahaifiyata kuwa shine na farko mallakar zoben Zaujatul Noor dake saye a yatsanki Wanda nayi yunqurin cireshi na kasa tun kina bacci na biyu kuma shine haihuwar wannan yaron da yake cikinki daya kasance gamayyar halitta wanda zaizo ya buwayi duniya, bincike ya nuna cewa mutum na biyu da zai kallah bayan mahaifiyarsa zai kasance shine masarrafin rayuwarsa duk abinda ya dorashi akai shi zaike aikatawa, wannan dalilin yasa mahaifiyata tayi alqawarin zata zama itace wannan masarrafin domin cikar burinta na mallakar sarakunan duniya a tafin hannunta, yake wannan gimbiya kiyi sani bayan cikar wadannan muradan namu tabbas zamu massheki gawa mu cillaki cikin ruwan dake qasan tsaunin nan kifaye suyi kalaci da sassan jikinki"




Murmushi Najmah tayi ta juya ta fuskanci Nurayyah sosai tana me fadada murmushinta tace “tun lkcn da rayuwata ta fita daga cikin duhu irin Wanda rayuwarki take ciki a yanzu na fahimci cewa ba duka burine ne da muradai suke cikaba saboda bakai kakeyiwa kanka ba Allah ne meyin komai a duk lkcn da yaso, haqiqa da buruka suna cika duka da baku samu damar satoni ba duk da haka na godewa Allah daya hadani da jarumi Kuma sadaukin miji tabbas bana ko inkari yana tafe gareni"
Tsawa Nurayyah ta daka Mata tace “qarya kikeyi yarinya babu mahaluqin da ya Isa yazo gurinnan da rayuwarsa domin hatsarin dake tattare da zuwa nan yafi maka sauqi ka fada wuta ka qone qurmus...." Itama tsawar ta daka Mata tace “qarya kike mushrika kafira wlh sai mijina yazo nan gurin da taimakon ubangijin muslumci Kuma saiya karya daularku ni ni dakaina zan datse kanki daga gangar jikinki na jefa gangar jikinki cikin ruwan dake gudana a qasan tsaunin nan kamar yanda kike da burin yimin, Nurayyah ni dake shege ka fasa dama fajirar zindiqiyar uwar taki abar tausayi abar jefewa tababbiya mara sauran albarka..."



Daga wa Najmah Nurayyah hannu tayi tace “ya isa debabbiya kada ki debowa kanki bala'i nan a cikin fadata kike dolene kiyi biyayya domin samun abinda zaki kuks da kanki idan kinqi zan iya watsi dake ki rube kiyi tsutsa anan na sanya qwarangwal dinki abin jinginewa Ina kallonsu kamar yanda na wadannan jabberun masu taurin kan ya kasance"
Dariya Najmah ta kwashe da ita ta matsa gaban Nurayyah ta sanya hannu ta Dago kanta tace “au waike da kin dauka na dogara da komai naki har na sanyashi abin tallafin rayuwata? Hhhhhh lallai kinyi kuskure domin ni na dade da sanin baki isa ki ciyar dani ko ki shayar Dani ba kazalika kema bai isheki ba fajira kawai"




Tana fadin haka ta juya ta shiga dakin da ta farka ta ganta a ciki ta sanya want qoqo ta debi ruwa tayi alwala ta dauki wannan gunkin tayi cilli dashi waje ta saiti gabas ta tayar da sallarta tayi sallolinta tananan zaune taji shigowar Nurayyah ta ajiye mata gasashen nama ta juya ta fice bata kobi takan naman ba ta bude wata batta dake saqale a kafadarta ta kwankwadi madararta ta koma ta zauna cike da shauqi da qaunar mijinta tare da tunanin halin da yake ciki na kadaicin rashinta yanzu haka.
Cikin kwananta na hudu ne matsafiya Juhaira ta samu nasarar tserewa daga filin dagar ta iso gda saida ta kwashe tsayin wata guda tana jinyar Sara da sukar da tasha a gumurzun kafin ta warware kullum zatazo ta duba Najmah sau biyu tare da kawo Mata abinci,
Zuwa yanzu rashin Yarimah Nurain ya fara damunta kullum da tunaninsa take kwana take tashi gashi kullum cikinta qara girma yakeyi, a mafi yawan lokuta tana kwana tana kuka tare da rera baitocin yabo ga abin qaunarta amma kullum babu wani sauyi.




***********


A bangaren Yarimah Isham kuwa lkcn da ya dauko hanya domin isowa wannan tsuburi sai yayi katarin haduwa dasu Boka Rundatu nanfah sabon yaqi ya rincabe aka rinqa gwabzawa har tsayin kwanaki uku kafin matsafiya Juhaira ta samu nasarar sulalewa ta gudu inda shikuma Rundatu ya samu nasarar sace Yarimah Isham ya nufi tsaunin Qursu dashi cikin hakin suma.
Yana zuwa ya hadashi da Uddatu da Uddaru mahaifan Najmah yaci gaba da azaftar dasu da nau'uka na azaba, cikin wadannan kwanaki ya suna shan wahala don ko abinci basa samu daga wannan azzalumin mushriki Boka Rundatu,
A wannan lkcn ne Kuma tafiya take qara miqawa gasu Yarimah Nurain suna haduwa da abubuwa kala kala nau'ukan halittu mabambamta wasu su yaqesu wasu kuma suyi amfani da hikima su qetare musu har suka iso dajin da yake gaf da dajin Qursu inda nanne matattarar masifa da bala'i nanne ake kira dajin mutuwa dajine da ko tsuntsu baya qetarawa ta samansa face ya zama gawa.
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:57 PM - Ummi Tandama: *MM3738* Anan suka qarasa kwana cikin halin gajiya kashegari suka sake gyara dammara suka nufi dajin Qursu Wanda shine dajin da kogon Qursu da iyayen Najmah suke ciki da Kuma Yarimah Isham a yanzu qarqashin sahalewar boka rundatu, tafiya ce me tsayi tsakanin wannan daji da kogon qursu.
Sun dauki lkc me tsawo kafin su Isa inda kogon yake suka tsaya suna qarewa dutsen da kogon yake kallo cikin mamakin qanqantar dutsen dubansu Sadauki Juhair yayi yace “ya shugabana wannan dutsen ya kasance daukarshi akayi aka daura a gurin saimun matsar dashi zamu samu damar ganin hanyar da zamubi mu shiga wannan kogo"




Qarewa gurin kallo yayi sannan yabada umarnin a bari da safe sai ayi aikin dauke wannan dutse kasancewar dare ya riga yayi haka kuwa akayi nan batare da bata lkc ba suka fara kafa tantina sannan suka hada wuta suka gasa naman da suka farauto a daji kowa ya yanka yaci sukayi sallar Isha suka kwanta, baccine ya fara daukarsu na wani dan lkc,
Ji Nurain yayi kamar an tsikareshi ya tashi da sauri tare da salati yana waige waige yakeyi miqewa yayi ya fita daga nasa tantin ya tsaya a tsakiyar gurin yana kallon gabas da yamma kudu da arewa kallo irin na nazari kafin ya fara takawa a nutse ya Isa jikin wannan dutsen yati Bismillah yasa qafa ya tureshi ya tsaya yana kallon yar siririyar hanyar da zata sadashi da cikin ramin.
Fara taka matattakalar yayi tare da Bismillah ya rinqa tafiya a qasan matattakalar har ya dira wani fili fetal da babu komai a cikinsa sai wata bishiya guda daya, mamaki ya sanya Nurain tsayawa yana kallon bishiyar kawai sai yaga bishiyar ta rikide ta koma wani qaton maridin aljani.




Wani gunji wannan maridi yayi ya nufo Nurain gadan gadan inda shikuma Nurain ya zare wannan takobin tasa ya tsaya tare da turjewa yana jiran qarasowar wannan maridi, isowar maridin keda wuya kafin qiftawar ido Yarimah Nurain ya daga takobin nan ya sokewa wannan maridi ciki take ya fadi qasa matacce.
Ya zare takobinsa ya goge jinin ya mayar da ita cikin kubenta ya sake nausawa cikin wannan kogon gabas yakebi saboda yafi hangen nasara acan, wani surquqi ya shiga me duhun tsiya dole tasashi zare takobinsa haskenta yanayi masa jagora yana wucce gurare mabambamta amma bayacin karo da komai har ya isa wani guri da ya kasance samansa budadde an zuba kayan qawa kala kala ya tsaya yana nazarin gurin tare da mayar da hankalinsa ga kallon wasu qofofi guda biyu da suke rufe kowacce an rubuta Maut a jikinta.




Matsawa yayi jikin ta farko ya sanya tsinin takobinsa ya yanke qatuwar sarqar da aka daure qofar da ita yayi Bismillah ya shiga qofar ta koma ta datse, wani gunji da haniniya na tashi a bayansa ya juya da sauri yana mai duban gurin yaja baya ya goce a tsorace saboda bangazar da wani qosasshen Zaki ya kawo masa.
Miqewa yayi da sauri kafin ya gama daidaita tsaiwarsa zakin ya Kuma yo kansa ya cukumeshi da kokawa suka rinqa kokawa a burin wannan zakin ya kama kan Nurain ya gutsure shikuma burin Nurain ya yaga bakin zakin biyu amma kowanne ya kasa kaiwa ga cikar burinsa.
Ganin wankin hula yana neman Kai Nurain dare ne yasashi yin wani tsalle yayi katantanwa a sama ya cafki maqogwaron wannan zakin suka Kuma zubewa a qasa zakin sai yaqushinsa yakeyi shikuma yaqi sakinsa har yayi nasarar zare takobinsa ya caka masa a maqogwaro ya sakeshi tare da zare makaminsa ya fadi gefe yana mayar da numfashi.




Ya dauki kusan saa daya a gurin kana ya miqe ya sake nausawa cikin wannan dakin ya Kuma bude wani daki ya shiga, wata qara ya rinqaji tana tashi ya nufi inda yake jiyo qarar da sauri ya daki qofar ta bude ya nausa ciki tare da haska hasken takobinsa da sauri yaja da baya ganin wasu narka narkan kunamu ne guda biyu suna saqale da juna suna ganinsa suka rabu sukayo kansa da wani gudu kama dana walqiya yayi saurin matsawa tare da sakar musu harbi a lkc daya.
Zubewa sukayi a tatattu hakan ya bashi damar direwa qasa wata qofar ta bude ya danna Kai ciki ga mamakinsa babu komai a cikin wannan dakin har yakai qofar gaba inda anan ya tarar da wata halitta kwance tanata sharar bacci ta cika dakin gabadaya babu wata hanya da zai taka ya wucce, tsayawa yayi yana nazarinta kafin daga bisani ya fara tafiya ta samanta yana karanta wasu addu'o'i wannan halitta bata farka ba haka ya wucce wannan dakin salin alin ya nufi na gaba....
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:57 PM - Ummi Tandama: *MM 3940* Kutsa Kai yayi cikin wani daki ya fara dube² na tsayin wasu yan mintuna sannan ya samu sa'ar bude qofar dake fuskantarsa ya shiga wata qatuwar fada ce da aka qawatata da duk wani nau'i na Jin dadin wannan qarni, bai wani bata lkcnsa wajen kallon wannan qawar ba ya kutsa Kai ya fara keta bangarori na fadar har yakai qarshinta,
A qarshen ne yaji wata tsawa kamar saukar aradu ya tsaya cik tare da zare takobinsa yana jiran isowar mamallakin muryar tsayin yan daqiqu sannan yaji an dafoshi ta baya ya juya da sauri sukayi ido hudu da Boka Rundatu abinda ya sanya Nurain ja da baya da sauri yana me kau da kai ga barin kallon wannan munin, dariya Rundatu ya kece da ita yace.
As as yaro da maza a gabanka haqiqa kaidin macene tunda har wannan qaramin munin zai firgita ka had takai hantar cikinka ta motsa, haƙiƙa naga namijin ƙoƙarinka na iya keto dazuga ta tsaunuka har takawoka ga shigowa wannan fada yakai wannan ɗan sarki kayi sani cewa baa taɓa shigowa gonata a fice salim alim kamar yanda ka keta alfarmata hsr ka ratso gonata to nima shakka babu zan keta martabarka na datse igiyar numfashi daga ƙirjinka"




Dariya sosai lamarina lamarin ya bawa Nurain yayita harda riƙe ciki yace "ita saa a gurin me nasara take yakai wannan mushirikin boka kayi sani nasara tana gurina saboda haka mubar batawa juna lkc kabsni abinda nazo nema ta salama ko kuma na cire numfashi daga jikin ruhinka na ɗaukesu na fice dasu kana kwance masshashe gawa bakada ikon hanawa"
Bai ida rufe bakinsa ba yaji Boka Rundatu ya daka masa tsawa yace 'nasarar tawace kwashasshe marashin albarka' to fahimta da nurain yayi rundatu na bata masa lkc ya sanyashi zare takobinsa shikuma rundatu ya rintse idonsa saiga wata irin takobi me kai ukuta bayyana a hannunsa, suka ja da baya suna tayar da ƙura sannan sukayi tsalle suka ruguntsume da azababben yaqi.
Hohoho wannan haɗuwa tabani citta saboda yanda ake gwabzawa abin zai burge me kallo sun ɓata sa'o'i suna gwabzawa kafin nurai yayi nasarar kai rundatu ƙasa ya jashi ya ɗaureshi jikin wata dirka yana cikin halin suma sannan ya cusa kai cikin dakin da Uddatu da Uddaru suke ɗaure.




Koda Uddatu yaga Yarimah Nurain sai yacika da tsananin mamakin wanzuwar bil'adama a wannan guri me matuƙar haɗari, to fahimtar kallon tsoro da mamakin da sukeyi masane yasashi kwance rawanin fuskarsa ya matsa yana me kwancesu yace 'nakasance suruki a gareku sunana Nurain Yariman masarautar FAZBAR dake ƙasar Faris haƙiƙa kun kasance ababen girmamawa a gareni'
Daga haka Nurain bai sake furta ko kalma ɗaya ba ya juya ya nufi hanyar fita daga fadar ganin hakanne ya sanya Uddatu miƙewa yabi bayansa da sauri haknne ya sanya Isham da Uddaru suma suka rufa masa baya sunyi tafiya me tsayi batare da kowa yace komai ba har suka fice daga cikin wannan kogo hasken rana ya bayyan garesu suka shiga murna Nurain ya zuba musu ido yana mamakin irin murnar da sukeyi.
Hanyar da zata sadashi da inda jama'arsa suke ya nufa sudai kawai binsa sukeyi Isham ne ya gaji da shirun ya magantu da cewa 'ka kuɓutar dani a wannan karon hakan ba yana nufin zakaci gaba da kuɓutar dani ba kuma wannan bashine yake nufin kayi nasara akaina ba, inanan zanci gaba da shirina domin ganin na dawo da abinda yake mallakina gareni yakai wannan ɗan sarki kayi sani nanda wani ɗan ƙaramin lkc izzata da buwaya ta zaake ambata a duniya nine zan gusar da taka ƙarshena rabaka da rayuwarka"




Shidai nurain bai tanka

Please Login or Register in order to submit comment