Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kai Nurain yayi ya shafa cikinta yace “bazan hanaki taimakon muslumci ba nima zan bada gudunmawa ta a wannan jihadi naki" rungume juna sukayi cikin shauqi suka tashi sukayiwa Maharbi Uddatu sallama sukaje suka kwanta suna kwanciya Yarimah Nurain yajata jikinsa yana sunsunar wuyanta yace.
Bana gajiya da qamshin jikin matata da ni'imarta shigewa tayi jikinsa tana shafa qirjinsa tace “dan tayin cikina Kuma ya gaji da wahalar da babansa yake bashi" dariya sukayi tare suka hade bakinsu suna shaqar numfashin juna da haka komai ya canza.
Watanni biyu cikin ikon Allah da asuba Najmah ta haifi diyarta mace wannan "barakallahu ahsanal khaliqin" haqiqa wannan yarinya ta gigita duniya domin maganar kyau kam an qareshi ta hade kyawun uwarta dana ubanta duka a kanta ita daya.




A ranar da akayi haihuwar Sarauniya Badiyyah ta dira qasar Faris wani ruwan magani tayiwa yarinyar wanka dashi ta dura Mata ta baki da hanci sannan ta turareta da wani turaren magani ta lullubeta.
Bayan ta gama ta kalli Najmah tace “sabuwar masifar da zamu shiga tafi ta baya Gurail Uzair yace lallai ku kula da masu zuwar muku barka idan da hali ma ku hana ganin Samrah ta kasance cikin tsaro idan ba haka ba Zaku haifawa duniya yaya"
Numfashi Najmah ta sauke tace “inaji a jikina daya cikin yayana bazai rayu dani ba tabbas idan har Muftahu ne bazanji komai ma Amma idan ya kasance Samrah ce to zan wanzu cikin damuwa da kuka mara yankewa"



Tana gama fadin haka ta miqe ta bude fuskar Muftahu da yake bacci yana murmushi ta leqa fuskar Samrah taja zuciya ta koma ta zauna tare da daga hannunta tace “ina roqon ubangiji ya tsaremin ahlina a duk inda suke" daga hak yaa bata qara cewa komai ba ta kwanta tana me tofa musu addu'a bacci ya daukesu.
Hakanan ta wanzu tana rainon yayanta cikin tarbiyyar islama inda a bangare daya Nurain ya mayar da hankalinsa wajen koyawa Muftahu salo na yaqi ita Kuma take koyar da Samrah, Samrah ta kasance yarinya me tsananin basira kaifin qwaqwalwa da zafin nama hakan yana yiwa iyayenta dadi,
Yau ta kasance juma'a bayan sun gabatar da sallar La'asar suka shirya kamar yanda suka saba da nufin fita kilisa kowa zai hau dokinsa daban amma saboda tsananin soyayya ta tsakanin da da mahaifi Gimbiya Najmah bata yarda Samrah ta hau doki ita daya saidai su kasance tare.




Haka wannan kilisa ta kasance suna gama Nurain da Muftahu suna biye dasu har suka isa inda akayi musu shimfidar kilisai suka zauna suna masu tattaunawa miqewa Nurain yayi ya harbi wata barewa inda Muftahu yabita da gudu shima Nurain ya rufa masa baya.
Barewar tana gudu suna binta har suka samu suka cim Mata Muftah ya sabota a kafadarsa Nurain yana biye dashi suka iso inda suka bar Najmah da Samrah suka yanka barewar suka saka a jakar da suka taho da ita ashe Basu sani ba wannan barewa ta tsafi ce,
Suna zuwa gida suka bude wannan jaka Nurain yaja baya da sauri ganin wannan barewa ta zama dutse Muftahu ni ya dana kibiya tare da Bismillah ya harbi dutsen take ya tarwatse Samrah tanata dariya, suka rankaya suka shiga ciki Muftahu yana tambayarta abin ya qayatar da ita ko? Ta daga Masa kai, bayan sun hadu a wajen cin abincin dare sunci sunyi karatun qur'ani da wasu cikin littafan addini suka kwanta cikin dare suka rinqa jiwo ihun Samrah tana kiran Abul Ummuh Muftee miqewa Nurain da Najmah sukayi cikin tsananin tsoro suka kunna fitilar suka nufi dakinta shima Muftee ya fito ya wuccesu a guje ya shiga dakin qanwar tasa abin mamaki tana zaune a gadonta idanunta ya kada yayi jajir jikinta yayi baqin qirin lamarin daya tashi hankalin Nurain Najmah da Muftee.
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:58 PM - Ummi Tandama: *MM4950* Matsawa Najmah tayi ta Kama hannun yar taka sai tajita a sandare take ta zame ta fadi ta fara bacci zama sukayi sunayi Mata addu'a a hankali jikinta ya rinqa washewa ya rinqa washewa asalin fatarta ta bayyana suka sauke numfashi sukayi suka tashi suka fice suka koma dakinsu,
Kwanciya sukayi dukkansu babu bacci a idonsu sai juyi, washegari da asuba bayan anyi sallar asuba Najmah ta koma dakin Samrah ta isheta tanata bacci ta shafa fuskarta tare da qoqarin tashinta daqyar ta tashi tasata tayi sallah sannan ta sake kwanciya.
Wayewar gari ce ta sanya Gimbiya Najmah komawa sashinta ta zauna tana mamakin abinda ya hana yar tata isowa gareta Muftee ne yaketa dawainiya da Samrah ya fahimci batada walwala kamar ko yaushe, sai dare yayi Mata sallama ya tafi ya kwanta Gimbiya Najmah ma bayan taje da taganta tayi Mata addu'a ta tura Mata daya cikin bayin da suke kula da ita domin ta kula da ita.



Misalin Biyu na dare yauma kamar jiya sukaji ihunta tana kiran sunansu wannan karon Najmah ta riga kowa fita ta nufi dakin nata tajishi a qarqame sai wani gurnani da yake tashi da wata qara, haka Nurain da Muftee sukazo suka ishe Najmah tanata dukan qofar tana Kiran sunan yar tata Amma taqi budewa har saida Muftee ya da Nurain suka balle qofar suka haska dakin tare daja baya da sauri tsoro ne ya cika su Najmah ta durqushe da sauri ba komai ne yatada hankalinsu ba sai yanda sukaga Harsina baiwa kwance male male cikin jini an qwaqwule mata ido cikinta a farke an fitar da kayan cikin, babu numfashi a tare da ita, miqewa tayi da sauri ta matsa gaban gadon da Samrah take ta tarar da ita tanata baccinta cikin kwanciyar hankali,



Numfashi suka sauke dukkansu suka fara leqe leqe lungu da saqo babu abinda suka gani hakan ya sanyasu gyara gurin da kansu suka dauke gawar Harsina suka fita da ita cikin tunanin abinda yayi Mata wannan kisan gillar, ranar a gurin Samrah suka qarasa kwana da safe ake mayar da zance Samrah dai bata cewa komai sai kallon kowa takeyi yanayin yarinyar me shekaru biyar gabadaya ya canza abinda yake dagula rayuwar iyayenta.
Abinda ya qara firgitasu wannan daren ma abinda ya faru kenan aka sake tura Mata bayi biyu Suma haka aka daukosu cikin irin yanayin da aka dauko Harsina, a dare na uku ne iyayen sukayi nufin kwanada ita domin ganin abinda yake kashe bayin dake kwana da Samrah Najmah ce ta kwanta a gefenta Nurain yana qasa yana kishingide, can talatainin dare ya rinqajin gurnani na tashi ita kuma Najmah ta rinqajin ana zagaye cikinta da wani Abu kamar wuqa batare da bata lkc ba ta riqe hannun dake zagaye Mata cikk tama me addu'a ta bude idonta tar akan Samrah daketa dalalar da yawu tana wani irin gurnani tana qoqarin qwacewa daga riqon da Najmah tayi Mata miqewa Najmah tayi ta dura daga gadon shima Nurain ya matso ya riqe Samrah suka danneta sunayi Mata addu'a ita Kuma sai kuka takeyi tana Kiran ”jini! Jini!! Zansha jini" qololuwar tashin hankali Wadannan iyali sun shiga addu'a sukeyi Mata Amma sake shidewa take tana Kiran “Durrah zansha jini! Jinin Mahaifiyata me qaramin ciki zanci jininki zan sha"




Basuyi aune ba ta damqi wuyan Najma ta kafa Mata farata suka rinqa kokawar qwacewa itan Kuma taki saki Najmah ta gama galabaita sai kakari takeyi duk qarfin jarumtar Nurain ya kasa qwatar Najmah kwatsam sai Allah ya jeho Muftee kamar zarae qaya kawai sai Samrah ta zube sumammiya ta saki wuyan Najma da itama take cikin halin Suma Muftee ne ya matsa gabanta ya hasketa yana me qare Mata kallo yace “yakai Mahaifina cikin baccina akq sanar dani wani Abu ya faru daku kayi gaggawar sanar dani na rantse da ubangijin da yake busamin numfashi sai na dauki fansa"
Kallonsa yayi yace “yakai Dana kayi sani dara a waje ake daukar fansa idan yaci gida rufewa akeyi kayi sani cewa wani baqon al'amari ya shigo rayuwarmu qanwarka tana cikin wani mawuyacin hali har yakai ga tana neman hallaka mahaifiyarku kayi sani cewa qanwarka itace take hallaka duk bayin da suke mutuwa a dakin nan tana shanye jininsu.....


_Manage_
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:58 PM - Ummi Tandama: *MM5152* Cikin tashin hankali Muftee yake kallon mahaifinnasu da wata fuska ta razani, juyawa yayi ya fice da sauri daga dakin nurain yabishi Amma Bai gansa ba bayan wani lkcn sai gashi ya fito dauke da wata tsohuwar hula ya sake wucce su ya shige dakin da Samrah take kwance ya Isa gabanta ya dora Mata hular take ta wani firgita ta miqe tsaye tana wani irin ihu tsayin lkc sannan komai ya lafa ta zube a qasa.
Duban juna sukayi Najmah ta matsa gabansa da sauri ta riqeshi tana me cewa “yakai daina meyene ma'anar hakan?" Gumi ya sharce yace “kiyi sani wannan hular a mafarki aka bani ita aka umarceni da na sanya Mata hakan zaisa mu fahimci inda matsalar take kuyi sani wannan barewa da muka harbo an aikota ne domin ta sace Samrah Kuma zata saceta din domin kuwa har yanzu tana rayuwa a cikinmu, saceta ba yana nufin yankewar farin cikinmu ba ni nine zan karbota"
Jikinsu yayi matuqar sanyi Najmah ta koma jikin Nurain ta kwantar da kanta a qirjinsa tana kuka me ban tausayi shikuma yana shafa bayanta a haka har gari ya waye musu,




Tun daga wannan ranar ya zamana kullum da dare zasu kwanta da Samrah amma da safe sai suji ance an qwaqwulewa wane ido an farkewa wane ciki, sai ya zamana a masarautar Fazbar andena yawon dare kowa yana tsoron ya zama gawa, a wannan yanayin ne Gimbiya Najmah ta shirya domin cika alqawarin da tayiwa kanta na kawo sauyi a rayuwar mutanen alqaryarsu, suna kuka haka sukayi bankwana ta nufi birnin Jawal cikin qarfin gwiwar jihadi don qarfafa kalmar Allah.
Tafiya ce bata yanzu ba bata Anjima ba haka ta rinqa ratsa tsaunuka da dajuka harta isa wani daji na wasu mazauna daji tana tafiya ne cikin kariyar ubangijinta fuskarta nade cikin wani farin nadi taji sun kewayeta ta tsaya a tsakiyarsu sunayi Mata kallon mamaki itama tanayi musu.




Daya cikin mutanen ya matso gabanta yace “yake wannan yarinya shin meye ya ratso dake ta wannan daji Kuma daga Ina kike?" Itama dubanshi tayi tace “ni na kasance baiwar Allah na fito daga qarar Faris qarqashin masarautar Fazbar da nufin zuwa masarautar Jawal domin jihadi da Kuma kawo musu qarshen halin da suke ciki domin ni na kasance hadima ta Ubangiji a doron qasa"
Mamaki ne ya cikasu suka rinqa kallonta wani cikinsu yace “ya zaayi kina mace kice Zaki tafi wata nahiya domin wannan gagarumin aikin meye yasa Yarimah Nurain bazai je ba saike bayan kema kin kasance kinada mara lfy tabbas yarki Samrah tanacan a halin yanzu ta hallaka kakanta mahaifin Yarimah Nurain sarki Fawwaz wani Abu da baku sani ba tun daren farko da kuka Kai wannan barewa gdanku ta sace yarku ta ajiye muku wannan mayyar yarinyar da nufin ta hallaku saboda sun tabbatar da cewa hakance kawai zatasa suyi nasara akanku"



Zaro ido Najmah tayi tace “ya akayi hakan ta faru?" Dariya wadannan mutane sukayi daya cikinsu yace “sunana Lukman mun kasance mazauna dajin nan tsayin shekara bakwai mun kasance muna kusa da birnin Jawal lkcn da suka gama da junansu ya kasance babu wani sauran mutum daba maye ba a wannan gari sai suka fara shigowa garinmu sunayi mana dauki daidai tare da debe mana amfanin gona ganin suna neman halakamu ne yasa mukayo qaura muka dawo nan da zama yake wannan gimbiya haqiqa da zaki iya Zaki samu lada kasancewarki yar wannan alqarya shigarta zatayi miki sauqi Amma bazaki iya fada da wadannan mayun ba Ina me shawartarki daki koma ki nemi yarki zaifi miki fiye da kije wannan alqarya"





Numfashi Najmah ta sauke tace “karsashin musulmi na qwarai baya sarewa saboda labarin me labari yakai wannan dattijo kayi sani ceton rayukan al'ummah da yawa yafi na tsaya domin ceton rayuwar yata Samrah ita kadai inada tabbacin zata kasance cikin kariya da tsaron Ubangiji Kuma Ina roqon Allah yabata nasara a duk inda take, tabbas buwayar izzarmu zata game duniya nanda dan qanqanin lkc"
Daga haka bata Kuma cewa komai ba ta kada linzamin dokinta tayi gaba suka bita da ido har saida ta kusan qulewa sannan wannan Dattijon Mai suna Lukman ya taso wasu zaratan Mata guda uku yace su rufa Mata baya, taso hanawa amma suka kafe akan Suma sunaso suyi jahadin dole ta qyalesu sukaci gaba da tafiya suna yada zango a qauyuka da birane sallah ce kawai take tsayar dasu da cin abinci da haka har suka isa qofar birnin Jawal dakatar da kowa Najmah tayi tace “inason mu fara nazarin canjin da aka samu a wannan birni kafin shigarsa".....
9/10/20, 8:59 PM - Ummi Tandama: *MM5354* Koda gama fadin haka saita nufi qofar birnin tare da rintse idonta cikin kariyar Ubangiji masu gadin qofar suna ganinta Amma Basu iya yi Mata mgn ba harta wuccesu ta nufi cikin birnin bisa saman ingarman dokinta tana tafe tana karanto addu'ar neman tsari,
Kallon kowa takeyi kowa yana kallonta harta isa inda tsohon gidan iyayenta ga mamakinta bata tarar da komai a gurin ba hasali ma ganitai gurin ya shafe ya zamana babu wata alama da take nuna an taba zama a gurin, numfashi ta sauke ta juya domin tafiya ta taho da wadannan yammata Amma me? Sai taga mutane sun kewayeta, mamaki ya cikata ganin su har yanzu Basu canzaba sunannan da jahilar al'adarsu data sansu da ita sai kallonta sukeyi suna dalalar da yawu.
Daya cikin mutanen ya nufota gadan gadan ganin hakan ya sanyata gyatta tsaiwarta taja daga tare da zare takobinta wani haske ya fita daga cikin kuben takobin ya haske gurin abinda ya janyo hankalin Yarimah Isham da tunda ya dawo daga farautarta ya rasa saa yayi zuciya ya kulle kansa a wani daki me duhu inda babu wani haske da yake ratsa dakin.



Bincikensa na tsafi ya tabbatar masa zatazo gareshi hasken takobinta ne kawai zai iya ratsa wannan dakin da yaketa tsuma kansa a it ciki domin yaqarta ya Kuma yaqi Nurain, Koda ganin wannan hasken saiya miqe cikin matsanancin farin ciki ya balle qofar da qarfin sihirinsa ya fito a cike da farin ciki ya nufi wajen masarautar tasu ya rinqabin hasken takobin har ya Isa gurin da ake tafka yaqin tsakaninta da wadannan mayu, take ya daka musu tsawa suka dare jikinsu na bari ya nunasu da yatsa dukkansu suka zagwanye suka zama ruwa.
Bin gurin tayi da kallon mamaki ya tuntsure da dariya yace “barkanki da zuwa masarautar mayu a karo na farko bayan barinki cikinta yake wannan kyakkyawar Gimbiya uwar kyawawa sirrin nasarar data sanya duniya cikin halin ha'ula'i



Murmushi tayi ta sauke takobinta tace “ba jayayya ta kawoni ba mafita nazo muku da ita Alan wannan ciwon da yake addabarku wajibi ne kuyi biyayya domin tseratar da al'ummah daga sharrin wannan maitar da aka gada mawa jama'ar wannan gari tabbas ko sarki Jamal ya kawomin matsala cikin aikina zan sare kansa ne kafin na Isa ga gunkinku da kuke bautawa wato Harsan na cire muku aya cikin tsakuwa..."
Tsawa ya daka Mata ta tsaya tana kallonsa ya nunata da yatsa yana huci yace “ko mijinki yayi kadan Najmah balle ke qaramar qaramar halitta kiyi sani baki Isa ki warkar da mutanen garinnan daga ciwon da suka gada iyaye da kakanni ba wannan maitar" kaki yayi ya kako wani gudan jini lagwaigwai kamar hanta sannan ya sakeyin kaki ya Kuma kako wani kore yace “wannan itace maita baki isa ki rabamu da ita ba domin ta zame mana gata Kuma garkuwa a duniya, bari kisan wani Abu a halin da ake ciki yanzu duk Wanda ya shigo wannan masarautar baya fita face mun mayar dashi maye saboda haka..."




Kafin ta ankara tajita daure tamau cikin wata sarqar jan qarfe tayi duk me yuwuwa domin ta kwance ta kasa kawai sai tayi murmushi tace “a hakanma saina yaqeku shammata ta ragoce fadan tsafi na ragone ka bari mu gwada qwanji tanan ne zaa bambamce tsakanin macen mazaje da namijin mataye..." Wannan kalma ta mataye itace ta fusata Isham ya sake aika wani haske ita Kuma ta hada qarfinta ta zare takobinta take wannan hasken ya sake fitowa yayi qasa da jan hasken da Isham ya turo yabi sarqar ya rinqa kacaccalata Saida tayi gutsu gutsu ta zama gari.
Sakin baki Isham yayi yana kallonta tayi murmushi tace “ya kaga salon wasan?" Bai bata amsa ba sai kafeta da yayi da ido yana qiyasta irin kyawunta amma kullum boyesa takeyi, sake takowa tayi zuwa gabansa tace “a karo na biyu bayan mijina yayi maka tayin shiga addinin gaskiya wato musulumci nima inayi maka idan kaqi kuwa to karo na uku zai kasance tayin dole karbar dole ko baquntar lahira babu shiri"




Wani naushi da yakaiwa bakinta yasata saurin duqewa ya naushi iska ta dago tare da cije lebe tace “banso ta kaimu ga haka nafiso muyi komai cikin fahimta idan kuma hakan kakeso to nima na shirya" kafin ta gama rufe bakinta ya zare takobinsa saboda a ransa ji yakeyi gara ya kasheta ya huta yanzu burinsa yabar kanta duk da idan ya samu dama yanaso ko gawarta ya kwanta da ita Amma yafi kwadaituwa da Samrah yayi alqawarin zai raineta na tsayin shekara biyar sannan ya aureta tunda be samu uwarta ba.
Sara ya kaiwa Najmah ta kare da zafin nama itama takai masa cikin saa kuwa tashin farko ta sareshi a qirji abinda ya dugunzuma hankalinsa ya haukace ya rinqa Kai Mata Sara da suka ta kowanne bangare tana karewa bata damu da mayar da martani ba Amma duk sanda ta mayar masa saita yankeshi kafin kace wannan sunyiwa juna jina jina suna neman makasar juna wani Abu ya zaro ta cikin bakinsa ya busa take wadannan mutanen daya narkar suka miqe ya nuna musu ita sukayi kanta suka rinqa fadan mutuwa suna tura mata da sirrikansu na tsafi tana koresu da qarfin addu'a tanayi musu kisan gillah har saida takai tsaf ta qarar dasu tana gamawa kawai sai taga wasu sun fito daidai lkcn da dakarunta Mata uku suka biyota yaqin ya rincabe hardasu aka rinqa bata kashi cikin abinda Bai wucce Rabin saa ba suka gama da wadannan dakarun da gudu Najmah tabi bayan Isham da yaja da baya ganin yanda akeyiwa dakarun nasa kisan kiyashi baisan da tahowarta ba saiji yayi ta soka masa tsinin takobi a wuyansa tace “Inayi maka tayi a karo na qarshe".....
9/10/20, 8:59 PM - Ummi Tandama: *MM5556* Bangaren Gimbiya Samrah kuwa tunda Mahaifiyarta tabar garin ta samu dama kullum zata tashi cikin dare ta rikide ta zama wani qaramin qwaro ta shiga cikin gari duk Wanda tayi katarin haduwa dashi to sunansa gawa domin kuwa da safe zaa tsinceshi a yashe a qasa an qwaqulai masa kayan ciki an cinye, al'amarin daya tashi hankalin al'umar wannan gari suka duqufa addu'a domin gano inda wannan masifar ta bullo.
Yarimah Nurain ne yaje ya ishe mahaifinsa yake fada masa abinda ke faruwa inda take Sarki Fawwaz yasa aka dauko Samrah aka taho da ita fadarsa ya shiga bincikenta cikin mamakin ta inda ta samu maita wani daki dake cikin fadar yasa aka shigar masa da jikar tasa ashe Bai sani ba ajaline dama shine target dinta na farko, ana shiga da ita shima ya shiga tare da umartar Nurain ya tsaya a bakin qofar addu'a ya farayi Mata tare da bin wasu hanyoyi da zasu taimakeshi gane gaskiya.




Kawai saiji yayi an caka masa wani abu a bayansa ya hudo zuwa qahon zuciyarsa ta ya kwalawa Nurain Kira ya zube qasa yanata matagugu da gudun tsiya Nurain ya shigo ya isheshi a wannan mawuyacin yanayi yarinya Samrah ta rikide ta zama wata halitta daban ashe abinda ta cakawa Sarki Fawwaz ba makami bane yatsanta ne shine makamin,
Durqushewa Nurain yayi gaban mahaifinsa yana Kiran sunansa kamo hannunsa yayi yana Jin azabar wannan dafi data zuba masa yace “kada ka bata lkc akaina har tasamu nasarar gudu wannan ba yarka bace kamar yanda aka canza maka mata haka itama aka aikota domin ta kashemu da daidai yakai dana kayi gaggawar aikata lahira sannan kabi matarka zuwa jihadin data tafi kada ka qyale Dan Sarki Jamal Isham ya rayu domin shine ya aiko aka sace yarka aka ajiye mana wannan da take kashe mutanen mu..."
Yana fadin haka numfashinsa ya fara janyewa yana maimaita kalmar shahada take jikinsa ya saki Nurain ya miqe jikinsa na bari ya zare takobinsa ya nufi wannan mummunar halitta suka rinqa zagaye dakin tare da kai mata sara tana gocewa sun dauki lkc suna fafatawa sannan Allah ya bashi nasarar sare kan wannan halitta ya sokeshi da tsinin takobinsa.



Yana fitowa Kai tsaye bargar dawakai ya nufa yayiwa dokinsa sirdi ya hau ya fice daga gidan sarautar da gudu, yayi tafiya me tsayi kafin ya daina hangen masarautar tasu sannan ya sassauta da gudun ya fara tafiya a hankali yana sassarfa, inda ya nufi birnin Jawal shima kamar NAJMAH ya tarar da wannan alqarya da yan gudun hijira suka kafa anan yake samun lbrn kwana biyu kenan da huccewar matarsa nan ya qara qaimi domin yasan zuwa yanzu anacan anata bata kashi.
Haka kuwa akayi lkcn daya isa qofar birnin baya ganin komai sai tashin qura da qarar makamai take ya qarawa dokinsa linzami domin wuccewa Amma sai wadannan sarakunan qofa suka tareshi yayi saurin tsayawa suka fara tuhumarsa daga Ina yake Kuma me yazoyi bai bata lkcnsa ba ganin sun rufar masa yayi musu kaf daya ya qara zaburar dokinsa ya nufi qofar fadar inda acanne gumurzun ya rincabe harda sarki Jamal akanta ita daya da mutanenta guda uku amma sun kasa cimmata tsafinsu yaqi aiki sukuma sai barna sukeyi musu Nurain bai bari yaganta ba ya shammaci sarki Jamal ya fille masa kai,
Ganin kan Sarki Jamal na yawo a Sama yasa gwiwar mutanensa sarewa hatta Yarimah Isham sai ya zube akan gwiwowinsa ya runtuma uban ihu, cikin wata irin mamaya Nurain ya sake shammatar sa ya sanya masa wani sasari ya daureshi ya dago idanunsa da suka kada sukayi jawur ya kalli Nurain ya dubi Najmah da take qoqarin hawa mumbarin fada ya sunkuyar dakai yana hawayen takaici,




Kamar daga sama yaji zazzaqar siririyar muryar Najmah na cewa “Assalamu Alaikum waramatullahi wabarakatuhum yaku al'ummar musulmin da suka fito jahadi domin daukaka kalimatusshahada haqiqa Allah shine cikakken me iko akan kowa sannan me zartar da hukunci akan Wanda yaso tabbas al'ummar duniya tana fuskantar matsi da tsananin rayuwa sakamakon mamayar da mushrikai matsafa maqiya Allah sukayiwa kowacce kusurwa ta duniya,
Kuyi sani cewa wannan hasken tsafi da mamayar kafirci yana daya daga cikin abinda ya jefaku cikin wannan halin da kuke ciki yanzu maita! Maita!! Maita!!! Kunzama dodonni abababen qyamata wa kowa a duniya ana gudunku saboda hadarinku yaku Jama'ar wannan birni na Jawal shekara sama da dari hudu kun zama ababan tsoro kullum kun kasance cikin baqin talauci kuna tsangwami kawunanku kuna tsoron kanku, tabbas da zaku karbi addinin gaskiya addinin annabi sulaimanu alaihissalam ku saki shirka da tsafi ku Kama Allah shi daya da kun kasance kun rabu da wannan lalura da aka gadar muku idan har hakan ta faru zaku kasance kamar kowa zaku samu yalwar arziqi zaku fita daga duhu ku dawo haske"
Wata iskace data taso daga wani bangare na fadar tasata katse zancenta kawai sai gani sukayi jini yayi tsartuwa a sama yayi sama yana wani tsiri, dukkansu suka zubawa sarautar Allah ido cikin abinda Bai wucce daqiqa arba'in ba sukaga jinin ya zama wani baqin hayaqi ya bace bat bayan wuccewar wasu yan daqiqu saiga Nurain ya bayyana a gabansu,
9/10/20, 8:59 PM - Ummi Tandama: *MM5758* Takobinsa na tsiyayar da jini ya dagata sama tare dayin kabbara take jikin kafiran nan ya qara sanyi ganin ya tunkari Isham shima isham cikin kaduwa yace “na yarda Kuma na amince babu wani addini na gaskiya bayan naku na gasqata hakan Kuma zanyi mubaya'a take mutanen dake gurin Suma sukayi na'am cikin tsananin farin ciki suka basu kalmar Shahada suka maimata sannan gurin ya kaure da kabbara Nurain ya matsa gaban Isham ya kwanceshi daidai lkcn da wata baqar tawagar aljanu ta nufosu.
Tun daga sama Nurain yayi umarnin da a fara yi musu barin kibbau aikuwa haka akayi

Please Login or Register in order to submit comment