Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri taga farin hasken manzon Gurail Uzair ta rusuna gabansa yace.
“Yake wannan Sarauniya kiyi sani cewa Shugaba Uzair yace lallai a daren nan kibawa Yarimah Nurain matarsa wannan dare shine sa'arsa ta farko Kuma a wannan daren ne zoben Zaujatul Noor yake cika shekaru dubu biyu da samuwa idan har basu kasance tare ba to kuwa shakka babu mushrikai zasu samu damar qwatarsa daga hannunta saboda a wannan daren duk Wanda ya kusanci zoben nan yakan kasance cikin nannauyan bacci wanda hakance tabawa kakanki damar mallakar zoben nan ya qwaceshi daga hannun Munurul Ubbar idan har basu kasance tare ba zatayi bacci shima zaiyi bacci yin baccinsu na nufin rushewar daular muslumci.




Yana gama sanar da ita ya bace bat" da sauri cikin kaduwa dajin wannan lbrn ta miqe ta fita ta nufi dakin da Najmah ke kwance ta fara haske mata ido hakan yasata motsawa ta daki matashin kanta ta miqe zumbur tana dube dube ganin surukarta yasata yin qasa da girmamawa tace.
“Bamuda lkc yake wannan gimbiya kiyi sani mijinki yana buqatar taimakonki ki Isa gareshi da fuskar tausayi da imani" kalaman na Sarauniya daurewa Najmah kai sukayi ta dago zatayi mgn Sarauniya ta dora hannunta a bakinta ta fara janta harda gudu gudu suke hadawa suka fito farfajiyar gdan suka sake kutsawa tafiya me tsayi sannan suka isa bangaren na Yarimah Nurain dogarawa suka miqe sukayo kansu tayi saurin haska fuskarta da fitilar aci balbal din hannunta suna ganinta suka zube ta wucce suka miqe haka suka rinqa ratsa faluka Saida suka ratsa falo tara manya na biyu yafi na daya na hudu yabi na uku har suka isa qarshen qawa wato falon qarshe falon tara tsorone ya kama Sarauniya ganin Yarimah Nurain zaune a saman kushin ya hade kai da gwiwa yanata sauke ajiyar zuciya.
Sakin hannun Najmah tayi ta matsa gabansa ta dafa kansa ya dago firgigit tare da furta “A'uzubillahi minasshaidanur rajim" ganin mahaifiyar tasa da matarsa yasashi saurin miqewa ya matsa da sauri ya kamo Najman ya mannata da jikinsa yaja wata wahalalliyar ajiyar zuciya abinda ya sanya Sarauniya Badiyyah zubar da hawaye tunda takejin tarihin kara da kawaici bata tabajin irin na Yarimah Nurain ba, yanzu inda Gurail Uzair bai bata wannan umarnin ba ko zai mutu saboda buqatar matarsa bazai taba iya nuna Mata ba damuwarsa ba.





Juyawa tayi da sauri saboda yanda taga ya fita daga hayyacinsa da alamun ma ya manta tana gurin, Saida ta juya ya tuna ya shafa kansa tare da sanya hannunsa ya daga Najmah cak ya nufi dakin baccinsa da ita,
Kamar wacce aka tsaface duk tsoronta sai ta kasa furta masa ko kalma daya tanaji ya rabata da komai na jikinta ya fara tura Mata saqonni itadai tsoro ya hanata motsi gata batada wata kalma d zata iya tunawa ta neman taimako hatta kalaman da take ibada dasu a baya sun bace mata.
Bata fara gane abinda yake faruwa ba saida Yarimah Nurain yakaita matakin qarshe ta saki wata siririyar qarar azaba daganan bata sake gane komai ba, shikuwa Yarimah Nurain komai ya kwance masa shagalinsa yakeyi bai samu kansa ba sai lkcn da yaji alfijir ya keto daidai lkcn da zoben Zaujatul Noor ya rinqa fitar da wani haske daya qauraye dakin.
Hakanne ya cirewa Nurain qumajin jinnantaka ya sanya masa na dan'adam taka ya dago kansa da sauri ya fara tuno abubuwan da suka faru a daren jiya tsakaninsa da matarsa gimbiya Najmah da irin nishin da yaji tayi lkcn da ya shigeta, a hankali ya fara janye jikinsa daga nata har ya fita da qyar ya zuba mata ido yana kallon yanda komai nata ya hargitse idanunta suke kakkafe kamar wata gawa tuni hankalinsa ya jima dayin fiffike yabar jikinsa ya fara kiran sunanta yana jijjigata.





Qwanqwasa musu qofa akayi daidai lkcn da hasken wannan zobe ya dauke duhu ya qara mamaye dakin yakai hannun ya kunna fitilar aci balbal din dakin ya lullubeta da mayafi ya dauki rigarsa ya zura tare da furta waye? Cikin tsoro tace “tuba nake ya shugabana nice likitar da Sarauniya ta aiko na duba lfyr gimbiya.
Ajiyar zuciya yayi yace “kije bama buqatar taimako" daga haka bai qara furta komi ba ya shige bandaki ya gyara jikinsa ya fitar da kansa daga janaba ya dauketa itama ya shiga da ita yayi Mata wankan kamar yanda yayi, ya ranar ko limancin da yakeyi baiyi ba a masallacin fadar tasu sai Sarki Fauwaz ne ya jagoranci sallar Yarimah Nurain yanacan yana jinyar matarsa da take cikin halin doguwar suma kunya ta hanashi ya budewa kowa yaga aika aikar da yayi duk wanda yazo saidai yace masa sufa basa buqatar taimakon kowa.
Sanin halin dan nata da masifar zurfin ciki yasata tashi da kanta ta nufi bangaren nasa tasan idan zata shekara buga masa qofa bazai budeba saboda haka ta jingini bango ta shiga cikin dakin yana zaune saman gadon yana danna Mata qirjinta,
Juyowa yayi ganin mahaifiyar tasa yasasa miqewa da sauri ya bude qofar ya fice tayi murmushi ta matsa ta shafa saman goshin Najmah tajisa zafi zau ta sauke numfashi ta dauketa cak kamar wata kiyashi ta bace bat daga dakin.





Bata direta ko inaba sai a turakarta saman gadonta ta dauki wani mayani ta dauko wani ruwa ta zuba wani magani ta rinqa danna mata a gabanta ruwan yanada zafi sosai shi yasa duk sanda ta danna sai Najmah taja zuciya har saida ruwan yayi sanyi ta dauko wani shikuma tofi tayi a ciki ta shafe Mata jikinta dashi take taja wata ajiyar zuciya tayi miqa Sarauniya Badiyyah taja bargo ta rufe surukar tata.
Wani sabon biki aka sake saka dambar yi Saida aka kwana aka yini anayi sarki Fauwaz ya nadawa Najmah kambunta duk da tana kwance ne bata dawo hayyacinta ba har yanzu.
Shikuwa Yarimah Nurain wasan buya suka rinqayi da mahaifiyarsa yaqi yarda Koda wasa su hadu tsayin kwanaki ukun da tayi tana jinyar Gimbiya Najmah sau biyu yake shiga kullum yaga jikin matar tasa shima sai ya daidaici lkcn da Sarauniya Badiyyah takiyin wurudi zai shiga yayi wuf ya fice.
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:37 PM - Ummi Tandama: *MASARAUTAR MAYU*

*UMMUH HAIRAN*

*PAID BOOK*
_Gareku masoyana inason nasan kunasona tayayan zan amince da abinda bakunanku ke furtawa?_
_Karki damu kedai kiyi qoqarin nunamin qauna ta hanyar siyan littafina_
_Regular 200 VIP 500_
_Ki biya ta wannan acc din   0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Idan katine ki dauka hotonsa ko pin lambobinsa ki tura ta WhatsApp number 09013718241: idan VTU ne ki tura ta wannan number_
      👇🏻
_09031307566_


MM 17-18 Lamarin Yarima Isham da Aljana Nurayyah kuwa lkcn da Nurayyah ta gama fada masa dalilinta nason zuwa fadar Fazbar, sai tayi want surkullenta wani maridin aljani ya bayyana gabanta ta dubesa tace “a cikin sa'o'i sittin nakeso ka isa masarautar Fazbar.
Sujjada yayi mata daidai lkcn da shima Yarima Isham ya kira nasa aljanin yazo suka dunguma sararin samaniya basa tsayawa sai idan sun kasance suna buqatar wani abu cikin saa kuwa basu samu wata matsala ba saboda saida suka daure dazukan kafin tahowarsu haka suka rinqa keda dazuzzuka sa kwazazzabai wani lkcn da alqaryu,
Suna tafe ne suna tsara yanda zasuyi su sace Gimbiya Najmah inda qasan zuciyarta Nurayyah take shirya yanda zata kashe Isham ta mallaki Najmah ita kadai wanda takeda tabbacin ita hanyarta ne kawai zata samu damar mallakar zuciyar Yarimah Nurain.



A lkcn da sukaci rabin tafiyar sai ya kasance hanya ta kwace musu dole saida suka sauka a cikin wani daji me yawan bishiyu da dogayen tsaunuka suka nemi bakin wata qorama suka sauka suna ganin ruwan suka nufeshi da sauri saboda qishirwar da sukeji sukasha suka wanke jikinsu suka koma sukayi shimfida kowane ya kishingida domin hutawa, ashe Basu sani ba shi wannan guri da suka kwanta qasansa idan wani maciji ne da ya safe shekaru dari takwas a gurin ya kasance girman yayi girman tsaunin Uliyal khaulah wanda ya kasance shi kadai da matarsa suke rayuwa a wannan daji babu wani mahaluqi da yake ratsowa cikinsa ya fita lfy face sun massheshi gawa.
Koda Yarimah Isham yayi arba da wannan maciji wanda girman kansa ma kadai abin sanya zuciya cikin wasu wasine, sai ya zabura ya miqe ya zare takobinsa itama Aljana nurayyah hakan tayi sukaja da baya cikin halin tsoro saboda iyakar bincikenta data shafe shekaru tanayi Bai taba nuna Mata zata hadu da wata matsala a hanyarta ta zuwa fadar Fazbar ba, wata iska sukaji ta taso cikin wani matsanancin yanayi Mai dauke da wata baqar qura take dajin yayi duhu bishiyu suka rinqa karyewa tare da wani sauti mara dadin sauraro, haka suka wanzu a gurin suna masu toshe kunnuwansu saboda tsab wannan sautin zai iya kurmantar da mutum,
Sun shafe tsayin sa'o'i sannu a hankali iskar raguwa har ya kasance ta tsaya cak suka bude idanuwansu kawai sai sukaga dajin ya zama fili fetal aikuwa suka zabura suka miqe cikin mamakin wannan aiki na sihiri kawai saijinsu sukayi a cikin sarqa an dauresu akayi sama dasu can qololuwa sannan aka sakesu sukayo qasa cikin wani mawuyacin hali kafin su gama direwa Yarimah Isham ya baza wata tabarmar tsafi suka fado kanta suka abin mamaki kafin su miqe wannan jibgegen maciji yayi wata kururuwa yayo kansu baki bude.




Cikin zafin nama Yarimah Isham ya miqe shima yayi wani gunji kawai sai ya zama macijin turus wannan maciji yaja ya tsaya suna kallon kallo lamarin daya fusata wannan macijin yayi tsalle da nufin fadawa kan Isham amma sai Isham ya goce ya fadi qasa tim cikin saa Isham ya caka masa wata yar qaramar wuqa a tsakiyar cikinsa take yayi wata haniniya ya saki kururuwa me gunji data sanya kwazazzabai suka rinqa ruftawa jini ya rinqa ambaliya Amma duk da haka bai risina ba Saida ya kaiwa Yarimah Isham raruma ya yankeshi da manyan haqoransa take naman gurin ya zagwanye ya zamana ya narke cikin tsananin azabs Yarimah Isham yayi baya taga taga zai fadi nan take Aljana Nurayyah ta kawo masa agaji ta hanyar kafa tsinin takobinta a tsakiyar kan macijin yayi gunji yayi gunji ya fadi gefe Tim yana matagugu,
Abinda yabawa Aljana Nurayyah damar sabar Yarimah Isham ta azashi bisa aljanin daya daukoshi suka bar dajin tare da wannan maciji da yaketa kururuwa, bude wata jaka dake rataye a wuyanta tayi ta dauko wani garin magani ta bude inda wannan maciji ya sari Yarimah Isham taga yanda dafin macijin yasa jikin Yarimah Isham yayi baqin qirin, da sauri ta zazzaga masa maganin ta lullubeshi da wani bargo sihiri data samar dashi a lkcn na tsayin saa guda sannan ta budeshi.




Tana budeshi ya miqe zaune yana rarraba ido ta kece da dariya tace “haqiqa Kai sadaukine duk da kasancewar wani lkcn jarumta bata qwatar rai daga hannun masheqi Amma hikima takan zama mafita a lkcn da aka tsinci Kai cikin gararin fadawa Wani Qangi me wuyar kaucewa.
Numfashi ya sauke ya dauki battar ruwansa ya bude ya kwankwada ya zubawa hanya ido sukaci gaba da lulawa cikin gajimare batare da kowa yace da kowa komai ba zuciyar Yarimah Isham tana gurin Gimbiya Najmah wacce ya jarabtu da tsananin qaunarta gashi tana neman yimasa nisa tabbas yazama wajibi a gareshi ya sare kan Yarimah Nurain domin tabbatar da cikar izzarsa, ya zama doke ya dawo da Najmah cikin rayuwarsa ya zama dole ya sanya zoben Zaujatul Noor a yatsansa domin samun damar mallakar daular Askan wacce ta kasance itace babbar daular aljanu a wannan lkcn wacce take qarqashin jagoranci Sarauniya Badiyyah wacce a yanzu duk aljanin da yake musulmi to qarqashin iko da buwayar mulkinta yake.
Itakuwa Nurayyah babban burinta a duniya rayuwa da Yarimah Nurain Koda kuwa bazai sota ba tanason cika burinta da alqawarin da tayiwa Mahaifiyarta Bokanya Juhaira na kasancewa dashi tare da karya masa tsaronsa ta hanyar aikata Zina da ita wadda ita dayace hanyar da zata samu damar aiwatar da qudurinta na kashe Najmah ya kasance ta dawo da matsayinta na baya na zamowa Sarauniyar kyawawan duniya ta wannan qarni da samuwar Najmah yasa aka daina zancenta idon duniya ya tashi daga kanta ya koma kan Najmah ya kasance duk wani me qarfin iko da fada aji a duniya burinsa ya mallaki sirrin Nasarar dake jikin Najmah da kuma kwatar zoben Zaujatul Noor da yake hannunta a halin yanzu wanda takeda ittifaqin Najmah batama san amfaninsa gareta ba ita dai kawai ta daukeshi adone a gareta.


***********

Bangaren Boka Rundatu kuwa tunda ya baro kogon dutsen qursu da yake rayuwa a ciki yaketa buga saarsa amma ya kasa samun damar ganin halin da Najmah take ciki har sai daren cikar Zoben Zaujatul Noor sannan ya samu nasarar yayewar hijjabi tsakaninsu ya hangeta kwance tana bacci dakarun aljanu musulmai dubu hamsin suna gadin ta ta sama da qasa gabas da yamma kudu da arewa.
Yaga lkcn da Sarauniya Badiyyah ta tashi yaga lkcn da aka aiko Mata saqo amma baiji meye aka fada Mata ba yagadai ta tashi ta fito ta nufi dakin da Najmah ke bacci yaga sanda ta tasheta yaga sunyi mgn nan ma baiji maye suka tattauna ba, yaga sanda taja Hannu Najmah suka fito a lkcn yaso aikawa a satota amma aljanin da zai tura yace a wannan daren babu wanda ya isa ya ratsa birnin Faris gabadayansa balle ya samu damar shiga masarautar Fazbar.
Haka dole ya hqr yaci gaba da kallon yanda abubuwa suke kasancewa har zuwa lkcn da suka shiga ga Yarimah Nurain yaga lkcn da Nurain yaja Najmah ya rungumeta tare da sumbatarta har zuwa lkcn da Sarauniya Badiyyah ta juya ta fita kawo lkcn da Yarimah Nurain ya daga Najmah ya nufi turakarsa da ita daga wannan bai qara samun damar ganin komai ba.




Hakanan yayita bugawa tunda yasan qarshen mgnr a yau Yarimah Nurain zai tara da Najmah wanda hakan na nufin ya mallaki wannan sirrin nasarar dake jikinta rikicin zai kons tsakaninsu dashi tunda zai kasance yanzu shine me juya kowa da komai hakan na nufin karyewar daulolin tsafi, faruwar fari da karyewar tattalin arzikin qasashen da suka kasance kafurai masu bautawa addinin tsafi da addinin gargajiya.
A lkcn da yaketa wannan qoqarin na hana shigar wani Abu tsakanin Yarimah Nurain da Najmah a daidai lkcn ne yaji wata siririyar murya ta saki qara tare da kabbara gami da mamayewar wani haske daya mamaye duniya gabadayanta wannan lkcn duk wani matsafi dake rayuwa a doron qasa Saida ya zabura ya miqe tsaye miqewar da suka kasa komawa su kwanta kasancewar sun dade da sanin wannan haske abinda yake nufi.
Wani ihu Boka Rundatu ya taqarqare ya fasa wanda ya sanya aljanin dake sauke dashi direwa a saman tsibirin Uliyal khaulah dake tsakiyar teku saukowa Boka Rundatu yayi ya fadi a qasa ya rinqa birgima yana ihu shikenan ta faru ta qare Nurain yasan Najmah ya mace shirinsa na shekara sama da dari ya rushe kaico da wannan mummunar tabewa da asara da yayi,




Miqewa yayi ya shige cikin wani kogo da yasa aljanu suks samar masa cikin kwana uku ya baje kayan tsafinsa ya matsa jikin wutar sihirinsa ya dauki tsawirar zanen halittar Najmah ya dora saman wutar ya dauki wani ruwa ya zuba samanta ya fara karanto wasu siddabarunsa tsayin lkc sannan wata aljana ta bayyana ya dubeta yace “ki kasance tare da wannan taswirar domin samun damar cikar burinki na duniya, fadin haka keda wuya wannan aljana ta shige jikin wannan taswira take saiga Najmah ta tashi, Boka Rundatu ya sheqe da dariya yana cewa “nasara! Nasara!! Tabbas nasara tawace zan yaqesu dake".......
*UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:37 PM - Ummi Tandama: _Ki biya ta wannan acc din   0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Idan katine ki dauka hotonsa ko pin lambobinsa ki tura ta WhatsApp number 09013718241: idan VTU ne ki tura ta wannan number_
      👇🏻
_09031307566_


*MM 19-20* Ciki kwanaki biyar Najmah taji sauqi sosai ta murmure ga wani haske da tayi na musamman sai daukar ido takeyi Sarauniya Badiyyah ko motsin kirki bata barinta tayi inda shikuwa Yarimah Nurain yaketa tserewa haduwa da mahaifiyar tasa saboda shidai bazai iya kallon idonta gashi zuciyarsa na azabtuwa da qaunar matarsa yanason jinta a kusa dashi,
Yau takama cikon kwanakinta bakwai ta samu sauqi sosai kamar wani Abu bai faru ba wannan dalilin yasa Sarauniya shiryata domin mayar da ita dakinta, da dare ta sanya aka rakata murna gurin Yarimah Nurain kamar anyi masa sarki, tana zaune saman kilishin dake shimfide a falon qarshe ya shigo ya zauna kusa gareta ya sanya hannu ya dago fuskarta yayi Mata murmushi.



Sauke idonta tayi qasa yace “ina cikin farin ciki mara misali yau yake wannan gimbiya kiyi sani nayi kewarki tsayin lkc" sakeyin qasa tayi ya dagota yace “zanyi nafila nazo mu kwanta inason gobe zamu fita kilisa da safe" itadai ta kasa cewa dashi komai sai binsa da takeyi da ido ya riqe hannunta suka shiga ciki gabadaya a tsorace take dashi tanajin tsoron kada yace zai sake tarawa da ita saboda tasha wahala.
Koda suka shiga ciki zare mata alqabbar yayi ya kwantar da ita ya dauro alwala yazo ya shimfida buzu ya tayar da sallah, juyowa tayi tana me kallonsa addinin nasu zuwa yanzu ya fara shiga jikinta tanajin aminta dasu dari bisa dari komansu cikin tsafta da nutsuwa, a hankali tace “Allah! Allah!! Allah!!! Ubangijin Annabi sulaimanu"
Sallamewa yayi ya soma addu'a kullum addu'arsa tunda ya sameta Allah ya cusa Mata so qauna da kishin addinin gsky addinin da bashi da tamka, yana shafa addu'ar ya Isa gareta ya dauko tambul da ruwan tataccen inibi ya bata tare dayi Mata Bismillah ta karba tasha yayi murmushi yasa a bakinsa ya kurba ya ajiye ys janyota jikinsa ya dora bakinsa a tsakiyar kanta ya sumbaceta yace.




“Ki kasance me hqr da abinda Allah ya zaba miki zakiyi nasara a rayuwa ya matata" Jinjina masa Kai tayi tana shigewa jikinsa tace “Addininku yana birgeni musamman wannan abinda kukeyi kuna sarrafa jikinku ya mijina shin nima zan iyayi?" Wani farin cikine ya mamaye zuciyar Nurain yace.
“Idan kin yarda zaki karbi addinina zanyi farin ciki kuma zamu rayu cikin aminci domin Zaki samu tsarkin zuciya" ajiyar numfashi tayi tace “kuma a Ina ake karbar addinin naku" kallonta yayi tayi masa murmushin daya kashe masa jiki ya lumshe idonsa ya rungumeta a jikinsa sosai yace “idan kika tsarkake zuciyarki kika yarda babu wani addini da yake gaban addinin Islam kika kadaita Allah shi daya kika yarda bashi da tamka kin gama sauranki kalimatusshahada"
Dagowa tayi tace “mece kalimatusshahada?" Cikin farin matsanancin farin ciki yace kin amince Zaki shigo cikinmu mu yaqi kafirci da kafurai" daga masa kai tayi ya laqana Mata kalimatusshahada ta maimaita yayi kabbara tare da rungumeta tsam a jikinsa cike da tsananin farin cikin wannan babbar qaruwa da musulumci ya samu.




Sarrafata ya rinqa yana nuna Mata murnarsa tare da dagata cak yace da kaina zanyi miki wankan shiga musulumci kin fita daga cikin duhu haske ya bayyana a rayuwarki zakiyi rayuwar da baki tabayin irinta ba" a kunyace ta bari yayi Mata wankan ya cire Mata duk wani abu da yasan yana alaqa da addinin gargajiya.
Dawowa sukayi suka kwanta wannan rana sun kwashe amarci sosai cike da qauna tare da yiwa junansu alqawurra masu yawan gaske da asuba bai fita masallaci ba bayan sunyi wanka sun fitar da kansu daga janaba shine yajasu sallah Koda suka idar ya dauka qur'ani me tsarki yana karantawa cikin muryarsa tana sauraronsa bayan ya gama ya fara koya Mata muhimman abubuwan daya kamata ta sani a matsayinta na baliga.
Irinsu tsarki da duk wani Abu da yake na dole ta kiyaye ya shirya ya fita zuwa fada saida ta rakashi har farfajiyar gdan sukayi sallama ya tafi ita Kuma ta juya ta sake kwanciya domin hucce gajiya tare da bitar abubuwan daya sanar da ita da haka bacci ya dauketa cikin baccin tayi wani mafarki daya razanata.




Ganinta tayi cikin wani daji me duhuwa da tsaunuka ga kwazazzabai sarqaqiyar dajin ta hanata gane gabanta ko bayanta tanata gudu a diririce batasan taqamaiman inda zataba hannunta dauke da jinjiri sabuwar haihuwa bayanta wani basamuden dodone ya biyota tsakaninta dashi baifi tsayin taqi goma ba.
Juyawa tayi taganshi gaf da ita ta saki ihu tana Kiran sunan Allah kawai sai taji an warce jaririn dake hannunta anyi sama dashi itama an cafki gashinta anyi sama da ita, ta tashi a firgice tana me ambaton sunan Allah.
Daidai lkcn da Hadima Ishmiyya ta shigo turakar tata ta fadi gabanta tace “yau masarautar Fazbar ta kasance cikin farin cikin shigowarki cikin addinin gsky addinin da babu nadama ga duk Wanda ya kasance a cikinsa ya shugabata kiyi sani cewa a duk sanda haske ya bayyana baqin duhu yayewa yakeyi"




Numfashi ta sauke tace “na kasance cikin rudani Jakadiya mafarki nayi ya girgizani ki nemomin me fassarar mafarki ya fassaramin mafarki na inason sanin me ya qunsa" Jinjina Kai Ishmiyya tayi tace “duk abinda kikace shi zaayi ya shugabata amma barin gaibi a matsayinta na gaibi yafi alkhairi fiye da tono abinda Allah ya riga ya boye"
Lumshe manyan idanunta tayi tace “shikenan qyale kawai basai kin nemo ba" daga haka bata sake cewa komai ba ta tashi ta wanke bakinta ta dauki tuffa ta gutsura ta tauna tanajin dadinta ta lumshe idonta tana tuno yanayin da suka kasance jiya da mijinta.
Taci yayan itatuwan sosai ta kora da ruwan tataccen ruman tayi gyatsa tare da hamdala suka koma falo suka zauna hadimanta suka zagayeta wata na gyara Mata gashinta wata tana yanke Mata farce wata tana matsa Mata jikinta, sun dauki lkc a haka sunata sanar da ita abubuwa na qaruwa cikin hikima a addini itama tana tambayarsu,
Sai yamma liqis Yarimah Nurain ya dawo Hadiman suka fashe suka barsa da matarsa yana zuwa ta kwantar da kanta a jikinsa tace “inajin babu dadi a jikina amma idan na tuna Ina kusa dakai namafi kowa kusanci da sadaukin duniya sai naji na samu nutsuwa, yakai mijina idan har bazan bata maka ba inaso ka sanar dani waini wacece ne na kasa tuna komai game dani"......
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:37 PM - Ummi Tandama: *MASARAUTAR MAYU*

_Ki biya ta wannan acc din   0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Idan katine ki dauka hotonsa ko pin lambobinsa ki tura ta WhatsApp number 09013718241: idan VTU ne ki tura ta wannan number_
      👇🏻
_09031307566_

*MM 21-22* Murmushi yayi Mata yace “meyesa kikeso ki san wani abu game da rayuwarki ta baya?" Sake kwantawa tayi a jikinsa tace “kawai dai inason sani ne yakai mijina jikina yana fadamin akwai wani abu boyayye a game dani"
Gyara zamansa yayi ya dago fuskarta yace “haqiqa kin kasance mace mafi qololuwar daraja a wannan zamanin da kowanne namiji harma mata yan uwanki suke burin mallaka badon komai ba saidon samun damar qaruwa da sirrin da ubangijinnmu ya tanada a jikinki ki"
Nan take ya warware Mata komai game da ita tare da cewa “haqiqa yake matata kiyi sani a halin yanzu mahaifanki suna hannun taqadirin mushrikin nan da kuke fautawa a baya wato boka rundatu yana azabtar dasu da nau'uka na azaba kala² domin kawai su sanar dashi inda kike, saboda azabar da yakeyi musu nasa aka zare kariyar birnin nan guda daya domin ya samu damar ganin inda kike alhmdllh ya gani harma yayo hawa ya taho Nahiyar nan domin qwatarki ya tafi dake"
Kallonsa takeyi jikinta a mace tace “amma meye yasa yakeson mallakata shima?" Miqewa Yarimah Nurain yayi ya nufi dakin baccinsu da ita ya zaunar da ita bisa gado yace “wani bangare na duniya sunason mallakarki saboda amfani da jininki domin daukakar darajarsu inda wasu kuma kaso masu yawa sukeson mallakarki domin karbar wannan zoben dake hannunki a yayin da yayan sarakai irina keson mallakarki saboda su massheki sadakarsu suke kallonki sunajin dadi i zuwa yanzu masu burin mallakarki domin budurcinki ya haska buwayar izzarsu da daukakarsu sun riga sun makara kasancewar ni daya Ubangiji ya bawa wannan damar saura mataki na gaba wanda duniya ta miqe tsaye dominsa"



Numfashi yaja ya fara shafa saman kanta tare da durqushewa ya dora hannunsa saman qirjinta yace “idan ya kasance ubangiji ya nuna buwayarsa a karo na biyu mun samu rabo a dararenmu guda biyu an sake samun cudanyan gamayyar halitta a karo na biyu to shakka babu hankalin matsafan aljanu na duniya zai qara tashi kasantuwar suna baqin ciki da cudanyar biyu a cikin daya,
Idan har jinsin halitta biyu ya

Please Login or Register in order to submit comment