Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa ba har suka isa masaukin su nurain, hankalin nurain yayi ƙololuwar tashi ganin gawarwakin mutanensa burjir a ƙasa ya durƙushe ya fasa ihu yana kiran sunan Allah daƙyar ya samu nutsuwarsa ta dawo daidai lkcn da sarki Urzan ya zagayo ta bayan wani tsauni shida tsirarun mutanen da suka rage cikin dakarun suka zube sums agaban nurain suna masu sharar hawaye.
Miƙewa yayi ya nufi wani bangare na dajin yasa aka fara haƙar rami aka binne mutane tamanin da shiddan da suka mutu nurain ya durƙushe gaban kushewar yana kuka yace 'na tafi ni kadai domin tsairatar daku daga hallaka ashe ni nakasance nine nayi wauta ƙila dana tsaya tare daku da baku hallaka ba'
Saurin dakatar dashi Sarki Urzan yayi da cewa 'kasani ya shugabana kaine kake sanar damu cewa babu ruhin da zai fita daga gangar jiki face kwanakin shaƙar iskarsa a wannan duniya ya ƙare, daren jiya mun kasance masu baccin asara har yakasance wasu gungun maridai sunzo sun kewayemu sun fara tattakamu suna wuccewa bamu ankabara ba saida sukayi mana barna sosai sannan muka tashi bamu da ƙarfin kare kanmu saboda yawansu ya gawurta da alamun ƙaura ma sukayo daga wata nahiyar suka dawo wannan, wannan dalilin yasamu sulalewa muka gudu muka barsu da gawarwakin da suka kashe tabbas da bamuyi hikimar gudu ba da mun kasance muma matattu''




Miƙewa Nurain yayi ya saɓa battarsa da kuben takobinsa ya nausa cikin dajin batare daya yiwa kowa magana ba hakanne ya sanyasu suka tattare shirginsu suka rufa masa baya suka shari hanya babuji babu gani a mafi yawan lokuta Uddatu ke nuna musu inda ya kamata subi saboda masanin dajine sosai.
Komai da zai faru cikin kwanakin Uddatu yakanji a jikinsa ya fadawa sarki Urzan shi kuma ya fadawa Nurain yakance baya buƙatar haɗa hanya da tsafi, wata hanya sukabi me yawan ramuka da kwazazzabai ga manyan tsaunuka dasuka kewaye dajin da sauri Uddatu ya shiga gabansu ya dakatar dasu yace.
'Wannan daji ya kasance na biyu a duniya wajan haɗari babu komai a cikinsa face wasu manya halittu ragowar jinsin samudawa da suka rage a duniya suna rayuwa tare da wani jinsi na arnan daji wadanda sukecin naman mutane haƙiƙa shiga wannan dajin yana buƙatar hikima domin duk wannan ramukan da idanunmu yake gani ba komai bane face sawayen ƙafafun waɗannan samudawa sannan sukuma waɗannan arnan daji suna jiyo ƙamshin mutum tun daga tafiyar kwana biyar kafin a iso inda suke.
Yakai wannan sadaukin jarumi kayi sani cewa a wannan gaɓar ƙarfi ko jarumta bazai kuɓutar damu ba face tsantsar hikimar yaƙin sunƙuru bazamu bayyana garesu ba duk da zasu kasance sunajin ƙamshinmu a kusa dasu hakan zai sanyasu su bazama neman mu mukuma zamuyi amfani da wannan damar mu rinƙa yimusu ɗauki ɗaiɗai da wannan hikimar ne zamu samu damar rage yawansu sannan saimu bayyana garesu muna masu yaƙarsu ta hanyar harbin tsakiyar goshinsu domin ananne rayuwarsu take a wannan faɗa na ceton rai babu maganar dogara da wane kamar baya dolene kowa yayi ƙoƙarin ƙwatsr kansa idan kuwa mutum yaƙi to shakka babu zai wayi gari ya iskeshi a lahira"



_Idan kina buƙatar cigaba da karanta wannan labari ki tura 200 ɗinki anan 0255526235 GTB ko card ta 09013718241_
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:58 PM - Ummi Tandama: *MM 4142* Ina labarin Gimbiya Najmah ne?
Wayewar garin ranar da ta cika kwanaki arba'in a tsare tare da Nurayyah da Juhaira ranar wani al'amari ya faru da ita domin a lkcn cikinta yake cikin watanni na takwas tanayin komai bisa qarfin hali irin nata ne kawai daqyar take zama daqyar take tashi, kullum Juhaira takan zo taganta sau biyu to a wannan rana sai ta shigo da wata gorar ruwa a hannunta ta ajiye gaban Najmah tare da daga hannunta ta bude cikinta ta dauko ruwan zata shafa Mata saboda ta sanya wasu sadaukan aljanu su daure Mata ita a nufinta na fara juyar da ƙwaƙwalwar ɗan cikin Najmah tun kafin zuwansa duniya.
Amma me zai faru? Ta tsiyayo wannan ruwa a hannunta takai d nufin shafawa Najmah kawai sai taji wata iska me ƙarfi tayi wuf da ita ta haɗata da garu take ta fado qasa matacciya cikin halin malalar jini ta baki da hanci take hankalin kowa ya tashi a wannan fadar tsafi wannan ginin tsibiri dake tsakiyar ruwa ya rinqa tsattsagewa ruwa ya rinqa tsiri yana ambaliya yana haurowa ciki.



Itakam Najmah baccinta taketayi hankalinta kwance batasan komai daya faru ba sai farkawa tayi ta ganta kwance jikin wata bishiya saman wani kilishi, ta miqe da sauri tana dudduba yanayin gurin kawai sai taji an dafata ta waiwaya da sauri taga wata dattijuwar Mata tayi Mata murmushi tace “sunana Indee mijina Idram mun kasance muna yawon farauta ne sai muka tsinceki ruwan da yayi ambaliya ya cilloki gabar kogin shine muka yanke shawarar taimakonki yake wannan gimbiya kiyi sani cewa mu mun kasance muna rayuwa a wannan daji ba tare da kowa yasan inda muke ba"
Jinjina Kai Najmah tayi shikenan ita Kuma inda Allah yayi da ita kenan, da wannan tunanin ta miqe tace “amma ya akayi kukasan wacece ni?" Murmushi dattijuwa Imdee tayi tace “na kasance duk wani abu dazai faru damu mijina yana ganinsa a cikin mafarki, tun lkcn da wadannan mushrikai suka saceki yayi mafarkin bayyanarki garemu haqiqa munyi farin ciki da zuwanki duk da bamu da tabbacin cigaba da rayuwa dake kasancewar koyaushe cikin farautarki ake Amma dai karna cikaki da surutu kije kiyi alwala kiyi sallolinki da suka tsere Miki" da wadannan kalami Najmah ta miqe take ta dauro alwala tayi sallah ta zauna tana addu'a. Idram ya shigo sabe da wata qatuwar gada ya ajiye ta tare da yankata suka gasa naman suka kawowa Najmah ta karba taci tare dayi musu gdy, suna zaune dattijan sunata yimata Hira suka jiyo wata haniniyar dawakai take Idram ya umarcesu da kowa ya rufe idonsa.



Haka kuwa akayi suka rufe idonsu haniniyar na qara tunkarosu sunaji mahayan sukazo suka tsaya a gurin sunata dube dube wani har bige Najmah yayi Amma Allah bai Basu ikon ganinsu ba sukace “kuma ance suna nan gurin gashi munzo babu ita" wani cikinsu yace “saura kwanaki uku Yarimah Nurain ya iso gareta haqiqa idan muka koma ga shugaba haka kamar mun kashe kanmu ne saidai mu nemi guri a bayan wannan tsaunin mu kafa tanti mu jira zuwanshi idan ya iso saimu yaqeshi mu sace ta da dan da zata Haifa"
Qirjin Najmah ya rinqa bugawa har saida taji Shiru ta dainajin takun dawakansu sannan ta sauke numfashi Idram ya basu umarnin bude idonsu suka bude ya dubeta yace “sunzo ne domin saceki su kaiwa shugabansu Shahas ke Wanda ya bata tsayin shekaru yana jiran isowarki yankinsa yaqi aure saboda ke yakanyi jinya saboda ke Kuma ya kasance yana bauta wa Rana ne"




Numfashi ta sauke batare da tace komai ba tana Jinjina girman wannan galantoyi da takeyi a duniya tare da tunano halin da mijinta yake ciki a halin yanzu haka ta wanxu tana rayuwa da waddannan mutane suna kulawa da ita tare da tattalin lfyrta Amma ita hankalinta yana wajen mijinta, tsayin kwanaki tana tsammanin isowarsa gareta kamar yanda taji wadannan mahayan sun fada Amma Shiru bai isoba hakanne ya tashi hankalinta take ware kanta tana kukanta tana rera baitocinta na qauna wa Yarimah Nurain.


*****

Tafiya sukeyi babu dare babu Rana tare da boyewa wadannan Arnan daji da samudawa inda sukan gansu sunzo sun wuce a haukace suna masu dalalar da yawu suna lasar baki, idan sunga haka sai sukuma su saitasu a goshi su sakar musu harbi har takai sunyiwa wadannan Arnan daji barna bata wasa ba a wannan lkcn ne wani basamude ya hango Nurain ya miqa dogon hannunsa ya cafki bayansa ya dagashi sama yana wata dariya ya dagashi daidai fuskarsa yana kallonta qanqanta irin ta Nurain.
Baiyi aune ba yaji an sakar masa harbi a qeyarsa ya saki Nurain yayi baya ya fadi wannan Abu shi ya ankarar da sauran abinda ke faruwa sukayiwa Nurain qawanya arnan dajin sunata lasar baki inda sukuma samudawan suke ta dariya sunga qaramar halitta.
Hakanne ya tilastawa dakarun Nurain futowa daga maboyarsu ciki harda Isham wanda ya qudurta a wannan karon da kansa zai murqushe Nurain, fadane ya ruguntsume baji ba gani sukam samudawan Basu da wuyar mutuwa da an saresu sai su fadi qasa amma arnan dajin baa cewa komai don kusan awa uku aka debe ana bata kashin Amma sun kasa qarar dasu gasu da mugun yawa wai danma Uddatu yana taimaka musu da harbinsu a tsakiyar Kai.




Haka wannan rana ta qare gumurzun bai qare ba dare ya shiga anata Kai ruwa rana daqyar da taimakon wasu gungun mayaqan aljanu suka samu suka gama dasu, sunso hutawa anan Maharbi Uddatu yace aa suyi qoqarin fita daga dajin saboda su wannan arnan dajin basa wucce sa'a uku a mace ake dawo musu da rayuwarsu Kuma idan har suka tashi barna zasuyi,
Hakace ta sanyasu daukar hanyar barin dajin dukkansu sun gaji suka nufi daji na gaba wanda babu komai cikinsa sai kunamu haka suka rinka soke kunamun suna wuccewa har sukayi katarin fita sannan suka zauna suka fara hutawa, a wannan zama ne wadannan mahaya sukazo suka ishesu sukam sun San waye Nurain shiyasa basuyi yunqurin budawa dashi ba saima gudu da sukayi.
Bayan sun huta ne suka fahimci ashe Isham baya cikinsu take suka fara tambayar junansu inda yake nan ne wani yace ai sun yabi wadannan mahayan, Nurain bai wani damu ba yaja zugarsa suka qara gaba gabadayansu yanzu basufi su ashirin ba.




Maharbi Uddatu shine a gaba shine yakeyi musu jagora zuwa wannan tsibiri da aka boye Najmah a ciki suna tafe suna yada zango suna hutawa har suka isa bakin tekun da tsibirin yake kai suka fara zagaya wannan tsibiri Amma babu wata alama ta antaba halittar wani mahaluqi a gurin nan take hankalin Nurain ya qara dugunzuma ya durqushe ya zunduma ihu na tashin hankali.
Daidai lkcn wata guguwa me qarfin gaske ta taso ta turnuqe inda suke cikin guguwar sukaga wani haske me tashi yazo ya giftasu a haka Nurain ya tashi ya hau dokinsa ya zabureshi ya rinqa bin wannan haske suna gudun wucce sa'a daidai lkcn da haske ya ratsa jikin wata bukka ya wucce daidai lkcn da yaji kukan jariri ya kewaye wannan daji gabadaya take wata kabbara me qarfi, tsayawa yayi yanason gane ta inda kukan jaririn yake tasowa,
Sake zaburar dokin yayi yabi wata siririyar hanya da yakejin kukan jinjirin nayi masa jagora da sauri da sassarfa yake tafi cikin duhuwar itatuwan da kwazazzabai har ya ishe inda yakejin kukan jinjirin na qara tunkarosa bayan wani dutse ya zaga ya tsaya anan yaji kukan jinjirin ya tsaya sai nishi kawai da ajiyar zuciyar jaririn, kutsa Kai yayi tsakankanin wani dutse anan ne yayi arba da Najmah kwance cikin jini ga jaririn kwance samansu lullube da wani qyalle anyi rubutun muftahul Islam.


_Paid book ne, idan ku biya ta wannan hanyar 0255526235 Fauziyya Tasi'u GTB or card ta WhatsApp a wannan number 09013718241 pls banda VTU idan VTU zakiyi kiyi ta wannan 09031307566_
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:58 PM - Ummi Tandama: *MM 4344* Kabbara Nurain yayi ya sauka daga kan dokin ya tsugunna da sauri ya dauki dannasa me tsananin kama dashi ya rungumeshi a jikinsa yana tasbihi da taslimi ga Ubangijin halittu wanda ya azurtashi da wannan da cikin wannan yanayi da idanun duniya take kansu,
Ji yayi wata murya ta katse masa tinani da cewa “wannan kyauta ce daga mafi girman masu bada kyauta Kuma mafi amincin masu aminci ya zabeka ya baka kyautar mabudin Muslumci takobin datse kafirci haqiqa Allah abin kayi sujjada a gareshi ne" Koda Nurain yaji haka saiya durqushe gwiwowinsa a qasa yayi sujjadah yana me yiwa ubangiji kirari har zuwa gushewar wani dogon lkc sannan ya tashi ya zubawa Najmah dake bacci ido yayi murmushi tare dakai hannunsa ya dafa goshinta ya shafo gumin da yake tsattsafo mata, daidai lkcn da wata sukuwar dawakai ta tunkarosu ya miqe da sauri yana me zare takobinsa ya bada fadi.



Sukuwar tana qara tunkarosu qura na turnuqe sama gurin ya gauraye da kuka gami da haniniyar dawakai wani hasken tsafi suka sakarwa Nurain a idanunsa nan take ya daina ganin komai hakanne ya basu saar dauke Najmah da Islam suka gudu dasu,
Tafiya ce ta yini da kwanaki sukeyi da su inda sukabar Nurain yanata lalube yana ihu yana Kiran sunar matarsa da dansa a haka mahaifan Najmah da sauran tawagar mayaqan Yarimah Nurain suka iso suka isheshi baya gani amma haka ya nuna musu hanyar da sukabi da Najmah take suka rufa musu baya suna gudu na wucce sa'a.
Tun basa ganin qurar dawakan wadannan mahara har takai sun fara hango qurarsu, to Suma jin yanda ake bibiyarsu ne Kuma suna gani cikin madubin tsafinsu ya sanya suka bawa amintaccen Sarki Ma'esh ita da danta ya tafi dasu suka sukayi turjiya suka tsaya suna jiran qarasowar wadannan mayaqa.




Aaikuwa haduwar batayi kyau ba saboda suna haduwa basuyi wata wata suka ruguntsume da fadan inbakayi bani guri, tabbas wannan haduwa ta maza da maza ce domin mutuwar kasko suka rinqayi tsakanin mayaqan Ma'esh dana Nurain cikin wannan tafiya babu Wanda ya tsira sai Sarki Urzan da Maharbi Uddatu.
Suma cikin mayaqan Sarki Ma'esh babu Wanda ya tsira sai wannan mahayi daya tafi da Najmah da Islam, zubewa Maharbi Uddatu yayi a gurin yana razgar kuka a saboda yasan cewa idan har Najmah ta shiga hannun Ma'esh qaramin yaqi bazai fitar da ita ba domin zai juyar Mata da tunanin ne ta yanda zata sake mantawa da komai ciki harda mijinta balle kuma su yan karere.
Da wannan tunanin suka juya domin sanar da Nurain abinda ya faru suka isheshi cikin jini kwance kamar gawa, wannan al'amari ya qara tashin hankalinsu suka daukeshi suka nufi inda suka baro wannan bukka a baya anan suka fara yimasa magani tsoho Idram ya dorashi akan magunguna.


******

Shiko wannan mahayi bai zame ko Ina ba sai masarautar Istanbul Inda sarki Ma'esh yake mulki ya shiga a jigace ya kwantar da Najmah a gabansa, tasowa yayi da sauri ya bude fuskarta ya dago yace “itace Nalwan haqiqa ka tabbata amintacce na ka zaba daga duk wata nau'in dukiya dake cikin wannan masarauta da Mata ka dauka na baka Najmah itace cikon farin cikina, tabbas duk duniya nine nafi kowa cancantar mallakarta saboda ni ba nasararta nakeso ba ita nakeso, zan cire Mata komai na mantar da ita komai kamar yanda Nurain yayi Mata na dasa mata kaina haqiqa yayewar damuwata tazo quncin zuciyata ya yaye yanzu zan fara rayuwa"
Godiya wannan Bafade yayi ya tashi ya nufi inda zai sadashi da gidanshi shikuma Ma'esh ya dauki Najmah ya shiga da ita cikin gidansa bangaren daya tanada ya zuba masa tsaro dominta da danta Islam, dakansa ya rinqa yimata magani tsayin kwanaki bakwai sannan ta farfado.
Tana farkowa da kalimatusshahada ta farka bayan ita bata iya tuna komai ba sai danta dake kwance a gefenta data zubawa ido tana kallon Ma'esh tana kallonsa shikuma sai murmushi yakeyi Mata yace “na Kira Dana da Suna Muhsin" a hankali ta janye idonta daga nasa tace “Albarka da wadata qarfi da buwaya su tabbata ga Ubangijin daya halicci Islam yayishi a cikin musulumci Kuma ya kirashi da suna Muftahul Islam tabbas ni nakasance uwa a gareshi saboda haka na sabunta sunansa zuwa Muftahu"




Kama hannunta yayi ya sumbaceta yace “bazanja da duk abinda kikace ba yake wannan sarauniyar da ta shafe shekaru ashirin tana mulkin zuciyata zan kasance meyi miki biyayya ina fatan kema zakiyimin biyayya muyi rayuwar soyayya"
Kwantar da kanta tayi tana kallonsa fuskar Nurain take gani a fuskarsa saboda haka ta Jinjina masa Kai yayi murmushi ya miqe ya dauki Muftahu suka fice ita Kuma bayinta suka shigo suka taimaka Mata ta gyara kanta sannan akayi Mata kwalliya ta sarautar masarautar sukayi Mata jagora har fadar sarki Ma'esh yana ganinta ya miqe ya rusunna mata alamun girmamawa haka kowa yayi Saida ta zauna sannan kowa ya zauna.
Nan aka fara gabatar da shagalin bikin sunan Muftahu shagalin daya samu halartar manyan sarakunan yankin a cewarsa Matarsa ce ta haihu domin shekara biyu baya ya aika musu da takardar cewa yayi aure haka aka yini ana shagalin da dare ya raba aka shigar da Najmah turakarta tayi Shirin bacci sannan ta dauki danta ta fara shayar dashi kamar yanda kowacce uwa take yiwa danta tanajin wani Abu na yawo a zuciyarta data kasa tuna menene.




Bayan ta gama shayar dashi ta kwanta bacci ya dauketa bataji shigowar Ma'esh ba sai jin hannunsa tayi yana yawo a jikinta ta janye da sauri tare dajan a'uziyyah yayi saurin matsawa daga jikinta yana me sauke numfashi yace “nazo na kwanta kusa da abar qaunata da dana Ina fatan hakan bazai zama matsala ba?"
Sauke kanta tayi tace “zanfi farin ciki idan ka nisanta kanka Dani har zuwa ranar dazan neme ka" miqewa yayi a kasalance ya juya ya fice da sauri saboda son da yakeyi Mata bazai taba bashi damar jayayya da duk abinda ta nuna tanaso ba.
Itanma bawai dan taso hakan ba saidon takasajin abinda takeji baya game dashi ne, haka ta koma ta kwanta tanata tunanin abubuwa mabambamta wani bangare na zuciyarta ya tunano Mata rayuwarta da iyayenta sai taji kamar mafarkine tayi jiya wani bangare ya tunano Mata rayuwarta da Nurain a masarautar Fazbar itama saita wucce kamar mafarki haka ta wanzu wannan dare tana saqawa da warwarewa da haka har bacci ya dauketa cikin baccin tayi mafarkin Nurain da halin da yake ciki tare da umartarta da taje gareshi shine asalin nata.



_Paid book ne, idan ku biya ta wannan hanyar 0255526235 Fauziyya Tasi'u GTB or card ta WhatsApp a  wannan number 09013718241 pls banda VTU idan VTU zakiyi kiyi ta wannan 09031307566_
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:58 PM - Ummi Tandama: *MM4546* Kwanaki suka rinqa turawa da abubuwa mabambamta komai yana canzawa game da Najmah da danta kulawa sosai Ma'esh yake basu rayuwarsu gwanin sha'awa Abu daya yake ci musu tuwo a qwarya itan taqi yarda dashi matsayin miji inda shikuma yaqi hqr ya qyaleta kullum zuwar Mata yakeyi da sabon salo da sabuwar qauna.
Lamarin dayake mantar da ita komai Amma qasan zuciyarta yana fada mata kullum akwai wani Abu me muhimmanci data rasa a rayuwarta, wani Abu dake bata mamaki shine yanda Muftahu yaqi yarda da Ma'esh duk tsanani yana manne a tare da uwarsa,
To yau tun safe Najmah takejin faduwar gabanta na tsananta haka dai ta yini a daddafe wajen faduwar rana sukaga garin Istanbul yayi baqin qirin lamarin daya daga hankalin kowa dake rayuwa a garin Amma banda Najmah wadda a lkcn take gabatar da addu'o'inta.




Ji tayi numfashinta yana daukewa tayi saurin dauko danta Muftahu ta rungume a jikinta ta kwanta tana me ja musu bargo Amma me? Kawai sai taji Ma'esh ya danno dakin da sauri yana qwala Mata kira ta miqe da sauri ya shigo tare da mayar da qofar ya rufe yace “nagaji da kiwon makahon doki kullum saidai na baki kici Kisha kin kasa anfanar dani Najmah a daren nan sai kin bani abinda kike tanadinsa domin Nurain saboda nafishi cancantar mallakarsa"
Zaro ido tayi tana maimaita “Nurain! Nurain Yarimah Nurain Fazbar Qubhar" haka abubuwa suka rinqa dawo mata daidai lkcn da yake cire kayansa ya nufota da sauri ita Kuma ta janye da sauri nanfah suka rinqa zagaya dakin har yayi nasarar kamata abin mamaki suka rinqa kokawa ya kasa kaita qas daqyar ya budata yana qoqarin zare Mata rigarta kawai ta baya sai taga nan kama wuyan Sarki Ma'esh an dagashi sama ta miqe da sauri cike da tsoro.
Matsawa ta keyi wani shirgegen mutumin yana binta ta sunkuci danta daidai lkcn da yayi cilli da Sarki Ma'esh ya fado qasa sumamme daidai lkcn da ita Kuma ta samu nasarar daukan danta ta kwasa da gudun tsiya wannan shigegiyar halitta tana binta tana gudu tana waiwaye ga danta a matse a qirjinta.
Abin mamaki sai taga garin babu kowa sai iyayen gawarwaki wasu an qwaqule musu ido wasu an farke musu ciki gasu nan dai abin babu kyawun gani, ita kanta mamakin gudunta takeyi kamar walqiya haka take keta gurare tana wuccewa itama wannan halitta tana binta.




Da haka har Najmah tayi nasarar ficewa daga wannan birni ta keci daji tana gudu kamar zata tashi sama haka suketa keta dajin kawai sai taga wannan shirgegen mutumin ya rikide ya zama wata qatuwar bauna take ta saki qara ta sake qara qaimin gudunta wasa wasa Saida suka kwana suna keta dajin daidai ketowar alfijir qarfinta ya qare ga wani wawakeken rami da take hangowa,
Qara nufar ramin takeyi tazararta da wannan bauna tana qara raguwa har takai ta qure nisan ramin taja ta tsaya cikin tashin hankali irin Wanda bata taba shigaba ta sake qanqame danta ta tsaya cak domin tana qara taku daya cikin ramin zata fada itama wannan Bauna tana isowa ta dunguri qasa tayi girgiza ta dawo asalin suffarta qara matse danta tayi lkcn da wannan halitta ta daga zaqo zaqon faratanta zata saukesu akan Najmah ita Kuma ta rintse idonta tana Kiran sunan Allah,
Kusan rabin saa ta shafe idanunta a rintse tana jiran tajita a wata duniyar ba tasu ba Amma sabanin haka sai tarinqa jin sanyin iskar gurin na canzawa zuwa wani daddadan qamshi da bazai taba gushewa kwanyarta ba a hankali Kuma cikin sanyin muryarsa ya matsa gabanta yasa hannu da nufin karbar Islam ta qanqameshi yayi murmushinsa na saraki yace “Nine fah Gimbiya Najmah me kikejin tsoro?"



Ita kanta muryar bazata taba gogewa a tunaninta ba hakance ta sanyata sauke ajiyar zuciya tare da bude idonta a hankali ta saukeshi cikin nasa yasa hannu ya karbi Islam yana fadada murmushinsa yace “tsarki ya tabbatar ga Ubangijin daya sake hadani da ahlina bayan sunyi nisa dani tsayin shekara guda" janyota yayi jikinsa ya rungumesu dukkansu yana me sauke numfashi yajasu sukabar bakin ramin yana cewa “rayuwa bazatayi haske ba harsai mun hada qarfi da qarfe mun yaqi duniyar tsafi da kafirci tabbas ke haskece a wannan duniya dukka hankalin duniya akanki yake matata bayan mun huta yau zan wucce dake Qubhar canne nakeda tabbacin zaki samu tsaro"
Sunyi tafiya me tsayi kafin suka isa tantinsu ya bude Mata ta shiga ya kwantar da Muftahu da yake baccin wuya ya juyo gareta ya kamota ya hadata da jikinsa ya dora bakinsa saman kuncinta ya sumbaceta suka sauke ajiyar zuciya yanajin wani shauqi na ratsashi, fita yayi ya nemo mata abinci ya dawo ya bata taci sannan labarin ya canza sukayi qara'in abubuwa da yawa a wannan safiya sunji dadin kasancewa da juna sannan sun yardarwa kansu sunyi kewar juna.
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:58 PM - Ummi Tandama: *MM4748* kwanaki takwas sukayi suna rayuwa a wannan daji cikin kariyar ubangiji a kwana na tara ne suka dauki hanya domin komawa birnin Qudhar inda suka dauki tsayin wata biyu suna tafiya kafin su isa birnin suka Sarauniya Badiyyah da mutanenta sukayita murnar wannan arziqi da sukayi ga Muftahu har yayi wayo nan aka shiga bikin murnar dawowar Najmah garesu.
Haka suks wanzu a wannan birni cikin kulawa da tattalin juna duk da kasancewar Najmah kullum cikin miyagun mafarkai amma ta kwantar da hankalinta tana rayuwa tare da danta da mijinta cikin qauna da tattalin farin cikin juna, a cikin shekararsu biyu a birnin Qudhar suka koma Fazbar inda anan ne suka samu wata tawaya data zame musu matsala cikin rayuwar data cika da farin ciki



A masarautar Fazbar Najmah ta tarar da mahaifinta tayi murna ta rungumeshi sabida ganinsa ya dawo Mata da tunaninta na baya anan ne take tambayar sa mahaifiyarta nan yake sanar da ita ai a gumurzun da akayi wajen ganin an cetota mahaifiyarta ta mutu.
Sosai tayi kukan rashin mahaifiyarta kafin ta hqr suci gaba da Hira yana fada Mata halin da ake ciki a garinsu da dalilinsa na dawowa nan da zama hankalinta ya tashi ta rinqa tunanin mafita kafin ta kalli Nurain tace “ina neman izinin mijina idan Allah ya saukeni lfy na haife abinda yake cikina zanje garinmu domin jihadi tabbas amafarkina kullum ana nunamin cewa inhar mutanen dake rayuwa a wannan qasa zasu karbi addinin musulumci to tabbas kashi saba'in na matsalolinsu zasuyi qaura"



Jinjina

Please Login or Register in order to submit comment