Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mama da baba sai shirin bikin suke shuairat kam ko a jikinta kawai ta dinka anko nasu na kawayen amarya kuma ita ta zabi kalar kujerun da xaa xuba a falon amarya, suma sun canza nasu kujerun an sake wa gidan sabon fenti yayi kyau sosai ynxu kam se shirin xuwa mubi don gabatar da bikin.
Tana kwance a daki tana karanta novel din "behind our Lov" na miemie bee๐Ÿ˜˜
Novel din ya burgeta sosai hnklinta ya tafi ga karatun dama a watsap ne aka tura a grp din *gidan gyara*๐Ÿ˜Šteemah ashaka CE ta tura musu...wayarta ya fara ringing bakuwar lamba CE ta ja tsaki ckn jin haushin katse ta aka yi

"Hello! Ta amsa kamar bata so

"First lady ina son ganinki ynxu"
Yana fadin haka ya katse wayar toh waye shi? Oh mr President kenan? Tasan dai shi kadai yake kiranta da wannan sunan toh a ina ya samu num ta ? Hmmm shine wai ina son ganinki ynxu wato ma har wani gadara yake mata...mtsswww se shegen girman kai ๐Ÿ˜
Bata motsa ba ta cigaba da karatunta ckn kwanciyar hnkli kofar dakinta aka bude bash ne ya shigo tare da sallama tayi banxa dashi tmkar bata San ya shigo bah

"Baby magana xamuyi but muje mr President na son ganinki first "

"Bani da lokacin magana da kowa"

"Look am serious about it pls" ya fada yana kallonta ta daga kai Suka hada ido tayi saurin dauke kanta nan kuwa ta soma kuka a hnkli, ya taka ya xo kusa da ita ya jawota jikinsa ya fara magana a hnkli

"Am sorry pls nasan nayi laifi baby kiyi hakuri kin ji koh my baby"
Ta cigaba da kukan da take Mara sauti

"Sorry yaya bai kyauta miki bah but am sorry now plss....
Ta tura baki ckn shagwaba tace

"Ba kaine bah wai kana fushi dani baka tsaya ka saurari me xan gaya maka bah

"Naji is ok now ynxu nagane ba laifinki bane sorry koh

"Uhmm"
"Toh tashi ki shirya idan mun dawo sai muyi maganar koh"
Haka dai ya lallabata sannan ya koma falo yana jiran fitowarta.

Wani dankareren lace ta saka green da touches din wyt n golden ta saka yan kunne cika wuya golden masu uban kyau ta fesa turare masha Allah tayi kyau sosai.
A gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta ba karya ta hadu Iya haduwa..ynxu kwalliyan nan tayi shi ne don mr President?
No! ta bawa kanta amsa kawai tayishi ne don kar a Reina ta kuma a matsayinta na budurwar mr President she have to look unique always.light make up tayi a gurguje sannan ta fito falo yayanta ya sakan mata murmushi yace

"Wow! My sisy is looking cute"
"Tnx" ta fada daga nan Suka dau hanya ...


๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜tnx 4ur support my fans Lov u all
*Reefat ce*
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*25*
By *Reefat yahya*


Mr President yana xaune a filin hutawarsa yayi shiru daga gani yayi nisa ckn tunani ta karasa tare da sallama baima San ta iso bah xama tayi a gefensa qamshin turarenta ne yasa ya juya don ganin ko wayene ido ya kura mata babu ko keftawa
Wani kunya ne ya lullubeta ta sunkuyar da kai dakyar ya saita kansa sannan yayi gyaran murya ya fara magana

" first lady ko xan Iya sanin dalilin da yasa kikayi wannan kwalliyar kodai kin kamu da son tsohon neh๐Ÿ˜‰"
Ya fada yana kallonta ta daga idonta Suka fada ckn nasa lallai mutumin nan

"Ko kadan Aisha bello bazata auri tsoho ba kuma tana da saurayi mai sabon jini me xatayi da tsoho ?
Yayi murmushn yake yace

" wa ya sani Abu a hudu kuma waya San inda rana xata fado"

" mr President kenan ai kowa yasan cewa a yaMma rana take faduwa "

" shikenan...ynxu na nemeki ne saboda kisan halin da ake ciki
Kin rabani da ya'ta ynxu haka tana fushi dani kuma kin hadani da iyayena kinsa mahaifina yace lallai xai xo nema min aurenki "

๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณta xare ido ckn tsananin firgita shima kallonta yake

"Yes! First lady, kina tsammanin cewa maganan xe wuce haka kawai ne? Dama saida na gaya miki kin tafka kuskure gashi ynxu outcome din kenan, kuma duk duniya an baza kunne ana jiran ranar aurena da ke"

Me shuairat xatayi in ba kuka ba๐Ÿ˜†๐Ÿ˜†๐Ÿ˜† mr President yayi shiru yana kallonta tun tanayi a hnkli har ta fara da karfi wani security ne ya leka don jin muryar ta yana son ganin ko lfy daga ganin mr President a gefe yayi saurin komawa bakin aikinsa.
Mr President ya tashi ya koma kusa da ita har suna jin hushin juna.

Ya kai hannu xe share mata kwallan da ya bata mata fuska tayi saurin kawar da fuskan gefe yana murmushi yace

"Toh ai laifinki ne my first lady, kefa kika fito kika gayawa duniya cewa mun Dade muna soyayya koh?
Harara ta galla masa tace

"Kai de kace kaga Ya'r budurwa kana so shine ka gayawa dad naka amma ka daina labewa da wani magana daban"
Dariya sosai ta basa yace

"So? Toh ai ni bansan wannan Kalmar bah kuma ban taba yinsa ba a rayuwata , xancen aure kuwa tunda na rasa matata ban taba tunanin sako auro wata bah don haka ki kwantar da hnklinki ni bansan wani Abu wai shi so bah"
Tana kallonsa ckn mamaki sannan tace

"Y not ka gayawa dad naka gaskian lamarin"

"Ban taba masa gardama kuma baxan fara a kanki bah amma idan xaki Iya fuskantarsa ki gaya masa da zan fi kowa jin dadin hakan"

"Me xan gaya masa?
"Oho!duk abunda kike so"
Sunyi shiru kowanne da tunanin da yake can ya daga kai yace

"Kije kiyi tunani a kai ko ki fito ki fadi gaskiya ko kuma ki yarda da auren kaddara da xai fado kanki nan ba da jimawa bah"

Yana kawo nan a xancensa ya tashi ya tsaya ya mata wani irin kallon da ta kasa gane maanar sannan ya koma ckn gida ya barta tana xaune ta shiga duniyar tunani...
Me abin yi????????

Hmmmm muje xuwa dai,
Lov u all๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*26*
By *Reefat yahya*


Bash ne ya katse mata tunani
"Sis ya naganki haka?
Kuka ta fashe masa ya jawota jikinsa
"C'mon let's go home ki share hawayenki pls ga securities suna ganinmu tashi mu tafi "
Nan ya Suka tashi bayan ya share mata hawaye tana gaba yana biye da ita a baya Suka fada mota ta tadata Suka hau hanya, bayan sunyi tafiya mai nisa yayi parking a gefen titi

"Now tell me me yasa kike kuka?
Nan ta kwace labarin komi tun daga farkon haduwarta da mr President har xuwa hirarsu na karshe ta shaida masa yayi shiru yana naxarin maganganun can ya nitsa yace

"Sisy kinyi Abu mai kyau da kika kare mutuncinki da na mr President but ynxu problem din shine mahaifinsa..dama iyayensa sun jima suna mishi maganan aure baya sauraransu kinga ynxu dole hnklinsu ya kwanta n 2b frank I tink mr President likes u a lot cos tunda nake dashi ban taba ganin ya xauna yana hira da wani har da dariya ba sai ke, idan kinga yana magana da wani dai toh bai wuce maganar siyasa ba se kuma yaransa su kadai yake sakewa fuska"

"And so wat yaya! Kana nufin na auri tsoho kenan?

"Baby ina son ki gane cewa aure mukaddari ne daga ubangiji kuma matar mutum kabarinsa n mr President mtumin kirki ne bashi da matsala ta kowane bangare, kuma idan kika amince da auren nan tmkar jihadi ne don kin rufawa musulmi Dan uwanki asiri.idan har baki auresa ba xaa fara jita jita kuma xai xama wata magana mai girma"

"But yaya...
"Baby kiyi adua Allah ya xaba miki mafi alheri kawai daz final kuka da duk wani bacin rai ba naki bane"

Daga nan ya tada mota Suka koma gida.
Bash yana kwance a dakinsa yana lissafin yadda aurensa xe kasance wayarsa CE ta fara ringing umaima ya gani akan screen yana murmushi ya daga
" hey best friend ina ka shiga ne?
"Friend ina nan aikine ya min yawa"

"Kullum aiki baka hutawa ne?
Murmushi yayi yace

"Hutu ai se manya irinku"

"Hmmm.xolaya koh"

"No! Daz d fact"

"Naji toh yaushe xaka xo mu fita "

"Yaushe kike so?
"Ko ynxu ma am ready"

"Kiyi hakuri xuwa gobe kinji my dear"
Ta lumshe ido tana jin wani farin ciki tace

"Shikenan ina jira Allah ya kaimu"

"Ameen bye"
Tare Suka ajiye waya umaima ta rungumi tabbas ta fada tarkon son bash Allah ne kadai yasan adadin son da take masa๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณhmmmm...umaima kin shiga tarko amma kash!!! Ance rashin sani yafi dare duhu bata San cewa saura kiris๐Ÿ‘Œ๐Ÿขash ya angwance bah



***********
Mr President kuwa yana xaune a falonsa yana tunanin hnyar da xaibi ya sasanta da umaima yrinyar Sam taki bashi fuska bash ne ya fado masa a rai tabbas shi kadai zai Iya shawo kan matsalan.
se kuma shuairat ta fado masa a rai yana murmushi shi kadai yarinyar akwai shagwaba kam maybe ita kadai iyayenta Suka Haifa da alama dai Ya'r gata CE ko su waye iyayen nata oho!

Se ynxu ya tuna baima San gidan nasu bah, idan dady yaxo yace su je tare fah?
Lallai dole ya nemo gidansu Amma wannan duk aikin bash ne..ya zaiyi da umaima bayan ya auri shuairat ? Ya zaman nasu xe kasance?
Shuairat xata amince da auren ne ko aa?
Idan tace aa'a me zai gayawa dadynsa ? Me mutane xasu dauke shi?



Ku biyoni don jin amsar tambayoyin๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
~reefat~
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*27*
By *Reefat yahya*


Mr President yana xaune a ofishinsa bayan sun gama ganawa da vice dinsa akwai xasuyi tafiya xuwa China don kula da harkar kasuwanci tsakanin najeriya da china .
Bash ne ya shigo masa da wasu files ya ajiye xe fita
" a moment pls"
Bash ya juya ya dawo a tsaya a gabansa mr President ya nuna masa kujera ya xauna wato alamarin da ya bashi mamaki kenan saboda tunda suke mr President bai taba masa hakan bah.

"Basheer wani taimako nake so ka min"

"Ina jinka mr President"
"Wato lura kusancinka da yata yayi karfi har nake ganin cewa xata Iya aikata duk abunda ka umarceta, basheer ina so ka bawa yata hakuri akan maganata da Aysha bello pls"

"Don't worry mr President xan mata magana insha Allah "

"Nagode" bash ya tashi har ya kai bakin kofa mr President yace

"N I want to know about Aysha bello"

"Ok sir! Ya bashi amsa sannan yasa kai fice.

A falonsu ya sameta da masu aiki suna mata gyaran farce tana waya, ya shigo tare da sallama
Fuskarta ne ya fadada da murmushi nan kuwa ta kashe wayar

"Aboki se yau"
"Yes my kawa" ya maida mata martani sannan ya samu kujera da yake kallon nata ya xauna nan ta sallami masu aikin bayan ta umarcesu da su kawo kayan motsa baki.

"Ya'r gatan dad ya kike"

"Lfy ya aiki"
"Alhamdulillh ya hutawa"

"Ya kadaici dai koh"
Sun Dan taba hira bash yace

"Kawa me yake damun dad naki ne kwanan nan duka naga yana ramewa"

"Oho! Maybe ya bata da budurwarsa"

"No! It can't b ki dai bincika ki gano matsalar he is ur dad after all"
Tayi shiru tana naxarin maganganun nasa kenan dad dinsu ya rame saboda tana fushi da shi? Dama haka ya damu da ita? Lallai bata kyauta masa bah, kamar yadda take fama da kadaici shima hakan yake fama amma meyasa tayi haka?
Hawayene Suka gangaro a fuskarta nan ta sunkuyar da kai kasa ta fara magana

"Laifina ne na daina kulashi ya bani hakuri har ya gaji ban saurareshi bah"
Nan kuwa ta fara kuka tamkar ranta xe fita

"Me kika masa umaima?

"Akan maganar wannan yarinyar "

"Haba umaima a ina kika taba jin anyi fushi da iyaye? Shin baki ganin irin biyayyar da dad dinku yake nunawa iyayensa ne? Meyasa baxakiyi koyi da halayensa ba?
Ta cigaba da kukanta ba kakkautawa bash kuma ya cigaba da magana

"Tabbas kinyi kuskure Amma is not late kije gun mahaifinki ki nemi gafararsa idan har baki son fadawa ga halaka ". Nan ya kwace labarin komi dangane da alakar shuairat da mr President ya gaya mata cki kuwa har batun aurensu jikinta ya mutu sosai ynxu ne ta gane cewa dad bashi da laifi ko kadan.
Bash ya mata nasiha me ratsa jiki sannan ya tashi ya tafi.

Mr President yana xaune ya buga uban tagumi a hnkli aka tura kofar umaima CE ta shigo tamkar barauniya.sum sum ta karasa kusa dashi

"Dad....
Se kuma hawaye sun taru a idanunta .
Hannu ya bude mata ta fada jikinsa tana kuka yana rarrashinta dakyar ta daina kuka tace

"Dad am sorry ka yafe min sharrin shaidan ne"

"Is ok baby, idan har kin fahimceni dai shikenan "

"Dad I understand ba laifinka bane kuma itama taimakonka tayi "

"Am happy dat u know ynxu me kuke bukata cos gobe ko jibi xan tafi China"

"Bana bukatar komi dad Allah ya tsare ka ya dawo da kai lfy"

"Ameen my baby"
Haka Suka kasance suna hira ckn farin ciki da jin dadi ya kalli fuskarta yace

"Baby kodai an samo min suruki ne"

"Laa...dad babu fah"

"Are u sure? Wat of basheer?

"Dad! Ta fada tana dariya bash da yake bakin kofa yayi murmushi sannan ya juya ya bar wajen.



๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜to u my fans
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*28*
By *Reefat yahya*


Karfe 5dai dai bash yayi parking a kofar gidansu na mubi yaran anguwan ne Suka tayasu shigar da kaya ckn gida.
Mama da baba Suka fito ana musu maraba da xuwa tuni shuairat kuwa ta kama hanyar gidan mutuniyar tata ckn xumudi ta shigo tare da sallama.
Inna tana tankade gari shukrah kuwa tana shara aikuwa sun kankame juna ckn jin dadi bayan sun gaisa da inna dakin shukrah Suka shige tare da sauke labule
( ni kuma nace baxaa barni a baya bah ..lolx)
" kai bestie kin ga hasken da kikayi kuwa? Se shining kawai kike yi"

"Ya'r rainin wayo na kaiki ne, ke amarya ce fah ansha gyaran jiki ana ta shinning"
" ya gida ya hanya ya su mama"
"Lfynsu lau ya shirye2"
Shukrah ta harareta ckn tsigar wasa tace
"Wane shirye shirye"
"Oh! Wa yaga su bestie amarya"
"Kya ji dashi ya'r nema"
"Oho dai! Ana so ana kaiwa kasuwa , yawwa baki ban labarin haduwarku da yaya bah kince masa I love u ko ya?

" munafuka ai shuairat kina fama wallhi"
"Lolx muna fama dai"
Haka Suka kasance suna hirar yaushe gamo shukrah ta kawo mata dambun xogale ta ci tayi hamdala har magarib sannan ta tashi ta kama hNyar gida shukrah tana mata rakiya shuairat ta juya ta kalleta tana murmushi tace

"Anti shukrah ki koma se munxo xance to nyt" shukrah ta kai mata duka suna dariya Suka rabu.

Hakan ko akayi bayan sallar isha bash ya shirya ckn kananan kaya se qamshin turare ke tashi a jikinsa yayi sallama ya tafi shuairat ta yi masa tsiya har ta gaji yana dariya ya tafi.
Bayan kwana biyu aka kai lefe jamaa na ta yabawa nan aka fara shirye2n biki ba kama hannun yaro su shuairat kirjin biki itace kan gaba a kowane bangare. babbar kawa kuma kanwar ango, sun shirya xasuyi kauyawa day da walima se kuma kamu night"


**********
A can birnin tarayya kuwa mr President ya tafi China don gudanar da harkokinsa
Umaima kuwa gidan ya mata fadi gashi ta nemi layin bash baya shiga kuma ta tambaya ance mata yayi tafiya sultan ne abokin hirarta se kuma watsap da Facebook, gashi makarantar su ana hutu .
Tana kwance a falonsu yau taji shaawar shiga watsap dinta ta bude kenan mssgs Suka fara shigowa anyi adding dinta a wani grp din *Gidan gyara* mata ne xalla a GRP din, batasan wacece admin din bah kawai ta ynke shawarar yin magana a grp din ta rubuta "salam" ta tura bayan minti2 Meenat da esha Suka amsa mata๐Ÿ˜Š "wslm"
"Pls wacece tayi adding dina a wannan grp din? Bayan wani Dan lokaci mssg ya shigo from *Reefat* tace "nice nayi add din ki" Mmn Ummul ta tura novel din *tana tare da ni"* kamar da wasa umaima ta fara karanta novel din se kuma taji grp din ya burge tah anata hira a grp din so lively haka, tun tana sharewa har ta fara contributing ta Dan saba da yan grp din har magariba tayi sannan kowacce ta tashi don yin sallah.

Bayan umaima ta idar da sallah ta sake daukan phn din ta shiga grp taga anyi posting din wasu pre-wedin pix kala2 batayi download bah ta cigaba da karanta novel din *yar Riko* da aka tura, chan an sake tura wasu pix din se a kasan aka rubuta

"Matan gidan nan u r invited auren yaya nah gobe kamu night"
Cmnts aka fara aikowa
"Wow couples din sunyi kyau"
Su Rabi Oga da su momi Ummi da zaheeda da sauransu duk sunce xasu je auren.
Haka nan umaima taji tana shaawar bude hotunAn tayi download daya yana buduwa
๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ dam....dam....xuciyarta ta buga guess wat?
Hoton shukrah CE da basheer sunyi kyau sosai nan take wani jiri ya fara diban umaima
๐Ÿ˜ณtoh fah....hmmmm"
Wani xaxxabi ne ya rufeta haka ta kwanta akan sallaya idanunta na fitar da wasu xaxxafan hawaye

๐Ÿ˜ฅ๐Ÿ˜ฅeyya umaima nah...

Lols Ku biyoni

*Reefat*ce๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*29*
By *Reefat yahya*


Karfe 7 katon multipurpose hall din Adamawa state university mubi, ta cika makil da jamaa ga yan mata samari manyan mata da dai sauransu can na hango amarya tare da kawayenta dai Kelli suke ansha kyau.
Decoration din hall din ma abin kallo ne anyi decorating da purple n silver se fulawas masu kyau abun dai se Wanda ya gani.
Kawayen amarya na sanye da purple head da material ash colour n silver wyl amarya kuwa ta saka purple material da silver n ash colour head tie sunyi kyau sosai an fara program sannN ango ya shigo da tawagarsa ckn fararen kaya masu kyau sai shinning suke.
Anfara gabatar da taro su shuairat anyi rawa har an gaJi ga abinci da drinks kala kala anci ansha an xuba kudi kamar ba gobe su Rabi Oga tun daga Jada aka tashi aka je auren๐Ÿ˜œ ga su nan dai matan gidan gyara birjik anyi ta kashe pix xaa canza dp.nima dakyar nasamu nayi pix 2 da amarya da kuma shuairat...
Bayan angama taro aka watse kowa ya kama hanyar gida.


A can Abj kuwa umaima aka kwantar a asibiti in banda kuka ba abunda take a waya aka hadata da mr President tmbayar duniyan nan ya mata Amma Sam tace xaxxabi ne ke damunta...( Kutt...Ashe dama she is in love wit yaya bash eyya poor umaima๐Ÿ˜ฅ๐Ÿ˜ฅ....lolx๐Ÿ˜œ)
Bayan an bata magunguna aka sallameta Suka koma gida tare da masu kula da lfyarta, yan uwan mamanta se kira sukeyi suna mata sannu haka nan iyayen mr President ma sun kirata sun gaishe ta.

****โ€ 

D next day da yamma su shuairat Suka hada walima na mata xalla anyi nasiha sosai akan hakkin aure shukrah ko har kuka se da tayi shuairat na tsokanRta
BayN wani lokaci Suka raba Qur'an da handfan da kuma memo daga nan aka raba abinci sannan akayi adua aka watse.

Ran jumaa aka daura auren shukrah Abubakar da Basheer Bello maiha daurin auren ya samu jamaa sosai.da dare aka kai amarya gidan mijinta.
D next day akayi fansar amarya da ango sannan da dare aka sallami kawaye shikenan jamaa kowa ya watse.

Shuairat CE tare da aminiyar tata tana bata yan shawarwari ynda xata xauna da mijin nata bash ne ya shigo tare da sallama shuairat CE ta amsa ya kalleta yace

"Ke me kike jira baki tafi gida bah"

"Ho...yaya korata xakayi yau"

"Ehh mana ba dole bah
"Hmmm...lallai gashi nikuma se nayi 1week kafin....

"1me? Tabdi ba dai a nan gidan bah, idan kinji haushi kema ki shirya a daura muku ke da wancan tsohon"

"Yaya....tsoho fa kace! Se na gaya masa kuwa"
Yana dariya yace
"Yi hakri ur Excellency kada a dakatar da salary nah na 1month"
Haka dai Suka cigaba da tadinsu ckn xolayar juna shukrah de bata sa musu baki bah daga karshe shuairat ta musu sallama Yayan nata ya ajiyeta a gida shukrah kuwa se hawaye take ๐Ÿ˜ni Reefat nace ki gama kukan munafurcin ki bada kai bori ya hau


Ku biyoni ku sha labari๐Ÿ˜œ

*Reefat* CE .....love u alll๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
Hop kuna manage da hausar tawa๐Ÿ˜œ
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*30*
By *Reefat yahya*


Bayan sati daya da auren shukrah da bash Suka dugunxuma xuwa Abj shukrah tayi kukan rabuwa da iyaye da yan uwanta sosai.
Baba da mama flight Suka bi sannan bash shukrah da shuairat kuwa Suka bi hanyar mota.

Da yamma Suka iso garin shukrah ma tana kalle-kalle har Suka shiga gidan nasu bangaren yaya bash ta wuce sannan shuairat kuwa ta shige bangarensu.bayan sunyi wanka sun huta shukrah ta share bangaren tas ko'ina se Kelli yake ta kunna turaren wuta nan take qamshin ya gauraye gidan bash kuwa yana sauke baccin gajiya , shuairat CE ta shigo musu da abinci tare Suka ci nasu bayan ta ajiyewa bash nasa.

Bayan sallar magrib gaba daya Suka hallara a falonsu mama ana hira har da shukrah ta sake sosai a gidan bata daukesu a matsayin surukai ba, wayar bash ne ya fara ringing "umaima ! Ya gani a rubuce kwata2 ya manta da ita se kuma yaga be kyauta ba saboda be taba kiranta bah kuma bai gaya mata xaiyi aure bah.
Yayi picking tare da sallama ckn sanyin muryarta ta amsa tare da cewa
"Ina son ganinka yanxu"
Tana gama fadin haka ta kashe wayar.ya kurawa wayar ido sannan ya tashi yace
"Baba ana nema na a gidan mr President "
A dawo lfy Suka CE masa daga nan ya fice



Tana xaune a falonta ita kadai sultan yayi bacci ta shigar dashi daki tana xaune ta buga uban tagumi ya shigo tare da sallama sanye yake ckn kananan kaya yana ta qamshi se shinning yake, suna hada ido ta fashe da kuka ai kuwa ya rikice ya xo kusa da ita ya xauna ya marairaice yace
"Umaima am sorry nasan ban kyauta bah na tafi ba tare da sallama ba"
Ta daga idanunta suna kallon juna se kuma ta sake sunkuyar da kai ta cigaba da kukanta har ckn ransa yana jin kukan Amma ya xaiyi? Ya lallabata amma taki dainawa.

"Umaima I said soryy naa kiyi hkri pls bana son jin kukan nan naki don Allah"
"Bash! Farkon haduwarmu da kai u promised dat xaka kula dani xaka xame min kadangar da xan jingina a kai ashe ba haka bane?
Bash har xaka iya aure baxaka sanar dani ba?
Damm...gabansa ya fadi, toh ya akayi tasan yayi aure?

"Kana mamakin ya akayi na sami labarin aurenka koh? Ba abin mamaki bane amma gskiya banji dadin hakan bah

"Am sorry umaima"

"Sorry 4wat? Sorry dat kayi aure ko sorry dat ka tafi baka sanar dani bah? O sory dat ka kasa cika alkawarin da ka dauka?

Carab! Suka hada ido, hawaye na diga tace

"Y basheer? U knw dat I kia a lot meyasa zaka min haka? But....

Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasar da maganan da take a hnkli ya jawota jikinsa๐Ÿ˜ณ๐Ÿ™Š.....
Gam ta kamkameshi tana kuka me ban tausayi.
Dakyar ya rarrasheta ta sagaita kukan

"Kiyi hakuri umaima auren ya xomin unexpected ne iyaye na Suka hadani da yarinyar wllhi ba wai...
Se kuma yayi shiru toh wai meyasa yake kokarin kare kansa ne?.

Shiru sukayi na Dan wani lokaci a hnkli ya daga kansa ga mamakinsa umaima har ta fara bacci haka Suka xauna har sunkai 1hr a xaune sannan ya xame jikinsa a hnkli ya kwantar da ita a saman kujerar 3str sannan ya fita ya shige motarsa ya kama hanyar gida.
A hanya ma yana tuki yana tuna kalaman umaima da kuma halin da ta shiga toh meya bata mata rai? Kuma yaga alamar damuwa a tattare da ita ko meyake damunta ne
Oho! Nima nace oho!


๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜lov u alll
[2/21, 2:38 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*31*
By *Reefat yahya*


Shukrah ta gama shirin kwanciyarta ta hau gado ta kwanta bash ne ya shigo dakin tare da sallama ta amsa cki-cki a dole fushi take ya karasa kan gadon inda take kwance yana murmushi yace
" my wife fushi kike dani"

Ko uffan bata CE masa ta kirkiro wani guntun murmushi

"Am sorry kiyi hakuri "
"Uhmm..ba komai"

"Sure"
"Uhmm"

"Toh ki danyi murmushi mana"
Hakan kuwa ta sake masa murmushi yana dariya yace

"Daz my wife, tashi mu ci abinci toh"

"Na koshi"
"Pls mana " ya marairece hmmm bash akwai

Please Login or Register in order to submit comment