Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta asusuna 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 idan VTU zaka/kiyi Kuma Zaki turane ta wannan number 09031307566: kada ki tura VTU ta number farko domin bazan gani ba only evidence of payment zaki turo a ita._
_Mutanen Niger ma zaku iya turo katin orange wanda zaiyi daidai da kudin dana ambata a sama ta number farko, na gde sai najiku._

_Sannan akwai littafin *WANI QANGI* 200 ne VIP 400 idan kina buqata Zaki tura ta wadancen numbers dake sama ko ta account din dake sama_
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:36 PM - Ummi Tandama: *MASARAUTAR MAYU*
*_(HISTORICAL AND ADVENTURE)_*


*WRITING AND STORY*


*UMMUH HAIRAN*


*MARUBUCIYAR*
👇🏻
AMINIYA KO KISHIYA
HABIBULLAH
QUEEN FARHA
GIDAN UNCLE
ADANDI
WACECE NI
AURAN BAZAWARA
DHOOM ISHAQ
MATAR LAMEER
DUBAI
AND NOW👇🏻
MASARAUTAR MAYU!
AND
WANI QANGI



Free *P 9-10*


Qasa Najmah tayi da kanta cikin yanayin mamakin wannan sarqaqqen qulli daya qulle zuciyarta tanaji tana gani aka zaunar da ita saman wasu kujeru guda biyu da aka qawatasu da kwalliyar dutsen lu'ulu'u da jauhar dubanta Yarimah Nurain yakeyi sosai ta dago idonta cikin alqabbar dake lullube da fuskarta suka hada ido yayi saurin dauke idonsa tare da dora hannunsa saman wani tire na gold ya dauki wani siririn zobe da yaketa walwali da daukar ido ya sunkuya a gaban Najmah ya zura hannunsa ya kamo hannunta ya lumshe idonsa daidai lkcn da fadar ta dauki wani shiru,
Yatsanta ya kama ya zura Mata zoben tare da Kama hannunta nata sosai cikin nasa yanajin dumin jikinta na saukar masa da wata kasala ya janyo hannunta daidai fuskarsa ya dora hannunsa nata a goshinsa, fadar ta dauki wani ihu suna fadin “Allahu Akbar shagali Jama'a musha lemo muci dabino mu some raquma yau yariman mu ya zama angon gimbiya Najmah" wasu hawayene suka zubo mata batasan sanda ya janye hannunsa daga nataba ya koma ya zauna wani dattijo ya shigo shima da yan bidi'arsa a bayansa ya gurfana gabanta ya ajiye wani qaton tire ya fara wasu addu'o'i na tsayin wani lkc kafin ya zana qasar ya dago ya kalli Yarimah Nurain yace “haqiqa wannan auren akwai albarka a cikinsa harda rabo Amma akwai rikici me yawa da zai biyo bayan kammaluwar komai"




Jinjina masa hannu yayi ya miqe ya fice hakadai mutane kala² sukayita shigowa kowa yana nasa surkullen a cewar Najmah ya fita Sarauniya Badiyyah ta miqe ta qaraso inda Najmah ke zaune ta kamota tace “atashi daga taro gimbiya ta gaji tana buqatar hutu"
Tana gama fadin haka ta kamo Najmah ta miqar da ita ta nufi wata hanya da ita ashe bangarenta Sarauniyar Badiyyah ne, basu tsaya ba saida suka dangana da wata babbar fada Sarauniya Badiyyah taja ta tsaya daidai lkcn da barorin suks rinqa zubewa a gabanta ta dubi wata amintacciya daga cikinsu tace.
“Ki Kai gimbiya wancan dakin da aka tanada dominta ina buqatar ta huta sannan ta kasance cikin tsaron Allah kafin lkcn da zaa gama shagalin biki a miqata ga mijinta" Kama hannunta wannan baiwa tayi ta nufi wata qofa ta bude suka shiga nan din ma wani bangare ne abin kallo da qawa an qawatashi da duk wani qyale-qyalen zamani da duk wani Abu na more rayuwa da jin dadinta, gwauron numfashi Najmah ta sauke ganin yanda wasu kyawawan yammata suketa bayyana duk inda ta juya,
Zagayesu sukayi suna wata irin waqa me ratsa jiki a haka suka rakata wani daki suka tsaya a bakin qofar ita da wannan amintacciyar baiwar ga mamakinta sai taga wannan baiwar ta zube a gabanta tace “ranki ya dade sunana Ishmiyya na kasance baiwa a wannan masarauta Kuma daya daga cikin amintattun bayin da Sarauniya ta zaba domin kasancewa tare dake da baki kulawa shin ko kina buqatar wani abu?"




Lumshe idonta tayi ta budesu akan Baiwa Ishmiyya tace “ina buqatar sanin abubuwa da yawa game da wannan masarautar da kuma dalilin da yasa Yarinmanku yake boye fuskarsa sannan da dalilin da yasa aka satoni aka kawoni cikinta shin wanne addini kukeyi Kuma wanene ubangijin Annabi Sulaimanu Dan Dawud da naji kuna yawan ambata a cikin wannan masarauta?"
Qasa wannan baiwa tai da kanta tace “ki gafarceni ya shugabata cikin tambayoyinki biyu kawai nake da ikon baki amsa sauran kuwa bakida me baki amsa face mijinki shugabana Yarimah Nurain" da sauri ta sake cewa “mun kasance munayin aure ne idan abin bauta Harsan ya amince ganyen suturar mace ya fadi a gaban mijin da ya zabs Mata sannan ne zaa kaisu yasa musu albarka daga haka sai su fara zaman aure to ku ya naku auren yake kasancewa albarkar wa kuke nema a cikin aurenku?"
Murmushi baiwa ishmiyya tayi a ranta tace “kafuri kafuri ne dama akwai wani abin halitta da zaka nemi albarkarsa da sahalewar sa cikin al'amuran rayuwarka?" Amma a fili sai tace “insha Allah zan baki wanna amsar Amma da farko ana buqatar kiyi wanka ki sha madara sai mu zauna nayi miki bayanin abinda kikeso ki sani ya shugabata"




Rakata tayi har bayin ta taimaka Mata ta cire Mata kayanta sannan ta ware Mata nadin fuskarta taja ajiyar zuciya tace “barakallahu ahsanal khaliqin" daga haka ta juya ta fice daga bayin ta barta domin yin wanka.
Koda ta gama wannan ta tsane jikinta da wani qyalle ta fito saita tarar da mayukan shafa da turarukan musk kala kala da turaren alharini, mayukan ta dauka ta shafa ta dauki turaren alharini ta shafa a wasu bangarori na jikinta shikuwa musk din bata tabashi ba ta koma ta zauna bayan ta sanya kayanta daidai lkcn da baiwa Ishmiyya ta dawo bayanta wasu barori dauke da manyan tire na abinci suka ajiye suka rusuna suka dora hannayensu saman goshinsu suka juya suka fice.
“Abinci baiwa Ishmiyya ta hada mata ta rinqa bata a baki tace “Mun kasance muna bautawa sarki guda daya Wanda bashida tsara bashi da abokin gamayya Wanda ya aiko annabi sulaimanu da gaskiya kuma ya sanyashi jakada gareshi domin aika saqon musuluncu zuwaga yayan annabi Adamu da Nana Hauwa'u wadanda suka kasance kakanni talikai"




Numfashi ta sauke tace “ya shugabata kiyi sani Ba kowa bane wannan abin bauta namu face Allah sarki daya gangaran gagara gasa Wanda bashida kishiya bashi da da bashi da Mata bai bayu wa qani ko qanwa ba shi tal ne Kuma qwal Wanda buwayarsa ta buwayi duk wata halitta dake rayuwa a doron qasa ni'imarsa ta kewaye duk wata halitta dake cikin ruwa ikonsa ya zagaye duk wata halitta dake qarqashin qasa baiwarsa ta lullube duk wata halitta dake sararin samaniya,
Ya shugabata ubangijina bai tsaya anan ba izzarsa da qarfin buwayarsa bata tsaya iyanan ba domin shine ubangijin kowa da komai shine mahaliccina shine mahaliccinki shine mahaliccin sarki Fauwaz shine mahaliccin sarki Jamal shine ya halicci Yarimah Nurain shine ya halicci dokin da kika hau shine ya halicci kyanwar nan dake zagayawa tsakina dake.
Sannan yakasance me bada iko akan fitar numfashi zagayawa iska da gudanar ruwa a saman qasa ya kasance shine me saukar da ruwan sama tsirrai su fito sannan ya rayasu har zuwa lkcn da zasu fitar da amfani mutane aljanu dabbobi da tsuntsaye su tsinka suci,
Ni'imarsa ta gagari lissafawa ya shugabata idan yaga damar rayawa yakan yakan fitar da rayayye a cikin matacce ya rayu babu uwa babu uba kuma yayi rayuwa me ingancin da me uwa da uba basuyi ba idan kuwa yaga damar kashewa ayarsa ce ya zare numfashina ko nake a take ya masshemu gawarwaki,




Baifa tsaya iyanan ba har saidai ya game duniya da halittinsa Kuma ya sanyamu muyi biyayya wa umarninsa ya aiko annabawa da manzanni domin su zamo jakadu a garesa ya umarcemu muyi abubuwa da yawa wanda cikinsa ya halatta mana aure domin samun nutsuwar zuciya da hasken ruhi Kuma ya sanya mana shauqi da sha'awar baren jinsi garemu mace takanyi sha'awar namiji inda namiji shima yakanyi sha'awar mace Wanda yake haifar da kusanci ta hanyarsa ne zaa samu kadaici daga kaidaici sai wani Abu ya faru bayanshi kuma idan yaga dama saiya sanya abinda ya fita da wanda ya shiga tsakanin mace da namijin ya hadu ya bayar da da a cikin uwa cikin mahaifa ya rayu da dumin buwayar ubangiji ya rinqa girma ana canza masa halitta tsayin watanni tara sannan a haifesa Allah buwayi gahara misali kenan.
Karkice ya tsaya iyanan haka zaiyita juya bawansa daga jariri ya zama yaro daga yaro ya zama babba daganan Kuma tsufa yashigo yayita wadataka da abubuwan tasarifin rayuwa, shin meye zai hanaka ka bauta masa?"
Dagowa Najmah tayi cikin matsananci mamaki tace “lallai wannan Ubangiji ya Isa buwayyeyen Sarki to a wacce nahiyar shi yake Kuma meye alaqarsa da Ubangijin masarautarmu Harsan kums meye alaqarsa da Ubangijina Rundatu?"





Girgiza kai Ishmiyya tayi tace “ba komai banesu face ababen halitta Harsan ya kasance qirqirarren abu wanda Sarki Gesbatin na masarautarku ya qirqireshi shekaru dubu daya da suka wucce a matsayin abin bautarsa a wannan lkcn ne Kuma wani matsafin aljani Lamarud yazo wuccewa ta qasarku kwai sai yaga wannan gunki ya bashi sha'awa kasancewar a adinin musulumci bamusan maita ba mudai munsan kambun baka,
Shikuma aljani Lamarud ya kasance saboda tsafinsa yakan sha jinin aljanu da mutane har yakan iya cin naman mutum danye, wannan dalilin yasa Nahiyar da yake suka koreshi to shine fah da yaga wannan gunki sai ya shige cikinsa ya buya, ya rinqa amfani da qarfin tsafinsa yana juya zukatan mutanen wannan masarauta na wancan lkcn har suka amince shine ubangijinsu ciki kuwa harda sarki Gesbatin daya qirqiri wannan gunki dakansa.
Ganin Lamarud ya samu wannan damar ne Kuma saiya saki wasu tsuntsayen tsafi daya sihirce da sirrin maitarsa ya sakesu a matsayin annoba suka rinqa cizon mutanenku a wannan lkcn duk Wanda suka ciza zasu sakar masa wani jinin tsafi shima daga wannan lkcn zai zama maye zaike cin naman mutane yan uwansa idan ya samu dama zai yanka ya gasa yaci idan bai samu dama ba daga kallo ma zai saki wani sinadari a idonsa ya shiga idon wannan mutumin da yayi niyyar cinyewa take zai lashe kurwar wannan mutumin ya zama gawa.




Shikuwa abin bautarki Rundatu ya kasance wani gawurtaccen boka wanda kakanninki suke bautawa wanda shine yake bawa zuri'a Uddawa kariya daga duk wani Abu na cutarwa shine yaci gaba da bawa zuri'ar gdan waziri Uddau kariya a lkcn da wannan annoba ta fantsama duniya tabbas a wannan lkcn a garinku an rinqa yima zuri'arku dauki daidai har saida suka qare wannan dalilin yasa Aljani rundatu yazo ya dauke kakanninki ya tafi dasu wata nahiya ya kafa musu tanti saboda qudurinsa na shekaru akan mahaifinki da zaa haifa shikuma ya haifeki wadda ke kin kasance sirrin buwayar duk wanda ya mallakeki har yayi kwanciyar farko dake ya karbi budurcinki daga gareki Allah ya aikoki a matsayin raba gardama tsakanin mutane da aljanu wanda kusantarki zaisa nasara ta lullube wanda ya samu wannan nasarar.
Mun yarda cewa komai Allah ne yakeyi amma shine yace mana idan bamuda lfy mu nemi magani idan munajin qishirwa mu nemi ruwa idan munajin yunwa mu nemi abinci tabbas burujinki da burujin yariman mu ya hadu wannan dalilin ya sanya aka tabbatar masa kece makaminsa na yaqar duniyar Tsafi da kafirci"





Jikin Najmah yayi sanyi tace “amma tayaya zan kasance makamin yaqar masarautata tayaya zan kasance a wannan matsayin, bayan na kasance nima inabin addinin gargajiya addinin iyayena da kakanni na sannan nakasance mutum shikuma Yarinmanku ya kasance gamayyar halitta"
Miqewa Ishmiyya tayi tace “ki gafarceni ya shugabata banida amsar wannan tambayar ina maganane bisa umarnin uwar gijiyata Kuma inda ta bani umarnin tsayawa kenan" daga haka ta fara tattare kayan abincin ta rusuna tace “nabarki lfy ya shugabata inada tabbacin Zaki kasance cikin kariyar Ubangijina a wannan fadar"
Juyawa tayi ta fice abinda ya sanya Najmah miqewa ta fara zagaya dakin cikin yanayi na nauyin zuciya da bugawan numfashi saɓɓaɓe da yanda ake fitar dashi ko yaushe.
Zoben kariyarta ne ya zame ya fadi tare da narkewa ya zagwanye ya zama ruwa ya bace bat taja da baya da sauri tana gwama numfashi tace “me hakan yake nufi?" Kafin ta gama wannan tunanin taji damtsenta ya murde ta saki wata razananniyar qara ta fadi qasa abin mamaki sai taga gurun sihirinta ya tsinke shima ya fadi qasa ya kama da wuta kafin ta gama jin wannan azabar taji gurin dake daure a qugunta shima ya kwance ya kama da wutar ta mirgina cikin wata muguwar azabar jiki ta koma gefe ta zubawa gurayen nata ido tana kallon yanda sukeci da wuta ta kasa tuna komai sai wata rawa da jikinta yakeyi kamar ana tsigar gashin jikinta haka takeji, bata iya bambamce komai taji an bude qofar an shigo taji sanda aka dagata daganan bata qara sanin meye yake faruwa ba.



_Assalamu alaikum_

_Masoyana inayi muku fatan alkhairi, domin cigaba da karanta wannan lbr na *MASARAUTAR MAYU* ki turo kudinki/ka VIP 500 regular 200 ta asusuna 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 idan VTU zaka/kiyi Kuma Zaki turane ta wannan number 09031307566: kada ki tura VTU ta number farko domin bazan gani ba only evidence of payment zaki turo a ita._
_Mutanen Niger ma zaku iya turo katin orange wanda zaiyi daidai da kudin dana ambata a sama ta number farko, na gde sai najiku._

_San danan akwai littafin *WANI QANGI* regular 100 ne VIP 300 idan kina buqata Zaki tura ta wadancen numbers dake sama ko ta account din dake sama_
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:36 PM - Ummi Tandama: *MASARAUTAR MAYU!*
*_(HISTORICAL AND ADVENTURE)_*

*WRITING AND STORY*


*UMMUH HAIRAN*


*MARUBUCIYAR*
👇🏻
AMINIYA KO KISHIYA
HABIBULLAH
QUEEN FARHA
GIDAN UNCLE
ADANDI
WACECE NI
AURAN BAZAWARA
DHOOM ISHAQ
MATAR LAMEER
DUBAI
AND NOW👇🏻
MASARAUTAR MAYU!
AND
WANK QANGI



*FREE* *P 11-12*



**********


*BIRNI JAWAL* Tsayin sa'a guda ana jiran fitowar baiwa Zaujar da Najmah Shiru babu labarinsu lamarin daya tashi hankali Yarimah Isham ya tashi wani amintaccen bafade yace yaje turakarsa ya gane masa meye yake faruwa, fita bafaden yayi ya nufi fadar Yarimah Isham din Koda zuwansa sai ya hangi qofar fadar a bude mamaki ya cikashi ya cusa kai ciki cikin tsananin mamaki da tunanin abinda yake faruwa,
Shigarsa keda wuya ya iske baiwa Zaujar kwance cikin halin suma al'amarin daya tashi hankalinsa ya juya da gudu ya koma dandalin taron ya fadi gaban Yarimah Isham yace “ka gafarceni yakai Yariman duniya haqiqa wani al'amari ya faru domin kuwa naje na tarar da baiwa Zaujar cikin halin Suma a daure da sarqar al'amudi,
Wata zabura manya fadawan dashi kansa sarki Jamal din sukayi kowa ya Kai dubansa ga shugaban bokaye Irdam shikuma a lkcn aka qara masa qaimi da qumajin aikinsa yayi wata kururuwa saiga sama ta bude tsuntsu Dilshad ya bayyana bayansa dauke da Najmah kafin su gama mamakin yanda akayi wannan tsuntsu ya ratso masarautarsu ya keta ta babbar fadar tsafi ya shiga turakarsa Yarimah Isham ya dauke Najmah kawai sai sukaji sukuwar dawakai tare da kabbara.




Take sadaukai suka shata layi kasancewar su dama sun kasance kullum cikin Shirin ko ta kwana suke take suka gyara tsaiwa wasunsu Kuma suka fara ruwan kibbau wa wannan tsuntsu tare da tashin tsuntsayen tsafinsu sukafi bayanshi abin mamaki yana keta hazo ya bacewa ganin nasu tsuntsayen.
Kafin isowar Yarimah Nurain yarimah Isham yayi wani ihu ya suke zuciyar wannan bawan daya tura ya gano masa meye yake faruwa take bawan ya fadi gawa ya daga takobin ya lashe jinin jikinsa na wata irin karkarwa kamar ana kada masa kugen yaqi ya fito filin cikin tsananin tashin hankali sadaukansa suka rufa masa baya wani mahaukacin yaqi ya ruguntsume qura tayi tsiri ta tashi sama ta lullube mayaqan baka iya hangen komai sai tartsatsin wuta cikin qura da haniniyar dawakai da ihun mazaje wani bangaren kuma kabbarar dakarun musulumci kawai ke tashi.
Gumurzu yayi gumurzu sai zubewa maza sukeyi amma zuciyoyinsu sun kasa rusuna kowa burinsa yaga yakai abokin karawarsa qasa, duk yanda yarima Isham yaso yakai ga isa wa Yarimah Nurain yayi masa kisan sauro amma ya kasa saboda yaqin na sumamene basu shirya masa ba kuma kada ma sun shirya fada da jarumi Nurain sai dubu ta taru.




Tabargaza dakarun rundunar mayaqan Yarimah Nurain sukeyi bata wasaba Saida ya kasance sun zubar da kashi sittin cikin dari na sadaukar masarautar jawal inda Suma aka zubar musu da sadaukai da dama amma basukai kwatan wanda suka kwantarwa da Yarimah Isham ba.
Abinda ya qara harzuqa zuciyar Yarimah Isham yayi wani ihu daya sanya birnin karbar amon muryarsa ya rikide ya zama wani haske ya rinqa zagayawa a tsakanin dakarun musulumci duk inda ya zaga Saida kaga gawarwaki na zubewa a qasa kamar sassabar gona aikuwa shima Yarimah Nurain ya taqarqare ya runtuma uwar kabbara ya diro dagakan dokinsa ya shafi dokin ya bace bat ya zare zare takobin muzhar takobin da kakansa sarki Uqdah mahaifin Sarauniya Badiyyah ya yaqi tawagar aljani Baghzar a zamanin sa ya ci gaba da maimata kabbara da kalimatusshahada ya keta cikin hasken ya rinqa saran hasken babuji babu gani,
Wani irin tururi ina narkakkiyar dalma yana ratsa Yarimah Isham take ba tare da shawara da kowaba wannan hasken ya bace ya fadi qasa Tim Yarimah Nurain ya nufeshi kafin ya Isa gareshi ya miqe ya nufoshi suka ruguntsume da wani azabbaben yaqi wanda ya haddasa qasa ta rinqa girgiza kowannensu yanaji da zafin nama da sadaukanta.




Wannan yaqi shine ya daukesu har tsayin kwanaki biyu babuci babusha babu sallah ga musulmai har saida suka barnata rundunar mayaqan ta masarautar jawal sannan Yarimah Isham yayi muguwar galabaita a matsayinsa na bil'adam shikuwa Nurain ko a jikinsa in zaa shekara ana yaqin baijin komai.
Gumu tayi gumu har takai Yarimah Isham ya fara gani dishi dishi ga raunukan da Yarimah Nurain yayi masa da suketa malalar da jini, yanagaf da faduwa wata iska ta taso me qarfin gaske ta rinqa zubar da duwatsu tana kakkarya bishiyoyi ta dauke Yarimah Isham tayi sama dashi abinda ya kawo qarshen wannan yaqin a karon farko.
Nan take mutanen dake cikin masarautar suka rinqa guduwa suna shigewa gidanjensu suna kullewa abinda ya sanya Yarimah Nurain bada umarnin a debe gawarwakin musulmu suje bayan gari suyi musu sallah su binne, haka kuwa akayi nan take dakarun suka rinqa debe gawarwakin suna dorawa bisa dawakai shikuma ya hau kan nasa dokin ya nufi inda aka kwatanta masa gidan iyayen Najmah domin ya daukosu ya tafi dasu masarautar Fazbar amma bisa rashin saa yaje ya tarar da gidan a rushe babu alamun an taba halittar gda a gurin saima wata baqar qasa data maye gurbin gidan.




Diban qasar yayi ya dagata sama yana kallonta zuciyarsa na tafasa ya durqushe ya saki wani ihu tare da sake watsa qasar sama, ni irin takaici yakeji na bata lkcnsa da yayi wajen fada da wancan qaramin qwaron har yakaishi ga wannan babbar asarar boka Rundatu yazo ya dauke mahaifan Najmah saboda dasune kadai zai iya samun nasarar qwatar Najmah a hannunsa.
Hakaya miqe cikin mutuwar jiki tare da sawa a ransa ubangijin daya aiko annabi sulaimanu da gaskiya bazai taba bashi kunya ba wajen karya daular kafirci, dokinsa yayiwa linzami ya fita daga birnin jawal ya koma sansaninsu,
Shikuwa Yarimah Isham wani aljani Lamarud ne ya fito daga jikin gunki Harsan yazo ya daukeshi saboda yasan idan yabarsa da Nurain bazaikai labari ba a karon farko zaiyi gunduwa gunduwa da naman jikinsa Wanda hakan ke nufin nasarar daular musulumci abinda ya dade yana shirya rushewarta a dainajin labarinta a duniya baki daya.




Tsayin kwana da yini sannan Isham ya farfado ya taqarqare ya fasa ihu tare da miqewa yana ambaton sunan Najmah da sauri Saubar da Jamal suka riqeshi tare da cewa “nasara tamuce yakai abin qaunarmu kayi sani faduwa a karon farko bashi yake nufin daqushewar nasara ba tabbas Kaine zaka mallaki wannan yarinya bazai taba cimma nasarar ketata ba Kaine zaka karbi budurcinta"
Wata uwar tsawa ya dakawa iyayen nasa yace “kuna cewa zanyi nasara tayaya zanyi nasara bayan kun kasance kasassu abin bauta Harsan ya kasa bani nasara a lkcn dana samu damar aiwatar da komai, tabbas akwai Wanda yakeyiwa wadannan maqiyan namu aiki a cikin wannan masarautar domin yasan cewa zasuzo su shammacemu su sacemin farin cikina shiyasa jiya ya zubamin benjour cikin giya nasha nayi bacci bankai ga kusantar Najmah ba, maza kusa a nemomin shi ko wayene shi zan yankashi na shayar da wannan qasqantaccen abin bautar naku jininsa na gasa zuciyarsa na cinye tunda ya kasance munafuki bayan na bare cikinsa yana raye na cire qodarsa na cinyeta danya"




Wata uwar tsawa Sarki Jamal ya dakawa dogaran dake tsaye take suka bazama bincike lungu da saqo bokan fada ya fara aiwatar da nasa aikin shima take madubin tsafin nasa ya tarwatse abinda ya firgita kowa kowa ya miqe tsaye, bokan bai daddara ba ya sake rintse idonsa yana karanto wasu dalasumansa na tsafi take wata barewa ta bayyana tana naquda a bayan gidan sarautar lamarin da yasa kowa nutsuwa.
Dagowa Boka Irdam yayi yace “wannan barewar zaku bincika asalinta ba barewa bace itace take daukar rahoton duk wani Abu dake faruwa tana kaiwa wani malami mai suna Uzair a masarautar Qubhar masarautar da mahaifiyar Nurain aljana Badiyyah take mulka shi Kuma yake sanar da Sarauniyarsa ita Kuma ta sanar da danta wanda shikuma ya kasance jagoran aiwatar da kowannen aiki haqiqa sakaci anyishi tunda har Najmah taje gurinsa duk wani shirinmu ya kunce a yanzu tsafi bazai taba tasiri ba indai ta shiga masarautar Fazbar kowanne irin tsafi na jikinta zai karye zata manta da kowa da komai zata fuskanci sabuwar rayuwa.
Kafin zuwansu wannan masarautar ma Saida suka daura aurenta da Yarimah Nurain suna zuwa gda zai sanya Mata zoben da duniya take rikici akansa zoben da sirrikan daular Zhumhar yake ciki wannan zoben shine kowannenmu yakeson mallaka manyan matsafan duniya sun mutu saboda wannan zoben a hanyarsu ta zuwa daular Qubhar domin karboshi a hannun Sarki Uqdah amma sun kasa cimma gaci sai Kuma wannan takobin muzhar da Nurain ya yaqi Isham da ita wannan takobin itace mahadin zoben nan an samesu ne a fadar sarkin da sulaimanu dan dawud ya bawa jagorancin aljanun duniya wanda shi ya kasance kakan kakan Sarki Uqdah mahaifin Sarauniya Badiyyah mahaifiyar Nurain idan har wannan zoben ya shiga yatsan Najmah to tariga ta zama tasa qarfin buwayar tsafine kawai zai iya tseratar da ita daga garesu kada ku manta Nurain ya kasance gamayyar halitta tsakanin jinsin mutum da aljan idan har yayi nasarar kusantar Najmah itama zata zama irinsa saboda dama an samar da itane dominsa"




Miqewa yayi ya fara tattare kayansa yayinda Isham ya umarci aje na nemo masa wannan barewa, ya juya ga Irdam yace “yanzu meye abinyi" murmushi yayi yace “ka tafi masarautar Fazbar amma ka ajiye duk wani Shirin tsafinki saboda bazaiyi aiki acan ba ka kafa tanti a bayan gari cikin wani kogo da ake Kira Najalal irdah nan ne kawai zaka boyewa Yarimah Nurain.
A cikin ranakun amarcinsa zai fito da Najmah domin suyi kilisa kaikuma sai kayi amfani da hodar gwama iska ka hura masa bacci ka saceta amma fah kada kasa a ranka zaka taba samun kanta da sauqi domin a wadannan kwanakin bazan iya cewa dakai ga abinda zai faru ba,
Rufe bakinsa keda wuya dakarun da suka tafi farautar barewar nan suka dawo sukace Basu ganta ba sai wata kyakkyawar budurwa tana tsinkar inibi a wata itaciya, take Yarimah Isham ya saba linzami ya shiga jejin cikin saa kuwa ya tarar da wannan kyakkyawar budurwa ta zauna tanashan inibin tana ganinsa ta miqe a tsorace, takobi ya zare tayi saurin bacewa.




A bayansa ta bayyana cikin wata zazzaqar siririyar murya tace “yakai wannan kyakkyawan dan sarki kayi sani ni na kasance hadima ce da aka aikoni domin aiwatar da umarni nasan bazaka iya kasheni ba kuma Koda ace ka iya to zan kasance me farin ciki domin na cika umarnin Sarauniya Badiyyah Yariman mu ya mallaki Salamar ruhinsa yanacan zai angwance da amaryarsa a wannan daren ka bini cikin sauqi ns sadaka da masarautar Fazbar idan kayi jayayya a hanya kafin isarka ka zama gawa"
Zuba Mata ido yayi yanason gano gaskiyarta hakanan yaji zuciyarsa ta amince da wannan yarinyar ya amince Mata tayi masa murmushin yaudara tace “hakan shine kawai mafitarka" dubanta yayi yace “kedin wacece?" Dariya tayi tace “sunana Nurayyah

Please Login or Register in order to submit comment