Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biki yau saura 1 week ciff.duk yadda bash yaso ganin umaima abun ya faskara saboda shuairat ta gindaya mata sharuda sosai bata xuwan ko ina kullum tana ckn dakin baccinta gashi an kwace wayarta bata aiki se kuka, ga yan uwa sun fara xuwa shuairat se shiga da fita take Sam bata da lokacin xama ita ta kira tela yaxo har gida ya karbi dinkunan da xaa yi, mr president ya bude bakin aljihu ya xuba kudi sosai duk abunda ake bukata sun rigada sun siya ..
Shuairat ce kwance a dakinta salman yana gefe yaron ya girma yayi wayo sosai gashi da girman jiki tamkar ya'yan turawa ga fara'a ga kyau tubarakallah..mr president ya shigo yana waya bayan ya gama ya juya gun matarsa suna fuskantar juna
" sorry my Lady gskiya kina kokari Allah ya miki albarka"
"Ameen my man"
tana murmushi ta koma kusa dashi ta xauna tare da cewa
"Nasan ka gaji kwanta na maka tausa"
Babu gardama ya mike akan gado kwanciya yayi rub da cki nan ta fara masa tausa har wani lumshe ido yake tamkar mai shirin bacci shuairat tace

"Dad umaima"
"Uhmm..
"Pls gida nake son xuwa "
"Yaushe?
"Ko xuwa anjima "
"Ba damuwa ki shirya driver ya kai ki"
"Tnx swt hrt"
Ta manna masa peck a kumatu murmushi yake haka ta cigaba da masa tausa har bacci yayi awon gaba dashi.
Ta gama shirinta tsab ta shirya salman sun yi kyau sosai ta sanar da masu aiki kan cewa su kula da umaima xata je gidansu baxata Dade bah, daga nan ta wuce gun mota driver ya ja Suka dau hanyar xuwan gidan su.
Falon babanta ta fara xuwa yana xaune da carbi a hannu dayake baa dde da yin sallar axahar bah..yana ganinta fuskarsa ya fadada da murmushi yace
"Ya'r baba..Barka da xuwa"
"Yawwa..
Waje ta nema kusa dashi ta xauna yasa hannu ya karbi salman yana cewa
"Waii...haka kike fama da wannan lukutin Alhajin yana wahalar min dake"
Dariya kawai take musu gskiya salman akwai nauyi kamar my boy *haneef*๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š.
Mama ta shigo tare da sallama ta tabe baki da ganin shuairat tace

"Oh..ni Fatima wato kedai kin nuna kinfi son mahaifin naki a kaina ..ah yayi kyau"
"Fateema wai kishi kike dani"
Baba ya fada yana dariya shuairat ta tashi ta fada jikin mama
"Mamana I miss u"
"Ba wani nan kin nuna kinfi damuwa akan mahaifinki"
"A'a mama kema kinsan ina sonku gaba daya"
Suna dariya mama ta dauki salman tana cewa
"Maigida nasan kai kam kafi sona koh"
Salman se wage baki yake kamar yana jin abunda take cewa baba ya karbe maganar yana cewa
"Wannan Dan lukutin maigidan naki yana ramar min da ya' "

"Alhaji kodai kishine"
"Haba..kishi da wannan maigidan ba chefene"
Suna ta raha daga karshe Suka gaisa mama ta kawo mata ruwa tasha Suka baje suna hira shuairat tace

"Ina majnoon neh kwana 2 bana ganinsa "
"Waye kuma majnoon"
Mama ta tambaya tana mai kallon shuairat
"Hhhhh.. Yaya bash mana"
Duka mama ta kai mata nan ta goce tana dariya tace
"Ehh..mana ai sunan ya dace dashi majnoon baban soyayya ko romeo ne"
"Bayan kun hanashi Ya'r taku me kuma xaki fada"
"Eyya mama rabone babu"
"Kiji dashi...Allah xai bashi wata"
Baba de se dariya yake musu haka shuairat ta yini har bayan sallan laasar ta tashi da cewa xataje gun shukrah kafin ta koma gida daga nan sukayi sallama tana rokon mama akan cewa don Allah taxo bikin , har mota Suka rabu nan driver ya ja Suka wuce gidan bash.

Shukrah tana xaune ta buga uban tagumi tunani fal a ckn xuciyar ta kamar a mafarki taji sallamar shuairat bata amsa bah shuairat tasa kai ta shigo falon tana faman sauke salman tare da cewa
"Kai mata kina nan shine baki amsa sallama ta bah, tunanin me kike haka"
Wata muguwar harara shukrah ta jefa mata tare da Jan dogon tsaki tace
"Allah wadaran naka ya lalace..mutum yayi asara tunda munafurci da hassada yasa a gaba"
Ckn rashin fahimta shuairat tace
"Ke kuwa waya tabo ki da yamma haka"
Dama jira take nan shukrah ta tashi tsaye tace

"Ke shuairat kada ki mayardani shashasha..kina jina, bayan kin gama hada munafurcin ki xaki xo kina raina min wayo..
"Haba shukrah meyayi xafi haka?
"Ehh..lallai kin nunamin halin yan duniya.ni kike tambaya? Hmm..shuairat kenan tsabar rashin kunya da bushewar ido har xaki iya fuskantata ki...
"Dakata madam! Bana son kwana2* ki fito fili ki gayamin meke faruwa"
"Danakari! Lallai yarinya kina da mugun rainin hnkli..bayan kin gama munafurcinki xaki dawo ki fake ki nuna Ke baki San komai bah??


Shuairat tayi jugum..wai meke faruwa ne?
Me shukrah take nufi??
Ni Reefat nace๐Ÿค”๐Ÿค” kodai xancen auren ya tabbata ne??
Toh...muje xuwa dai

*Dr Reefat*๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[2/21, 2:42 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*93*
By *Reefat yahya*

Shuairat taja wani gauron numfashi tace
"Look bestie..let's sit down n..
"Bestie! ..hmmm tsohon suna "
Shukrah ta tare numfashnta sannan ta cigaba da cewa
"Shuairat a da can baya idan wani ya gayamin cewa xaki iya aikata abunda kika min a ynxu wllhi baxan taba yarda bah amma ba abun mmki bane dama haka amintaka ta gada...cin amana da yaudara da munafurci"
"Haba shukrah wat r u talking about.. Nifa kin sani ckn duhu"
"Kinga malama ki tattara ki barmin gida Nah ..ko sai nan ma xaki nunamin gidan Dan uwanki ne?

"Pls shukrah let's talk abit "
"I don't want to...just get out now"
Shukrah ta fada tana nuna hanyar fita nan shuairat ta sabi salman tasa shi a kafada ta kama hanyar fita idanunta sun cika da kwalla tana mamakin sauyin halin shukrah kuma ta rasa gane dalilin.driver yana ganinta yayi saurin bude mata gidan baya ta xauna ya tada mota Suka koma gida.
Tana isowa ta share hawayen da ya bata mata fuska sannan ta karasa ckn gida baki ne a cike da falon suna ganinta Suka fara mata sannu da dawowa itama tana musu barka da xuwa se rawar jiki sukeyi a kanta wata ta karbe salman tana cewa
"Fine boy ya kke"
Dangin mahaifiyar umaima ne da kuwa wasu daga ckn yan uwan mr president sauran kuma washe garin xasu taho , shuairat ta shiga musu hidima se yabonta ake bayan ta tanada musu komai duk cewa masu aiki sun Riga sun kawo musu abinci har magrib ta samu ta koma dakinta tayi sallah bayan ta idar ta samu ta watsa ruwa har ynxu salman yana gun yan uwansa don haka ta shirya a nitse ta saka wata simple doguwar riga Mara nauyi ta fesa jikinta da turare nan ta kwanta a gado kalaman shukrah ne Ke yawo a kwa2lwarta ta rasa gane inda maganganun Suka dosa, mr president ya shigo har ya karasa kusa da ita ba tare da ta sani bah hannu taji ana shafa fuskarta yasa tayi saurin dagowa ya jawota a jiknsa ya rungumeta tamkar jira take nan ta fashe masa da kuka dakyar ya rarrasheta ta daina kukan wani light kiss ya mata na 2 mins sannan ya kwantar da kanta a saman kirjinsa tayi luff ta kwanta sosai ckn Muryar rada yace
"Tell me...
Babu gardama ta xayyana masa komai bata hakuri yake bata yana nuna mata cewa ta kwantar da hankalinta wataran xasu shirya daga nan ya fara mata wasu abubuwan da yasa ta manta da damuwar da take cki.

Washegari ...daddy da momsi Suka zo ga gida de a cike makil babu masaka tsinke a ckn dangin nata ne shuairat ta xabi kawaye 4 ta basu anko din ta shirya dinner hadadde bayan an daura aurene xaa yi , umaima kam tace ba ruwanta a cki ko walimah baxata yi bah..dakin umaima ta shiga ta xauna a gefen gado umaima ta tashi xaune tace
"Don Allah mom sultan ki taimaka ki barni naga uncle bash..wllhi ba dadewa zanyi bah kawai sallama zamuyi"
"Bbu inda zaki..so kike ki jawo min magana gun daddy koh, toh wllhi babu ruwana a cki"
" haba mana...eyya mom plsss"
ta marairaice shuairat tace
"xan kirashi yaxo nan gidan ya sameki"
" ehh..na amince don Allah ki taimaka"
Ta bata tausayi ba kadan bah..nan ta cire wayarta yayi ringing har ya katse baa daga bah, ta sake kira har sau3 daga bisani ya daga a wahalce yake magana
"Salamu alaikum"
Gaban shuairat ya fadi badai rashin umaima ne ya kwantar dashi haka bah ya salam! Muryarsa ne ya katse tunanin da take
"Baki jina ne"
"Yaya ina ji meyake damunka naji voice naka somhw"
tsaki yaja yace
"Wani Dan xaxxabine yake damuna amma naji sauki"
"Ahm..dama umaima ce take son ganin ka "
"Da gaske? tana ina?
"Yaya..tek it easy pls, kaxo gida ynxu amma kada ka bari mr president yasan da xuwan naka ok"
"Ok gani nan xuwa"
Nan ya kashe wayar tausayinsu ne ya kama shuairat jikinta ya mutu ta juya ga mmkinta hawayene a idon umaima tace

"Mom sultan kin gani koh...wllhi yana sona nasan yana ckn tashin hnkli ynxu"
"Umaima kiyi hakuri babu ynda muka iya umarnin iyaye ne Allah yasa hakan shine mafi alheri "
"No...ba alheri bane ni nasan aurena da uncle bash shine mafi alkairi "
Nan ta fashe da kuka shuairat tana bata hakuri dakyar ta sagaita kukan daga nan ta tashi tayi wanka ta xauna xaman jiran masoyin nata.
Har yamma babu labarin bash ga layinsa bayya shiga umaima ta birkita shuairat gaba daya ta xama tamkar wata mahaukaciya tun suna boyewa har jamaa Suka gane sun fara tambayar shuairat ko lfy shuairat de ce musu take kan umaima ta tuna da mahifiyarta shiyake sanyata yawan kuka.
Da dare suna xaune sunyi jugum shuairat ma ta shiga damuwa don rashin samun layin Dan uwan nata gashi tana kiran layin iyayen nata basa dagawa babu halin ta fita kuma don mr president baya gida.haka ta hakura momsi ta shigo dakin suna Dan taba hira sama2* dakyar Suka lallaba umaima ta yarda taci abinci, kadan ta ci ta kwanta.
11pm mr president ya shigo a wannan lokacin shuairat ta gama shirin bacci ta kwanta amma baccin yaki xuwa , ya shigo tare da sallama ta tarbesa tare da kawo masa abinci bayan ya gama wanka ya fito ya ci abincin sarai ya lura da halin da take cki amma ya share nan ya hau gado ya kwanta ckn sanyin murya ta kirasa
"Swt hrt!
"My lady yaya?
"Uhm..dama numban yaya bash ne baya shiga"
"Meya faru kuma meyasa kike nemansa"
"Uhm..dama ..daman "
Sai kuma tayi shiru ta rasa karyar da xata shirya ya kura mata ido yace
"Ina sauraronki"
"Uhm..numban mama ne idan na kira bata dagawa shine nake son ji ko lfy"
Murmushi yayi ya jawota yace

"Don't worry lfy suke babu abunda ya faru ok"
ta tura baki tare da marairaicewa
"How sure are u ko suna lfy"

"C'mon trust me..lfy lau don dazu na raka daddy yaje gun baba "
"Lfy dai koh?
"Uhm..kawai gaisuwa ce cos idan ya shiga hidimar bki baxai samu damar xuwa bah, kuma yayi inviting dinsa xuwa daurin aure "

"Ok yayi kyau"
Daga nan shiru sukayi kowa da tunanin da yake ya rungumeta sosai sannan ya kashe bedside lamp sukayi baccinsu.
*asuba ta gari masoya๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ*

~Gobene fah..๐Ÿ‘ฏ๐Ÿ‘ฏ๐Ÿ‘ฏrengem rengemgem gobe ne daurin auren umaima fah...rengem..rengem..gem..๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผdafatan xaku xo fah...rengem๐Ÿ‘ฏ๐Ÿ‘ฏ๐Ÿ‘ฏ๐Ÿ‘ฏ~ *dis1 naa gobe.. Oyakaka..original gobe..* ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜lolx don't mind me
U r all invited 2d wedding hop xaku xo fans..tohm duk mai xuwa ya daga hannu๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ

๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œsai naji daga gareku..Lov u all *Reefat CE*
[2/21, 2:42 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*94*
By *Reefat yahya*


*yesss oooh...2day na 2day...auren umaima n basheer๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ*

12pm bash yana kwance a falon mahaifinsa baba ya fito ckn shirin jumaa yasha manyan kaya farare sol dasu se xuba uban qamshi yake..ya harari dan nasa tare da cewa
"Kwanciyan me kake min a falo baxaka je masallaci bane"
Ya marairaice kamar zaiyi kuka yace
"Allah baba bani da lfy I dnt tink xan iya xuwa "
"Bana son shashanci ka tashi maza ka shirya ynxun nan mu tafi don a can xaa daura auren umaima nasan take-taken naka salon kar kaje daurin auren ne kuma dole se kaje wllhi"
"Baba pls...
"Bana son maganar banxa ka tashi maxa ina nan ina jiranka"
Sum sum ya tashi ya koma dakin da yake zama ckn kankanin lokaci yayi wanka ya fito blue shadda yasa kayan sun masa kyau ba kadan bah ga qamshin turare kala2* ya ajiye hula sannan ya fito baba ya bisa da harara daga nan Suka wuce central mosque a can xaayi daurin auren.
Umaima tana kwance ta duba agogon dake makale a bangon dakin Karfe 1:10 shikenan saura kiris ta xama matar ismaeel , shuairat ce ta shigo tare da sallama abinci ta kawo mata farfesun kaxa ne yasha hadi sosai ta tura plate din agaban umaima ckn tamke fuska tace

"Maxa ki cinye ki bani plate ynxu"
"Mom sultan wai fushi kke dani"
"Mtsww..toh me! Ke kin damu kanki akan mutumin da bai damu dake bah, da a CE yana sonki ai da yaxo tuntuni amma saboda bai damu ba kinga ya nemeki ne? Kina nan kina Neman halaka kanki "

"Haba kinfi kowa sanin irin son da uncle bash yake min..ni nasan ba lfy bah...
"Dallah malama..ki ci abinci ki tashi ki shirya"
Tana kumbure2* haka tasha farfesun don bata ga alamar wasa a fuskar shuairat.
Bayan ta gama ta shiga bayi ta Dade kwance ckn jacuzzi tana lumshe idanunta hoton fuskan bash kawai take gani nan hawaye ya cika mata ido ta dauki tsawon minti 40 tana kwance , shuairat ce ta kira sunanta daga waje nan ta fara wanka daga bisani ta fito.
3:10pm an shiryata tayi kyau sosai ckn wasu dankareren leshi mai kyawun gaske umaima tayi kyau kamar a saceta a gudu a harabar gidan aka fito da ita masu daukar hotuna ne birjik ga nan yan uwa da abokan arxiki ma ga yan gayyan sodi irinsu Reefat๐Ÿ˜†๐Ÿ˜† ga masu watsa labarai daga gidan telebijin da yan jarida , gidan de a cike makil da jamaa umaima de daurewa take tana kokarin boye halin da take cki shuairat ansha kyau ta xama tauraruwa sha kallo ga salman da sultan ma haka, abun de gwanin burgewa.
Momsi ta fito Suka fara daukar hotuna sunyi family pix kala2* dakyar na samu na dau kala 3nida shuairat da amarya se kuma Wanda mukayi tare da salman da sultan๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ.
Horn muka ji a bakin gate take maigadi ya wangale kofar motoci ne birjik har na kasa tantance ko guda nawa ne, securities na fara gani ckn bakaken suits nace ah abun na manya neโ˜นโ˜น..Nigerian president ne a gefen mr president (dad) ga Chinese President daga barin hagu se kuma new faces da bansan ko su wanene bah daga gani dai kasan shuwagabannin kasacen duniya ne don daga irin shigar kayansu da masu tsaron dake xagaye dasu xaka gane hakan.ga can daddy a baya tare da abokanansa manyan mutane se kuma ismaeel na hNgo fuskarsa dauke da murmushi sai kuma bash daga can gefe yana ta gaisawa da mutane yNa dariya fuskarsa kamar gonar audugA..haaa..am confused๐Ÿ™„๐Ÿ™„ ya naga bash haka?? ..uhmmm.
Dakyar mr president tare da tawagarsa Suka samu hanyar shiga ckn gidan saboda jamaa sunyi yawa babu masaka tsinke. A can babban falon gidan Suka xauna daddy kuma yana dayan falon tare da tawagarsa , abinci da na sha aka ajiye musu suna ci suna taba hira ana dariya daga bisani yan jarida Suka fara daukan hotuna don yadawa a gidan labarai, shuairat da umaima sun shigo falon anyi hotunan tare dasu ana tayasu murna.har 5pm ana abu guda dakyar shuairat ta jawo umaima Suka koma bangarensu a daki Suka xauna shuairat tace
"Ki shirya anjima xaa ne dinner"
Idanunta sun cika da kwalla tace
"Allah na gaji baxan iya xuwa bah"
"Shikenan bari naje na sanar da dad "
Ckn Sauri tace

"Ah'ah pls kiyi hkri xan shirya ynxu"
Murmushi shuairat tayi sannan tace
"Kije falona babu kowa a can angon yana son ganin ki"
"Eyya mom..Allah na gaji sosai"
"Ok bari na kirashi yaxo ya sameki "
Bata jira amsa bah tayi waje dama su 2 ne kawai a ckn dakin sauran jama'an suna can kasa suna faman daukan hotuna. Umaima ta hada kanta da guiwa ta fara rusa kuka..shikenan yau ta xama matar wani !
Kofar dakin aka bude ta cigaba da kukan da take ba tare da ta daga kai bah..a hnkli ya xauna kusa da ita ya jawota a jikinsa , qamshin turaren da har abada baxata manta dashi bah ckn Sauri ta daga ido tare da cewa
"Uncle bash๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ
Murmushi ya sakar mata mai sanyaya xuciya , nan kuwa ta turesa gefe tana hawaye tace

"Kasan de ynxu na xama matar wani"
"Har abada Ke matata CE mutuwa CE xata rabamu"
Wani murmushi mai ciwo tayi tana girgixa kai tare da cewa
"Kana magana tmkar baka San yau an daura aurena bah"
"Yes ofcoz an daura auren ki but da masoyinki aka daura auren"
Ya karasa magana tare da lakuce masa hanci ckn rashin fahimta tace

"Bangane bah"
"Yes umaima Allah ya cika mana burin mu an daura mana aure n...
Bai samu damar karasa maganar ba ta fada jikinsa ta rungumesa gam hawaye wani na bin wani..murmushi bash yayi tare da daura hannayensa shima ya rungumeta ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜
Sun kasance ckn wannan hali har na lokaci mai tsaho sannan umaima ta xame jikinta sai kuma kunya ya kamata tasa tafin hannu ta rufe fuska wai ita kunya๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ™„ daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa...๐Ÿ˜ฌ๐Ÿ˜ฌ๐Ÿ˜œ.

Toh ya akayi abun ya juya aka daura da basheer???
๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”
Fans ..just ignore d typing errors cos bana editin
[2/21, 2:42 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*95*
By *Reefat yahya*



Fuskokin nasu dauke da Murmushi suna kallon juna ..a hnkli bash ya jawota ya rike mata hannu tare da kura mata ido yace
"Baby no more kunya pls..kin xama matata u r mine n am urs murna xakiyi ki godewa Allah da ya cika mana burin mu"
ta daga kai tace
" but Bb ya akayi hakan ta faru har daddy ya amince aka daura mana aure"
"Ni zan baki amsa"
Shuairat ce ta shigo fuskarta dauke da murmushi ta cigaba da cewa
"Yau da safe na samu labarin but naki na gaya miki cos I want 2 surprise u"
Nan kuwa umaima ta ruga a guje ta rungumi shuairat tana dariya tace
"Tnk u so much mom..nasan da taimakon ki akayi wannan auren Nagode sosai Allah ne kadai zai biyaki tnx a lot"
"Mention not dia "
"Toh mom ki ban labarin ya akayi ..am waiting"
"Umaima hoo..irin xumudi haka"
Kunyace ya rufe ta nan ta koma gefen gado ta xauna bash kam se kallonta yake kamar wani tsohon maye ta birkita masa kwakwalwa ta kara kyau ba kadan bah..shuairat CE ta fara magana
"Jiya daddy yaje gun baba tare da dad naki sun dade suna hira har daddy xai dawo sai yake tambayan ina yaya don tunda yaxo be ganshi bah, aka ce masa yaya bashi da lfy yana bacci daga nan Suka dawo gida.yau da safe naje gun daddy bayan mun gaisa yake tmbyta ya me jiki ckn rashin fahimta nace masa waye ba lfy? Ckn mmki shima yace baki san yynki bashi da lfy bah? Nan hawaye ya cika idanu na hnklin daddy ya tashi ya fara bani hkri yace da yasan baa gayamin da baxai tmbyeni ba gashi ya dga min hnkli, nace masa ba batun rashin lfyn ne Ke sani kuka bah illa tausayin halin da yaya xai shiga nan gaba..daga nan na xayyana masa komai.fada yake ta inda yake shiga ba ta nan yake fita bah wai akan wane dalili xaa boye masa wannan lamarin, nace tun farko naso sanar da kai but baka saurareni bah daga nan ya kira baba nan ma fada yake akan cewa meyasa baba be sanar dashi bah.a takaice de haka ya kira ismaeel da babansa ya basu hakuri ya nuna musu yarinya bata so , haka Suka hakura har xuwa lokaci daurin auren ko shi yaya bai San cewa dashi xaa daura auren bah.toh kinji de yanda abun ya faru"

Wani dogon numfashi umaima ta sauke tare da cewa
"Ikon Allah kenan..tabbas wani baya auren matan wani, matar mutum kabarinsa hakika rabo in ya rantse babu mai hanawa don nikam tuni na fidda ran sake haduwa da Bb..Allah Nagode maka da ka cika min burina , mom Nagode miki da kokarin da kikayi kuma daddy ma dole na gode masa"
"Kai umaima ko Ya'r kunyan nan babu"
ta rufe fuska tana dariya shuairat ta tashi tsaye tare da cewa
"Ki shirya ynxu masu makeup suna nan tafe kinsan akwai dinner nima na tafi idan nayi sallah xan fara shiri na"
Basheer yayi murmushi yace

"Wait..sisy kina nufin kema xaki he?bayan kece mmn amarya"
Harara ta watsa masa tace
"Toh bari kaji har mijina ma sai yaje don abun tuwo na maina ne ...kuma a ckn gidan nan xaayi"
ta juya gun umaima tace
"Ke kuma ki xauna ki biye masa har lokaci ya kure Ku gaku nan romeo n Juliet , an de daura auren xamu gani ko xaku hadiye junanku"
Dariya sosai suke shuairat ta yi hanyar kofa bash yayi saurin cewa
"Kixo gidan mu ki ga yanda xaa hadiye juna ...ki xo na koya miki Lov yarinya"
"Ahaaff...wllhi karyan mutum yace xai koya min soyayya , duk kalan Lov da xakuyi de wasu sun Riga sun gama ..toh wai ma wane darene jemage bai gani bah"
"Daren goma sha hudu"
Ya fada yana dariya tsaki shuairat ta ja ta bar dakin umaima ta hararesa ckn salon so tace
"Mom ce fah..she is ur in law u have 2 learn hw to respect her"
"Lol..babu mai shiga tsakanina da baby so ki xuba mana ido kawai"
"Ni baby ! Ita baby! So which 1...gskiya ka xabi daya"
๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณโ˜นโ˜นuhmm ni Reefat nace toh fah...umaima tun ynxu๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ™„Dakyar bash ya fita ya barta ba don yana so bah nan ta fada wanka.

8:30pm garden din gidan mr president ya cika makil da jamaa an kawata wajen da kujeru da furanni masu kyau ga nan decoration de gwanin burgewa ga wutar lantarki ya haska wajen..yan mata da samari wasu suna xaune a bakin swimming pool suna ta hira manyan mata kuma suna can xaune daga masu cin abinci se masu shan drinks idan ka duba wani fannin kuma mr president ne tare da manyan mutane irin su US president Chinese president Nigerian president da dai sauran kasace daban2* daddy ma yana can tare da manyan abokanansa yan siyasa da yan kasuwa da ma talakawan gaba daya.amarya da ango sunyi ado sun sha kyau sai daukansu hotuna ake ana yadawa a social ntwrks suna can tare da frenz dinsu suna hira tare da xagayawa suna gaisawa da jama'a, shuairat tana xaune tare da manyan matan ministoci da shuwagabanni suna ta hira ckn nishadi.matured dinner irin Wanda baa taba yin irinsa ba a duk fadin kasar bcos babu irin kade-kade ko rawa da sauransu cool music kawai Ke tashi kowa na shaanin gabansa kyaututtuka kuwa wrapping ake sai a mikawa amarya da ango sannan security ya karba ya ajiye a wajen da aka tanada domin ajiye kyautar.gwanin shaawa jamaa da dama sun halarci taron Wanda baxan iya lissafa su bah.
Washe gari aka dauki amarya aka wuce da ita gidan mijinta dake can central area bayan shuairat da sauran yan uwan mamanta sun mata nasiha sosai..mr president kam yaki haduwa da ita don ya tuna da mahaifiyarta yinin ranar gaba daya a ckn daki ya kasance , shuairat ce take lallabashi.da yamma akayi fansa a can gidan iyayen shuairat shukrah ma ta daure taje fansar.
[2/21, 2:42 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*96*

Bayan an gama biki lfy jama'a sun watse amarya ta tare a dankareren gidan ta Wanda an narka uban dukiya a cki.da safe ta tashi ta gyara gidan ta kunna turaren wuta tare da fesa room freshener gidan ya dau qamshi ta fada wanka ta shirya ckn atamfa tayi kyau sosai ta ajiye daurin nan a gaban goshi se xuba qamshi take ta gaji sosai don bata saba da aiki bah gskiya dole a kawo mata masu aiki tana nan tsaye a gaban dressing

Please Login or Register in order to submit comment