Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na kasance ya ce a wajen wazirin fadar Qubhar masarautar da Sarauniya Badiyyah dake mulka na kasance Ina tsananin qaunar Yarimah Nurain har nakan kwanta jinya saboda shi amma shi yaqi karbata a matsayin masoyiya kullum nakanyi kuka har takai na kasa boyewa na samu mahaifina na sanar dashi shikuma ya sanar da Sarauniya inda Sarauniya tace ita batada ikon sanya Nurain yayi abinda bayaso hakan ya batamin rai har naci alwashin saina rusa musu duk wani shirinsu saiya yaqeshi na hanashi farin cikin rayuwa saina zamo masa ciwon ido a rayuwarsa"
Kama hannu Isham tayi tace “ka bani hadin kai mu hada qarfi da qarfe mi yaqeshi nasan sirrinsa fiye da yanda kake tunani banida shamaki da fadarsa zan shigeta a duk lkcn da najeso turakarsa ce bantaba shiga" wata dariya Yarimah Isham ya saki dajin ya amsa amon muryarsa yace “kinzo da aikin kwanya me kyau yake wannan kyakkyawar yarinya nikuma nayi miki alqawarin mallaka miki rabin abinda na mallaka muddin Najmah ta dawo hanuna"
Kashhh rashin sani yafi dare duhu tabbas da ace Yarimah Isham yasan gadar zaren da aljana Nurayyah take shirya masa dabai bata amamma yabita ba domin ita batama taba ganin Nurain ba burin dai ganin fuskarsa takeyi da akayi ittifaqin bayab mahaifiyarsa da mahaifinsa babu wanda ya taba ganin fuskarsa kullum yana rufe fuskarsa cikin rawani, ta buga ta buga a allon tsafinta ta gagara samun damar ganinsa hakan yasa ta farabin bokaye inda suka tabbatar mata da cewa Isham ne kawai zata hada Kai dashi yakaita bayan garin Fazbar daganan Kuma sai tasan yanda zatayi ta shiga garin.
_Wannan kenan_



_

_Masoyana Ina alfahari daku domin cigaba da karanta wannan lbr na *MASARAUTAR MAYU* ku nunamin qauna ta hanyar siyan littafinnan ki/ka turo kudinki/ka VIP 500 regular 200 ta asusuna 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 idan VTU zaka/kiyi Kuma Zaki turane ta wannan number 09031307566: kada ki tura VTU ta number farko domin bazan gani ba only evidence of payment zaki turo a ita._
_Mutanen Niger ma zaku iya turo katin orange wanda zaiyi daidai da kudin dana ambata a sama ta number farko, na gde sai najiku._

_Sannan akwai littafin *WANI QANGI* 200 ne VIP 400 idan kina buqata Zaki tura ta wadancen numbers dake sama ko ta account din dake sama_
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:36 PM - Ummi Tandama: *MASARAUTAR MAYU*



*WRITING AND STORY*


*UMMUH HAIRAN*
          


_Alhmdllh! Alhmdllh!! Alhmdllh!!!_

_A madadina da iyalaina munayiwa daukacin musulmin duniya barka da shigowa sabuwar shekarar musulumci *1442H* tabbas_ _abubuwa masu dadi da akasin haka sun faru a shekarar da mukayi bankwana da ita mun rasa makusantanmu dama😭 ina roqon ubangiji ya sanya wannan sabuwar_ _shekara ta zama haske Kuma alkhairi sannan mabudin qofofin biyan buqatunmu na alkhairi sharrin dake cikin_ _wannan shekara Allah ya musanya manashi ya zame mana alkhairi,_
_Happy_ _New_ _Islamic Year_
_١٤٤٢ A.H_


*LAST FREE PAGE*


*FREE P 13-14*



*TUNISIA* Lamari ne me wuyar ganewa rayuwa me cike da tarnaqi ita take gudana a fadar boka Rundatu tsakaninsa da Uddatu mahaifin Najmah da Uddaru, al'amura sun jagule duk yanda yake suke tunanin sauqi abin ya faskara alqaluman tsafi sun kasa tasirin hango musu halin da Najmah take ciki dukkannin bala'insu yana tsayawa ne a bayan Dutsen Najalal Irdah.
Sosai yake azabtar da Maharbi Uddatu da Uddaru a cewarsa suna sane suka bayar da cikon nasararsa wa Yarimah Nurain kullum yake sawa anayi musu azaba kala ashirin da biyar duk da haka Uddatu yaqi cewa komai Abu daya take maimaitawa cewa “haqiqa na kasance Mai biyayya wa umarninka nida yata da matata bamu kasance masu bijire maka ba saidai kai ka kasance ka bamu umarni wajen zuwan Najmah bikin Jawaleey wanda har ya zamo silar salwantar muraden manyan matsafan duniya"
Saboda baqin ciki saida Rundatu ya kwana guda yana kukan jini tare da kebe kansa cikin wani dakin sirri ya rinqa hada surrukan da yake tsammanin zasu kaishi ga nasara.




Duk bugun da zaiyi saidai ta hango masa dishin hoton Najmah cikin halin suma shima hoton baya fita gabaki daya saidai wani bangare nashi lamarin daya qara dugunzuma hankalinsa ya fito da shirinsa, tsakiyar dare ya dauki wani qaho ya fara busawa take ginin koton ya fara girgiza yana daddarewa cikin daqiqa sittin wani shirgegen aljani ya bayyana a gabansa yayi sujjadah.
Munin aljanin ne yasanya Uddaru sulalewa ta suma shikuwa Uddatu fitsari ya rinqa saki a wando, boka Rundatu ya kece da wata mahaukaciyar dariya data sanya tsuntsayen dake saman bishiyoyi yin fiffike su tashi yace “na hango matsafiya Nurayyah ta hada hannu da Yarimah Isham zasu dauki hanyar zuwa Qasar Farisa a nufinsu na isa fadar Fazbar haqiqa yaro da goruba sai lasa domin Bokaya Juhaira ta kwana uku a bakin birnin tare da shugaban maridan duniya Marisol suna jiran ranar da Yarimah Nurain zai fito kilisa da Najmah wanda ta wannan hanyar ce kawai zasu samu damar karbarta,
Yakai wannan babban hadimi nawa inaso kayi gaggawar daukata ka kaini tsuburin Uliyal khaulah ni anan zan jirayi zuwansu zan tsaya ne duk wanda ya samu nasara saina kasheshi na karbeta daga hannunsa idan naso na kasheta bayan na cire zoben zaujatul Noor daga yatsanta idan Kuma naga dama na barta na massheta sadakata"



Saurin kallonsa Uddatu yayi ya zagayeshi tare da sanya wata yar qaramar wuqa ya caki qirjinsa jini ya zubo ya sanya wani qoqo ya tare bai damu da ihun da Uddatu yakeyi ba ya matsa gaban Uddaru itama ya caki qirjinta jinin yayi tsartuwa ya tara ya cakuda dana mijinta ya matsa gaban wata wutar tsafi da takeci balbal ya dora wannan qoqon ya dauki wani ruwan sihiri ya zuba a ciki jinin yayi tsiri yayi tsiri ya koma cikin qoqon take wani wari ya turnuqe gurin.
Wani baqin duhu ya gauraye ko Ina tare da wani kuka me kama dana mage, wani gurnani ne ya rinqa tashi take wani haske ya kewaye gurin abin mamaki kawai sai sukaga wata budurwa ta taso daga cikin qoqon nan me tsananin kama da Najmah da sauri Uddatu ya washe baki yana cewa “yata ta dawo garen...."
Rufe masa baki Uddaru data farfado tayi tace “ba ita bace tabbas wannan kofi din yatace ba yata bace" dariya boka Rundatu ya kece da ita yace “da ita zan yaudaresu na kwace ta gaskiyar" yana fadin haka ya dafe bayan wannan aljani me manyan fuka-fukai take aljanin yayi wani shawagi ya cure guri guda ya zama qura ya keta kogon dutsen ta fita a guje.
Lamarin daya sanya duk wata halitta dake gurin durqushewa har saida rugugin da qurar ta haddasa ya lafa sannan komai ya koma tafiya daidai.



********


Acan kuwa fadar Fazbar lkcn da Najmah ta yanke jiki ta dadi cikin wani mawuyacin yanayi a daidai lkcn ne Sarauniya Badiyyah ta umarci Yarimah Nurain daya tashi yaje yagano lfyr matarsa, yana zuwa ya tarar da ita cikin wannan mawuyacin halin da sauri ya matsa ya sanya hannayensa ya dagata cak ya dorata saman gadon tare da zuba mata ido yana nazarinta.
Murmushi yayi tare da sanya hannunsa ya fara shafa kanta dogon kwantacce gashinta daya kwanto har saman girarta ya dauki hankalinsa, sosai ya shagala da kallonta yanajin shauqi da haka shima ya zame ya kwanta a gefenta yana hura mata iska a fuskarta har bacci ya daukeshi,
Zuciyarsa wasai yanada yaqinin cewa idan ta farka bazata tuna komai ba balle tabashi matsala wajen cikar muradansa tabbas shi ya kasance me saa cikin rayuwarsa, tsayin wannan rana haka suka yini suna baccin gajiya yana rungume da ita a faffadan qirjinsa.
Qiraye kirayen sallah ne ya tasheshi ya zame jikinsa daga nata a hankali yaja Mata bargo ya rufeta tare da sumbatar dan qaramin bakinta ya fice da sauri ya turo Hadima Ishmiyya yace taje tayi gadin gimbiya hakanan Najmah ta kasance cikin dogon bacci me kama da suma na tsayin kwana da yini inda a cikin gdan sarautar aketa shagalin biki babu amarya, kasancewar Yarimah Nurain ya sanar da iyayensa tana cikin halin baccin fitar sihiri a jikinta ya sa basu wani damu ba saidai suje su leqata su dawo.




A cikin rana ta biyune misalin lkcn ketowar alfijir ta farka da attishawa tare da wani tari me qarfi abinda ya janyo hankalin Ishmiyya dake wani bangare na dakin ta iso gabanta da sauri ta dagota tana danna Mata qirjinta amma shaquwar d tarin sunqi tsayawa,
Da sauri Ishmiyya ta fita domin sanar da iyayen gdan nata abinda yake faruwa Sarauniya Badiyyah ta taso dakanta tazo suna zuwa suka isheta a qasa tanata kakarin amai da gudu Sarauniya Badiyyah ta iso gaba gareta ta dagota tanayi Mata sannu, abu tun suna dauka zai lafa yaqi lafawa sai wani baqin amai takeyi tanata kakari.
Duban Ishmiyya Badiyyah tayi tace “kije gurin Gurail ki sanar dashi abinda yake faruwa yanzu yazo ko yabaki, da gudunta ta fita kafin wani lkcn ta dawo dauke da wani qoqo ta kafawa Najmah a bakinta ta kuwa kama tanasha jikinta na tsuma, bayan ta gama sha zuwa wani lkc sai komai ya lafa sai wani gumi da taketa ketawa daga haka ta sake sulalewa bacci ys Kuma dauketa a wannan ranar ne aka gama biki wajejen azahar ta farka ta miqe zumbur tana dube dube amma tarasa me ta manta tanaso ta tuna wasu abubuwa amma ta kasa miqewa tayi daidai lkcn da aka bude qofar aka shigo ta zuba masa ido cikin wata farar alqabbar da jan nadi yayi Mata kyau matuqa ji takeyi kamar karta daina kallonsa.
Batasan ya qarasoba saida tajita a qirjinsa cikin wata irin sassanyar murya dabata tabajin irinta ba yace Mata “barka da dawowa sabuwar rayuwa yake matata haqiqa tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya halicceni ya halicceki ya sanya qaunarki a zuciyata tun kafin na ganki, wannan kadai ya Isa ya tabbatar mana da cewa akwai Allah a ko Ina Kuma a kowanne lungu"




Lumshe idonta tayi tana shafa qirjinsa da hannunta ya sauke ajiyar zuciya tare da dago fuskarta ya zuba idanunsa akan fuskarta yaja wata qaqqarfar ajiyar zuciya, wani irin shauqi na fusgarsa gareta a hankali ya sanya hannunsa ya fara ware rawanin daya lullube asalin fuskarsa ya lumshe idonsa a yayin da ita Kuma ta zuba masa ido,
A gigice tayi baya lkcn da tayi arba da kyakkyawar fuskarsa kyawunsa ya caki qwayar idonta batasan sanda ta zube a gadonba ya watsa lallausan gashinsa daya sauka har kafadarsa baya ya zare alqabbar jikinsa ya ratayeta a wani maratayi ya haura gadon ya dagota jikinsa ya hura Mata iska a saman fuskarta yana sunsunar wuyanta a hankali suka sauke ajiyar zuciya jikinta yana rawa saboda firgita da ganin wannan kyawu da iyakar hasashenta bata tabajin lbrn akwai wani mahaluqi days mallakeshi ba duk kyawunta da duniya taketa ambato batayi rabin kyawun Yarimah Nurain ba, to meye yasa shi baa mgnrsa a duniya sai mgnrta kadai duniya takeyi, meye yasa kowanne isasshe a duniya burinsa mallakarta?
Wani dumi taji saman bakinta wanda ya sanyata wuntsilowa daga duniyar tunanin data tafi, hucin bugun numfashinsa ya sanyata bude idonta taga ashe bakinsa ne saman nata yana sauke mata wani salo na sumba daya narkar da ita wata kasala ta rinqa shigarta.




Hannunta ta dora saman kansa tana qoqarin janyewa yayi saurin haurawa samanta ya danneta taja numfashi daqyar saboda nauyin da ya sakar mata ji tayi kamar an dora Mata dutsen Najalal Irdah a hankali ya bude idonsa tare da hade jikinsa, ji tayi nauyin ya fara raguwa har ya kasance ma ta dainajin nauyin saiya kasance tanajin kamar ma karmami ne a samanta hakan ya bata damar motsawa.
Burinta daya ta janye bakinta daga nasa, yaqi bata damar hakan sauma sanya hanunsa da yayi cikin gashinta yana sosa mata tsakiyar kanta suna sauke ajiyar zuciya a hankali ya rinqa yawo da hannunsa a jikinta daga dogon wuyanta ya fara yana wasa da muqwallatonta ta lumshe idonta tanajin yanda tattausan hannunsa yake yawo a jikinta har ya ida saukeshi a qirjinta suka bude ido lkc daya tayi saurin riqe hannunsa ya janye bakinsa daga nata ya mayar dashi saman dokin wuyanta.
Gabadaya ya gama saukar mata da kasala tana qoqarin turesa ya fara motsa hannunsa daya dora saman qirjinta yanajan ajiyar zuciya wani zafi taji ta rintse idonta tana tureshi ta bude baki zatayi mgn yayi saurin dora hannunsa daya a bakin nata ya janye rigarta da dayan ya zubawa cibiyarta ido yanajin wani baqon shauqi na ziyartarsa a hankali ya zame qasa ya dora bakinsa a ramin cibiyarta yana lasa yana sauke numfashi duk ya fice daga hayyacinsa ita kuwa lamarin nasa ya fara tsoratata bakinsa a cibiyarta hannunsa a qirjinta sannan hannunsa ya rufe Mata baki shin to me yake nufi da hakan?



Ya jima yana tsotsar cibiyarta kafin ya dago ya zuba Mata ido ta lumshe idonta ya sauke bakinsa saman nononta ta ture hannunsa ta fasa qara yayi saurin janye bakinsa ya miqe da sauri ya koma gefe ya kwanta yana mayar da numfashi itama numfashin take mayarwa sun jima a haka kafin ya tashi yana kallonta itama tana kallonsa yace.
“Me kikejin tsoro?" Kalmar ce ta rinqa dawo Mata tana tunano wasu abubuwa abin ta'ajibi ta tuna da lkcn da suka taho daga sansaninsu lkcn daya furta Mata kalmar har kawo lkcn da gurun tsafinta ya tsinke daga qugunta zoben kariyarta ya narke dagowa tayi ta kallesa yayi Mata murmushi yace “kici abinci kiyi wanka zamuyi walima anjima a babbar fada daganan zamu shiga sabuwar rayuwa Zaki iya Najmah ki dainajin tsorona bazaki taba cutuwa daga wani Abu da yake nawa ba kinada muhimmaci a rayuwata.




Koda gama fadin haka ya dauki rawaninsa ya mayar ya sunkuyo daidai kuncinta ya sumbaceta ya daga Mata hannu ya fice da sauri saboda kallontan da yakeyi wani abune yake fuzgarsa a cikin kwayar idonta,
Itama miqewa tayi tana zagaya dakin tare da kallon kowacce kusurwa ta takura qwaqwalwarta akan ta tuno Mata wani Abu daya faru kafin zuwanta hannun Yarimah Nurain amma ta kasa.
Dukan kanta ta rinqayi a qudurinta nason saita tuna wani Abu kwata² hakan ya faskara a haka Hadima Ishmiyya ta shigo ta isheta ta rusuna a gabanta tace “tuba nake ya shugabata nazo da nufin taimakonki sai naji qamshin turaren Yarimah shine yasa na juya sai yanzu da naga wuccewarsa ta da'irar bayi sannan na iso"
Dagowa tayi da idanunta da suka kada sukayi jawur tace “wani Abu ya faru danine bayan zuwana nan zoben kariyata ya narke gurayen sihiri na duk sun bace, wanne irin tsafi kuke amfani dashi da har ya tabamin daraja ta?"




Qasa Hadima Ishmiyya tayi da kanta tace “Haqiqa ya shugabata baa kanki ba akan duk Wanda ma ya kusanci wannan fada haka tana faruwa lkcn da akayi yaqi tsakanin masarautar Fazbar da masarautar Ulul Sihr dake qarqashin Qasar Rum akai ganimar da aka samo ta yaqi aka kawota wannan birnin ciki harda ni dana kasance Baiwa ce wa masarautar Ulul Sihr.
Ya shugabata shigowarmu wannan fadar keda wuya duk wani sihiri dake jikinmu ya rinqa warwarewa kasancewar haka tsarin fadar yake sihiri baya tasiri a cikinta qarshema lalacewa yakeyi wannan dalilin yasa ta gagari matsafan duniya duk da suna harinta kullum da burin kifar da wannan daula ta Fazbar suke kwana suke tashi.
Haqiqa duk wanda ya kasanci wannan adalar masarauta bazai taba marmari ko burin barinta ba wannan dalilin yasa kullum muke raba dare wajen addu'a da roqon ubangijin daya aiko mana Sulaimanu da gaskiya yaci gaba da kare mana masarautarmu, zakiji dadi ya shugabata muma da muka shigota a matsayin bayi munajin dadi bare ke da kika shigo matsayin Qusa ta hudu a cikinta.




Tuni tama manta da dalilin tambayar sukayita Hira Hadima Ishmiyya tanata sanyata dariya tare da bata labarai masu dauke kewa har tayi wanka ta dawo a lkcn ne aka turo wata Hadima ta sanar dasu ana nemansu a fadar Sarauniya Badiyyah.
Alqabba Ishmiyya ta sanya mata ta kama hannunta suka fito duk inda suka ratsa hadiman sunata zubewa suna kwasar gaisuwa a qofar fita gawa wannan bangaren taga wani abin al'ajabi ashe wadannan yammatan da suka rakota ta shiga dakinnan ta kwanta sunanan inda suka barsu tana fitowa suka zube gabanta sunayi mata kirari itadai bin kowa takeyi da ido,
Da'ira sukayi Mata suka sanyata a tsakiya tare da baza Mata wani koren qyalle babba yayi Mata rumfa saman qyallen anyi rubutu da ruwan azurfa Zaujatul Noor zoben hannunta ta kalla shima abinda yake rubuce a jikinsa kenan da wannan tunanin suka isa fadar Sarauniya Badiyyah.
Bayin suka dare ta tareta da kanta hakanan Najmah ta samu kanta da durqushewa gaban surukarta hakan ya faranta ran Sarauniya Badiyyah tace “Albarka zataci gabada bibiyarki har bayan rayuwarki yake surukata" Dagota tayi suka shiga wani daki su biyu kadai kowa ya tsaya a bakin qofa suna shiga suka tarar da wata Mata a zaune da wata shimfidar alfarma a gabanta Sarauniya Badiyyah tace “an yabeki wajen iya shirya amaren yayan sarakai wannan ya zama qarshen basirarki ki kasance me qure tunaninki wajen shirya wannan amaryar da tafi kowacce amarya ta zamanin nan namu daraja yau zamu miqata ga mijinta tabbas bana fatan inason dana yasan cewa baiyi zamen asurka tsohon kareba.



_Yanzu zaa fara wasan wannan duk shimfida ce!_



_Masoyana Ina alfahari daku domin cigaba da karanta wannan lbr na *MASARAUTAR MAYU* ku nunamin qauna ta hanyar siyan littafinnan ki/ka turo kudinki/ka VIP 500 regular 200 ta asusuna 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 idan VTU zaka/kiyi Kuma Zaki turane ta wannan number 09031307566: kada ki tura VTU ta number farko domin bazan gani ba only evidence of payment zaki turo a ita._
_Mutanen Niger ma zaku iya turo katin orange wanda zaiyi daidai da kudin dana ambata a sama ta  number farko, na gde sai najiku._

_Sannan akwai littafin *WANI QANGI* 200 ne VIP 400 idan kina buqata Zaki tura ta wadancen  numbers dake sama ko ta account din dake sama_
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:36 PM - Ummi Tandama: *MASARAUTAR MAYU*

*UMMUH HAIRAN*

*PAID BOOK*
_Gareku masoyana inason nasan kunasona tayayan zan amince da abinda bakunanku ke furtawa?_
_Karki damu kedai kiyi qoqarin nunamin qauna ta hanyar siyan littafina_
_Regular 200 VIP 500_
_Ki biya ta wannan acc din   0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Idan katine ki dauka hotonsa ko pin lambobinsa ki tura ta WhatsApp number 09013718241: idan VTU ne ki tura ta wannan number_
      👇🏻
_09031307566_

_Sai najiku_



MM15-16 Jinjina kai tayi ta fara shirya amarya da ado irin nasu na sarakai cikin abinda bai wucce sa'a gudaba ta gama shiryata tsaf tayi kyau na ban mamaki ado kamar dawisu tasha sarqar lu'u'lu'u da murjani ta tsumu da turaren almuski da alharini qamshi sai tashi yake a jikinta.
Dago fuskarta Sarauniya Badiyyah tayi tayi murmushi tana Jinjina kyawun da zai hadu da kyawu tare da fatan kasancewarsu cikin farin cikin da ya zarta misalin baki, hannunta da qafarta aka zuba Mata zobunan gwal tayi kyau iyakar kallonka, Kama hannunta Sarauniya tayi ta zaunar da ita suka fita itada wannan sarkin qawar.
Fitarsu babu dadewa wasu Mata guda biyu suka shigo Suma cikin ado suke na ban mamaki suka rusuna gaban NAJMAH suka kwashi gaisuwa sannan daya cikinsu tace “mun kasance yan aikene daga Shugabanmu Yarima nurain ya bamu izinin tafiya dake fadarsa domin gabatar da walima"




Suna fadin haka suka Dagota ta kasance a tsakiyarsu daya ta nade Mata rigarta ta baya daya tana gyara Mata ita ta gaba suna fitowa wasu hadiman suka qara kangeta Suma suna shirye cikin korayen dogayen riguna ita kadaice ta kasance me fararen tufafi.
Abin saiya burgeta ta rinqa kallonsu ta cikin mayafin daya lullube fuskarta haka suka isa bakin harabar da aka tanada domin taron manyan kilisai aka shimfida a gurin daidai shigowarta daidai shigowarsa shima kallon filin takeyi da mutanen dake filin cike yake damqam da mutane kowa ita yake kallo tana takawa jikinta na rawa idanun mutanen na neman kayar da ita, yana takowa shima idonsa na kanta suka hade a tsakiyar filin tayi saurin janyewa fadawa jikinsa ta dago idanunta ya shiga cikin nasa yanzun ma nade yake da farin rawani komai na jikinsa farine hatta takalmin qafarsa.
Itamma wannan karon fuskarta a nade take cikin jan rawani da take mamakin dalilin yimata shi, bata gama wannan mamakin ba taga hannu ta bayanta yana miqo Mata takobi da garkuwa ta dago da sauri abin mamaki sai taga sarki Fauwaz ne da kansa.




Murmushi yayi Mata ya daga Mata kai ta juya ga Yarimah Nurain taga ya daga Mata kai alamar qarfafa gwiwa ta sanya hannu ta karba daidai lkcn daya zare tasa takobin walwali haskenta yana haska sararin da'irar sake kallonsa tayi ya nuna mata itama tayi abinda tayi kawai batasan sanda ta durqusa ta dafa qafar Sarki Fauwaz ba yayi murmushi tare da dagota ya sake Jinjina Mata kai a karo na biyu.
Idanunta ne ya ciko da qwallah tabbas tanaji a jikinta itan jaruma ce amma bataji zata iya fada da Yarimah Nurain ba to akan me ma zatayi fadan dashi? Cikin tunanin nata taji an buqa kugen yaqi Yarimah Nurain ya karci qasa da takobinsa yaja baya hakanne ya zaburar da ita batasan sanda ta zare tata takobin a cikin kubenta ba taja baya itama da sauri tana baya baya shima yanayi sukayi tsalle sama a tare suka kawowa juna suka da takubbansu take takubban suka hadu sukabada wata qara mara dadin sauraro suka sake alkafira a lkc daya suka dira a qasa kan gwiwowinsu.
Zabura sukayi suka miqe ya kawo Mata suka cikin zafin nama tasa garkuwar hannunta ta kare takai masa Sara ta qasa yayi tsalle ya kaucewa saranta saran yabi iska shima ya kawo Mata da azama cikin tsananin zafin naman da a iya sanin duk wani wanda yake gurin bazaa sameshi gurin bil'adam ba tayi tsalle ta shallekewa saran ta dura a bayansa takai masa suka yayi kwanciyar magirbi saran ya sakebin iska.




Wayyoh wannan dan qwarya qwaryan yaqi da dadin kallo da debe kewa yake kowa ya nutsu yagani tsakanin ma'auratan waye zaikai wani qasa sukuma sunata fafatawa kowannensu ya kasa samun damar Koda qwarzanar dayansu shikam Yarimah Nurain jarumtar matar tasa ta girmamewa tunaninsa duk yanda yake tunaninta ta shallake masa duk wata qofa da zai samu damar kaita qasa yakasa samu ita kuwa sau biyu tana samun dama sai tayi maza ta waskewa masu kallon daga Yarimah Nurain har Sarki Fauwaz da Sarauniya Badiyyah mamakin dalilin da yasa taketa sakin damarta sukeyi tare da tsananin ta'ajibin irin jarumtar yarinyar.
Sama da sa'a biyu ana fafata gumurzun ankasa cimma madakata gashi dukkansu sunqi gajiya cikin tsananin saa takai masa wani sara daya sanyashi diriricewa tabbas yasan idan har saran ya sameshi to kuwa zata illatashi hakan ya sanyashi shima yakai Mata suka ta qasa tayi baya da sauri yabita ya fada samanta tare da jifa da takobinsa da garkuwarsa.




Ya sanya hannu ya cizge rawanin fuskarsa rana ta farko da duk wani mahaluqi dake rayuwa a masarautar Fazbar ya fara ganin fuskar Yarimah Nurain hannu yasa itama ya ware Mata nata idanunta suka fada cikin nasa da suke da wani launi na daban qwayar idonsa shudiya ce da ratsin ruwan gwal.
Saurin lumshe idonta tayi cikin matsananciyar kunya batasan sanda ta zagaye hannunta da bayansa ba duk da hannun nata ya kasa rutsashi tafi aka saki lkc guda tare da kabbara hakan ne ya fargar dasu ashefa basu kadai bane yayi saurin dagata cike da kunyar iyayensa da sauran jama'ar gurin ya kamo hannunta ta miqe ya sumbaci goshinta suna a haka sukaji ruwan turarin Haramein yana ambaliya akansu take ya qanqameta tare da rufe mata fuskarta da qirjinsa.
Tsayin mintina anayi musu barin turaren kafin a dakata ya dago yana sauke ajiyar zuciya itama ajiyar zuciyar ta sauke ya Kama hannunta suka zauna a kujerun da aka tanada dominsu ba mutane ba hatta aljanun da sukazo taron wannan hadi yayi bala'in basu qawa ashe dai gaskiyane qwarya tabi qwarya! Kowanne allazi da nasa amanu dole Yarimah Nurain sai Najmah.




Bayan lafawar qura aka bude guri da addu'a sannan aka fara gudanar da walimar bikin basu tashi daga wannan taro ba sai talatainin dare a Kuma wannan daren Gurail Uzair ya taso dan aike daga Qudhar, a niyyar Sarauniya Badiyyah sai washegari amarya ta tare suna tashi tajata turakarta har ta fara bacci taji sallama tana tashi a dakin ta miqe da

Please Login or Register in order to submit comment