Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zanyi, batun aure kuma nasan ni baka sona shiyasa nake maka aduan Allah ya baka wacce zaka so"
Murmushi yayi sannan yace
" kedai yau kuma kishin ne ya motsa" ya rakata a bakin mota sukayi sallama tana daga masa hannu har driver ya ja motar Suka wuce airport daga nan kawai sai labarin mutuwarta ya riske shi.kuka sosai ya cigaba da yi tabbas shuairat ta tabo inda yake masa ciwo mutuwar ta dawo masa sabuwa
Ya Dade baiyi kuka irin na ranar bah.
Kalaman shuairat ya sake tunawa a karo na biyu " mr President me yaranka Suka fi so a rayuwarsu?
Ya salam! Anya ya rike amanar da mamansu ta bar masa kuwa?
Innalillahi wen last ya zauna dasu har yasan matsalarsu, baisan me suke ci ba bare me suke sha kwata-kwata bashi da lokacin zama dasu..lallai bai kyauta musu ba ga rashin uwa ga kuma rashin uba.
Ckn zafin nama ya tashi tsaye kofa ya nufa yana kai hannu aka bude masa duk da kansa na kallon kasa amma hakan be hana bash gane cewa wani Abu na damun uban gidan nasa amma ba halin tambaya.bangaren yaran ya nufa bodyguards Suka Mara masa baya ya iso dab bakin kofa ya daga musu hannu nan Suka tsaya shi kuma ya karasa ciki suna mamakin changin da mai gidan nasu yayi ckn kankanin lokaci.

Ya shigo tare da sallama babu kowa a falon direct dakin baccinsu ya wuce ya kwankwasa kofa
"Waye? Umaima ta fada ckn wani irin muryar da bazaka tantance ba
Yasa kai ya shigo tare da sallama tana xaune a saman gado sultan kuwa yana bacci a kan cinyarta , ya daga kai Suka hada ido idanunta sunyi ja kamar jini xai fita da alama dai itama taci kuka yaji tausayin yaran sosai.
A gefe ya xauna umaima ta kawar da fuskanta gefe ya rasa ta ina zai fara chan yace
" baby am so...
" dad! Muna lafiya kalau as u can c little ma dakyar yayi bacci yanxu sabida yau birthday din sa ya tuna da mom"
Hawayene ya kara diga a fuskar ta bayan tana kirkiro murmushin karfin hali.
Ya ilahi! Har ya manta yau birthdayn dansa? Me yake damunsa ne ? Tabbas ya cutar dasu Amma ta ina xai fara
" umaima kuyi hakuri nasan...

" oh dad kar ka damu nasan aikine ya rikeka u almost fgt dat muna existing a duniya ma"
"Umaima pls...
"Dad is ok! Muna Iya Rayuwa ko babu kai, muna cin abinci ana bamu kudi muna shiga motar da muka ga dama me yafi wannan dadi a Rayuwa?
Sam ta hanashi magana a hnkli ya jawota jikinsa ya rungumeta nan ta fashe da kuka , shi ma kukan yake yi Amma Mara sauti.
[2/21, 2:29 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*13*
By *Reefat yahya*

Haka mr President ya kasance an rasa mai rarrashin wani tsakaninsu dakyar ya daure ya share mata hawaye yana bata hakuri akan rashin kulawar da yake musu nan little ya farka yana ganin uban nasa ya rungumesa gwanin tausayi daga nan yace su shirya zasu fita.ya koma bangarensa bayan ya shaidawa bodyguards nasa ayi arranging na garden xaayi birthday, umaima da sultan sunyi kyau sosai se wani nishadi suke mr President ma ya sha manyan kaya mota daya Suka shiga .shopping Suka je yaran sun xabi duk abunda suke so daga nan Suka koma gida sun sake sabon shiri don xuwa birthday. Mr President yayi inviting na vice nashi da wasu yan kalilan Suka xo akayi program sultan ya yanka cake akayi hotuna ga yan jarida daban daban , umaima tayi inviting frenz nata irinsu *Meenat* *Zuby* *khady Mj* *eesha* *teemah* da sauransu su Zuby an turo baki ana selfie😜
Anci an sha sannan aka watse sultan ya samu gifts sosai.haka Suka kasance ckn farin ciki, ranar truout mr President yana tare da yaran nasa har abinci ma tare Suka ci se dare Suka rabu.
Mr President ya kwanta a gadonsa yana jin wani nishadi rabon da ya ji haka har ya manta, shuairat CE ta fado masa a rai tabbas ita CE sanadiyar daidaitawar su lallai baxe manta da ita ba haka ya kasance har bacci yayi awon gaba da shi.


Shuairat CE tare da yaya bash suna komawa gida bayan sun ajiye baba a airport ze tafi mubi Neman auren shukrah.
Shuairat CE ta katse shirun da cewa
" hmmm wa ya ga my yaya ya zama ango"

" xan buge bakinki wllhi kinsan baba baya nan

" yaya shukrah fa wayayyi CE nasan kana mata kallon Ya'r kauye"
" mtswww....wayayyi a ina? Yarinya se kunya yaushe zata zauna ta bani lokaci na

" don't worry zata daina"
" mtsww dallah can karki bata min rai"
Wayarsa CE ta hau ruri ya daga yayi magana na minti 3 sannan yace" gani nan xuwa "
Ya juya yana kallon shuairat yace

" baby kiyi hakuri mr President yana nema na urgent "

" toh yaya ka kaini gida mana first
" no! Kiyi hakuri ki shiga taxi ko kuma mu tafi tare"
Ta xumburaa baki tace

" ni ka ajiyeni xan samu taxi a nan baxan je gidan ba"
Murmushi yayi sannan ya ajiye ta bayan ya samo mata taxi ta wuce gida shi kuma ya kama hanyar villa.

Bayan kankanin lokaci ya iso gidan yayi parking yana Sauri ya wuce ofishin mr President yana xaune ya hada girar sama da ta kasa bash ya gabatar da gaisuwansa ko uffan mr President bai CE masa ba se ya jefa masa wani magazine a gabansa.
Bash ya dau magazine yana dubawa tarihin rayuwar mr President ya gani ..dum! Yaji xuciyarsa ya tsinke dakyar ya daga kai yana jiran umarnin mr President
" ina bukatar ganin yarinyar da take aiki a JF Journals din nan "
"Ok sir!

"Now! Bana son bata lokaci"
" angama sir!
Gumi ne ya fara keto masa shuairat y? Sai da ya hanata rubuta labarin nan but bata jin magana.
Motarsa ya ja yana guduwa tmkr xe tashi sama ckn kankanin lokaci yayi parking a kofar gidansu , shuairat tana kwance dama yau bata je aiki bah ya shigo babu ko sallama ya fisgo hannunta " yaya lfy?
" zaki sani ne ba ruwana ba kince baki jin magana ba"
" me nayi?
" ban hanaki publishing din tarihin rayuwar mr President ba? Na gaya miki ki rubuta Iya abunda ya gaya muku da bakinsa gashi ynxu yazo yaga tarihinsa kaf an baza duniya"
Shuairat tayi shiru ta rasa me zata gaya masa
" sorry yaya"
" bani zani cewa sorry bah muje mr President yana son ganinki saura kice ni na gaya miki"

πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ€—πŸ€—πŸ€—πŸ€—hmmmm ba ruwana nima saura tace *reefat* ce ta gaya min.kuttt wa zai je cell πŸ˜†πŸ˜†
Lolx.....Ku biyoni Lov u all😘😘😘
[2/21, 2:29 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*14*
By *Reefat yahya*


A gaban mr President shuairat CE tare da yayanta se kuma wasu bodyguards su biyu dakin yayi shiru baka jin komi sai bugun xuciyoyin su, mr President ya daga hannu alamar a barsu nan da nan Suka fita ya rage daga shi dai bash da kuma shuairat mr President ya daga hannu ckn rashin fahimta bash yace
" mr President sir! Kana bukatar wani Abu ne?

"Leave us! Ya fada kai tsaye nan bash ya juya ya fita yana mamaki saboda yasan ko ina suna tare da mr President ya akayi yau yafi son ya kadaice da shuairat ? Yana fita sauran bodyguards ma suna kallonsa ckn mamaki don sun San cewa akoda yaushe yana tare da shugabankasa a ko ina.
A hnkli mr President ya karewa shuairat kallo ba tare da ta sani bah don fuskarta na kallon kasa bata San me yake faruwa ba. Ya fara magana da cewa
" who ar u?
Se ynxu ta daga kanta a hnkli dakyar ta fara magana
" sunana Aisha bello"

Sun share minti 10 babu Wanda ya sake cewa komai sannan mr President ya sake cewa
" ina kika samu tarihin rayuwata?

"Ehmm ..ummmm
"Talk to me" ya daka mata tsawa kuka ta fara a hnkli kanta na kallon kasa.ta share minti 5bata CE komai ba, a hnkli ya taka yaxo kusa da ita suna fuskantar juna har ynxu kuka take.hayaniya Suka ji daga waje da karfi aka banko kofa, yan jarida ne suna fada da bodyguards a yayinda yan jarida suke kokarin ganin mr President bodyguards kuwa suna hanasu shiga.
Cak Suka tsaya ganin mr President da shuairat ckn yanayin da suke , bodyguards din kowa ya sunkuyar da kai yan jarida kuwa Suka fara daukan hotuna.ya fito da handkerchief a aljihunsa ya share mata hawaye ba tare da ya furta komai ba sannan ya tashi ya koma kujerarsa ya xauna.
Yaya bash yaje ya umarci shuairat ta tashi ya mayar da ita gida suna tafiya yan jarida sunyi shaa akanta suna tambayar ta me zata fada game da alamarin ko uffan bata CE musu ba dakyar bash ya bude mata hanya Suka fita Suka wuce mota ya ja Suka dau hanyar gida.

Mr President kuwa yana xaune yan jarida Suka sa shi a gaba suna jera masa tambayoyi ko daya bai amsa musu bah, securities Suka zo aka kori yan jaridan dakyar Suka tafi kowa na fadin albarkacin bakinsa.
A mota ma bata daina kukan ba, bash ya juya yana kallonta yace " sisy me ya saki kuka? Wani Abu ya gaya miki?
Kai ta gyada masa alamar a'ah.
"Toh meyasa kike kuka?
"Ba komi"
"Gashi kina kuka still kina cemin ba komai"
" yaya nace maka ba komi koh"

"Ok fine! Amma kinsan kin jawo wa kanki magana koh?
"How?ta tambaya tana kallonsa
"Yes of course, kinsan halinku na reporters dole zasu zargi wani abu musamman idan kikayi laakari da yanayin da aka tarar daku a ciki n kuma yana share miki hawaye a gaban idon jamaa."
Shiru suka yi kowannensu da tunanin da yake yi.tabbas itama tayi mamakin ganin mr President yana share mata hawaye, kodai ya tuna da matarsa ne?

Hmmmm....muje xuwa
Drop yah comments
~dr reefat~ 4u lov u all
😘😘😘😘😘😘😘😘
[2/21, 2:29 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*15*
By *Reefat yahya*

Duk kofofin yada labarai sun hallara a gidan shugabankasa don jin Karin bayani game da labarin hotunan da aka kai musu na mr President tare da matashiyar budurwa kyakkyawa wacce basu San komi game da ita ba.mr president yana xaune a ofishinsa shi da bash ya rike kansa yana tunanin amsar da ze basu game da wannan alamarin, bash ne ya katse masa tunani da cewa
" mr President me zaa gaya musu? Mutanen nan fa sun hanamu sakewa wai dole se sun gana da kai"
Shiru mr President yayi ya rasa me zai gaya masa can ya nitsa yace
" I rily don't know basheer "
" ok sir! Zanje in musu magana ina zuwa"
Ya fito ya tarar da yan jarida daban daban yace musu
" kuyi hakuri mr President yana da aiyuka dayawa a gabansa Ku dawo gobe"
Nan ya juya ya tafi ya barsu suna ta guna gunai ya koma ofishin mr President.
Yana nan xaune inda ya barshi kansa na kallon kasa yayi nisa ckn tunani, wayarsa ya hau ruri bash ya daga yace
" mr President senator Sadik ne akan waya"
Ya karbi wayan ya amsa daga dayan bangare senator yace
" mr President meyake faruwa ina jin wasu irin labarun da ban gane Kansu ba"
Ya sunkuyar da kai tare da kulle idonsa yana jin wani iri ya rasa amsar da zai bayar kawai ya kashe wayar.bash ya juya yana kallonsa ya rasa me yake damun mr President ne?
" are u ok sir?
" am fine basheer tank u"
Daga nan ya mike yace
" zan koma ckn gida ina bukatar Hutu"
Bash ya bi bayansa Suka fita bodyguards Suka Mara masa baya ya koma ckn gida dakinsa ya shige a yayinda bodyguards din Suka tsaya a bakin kofa , ya kwanta a saman gadonsa ko takalma bai cire bah ya shiga duniyar tunani shin ina Aisha bello ( shuairat ) ta samo asalin tarihin rayuwarsa?
Meyasa ya share mata hawaye?
Amsoshin da ya kasa samu kenan. An turo kofar dakinsa da karfi babu ko sallama ya juya don ganin mai shigowar umaima ce fuskarta a murtuke ckn bacin rai ta nuna masa iPad nata ckn mamaki mr President yaga hotonsa da shuairat yana share mata hawaye...
" wacece ita?
Umaima ta tambaya tana bin baban nata da ido, ya rasa me zai gaya mata ?
[2/21, 2:37 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*16*
By *Reefat yahya*


Umaima ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi ta fara magana tana cewa
" dad wato dama sabida yarinyar nan ne yasa ka daina kulamu?
" no...umaima pls ....
"Pls wat dad! Me zaka fada? Wannan shine amanar da mom ta bar maka kenan? Hw many years da rasuwarta har ka fara son wata?

"Pls umaima let me explain "
"Explain wat dad! Baka da abunda xaka gaya min....fuuu ta juya ta bar masa dakin ya rintse ido yana jin wani irin radadi..
Meyasa abubuwa suke faruwa dashi? Ya Allah
Ya xeyi yayi convincing din umaima? Yana ckn tunani aka kwankwasa kofa bash ne ya shigo ya sanar dashi cewa lallai akwai taron gaggawa ana nemansa ynxu ynxu .dole ya tashi ya watsa ruwa yayi sabon shiri sannan Suka fita don xuwa meeting.


Shuairat CE a office nasu ta zauna ta kurawa hoton da ta gani a internet ido, hoton mr President ya sa handkerchief yana goge mata fuska wani haushi da kunya ne ya lullubeta wato shiyasa yau tunda ta shigo ake binta da ido.ynxu shikenan duk duniya anga wannan hoton?
"No!!! "
Ta fada da karfi Sarah CE ta kura mata ido tace "lafiya shuairat?
"Ba komai "
"Ok oga na son ganin ki"
A hnxarce ta tashi ta shiga ofishin mr Muawiya yana zaune tare da Mahmud yana ganinta ya fara murmusawa , bayan ta xauna ya fara magana
" Aisha n Mahmud ina jin dadin aiki daku sosai, so yau ma ina son zan turaku meeting din da Senate Suka kira ina son samun labarin komai dangane da kiran gaggawa da aka wa mr President"
Dum..dum! Gaban shuairat ya fadi ita da mr President again?
"Shuairat dama kina da alaka da mr President ne? Muryar mr Muawiya ne ya katse mata tunani..
"Emm ...emm no! Ni ban sanshi bah"
" Aisha kada ki boyemin komai, hotunanku ake yadawa a koina kuma idan ban manta ba ke kika bamu takaitaccen tarihin rayuwarsa kuma idan nayi laakari da cewa jahar Ku daya dukkanku yan Adamawa ne sai naga kamar kuna da wata alaka mai karfi a tsakaninku"
Gumi ne ya fara keto mata tabbas ta daure kanta da labarin mr President da ta bayar
"Tashi Ku tafi"mr Muawiya ya sake mata magana sannan ta tashi Suka fita ita da Mahmud.
A ckn mota ma babu Wanda yace uffan tsakaninsu shi Mahmud haushinta yake ji sabida ya fada sonta kwatsam se ya ga hoton ta da mr President ynxu ya xaiyi idan mr President ne yake nemanta?
Shuairat kuwa tana tunanin haduwarta da mr President da kuma yan jarida Allah ne kadai yasan tambayoyin da zasu jera mata.
Shin xata amsa tambayoyin ne ko aa? Da ire iren tunanin har Suka kai inda ake meeting din, jamaa a cike makil a harabar wajen ga manya manyan yan jarida ga maaikatan gidajen rediyo da na telbijin da dai sauransu ai kuwa shuairat na fita aka fara nuna ta ana gulma wasu har daukanta hoto suke yi ta gane sarai ana nunata alamar gulmar ta akeyi don haka ckn dabara ta bar wajen ba tare da ta sanarda Mahmud bah.ckn building ta shiga tana dube dube tamkar me Neman wani Abu taxo dab wani lungu xata sa kanta carab aka rike hannunta juyawar da xatayi Suka hada ido da mr President😳😳😳
"Mr pre....
"Shhhhhh! Bai bari ta karasa ya toshe bakinta tare da Jan hannunta da karfi Suka koma da baya...



Hmmmmmmm..

Ku biyoni
~reefat~ Lov u my fans😘😘
[2/21, 2:37 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*17*
By *Reefat yahya*


Sun kurawa juna ido babu ko kiftawa bugun xuciyar shuairat se karuwa yake kasa kasa suka jiyo muryan yan jaridan na tattaunawa dangane da maganan mr President da shuairat daya daga cknsu yace
" dole ya fito ya fadawa duniya me hadinsa da yarinyar domin jamaa sun damemu da sakwanni"
Dayan yace

"Idan bai fito fili ya gaya mana bah tabbas xaa xargeshi da zargi mafi muni kuma hakan xeyi affecting na gwamnatin sa ko ince kujerarsa"

Shuairat ta kurawa mr President ido ynxu ne ta gane dalilin boyeta da yayi da xata hadu da wadannan yan jarida kuma dole su jera mata tambayoyi.
Ynxu me mafita?
Bayan wani Dan lokaci yan jaridan su wuce nan mr President ya sake mata hannu ba tare da yace mata ko uffan bah ya juya da niyyar tafiya tayi saurin cewa

" mr President sir! Me xakayi dangane da wannnan matsalar ?

"Ba damuwar ki bane"
" damuwata CE mr President"
Ya juya a fusace ya hadata da bango sun kurawa juna ido ya fara magana a hnkli

"Who d hell u tink u are da zaki dinga shiga affairs dina?
"Am nobody! Ta bashi amsa kai tsaye

"Mind ur own business den, ki fita sabgata "
Wal wal hasken camera CE ya haska su gaba daya Suka juya wasu yan jarida ne su biyu suna daukansu hoto ....

"Oh no! Mr President ya furta tare da sake Jan hannun shuairat Suka shiga ta wata kofar da be San ina xasu je bah.duk inda ya leka akwai jamaa ya rasa ya xaiyi nan ya sake mata hannu yana maida numfashi yace

"Look Ayshah! Ki nemi hnyar da xaki bi ki fita ba tare da kin saurari kofofin yada labarai dinnan kinji? Xan nemeki gobe plss "
Ya fada ckn rashin kuxari , bash ne ya karaso yana faman haki da alama ya gaji dayawa

"Mr president Wia have u bin tun dazu ina Neman ...bai karasa ba saboda ganin shuairat da yayi a gefe don da farko bai ganta ba mamaki ne zalla a fuskarsa yana binta da wani irin kallon tuhuma.
Mr President ne yayi gyaran murya ckn tsarguwa yace

"Ehmm ...bash pls help her n c her out"
Yana gama fadin haka ya juya ya kama hanyar xuwa dakin taron nasu.
Sun kai minti 5 babu Wanda yayi magana

"Wat is going on here little sis" yana mata kallon tuhuma

"Uhmmm...is just...
"Wait baby! Don't tell me dat abunda jamaa ke fada da gaske ne"
ta daga kanta Suka hada ido
" wat do u min?
"Wat Eva dai ,yau ne karo na biyu pls baby kada ya cika uku mind ur way he is not ur type"

"Me kake nufi yaya?
Bai CE mata komi ba ya fara tafiya ta juya tabi bayansa suna tfy suna labewa dakyar ta samu ta fito ta shiga ckn jamaa ba tare da an gane ta bah.Mahmud ta hango yana nan inda ta barshi
"Mahmud!
"Allah na shuairat ina kika shiga inata nemanki"
Hannu ya mikawa bash Suka gaisa bash yace " ka kula da ita pls"

Daga nan bash ya koma ciki su kuwa Suka wuce mota.a kan hanyarsu ta komawa kowanne yayi shiru da tunani fal a zukatansu

"Shuairat soyayya kukeyi da mr President? Ya jefa mata tambayar da bata San amsar da xata bayar bah

"Ki ban amsa pls"
"Ba abunda ya hadamu Mahmud"
"Hmmm...gara ki fito fili ki bayyanawa jamaa akan batun soyayyarku if not darajarsa da taki zasu xube"

"Kamar yaya darajarmu xata xube?

"Of course! Yau ankira shi meeting baice komi bah dangane da maganar, ynxu mutane sun fara cewa idan har baiyi magana ba dat mins ke farkarsa CE"

"Waat? Farka? Innalillahi wato abinda yaya bash yake nufi kenan da yace mata kada ta bari ya cika uku?

"Shuairat gaskiya xan gaya miki maganan ya girma fiye da ynda kike sammani domin ance zaa Iya sauke mr President akan kujerarsa idan har an tabbatar da zargin da ake yi da gaske ne, don haka gara ki fito ki dayawa duniya gaskiyar alamarin"

"Me kake nufi da gaskiyar alamari Mahmud? Kasan ni ba mazinaciya bace"

"Nasani but jamaan gari fah? Kiyi tunani akai shuairat"
Ya sauketa a gida yayi tafiyarsa ckn bacin rai, shuairat kuwa tunanin maganganun Mahmud take tana Neman mafita.

Hmmmmmm......akwai ~work~
Muje xuwa
Taku a kullum *Reefat*😘😘😘
[2/21, 2:37 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*18*
By *Reefat yahya*


Mr President ya koma gida a gajiye yake likis ga ciwon kai sabida hayaniyar da sukayi da jamaa a meeting nasu ya cire babbar rigarsa ya xauna a kan gado ya buga wani uban tagumi.
Umaima CE ta shigo tare da sallama ckn sanyin jiki ta xauna kusa da mahaifin nata ta sunkuyar da kai hawaye ne ya fara sauka
"Dad don Allah ka rabu da yarinyar nan kana sauke girma da darjarka too much"
Ta nuna masa sababbin hotunan da aka tura yau , kunya ne ya kama shi don ganin yanayin hotunan sun kurawa juna ido shi da shuairat umaima CE ta katse masa tunani

"Dad pls promise me"
"Don't worry my baby babu abunda yake tsakaninmu kinji? Ki kwantar da hankalinki hakan bazata sake faruwa bah"

"Promise?
"Yes promise" wani murmushn dadi tayi daga nan Suka fara hira sannan ta koma bangarenta ckn wani irin farin ciki.
A hanya Suka hadu da bash yana waya bai lura da ita ba sauran kadan suyi karo ta ja gefe ta bashi hanya ya juya kenan Suka hada ido ya kashe wayar ya sunkuyar da kai alamar girmamawa
Murmushi ta sakar masa tace
"Dama ina son magana da kai"
Mamaki ne a fuskarsa sabida yasanta da shegen girman kai ta gane hakan tace
"Kana mamaki koh? Don't wory wasu yan tMbayoyi ne zan maka"
Nan Suka zauna bayan ta bashi ixinin xama a harabar gidan ne akan wasu kujeru kyawawa.

"Na dade ina ganinka tare da mahaifina kuma nasan kai kana daya daga ckn mutanen da Suka fi kusa da mahaifina, don haka nake son sanin wani Abu dangane dashi da wannan yarinyar"

"Ranki ya dade ni bansan komi game da maganar ba , kawai nasan babu soyayya a tsakaninsu kuma babu wata alaka mai karfi a tsakaninsu"

"Toh kana nufin mahaifina yana bin matan banxa kenan?
"Subhanallah! Ya daga idonsa Suka fada ckn nata

"Yes! Idan babu soyayya ko wata alaka a tsakaninsu toh me hadinsu?
Ran bash ya baci sosai yace
"Ita wannan yarinyar ba karuwa bace"

"Who knows" umaima ta fada ckn kwanciyar hnkli idanun bash sun canza xuwa ja yace

"Kina xargin mahaifinki da aikata xina?

"Ya zanyi? Duk laifinsa ne shi ya jawowa kansa ana ta zaginsa a gari"nan ta fashe da kuka me ban tausayi tabbas abun akwai daure kai ynxu haka ake zargin Ya'r uwarsa? Kai baxai yiwu bah dole ya dau mataki.
A hnkli ya fara rarrashin umaima tmkar yace ta kara, bash dama yana da tausayi nan ya fara bata baki bayan ya cire handkerchief ya mika mata ta karba a hnkli tana share hawayen se kuma ta tuna hoton dad nata yana sharewa wata hawaye nan ta sake fashewa da sabon kuka.
Bash yayi shiru yana kallonta ya rasa me zai gaya mata
"Sorry pls is ok ki daina kuka ni na tsani ganin hawayen mace pls"
ta share hawayrn a hnkli ta daga kanta tana kallonsa shi ita yake kallo
"Tnk u"
"U ar welcom"
Ya fada yana murmushi sunyi shiru can ta tashi tace
"Zan koma ciki but pls ina bukatar num wayarka"
Babu gardama ya rubuta mata tana murmushi ta daga masa hannu sannan ta koma ckn gida shi kuwa yana mamakin chanjin halin nata.

Bash ya koma gida ya sami labarin cewa baba na nemansa a chan mubi saboda sa ranan aurensa don haka ya nemi ixini daga wajen aikinsa.
Shuairat tana kwance a falo tayi nisa ckn tunani wayarta ya hau ruri shukrah CE

"Kawata ya akayi"
"Uhmm...gani nan dai
"Baba yaxo Neman aure fah...

"Auren wa? Shuairat ta fada tana dariya
"Munafuka dama nasan kin San xe xo amma baki taba gaya min bah"

"Ya ake ciki "
"Oho! Nima bansani bah
"Gulma koh! Ana so ana kaiwa kasuwa kinsan yaya na mai tsada ne yarinya

"Kya ji dashi munafuka
"Ehh din, nasan ana son yaya na dai ana wani nokewa xamu gani ai"
Haka Suka cigaba da hira har na tsawon wani lokaci.
Bash yana kwance a falonsa ya kurawa wayarsa ido lambar shukrah CE kullum yana son kiranta Amma ya kasa, ga kwanakin se matsowa yake amma har yau be taba kiranta bah yau dai yayi ta maza ya danna kira yayi ringing har ya kusan katsewa sannan ta daga ckn wani irin murya mai dadin sauraro tayi sallama ya amsa se kuma yayi shiru

"Hello! Wa ke magana don Allah

"Yayanki ne
"Eyya..wanne daga cki
"Yaya bash
Nan taji wani irin kunya ta rufe ido tmkar yana ganinta dakyar tace

" ina yini yaya
"Lfy ya kike ya gida"
"Lfy alhamdulillh ya su mama"
"Lfynsu lau"
Nan

Please Login or Register in order to submit comment