Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

millionaires belt dinsa yace "Ohk a gaban kawayen naki xaki ce min A'a" Tace "Ka saba daukata ne?" Yace "Xan fara yanxu, shiga mu je" tabe baki tayi bayan few seconds ta kalli su Vanessa tace "Alryt, see you girls tomorrow" daga haka ta xaga ta bude front seat ta shiga ta kulle kofar, daga masu hannu yyi ya ja motar suka bar gun, basu yi tafiya me nisa ba yace "Twins sun isa lafiya?" Ta gyada kai tace "Sure" wayarsa dake ajiye kusa da ita yyi haske ta sauke kai tana kallon screen din, "Jawahir" sunan dake saman screen din kenan ta dauke kanta, bayan seconds kusan biyar ya dau kiran yace "Am driving baby, xan kira ki when am home" daga haka ya katse wayar ya mayar ya ajiye, suna isa gida yyi parking ta bude motar ta fita ta rufe ta nufi apartment dinta, xaro ido yyi ya bi ta da kallo.

Washegari Tuesday da yamma ta shirya bayan ta dawo makaranta don xuwa shopping mall ta yi shopping din turarurruka da man shafa, karamar jakarta ta sakale kafadarta ta fito ta rufe apartment dinta, ganin motarsa a parking space yasa ta gane yana nan don tun da ya ajiyeta jiya rabon da su hadu, babban shopping complex ne wajen ta gama daukan mayuka da turarukan da xata dauka, tayi deciding hadawa da disinfectant da antiseptics, Dettol babba ta dauka bata lura da mutumin dake bayanta ba kamar yanda shi ma din da alamar bai lura da ita ba don backing din juna suka yi, lkci daya suka juyo kusan a tare suka ci karo, pack din Sabulun dettol dake hannunsa ya fadi kasa, da sauri suka durkusa kusan a tare again ta rigasa daukan sabulun kafin ya kai hannunsa tace "Ohh sorry pls, I...i..." dai dai sanda suka mike tsaye ido cikin ido, shekaru kusan hudu kenan rabon da ta ji abinda taji a xuciyarta lkcn, a hankali ta saki dettol din hannunta tana kallonsa bbu kiftawa, wani kallo shi ma yake mata da wani expression, yana son magana amma da alama words din sun kasa fitowa, lkci daya words din yyi escaping lips dinsa cikin wani yanayi yace "IMANN...." Juya masa baya tayi tana ganin turawan da ke d'an nesa da ita doubled doubled, kawai ta nufi kofar fita complex din, tana jin yana kiranta da alamar bin ta yake ta kara saurinta, cikin sarkewar murya tace ma baturen gun ta mance ATM card dinta a gida yana bude mata kofa ta fice fittt without thinking twice ta nufi bayan mall din kamar xata tashi sama, ta xauna nan kasa jikin bango ta kai hannu dai dai kirjinta ta runtse ido, ta fi minti sha biyar wajen xaune, ji take kamar an mata alluran tsayar da Adrenaline ne don komai na jikinta gani take ya daina aiki kamar ba nata ba.


*Haske Writers Association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨





_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻






10....

Hadarin da ta gani garin ya kara mata kwarin gwiwa ta tashi da kyar tana layi kmr warce ta tashi ciwo ta samu taxi bayan ta fita haraban mall din, sai da suka dau hanya kafin ta iya bude baki ta gaya masa inda xa ta, kanta ta daura a kafarta har suka isa, tana jin yana ce mata sun kawo amma ta kasa dagowa, har sai da ya fito da sauri ya bude bayan motar yana cewa "Madam, are you okay" mugun karfin hali tayi ta dago tana dubansa da idanuwanta da suka yi jajur, yace "You look sick..." Da taimakonsa ta fito taxin, bai karbi kudi ba ya ce taje ta sha drugs ta gyada masa kai ta shiga gida tana hade hanya, Ikon Allah ya kai ta bakin kofar flat dinta ta fadi dai dai kofar Khaleel tana dafe da xuciyarta da take jin kamar an caka mata mashi, bugu daya ta ma kofar ta hade kanta da kasa, bude kofar aka yi, Khaleel ya d'an ja baya yana kallonta da mamaki, saurin durkusawa yyi yace "Subhanallah, Are you okay...." Ta dago da kyar hawaye na sakko mata ta nuna masa kirjinta ya rikota da mamaki yace "Me ya same ki" girgixa masa kai ta dinga yi ta kasa cewa komai, tun tana ganin sa dishi dishi a hankali kuma bata kara ganin komai ba. A hankali ta bude idanuwanta da suka mata nauyi tana bin dakin da take da kallo, dai dai nan aka bude kofa wani matashi ya shigo Khaleel na biye da shi a baya, mutumin ya karaso inda take ya duka ya d'an yi murmushi yace "Hello...." Kallonsa kawai take, yace "How are you feeling now?" Tayi shiru, yace "Sannu, Allah ya sauwake, babu inda ke maki ciwo yanxu koh?" A nan ne ta gyada masa kai, ya juya yana kallon Khaleel dake rungume da hannunsa yana tsaye bakin kofar, likitan yyi murmushi yace "Quack MD do you mind coming over" d'an murmushi Khaleel yyi ya karaso kamar bai son tafiyar ya isa kusa da ita idonsa a kanta a hankali yace "ina ke maki ciwo yanxu?" Shi ma dai bata ce masa komai ba, likitan dake kusa da shi yace "Xa ki ci abu yanxu, sai yyi maki allura ya baki magani kin ji" kallonsa nayi ban dai ce komai ba, ya kara min fatan samun lfya sannan ya nufi kofa yace "Dr I will take my leave....." bin bayansa Khaleel yyi suka fita waje, da damuwa Dr Ahmad yace "But... Tayi k'ank'anta da wannan matsalar, naga kamar she is in her early 20's...." Khaleel ya sauke ajiyar xuciya yace "Probably it's an inheritance...." Ahmad yyi dariya yace "Kai kuma ina mamakin wani irin Dr ne kai wani lkcn wllh...." Dakatar da shi Khaleel yyi yace "No you ought to have known me for long, I don't treat people that are close to me, ban iya bane..." Dr Ahmad yace "Close to you? Yanxu kana nufin yarinyar nan is close to you? A ina ka santa" Khaleel yace "Noo ba haka nake nufi ba malam" Ahmad yace "Seriously you need to get rid of that behavior Dr, Allah ya bata lfya, ka sama mata abinda xata ci yanxu sai ka mata alluran ko shi ma baxa ka iya ba?" Khaleel ya hararesa yace "Wa ya sani...." dariya Ahmad yyi yace "Toh shknn ni dai bari inje in d'an yi karatu kai kam nasan tun ba yau ba ka gama, abun ka da manya" Khaleel ya shafa kai yace "Xan dai yi, tnx for ur care frnd" daga haka suka yi sallama Khaleel ya koma ciki, a hankali ya tura kofar bedroom din nasa, har lkcn tana xaune ta dago kai tana kallonsa, yace "What will you eat Khadija?" Bata ce komai ba, ya d'an yi jim yana kallonta, juyawa yyi ya fita, ba a dau lkci ba kuma ya dawo rike da cup din shayi, da kyar ta yarda tasa hannu ta karba shayin da yake mika mata ganin yanda ya kafe ta da ido, ta dinga sha kamar magani don bbu wani xafi, xaunawa yyi gefen gadon, bayan wani lkci ta mika masa sauran shayin hawaye cike idonta, ya tsura mata manyan idonsa, murya can kasa yace "Meye matsalarki Khadija, tell me what ur problem is" girgixa masa kai kawai tayi, ya mike ya fita da shayin ya dawo, allurorin ya shiga hadawa har ya gama sannan ya dawo gefenta yace "Let me inject you sai ki sha magani you will be relieved soon in sha Allah" ganin jiranta yake ta d'aga rigar a hankali ta kwanta yyi mata sannan ya dauko mata magungunan da goran ruwa ya ballar mata su ya mika mata ta karba ta sha, tashi ta shiga kokarin yi tace "Ina son xan yi sllh" ya nuna mata bathroom, ta kusa minti daya bata tashi ba bata ce komai ba, can ta mike ta shiga ta dauro alwala ta fito, Fita yyi xuwa apartment dinta don dauko mata Hijab, a hankali ya tura kofar bedroom, idonsa ya fara sauka kan enlargements dake dakin na hotuna, a hankali ya karasa dakin yana kallon cute twins dake hoton da ita kanta, sun rungumeta gaba daya tana murmushi, ya sake mayar da dubansa kan daya enlargement din da suka manna mata kiss gaba daya, dauke idonsa yyi ya dau Hijab da ya gani linke kan gadon ya fita dakin, kan gadonsa ya ajiye mata Hijab din sannan ya fita. Ta jima xaune kan darduman bayan ta idar da sallahn magrib da isha, ido ta kafe ma wani hotonsa dake gaban mirror yana sanye da farin labcoat da stethoscope rataye a wuyarsa, a hankali ta sauke idonta daga kallon hoton, can tayi wani murmushin ta mike da kyar tana dukkan kokarin ganin bata yrda hawayen dake makale idonta ya xubo ba, ta linke masa lallausan pray mat dinsa ta ajiye sannan ta dau dankwalinta dake kan gadon ta yafa ta nufi kofa kamar mai counting steps dinta ta fito parlor, xaune ta gansa kan kujeran parlorn idonsa a kan wayarsa dake hannunsa yana operating, ya daga kai ganinta yace "You want something?" Girgixa masa kai tayi tace "No, am going to my apartment, thanks for ur care" daga haka ta nufi kofa yace "But...." Juyowa tayi tana kallonsa yace "Are you sure you will be okay all alone" tace "Yea sure" karasawa yyi kusa da ita ya mika mata makullin hannunsa ta karba ta bude kofa ta fita ta rufe masa. Bedroom dinta ta wuce direct ta fada kan gado, sae a sannan wani kuka ya xo mata, kukan da ta kasa yi tun daxu, Allah ya sani ta samu relief sosai kukan da tayi domin kuwa taji saukin abinda xuciyarta ke mata, har lkcn ta kasa gaskata wanda ta gani, why all of a sudden. Bata wani rintsa ba daren ranan don da baccin ya dauketa xata farka a firgice, daga karshe ma hakura tayi da baccin ta dauro alwala ta yi ta sllh sae dab da asuba wani bacci me nauyi yyi awon gaba da ita.

A hankali Aliyu ya bude idanuwansa jin kwankwasa kofa da ake ta yi, ya tashi xaune yana kallon kofar yace "Who's there?" Muryar small mum dinsa yaji tana cewa "Are you okay Aliyu? Baka fito sllh yau ba" a hankali yace "Nayi a nan Anty... Was having a slight headache ne" tace "Toh Allah ya sauwake, ka fito kayi break sae ka sha magani" daga haka tayi wucewar ta, mikewa yyi yana dafe kansa da yayi masa nauyi ya nufi window ya tsaya, lkci daya ya dawo ya xauna gefen gadon ya rike kan yace "Noo, nasan ba ita bace, ba Iman bace, it's her look alike.... But...." mikewa yyi da sauri cike da damuwa da confusion yace "Why did she run then, me yasa ta gudu?? Does it mean ita ce? Ya Allah...." Jingina yyi da bango ya runtse ido, ya kusa minti ashirin a haka aka sake bubbuga kofa, ya bude ido a hankali cikin sanyin murya yace "Who's there?" Muryar Maryam cousin sis dinsa yaji tace "Yaya ni ce" yace "Ya aka yi" bata ce komai ba, hakan yasa ya karasa ya bude kofar tace "How was ur nyt?" Ya dauke kai yace "T'was good" Tace "Mumy wai ka fito ka yi breakfast" yace "Ohk" daga haka ya rufe kofar ya koma gefen gado ya xauna, kallon agogo yayi ganin takwas ya tashi ya shiga bathroom, wanka yyi ya fito, ya fi minti sha biyar kwance jin kamar xaxxabi xai rufesa, can yyi ta maxa ya mike ya shirya ya dau makullin motarsa ya fice gidan ba tare da ya bari Small mum dinsa taga fitarsa ba. Mikewa xaune Khadijah tayi da sauri daga baccin da take ta dalilin bell da aka danna, ta tashi a hankali jin jiri na dibarta, ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta wanke baki sannan ta fito ta dau hijab ta sa ta fito parlor ta bude kofar, har lkcn yana tsaye gun, yana kallonta a hankali yace "Bacci kike na tashe ki?" Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace "Na tashi" yace "How are you feeling now?" Tace "Alhmdllh, ina kwana" yace "Lafiya lau" jin yyi shiru ta dago kai suka hada ido, saurin sauke idonta tayi, yace "You cried!" Ta girgixa masa kai kawai, yace "Noo you cried malama" lkci daya hawaye ya kawo idonta ta kasa ce masa komai, shiru yyi bai sake cewa komai ba, bayan wani lkci yace "Shiga ciki" ba musu ta juya ta koma ciki ya rufe kofar, daki ta koma ta kife kai da pillow wasu hawayen na xubo mata, duk taji ta tsani xaman UK din, ta tsani karatun, dago kanta tayi da sauri ta dalilin *SUDAIS* da ya fado mata, bata san lkcn da tayi murmushi ba kawai taji kamar an yaye mata bakin cikinta, tayi tagumi a sanyaye.... Ta fi minti sha biyar a haka, ji tayi duk duniya bbu wanda ta tsana... tsanar da bata da iyaka irin wanda tayi tozali da jiya a mall, taji an bude kofa ta dago da sauri, jin shiru ta mike ta fito parlor tana goge idonta, xaune ta gansa kan kujera yana hada allura, ya dago ya kalleta, lkci daya ya hade rai , bata yrda sun sake hada ido ba, ya ajiye alluran hannunsa ya mike yace "Are you alright? under this condition stil xaki dinga xama daki kina kuka haka, dama kuka na magani? idan ma damuwa gare ki baxa ki sa Allah ran ki ba" bata iya tace komai ba bata kuma yrda ta dago ba, ya koma ya xauna, bayan kusan minti uku ya nuna mata cup din shayi da bread dake ajiye kan table yace "There" ta karaso ta dau shayin yace "With d bread" girgixa masa kai tayi ta fara shan shayin, murya can kasa yace "Look..." ta dago idanuwanta ta kallesa ya nuna mata kujera, a hankali ta karasa ta xauna, ajiye cup din tayi bayan ta sha shayin, yace "ur injection" tashi tayi ta wuce daki ta daura xani cikin Hijab din jikinta ta fito, nan parlorn yayi mata alluran ya bata maganinta, yace "You go get some rest now, ki yi bacci da yawa kin ji" yyi kasa da murya yace "And please kar sake kuka ur condition isn't encouraging, always remember Allah xaki samu natsuwa sosai..." Bata ce komai ba ta mike ta wuce daki ya bi ta da ido, tashi yyi ya dau cup din ya fita. Sai bayan azahar ta farka daga baccin da tayi, sosai taji xuciyarta ya mata saukin xafin da yake mata don ta samu bacci da yawa, kuma taji ddin drugs din, yunwa taji na dawainiya da ita, ta tashi ta shiga bathroom ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, shafe shafe tayi ta dau gown mara nauyi da tsayi ta sa ta shimfida darduma ta saka hijab har kasa ta tada sllh, tana idarwa ta cire Hijab din ta linke sannan ta fito parlor don dafa ko da indomie ne ta ci, still tayi ta juya baya da sauri a parlorn ganinsa da tayi dai dai center table ya ajiye ledan hannunsa da alamar shigowarsa kenan, Bata jira ta ji abinda xai ce ba ta nufi daki da sauri ta rufe kofa, xama tayi kan gado ta hade kai da gwiwa duk taji kunya ya kamata, ta fi minti goma a haka, can dai ta mike a hankali ta saka Hijab din da tayi slh ta fito parlorn, bbu kowa ciki ta karasa gun ledan ta bude taga abinci ne da drink, kadan ta ci ta fara gyaran gidan, dab da la'asar aka danna bell, ta kasa xuwa ta bude, can dai taa isa gun kofar tace "Who's there?" Yace "Koh" bude kofar tayi ta juya ta dawo parlorn ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yace "Sorry...." Da sauri ta katse sa tace "Ohh bakomai" yace "Bakomai me?? ai baki jira kin ji abinda xan ce ba malama" ta d'an kallesa, sai taji kunya, ya buda ido sosai yace "Dama cewa xan yi, sorry... me yasa kika gudu daxu?" Bata ko kallesa ba balle tace komai, yyi murmushi yace "Toh kin ci abincin" kai kawai ta gyada, yace "How you feeling now" tace "Naji sauki" duk wannan abun bata yrda ta juyo ba sai gyare gyare take, yace "Alluran ki..." Da sauri tace "No naji sauki, xan sha maganin" shiru yyi na kusan thirty seconds, yace "Malama" sai a sannan ta juyo suka hada ido, jallabiya ce Milk colour jikinsa da ya fiddo da ainahin kamanninsa na larabawa, shi ya fara dauke kansa sai kuma yace "ohk... Ki sha maganin" daga haka ya fita ta bi sa da ido har ya rufe kofar.


*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨






_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻






11....

Shiru Aliyu yayi bai ce komai ba yana sauraren fadan Kanwar Dad din tasa, A fusace tace "Wai ba da kai nake ba ka min shiru Aliyu" ya dago ya kalleta da kyar don har wani ciwon kai fadan ke sa masa, ya marairaice fuska yace "Wllh ina ji Anty, ina jin ki" tace "Nace ka gaya min me yasa ka bar min breakfast kayi ficewar ka daxu?" yace "kiyi hakuri mum, ban san xan jima haka bane" Tace "To xaka ga uwar da xata baka dinner yau a gidan nan kuwa" murmushin karfin hali yyi ta juya tayi ficewarta, komawa yyi ya kwanta kansa na ci gaba da sara masa, tun safe har xuwa lkcn bbu abinda ya ci ban da ruwa da yake sha, bbu inda bai shiga ba a wasu daga streets din UK ko xai ga Iman amma sam bbu alamarta, shi ya ma rasa gane ko ita ce ya gani ko ba ita ba, ya mike xaune da damuwa yace "Ya Allah..." Har agogo yyi stucking karfe shidda na yamma yana xaune dakin, aka bude kofa tare da sallama, Maryam ce ta shigo dakin tace "Yaya Aliyu are you sick?" Ya kalleta yace "No I am not Maryam" ta xauna gefen gadon tace "Toh naga tun jiya duk ka xama wani iri, gashi daxu ko breakfast baka yi ba ka fita, nasan baka yi lunch ba ma" yace "Kirana aka yi na fita" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ya school ko baki je ba yau?" Tace "Naje daxu na dawo" yace "Ohk, ina su Baby da Fadil" tace "Suna assignment a daki" yace "Idan Anty ta gama lunch ki dibar min kadan ki kawo min" tace "Toh" sannan ta mike ta fita, ba a dau lkci ba kuma ta kawo masa abincin da ruwa ta ajiye masa.
Kulawa sosai Khaleel ke bata a kwanaki ukun da tayi a gida bata je makaranta ba duk da shi ya hanata xuwa makarantar sae taji sauki sosai, kuma cikin ikon Allah ta warware bata jin ko wani ciwo sae dai Kawai ta kasa mance incident din ne, ba a minti goma Aliyu bai fado mata ba, ko kadan Khaleel bai son ganinta cikin damuwa, he's as kind as she never expected, duk da wani lkcn he is pretending not to be, kamar dai yasan tana da damuwa, bata kuma yi mamakin ya gano haka ba tunda likita ne shi din, duk Safiya kafin ya fita sae ya tabbatar ta karya ta sha magungunan ta, da yamma kuma idan xae dawo it's either ya taho mata da fruits ko abinci, har books masu dadi na turanci ya kawo mata ta dinga karantawa, ae kuwa books din also contributed don nishadi suke sa ta idan tana karantawa, idan kuma ta gaji da karatun ta dauko hotunan su Sudais da Shuraim tun daga lkcn da suke jarirai har xuwa girmansu, yawanci kuma hotunan duk tare da *Sudais* ne wannan dalilin yasa bata gajiya da hotunan, ko gida bata fadi ma su Umma bata da lafiya ba. Yau kamar ko da yaushe tana kwance parlor bayan ta raka su Vanessa da suka xo gaishe ta tun da rana, bell aka danna, ta mike don tasan shi ne, ta isa gun kofar ta bude, gaishesa tayi tana kallon sa, ya amsa yana mika mata ledan hannunsa, lkci daya kuma yana tambayarta ya jiki, ta karba tace "Da sauki" yace "Maa sha Allah" xae juya tayi saurin cewa "Are you sick?" Juyowa yyi yana kallonta yace "Just Stomachache, but na sha drugs da sauki sosai" da damuwa tace "Allah ya sauwake" yace "Ameen" daga haka ya rufe mata kofa ya shiga apartment dinsa. Ajiye ledan tay kan table ganin fruits ne, tana ta xaune parlor har kusan Magrib kafin ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, nan parlorn tayi sllh, ta gama addu'o'inta sannan ta mike ta shiga kitchen, tunanin me xata dafa ta shiga yi don yunwa take ji, garnished cous cous tayi da yaji kayan hadi, duk da bashi da yawa kawai tayi deciding ta debar masa, ta zuba a karamar warmer snn ta sa hijab ta fita kai masa, a hankali ta kai hannu ta danna bell, sai da ta sake dannawa ya bude kofar, singlet ne jikinsa da dogon wando, kallon sa ta tsaya yi ya juya ya koma kan kujera ta bi sa da ido, can ta bi bayansa ta rufe kofar, ajiye abincin hannunta tayi ta durkusa gefensa tana kallonsa da damuwa tace "Cikin ne har ynxu?" Gyada mata kai yyi a hnkli yace "But... Sure I will be okay" cike da karfin hali yyi maganan, shiru tayi tana kallonsa taji tausayinsa sosai, a hnkli ya sauko kan kujeran ya duka kan gwiwowinsa, kamar xata yi kuka tace "Ko xaka je asibiti" girgixa mata kai kawai yyi, sai kuma ya kwanta nan gun, kana ganinsa kasan namijin kokari kawae yake, hawaye ya cika idonta, tashi xaune ya kara yi yana runtse ido a hankali yace "Get me water pls" tashi tayi da sauri ta nufi fridge ta bude taga duk masu sanyi ne, ta shiga kitchen ta dau glass cup ta dibo masa na tap, tana dawowa ta duka gun sa ta mika masa ya karba ya fara sha, sae kallon sa take sai ka rantse tare cikin ke masu ciwo ynda tayi da fuska, lkci daya ya ajiye glass din ya mike ya nufi bathroom dake parlorn, ita ma ta mike tsaye, amai sosai yake yi a bathroom din, ta kasa motsawa daga inda take, can ta durkusa ta fashe da kuka, yana fitowa parlorn ya hade kansa da kujera, tashi tayi ta isa kusa da shi cikin rawar murya tace "Don Allah mu tafi asibiti plss" ya dago idanuwan sa da suka sauya xuwa ja, komawa baya tayi da sauri don idanuwan suna kalau ma tsoronsu take barin kuma yanxu da suka kara wani kala kan na da, da alama ya kasa mata magana don girgixa mata kai kawai yayi, xai komar da kansa kan kujerar tayi karfin halin rikosa da sauri tace "Doctor plss let me drive us to the hospital, ina makullin motar yake" murya can kasa yace "I will be alright Khadija, go to my room xa ki ga 1st aid box..." Bata jira ya gama ba ta mike da sauri ta shiga dakin, da box din ta dawo, ta ajiye kusa da shi, ya xamo kasa idonsa lumshe ya bude box din, bayan yan sakwanni ya bude idon ya dau wani allura da syringe ya mika mata, ta bude ido da mamaki ta dai karba ya mayar da kansa kasa, rasa abin cewa tayi, can dai ta balle bakin alluran ta xuke a syringe tayi karfin halin cewa "Ga shi nan" ja baya tayi tana xare ido ganin ita yake nufin xata masa alluran, duk da ta iya kawai niyyar nuna masa bata iya ba ta yi, amma tausayinsa da yanda shi ma ya nuna damuwarsa lkcn da bata da lafiya yasa ta kasa, hannunta na rawa tayi masa alluran, kin bude ido yyi ta koma baya tana kallonsa, bayan wasu mintuna ya mike da kyar ya kwanta kan kujera, ko minti goma bai kara ba bacci ya dauke sa, dawowa tayi kusa da shi tana kallon sa da tausayi ganin alluran bacci yasa tayi masa, mikewa

1 Comments On NOOR AL HAYAT
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls inason novel dinnan cplt

Please Login or Register in order to submit comment