Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi ta dauke glass cup din da abincin da ta kawo ta kai kitchen, ta mayar da box din 1st aid din daki, tayi disposing alluran da tayi masa sannan ta xauna kusa da shi tana kallon sa, giransa kadai ma abun kallo ne a fuskarsa kafin a xo ga long lashes din idonsa, a hankali ta sauke idanuwanta kan dogon hancinsa da ko Kadan bai da miskila xuwa bakinsa, kai kana ganinsa kasan duk yanda aka yi yana da alaka da larabawa, dauke idonta tayi tana wasa da fingers dinta, da sauri ta tashi tunawa da tayi bata yi isha ba, alwala ta sake yi ta gabatar da sllhn nan parlor, tana xaune tana azkar wayarsa ya fara ring, har ya katse bata mike ba shi ma kuma bai ko yi motsi ba, ganin an sake kira ta tashi a hankali ta nufi kusa da shi ta durkusa tana laluban aljihunsa ta fiddo wayar tana kallon screen din, Jawahir ta gani jikin screen din wayar, har ya katse tana kallon wayar, can ta ajiye a hankali ta daura chin dinta bisa gwiwowinta tana kallonsa, bacci yake sosai, ta so tashi ta wuce apartment dinta amma ta samu kanta da kasa yin hakan, bayan minti kusan ashirin ta dago kanta ta jinginar kusa da shi, daga haka bacci yyi gaba da ita a yanda take, A hankali ya bude idanuwansa yana bin parlorn da kallo, lkci daya idonsa ya sauka kanta, ya mike xaune da sauri yana kallonta, kallon agogo yayi yaga biyu har yyi, fuskarsa ya kai dai dai nata, cikin bacci taji hannu a forehead dinta, ta bude ido da sauri, a hankali ya manna mata lips dinsa a kumatunta, a tsorace ta ja baya xata mike yyi saurin riketa, 6ata fuska tayi hade da buge hannunsa tace "Meye haka" sakkowa kasa yyi yace "Me kike yi a nan?" Sakin baki tayi tana kallonsa, can ta turasa xata mike ya ki saketa, hawaye ya cika idonta tayi da ta sanin kulasa ma da tayi, ya jawota jikinsa yana murmushi a hankali yace "Thanks for ur care Khadija, Neva knew you where this sweet...." Ta kara hade rai tace "Sake ni malam" ba musu ya saketa, ta mike ta nufi kofa, yace "Uhn.. it's pass 2 now fah" da sauri ta kalli agogo, dawowa tayi kamar ya fada mata mugun abu ta marairaice tace "Lahh ban sani ba... I don't know it's late...." yace "Wait... But... But it seems u came with food daxu, ina abincin" da kamar baxata ce masa komai ba sai kuma tace "yana Kitchen" yace "I am just hungry" kitchen ta wuce ta kawo masa abincin sai a sannan ta tuna ita ma bata ci abincin ba ai, tashi yyi ya shiga toilet din dakinsa sai da ya wanke bakinsa yyi wanka snn ya fito sanye da jallabiya yana goge gashin kansa da karamin towel, duk ta gaji da jiransa ya fito ya rakata, ya xauna ya bude abincin ya dau cokali ya fara ci, kallonsa take ta yi kafin ta mike ta tafi ta bude fridge ta dauko masa ruwa, sai da ya kusa cinye abincin ya sha ruwa sannan ya kalleta da sauri yace "But daxu kamar ruwan tap kika bani koh" tace "Uhn" xaro ido yyi yace "Subhanallah, but I don't take...." sai kuma yyi shiru, ita dai bata ce komai ba banda hararansa da take, jinginar da kai yyi da kujera ya lumshe ido, mikewa yayi ya shiga bathroom din parlor ya fito da alwala, a hankali tace "Ka raka ni pls dare yyi sosai" kallonta yyi kafin yace "Ohk as you wish tunda cinye ki xan yi a nan" daga haka ya nufi kofa tana biye da shi a baya, yana bude kofa ta matsa kusa da shi da sauri, ya fita tana biye da shi a baya suka shiga apartment dinta ya rufe kofar, ta sauke ajiyar xuciya tana bin parlon da kallo yace "Toh tafi ki kwanta" daki ta nufa yyi saurin cewa "Waittt... Xo ki kulle kofar tukun" dawowa tayi tana kallonsa ya buda ido yace "Sai da safe, I appreciate ur care" bata ce komai ba xai fita tace "You have.... A call" ya juya ya kalle ta, duk sai taji she sounds stupid, yace "Did you pick?" Tayi saurin cewa "Nooo, I just remembered now, I didn't even check, just heard the phone ringing" ita kanta tasan kame kame kawai take, yayi murmushi yana shafa lallausan gashin kansa.

12...

Da asuba tana kitchen ta gama goge goge xata hada breakfast taji muryarsa ta waje yace "Morning" da sauri ta kalli direction din window taga bata hangosa ba, ta leka a hankali taga gym yake, ta bar gun da sauri ta ci gaba da hada ingredients din da xata soya eggs din da xata yi toasting da bread kasancewar bata yi da raw eggs, bayan wasu mintuna tace "How you feeling now?" bai amsa ba shi ma, hakan yasa ta juya ta kalli window direction, dai dai lkcn da ya iso kusa da window din kenan suka hada ido ya karyar da kai yana kallonta daga sama har kasa, juya baya tayi da sauri don rigar bacci ne jikinta, yace "Uhn... You look cute in that..." mamaki ne ya cikata ta kasa juyowa, ya ce "Ki shirya xaman gidan ya isa haka ki tafi makaranta yau koh" daga haka ya bar wajen, ko bai fada mata ba dama tayi niyyar tafiya makarantar yau. Karfe tara ta fito cikin shirin tafiya makaranta, fitowa yyi ya tsaya bakin door dinsa yana kallonta yace "Makarantar xa ki tafi yanxu?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Yeah" yace "Alright you wait for me" daga haka ya koma ciki, k'asa wucewa tayi tana ta tsaye wajen har ya fito rike da makullin motarsa, as usual kananun kaya ne jikinsa, kallo daya tayi ma wandonsa ta dauke kai a ranta tace aiki, yace "to mu tafi" parking space ya nufa ta bi bayansa, sai da ta jira yyi warming motar sannan ta bude ta shiga. Haka kawai gabanta ke faduwa ta rasa dalili, idonsa na kan titi yana driving yace "Do you have problem with anybody here?" Ta kallesa da sauri, shi ma ya kalleta, mayar da dubansa yyi kan titi, tana girgixa kai tace "I don't think it's any of ur concern" shiru ya d'an yi kafin yace "Ohk then" bai sake ce mata komai ba har ya isa makaranta, bata yarda sun hada ido ba ta bude motar ta fita tace "Thanks" daga haka tayi wucewarta. Tafe suke da course mates dinta bayan sun fito lectures din karfe goma da suka shiga, cafeteria suka nufa ita kuma tace masu xata je library karatu, bayan sun rabu bata je library din ba, kawai she want to be alone ne dama, guri me shiru ta samu ta xauna ta tsura flower dake wajen ido, ta kusa minti talatin a wajen kamar ance ta dago suka yi ido hudu da khaleel dake xaune d'an nesa da ita da wata baturiya dake karatu ita ma, mikewa yyi bayan sun hada ido yana kallon baturiyar yace "Stephanie c yah later" mikewa khadijah tayi ta riga sa barin wajen. Da safe misalin karfe takwas ta fito apartment dinta, yau dai kam ta makara sosai, tsaye ta gansa parking space waya kare kunnensa, suna hada ido ya dauke kai, ita ma bata sake kallonsa ba har ta fita daga gidan a xuciyarta tace "Can ta matse maka" Ita kadai ce xaune Cafeteria bayan sun gama lectures din ranan, Vanessa tuni ta bi saurayinta suka tafi tun bayan da suka gama cin abinci, ita kanta ta rasa me yasa ta ki barin gun har lkcn gashi tana son wucewa, chatting take da kawarta Salima dake Nigeria a WhatsApp kanta a duke, kamar ance ta daga kai tayi still ganin wa enda suka shigo Cafeteria din, a hankali ta saki wayar hannunta ya xame ya fada kan cinyarta, da sauri ta kauda kai xuciyarta na mugun bugawa, table dake gefen nata ya xauna kan kujerar shi da Baturen da suka shigo wajen tare, cikin sanyin muryarsa yake cewa "I don't have intentions of coming here frank, let be fast" baturen yace "Yeah, they will be here soon..." baturiyar dake tsaye kansu ta mika masu takardar list din abinci dake hannunta, muryarsa ya kuma dakan codon kunnenta da accent din turawa yace "Number 6 content for my frnd, just table water for me....." Kamar ana tilasta sa yyi maganan, a hankali khadijah ta mike kamar an xare mata abu a ciki, tana boye gefen fuskarta da mayafin kanta ta nufi kofar fita sum sum tana hade hanya, satan kallonsa tayi suka yi ido hudu don bin ta da kallo yyi, lkci daya ya mike ya xaro ido yana kallonta, tana ganin haka ta kwasa a guje, bin ta yyi da sauri yana cewa "Imannn..... Imannn plss wait, Iman....." hankalinta bai gama tashi ba sai da taga bin ta yake tsakaninsa da Allah gashi ya kusa kamo ta, ta jefar da takalman kafarta da jaka ta fashe da kuka sosai, gudu take kamar her life depends on it, tana yi tana waiwayowa a tsorace, Gani tayi wasu wanda da alaman Africans ne sun rikesa suna tuhumarsa me yasa yake bin ta, hakan ya kara mata kwarin gwiwan gudun, taxi ta samu ta shiga tana waige waige muryarta na rawa tace "Bridge street" tuni mai cab din ya ja suka dau hanya, lumshe ido tayi hawaye masu xafi na sakko mata, tana son fashewa da kuka ko xata ji dadi amma tayi controlling kanta ganin inda take, number gidan ta gaya masa bayan sun kai yyi parking ta bude motar ta fita, tunawa tayi bbu kudin da xata basa, tana kallonsa a sanyaye tace bari ta shiga ta dauko masa kudi, a hankali take tafiya compound din tana goge hawayen dake sauko mata, dai dai fitowar Khaleel part dinsa rike da makullin mota da wasu takardu, tsayawa yyi yana kallonta daga sama har kasa mamaki dauke fuskarsa, hade rai tayi sosai ta turo baki ta dauke kai ta kuma ki motsi daga inda take, taku daya biyu ya iso gabanta tayi saurin barin gun, fixgota yyi ta fashe da matsanancin kukan dake cin ta tun daxu, da mamaki yace "What's wrong with you, me ya faru? where are you coming from?" Kin cewa komai tayi sai kukan da take yi sosai, damuwa ne sosai fuskarsa yace "Talk to me plss, me ya same ki?" Ta hadiye kukan da kyar tana share hawayen idonta cikin rawar murya tace "Ban ba mai Cab kudi ba...." Kallon gate yyi, can ya sake ta ya fita, Durkushewa gun tayi ta dinga rera kuka xuciyarta na mata xafi, a haka Khaleel ya dawo ya sameta, ya hade rai yace "malama tambayar ki nake where r u coming from" mikewa tayi tana share hawayen idonta har lkcn bata daina kukan da take ba xata bar wajen ya rikota yana mata wani kallo a d'an tsawace yace "Me aka maki nace, where r u coming from?" Ganin ba magana xata yi ba yana rike da hannunta ya wuce part dinsa da ita, xaunar da ita yyi kan kujera a parlor ya duka gabanta yana kallonta cikin sanyin murya yace "Now tell me what happen" cike da karfin hali tace "Nothing" ido ya xuba mata bai sake cewa komai ba, can ya mike ya koma bayan kujera ya rungume hannu ya tsaya yana kallonta, ta gama cin kukanta ta jinginar da kanta da kujera, tafi minti sha biyar a haka bbu kalan tunanin da bata yi ba har bacci ya dauketa. Shi kam yana tsaye har lkcn bayan kujera yana kallonta yana mamakin irin taurin kanta, sai da ya ga bacci ya dauketa sannan ya xagayo ya iso gabanta ya durkusa kusa da ita, shi dai ya san tausayinta kawai yake ji har ransa, though he don't know her that much but he knows she's pained, coz she looks so, lumshe ido yyi ya bude yana kallonta, Khadijah is just the definition of cool Beauty, tall.... fair.... Slim with a perfect shape, Best of all she have got d most sexiest lips and eyes, her nose..... Kauda tunanin yyi, a xuciyar sa yace not as beautiful as Jawahir, a hankali ya mike ya dafata da xumar yace mata ta kwanta, a firgice ta farka tace "Aliyuuu...." Ja baya yyi yana kallonta. Da kyar ta karashe bude idonta da yyi mata nauyi ta daga kai tana kallon sa, xamowa kasa tayi a hankali, ya mike ya rungume hannayensa yana kallonta a ransa yana nanata sunan da ta kira, tashi tayi ta runtse ido ta juya xata fita parlorn, murya can kasa yace "Malama" sake juyowa tayi, yace "Where are u coming from" bata iya ta kallesa ba cikin sanyin murya tace "School" yace "Me ya same ki a can?" Tace "Am not feeling fine" bai sake cewa komai ba ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita. Magungunan ta ta dauka ta sha lkci daya kuma bacci ya dauketa, bata farka ba sai da asuba shi ma ta dalilin yunwa, ganin lkcn sllh bai karasa ba ta shiga kitchen don neman abinda xata ci, motsi ta dinga ji a waje ta leka a hankali, gym ta gansa yana yi jikinsa sanye da 3qtr kadai, suka yi ido hudu tayi saurin barin gun, parlor ta koma ta dauko Hijab ta sa sannan ta dawo kitchen din, har ta gama abinda xata yi bata sake leka waje ba, ta koma parlor da Indomien ta, tun da tayi wanka bayan tayi sllh gabanta ke ta faduwan xuwa schl gashi tana da test, hawaye ta dinga yi duk xuciyarta tayi rauni, gaba daya xaman kasar ya isheta taji gida take son komawa, to karatun fa, shekara bai kai biyu ya rage mata ba, danna bell aka yita mike a d'an tsorace, don ynxu kam gaba daya a tsoracen take, hijab ta saka ta fito, a hankali tace "Yes?" Yace "How you" bude kofar tayi ta gaishesa, yace "Baxa ki schl din bane yau?" Kamar xata yi kukatace "Ban sani ba" kallonta kawai yake bai ce komai ba, bayan yan sakwanni yace "Toh ki shirya, I am waiting for you" daga hka ya juya ta rufe kofar. Har dept ya ajiye ta, kowa ya ganta a lkcn yasan a tsorace take, yace "Yaushe xa ki gama lectures din?" Tace "Quiz ne" yace "Shi kadai?" Kai ta gyada masa, yace "ohk am around I will call ltr in ji ko kun gama" buda masa hannu tayi tace "Jakar ya fadi jiya ai" Kallonta ya tsaya yi, can ya ciro waya aljihunsa ya mika mata yace "I will call" ta karba tana gyada masa kai, daga hakata fita motar, shi ma ya fito yace "I think I will leave the car here" bin satayi da ido har ya wuce kafin ita ma ta bar wajen da sauri.

*Haske Writers Association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

_Khaleesat Haiydar_📚✍🏻

13....

Bata yarda ta fito dept ba tun bayan gama test dinsu, duk gaba daya a tsorace take, gani take kamar at anytime xata iya ganin Aliyu a gabanta, karfe sha daya da qtr wayar khaleel dake Jakarta ta fara vibrate, fiddowa tayi taga Emoji biyu na love gaban screen din, ta yi jim don bata san ko shi bane, har ya kusa katsewa sannan ta daga ta kai kunne tayi shiru, muryar mace taji tace "Hello Baby...." hakan yasa ta katse wayar, sake bugowa tayi bata daga ba har ya katse. Tana ta xaune da wani course mate dinta dake second degree dinsa d'an Nigeria but residing in Malaysia yana ta mata hira ita dai sai dai tayi murmushi tana saurarensa, dai dai nn wayar hannunta ya sake vibrate ta daga tana kallon number, sai kuma tayi picking ta kai kunne, daga daya bangaren taji yace "Are you done?" Tace "Umm" yace "Aiitt am waiting..... Near the car" daga haka ya katse wayar, ta mike tana kallon course mate dinta tace "Wanda xai daukeni yana jirana, xan tafi" ya mike shi ma yace "To bari in raka ki" da kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "Ohk" tana gaba yana biye da ita har suka iso gun motar, Tun daga nesa Khaleel ke kallonsu, sai da ya ga sun iso ya dauke kai, Usman yace "Assalamu alaikum" sake juyowa khaleel yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma ya bude motar ya basa hannu suka gaisa, Khadijah ta tabe baki ta xaga daya side din motar tana kallon Usman tace "Thanks.... sai gobe in sha Allah" Usman yace "Aiiit Allah kai mu lfya" Sallama yyi da khaleel sannan ya wuce, Khaleel ya tada motar suka bar wajen, har suka hau kan titi bai ce mata ba, ita ma bata ce masa ba, wayarsa dake hannunta ya fara vibrate kuma, kallon screen din tayi taga number daxu ce ta mika masa, sai da ya kalli screen shi ma kafin yyi parking gefen titin, ya jira wayar ya katse sannan ya kira yace "How you...." Satan kallonsa khadijah tayi ta dauke kai tana kallon waje, bayan yan sakwanni yace "Like serious, alryt sorry for that wayar baya gu na ne" d'an murmushi yyi yana shafa lallausan bak'in gashin kansa dake sheki yace "I left the phone with a frnd, and I guess....bata san ke bace da baxata dauka ba, yanxu dai I will cal back in 10 mins time, I am on the road" daga haka ya katse wayar yace "Why did..... You pick her call?" Kamar me counting words din yyi maganan ya juyo yana kallonta, bata kallesa ba bare ta basa amsa, hakan yasa ya ci gaba da driving dinsa, sai da suka kusa gida yace "Who was that guy?" Ta juya tana kallon sa da kyau tace "And why are you asking?" Tabe baki yyi bai ce komai ba, sai da yyi parking ta hade rai tace "Da Kasan da xata kiraka ka bani wayar" daga haka ta juya xata bude motar ta fita yasa lock, juyawa tayi tana kallon sa, yace "Ki dai bi a hankali da guys din makaranta da kike kulawa, and you even let him accompany you to where I am, toh ni meye hadina da shi?" Mamaki ne ya cika ta ta saki baki tana kallon sa, a mugun fusace tace "Ina ruwanka ma idan na bi samarin makaranta, I guess it shud be none of ur concern, let me outta here immediately.... Ka bude min mota in fita" Tun da ta fara ya kwantar da kujeran motar ya lumshe ido yana saurarenta, jin tayi shiru ya dago kujeran ya xauna yana kallonta yace "Kin gama?" Ta dago tana kallon sa ranta na suya, bude lock din motar yyi yace "Ok then, kindly move out and close d car door behind you" bude motar tayi kamar xata tashi sama ta nufi apartment dinta ba tare da ta kulle masa motar ba. Wayan da tayi ta yi da su Shuraim yasa ta mance duk damuwar dake tare da ita, ganin lkcn kwanciyarsu yyi tayi sallama da su ta kwanta don tayi shirin bacci tun bayan da tayi sllhn magrib, lkci daya baccin ya dauke ta. Tun da ta tashi take ta tunanin yanda xata tafi schl don kusan tests suke, tunanin hakan yasa ta rushe da kuka tace "Do I ever have to meet with him in my life again??" Ganin lkci na ta wucewa ta mike a sanyaye ta dau jakarta da mayafi ta fita parlor, kallo daya tayi ma motar khaleel dake parking space ta hade rai ta dauke kai ta rufe apartment dinta, a hankali take tafiya har ta isa titi, cab ta shiga suna isa makarantar ta biyasa kudinsa ta fito tana kalle kalle kamar munafuka, tafiya take da sauri ta shiga schl don a waje ta sauka daga cab din, kawai mota taga ya tsaya gefenta bata ankara ba sai ganinta tayi cikin motar ta fasa ihu a tsorace amma tuni aka ja motar. Khadijah ta bude idonta a hankali ta na bin parlorn da take ciki da kallo, ta mike da sauri xuciyarta na bugawa tana kiran Allah a xuciyarta, kamar ance ta juya bayanta ta ga mutum tsaye yana kallonta, xuciyarta tayi mugun bugawa tayi saurin dauke kanta, karasowa yyi parlorn cikin sanyin murya yace "Imannn" bata san lkcn da ta xube wajen ba ta fashe da wani matsanancin kukan takaici, durkusawa yyi gabanta a hankali yace "Imann... I...." Mikewa take son yi ya rikota fixge hannunta tayi da karfi, yyi still yana kallonta ko kiftawa bbu, tayi saurin dauke kai tana kuka sosai ta hade kai da gwiwa, mikewa yyi ya dago ta yyi hanyar wata kofa da ita, tashin hankalin da ba a sa masa rana, ihu ta sakar masa tana turasa amma da yake karfinsu ba daya ba sae da ya shigar da ita kofar ya rufe, cikin rawar murya take cewa "Me ka dawo yi rayuwata kuma Aliyu, I am no longer under you or ur family, let me plsss am begging you in the name of Allah, ka rabu da ni......" Jinginar da ita yyi da bango yana kallonta da idanuwansa da suka kada yace "Kinsan shekarun da na dauka ina neman ki xa ki ce in rabu da ke" a tsawace ya kare maganan, cakumosa tayi tace "Kana nemana?? in maka me Aliyu? Neman me kake min, ka rufa min asiri ka kyaleni in tafi don Allah" yyi wani murmushi yace "In kyale ki ki tafi? Haka kawai in kyale ki ki tafi?" Turasa tayi iya karfinta amma ko gezau ta kuma fashewa da matsanancin kuka xuciyarta na mata xafi da suka, cikin kuka sosai tace "Aliyu ba don ni ba kayi hakuri ka kyaleni" yana kallonta a hankali yace "Ki yafe min Iman...." Tsayar da kukan da take tayi tana murmushin takaici tace "In yafe maka? Aliyu dama kayi min wani laifi ne da xan yafe maka, gaskiya ban san shi ba, idan ma akwai to shari'armu sae a lahira" finciko ta yyi da idanuwansa da suka yi mugun kadawa yace "A lahira?" Kasa amsawa tayi ganin ynda ya sauya kamannin fuska, jefar da ita yyi kan gado ya karaso yana mata wani kallo yace "Wani Shari'ar ce sai mun je lahira xa ayi ta? Ki fadi me nayi maki?" Ta dinga ja baya tana ganin dishi dishi, a hankali ta kira sunansa tana girgixa kai daga nan kuma bata sake Sanin abinda ya faru ba ta dai bude ido a hankali ta dalilin axaban da xuciyarta ke mata, Kwance ta ga ta kan gado ita kadai dakin, da kyar ta mike xaune ta dafe xuciyarta, lkci daya ta sauka gadon ta nufi kofarta bude taji a rufe da key, sulalewa kasa tayi ta dafe kirjinta tana kiran Allah a xuciyarta, bude kofar taji kamar ana yi ta tashi tsaye da sauri ta koma bayan kofar ta tsaya aka bude ya shigo cikin dakin yana kalle kalle, da gudu ta fice dakin ya juya da sauri, bin bayanta yyi yana kiranta, ganin bbu inda xata tsira parlorn ta nufi dinning table ta dau wukar da ta gani kai ta juyo tana kallon sa hawaye na sakko mata, girgixa mata kai yyi yace "Wait Iman...." cikin sarkewar murya tace "I swear to Allah who made me kana isowa kusa da ni xan kashe kaina Aliyu" still yyi yana kallonta ya kasa motsi wajen, ta nufi kofa tana rike da wukar hawaye na xubo mata sosai, cikin sanyin murya yace "Noo khadija karki tafi don Allah" da baya da baya take tafiya har ta isa kofa ta fice, ikon Allah kadai ya kai ta gida duk da daren da yyi, ganin halin da take ciki mai cab din ma bai karbi kudi bata shiga gida, nan bakin kofa ta durkusa don bbu jakar makullin, ta kai minti biyar a haka kafin tayi karfin halin buga kofar khaleel, va a dau lkci ba ya bude, ja baya yyi yana kallonta da mamaki, can ya durkusa yace "Are.... are you okay?" Girgixa masa kai tayi numfashinta

1 Comments On NOOR AL HAYAT
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls inason novel dinnan cplt

Please Login or Register in order to submit comment