Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taku biyu tayi ta karasa inda yake

"Mahmud ina son yin magana da kai"

"Sorry am busy"

"I knw but maganar is very important"
Ba gardama ya tashi Suka fita waje

"Mahmud wane laifi nayi to deserve dis?

"Bangane bah ! Wani Abu ne ya faru?

"Mahmud pls ka gaya min me namaka plss...

"Shuairat baki min komai bah"yana gama fadin haka ya juya ya koma ciki ya barta nan tsaye tsaki taja ckn jin haushin kanta wato ma har wani rigima yake mata mtswww...
Nan ta tare taxi ta kama hanyar gida.

Mama CE zaune a dakinta tayi shiru tana tunannin kalaman aminiyarta Hajiya mairo
"Amina ki godewa Allah da irin kyautar da ya baki ki kwantar da hankalinki , ai wannan shine arxiki na binka kana gudunsa idan ba haka ba waye xaiki amincewa da auren shugabankasa? Kawai ki nusar da shuairat ki gyarata sosai ki koya mata dabarun xama da miji ba wani batun ya tsufah ki manta da zancen shekaru ki tashi tsaye ki nemawa ya'rki hanyar da xatabi ta zauna da mijinta lfy wannan shine abunda ya dace kiyi tagumi ko tunani ba naki bane"....shuairat CE ta katse mata tunani ta shigo tare da sallama ta fada jikinta tana juyi

"Oh mama! Kin tsoratani I tot wani Abu ne ya sameki tank God u ar fine"
Murmushi mama tayi tace
"Lfy ta kalau na kiraki ne ina son muyi magana"

"Go ahead ina jinki"
"Dazun nan mahaifin shugabankasa ya bar nan, ya zo Neman aurenki"
Dumm...xuciyarta ta buga nan ta tashi xaune

"Waat? Neman aurena? Me baba yace masa?
"Me zai fada kuwa an saka ranan auren nan da...

"No! Mama it can't b nikam baxan auri tsoho bah"

"Aww really? Bazaki auri tsoho ba kika fito gaban dubban jamaa kika bayyana cewa kuna soyayya? Kiyi amfani da hankalinki shuairat ke fa kika amince masa ya turo iyayensa me kika maida mu?

"Haba..mama kinfa San komai akan alamarin nan na gaya miki yanda abun ya faru kuma wllhi bamu taba wani xancen soyayya dashi bah ..ni ..ni"
Se kuma ta fara kuka
Mama ta tabe baki tace
"Kanki ake ji yarinya da can wani ne ya turaki kika CE kuna kaunar junanku? Ko a wancan lokacin baki San shi tsoho bane se yanxu? Bazaki maidamu mutanen banza bah bari kiji gara ma ki saita kanki kisan abunda kikeyi"
Nan mama ta tashi ta bar mata dakin shuairat ta nemi hawayen ta rasaπŸ˜†πŸ˜† da can ta dauka mama xata rarrasheta ne aikuwa ta tashi ta nufi bangaren shukrah a falo ta sameta tana buga game
"Yadai mutuniyar"

"Mtswww...wato kina xaune ckn kwanciyar hnkli baki damu da halin da nake ciki ba koh"

"Me ya faru bestie" shukrah ta fada a yayinda take ajiye wayar hannunta ta gyara xama
Shuairat ta tura baki tace
"Kina ji wai daddyn mr President yaxo neman aure nah"

"😳😳kai ...dama shine yaxo gun baba dazun nan?

"Mstsww...ke ana serious kina wani mtsww

"Yi hakuri bestie dama kina soyayya da mr President ne baki taba gaya min bah"

"Allah na! Shukrah! Haba try to understand mana haaa da muna son juna xan damune ?😏😏

"Okkk...calmdown n tell me meyake faruwa"
Nan shuairat ta kwashe labarin kaf ta gaya mata murmushi shukrah tayi tace
"Trust me kuna son junanku just dat Baku fahimci hakan bane but wit tym...

"Hey hang it girl! Ar u kidding me? Ya zan fara soyayya da tsoho ne ..yurk! U know I can't "

"Babe baki gane ....
"Pls bestie stop it! Shi tsoho ne bai San me ake cewa love bah n shima ya gaya min bai taba yi bah"

"Tsoho? Ya kai 80 ne?
"Ahh..haba he is 40+"

"Hmmm bestie he is still young u can handle it, waima lemmi ask u salman khan na Indian film shekarunsa nawa?
"40+"

"Wat of sharukh khan?
"40+"
"Akshay kumar fah?
"πŸ™„πŸ™„πŸ™„ shima haka"
"Me zasu nunawa mr President? Kyau? Ilimi ko arziki? Hey girl wake up! Mata nawa suke neman mutanen da basu kai mr President bah? About 1000+ n duk fadin duniya babu macen da zata ki auren mr President but y bestie? Kiyi aiki da brain naki pls ke da kanki kika CE he is so cool..meyafi hakan toh namiji kyakkyawa ga ilimi ga hankali ga tausayi ga arixizi ga ga ...komai ya tara me laifinsa? N tell me ke din kintaba son wani namiji? Maza nawa Suka so ki Amma baki sauraresu bah kinga kenan Allah ne ya hadaku shi bai taba soyayya ba kema haka kiyi tunani akai shuairat u can do it u can handle it after all u ar a lady ni kaina ke kika koyamin wasu abubuwa da dama y not kiyi amfani da su? Ki zauna da kyau kiyi tunani"
Daga nan shukrah ta tashi ta shige kitchen ta bar shuairat da dogon tunani akan kalamanta...



Hmmmmm
[2/21, 2:39 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*38*
By *Reefat yahya*


Mr President tare da daddy da sultan suna cin abincin dare a dinning table na bangaren mr President umaima kuwa taki xuwa a dole wai tana fushi daddy ne ya fara magana

"Boy u ar lucky wallhi surukinka mutumin kirki after ol Dan Adamawa ne"

"😳 ..uhmmm ehh dad namanta ne ban gaya maka cewa shi Dan Adamawa ne ba "
Lallai shi da bai taba xuwa gidan surukan nasa bah ina zai San halayensu...

"Boy kana ji nah"
"Ehh..ina jinka daddy"
" idan na koma zanyi magana da momsin ka batun hada lefe xatayi magana da sakeena ya'r wanta wacce take business na kaya zaa hada komai a kawo daga nan sai a kai gidan nasu koh"

"Ok daddy nagode but da nace kudi zan bata ta siya da kanta"

"No! Mu zamu siya komai kuma babanta yace baya son almubazzaranci saboda haka komai dai2 gwargwado zaayi"

"Ok daddy nagode Allah ya kara tsawon rai "
"Ameen! Auren naku nan da 3weeks ne"
😳😳wani tari ne yaxo masa wani bugun xuciya yaji...damm

"Boy ar u ok!
"Ehm..umm.am ok daddy am am fine"
Gub...gub haka xuciyarsa ya cigaba da bugawa innalillahi kawai yake maimaitawa can yaji muryan daddynsa na cewa
"Sultan tashi muje muyi hiranmu koh kasan gobe jirgin 7 zanbi insha Allah"
Daga nan Suka tafi aka barshi shi kadai nan ya fada duniyar tunani ....yanxu da gaske aure zaiyi? Ya zasu kaya da umaima? Ya zaman nasu zai kasance? Shuairat zata zauna lafiya ta rike masa sultan ? Anya xai iya kallonta a matsayin mata? Wace irin rayuwa zasu yi? Hmmm lallai yana da babban aiki a gabansa...haka dai ya cigaba da tunane tunanensa..



****************
Shuairat CE xaune a gaban dressing mirror tayi jugum tana tunani wai ynxu da gaske aure zatayi? Mr President xata aura? Ze iya bata romantic lyf da ta Dade tana mafarkin samu? Zai iya kallonta a matsayin matarsa? Zata iya zama da umaima da sultan? Ya rayuwarta zai kasance? Ya.....
Bude kofar dakin da akayi ne ya dawo da ita daga kogin tunanin da take mama CE rike da waya a hannunta ta mika mata

"Hajiya mairo xata miki magana"

"Ok" nan ta sa hannu ta karba ta kara a kunne tare da sallama
"Ina yini anti"
"Lfy my baby ya kike ya aiki"

"Lfy alhamdulillh"
"Baby nah magana xamuyi ta fahimtar juna"

"Ok anti ina jinki"

"Mama ta gaya min halin da kike ciki Amma ina son ki kwantar da hankalinki ki gane cewa aure nufi ne na Allah kuma matar mutum kabarinsa ki daure ki amince da zabin da Allah ya miki alkairi ne insha Allah, ki sake ranki ki cigaba da activities dinki kinji?

"Ok anti nagode"

"Ki kwantar da hankalinki munyi magana da yayanki zai sama miki ticket ki bi flight gobe kixo Kano gida kinji"

"Ok anti tnxx"

"Yawwa my baby takkia sai na ganki koh"

"Ok anti bye"daga nan ta mikawa mama wayar ta kashe ta juya suna fuskantar juna mama tace

"Ki shirya kayanki gobe jirgin safe zaki bi ki tafi Kano "

"Ok mama "
"Batun events kuma walimah kadai ya wadatar ko kuwa akwai program da zaki yi"

"Walima is ok "
"Toh shikenan ki fara shirya kayanki yanxu"
"Ok toh" daga nan mama ta bar dakin shuairat ta hada kayanata kala10 a travelling bag bayan ta gama se ta shiga watsap mssgs Suka shigo dama ta kwana2 bata shiga bah. Mssg din princess maimah ta gani

"Hi dear fren ya kike
"Fyn " ta mata reply tana online dat tym se ta tura
"Wia have u bin shiru 2days"

"Ina nan just busy ya gida n evrtin"

"Fine alhamdulillh kawai gt a little prblm wit dad ne"

"😳ur dad? Haba y?

Nan ta gaya mata abunda ya hadasu shuairat tace

"Haba kawa ba kyau fushi da iyaye"

"Ok tanx xan kiyaye next tym"
murmushi princess tayi a dayan bangaren a xuciya tace she is just like her bro.haka Suka cigaba da chat nasu har na tsawon lokaci sannan sukayi sallama.



Ku biyoni....😘😘😘😘😘
[2/21, 2:39 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*39*
By *Reefat yahya*


A airport mr President yayi sallama da mahaifinsa yana rike da hannun sultan suna dagawa daddy hannu har sun juya xasu tafi daddy ya sake dawowa gun mr President yace

"Boy is gud kaje ka gaida surukinka"

"Ok daddy xan samu lokaci"

"No! Son xanso ace yau xaka je"

"Ok insha Allah zanje"
"Ok gud na tafi sai munyi waya"

"Safe trip a gaisheda momsi"

"Ok zata ji" daga nan mr President ya ja hannun sultan Suka shiga mota Suka kama hanyar gida.
Da yamma misalin karfe 4:30 mr President yasha manyan kaya se qamshin turare ke tashi an jera motoci bash na gidan gaba tare da driver a yayinda mr President ke xaune a gidan baya hannunsa rike da magazine yana karantawa , a kofar gidansu shuairat akayi parking na motocin dama can baba ya San da xuwan surukin nasa batare da bata lokaciba Suka shiga ckn gidan bodyguards Suka tsaya a waje bash na gaba mr President na biye dashi.baba na xaune a falo Suka shigo tare da sallama bayan sun gaisa an jerawa mr President kayan marmari iri2 Amma ko ruwa bai iya ya sha bah saboda kunyan baba yake ji, basuyi wani dogon hira bah shiru Suka yi tamkar babu kowa a falon chan baba ya daure yace

"Duk da naji cewa kana kaunar ya'ta amma don Allah ina rokonka ka riketa bisa gaskiya da amana bana son wani Abu ya sameta"

"Insha Allah baba na dau alkawarin kula da ita babu abunda zai taba ta "

"Nagode! Allah ya Baku zaman lafiya da zuria mai albarka"

"Ameen" mr President ya amsa ckn jin kunya daga nan mama ta fito Suka gaisa ta koma ciki ta barsu, haka nan sukayi sallama mr President ya tafi sannan bash ya shigo da bandir din kudade ya ajiyewa baba shi kuma se fada yakeyi wai akan me bash xe karbi kudin bai sauraresa ba yayi ficewarsa saboda ana jiransa a waje xasu koma gidan mr President.


*******************
Shuairat CE zaune a dakin da aka sauketa a can Kano ta ajiye kazar da ta sha hadin magunguna a gaba ta rasa ya xata fara cinsa gashi ta taba ta jishi ba dadi anti mairo CE ta shigo tare da sallama

"Lalala..baby har yanxu baki cinye bah? Gaskiya xamu bata dake"
ta tura baki tare da yatsina fuska tace

"Allah anti ba dadi bazan iya ci bah"

"Baby ki daure haka ki ci if not xamu bata oya ..now "
Haka tasa shuairat a gaba dole ta cinyeshi tass tana maida numfashi dakyar.bayan ta huta kadan mai gyaran jiki ta fara tata aikin haka Suka yini ranar gaba daya se gyarata ake yi har dare bata huta bah wani hadin tsimi aka bata dole ta shanye.
Misalin 9:00pm ta watsa ruwa tayi shirin bacci kenan ta kwanta a gado dama dakin ita kadai CE a ciki ta bude data mssgs na watsapp dinta Suka fara shigowa se kuma wayar ta fara ringing sabuwar num ne kuma special har ya kusan tsinkewa sannan ya daga ta kara a kunne tare da sallama

"Hey reporter ina kika je ? Wato baki xaman gida koh?

"Pls who is on d line?
"Baki ban amsa bah"

"Mr president?
"Baki xaman gida ina kike xuwa?

"Mr president ko kamanta cewa am a reporter so I have....

"Luk Ayshah daga yau nayi banning duk fitanki har xuwa ranar daurin auren"

"Aww..da gaske?
"Tambaya kike? Dont u have som respect?

"Umm..am sorry"
Shiru sukayi dukkansu biyu kowannensu ya rasa abun fada daga karshe ya kashe wayar.daga can bangarensa tunani yake meyasa ma ya kirata? Kuma idan tana fita ma meyasa zai damu? Daya bangaren xuciyarsa yace of coz matata tace dole na damu, no! I don't have too" shiii...ya sunkuyar da kai yana tunani ya kasa samun amsa ko daya.shuairat ma haka abun ya kasance mata ta kurawa wayar ido tana tunani daga karshe ta share maganar kawai ta shiga watsapp dinta Suka fara chatting da princess maimah da kuma shukrah.


Ku biyoni....
Love u all 😘😘😘
[2/21, 2:39 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*40*
BY *Reefat yahya*


Bayan sati daya aka kawo lefen shuairat mata biyu ne kacal Suka xo anyi musu kyakkyawar tarba an karbesu ckn mutunci akwati set 2 ne cike makil da kaya masu kyau Wanda bazan iya siffantasu ba sai dai masu karatu su kimanta da kansu😜 daga karshe sukayi sallama Suka tafi bayan an cikasu da snacks da drinks kala2.shukrah kam se santin kayan take xubawa aikuwa tayi snapping ta tura a instagram da watsapp cewa ga kayan lefen aminiyarta amma bata bayyana cewa mr President ne xai aureta. Shuairat ma ta yaba da kayan sunyi kyau ba karya , shirye shiryen biki ake Amma mr President ya hana duk wasu programs da zaayi ciki kuwa har fansan amarya yace bayaso sabida yasan yan gulma zasu cika wajen shuairat CE zatayi walima shikenan.


****************

"Umaima lfynki kuwa? Yarinya kin dau karan tsana kika dora akan mahaifinki bayan kinsan Allah ne ya hallata masa auren kin isa ki hana ne?

"Wllhi anti khady wannan cin amana ne yanxu shekaru nawa ne da rasuwar mom amma har ya manta da ita? Se kuma ta cigaba da kukanta anti khady ta sake baki tana kallonta sannan ta cigaba da cewa

"Nidai baxan goyi bayanki ba umaima wannan ai rashin gaskiya CE , Allah ya halasta masa auren mata 4 ke kice baki so yayi auren? So kike ya kare rayuwarsa haka?

"Anti kinga yarinyar karamace fah wllhi tun bata shigo ba ya daina kulamu kuma...

"Ki bude kunnuwanki kiji abunda zan gaya miki, ki tashi ki koma ki bawa mahaifinki hakuri ki rungumi kaddara ki xauna lafiya da matarsa Allah ne ya kaddara baki isa ki hana bah "

"Gaskiya nikam baxan iya bah, ynxu dama duk son da yakewa mom ya...

"Dakata umaima bari kiji labarin da baki taba ji bah, dad da mom dinku auren xumunci aka hadasu dad naku ba shi ya nemi auren mom naku bah biyayyace ta sa ya amince ya aurota har Suka xauna tsawon xaman da sukayi.dad dinku bai taba yin soyayya a rayuwarsa bah kuma....

"Wait..an..anti kina nufin duk xaman da sukayi babu soyayya a tsakaninsu?

"Bansani ba umaima Allah shine masani nidai nasan dad mutumin kirki ne yana da kara sosai har gobe baraa sami yaro mai biyayya irinsa bah a duk fadin danginmu"
Shiru umaima tayi tana tunani kanta ya kulle kwakwalwarta ya to she anti kady CE ta dafata a kafada tace

"Kiyi hakuri ya'ta nasan kina taya mom naki kishi but koda ace tana raye itama bata da ikon hana wannan auren kiyi hakuri ki shirya ki koma gun mahifinki"

"Zan koma amma ba yanxu bah, sai bayan bikin nasu "

"Shikenan xan kira dad na fada masa kada ya tada hankalinsa gun nemanki "

"Ok anti nagode"
Haka ta cigaba da xubda hawaye tana jin wani radadi a ckn xuciyarta.


*********
Shuairat CE a gaban dressing mirror tana kallon kanta tabbas ta canza ba kadan bah fatar jikinta se sheki yake ga gashin kanta da ya sha gyara se kuma dadaddan qamshin da yake tashi a jikinta murmushi tayi a yayinda ta cigaba da kallon fuskarta tana admiring din kanta lallai mr President yayi daceπŸ˜€πŸ˜€tunaninsa ne ya fado mata a rai fuskarsa ta hango , kyakkyawan karshene ita kanta tasan da hakan kuma yana da karamin ruwa idan bakasan shrkarunsa xaka CE Dan shekara 32 ne ta lumshe ido tana tuna farkon haduwarsu yana magana so cool yana da class sosai kuma yana da tausayi musamman idan ta tuna ranar da ya share mata hawaye lokacin da take kuka, shin zata iya soyayya dashi? Anya kuwa? Hmmmm ko kadan bata taba mafarkin cewa taxa auri babban mutum kamarsa bah sai kuma rayuwarta na baya ya fara dawo mata a kwakwalwa.....


Muje xuwa....
*Reefat*
[2/21, 2:39 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*41*
By *Reefat yahya*


*wacece shuairat*???

Alh Bello mamman hafaffen garin maiha ne na jahar Adamawa su hudu ne a gun iyayensu Ahmadu Salihu bello da kuma zainabu a can garin maiha aka haifesu duka amma shi bello ya koma garin mubi da xama gun wan mahaifinsa a can yayi primary da secondary sannan ya wuce jamia ta bayero Kano a can ya karanta bangaren education, bayan ya gama ya dawo gida a Yola yayi bautar kasa a wannan lokacin ne ya hadu da Fatima ya'r layinsu mahaifinta ne limamin unguwarsu a can karamar hukumar maiha ta jihar Adamawa.
Bayan ya gama bautar kasa akayi aurensu da Fatima shi kuma ya samu aikin koyarwa a makarantar secondary na technical school a can mubi.Bello da Fatima suna son juna sosai kullum suna cike da begen juma haka Suka xauna ckn rufin asiri , sun share sama da shekara 6 Allah bai basu haihuwa bah amma duk da haka bello bai taba nuna damuwarsa bah, Fatima tayi2 ya kara aure yaki sauraranta har ta gaji don kanta ta daina kawo masa xancen.kwatsam Allah ya bata ciki sunyi murna sosai hKa Suka kasance ckn farin ciki har Allah yasa ckn ya cika wata9 da yan kwanaki Fatima ta haifi kyakkyawan danta fari tas babu inda ya bar fuskarta cki kuwa har hasken fata saboda Fatima fara CE sosai, ranar suna yaro yaci suna Basheer.

Haka Suka cigaba da rainonsa har ya girma yayi wayo aka sashi makarantar firamari har ya gama Allah be kara basu wani rabon bah , basheer ya gama primary ya shiga secondary har ya kai ss1 sannan Allah ya bawa Fatima wani ckn batun murna kam baa magana basheer duk yafi xumudi akan cikin kullum hirarsa be wuce xancen a haifa masa kanwa ya'r kyakkyawa.
Bayan wata9 ciff Fatima ta haifi kyakkyawar ya'rta wacce tayi kama da bello tamkar anyi kaki an tofar yarinyar baka CE Amma ba sosai bah tana da Dan hasken fatA , haka aka saka mata suna Aisha ana kiranta shuairat.
Shuairat ta tashi ckn gata gaba da baya koina sonta ake musamman yayanta basheer baya barin kowa ya taba ta, a wannan lokacin Alh bello yana koyarwa a jamiar federal university of technology Yola. Daga kan shuairat haihuwa ta tsaya musu cak da wannan lokacin ko bari Fatima bata sake yi bah, haka Suka rungumi yara biyun da da Allah ya basu.bash ya gama secondary dakyar ya yarda ya tafi jamia wai shi baya son ya tafi ya bar kanwarsa dakyar aka lallabashi ya tafi jamiar Ahmadu bello zaria bayan ya kammala ya dawo yayi bautar kasa sai kuma aka daukesa aiki da state security service , shekaru sun gabata Alh bello yayi retire ya koma gida yana hutawa se kuma dansa ya samu canjin aiki xuwa fadar shugabankasa a wannan lokacin ne shuairat take Jin karshe a federal polytechnic dake can mubi har ta samu ta kammala inda ta karanta bangaren mass communication...
Wannan kenan shine takaitaccen tarihin rayuwarta.

A hnkli ta ja wani gauron numfashi kamar a mafarki take ganin duk abubuwan da suke faruwa a rayuwarta "ikon Allah kenan"
ta furta a hankali ynxu matsalarta shine ya xata fara nunawa mr President so? Anya zai kulata kuwa? Wane irin zama zatayi da umaima? Tabbas tana da aiki a gaba idan batayi da gaske ba xata fuskanci matsala a gidan wayarta ta hau ruri sunan shukrah ta gani nan ta daga
"Matar Yayan"
"Amarya bakya laifi ko kin kashe Dan masu gida"

"Lallai sai dai idan baa kashe din bah , ya kike ya gidan"
"Lfy lau yaushe zaki dawo"

"Umm..kinyi missing dina ne "
"Bani kadai ba harda angon mah"

"Bangane bah"
"Ehh..mana wai dama baki gaya mishi zakiyi tafiya bane?

"Y? Meyasa xan gaya masa?
"Hmm...dazu ya tura bodyguards wai yana son ganinki"

"Uhmm..yayi kyau"
"Munafuka kina so kina nokewa"
"Ehh..sai akayi yaya"

"Nidai ki dawo da wuri kan a buga mana news paper cewa mr President yana Kano"
"Wannan kuma maysalrku "

"Uhmmm..in tayi tsami ma ji"
"Babu abunda zakuji"

"Se anjima toh "
"Ok bye sai na kira "
"Ok takkia"
Tare Suka katse wayar shuairat tayi jugum tana tunani lfy mr President yake Neman ganinta?
Oho!


Nima nace oho! Ku biyoni
[2/21, 2:39 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*42*
By *Reefat yahya*


A bangaren mr President kuwa yana xaune a dakinsa yayi shiru yana tunani anya zasu zauna lfy da yarinyar nan? Ta fiye takama da nuna isa, ysushe sukayi waya amma taki ta sanar dashi cewa tayi tafiya?.mtsww meyasa ya nemi ganinta ma? Lols Reefat tace cos u miss her preety face" wayarsa ya cire yana son kiranta sau 2 yana dialing sai kuma ya fasa a karo na ukun ne yayi ta maza ya kira har ya kusan katsewa sannan ta daya ckn sanyin murya tace

"Ur excellency"
Haka kurum yaji dadin sunan da tayi adressin nasa da shi wani murmushi ne ya subuce a fuskarsa
"My stubborn first lady! Ya kike"

Murmushi tayi da jin sunan stubborn ta gane abunda yake nufi

"Am sorry ur excellency nayi tafiya ba tare da na sanar maka ba"

"Is ok! Zaki iya yin duk abinda kike so as of now b4 ki shigo gidana"

"Don't worry a gidanka ma abunda naga dama zanyi cos am d first lady"
maganar ya sashi dariya sosai yace

"Well..we shall c! Anyway dama ina son ganinki ne saboda ina son sanin programs naki da kuma amount da kike bukata"

"Ur excellency ka kwantar da hankalinka bana bukatar komi iyayena xasu min idan ma akwai bukatar hakan"

"Nasan da haka but is my duty ..anyway zan tura miki 2mil kiyi shopping idan akwai bai isa ba let me know"

"😳2wat? No! No! Me zanyi da 2milion? Walima CE zanyi fah n olredy iyayena sun riga sun tanada komi na walimar so no need pls"

"Bana son jayayya sai anjima"
Nan ya katse waya shuairat ta kurawa wayar ido tana nanatawa 2mil ? Hmmm lallai ma ai wannan almubazzaranci ne.mr president kuwa ya tsinci kansa ckn wani farin ciki haka kawai yana murmushi yana lumshe ido daga nan ya kira bash ya shaida masa yana bukatar account number din shuairat.


***********\\
Jirgin yamma Suka bi sai gasu nan a Abj shuairat ta kara haske fatar jikinta ta murje tayi kyau sosai duk Wanda ya daga ido ya kalleta dole ya kara kallonta a karo na biyu. Bash ne yazo daukansu ita da anti mairo da diyarta Sadiya wacce take saar shuairat daga nan Suka kama hanyar gida .
Gidansu a cike yake makil da jamaa babu masaka tsinke saboda saura 4days daurin auren shuairat , bangaren shukrah ta shiga a yayinda haj mairo ta wuce gun aminiyar tata ga danginsu nan birjik mutanen Adamawa kyawawa dasu falon shukrah a cike makil da jamaa ta sa kai tare da sallama shewa Suka fara yi wata ya'r kawun shuairat me suna Ummi ta tashi Suka rungumi juna da shuairat se ihu suke sai ga shukrah ma ta fito ta Ruga a guje Suka rungumi juna ta kalli shuairat tayi wani guntun dariya tace

"Gaskiya ne mata a gidan Dr Suleiman Muhammad first ladyn Nigeria da kanta, kasar ta kusa ta dawo hannunmu sai yanda muka juya ta"
Aikuwa sauran yan matan Suka fara shewa
"Aiyuriri ...mata a gidan shugabankasa Allah ya bar mana ke"
Dakyar shuairat ta samu ta shige dakin yayanta ita da shukrah da Ummi da kuma Sadiya.shukrah ta kawo musu lafiyayyen abinci ita da Sadiya Suka ci sukayi nak sannan aka baje a gado aka fara xuba shukrah tace

"Bestie kawaye nawa kika zaba"

"Ummi da Sadiya da maimuna ya'r anti luba sai kuma Hafsat mubi"

"Ok! Dama mr President ne ya turo yayanki yazo ya tambaya kuma tym din layinki baya shiga""

"Ok na kashe wayar ne tym da zamu tashi"

" mr President fah yana ji dake yarinya ! Kinga kalan zirga -zirgan da yan gidansa suke?

"Allah ko"
"Ehh ..mana wllhi ki rike tsohon nan da kyau don na lura yana sonki sosai"
Gaba daya Suka kwace da dariya Ummi tace
"Wa ya gaya muku shi tsoho ne? He is just 40 somtin ne fah "
Sadiya tace

"Gaskiya kam! Kimanta da zancen wani tsoho ki fito ki nuna masa so zalla Ku zauna lfy ya fiye

Please Login or Register in order to submit comment