Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hadu tsakanin jinsin mutum da aljanu to wannan da da aka samu a wannan kadaici yakan tashi da wani qarfi na buwayar duniya a inda yakan zamewa jinsin mutane dama aljanu abin shayi, kamar daini a yanzu Yake wannan Mata tawa kiyi sani  akwai damarmaki da yawa da zaa iya ratso birnin Faris a shigo fadar Fazbar amma kasantuwa ta a cikinsa ya hana wannan damar tasiri, abu dayene zai kasance gushewar nasarata akan duk Wanda mukayi gaba da gaba dashi, ba komai bane wannan face fadawa abinda yake barratacce daga abinda Allah ya halattamin da daga nau'in qawa da jin dadin rayuwa, tabbas a ranar da wannan qaddarar zata fada kaina zanyi baqin ciki mara misali harma zan kasance cikin marhabin da mutuwa ta fiye daci gaba da rayuwa Najmah ba komai bane wannan abu face zina tabbas duk ranar da hakan ta faru nikuma zan iya kashe kaina duk da nasan bazan iya kare kaina da komai ba sai abinda Allah ya kareni dashi"
Kallonsa takeyi a mamakance tace “me zaisa hakan ta faru dakai bayan ka kasance me raba darenka wajen bautar ubangijin muslumci ka kasance me kiyaye dokokinsa sannan Kuma ina tare dakai?"


Lumshe idonsa yayi yace “gabbai sukanyi yaqi kamar wasu sadaukai amma basa iya yaqi da alqalamin qaddara saidai sukayi qumaji wajen kauce Mata, Yake matata kiyi sani kamar yanda ake farautarki a matsayi mabambamta nima haka matan sarakunan aljanu da yayansu dama na bil'adam suke farautata Abu daya yake kareni cikin kariyar Allah shine suturta fuskata da nakeyi na kasance tun Ina yaro mahaifana basa barmin fuskata a bude wannan umarnin Gurail Uzair ne har kawo lkcn da kika kasance mata a gareni, kin kasance kece mutum ta uku data taba ganin fuskata a zahiri, kema don kin kasance mata ne a gareni dole ne ko ban bayyana miki kaina da rana ba zan bayana miki da dare wannan dalilin yasa naga banga amfanin boye miki abinda ya kamata ki sani ba"
Jinjina Kai tayi tare da Dora hannunta saman qirjinsa ya dago ya hauro gadon ya rufeta da faffadan qinjinsa tare da zuge musu labulen sutura ya dora hannunsa a kan qirjinta yana zagayewa tare da wasa da duk wata gabba ta jikinta itama tana tayasa sunajin dadinsu sosai namijin gaske ya mantar da ita tunanin inda zata fara domin samo iyayenta, ya jiyar da ita dadi mara misali a wannan rana sun kasance cikin wata ni'ama ta musamman har zuwa yamma sallah kawai ke tashinsu suyi suci yayan itatuwa su sake komawa cikin halwar qauna,


Koda dare ma bai fita ba yana manne da matarsa sunata bawa furensu ruwa qauna ce me qarfi take shiga tsakaninsu wacce kowannensu yakejin idan babu daya bazai iya rayuwa ba, masoyan asali basusan cewa ga wata qura can ta tunkarosu ba.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya a yanzu Najmah nada sati uku da zama cikakkiyar mace duk yanda Yarimah Nurain yakeso ya dauketa su fita domin zagayawa kilisa iyayensa sun hanasa kullum cewa sukeyi su bari akwai lkc hakanan suke hqr har zuwa lkcn da canje canje suka fara bayyana a tare da Najmah na shigar ciki jikinta.
Wayyoh murna a wannan masarauta Sarauniya Badiyyah da Sarki Fauwaz kamar su hadiye yayan nasu shikuwa Yarimah Nurain sai wani sussunne Kai yakeyi tare da tsananin kunyar matar tasa da iyayensa baya yarda su hada ido da daya daga cikinsu, itakam Najmah mamaki kunyar mijin nata take bata ita da take mace bataji kunyarsa ba sai shine yakejin kunyarta.



Haka suke rainon wannan ciki cike da kulawa da tattali har zuwa lkcn da yakai watanni uku a lkcn ne Kuma jita jitar samuwar cikin ta karade duniyar wannan qarnin, wata rana suka shirya domin zuwa Qudhar masarautar Sarauniya Badiyyah kasancewar dama watanni take rabawa tsakanin masarautar Fazbar da Qudhar.
Sunyi shiri na ban mamaki tare da shirya dakaru suka dauki hanya tafiyar qasa ce zasuyi bisa dawakai kasancewar Gurail Uzair ne ya shawarcesu da suyi hawan turba saboda a wannan lkcn gungun matsafan aljanu suna meeting na yanda zasuyi su sace Najmah da abinda ke cikinta.
Haqiqa Allah yakan bawa kafiri dama ne akan mumini bawai don kasawa ba aa saidon gwada qarfin imanin muminin da Kuma qara dulmiyar da kafiri cikin duhun bata bayyanan ne, hakance ta faru da wannan ayari.



A rana ta ashirin da hudu daren goma sha hudu da fara tafiyarsu suka isa wani kyakkyawan daji me cike da ni'imar dogayen bishiyoyi da tsaunuka gami da ciyayi masu sanya zuciya kwadaituwa da yada zango a gurin, Gimbiya Najmah dake kwance jikin Yarimah Nurain ta dago ta dubeshi shima itan yake kallo tayi masa murmushi tace,
“Haqiqa zuciyata ta kwadaitu da son hutawa a gurin nan, kayiwa Dakarun musulumci  umarnin bincikar dajin idan lfy yake su kafa mana tanti zanso hakan Kuma zanji dadi yakai mijina" shiru yayi yana nazarin mgnrta kafin daga bisani ya sauke numfashi yace “kinsan dai da cewa farautar rayuwarki akeyi"
Murmushi tayi tace “na yarda da cewa babu abinda zai sameni face abinda ubangijin Muslumci ya qadarta min nidai inason gurin nan mijina kayimin alfarmar nan" baiso tsayawar ba saidai yanason farantawa matar tasa hakanne yasashi bada umarnin dakatawa take dakaru suka tsaya yayi musu Umarnin bincikar dajin haka kuwa akayi suka bazama suka shiga dajin suka dubashi sosai ganin babu wata alama ta wani abu na cutarwa suka dawo suka kafa tantina tare da tafiya neman ruwan sallah, tafiyarsu keda wuya Gimbiya Najmah ta shiga tantinsu ta kwanta bacci me dadi ya dauketa, yana zaune yana kallonta yana shafa cikinta yaji wani qugi yana tasowa ta qarqashin qasa ya zabura ya miqe tare da zare takobinsa ya tsaya yana jiran tsammani.


_Assalamu alaikum_

_Masoyan wannan lbr na *MASARAUTAR MAYU* da suke amfani da Facebook amma basa WhatsApp Kuma zaku iya samuna ta account dina na Facebook kamar haka._

Username
        👇
Fauzat Tasi'u

Please ki tabbatar kin/ka shirya turo kudinka kafin kiyimin mgn, kada ki manta katin MTN na dari biyu ne zaki/ka turo nayi add naki/ka a group dina, na gode.
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:37 PM - Ummi Tandama: _Ki biya ta wannan acc din   0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB_
_Idan katine ki dauka hotonsa ko pin lambobinsa ki tura ta WhatsApp number 09013718241: idan VTU ne ki tura ta wannan number_
      👇🏻
_09031307566_


*MM 23-24* Wannan qugin da yakeji yana tasowa ya lafa tare da mamayewar wata iska me sanyin gaske take kuma cikin qanqanin lkcn ya sulale qasa cikin halin bacci, lamarin da yayiwa matsafiya Juhaira da sauran tawagar matsafan mugun dadi suka isa gaba ga Gimbiya Najmah Amma suka kasa tabata saboda wani turiri da yake tashi ta jikinta.
Matsawa kowa ya rinqayi sunajin kamar anayi musu ruwan dalma, kowa burinsa ya mallaki gimbiya Najmah da abinda ke cikinta Kuma gashi qiri² suna Shirin ganin samu da rashi a jere, a daidai wannan lkcn ne Aljana Nurayyah da Yarimah Isham suka iso da'irar sansanin nasu Gimbiya Najmah,
Da sauri suka tsaya tare da kallon kallo tsakaninsa da Nurayyah yace “ya naga mahaifiyarki da sauran tawagar hadin kanta sun tsaya batare da sukai ga dauko Gimbiya Najmah ba?" Numfashi Nurayyah ta sauke tace “a hakin da ake ciki babu Wanda ya isa ya taba gimbiya Najmah sai kai kadai kasancewar jinsinku daya kayi sani yakai wannan dan Sarki gimbiya Najmah ta karbi irin addinin mijinta saboda haka ta kasance cikin kariyar da duk wani matsafi bai Isa ya rabi jikinta ba"




Wata dariya Yarimah Isham ya kece da ita tare da zare duk wani abu daya dangantashi da tsafi ya miqawa Aljanin da yake tare dashi ya diro qasa tare da nufar cikin tantin, ya tsugunna batare da matsalar komai ba ya sabo gimbiya Najmah a kafadarsa ya fito da ita tare da tsayawa akan Nurain yayi murmushi yace “dama na fada maka Najmah tawa ce, a halin yanzu Ina jarumtar taka data kasa amfanar dakai da komai sai bacci?"
Dariya ya sake sheqewa da ita yaci gaba da tafiya tare da matsawa gaban Nurayyah ya ajiye Najmah domin daura gurayensa ns tsafi take aljana Nurayyah ta shammaceshi ta buga masa wani Al'amudin tsafi a kansa yayi taga taga ya fadi tim a qasa abinda ya bata damar sunkutar Najmah nan take manyan matsafan nsn suka iso gurin sukayi musu da'ira tare da fara tunanin ta inda zasu kwaci Najmah a hannunsu inda ita Kuma matsafiya Juhaira tayi amfani da hikimar tsafinta ta bude qasa Nurayyah da Najmah suka shige cikin.
Nan take wani fitinannen yaqi na matsafa ya balle duk a qoqarinsu na ganin sun amshi Najmah daga hannunsu matsafiya Juhaira inda shikuma boka Rundatu ya koma gefe yana kallonsu tare da fito da wannan hoton surar yayi siddabarunsa ya bata unarnin komawa tantin da aka sace Najmah ta kwanta a gadon kamar najman gaske, yana gama wannan aikin shima ya keta qasa yabi bayan Nurayyah abinda ya sanya fadan tsafin da Juhaira da sauran tawagar matsafan duniya sukeyi ya tsaya suka runtuma Suma sukabi bayansa gurin ya rage sai Nurain kadai kasancewar aljanin dake hadimi gurin Isham ya daukeshi shima sunbi bayan tawagar.




Suna bacewa daga gurin Yarimah Nurain yayi firgigit ya tashi daga wannan bacci me kama da suma yayi salati tare da fara dube² yanajin rashin yarda na shigarsa, da saurinsa ya shiga tantin ya matsa gaban shimfidar da Gimbiya Najmah ke kwance ya bude mayafin da take rufe dashi ys tsaya yana qare mata kallo so yake ya bambance wani abu da yake gani kamar bashi ba amma ya kasa,
Murmushi yayi daidai lkcn da tawagar dakarun suka iso sukayi alwala sukayi sallah shidai zuciyarsa cike da mamakin abinda ya sanyashi bacci dazu.
Zuciyarsa tana rawa game da najman dake gabansa yanzu tanata sharar bacci musamman lkcn da la'asar tayi yasan najmah indai akayi Kiran sallah kome takeyi saita tashi amma yanzu gashi salloli uku tana bacci, lkcn da suka idar da sallar isha ita kuma ta tashi daga dogon baccin daya dauketa tayi miqa tare da fara kalle kalle jin batayi salati ba ya sanya nurain matsawa gaba gareta ya sanya hannunsa ya juyo da ita tayi saurin yin qasa da idonta kasancewar Boka Rundatu ya sanar da ita duk tsanani kada ta bari su hada ido dashi iyakar zaman da zasuyi,
Kiran sunanta yayi yace “bakiyi la'asar ba ga magrib gashi har munyi Isha ko zan iya sanin meye yake faruwa?" A hankali take qoqarin shigewa jikinsa shikuma ya janye ya fara duba wani abu tace “bansan meye ya sani dogon bacci haka ba ina ganin gajiya ce gashi inajin yunwa"



Ci gaba yayi da duba taswirar yanda tafiyar tasu zata kasance ta jiya ta fita tana duba dakarun tare da nazarin ta yanda zata gudanar da aikinta, hadimai ne suka iso gareta suka kawo Mata ruwa don alwala tsugunnawa tayi Saida taga hankalinsu bashi a kanta sannan ta miqe ta koma ciki ta dauke tatacciyar madarar da gurasa ta matsa kusa dashi yana karatun hisnul Muslim tana qoqarin shigewa jikinsa ya daga mata hannu tare da dagowa tayi saurin qasa da kanta.
Kwana biyu sukayi a wanna guri sannan tawagar ta sake tashi a cikin kwanakin biyun nan hakanan dangantaka tayi tsami tsakanin Wannan aljana da aka samar a makofin Najmah da yarimah Nurain duk wani shirin mushrikan yaqi tasiri akansa, hakadai ake wannan zama na doya da manja dayagama takurarta zatayi yawa sai ya fara nesa da ita shi kansa yana mamakin dalilin da yasa yakasa sakin jikinsa da matar tasa tafiya ce sosai sukeyinta su tsaya a wannan alqarya su sauka a wannan tsuburi har tsayin watanni uku sannan suka fara jiyo qamshim Birnin Qudhar.



********

Al'amarin Aljana Nurayyah da Gimbiya Najmah kuwa tafiya sukeyi a qarqashin kasa Saida sukazo gabar kogin qasa sannan suka fito saman turba sukaci gaba da gudu cikin walqiyar sihiri gudun da sukeyi ya wucce misali wannan dalilin ya sanya sukayiwa ayarin dakarun matsafan nisa har wannan lkcn Gimbiya Najmah cikin bacci take tafiyar kwana biyu ce da yini daya zata kaisu fadar tsafin matsafiya juhaira.
Kasancewar cikin taimakon tsafini a cikin yini guda suka isa fadar Nurayyah ta shigar da Najmah cikin wani daki ta kwantar da ita ta tsaya akanta ta zuba mata ido tana kallon abin ta'ajibi duk yanda take ganin ita kyakkyawa ce saita raina kanta ga inda asalin kyau yake,
Numfashi ta sauke ta fice daga dakin ta nufi dakin tsafin mshaifiyarta ta fara duba halin da Masoyinta Yarimah Nurain yake ciki abin mamaki sai ta hangeshi zaune saman buzu yana karatun littafinsu gefensa ga wannan aljanar da Boka Rundatu ya suranta da Najmah tanata rawar sanyi da alamun ksratun ne take dagargazar bargonta tananan zaune ta zuba masa ido tana kallon yanda yake sarrafa harshensa tana hawaye tare da baqin cikin kasancewarsa mallakin wata ba itaba miqewa tayi da sauri tare da daukar alwashin ganin bayan Najmah saboda cikar nata burin.
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:38 PM - Ummi Tandama: *MM 25* Lokacin da wannan hadimin aljanin ya dauki Yarimah Isham sukabi bayan su boka Rundatu sunyi tafiya Mai tsayi sannan ya farka, batare da ko alamun Aljana Nurayyah sun ganiba lamarin daya tashi hankalin Isham ya rinqa saqawa a zuciyarsa ashe aljanu da gaske basu da amana suna fifita muradansu fiye da muradin kowa meye dalilinta na yaudararsa yayi Mata jagora ita kuma ta gusar masa da hankali ta dauke masa cikon duniyarsa?
Da wadannan tunane tunanen sukayita keta dazuzzuka tare da tsallake hatsarurruka da yawa lamarin daya dugunzuma hankalinsa ya fara tunanin yanda zaiyi ya Isa gaba ga aljana Nurayyah kafin ta cutar da Najmah.
Suna cikin wannan halin ne yaga zoben tsafinsa yayi duhu al'amarin daya sanyashi bawa wannan hadimin aljani umarnin sauka qasa ya sauka shima ya dura daga kan aljanin ya dauko madubin tsafinsa ya haska saiga fuskar mahaifiyarsa ta bayyana yace “meye Kuma ya sake tasowa da kike kirana a daidai wannan lkcn?"
Kuka ta fashe dashi tana mai cewa “haqiqa yakai dana mun kasance cikin wani mawuyacin hali na yunwa da qishirwa takai ta kawo yanzu naman yan uwanmu shine abincinmu saidai musha jini mu kwanta idan nama yana maganin yunwa aishi jini baya maganin qishirwa sannan kuma a da dare muka wayi gare da annobar wasu tsuntsaye kwatan kwacin wadanda iyayenmu suka bamu lbr na annobar maita lkcn sarki Gesbatin haqiqa wadannan tsuntsaye sun kasance suna samun mutum suke hudashi da dogon bakinsa takai ta kawo ma yanzu babu me fita kowa yana gda a kulle saboda da ka fita kodai kayi gamo da tsuntsayen nan su hudaka su sake zuba maka maita ko Kuma kayi gami da wadanda tsuntsayen suka zubawa su rinqa yagar naman jikinka danye sunaci"



Numfashi ya sauke ya rufe madubin tsafin shi wannan bai isheshi abin taba lkc akai ba sake bude wata taswirar sihiri yayi ya debi wata qasa ya watsa akai take saiga wata siririyar hanya ta bayyana qarshenta wani dutsene hasken yabi hanyar har saida ya dangana wa dutsen sannan ya ratsa dutsen ya shiga saiga Gimbiya Najmah kwance saman wani gado Nurayyah tsaye a kanta tana qare mata kallo,
Hannu ta daga domin takai wa cikin Najmah Amma ga mamakinsa sai yaga wani farin haske yayi jifa da Nurayyah gefe ta fadi qasa summamiya, take ya juya akalar bincikensa zuwa ga bangaren su boka Rundatu inda ya hangesu sunata gwabza yaqi tsakanin matsafiya Juhaira Sarki Nuddrah na qasar Kisra da Kuma boka Rundatu.



_Kiyi hqr da jina Shiru da kukeyi Hairan na batada lfy ne hankalina ya kasu biyu_
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:39 PM - Ummi Tandama: *MM 26-27* A bangaren Yarimah Nurain kuwa lkcn da suka isa qofar masarautar Qudhar zaratan aljanun da suke gadin qofofin suka bude musu tare da rusunawa suna kwasar gaisuwa gurin Yariman masarautar tasu, hannu yake daga musu da alamun Jinjina da girmamawa ya juya ya kalli Najmah da tayi qasa da kanta yasa hannu zai dago fuskarta sai Kuma ya fasa sukaci ga da tafiya har sukakai ga qofar fadar.
Wangame musu akayi suka sanya kai ciki shigarsu keda wuya Gurail Uzair ya miqe da sauri tare da nuna wannan aljanar dake a matsayin Najmah da sandar hannunsa nan take ta fadi qasa sumammiya tayi wani baqi tana fitar da wani hayaqi take ta koma asalin surarta tsoro ya kama Yarimah Nurain yaja da baya da sauri,
Bashi ba kowama dake gurin Saida yaja baya cike da tsoro, sarauniya Badiyyah ta miqe lkcn da Gurail Uzair yabada umarnin a dauki wannan aljana a shiga da ita ciki, matsawa yayi ya tsaya a gaban Nurain yace.




“Haqiqa wani abu mummuna ya faru a cikin tafiyarku na umarceka da kada kayada zango a kowanne guri saboda kare lfyrka data iyalinka saiya kasance ka sabawa wannan umarni saboda son faranta ran abar qaunarka, ka sani yakai wannan dan sarki a wannan lkcn da kuka sauka domin hutawa a daidai lkcn ne wannan tawagar matsafa dake bibiyarku suka samu nasarar hura maka Iskar bacci har takai sunyi nasarar sace Gimbiya Najmah da abinda ke cikinta.
Yanzu haka zancen da nakeyi maka tana wata nahiya ta matsafa me hatsarin gaske wacce babu wata halitta da take iya zuwa gurin nan face ta bayu gawa, haqiqa Matarka da cikin jikinta suna cikin hatsarin gaske domin kuwa da manufa uku aka sacesu, manufar farko itace ta burin mallakar zoben Zaujatul Noor dake saye a yatsanta wanda zai zame mata kariya har zuwa ranar da dauki zaije musu cikin buwayar ubangiji, manufa ta biyu itace saboda a karya garkuwar tsaronka wannan dalilin yasa aka samar da wannan taswirar sihiri me surar matarka aka bar maka ita a zuwan itace matarka tabbas badon mun ankara da wuri mun roqi Allah ya cire maka sha'awa ba da tuni aikinmu ya lalace maqiya Allah sun samu nasara a kanmu.
Manufa ta uku itace ta cikar burin Nurayyah ya a gurin Matsafiya Juhaira wadda ta rayu da qaunarka tsayin rayuwarta tare da burin mallakarka, bincike tayi sosai akanka inda bincikenta ya tabbatar Mata da cewa babu ta yanda burinta zai cika face ta sace matarka ta cusa mata qiyayyarka ta mantar da ita Kai sannan idan matarka ta haihu ta sace dan ta massheshi nata"




Wani gumine yake karyo Yarima Nurain tashin hankalinsa na bayyana akan qwanjinsa ya sulale ya zube qasa bisa gwiwowinsa baisan sanda ya taqarqare ya kurma ihu ba yana Kiran sunan Najmah, ashe shi ya dade dayin sakaci maqiyansa sun sace masa Mata da dansa dake cikinta aikiwa tabbas baiga ta zama ba dole ne yayi Shirin tafiya domin qwato iyalinsa da dawo da ita gareshi.
Miqewa yayi cikin tsananin fusata da zafin nama zai fice Gurail Uzair ya riqeshi yace “ba tafiyarka ce natsala ba nasara ta Allah ce inda zaka fara tunkara shine babbar matsalar a halin da ake ciki yanzu ba matarka zaka fara cetowa ba iyayenta zaka fara cetowa daga fadar matsafi Rundatu, hakan shine zai baka damar tsallake dazuzzukan saba'in dake tsakanin kowacce kusurwa ta duniya da wannan tsauni da iyalinka suke boye cikin kogonsa"
A fusace yajuyo yace “meyesa dole saina fara ceto mahaifanta?" Murmushi Gurail Uzair yayi yace “kada ka fita cikin zafin zuciya ya shugabana akwai hikima cikin hakan, kayi sani a kaffatan halittun dake rayuwa tsakanin jinsin mutum da aljan Uddatu mahaifin matarka shine mutum days tilo da yasan sirrin dazukannan bayan shi sai Matsafiya Juhaira wadda ke rayuwa a cikinsa Yarimah kada ka sabawa umarni a karo na biyu Kuma kada kayi gaggawa tafiya sannu sannu kwana nesa kazalika sannu batai hani na aje saidai ace an jima baa isaba"




Juyawa Gurail Uzair yayi yace “zan matsa wannan aljanar da ayar Allah ita zatayi mana bayanin yanda zaayi a isa dajin Qursum inda Boka Rundatu yayi garkuwa da surukanka" yana gama fadin haka ya juya shima Nurain dole yabi bayansa suka shiga cikin gdan sarautar suka nufi dakin da aka tsare wannan aljana Gurail Uzair ya kalleta tare da daka Mata tsawa sai gashi ta fara zunduma ihu tana roqonss kada ya qonata dama Saida taso turjewa wabin umarnin Boka Rundatu amma yayi Mata barazanar kisan wulaqanci.
Koda Gurail Uzair yaga aljanar tayi laushi sakamakon azabar da taci wajen dalubansa da suka rinqayi Mata ruwan ayoyin Allah wannan dalilin yasashi zama a saman wani dutse dake dakin ya dubeta ta durqushe a gabansa tace “ka tambayi duk abinda kakeso haqiqa zan fada maka gaskiya ba tare da nayi maka qarya ba"
Dagowa yayi bayan ya binciki zuciyarta yaga gaskiyarta yace “meye sunanki sannan meye dalilinku na raba tsakanin ma'auratannan?" Cikin rawar jiki na wanda yaga mutuwa ta farayi masa bayani har saida ta sanar dashi inda zasu samu Uddatu da matarsa Uddaru mahaifa a gurin Gimbiya Najmah.
Miqewa Nurain yayi ya juya zai tafi tayi saurin cewa na kasance me buri da son kasancewa cikin addininka ya shugabana tabbas zaman da nayi daku ya sanya zuciyata karaya har naji babu addinin daya dace Dani face addinin musulumci tabbas inason karbarshi da zuciya me tsarki Kuma inason binka zuwa wannan jahadi daukaka kalmar Allah da qwato cikon farin cikin duniya daga hannun azzalumai"




Kabbara sukayi take Sarauniya Badiyyah ta laqana Mata kalmar shahada ta karba aka bata ruwa tayi wanka sannan aka bata abinci taci, duk yanda Sarauniya Badiyyah taso Yarimah Nurain ya bari sai kashegari ya tafi fir yaqi saima sake tubure Mata da yakeyi dole a daren aka shiya masa dakarun aljanu sukayi dango suka fita daga birnin Qudhar suna masu maimsta ambaton kalimattusshahada.
Tafiya ce da zata daukesu watanni biyar sunayinta tsakanin sama da qasa tafiyace da komai zai iya faruwa, tafiya ce ta ko amutu ko a rayu, wannan karon Yarimah Nurain da shirinsa ya fito na fara yaqi da daulolin kafirci da kafurai bakidaya.
Tafiya ce da ta hada aljanu da mutane wannan tafiya anayinta ne da zuciya bada jiki ba kasancewar ran jagoranci musulumcin duniya ya harzuqa da sace matar garkuwar musulumci da Kuma Dan dake cikinta, abu biyu yake tsayar da wannan tawaga shine sallah da cin abinci.
A cikin tafiyar tasune suka ratsa ta saman wata alqarya Mai suna Uzran nadah qaramin garine amma yanada kyau da alamun wadatar arziqi sosai a alqaryar masanin nahiyoyi da alqaryu bafatake Juhair Yarimah Nurain ya kira yace “bani labari game da wannan kyakkyawar alqarya yakai Juhair"
# *UMMUH HAIRAN*
9/10/20, 8:52 PM - Ummi Tandama: *MM 28-30* Duban garin yayi yana nazarinsa yace “wannan alqarya ta kafu shekaru dari shidda da suka wucce ya shugabana mazaunan wannan alqarya sun kasance fatake ne masu tafiye tafiye wannan dalilin ne yasasu yankan wanna guri suka kafa birninsu sun kasance suna bautar wutane sun dauketa a matsayin abar bautarsu.
Sarkin fataken shine yake a matsayin sarkinsu haqiqa sun kasance manoma sannan makiyaya sannan fatake wannan dalilin yasa suke zaune cikin wadata da yalwar arziqi" numfashi Yarimah Nurain ya sauke yace “nayi sha'awar shiga wannan alqarya na kafa tutar musulumci" magatakarda ya kira ya turashi da takarda yace yakaiwa sarkin wannan alqarya,
Tafiya magatakarda yayi ya shiga wannan alqarya bai jima ba ya dawo da kyakkyawan albishir yace “ya shugabana al'ummar wannan alqarya sunyi marhabin da zuwanka sannan sun bamu izinin shiga cikin garinsu da salama" hamdala Yarimah Nurain yayi yabawa mutanensa izinin shiga suna shiga suka tarar an turo yan aike su isar dasu fadar sarki Urzan Koda shigarsu fadar sai Sarki Urzan ya taso ya tari Yarimah Nurain.




Sukayi musabaha yace “nayi farin ciki nayi farin ciki da bayyanar wannan haske a cikin masarautar mu haqiqa bayyanarka haskene a garemu yakai wannan dan sarki daya gagari matsafan duniya kayi maza ka shigar damu addininka domin kubutar duniya daga duhun zalumci haqiqa na dade Ina jiran zuwan wannan rana da zamu kasance zaune muci abinci akushi daya" farin cikine ya mamaye zuciyar Yarimah Nurain da mutanensa batare da bata lkc ba suka bawa al'ummar sarki Urzan kalmar shiga musulumci suka riqa take aka shiga shagali a wannan birni.
An dauki lkc ana shagalin kafin Yarimah Nurain da Sarki Urzan su samu kebancewa sarki Urzan ya dubi Yarimah Nurain yace “yakai wannan sadaukin dan sarki kayi sani nasan cewa ba takanas domin wannan alqarya kayo hawa ka taho ba dole zai kasance hanyace ta biyo dakai ta wannan birni namu, shin ko zan iya sanin dalilin tafiyarka ciki ko akwai abinda zan taimakeka akwai?"




Numfashi Yarimah Nurain yayi me huci yanajin yanda zuciyarsa ke tafasa ya dago ya dubi

Please Login or Register in order to submit comment