Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

xaki saloon din baxan iya wahala ba, dubi idanuwanki kamar warce aka yi ma duka, ke ba yarinya ba ki dinga ma mutane ihun kitso" Khadijah ta kwanta kan kujera bata ce komai ba, Umma ta fita ta shiga kitchen ta dau indomie biyu ta fito, Hasana ce tace "Gaskiya Abban fadila ya dawo ya kasa ma kowa indomie ya ajiye a dakinsa tun jiya ake ta shiga ana daukar indomie abinda yaran gidan ma sai su yi sati basu ci ba, wnn ai mugunta ce" Umma tayi yar dariya bata ce komai ba ta shiga ciki, dama da kwai hudu ta dawo gidan, don haka ta girka indomien a daki ta dafa kwan ta tada khadijah da ta fara bacci ta bata nata sannan ta fita yin alwala, Da daddare yau ma kamar jiya a karamar cooler shafah ta aiko ma Umma abinci, Tea ta hada da yake tana da kayan shayin a daki ta fita da kanta ta siyo bread ta ba khadijah ta ci ba tare da ta bi kan yan gidan ba. A can katsina kuwa neman duniya kawu da matansa sun ma khadijah amma bbu ita babu labarinta, gidan da suka fara xuwa kuwa gidansu sadeeq ne, nan mahaifiyarsa ta nuna masu the other side of her don har sai da suka tsorata kuma tace kada warce ta sake shigo mata gida, har station kawu yaje da gidan radio, bai taba kawo wa cewa Umma ta san gidansa ba balle ta xo ta dauke khadijah, Duk da ba wai abun ya wani dame su Hajiya salaha da Hajiya maimuna ba amma ganin yanda mai gidan nasu ya dage yana nemanta yasa su ma suka xage, har shawara Hajiya salaha ta bada su kai karar Hajiya Amina da d'anta, kawu ya gwaleta cike da masifa yace "Kinsan waye uban yaron?" Hajiya Maimuna tace "Alkali" Kawu yace "Shine xata dinga magana kamar mahaukaciya?" Ita dai Hajiya Salaha bata ce komai ba. Washegari da safe Umma ta fita tare da Khadijah don sama mata islamiyyan da xata fara xuwa, bata yrda ta kai ta wanda yan gidan ke xuwa ba ta kai ta wani dake gaba da shi sosai, bayan ta biya komai ta wuce kasuwa tare da ita don yankar mata uniform daga can tayi mata siyayya kananun kaya. Da yammacin ranan Umma ta amshi girki, tuwon shinkafa da miyar vegetable take girkawa, Khadijah na xaune kan tabarma bakin kofar Umma tana cin gyadar da Umma ta siya mata a hanyarsu ta dawowa, da ta bare sai ta jefa ma wani kadangare dake tsakar gidan yana yawo bawon gyadar, tsawa taji an mata ta waiga da sauri Hasana da fitowarta kenan tace "maxa tashi ki tsince su don baki da bawa mai shara a gidan nan" Umma kallo waje tayi daga kitchen din bata dai ce komai ba ta ci gaba da girkinta, mikewa khadijah tayi ta isa gun da ta ke ta jefa bawon ta shiga tsince su tana xubasu a shara har ta gama, Hasana ta nuna mata wasu bola dake kusa da kofar Shafah wai taje ta tsince, Umma ta fito tace "Wannan kuma ne baki isa ba" kujerar da ke kusa da kofar kitchen ta nuna ma khadijah tace "Sit here" khadijah ta karasa da sauri ta xauna, Hasana ta rike ha6a tana kallon Umma bata dai ce komai ba. Umma bata bar khadijah ba sai da ta tabbatar ta yi bacci sannan ta tafi bangaren Abban Fadila, bata yi mamakin ganin kishiyoyinta ba a xaune parlorn, da kuma alamar yana shigowa suka bi sa don bai jima da dawowa ba, har Umma ta ajiye tray din abincin hannunta kallonta yake, ta xauna ta gaishesa, bai amsa ba yace "Dama kin taho da yarinyar nan ne don ki ci xarafin mutane Amina?" Umma ta kallonsa tace "Ban gane ba" yace "Toh daga yau kar ki sake nuna iko a kan ta Idan ba haka ba ki mayar da ita dangin ubanta, banda janyo yaro ya raina babba don me Hasana zata sa ta aiki ki hanata, akan me? Meye amfanin xamanta gidan idan baxa a ci moriyarta ba!" Umma dake saurarensa tayi murmushi tace "Tun da na shigo gidan nan cikin yaransu akwai warce na taba sa aiki ta min? Babu.... domin kuwa duk sun hanasu amma na taba kai maka kara? Ni wllh matan ka basu isheni kishi ba Alhaji, banda kaddara ba lallai su gan ni cikinsu ba balle su sa ni gaba, ina ce ni ka fara sani ma kafin su? Wllh basa gabana balle inyi kishi da su, marainiya ce dai na daukota sae dai bakin ciki ya kashe su tunda ba a kansu xata xauna ba" Tana kai wa nan ta fice daga parlon idan sun fita sai ta dawo. Ka'ida ce duk safiya a gidan su Fadila ne ke yin wanke wanken safe da sharan tsakar gida ko ma wacece ke girki kafin su tafi makaranta, yau kam suna tashi da safe wanka suka yi ko wanne ta tafi ta saka uniform, Umma bata ce masu komai ba tana ta soya dankalin irish da xa ayi breakfast da shi a gidan, Khadijah na durkushe kitchen din sai dai ta bude babban cooler a Umma ta xuba wanda ta soya, Umma ta gama soya Irish din da ta fere gaba daya ta soya kwai, kananun yaran gidan ne suka dinga tahowa karban nasu duk ta basu ko wanne sa cup din shayi da ta hada, Khadijah dake ta kallonsu tace "Umma why are they so plenty?" murmushi umma tayi tace "Just as the one ur uncles home" Khadijah ta langwabar da kai tace "Noo, they are nt as much as this" Fadila ce ta taho kitchen din tace "Anty ina kwana, ina dankalina" Umma ba tare da ta kalleta ba tace "Idan kin gama wanke wanken can xan xuba maki" juyawa tayi ta wuce sai ga Shafah ta fito, "Amina ban gane baxa ki ba Fadila kalachi ba, meye dalili" Ko tanka ta Umma bata yi ba, ta hau masifa tayi mai isarta daga karshe tace "Bar ta ita ce mayunwaciya Fadila, ta hada da Wanda ta ajiye ma kanta da agolar da ta kawo su cinye, mu je in baki kudi ki siya kosai da bredi a hanya, wanke wanken su shekara nan, in dai baxa ta ba ma agolarta tayi ba" daga haka ta wuce ciki Fadila na biye da ita a baya, daga Hasana har Shafah bbu warce tayi kalaci da girkin da Umma tayi, duk wainar shinkafa suka aiki almajiri ya siyo masu a makwabta, Umma kam ko a gyalenta, wanda ya rage ra kira almajirai ta basu ta hada kayan wanke wanke xata yi, Khadijah tace "Umma na iya wanke wanke fa yanxu xan yi" da kyar ta amince ta bar ta, Ganin yanda ta fara jika kayan jikinta Umma ta karbi kayanta ta shiga yi tace mata ta tafi daki ta kwanta. Da rana cous cous umma ta girka gidan d'an dai dai, daga ita sai khadijah a gidan don tun misalin goma su Shafah da Hasana suka fita basu dawo ba, ta dibar ma kananun yaran gidan a warmer ta kai can dakinta da miyar ta ajiye bayan ta xuba ma Khadijah, ta dawo ta tsaftace kitchen din ta wanke tukwanen da tayi amfani da su da utensils sannan ta koma ciki. Sai kusan karfe Uku su Shafa suka shigo gidan Hasana na cewa "Wash wajen nan ba dai nisa ba Maman fadila, na xata bai fi tafiyar minti talatin ba fa" Shafa tace "Nima farkon xuwa na na sha wahala sosai, ga hanyar bbu kyau mutum na mota kamar ya hau jaki duk jikina ciwo yake..." Shiru Umma taji sun yi suna kallon kofar ta, ita ke ganin su ta labule amma su basa ganinta, suka kalli juna basu dai ce komai ba, kitchen Shafah ta wuce, can sai ga ta ta fito tana kallon Maman walida tace "Ke kamar fa bata yi girki ba" Maman Fadila tace "Bata yi girki ba kuma? Kin ga uban yunwar da nake ji ga shi bani da kosisi kudin sun kare a kudin motar" Daga labulen Umma Maman walida tayi suka yi ido hudu, d'an kame kame ta fara da farko, sai kuma tace "Ba a da niyyar yin girkin rana ne yau a gidan nan ga yara su kusa dawowa" Umma tace "Ehh" sake labulen tayi ta bar wajen Maman fadila ta bi bayan ta, tana jin Shafah na jajjage a kitchen xa su dafa indomie, ita dai tana xaune inda take. Uku da rabi yaran suka dawo kuwa, nan Umma ta xuba ma kowa abincinsa ta ajiye masu tsakar gida, Shafah dake kan tabarma ta kalli kishiyarta dake bakin kofar ta ita ma a xaune, yaran suna gama ci suka fara shirin tafiya islamiyya, Umma ta sa Khadijah ta shirya cikin dinkekken uniform din da tela ta kawo mata daxu, sai murna take har ta gama shiryawa, har bakin makarantar umma ta rakata na ranan kadai sannan ta dawo gida. Umma na kitchen tana girkin dinner ta dinga jin kamar kukan khadijah, ta mike da sauri ta nufi kofar fita, su Shafah da Hasana dake xaune kusa da juna suka bi Umma da ido, a bakin kofa ta kusa cin karo da Khadijah ta riko hannunta tana kkrin cire Hijab din da ta rufe fuskarta tace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "Umma wannan yarinyar dake gidan nan ne ban mata komai ba na gansu a hanya, she just slapped my eyes and pushed me na fadi a kan wani dutse" Umma da ranta ya gama baci tace "Wace yarinya kenan?" Dai dai nan walida ta shigo fuskarta tsuke, Khadijah ta nuna mata ita tana shessheka, fixota Umma tayi ta wanka mata mari ta ja kunnenta tace "Don uwarki kika sake taba min 'ya sai na cire maki hakori wallahi, muguwa kawai mai halin banxa" daga haka Umma ta hankadata, walida ta fasa wani ihu kamar xata tsaga gida tana kiran uwarta. Mikewa Hasana tayi baki bude tace "Amina??? Ita walidar kika mara??" Umma ta juya tana facing dinta tace "An mareta, ki taho ki rama mata, d'a ya fi d'a ne, ai wllh duk shegiyar da tace 'ya ta baxa ta xauna lafiya ba gidan nan sai dai ita ta rasa xaman lafiya, me marainiyar ta maku? Ko ba a cin arxiki dama a duniya, kishin naku ya tsaya iya kai na mana, toh wllh duk ku ja ma 'ya yan ku kunne, duk wanda ya sake ko da yi ma khadijah kallon banxa ne, sai nayi masa abinda bai yi xato ba" tana kai wa nan ta tafi daki da Khadijah ta tura ta ciki tace "Maxa ki canxa kaya" daga nan kuma ta dawo kitchen ta ci gaba da abinda take rai bace, daga Hasana har Shafah haka suka bude baki suna kallonta bbu wanda ya iya cewa komai cikinsu. Da daddare Abban Fadila ya dinga kwalo ma Umma dake xaune kan darduma kira, ta mike ta fita don bata ma ji shigowarsa ba amma tuni har ya shiga parlon sa, bin bayansa tayi ta shiga parlon tana masa sannu da xuwa, bai amsa ba ta xauna ba tare da ta yarda ta kalli kishiyoyinta dake xaune parlorn ga Walida a durkushe a kasa, Abban Fadila yace "Amina, so nake xuwa gobe ki mayar da yarinyar nan dangin ubanta da kika daukota, I agree zan yi sponsoring dinta ko tana can din, idan ya so duk bayan watanni uku ko hudu sai ki je ki dinga dubata, I think that will better, I didn't buy d idea of her staying here anymore...." Tun da ya fara Umma ke kallonsa a sanyaye, Hasana da Shafah da aka wani hakikance kan kujera kamar wasu Hajiyoyi xa a iya ganin murnar dake shimfide fuskarsu, trying hard to control her tears Umma tace "Saboda me kace haka Alhaji? Kada ka mance yarinyar nan marainiya ce ba ta da kowa, tun tana yar shekara biyu mahaifiyarta ta rasu, mahaifinta kuma bai mata gatan nuna mata dangin mahaifiyarta ta ba, da na sansu da can xan kai masu ita baxan kawo ta ba gidan ka Alhaji" Abban fadila yace "Kiyi hakuri iyakar taimakon da xan ma yarinyar kenan, ko nawa ne kudin karatunta xan biya idan ya kama ma da feeding expenses duk xan ba da, kawai dai gidana ne baxata xauna ba, kuma baki min kara ba da har xaki daga hannu ki mari diyata a ido don abun su can ya hada su, so tafiyarta xai fi, I think that's all... Gobe ki hada kayanta ki maida ta inda kika dauko ta" Umma da hawaye ke xuba idonta a hankali tace "Ina jin da ka sauwake min kawai in tafi da ita xai fi don ni baxan mayar da ita dangin mahaifinta ba" yana gyada kai yace "Kema xa ki iya sauwake ma kanki ai Amina ba sai na sauwake maki ba" mikewa Umma tayi ta fita ta koma bangarenta, ta shiga daki tayi kukanta mai isarta, duk tausayin khadijah ya cika xuciyarta, to yanxu ina xata kai marainiyar nan, ita ba ta da kowa mahaifiyarta ta rasu da sai ta kai ta gun ta tasan xata rike mata ita, bata da wani abun hannu don duk cutar ta yayyin mahaifin khadijah suka yi a rabon gado bayan ya rasu, domin kuwa kafin a ankare sun boye abubuwa da dama cikin dukiyarsa, banda haka da ko boarding sai ta kai khadijah, har gari ya waye Umma bata ritsa ba tana ta tunanin inda xata kai khadijah domin ta ma kanta alkawari first thing da safe xata fitar da ita da gidan, yayarta warce suke uba daya dake Kaduna ta fado mata ta yi shiru tana naxari.

Daukar waya Umma tayi ta shiga kiran layin step sister dinta Yakumbo amma baya shiga alamar dai wayar a kashe yake, da safe bbu abinda ta girka ma mutan gidan a madadin breakfast, ta dai hada ma Khadijah tea ta siyo mata bread ta bata, Karfe takwas ta shiga bangaren mai gidan nasu ta sanar da shi xata mayar da Khadijah gida, ya kirgo dubu biyar ya mika mata yace "Gashi ku yi kudin mota, idan kin dawo sai a san yanda xa ayi batun makarantar nata in ji ko nawa ake biya" Umma ta girgixa kai tace "A'a ka bar shi mun gode Alhaji, muna da kudin mota" Yace "Shi kenan, Allah ya tsare" mikewa tayi ta fita dakin, a cikin wata karamar jaka Umma ta hada ma Khadijah d'an kayan da ta fara siyo mata, suka fito parlor ta sa ma kofar kwado bayan ta rufe, khadijah dake sanye cikin doguwar riga da karamin Hijab tace "Umma ina xa mu?" Umma ta kasa kallonta tace "Xa mu d'an yi tafiya ne khadijah" daga haka ta kama hannunta suka nufi kofa, tana jin su Shafah da Hasana na dariya suna cewa "Toh a sauka lafiya, sai a kara gaba can da ita" ita dai bata tanka su ba har ta fita. Tasha suka tafi cikin a dai dai ta, can suka samu motar Kaduna, bayan wani lokaci motar ta cika suka yi set off xuwa Kaduna garin gwamna... Ko barin kano basu yi ba khadijah tayi bacci jikin Ummanta, har suka isa Kaduna bata tashi ba, suna isa kawo bayan driver yyi parking kowa ya fara alighting daga cikin motar, Umma ta tada khadijah suka sauka su ma, sai kalle kalle khadijah take tace "Umma where is this?" umma tace "Kaduna" Khadijah tace "Wow I've heard of Kaduna in school" Umma ta samar masu napep suka yi ciniki sannan suka shiga xuwa hayin rigasa Unguwar da yakumbo take, tafiya ce mai nisa kafin su iso rigasa, da yake Umma sunan layin kadai ta sani ba wai ta wani san gidan yakumbo bane a bakin layin tasa mai napep din ya sauke su ta basa kudinsa tana rike da hannun khadijah suka shiga layin umma na bin ko wani gida suka xo wucewa da kallo don ta haka kadai xata gane gidan yayarta kasancewar ta jima bata xo wajenta ba, sun fi minti talatin suna bulayi a layin, Khadijah sai tambayarta take "Umma where is this, everyway is dirty, they are smelly gutters everywhere" Umma tace "look I don't want to here ur mouth again" shiru khadijah tayi, daga karshe dai wata mata da ta gansu suna ta yawo ce ta tambayesu gidan da suke nema, Umma tayi shiru tana tuna sunan da aka fi sanin yakumbo da shi, can tace "Kulu mai waina" Matar tace "Ikon Allah, yo ai ga gidan can kun wuce" Umma ta juya tana kallon gidan da matar ke nuna mata, matar tace "Wancan gidan mai keke a gaban sa" Umma tayi murmushi tace "Kin ga kuwa sai yanxu na gane, gaskiya na nagode sosai" daga haka suka juya khadijah na biye da ita a baya, tsallake gutter din dake kofar shiga gidan Umma tayi Khadijah ma ta yi haka sannan suka shiga xauren gidan, gida ne ginin kasa duk ya kwarabe, Khadijah ta xaro ido tana bin gidan da kallo, Yakumbo ce xaune tsakar gida tana hura icce duk hayaki ya cika ko ina, Umma tace "Yaya" dagowa yakumbo tayi ta xaro ido tace "Aminatu" karasawa Umma tayi ta rungumeta tace "Rai kan ga rai yaya" cike da farin ciki Yakumbo tace "Sannu da xuwa Amina, daga ina haka? ya mai gidan naki?" Umma tace "Wllh daga kano Yaya, yana nan lafiya yace duk a gaida ku" Yakumbo tace "Maa sha Allah sai dai kin rame kan lokacin bikin, wacece wancan" Yakumbo ta fada tana nuna Khadijah, A hankali Umma tace "Yar marigayin mijina ce Alhaji Muhammad" Yakumbo ta rike haba tace "Ikon Allah gashi ta kusa xama budurwa, sun hakura sun baki ita kenan?" Umma tace "uhn, labari ne me yawa yaya bari dai mu yi sallah" Yakumbo tace "Gaskiya ne bari in kawo maku ruwa" tabarma ta fara shimfida masu kafin ta tafi debo ruwan alwala, Umma ta xauna ta nuna ma khadijah dake tsaye gefenta, khadijah ta karaso tana tsattsallake bololin dake watse tsakar gidan, Umma tace "yaya ina mutan gidan?" Yakumbo tace "Toh jikokin nawa sun fita wasa, tun safe rabona da su, yaran makwabtana kuma duk sun tafi talla, iyayensu kuma aikatau suke na yini, Ladi ce kadai ta shiga makwabta daxu, nima anjima xan fita suyan wara da dankali a bakin titi" shiru Umma tayi jikinta yayi mugun sanyi, yakumbo ta kara da cewa "Ai Allah ma yyi ban tashi a gidan nan ba kika xo, don duk mai gidan ya ba mu notice xai rushe gidan wai, to gida ne duk ya rube" Umma ta kalleta da sauri tace "Ina xa ku koma yaya?" Yakumbo tace "Oho dai har yanxu ina lalube ne, kudin kama wani gidan ma ai xaune yake da kugunsa, talauci yyi yawa ta ko ina, ko daxu na fita duba gida don sati daya ya ba mu xai watsar mana da kaya waje" Umma tace "Ikon Allah" Yakumbo tace "Ai ke dai kawai sai du'a'i duniyar ta xama abinda ta xama" Yakumbo ta kalli khadijah da ta takure gu daya tace "ke yar nan tashi ki fita waje gun mai kanti ki siyo min farin maggi" Umma tace "Yaya ai bata san ko ina ba" Yakumbo tace "Ka ji ki, nan nan ga masu kanti kamar jampa a jos ta ko ina a anguwar nan, tana fita duk inda ta bi akwai mai kanti" daga haka Yakumbo ta kunce kullin xaninta ta fiddo wani naira ashirin dake a dunkule ta jefa ma khadijah, mikewa khadijah tayi ta karasa ta duka ta dau kudin tana kallon Yakumbo tace "How much own" yakumbo ta d'an bude ido tace "Eh??' Umma tace " twenty naira" khadijah ta juya ta fita, yakumbo tace "Sai na ji kamar yare tayi" Umma tayi murmushi tace "Turanci tayi" Yakumbo tace "Au tohhh abun na manya ne Ashe" ita dai Umma bata ce komai ba ta mike taje tayi alwala ta dawo tayi hau kan tabarman ta tada sallah, jin shiru shiru Umma na idarwa ta bi bayan khadijah, a bakin xaure suka kusa cin karo Umma tace "Ina magin kuma me ya sa kika dade?" Khadijah tace "Umma I've forgotten the one she mentioned" Umma ta hade rai tace "Bani kudin" mika mata khadijah tayi ta umma ta koma ta dau dari a Jakarta ta fita, farin magin hamsin ta siyo mata da maggi star saba'in sannan ta dawo gida, garau garau na dafaduka Yakumbo ta girka masu, ta xubo a faranti. Umma kadai ce ke cin abincin a sanyaye tana tausayin khadijah dake tsintar shinkafar, yakumbo kuwa na ta yankan warar da xata fita soyawa kamar yanda tace suna yi suna hirar xumunci da yar uwarta, la'asar nayi Yakumbo ta kira almajiri ya kai mata kayan bakin titi gun da take suyar, Tana kokarin saka Hijab dinta da yyi dukun dukun tace "Toh Amina xan fita kasuwa, idan kun ji yunwa ku kara deban abincin, sai ki d'an taimaka ki share min daki ki fiddo kayan wanke wanken ki ajiye su bakin kwararon can ko yarinyar nan ki sa tayi" Umma tace "Toh yaya, amma fa har yanxu yaran basu dawo ba" Yakumbo tace "Rabu da gantalallu suna makwabta na sani, idan yunwa ta kwakulesu xa ki ga sun dawo da daddaya da daddaya" daga haka yakumbo ta fita rike da roban dake dauke da dankali a ruwa, Umma ta bi ta da kallo, Khadijah ta yatsine fuska tace "Umma the food is somehow" Umma ta hade rai tace "Haka nan xa ki ci, ko ni ma baki ga hakan na ci ba" Khadijah bata ce komai ba, Umma ta mike ta shiga d'an karamin dakin yakumbo, har wani wari dakin yake gashi bbu ventilation don windown dan karami ne, ga kaya ta ko ina, plastern dakin duk ya faffashe gashi ko leda babu, jikin umma yyi sanyi ta daga dan karamin katifar da tayi bakikirin ta shiga gyaran dakin ta fidda duk kwanukan da har da funfuna jikinsu sannan ta fara sharan dakin. Ko da ta fito bayan ta gama bacci ta tarda khadijah na yi, ga shinkafar ta bar sa, Umma ta tada ta ta bata Dari biyu tace "Kije kantin da kika je daxu ki karbo Nutri milk da biscuit din hamsin ki xo ki ci" Karba khadijah tayi ta fita. Sai kusan karfe biyar jikokin yakumbo uku suka dawo gidan sun yi dukun dukun da dirty, duk kanana ne yaran, Umma ta masu wanka da sabulun wankin da ta gani, ta xuba masu abinci, Khadijah dai na xaune sai kallonsu take da wani expression, nama Umma ta fita ta nemo a anguwar ta xuba masu kan abincin ko khadijah xata ci, nan ta tsince naman ta bar mata shinkafar wai ta koshi, sai dab da Isha yakumbo ta shigo gidan tare da Almajiri da ya dauko kayan suyanta, Sannu ta dinga ma su Umma, Umma ta mike ta taya ta karban kayan.... sha dayan dare bayan su khadijah sun yi bacci Umma ta shiga yi ma Yakumbo bayanin abinda ya kawo ta da Khadijah, bayan yakumbo ta gama saurarenta tace "Ikon Allah, mugunta fa yyi yawa a duniyar nn yanxu ki kuluwa" Umma tayi shiru bata ce komai ba, Yakumbo ta kyabe baki tace "Toh ni wannan ai ba matsala bace, don dai in rike marainiya, bakomai wllh" Dubu 30 Umma ta kirgo ta ba yakumbo tace "Wannan sai ki siya kayan abinci da indomie ki ajiye yaya" makaranta kuma ayi mata Register da ta gwamnati idan Allah ya hore min sai in canxa mata, dubu ashirin ta kuma bata tayi ma khadijah siyayyar makaranta, yakumbo ta dinga godiya kamar ita ta ba kudin, sai kusan karfe daya suka kwanta bayan yakumbo ta gama tsine ma matan mijin Umma, da su kawu. Washegari da safe Umma ta dau hanyar kano bayan ta rubuta ma Yakumbo lambarta kan cewa duk inda suka koma ta sanar da ita in case xata dawo duba khadijah, dubara aka ma khadijah aka aiketa daga nan Umma ta

1 Comments On NOOR AL HAYAT
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls inason novel dinnan cplt

Please Login or Register in order to submit comment