Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

" am not trying to my dia , I just want u 2understand d situation"
" hmmm yaya kenan baka son laifin megidanka koh, gaskiya am disappointed ban taba tsammanin haka yake treating na talakawa ba....
" hey sis! Ina son ki gane cewa Mr president bashi da laifi is just dat yana busy ne"
" ok fine naji" daga nan kowannensu yayi shiru .bash ya tashi ya koma dakinsa ita kuwa ta kira shukrah a waya Suka sha hirarsu.

Karfe 10 na safe ya samesu ne a gidan mr President, yauma irin na jiya ne ko kuma a CE gara jiya tunda sun sami ganinsa duk da cewa basu gana ba.haka Suka yini ko gistawa mr President beyi bah kuma an hanasu shiga har yamma Suka koma gida. A takaice de kwana 4 a Jere suna xuwa basu cimma burinsu bah.
Suna xaune ckn mota a harabar gidan shuairat ta juya ta kalli Mahmud tace " kasan Allah! Yau baxan koma ba se na gana da Mr president". Dariya ne kubcewa Mahmud yace " kada kice haka shuairat"
" is not funny Mahmud trust me"
" ok fine.. I trust u" motocine a kalla xasu kai 11 kyawawa masu tsada Suka jera xasu fita da alama de mr President xashi wani wajene .
" Mahmud kabi bayansu pls". " ke lafiyanki kinsan ina zasu je ne?
" kada ka bata min lokaci pls" ba gardama Mahmud ya juya yana bin convoy na shugabankasa.sun kai 20mins suna tafiya shuairat ta umarci Mahmud yayi over taking ya je kusa da wata farar mota mai bakaken glass da alama shine wanda shugabankasa yake ciki.ckn tsoro Mahmud yace shi baxe Iya bah, shuairat ta cigqba da rokonsa dakyar ya amince yayi over taking yaje dab da motar. Sauran motocin Suka fara horn Mahmud kam ya razana , nan sauran motocin da suke gaba Suka ja birki wannan farar motar itama taja ta tsaya don son ganin wanene ke bin mr President.
[2/21, 2:29 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*7*
By *Reefat yahya*


Gaba dayan motocin sun xagaya su shuairat da kuma wannan farar motar.securities Suka fito rike da bindigogi babu bata lokaci Suka tunkari motar Mahmud Wanda yayi mutuwar xaune yasan lallai yau kashinsu ya bushe ya juya gun shuairat tana xaune ckn kwanciyar hnkli ta xare I.d card nata tana murmushi tace" idan kunsan wata Baku San wata ba ai"
Mahmud kam yana ta mmkin halayen yarinyar tana da confidence akan komi bai gama tunani ba ta sa hannu ta bude kofa ta fito rike da I.d card da kuma jotting book nata tana wani shuumin murmushi "freeze! Wani bakin security katon gaske ya fada da karfi a yayinda ya nuna ta da bindiga , hannayenta ta daga rike da I.d card da jotter tana murmushi. Securities din suna kallon juna suna mamaki kuma Kansu ya daure don basu taba tunanin cewa mace CE a ckn motar ba.shuairat ta kalli wannan bakin security tace " I min no harm am just a reporter"
" hw can I trust u young lady" ta cire I'd card din ta mika masa yasa hannu ya karba a hnkli don su basu yarda da ita bah ganin ta suke tamkar wata Ya'r ta'adda wacce aka turo don kulla wani makirci.ya gana duba I.d card din yace " me kike so?
Babu bata lokaci ta gaya masa bukatarta nan ya juya gun wannan farar motar a hnkli aka sauke glass .mr President yana zaune a baya da jarida a hannunsa ba tare da ya daga kai ya kalli securityn ba ya fara magana" me take bukata" " she is a reporter sir!
" let her in"
๐Ÿ˜ณurxcellency!
" yes let her com in here". " but sir we can't trust her"
" Adams dis my command not a request". Ok sorry ur xcellency sir! Nan ya juya gun shuairat ya bata ixinin shiga wannan farar motar bayan ya bude mata kofa.mamakine karara a fuskokin bodyguards din kowannensu da tunanin da yake nan Suka sallami Mahmud.mr president ya basu umarnin tada motocin don xuwa meeting da zashi.shuairat ta daga kai a hnkli ta sake saukeshi saboda kwarjininsa tayi shiru ta kasa magana
" young lady ba interview kika zo yi bah? Shiru tayi ta kasa magana dakyar tace " mr President idan bazaka damu ba ina son ka bani tym da zamu sameka a office ni da abokin aiki za....

" kina nufin ke bazaki Iya min tambayoyi ba se abokin aikin ki? Nan ma shiru tayi .yaga dai bata da niyar magana kawai ya umarci p.a dinsa Wanda yake xaune a gidan gaba cewa a rubutawa shuairat notice gobe ta samu ixinin ganin mr President a office. Tayi godiya ta karba sannan aka sauketa a gefen hanya, wani dogon numfashi taja gashi ba waya a hannunta bare ta kira Mahmud kawai ta sami taxi ta wuce office ta karbi kudi gun Sarah ta biya tana shigowa Suka gaisa Sarah tace" ynxun nan Mahmud ya shigo yana gun manager"
" ohh dama yana nan ? Ta tambaya a bukace
" manager ne ya kira shi yana ta fada wai gobene dateline din aikin da ya Baku" hmm manager baxai gane bane is not easy fah"
" har ynxu basu Baku chance bah? Sarah ta tamabaya tana kallon shuairat
" sarah aikin nan fah akwai wahala"
" yeah I knw , anyway wish u best of luck "
" tanx dear"
Mahmud ne ya fito daga ofishin mr Muawiya fuskarsa a hade amma suna hada ido da shuairat yaji wani sanyi a ransa." Zo mu gana kanwata" nan yaja hannunta sukayi waje mota Suka shige ya juya suna fuskantar juna" gaskiya u did well"
" tanx" " so ya labari"
" babu fan nikam nace masa gobe zamuje mu same....
" God ! Kin kwabsa girl kinyi wasa da opportunity y?"
" Mahmud mutumin yana da kwarjini sosai wllhi na kasa yin magana a gaban idonsa kuma kasan ni ban taba yiwa wani interview bah"
" haka ne nasan dis ur first tym , but kinsan me? Yanxu xan rubuta miki tambayoyin da zaki masa gobe idan munje ke zakiyi magana"
" but Mahmud....
" shhhhhh! Ya katse ta tayi shiru sannan yace " idan na baki questions din sai ki kara da naki ok"
"Ok! Nan ya tada mota Suka kama hanyar gida.
[2/21, 2:29 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*8*
By *Reefat yahya*

11:10pm tana kwqnce a saman gadonta bayan ta gama haddace tambayoyin da zata yiwa mr President sai kuma ta fara tunani toh yaransa nawa? Shin ina matarsa? Don gaskiya bata taba jin wani ya ambaci sunan matarsa bah.wayarta ta fitar ta danna layin yaya bash ringing biyu ya daga yace " reporter bakiyi bacci bah?
" yaya I need ur help"
" ok ki bude min kofa gani nan xuwa"
Ckn kankanin lokaci ta fito falo ta bude kofar shiga flat din tana xama kenan ya shigo tare da sallama.
" yaya matan mr President nawa n yaransa nawa?
" y not gobe ki tambayesa zai gaya miki ai" " no pls yaya ka taimakeni"
"Ok fine! Mr president bashi da mata a ynxu haka"
" sun rabu kenan?
" ok bari in baki takaitaccen tarihin rayuwarsa....
Suleiman Mohammed Dan asalin jihar Adamawa ne haifaffen garin mayo-belwa shi Fulani ne gaba da baya, shi kadai ne a gun iyayensa babansa maaikacin banki ne ya tashi a Lagos can yayi karatun primary da secondary sannan yayi first degree a UK ya karanta public administration sannan yayi masters kafin ya dawo ya auro matarsa zainab wacce aka hadasu auren xumunci .sunyi zaman lafiya sosai da ita bayan shekaru 3 Suka haifi ya mace sunanta Aisha ana kiranta umaima daga nan Suka koma Cyprus yayi PhD dinsa a bangaren international relations kafin ya dawo Nigeria ya fara aiki a Lagos, president na wancan lokacin abokin babansa ne shi ya kirasa ya bashi minister of d federation haka ya fara politics bayan shekaru da dama ya rike manyan offices har zuwa tym din president Joshua okafor aka bashi vice president, bayan an sami matsaloli a bangaren mr Joshua senators sukayi meeting aka cireshi aka bawa Suleiman acting president kuma suna son yayi contesting na next election da zaayi.Suleiman is a nice n friendly person b4 mutuwar matarsa , tayi accident da jirgi ta rasu ta bar shi da yara 2 umaima ya'r 18 yrs da sultan 7yrs old.daga nan ya zama shiru shiru kullum baya ckn walwala, kuma baya son shugabancin da aka bashi yana son ajiye aikin a halin da ake ciki wannan shine tarihin rayuwarsa kenan.
Hmmmm.....shuairat ta ja wani dogon numfashi " shekarunsa nawa "
" he is 45yrs old" " gaskiya yana da jiki mai kyau, bazaka taba cewa yana da ya' har 18yrs bah"
" shikenan koh?
" ehh tank u yaya "
" je ki kwanta toh" har ya kai bakin kofa ya juya yace "ohh namanta naji labarin yau kun hadu dashi koh? " yaya ...
". Yeah kinyi kokari kin kafa tarihi" daga nan ya sa kai ya fita ta tsaya tNa murmushi ita kadai.bayan ta kulle kofa ta koma dakinta ta fara nazarin labarin da yayanta ya bata na mr President. Allah sarki no wonder aka CE yana da girman kai don bai Faye magana ba, tabbas yana ckn matsala Wanda Allah ne kadai xe fitar dashi toh meyasa bai kara aure bah? Oho ta bama kanta amsa haka ta cigaba da sake sake har bacci yayi gaba da ita.

( lols..som people will b wondering wai president 45 yrs old? Anyways don't mind me am just trying to entertain ๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š)
Happyy reading hop kuna jin dadin labarin ....Lov u all๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[2/21, 2:29 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*9*
By *Reefat yahya*


Da safe ta gama shirinta tayi brkfast ta gama komi tana zaman jiran Mahmud bayan wani lokaci kadan ya kirata a waya ya shaida mata yana kofar gidansu tayi sallama da mama sannan ta fita Suka dau hanyar xuwa villa.
Ta nunawa wani bodyguard note din da mr President ya bata akan cewa zasu gana dashi yau, firr mutumin ya hanasu shiga haka Suka hakura Suka koma Suka xauna.wasu bodyguards ne Suka fito daga wani bangare sun saka wata yarinya Ya'r kyakkyawa a tsakiya tana tafiya tana waya daga ganinta shuairat ta gane cewa ita CE umaima , a bude mata kofar shiga ofishin baban nata suka wuce ita da bodyguards nata.a ranar ma haka Suka yini ba tare da ganin mr President bah har yamma Suka tashi ckn bacin rai Suka kama hanyar gida. Mahmud ya lura da yanayin da shuairat take ciki na bacin rai don haka ya fara tuannin hanyar da xaibi don ganin ya faranta mata yayi parking a gaban wani supermarket na *cash n carry* ya juya Suka kalli juna yace " sis ki rakani ciki pls"
" no Mahmud am not in d mood kaje kawai"
" yi hakuri muje"
" no just go " haka Mahmud ya hakura ya shiga ya danyi light shopping ya siya mata turare da kuma chocolates sannan ya fito ya ja mota babu Wanda yayi magana bai tsaya ko ina ba sai national stadium.shuairat ta juya tana kallonsa bcos bata taba xuwan stadium din bah murmushi yayi yace " bismillqh " ba musu ta sauka bayan ya kulle mota yana rike da chocolate a hannu Suka fara trekking har xuwa inda aka tanadi kujerun xama stadium din a cike yake Amma ba makil bah ana kallon wasa ko na ina ne oho! Shuairat dai sai kalle kallenta take nan Suka xauna ya siya musu popcorn da drinks ya mika mata chocolate ta fara ci haka Suka kasance bayan wani lokaci Suka tashi Suka zaga ckn stadium din yana nuna mata ko ina sun dauki hotuna da dama. Daga nan *children's park n zoo* Suka wuce nan ma ya siya musu icecrm Suka dauki hotuna da dabbobi suna tafiya yana bata labaru masu ban dariya har magariba Suka fita ya ajiyeta a gida tare da mika mata ledar cash n carry tayi godiya sosai sannan Suka rabu.

******************
Ta idar da sallar isha tana zaune tana tunanin hanyar da zasu bi su cimma burinsu, wayarta CE ta fara ringing shukrah CE nan ta daga Suka sha hirarsu shukrah tana bata labarin saurayinta Abkr yayi aure .bayan sun gama wayar ne ta ajiye kenan mama da babanta Suka shigo falon hira sosai suke baba ne kawo xancen auren yaya bash yace"
Yaron nan bashi da niyar aure ina ganin jibi xan tafi can Adamawa xan nema masa auren shukrah'
" yeee baba Allah da ka kyauta kuwa"
" ke dallah rufe mana baki auren dole zaa masa ne malam?
" haba Fatima kina ganin yaron nan ya girma yana da 30 da doriya zaman me yake yi?
" malam ka Dan bashi lokaci man "
"Ke dai baki son laifin danki"
" Allah baba shukrah zata dace da yaya" shuairat ta fada ckn marairaicewa
" rufemin baki, ke da kike zancen yayan naki ke ma kin girma ai aurar dake zaayi" mama ta fada tana kallon shuairat. Bash ne ya shigo tare da sallama ya nemi waje ya xauna " yauwa Dan albarka dama xancen auren ka mukeyi" a hnkli bash ya daga kai Suka hada ido da baban sa." Gani nayi har ynxu baka kawomin wacce kake so bah shine nace mezai hana Ku daidaita da shukrah Ya'r wajen malam Habu"
Shiru yayi shi baya son yayi gardama da iyayensa kuma shi bazai CE yana son shukrah bah kuma bazai CE baya sonta ba hasali ma shi bai taba yin soyayya bah

..."kayi shiru baba na"
Muryan mahaifinsa ne ya katse masa tunani

" ba komai baba na amince a je a nema min aurenta"

" masha Allah Allah ya muku albarka"

" ameen " gaba daya Suka amsa.
Shuairat kuwa dadi kamar ta hadiye yayan nata nan kuwa ta rungumesa tana jin dadin amincewar da yayi.
mama ma ta Sanya musu albarka
Haka Suka cigaba da hira suna shan fruits suna kallon news har xuwa 11pm sannan kowannensu ya koma dakinsa da shirin bacci.
Asuba ta gari 1 family



Lov u all my fanx
07030077024 4corrections o advise
๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[2/21, 2:29 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*10*
By *Reefat yahya*


Yau shuairat bata da niyyar xuwa wajen aiki bayan tayi sallan asuba ta koma bacci bata tashi da wuri bah mama taji shiru shine ta leka dakinta tana nan tana baccinta ckn kwanciyar hnkli a hnkli ta fara tashinta dakyar ta bude ido.
Bayan tayi wanka ta shirya tana karyawa mama ta bita da kallo tare da cewa " me ya hanaki tashiwa da wuri"
" uhmm mama ni fah yau baxanje aiki bah"
" akan wane dalili? Ko wata daya baki yi ba ki fara....
" toh ni mama...ta katseta tana xumbura baki
" kinga malama bani xaki gayawa bah, ki bari yayan naki yaxo se ki gaya masa tunda shi ya sama miki aikin" daga nan mama ta tashi ta bar mata falon shuairat kuwa se kumbure kumbure take .
Ko ya Mahmud ya tashi oho se ynxu ta tuna da cewa wayarta na silent wuff ta koma daki tana daga wayar taga misscalls 15 yayanta , shukrah da kuma Mahmud ta rasa was xata fara nema.
Falo ta koma ta tattara kwaninkan da tayi amfani da su ta wanke tana fitowa taji sallama lallai muryan Mahmud ne. Ta zare mayafi tayi waje, yana nan tsaye a bakin gate ta sakar masa murmushi a yayinda shi kuma ya watsa mata harara tana murmushi tace " tuba nake big bro "
Beyi magana ba ta kama kunne ta marairaice tace
" sorry naa" wani irin Yarr Mahmud yaji dakyar ya saita kansa yayi gyara murya yace
" is ok ya wuce Amma gskiya kin bata mana show, kinsan mr President da kansa yace a kira JF Reporters but baki nan na kira wayarki har na gaji baki daga ba, na nemi yaya bash shima yace baki daga ba"
" sorry yayana " nan ta wuce tayi sallama da mama sannan ta dauki handbag dinta da duk wani abunda take bukata.
Yana ckn mota yana jiranta ta bude gidan gaba tare da sallama nan ya tada mota Suka dau hanya.shiru Suka can Mahmud ya katse shirun da cewa

" who knws ma ko ya kira wasu journals olredy"
" c'mon yaya I said sorry naa"
" I knw ! Ni ba wai ina blaming naki ne, kawai ina ganin munyi loosing opportunity ne"

" kada ka damu insha Allah zasu bamu second chance" a haka Suka cigaba da tattaunawa.

Sun shigo dakin ana ta binsu da ido saboda kowa yaji cewa shugabankasa na son ganawa da su, mutane suna ta gulma ana nunasu shuairat cewa ga yan *jf* din da yake son ganawa da su ko meye dalili oho!
Wani bodyguard ne shuairat ta masa magana tayi mishi bayanin komai nan yace mata yana xuwa
Bayan kankanin lokaci ya fito ya kira shuairat ya bata ixinin shiga , ta kira Mahmud bayan an duba I.dcard nasu sannan an duba jaka da komi nasu aka basu ixinin shiga.
Bodyguard din yana gaba suna biye dashi a baya wata Ya'r tafiya sukayi ko ina securities ne suke zarya kai tsarin ginin yayi , wata kofa Suka bi sannan ya sada su da wani ofishi kamar falo mai dankareren kyau wani matashi ne yana xaune ya dukufa se faman rubuce rubuce yake ga kuma securities nan birjik , sun sake shiga wani ofishi kafin Suka iso inda mr President yake ganawa da baki.
Dankareren daki ne kamar conference room ga kujeru masu kyau, kai a tsaya baiyana kyaun wajen ma bata lokaci ne, yana zaune a kan kujera hannunsa rike da jaridar daily trust yasha fararen manyan kaya masu uban kyau da tsada idanunsaa sanye da farin gilashi nan shuairat ta kafa shi da ido tana kallonsa guy din ya hadu๐Ÿ˜œ( Allah yasa dai Meenat bata fole ba)
Hannu ya daga nan da nan bodyguards din duk sun fita se yaya bash kadai ya rage yana tsaye a gefen mr President ya wani sunne kai tamkar ma bai taba ganin shuairat ba.
Shuairat ta lura cewa idan zasu yini a wajen mr President baxai taba cewa ko uffan bah, sabanin Mahmud da yake rawar dari sabagen kwarjinin mr President๐Ÿ˜œ๐Ÿ‘คakyar ta daure tace
" sir! We ar here 4d interview"
Se da ya kai minti 3 sannan yace
" I knw"
[2/21, 2:29 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGAN KASA๐Ÿ’ž
*11*
By *Reefat yahya*

"Sir!
Ta furta a hnkli ya daga kansa ya kai dubansa gareta a yayinda Suka hada ido tayi saurin sunkuyar da kai tana kallon kasa .
Ya fara magana ckn harshen turanci
" ke wace irin yarinya ce wacce bata San aikinta bah? Tun dazu na kiraku baki zo ba, dama haka kika saba yi a wajen aiki?

" sorry sir! Ta fada a hnkli tmkar Mara gaskiya.
" irin kune Baku xuwa aiki idan anzo ba a biya salary ba kuma xaku fara korafi"
" sorry mr President sir!
Ya sake kallonta daga sama har kasa ya maida hnklinsa kan jarida.Mahmud ne ya daure yace
" sory mr President idan Allah ya yarda hakan baxe sake faruwa xamu kiyaye"
Ya share 5mins sannan ya duba hadadden agogon dake makale a hannunsa yace
" well! Na Baku minti 10 "
Shuairat da Mahmud Suka kalli juna tare da xare ido cos sun San cewa 10minz yayi kadan Amma ya Suka iya.
Shuairat ta fara magana
" mr President sir! We will like to know abt u"
" am Suleiman Mohammed d acting president of federal republic of Nigeria, am from Adamawa state.

Ya cigaba da duba jaridarsa shuairat tayi Jimm...toh shikenan abunda xai Iya gaya musu kenan? Anyways
Ta sake cewa
" sir! Munji labarin cewa zaka fito Dan takarar shugabankasa nan....
" no! Bani da burin haka kuma yanxu ma ba da son raayi na ne na zama acting president ba, bana bukatar mulki ko wani shugabanci"
Ya katse shuairat tun bata gama fadar abunda tayi niyan cewa ba.
" mr President shin xamu Iya jin ko yaranka nawa "
Ya daga kai yana kallonta sannan yace
" ina da yara biyu mace da namiji"

" wane lokaci ne Wanda baxaka taba mantawa dashi ba a tsahon rayuwarka, na farincki ko bakin ciki

Tsitt dakin yayi babu Wanda yayi magana mr President ya ajiye jaridar hannunsa tare da mikewa yace
" mintuna 10 da na Baku ya kare u can leave pls ina da abun yi"
Shuairat ta gama rubuce rubucenta sannan ta juya tace
" mungode da lokacin da ka bamu , but mr President wane irin Abu yaranka suka fi so kuma....
" leave now!
Ya fada da karfi har shuairat ta tsorata nan ta tattara takardunta tana rawar jiki bayan Mahmud kuma ya dauko camerarsa sukayi waje yaya bash ya kulle kofa sannan ya dauko ruwan sanyi ya mikawa mr President Wanda take yaji wani ciwon kai na damunsa.
A waje Suka tsaya ta gama har hada takardun Mahmud ya kalleta yace
" kinyi kokari sis Amma kema meyasa zaki yi tambaya akan personal lyf dinsa"

" babu wani personal life kawai de baya son ya tuna wani Abu ne da yake ci masa tuwo a kwarya"
" wane irin abune haka" murmushi tayi tace
" mu tafi kawai kada ka damu xakaji komi"
Nan Suka wuce anata kallonsu suna jin dadin samun nasara yau de sun huta da balain mr Muawiya.
Mota Suka shiga direct office nasu yayi parking Suka jera har ciki, ba karamin dadi mr Muawiya yaji ba duk da cewa sun sanar dashi mr President be basu time sosai ba nan Suka fara tataunawa akan yanda xasuyi publishing don samun cigaba a kamfanin nasu shuairat kuwa tayi alkawarin kara musu wasu bayanai daga ckn tarihin rayuwar mr President Wanda ta sani game dashi.
Bayan sunyi sallama da kowa akan gobe zasu fara aikin nan Mahmud ya sauketa a gida sannan ya wuce nashi gidan.

Lov u mah fanz drop yah comments๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
*Dr Reefat Lov*
[2/21, 2:29 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*12*
By *Reefat yahya*


Da misalin karfe 10 na safe sun hallara a office dinsu nan Suka fara editing na interview da sukayi da mr President, shuairat ta kara basu wasu information da basu sani bah nan Suka tura xuwa website nasu da blogs da Facebook da sauran social media bayan sun buga shi a magazine nasu.
Ckn kankanin lokaci Suka fara samun likes da comments ko ta ina , farin ciki a gun mr Muawiya baa misalta shi ckn jin dadi ya musu ordering na snacks da drinks suna celebrating din samun nasara.

Mr President yana xaune a dakin hutawarsa shi kadai bayan ya sallami masu tsaronsa suna daga waje a bakin kofa , yana son kasancewa shi kadai yana bukatar Hutu ya kurawa hotor wata mata ido babu ko keftawa kalaman shuairat ne ke yawo a kwakwalwarsa
" wane lokaci ne bazaka taba mantawa dashi a rayuwarka, na farin ciki ko bakin ciki"
Ya fashe da kuka tamkar karamin yaro ya rungumi hoton a kirjinsa bai San cewa yana son matar tasa ba sai da ya rasata
Yana tuna irin xaman da sukayi a farkon ranakun aurensu , baya nuna mata kulawa kawai biyayyane yasa ya amince ya aurota. Ya tuna kalamanta na cewa " yaya Suleiman kayi hakuri nasan an hadamu auren nan ba don son raayinka ba, amma duk da hakan bai hanaka xama dani bah baka taba wulakantani ba, shiyasa nake maka adua Allah ya baka wacce zaka so itama ta so ka Ku xauna har abada"
Wiwi ya cigaba da kuka tabbas yayi rashi saboda zainab macece mai hnkli da hakuri tana da kawaici sosai.
Ya tuna ranar da zata tafi lokacin da ya ta sameshi a falonsa zata masa sallama ta so suje airport tare Amma ya nuna mata yana da aiyuka a gabansa , ckn sanyin jiki ta fara magana
" Dadyn umaima ga amanar ya'ya na ka kular min dasu kada ka bari wani ya cutar dasu , kai kuma ina maka fatan alheri kuma Allah ya baka mace ta gari wacce xata rikeka tsakani da Allah"
"Haba zainab don zakiyi tafiya shine kike irin wadannan maganganun? Ya bata amsa ckn sakin fuska
" no ina nufin ka kula dasu kafin na dawo daga tafiyar da

Please Login or Register in order to submit comment