Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya salo..lolx
Nan ta tashi ta xauna nama ne da exotic mai sanyi ya CE shi xai shiga wanka ta fara ci daga nan ya wuce dakinsa ya watsa ruwa tare da sa kayan baccinsa ya dawo ya sameta a inda ya barta.
Yana lallabata tana ci tana yaukiπŸ˜†πŸ˜† kamar bata so har Suka gama Suka kora da juice nasu se kuma Suka dawo falo ya kunna musu wani series film *walking death* suna kallo.

Shuairat kuwa 11pmta tashi daga bacci dama tun suna hira ita ta shige daki ta kwanta . falo ta nufa don yunwa take ji sai kuwa tayi saa foil pepa ta gani tana budewa taga nama a ciki nan ta hau ci se da ya isheta ta sha ruwa sannan ta koma dakinta xama tayi a carpet saboda bata jin bacci ta rasa me zatayi sai ta kunna data dinta watsap ta shiga mssgs Suka fara shigowa new number ta gani an tura mata hi"
Ta shiga ta ga num na online
"Helo!
Babu bata lokaci aka mata rply da
"Hw u"
"Fine alhamdulillh n u"

"Same"
"Eyya waye ne"
"New friend dinki ne princess maimah daga grp din gidan gyara "

"Aw Ayya am Ayshah"

"Nice meeting u"
"U too "
"Will like 2b ur kawa idan baxaki damu bah"

"Aww..really ! Naji dadi sosai u r welcm"

"Tnx ya gida yasu mum n ya yayanki da amaryarsa "

"Lfynsu lau..amma nayi fushi bakizo auren bruh bah"

"Eyya sory wllhi bana Adamawa ne daz y"

"Ok wane gari kike"

"Ina kd"
"Wow..daz gud"

"Ki ban labari toh" shuairat tayi murmushi tana jin dadin chat nasu da alama dai princess bata da girman kai sai tayi rply

"Me ya hana princess bacci ko dai tunanin prince ne😜

"πŸ˜ƒπŸ˜ƒlaaahh...wa ya gaya miki? Nayi bacci fah ynxu na farka shiyasa"

"Aww...just like me wllhi"

"Baxaki ban labari ba koh"

"Toh princess wane irin labari kike so"

"Ur love story"

"Lolx...wllhi ban taba yin soyayya bah "

"Ar u serious Ayshah? Nima haka wllhi"

"Meyasa toh"

"Babu fah kawai ban taba bah kuma Wanda nake so din yayi aure"

"Allah sarkiπŸ˜₯ naki tausayin ki sorry"

"😊😊tnx"
"Amma ya akayi kika bari yayi aure ko kun bata ne?

"😊is a long story"

"Ok hard luck"

"Tnx" haka Suka cigaba da hira har 1 sannan Suka rabu kowacce ta kwanta .

Asuba ta gari first ladyπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ


Love u all😘😘😘
[2/21, 2:38 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*32*
By *Reefat yahya*


Da safe shukrah ta hada lafiyayyen brkfast ta ajiyewa maigidan nata ta chaba ado ckn atamfa ya'r holland tayi kyau sosai bangaren su mama ta je ta gaishesu suna falo sabida baba kullum se ya kalli news na safe ta ajiye musu brkfast sannan ta shige dakin shuairat bacci takeyi ckn kwanciyar hnkli shukrah ta kai mata duka nan kuwa ta bude ido tare da Jan tsaki ta koma baccinta wani dukan ta sake kai mata a baya aikuwa taja bargo ta gyara kwanciya

"Ke baxakije aiki bane"
Firgigit ta tashi xaune kwata2 ta manta yau xata koma bakin aikinta ban gida ta fada tayi wanka bayan ta fito shukrah bata nan ta shirya kanta ckn material tYi kyau sosai ta fito falo bayan sun gaisa da iyayen nata ta wuce bangaren shukrah.

Suna kari da mijinta ckn so da kulawa ta shigo tare da sallama ta gaida su sannan ta nemi wajen xama abinci ta deba iya cin ta tana ci suna hira bayN sun gama tare Suka fita da Yayan nata ya ajiyeta a wajen aikinsu.


************
Mr President tare da tawagarsa Suka sauko daga ckn jirgi ga jamaa nan birjik ana ta daukansu hotuna daga nan Suka shiga motocin da aka tanada musu Suka dau hanyar villa.
Bayan ya huta ya bada umarnin cewa bazai ga kowa ba se xuwa gobe saboda yana bukatar Hutu. Ckn gida ya wuce bangaren yaransa bodyguards na binsa a baya ga bash kuma a gefe ya iso dab da falon sauran sun tsaya amma banda bash , tare Suka shiga katafaren falon tare da sallama umaima tana kwance tana chat sultan kuma yana buga game . suna ganin mahaifin nasu Suka ruga a guje Suka shige jikinsa ya rungumesu gam gam gwanin tausayi yaran daga gani ansan cewa kadaici da maraici na addabarsu sun kai minti2 a rungume da juna sannan Suka sake shi yana murmushi yace

"My sultan ya kake"

"Lfy dad I miss u"

"I miss u more my sultan ya jikin sisy"

"Dad bansan meya sameta ba kullum se tayi kuka"
Mr President ya juya yana kallonta ta sunkuyar da kai bash ma ita yake kallo.a hnkli ya rike hannunta ya fara magana

"My baby me yake damunki"

"Ba komai dad"

"No tell me pls"
Sai kawai ta fashe da kuka nan ya jawota jikinsa ya fara rarrashinta dakyar ta bar kukan Suka xauna a kujera daya ya fara jansu da labari suna kwance a jikinsa.
Duk sanda umaima ta daga kai sai sun hada ido da bash , mr President ya kira iyayensa a waya ya hadasu sun Dade suna hira grandpa ya shaida musu yana nan tafe nan ba da dadewa bah haka Suka Dade a falon yana ta basu labarin China sosai ya cire mata radadin da take ji ya rage mata damuwanta , bash kuwa hnklinsa yayi nisa yana son ya gano matsalar umaima Amma ya kasa tuna komai.
Bayan tsawon lokaci mr President ya musu sallama ya tafi bash kuwa ya xauna yace magana xaiyi da umaima.

"Umaima ki gaya min me yake damunki"

"Babu"

"Umaima look at me"
Ta daga kanta idanunta Suka fada ckn nasa tayi saurin kawar da nata

"Umaima dama baki daukeni a bakin komai ba daz y kike boyemin damuwarki"

"Ba haka bane bash"

"No! Nagane matsayi na tnx"

Yana gama fadin haka ya tashi ya fara tafiya se kuma ta fara kuka cak! Ya tsaya ya juya yana kallonta haka nan sultan ma ita yake kallo "ya ilahi me yake damun yarinyar nan ne"
Ya taka yaxo ya sunguna a gabanta yace

"4Allah's sake umaima ya kike so a miki? Ki fadi matsalarki kin kasa fada kullum se kuka"

Tayi shiru batace komai bah
" pls ki daure ki gaya wa dad dinki tunda ni baxaki iya gayamin bah, kuma ki rage yawan tunani kar ya jawo miki prblm pls"

"Nagode" ta furta a hnkli daga nan bash ya tashi ya tafi tabi bayansa da kallo Allah Sarki bash baisan ma tana yi bah ita kanta takanyi mamakin irin son da takewa bash Wanda bata San yaushe ta fara shi bah haka nan bata San ranar dainawa bah.
Ita dai tayi imanin cewa tana sonshi Amma ko xata mutu ne baxata taba furta mishi bah, kuma bata tunanin cewa xata so wani mahaluki a duniya bayan basheer bah.maybe ita ma auren xumunci xaa mata cos ita kam basheer kawai take so a rayuwarta.

Allah Sarki umaimaπŸ˜₯πŸ˜₯


Muje xuwa love u all 😘😘😘
[2/21, 2:38 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*33*
By *Reefat yahya*


Shuairat tana xaune a ofishinsu bodyguards Suka shigo Suka sanar da ita cewa mr President na bukatar ganinta ba tare da bata lokaci ba Suka fice tare.

Yana xaune a dakin hutawarsa ta shigo tare da sallama ya amsa ba tare da kalleta bah yana rike da wani Dan karamin cup black coffee ne a ciki yana sha a hnkli , waje ta samu ta xauna shiru sukayi babu Wanda yayi magana har tsawon minti 10 shuairat CE ta gaji da xaman nasu tace

"Mr president ka aika a kirani ina aiki n u din say anytin"

"My first lady yaushe xaki koyi gaisuwa ne? Ko baki iya respecting magabatanki"

Wani irin kunya ne ya lullubeta amma bata son ya gane hakan tayi gyaran murya tmkar Mara gaskiya tace

"Emm...uhmmm sorry about dat actually...

"Is ok! Neva mind , anyway na kira ne saboda ina son sanin hukuncin da kika yanke ko kuma in CE shawarar da kikayi batun maganar da mukayi som few weeks ago"

Ya tare numfashimta tare da kura mata ido

"Mr president I don't knw wat to say about it"

"Look Ayshah lokaci yana tafiya ya kamata ki fito fili ki gaya min cos my dad is on his way soon kuma xancen auren ne xe kawo shi"

Shiru sukayi kowanne da tunanin da yake yi ckn sanyin murya shuairat tace
"Mr president idan nace baxan aure ka bah wat will b d outcome"
Murmushi yayi yana girgiza kai yace

"Funny girl! Me a ciki ? Kawqi ki fito ki gayawa yan jarida da sauran jamaa cewa karya kikayi tun da can ba abunda yake tsakanin mu kinyi hakan ne....
" mr President ya xakayi da ...

Hannu ya daga mata yace
"Don't worry about me, kawai ki fito ki gaya musu gaskiyan idan xaa cireni akan mulkin ma fine I don't kia n xanyi tunani akan abunda xan sanar wa mahaifina so kada ki sa damuwa a ranki"

Ta rintse ido ya ilahi wannan wace irin jaraba CE? Shin ya xatayi? Ta amince da auren ko kuwa ? Toh idan ta fito ta fadi gskiya tabbas jamaa xasu mata kallon mutuniyar banxa daga ita har mr President yanxu me abun yi? Muryan mr President ne ya katse mata tunani

"Ayshah u don't have to worry about me"

"About u? Mr President dis is about us ya shafeni ka gane koh?
Murmushi yayi yace

"Nasan ma kina son auren kina wani nokewa pls feel free Ayshah"
Ta daga idanunta Suka fada ckn nasa ta murguda masa baki tare da cewa

"Meyasa xan so auren tsoho ? Kawai de kai kafi bukatar auren ba ni bah"
Tana gama fadin haka ta juya tabar masa falon yana murmushi shi kadai.

A waje Suka ci karo da umaima kallon kallo Suka tsaya yi daga karshe shuairat tasa kai xata wuce umaima ta fisge hannunta da karfi
"Ina xaki je munafukar karuwa kawai kin xo kin like wa mahaifina daga ganin arxiki koh"

Wani shuumin murmushi shuairat ta sakar mata tare da cewa
"Karuwancin ma iyawa ne wata idan tayi ta samu kudi wata idan tace xatayi duka xata sha"

Hannu umaima ta daga da niyyar Marin shuairat cas ta cafke hannun tana murmushi ta nunata da yatsa
" yarinya kinyi kadan wannan fuskar ba kowane mahaluki bane xe iya taba shi ba kingane koh, n don't 4get saura kankanin lokaci na xame miki uwa "

"Har abada Baxaki taba xama matsayin uwa a gareni bah"
Nan kuwa umaima ta fara hawayen jin an ambaci sunan uwa ta tuna da mahaifiyarta shuairat ta sake mata hannu ta juya xata tafi umaima ta sake Jan gyalenta da karfi ta juya suna fuskantar juna tace

"Ke umaima kike ko wa ki shiga taitayinki ni ba Saar yinki bane da mahaifinki nake dealing ba da ke ba , so ki kiyaye"
Bash ne ya hangosu ckn Sauri yaxo ya shiga tsakaninsu umaima ta fashe da kuka dai2 nan mr President ya fito don ganin meke faruwa shuairat ta juya ta kakkabe gyalen ta fara tafiya sai kuma ta juya ckn gadara tace

"Mr president I tink ya'r ka bata da tarbiya yana da kyau ka sanar da ita cewa aurenmu yana nan xuwa bada dadewa bah xan dawo gidan nan da xama she shul learn how to respect me "

Mr President da bash baki Suka bude suna kallon shuairat wacce ta wuce direct gun mota aka bude mata ta shiga umaima kuwa ta fashe da sabon kukan bakin ciki dad nata ya juya xai mata magana ta daga masa hannu alamar cewa bata bukatar jin komi daga garesa , wani dogon numfashi yaja sun hada ido da bash ya masa nuni da ido akan yaje ya mata magana hakan kuwa akayi umaima ta koma bangarenta bash yabi ta baya.






😘😘😘lov u all
[2/21, 2:38 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*34*
By *Reefat yahya*


Ta xauna dirshan a kasa wani irin bakin ciki take ji bash ne ya shigo yana mata murmushi ta kawar da fuskarta gefe handkerchief ya fara mika mata ta karba ta share hawayen sannan ya tashi ya bude fridge ya dauko mata ruwa mai sanyi nan ma batayi gardama ba ta karbi goran ta shanye tana sauke numfashi a hnkli nan kuwa taji hnklinta ya kwanta

"Umaima kiyi hakuri I know hw u feel"

"Hakurin me xanyi basheer? Nasan laifi na ne ni nafara nemanta da fada but...
Kuka ta fara yi bash ya cije lebe yana tunani halinsu iri daya da shuairat se saurin hawaye ga Neman magana koda yake mata ma dukkansu suna son kuka

"Bash baxan jure ganin dad da wata bah a matsayin matar da xai aura, it always reminds me of my mom"

"But umaima ya xakiyi? Allah ne ya kaddara hakan y not kiyi hakuri ki xuba musu ido"

"But na kasa bash! I can't baxan jure ganinsu bah wai ma dad har soyayya yake da wannan yarinyar?

"Umaima...
"No bash! Kasan me yake bata min rai? Tun ynxu fah idan ta fadi Abu dad baya tsallakewa idan sunyi aure fah?

"Umaima don't worry kiyi hakuri komi xai daidaita , nide ki rage yawan fushin da kike yi pls kuma ki daina disrespecting din dad naki pls"

"Ok "
"Pls promise me dat baxaki kara fushi da dad bah"

"Ok I promise"
"_gud girl daz y I like u"

Murmushi take ita kadai tasan abunda take ji, haka bash ya xauna yana debe mata kewa daga karshe ya mata sallama ya tafi.waya ta cire ta kira wata yar mamanta bayan sun gaisa take shaida mata cewa dad nasu xeyi aure haka anty kadi ta bata hakuri akan cewa ta kwantar da hnklinta dama dole wata ran xeyi aure ko ba ynxu ba.


***********

Shuairat CE tare da shukrah suna xaune suna hira a falon shukrah ya shigo tare da sallama shukrah ta karbe jakan hannunsa shuairat ma ta masa sannu da dawowa yace

"Baby I don't like wat u did today"

"Yaya ba laifina bane"
"I know but da kin kyaleta kawai"

"Haba yaya ya xaayi...
"Baby kada ki manta aure xakiyi ki koma a gidan bai dace Ku fara samun matsala tun ynxu bah"

"Yaya kasan baxan taba barinta ta mare ni ba koh"

"Yes na sani kuma ki rage nuna gadara da iko a gaban mr President he deserve som respect , duk da bansan limit na soyayyarku bah"
Shiru sukayi suna kallon kallo shukrah CE ta fito daga ckn daki tana kallon halin da suke ciki tace

"Lfy? Meke faruwa?
"Ba komai bash ya bata amsa sannan ya tashi tayi shigewarsa daki ya barsu ta juya gun shuairat tace

"Bestie menene?

"Ki tamabayi mijinki "
Nan itama ta fice ta koma bangarensu dakinta ta shiga ta fada gado ta rike kanta
"Ya Allah Kaine gata na ka xabamin mafi alheri tsakanina da mr President " ta lumshe idonta nan ta fara tuna fuskar mr President farine Sol dogo mai matsakaicin jiki yana da saje da dimple gashin kansa baki mai laushi yana da shanyanyun idanu farare gashi nan so cool bai iya fada bah baya son hayaniya duk abunda tayi se ido kawai yake xuba mata baxai furta komai bah
"He is too young 4his age"
ta furta a hnkli se kuma tayi murmushi .

Hmmmmm *Reefat* tace
"Shuairat ar u in love???
Hmmmm muje xuwa


😘😘😘😘
[2/21, 2:38 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*35*
By *Reefat yahya*


Alh Mohammed mahaifin mr President ne yake saukowa daga benen jirgi ga nan jamaa da dama ciki kuwa harda mr President ga yan jarida birjik se daukansa hotuna suke mr President ya karasa ya rungumi mahaifin nasa ckn farin ciki ya rike shi a kafada suna dariya Suka wuce filin motocin da aka tanada musu convoy na motocin Suka dau hanyar xuwa gidan mr President.

"Daddy nah I miss u so..much"

"I missed u too my boy"
Suna dariya bash ma yaso yin dariya Amma ya danne sarai mr President ya gane hakan se ya juya gun mahaifin nasa yace

"Daddy kaga wai kirani boy shine yake basu dariya"
Mahaifin nasa ya juya yana murmushi ya kalli bangaren da bash yake a gaban mota yace

"Yes! He is my boy cos shi kadai Allah ya bani kuma har ynxu ganin karamin yaro nake masa"
Murmushi sukayi haka Suka kasance har Suka karasa gida.
Umaima da sultan Suka fito da gudu Suka fada jikin kakan nasu yana dariyar jin dadi ya rungumesu sosai yaran na basa tausayi musamman idan ya tuna irin shakuwarsu da mahaifiyar tasu bayan sun shige katafaren falon mr President nan masu aiki Suka cika dinning da abinci kala2 ga yan xuwa barka da xuwa nan birjik bayan jamaa sun da tsagaita ne Suka wuce dinning table don cin abinci.
Mr President yana xaune kusa da mahaifinsa umaima kuwa tana gefen bangarensa na hagu sultan ne gefenta anyi serving dinsu kowa ya fara cin nasa, Alh Mohammed ne ya fara magana

"Son am so happy batun auren nan naka ka farantamin rai sosai"
Mr President ya fara tari daga nan ya dau ruwa yana kurba a hnkli sun hada ido da umaima ta kawar da fuska gefe.ya cigaba da cewa

"Dama naxo ne xancen auren naku , gobe xanje mu gana da iyayenta mu sa rana"

"Daddy y not...
"Boy bana son musu pls"

"Ok daddy Allah ya tabbatar da alkairi "

"Yawwa haka nake son ji.ynxu in banda abinka shkru nawa da rasuwar matarka amma ka kasa samun wata ko don yaran nan naka baka tunanin suna bukatar wacce xata debe musu kewa da rashin mahaifiyarsu?

Se ynxu umaima ta sa baki
"Granny mu bamu da matsala idan sultan ne kuwa yana da nannies masu kula dashi ba sai ya auro wata ya kawo bah"

"Oho! Ynxu nagane me yake hanaka aure wato wannn ja'irar ya'r taka ce bata son kayi aure koh? Toh karya kike umaima aure kam dole sai yayi kuma nan ba da dadewa bah"

"Daddy pls..
"Rufemin baki, baka da abunda xaka gaya min.Amma ka bani mamaki wallahi "

"Daddy plsss...
Fuu..umaima ta tashi ta bar falon ta tafi bangarenta Alh Mohammed ya juya yana kallon Dan nasa yace

"Boy! Irin tarbiyar yaranka kenan? Gaskiya nayi mamakin ganin haka a ckn gidanka son.kai kadai Allah ya bamu mun dauka son duniya mun dora a kanka amma hakan bai hanamu baka tarbiya mai kyau bah but y?

"Daddy am sorry wllhi umaima bata jin magana na ban....

"Quiet! Boy...kai ka haifeta ko ita ta haifo ka? Which one? Tell me!

"Daddy am sorry"
Mr President ya marairaice tmkar xeyi kuka nan kuwa mahaifin nasa yaji tausayinsa yasan sarai Suleiman be iya fada bah he is too cool shiyasa umaima take yin abunda ta ga dama can yace

"Ok son! Gobe insha Allah xan gana da mahaifin yarinyar xaa saka ranar aurenku nan ba da jimawa bah, aurenka na fari ni na xaba maka matar da ka aure n dis tym ka kawo wacce kake so dole xan jajirce don ganin na cika maka burinka.Allah ya bada xaman lfy insha Allah wannan yarinyar xata xame mana alkairi xata kawo farinciki a rayuwarka believe me son"
Yana magana yana kallonsa bayan ya gama ya tashi yayi shigewarsa dakin da ya saba sauka duk lokacin da ya kawo musu xiyara.sultan yabi bayan kakan nasa aka bar mr President shi kadai a xaune yasa abinci a gaba yana tuna kalaman mahaifinsa "shin da gaske Aysha xata kawo farinciki a rayuwarsa? How? Meyasa daddy ya fadi haka?

Hmmmmm..... Ya xata kaya tsakaninsu?
Muje xuwa

😘😘😘
[2/21, 2:38 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*36*
By *Reefat yahya*


Mr President ne xaune a falonsa yayi nisa ckn tunani bash ya shigo tare da sallama

"Mr president sir!
Firgigit ya motsa a hnkli yace

"Ehmm...basheer pls ina son ka kai daddy na gidansu Ayshah Bello"
Jim bash ya tsaya yayi shiru se kuma yace
"Ok sir!
Daga nan yayi waje wayarsa ya fitar yayi dialing din numbar mama ckn kankanin lokaci ta daga tare da sallama

"Mama ya gajiya"
"Lfy ya aiki"
"Alhamdulillh, dama mahaifin mr President ne zaizo Neman auren baby ynxu haka xamu taho tare shine nace bari na sanar daku"

"Tohh! Ikon Allah , dama shuairat ta daidaita da shugabankasa shine bata gaya mana bah?

"Mama kada ki sa damuwa a ranki kawai ki sanar da baba gamu nan xuwa yanxu"
Ya katse wayar a dai2 nan daddy ya fito yasha many an kaya se uban qamshi ke tashi bash ya fara soshe 2 kamar Mara gaskiya daga nan aka bude musu mota Suka dau hanyar kubuwa xuwa gidansu shuairat. Bash ya turawa matarsa text akan ta tanadi kayan motsa baki danginsu snacks da fruits se kuma lemuka masu sanyi ya sanar da ita gasu nan a hanya yana tare da manyan baki.

Baba da mama suna xaune a falo mamakin alamarin sukeyi domin basu taba tunanin cewa mr President xe auri ya'rsu bah suna nan xaune suka ji dirar motoci a kofar gidan bash ne ya sauka da sunan zeyi sallama don a basu ixinin shiga ya tura kofar gidan a hnkli yasa kai a ciki (basu San cewa gidansu bane lol) bayan kankanin lokaci ya fito ya shaidawa daddy ya fito nan Suka shiga har falon baba yana xaune shi kadai daga nan bash ya bar musu falon...
Bayan sun gaisa nan Suka fara hira tamkar sun Dade da sanin juna daddy ya shaidawa baba kan cewa shi Dan jahar Adamawa ne haka nan shima ya gaya masa shi Dan Adamawa ne sosai sunyi hira harda dariya tamkar sun saba da juna tun asali
Shukrah CE ta shigo tare da sallama ckn ntswa ta gabatar da kayan motsa baki bayan sun gaisa ta sa kai ta fice ta koma bangarenta bayan wani Dan lokaci mama ta fito Suka gaisa da daddy sannan ta koma ckn daki daga nan daddy ya gabatar da bukatarsa na Neman auren shuairat baba yayi shiru can kuma yace

"Alh da zaka bani lokaci zan...

"Haba Alh bello ai anzama daya, kuma yaran nan suna son juna tunda sun fito fili sun bayyana hakan.kuma shi yaron matarsa ta Dade da rasuwa munyi iya bakin kokarinmu ya kara aure amma Sam yaki, don haka ina rokonka ka taimaka ka bamu ya'rka tunda de sun daidaita suna kaunar juna"

"Alh Muhammad bawai zan hanaku bane, kasan shaanin yara"

"Haba Alh..Suleiman fah ba yaro mana shekarunsa 40 da doriya na tabbata xai rike ya'rka bisa gaskiya da amana , nidai burina ka amince mu sanya musu albarka kuma in son samu ne a daura auren nan da sati 2 masu xuwa"

"Ahhh..abun ma da wuri haka ne?

"Ehh mana..burina shine ka amince batun wani shiri koma menene bai taso bah ba se ansiya mata komai ba ni xanyi kayan daki da duk wani abunda zaa bukata na auren"

"Haba Alh Muhammad bazaayi haka bah"

"Alh bello bazaka gane farinciki da nake ciki bah, Suleiman shi kadai Allah ya bani a duniya burina shine naga ya tara min jikoki dayawa se kuma Allah ya kaddara matarsa ta haifi yara2 ta bar duniya.don haka nake son ayi wannan auren da wuri ko Allah zaisa da rabo a ciki"
Baba yayi shiru yana naxarin kalaman daddy

"Kayi shiru Alh bello, kada ka manta yanxu mun xama yan uwan juna fah " ya fada yana dariya baba yace

"Shikenan Allah ya tabbatar da alheri ya basu zuria ta gari masu albarka"

"Ameen yanzu naji magana! Nagode sosai ALh bello Allah yabar xumunci ya saka da alheri" nan ya xare bundir na yan dubu sabbi fil har bandur 3 ya ajiye a gaban baba

"Me wannan Alh Muhammad? Kaga abunda bana so kenan, ni ban nemi koda sisi ba daga gareku don Allah ka maida shi kuma auren nasu idan yazo bana son almubazzaranci a kimanta komi a yishi dai2 gwargwado nasan kuna da kudi amma ni bana son hakan"

"Alh Bello jahar mu daya da kai kasan al-adunmu na Adamawa idan anzo Neman aure da goro ake xuwa , nikuma ban siyeshi ba saboda ina marmarin xuwa don haka wannan kudin goron Neman aurene ba komai bah"

"Nasan da hakan Amma na yafe"

"Aa'a bazamuyi haka da kai bah alada CE dole sai anyi , batun almubazzaranci kuma insha Allah bazaayi bah na maka alkawarin hakan"

Baba ya xare bandir daya ya maida sauran yace

"Allah yayi albarka ya sanya alheri nagode"

"Sauran kudin fah Alh"

"No! Wannan ma yayi yawa kawai bana son gardama ne"

"Toh nagode sosai Alh bello se a fara shirin daurin aure nagode sosai"
Nan sukayi musabaha baba ya rakashi har bakin mota sukayi sallama driver ya ja a yayinda bash yake zaune a gefe Suka dau hanyar gidan mr President.


Hmmmmmm.muje xuwa
[2/21, 2:39 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*37*
By *Reefat yahya*


Shuairat tana xaune a ofishinsu ta buga uban tagumi wayarta CE ta hau ruri numban mama ta gani ckn mamaki ta daga sabida mama bata taba kiranta ba muddin tana wajen aiki
"Hello mamana"
"Baby kizo gida yanxu"
"Lfy dai koh?
"Kizo ina jiranki"
Ta kashe wayar tayi jugum se kuma ta tashi ta fara harhada takardunta bayan ta gama tayiwa Sarah sallama akan cewa ana nemanta a gida carab Suka hada ido da Mahmud yayi sauri kauda fuskarsa gefe

Please Login or Register in order to submit comment