Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruwan ki da k'uda idan ba rainin wayo ba, ki bar abincin kar ki ci, kuma maxa ki tafi ki wanke kwanukan yanxun nan" juyawa khadijah tayi ta bar wajen, Hajiya Maimuna tace "Idan ba ma tsoron Allah ba har Alhaji xai yarda ya rike er Muhammad, uwar me ya tsinana sa yana raye" Khadijah dake ta turo baki ta dau omon da ta gani da sosan wanke, tsaye tayi ta rasa ta inda xata fara wanke wanken, can dai ta dauko babban bahon da ta gani ta tari ruwa ya kusa cika sannan ta xaxxage d'an omon, muryar wata mata da shigowarta gidan kenan taji tana cewa "Ke ya haka, da uban ruwan nan xaki kada kumfa?" Khadijah ta kalleta kamar xata yi kuka tace "Toh ban sani ba" matar ta karaso baki sake, nan ta rage ruwan ta kara mata omon sannan tace "Haka ya isa" parlor matar ta shiga wajen su Hajiya tana cewa "Ku kuma ina kuka samo wancan Ajebon" Karfe kusan hudu da rabi Hajiya Salaha ta fito bayan tafiyar bakuwarta, sakin baki tayi tana kallon Khadijah dake durkushe bakin pampo har lkcn, kwanuka ta ko ina, duk ta hade gumi ta jike kayanta jagab, kai kana ganinta kasan bata taba ba ne, Hajiya ta kwalo ma kishiyarta kira ta fito da sauri, ita ma ta xaro ido tace "Me xan gani ni Maimuna, wanke wanken awa biyu?' Khadijah dake kallonsu kamar xata yi kuka tace " plates din sun bushe, ya ki ya fita" Hajiya Maimuna ta rike ha6a tace "Ehh lallai muna da aiki, yanxu tsalelliyar budurwa kamar ki baki iya wanke wanke ba shekara sha uku sa'ar Murjata" Hajiya Salaha da ita ma ta bude baki ta kalli kishiyarta tace "kina da aiki dai, don ba ni aka kawo ma ita ba, mutum yaji da nasa 'ya yan mana, shima Alhaji wllh, da ba sai ya bar ta gun kishiyar marigayiyar uwarta ba" Juyawa Hajiya Maimuna tayi tace "Toh Allah ya kyauta" daga haka ta shiga ciki, Hajiya salaha ta mata tsawa tace "Tashi mana kan kwanuka yar banxa kawai, ke ga yar masu kudi ko, to xa ki ci kwakwa a gidan nan don bbu shegen da xai dau iskancin ki, kawai kin bi kin ma mutane asarar omo, maxa kuma ki dau tsintsiya ki tattare gaba daya gidan nan idan shima kuma baki iya ba sai in ga" khadijah da ta bata fuska xata yi kuka ta karasa ta dau tsintsiyar da take nuna mata ta fara sharan, takaici ya rufe Hajiya ganin gwara ma ta shekara a tsugunne bakin pampon da wannan sharan da take na yan iska, juyawa tayi ta bar gun daga karshe tana cewa "Xaki san inda kika xo yarinya" da daddare Khadijah na rakube jikin kujera gaba daya hankalinta da soul dinta na kan kallon cartoon da kananun yaran kawu Jibril suka sa a TV, an kirata ya fi sau uku amma inaa, hauri Sajida er Kawu ta biyu ta kai mata tace "Yau naga mayyar kallo ana magana bata ma san ana yi ba" a firgice ta mike sai dai har lkcn idonta na kan TV, Hajiya Maimuna dake lekosu daga kitchen don ita ke kiran khadijar ta xo ta karbi abinci, ta karaso a fusace ta kai mata dundu, firgita ta juyo Hajiya Maimuna ta murda kunnenta tace "Gafara shegen kallon nan xai maki ne hala, ka ji min yar kaza kaza" sunkuyar da kai khadijah tayi kamar xata yi kuka, Hajiya Maimuna ta turata kitchen tace "Ga tuwon ki can a kitchen ki dauka, gayyar tsiya kawai" tafiya kitchen din tayi tana yi tana waiwayo TVn ta dauko tuwon a wata yar roba an ya6a masa miyar kuka koriya shar, sai kallon miyar take kamar idanuwanta xa su fito, ta dawo parlon ta xauna cikin yara dake cin abinci su ma ta ci gaba da kallonta Hajiya Salaha ta shigo parlon tace "Wato kinsan idan mutum ba ayi masa tarbiya ba sai na kallo, kinga saura kadan ta xubar da tuwon tana kallo" da sauri khadijah ta kalli tuwonta taga ba daidai ta ajiye sa ba, Hajiya salaha ta fixgota a fusace ta juyar da ita tana kallon kofar kitchen tace "Duk kika sake juyowa sai na kashe ki" Khadijah dai bata ce komai ba ta kai hannu a hankali cikin tuwon ta mintsili kadan ta kai baki, yamutsa fuska tayi tana hadiyewa da kyar sai kuma ta kalli Er Kawu ta uku mai suna Rabi tace "Anty akwai indomie?" Yarinyar ta fashe da dariya sannan ta gaya ma Uwarta Hajiya Salaha, Hajiyar tace "Ehh akwai wanda ubanta ya kawo mana daga kabari" Khadijah dai bata ce komai ba, haka tayi ta kallon tuwon ta kasa ci, daga karshe haka ta mike ta kai kitchen ganin kowa na kai kwanonsa can, Hajiya Maimuna ta kwalo ma kishiyarta kira ta nuna mata tuwon da ta bari tace "kin dai ga koh? To wllh har in fita girki sai dai yunwa ya kashe yarinyar nan"

*Haske Writers Association*💡

07087865788 Contact me here.

✨ *Noor-Al-hayat*✨






_By Khaleesat Haiydar_






_Littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne, kindly patronize ur writer and read happily, duk wanda bai ji dadi ba hakan, yyi hakuri plss_





Washegari talata Khadijah na ta share tsakar gidan da aka sa ta tayi tun asuba har lkcn bata gama ba Kawu ya fito cikin shiga ta alfarma da daya daga kayan mahaifin Khadijah, matansa sun rakosa xuwa balcony ana yi masa Allah ya tsare hanya, ganin Khadijah da yayi ya juya yana kallon matan nasa yace "Gobe er can ta shirya da safe xa a kai ta makarantar boko" Hajiya Maimuna tace "Wanda su Sumayya ke xuwa?" Wani kallo yyi mata yace "Ke xa ki biya, ko ina naga kudin biyan wannan makarantar, makarantar da yaran Bala ke xuwa xa a kai ta, ina jin ko a Jss2 aka ce take ko one" Khadijah ta mike tace "Aa jss2 nake Abba" Wani shegen kallo yyi mata yace "Kun ga irin rashin tarbiyar ko, kun gani ko, to yanxu wa ya sako bakinta, dama na samu labarin an baki tuwo ki ci jiya da daddare kin ki ci tunda kin taho da abinci daga gidan marigayi Muhd, to wllh xa ku yi aiki hand in hand da yunwa in har baxa ki ci abinda ya sauwwaka ba, baxa ki taho gidana kina min sangarta ba" daga haka ya nufi daya daga motocin dake tsakar gidan, Khadijah ta ci gaba da sharanta na yan koyo da take yi. Throughout haka ta dinga aikin da ba ta iya ba bata taba yi ba a gidan, duk ta gaji amma ko kadan bata ce haka ba sai turo baki da take ta yi, Hajiya Salaha ta kai mata dundu yyi sau biyar daga karshe ta gaji da bin ta tana mata dundun ta kyaleta, Hajiya Maimuna kuwa ta surfa mata xagi ya fi a kirga, duk wnn abun sai dai ta turo baki ko ta bata fuska daga nan kuma shkkn, kunu da kosai a gantale aka bata a cup, ita ma ta ci a gantale ta bar masu abinsu don ba saba ci tayi ba, sai da suka yi baccin rana sannan ta samu tayi sallahn zuhr ta lallaba ta kunna TV ta rage volume ta xauna tana kallo happily, dauke wutan da aka yasa ta turo baki, a hankali ta kwanta nan kasan parlon nan da nan kuma bacci ya dauketa don tun tashin asuba. Ko abincin rana ba a bata ba wai sai yaran gidan sun dawo, basa kuma dawowa sai karfe biyar, suna dawowa kuwa da yamma aka xuba ma kowa shinkafa da wake da mai da yaji da Hajiya Maimuna ta girka, Hajiya Salaha ta sa Sumayya ta xuba ma Khadijah don ita Hajiya Maimuna rantsuwa tayi baxata bata ba, khadijah ta tsura ma shinkafa da waken ido da aka barbada ma yaji, a hankali ta kai hannu ta dinga tsince waken tana ajiyewa a kasa gefenta, Hajiya Maimuna dake ta kallonta ta mike ta karbe kwanon abincin ta kai kitchen ta rufe, abincin da ba ta ci ba kenan har aka yi magrib sannan isha, tana ganin aka ba kowa shinkafa da miyar da Hajiya maimunar tayi amma ban da ita, bayan ta idar da sllh ta samu Sajida dake waya ta duka gefenta a hankali tace "Anty ni ba a ban shinkafar ba" ta mata wani kallo tace "Toh ni na dafa ki samu su Hajiya mana" mikewa tayi ta wuce dakin Hajiya salaha, ta samesu xaune da yaranta ana assignment, kallonta tayi tace "Lafiya??" ta girgixa kai tace "Ni ba a bani abincin ba ina jin yunwa" tsawa tayi mata tace "Fita ki ban waje, ba dai shayi da soyayyen kwai kike jira ba yunwa xai kashe ki gidan nan" a hankali Khadijah ta juya ta fita, ta tafi gun kwanciyarta ta rakube hade da rufe ido tana tuno Ummarta. Washegari kamar jiya da asuba aka tasheta, har gari ya waye tana shara, sai da duk yaran suka wuce makaranta sannan Hajiya maimuna tace idan ta ga dama ta wuce tayi wanka ta shirya, tsaye khadijah tayi a bathroom dake tsakankanin dakunan su Hajiya, soson wankan ta da Abbanta ya siyo mata daga Kasar waje ya xama na kowa da kowa hadda sabulunta mai tsada, ta turo baki ta dau sabulun kadai ta yi wanka da shi ta fito cike da kyankyanin bayin, tun da ta fito parlor Hajiya Salaha ke kallon kayan jikinta, khadijah ta durkusa gefenta a hankali tace "Na gama" tabe baki Hajiya salaha tayi ta nuna mata cup din kunu tace "Gashi can ki dauka, kosan ya kare" Khadijah ta leka cup din da sauri a xaton ta shayi ne, a hankali ta mike ganin ba shi bane ta isa gun cup din kunun ta dauka, Hajiya salaha tace "Ko yau ma baxa ki sha ba" bata ce komai ba ta dinga shan kunun da yyi mata tsami a baki tana d'an yamutsa fuska, sai hararanta Hajiya salaha take tana kwafa, daga karshe kadan ta sha ta ajiye ta mike tace "Na koshi" duk da uban yunwan da take ji cikinta na kugi, Hajiya Salaha tace "Toh ki hutar da kanki tafi ki juye a flask ki hada duk kwanukan ki wanke, kuma ki min irin na ranan in fasa maki jiki da wayar wuta" ita dai khadijah bata ce komai ba ta mike taje yin yanda tace nata. Wani almajirin Kawu ne ya taho kai ta makarantar, shegen nisa ce da makarantar kuma almajirin me suna musa yace da kafa xata dinga xuwa kullum don haka gwara ta dinga kallon hanyar da kyau, tunda suka shiga makarantar Khadijah ke kalle kallen ko ina, don ita dai bai yi mata kama da schl ba, gashi ko plaster ba ayi ba, yaran ma basu da yawa, Musa ya shiga gun wani wanda da alama shugaban wajen ne, ita tana tsaye waje, tana jin mutumin na ce ma musa ai lesson ne wa yaran da basa gane karatu, kuma na shekara daya ne kafin yaro ya shiga boko, musa ya tambayesa nawa ne yace dubu uku da dari biyar, nan take musa ya basa kudin, ita kuma aka kira wata daliba ta kai ta ajin karshe musa ya wuce, su kusan goma ne a ajin, ita dai tunda ta shiga ajin take kallon malamin dake ta koya sentence making, "The boy was tall..." Shine abinda malamin ke ta nanatawa yaran na fadi su ma, khadijah dake ta kallon sa tace "Excuse me, but you said present tense sir?" Malamin yace "Yes" tagumi tayi tace "Sorry but that's past tense class master" kallon board din yyi da sauri sannan ya kalleta, bai kulata ba ya ci gaba, nan ma kuma sai da ta sake masa gyara, hade rai yyi yana kallonta, can ya basu classwork ya koma ya xauna, sai bayan kusan minti sha biyar ya karba sannan ya fara koyar da Multiplication a board, sai da ya gama tas, sannan ta kai masa gyaransa a littafi tana nuna masa, fita malamin yyi xuwa gun shugabansu, ba a dau lkci ba ya kirata, tana tsaye yace "Ke tunda baki da kunya kar ki sake xuwa makarantar nan daga yau, tunda kin iya abinda ake koyarwa ki xauna a gidan ku ko kuma a kai ki school ga kudin ku" karba tayi tace "Ohk, in tafi yanxu" yace "Tafi" juyawa tayi ta fice daga uncomplete building din, gano gida bai mata wahala ba saboda sharpness dinta, su Hajiya salaha dake xaune parlor suna hira suka saki baki suka ce me kika dawo yi, tace "Ba abinda suka iya fa a wajen, they are just teaching rubbish, ni bana son wajen school nake so, am in jss2" Hajiya maimuna tace "Shine kika dawo" gyada mata kai tayi ta mika mata kudin hannunta, ta tafi jikin kujera ta rakube ta xauna, duk suka bi ta da kallo baki sake. Yunwa sosai take ji amma bata ce komai ba, Kawu ne ya fito a shirye xae fita wajen karfe goma da rabi, ganinta yace "Wannan yarinyar musa bai kai ta makarantar bane" Hajiya salaha tace "Uhn gata nan ya kai ta ta dawo wai bbu abinda suka iya kilan mai tsada take so" ya juya da sauri yana kallonta yace "Me ya dawo da ke?" Tace "Abba they are teaching rubbish there, kuma ina ta correcting dinsa, ban san whether he reported me bane, sai aka kira ni wai in tafi kar in sake dawowa, har da kudin ma an bani na dawo da shi" Kawu ya gyara tsayuwa yana gyada kai yace "Ohhhw haka aka yi kenan, toh kin ma kanki, Alhmdllh Muhd baxae gan ni da ko wani laifi ba don na kai ki makarantar kika gudo, don haka sai kiyi ta xama gidan" daga haka yyi ficewarsa, ita dai bata ce komai ba, Hajiya Maimuna tace "Wato ke isassa kin raina makarantar shine kika je kina ma malaman fitsara ko, uban wa ke da kudin asaran da xai kai ki irin makarantar da ubanki ya sa ki tun farko?" Khadijah dai sai kallonta take, Hajiya Salaha tace "Ni da nace xan fara awaran siyarwa xan dauko mai aiki wllh da Alhaji xai yarda da sai ta dinga kai min can bakin kasuwa, kinga ai ba talla bane wnn, xama waje daya xata yi" Hajiya Maimuna tace "Ae ko da xai yarda nima sai in hada mata da Omon siyarwa na" Hajiya salaha tace "Toh bari ya dawo dai mu ji" suka gama dai hirarsu duk suka shiga dakunansu domin kwanciya suka bar ta ita kadai a parlorn ga yunwa dake dawainiya da ita, da rana yau kam taliya da wake suka girka, gashi ita bata cin wake tun tana karama, Hajiya salaha ta dan yarfa mata a kwano ta bata, kamar xata yi kuka tace "Ni ban iya cin wake ba" Hajiya salaha tayi er dariya ta mayar da abincinta cikin tukunya ta fito kitchen din, sai a sannan khadijah ta fara hawaye don tunda take bata taba jin yunwa irin wannan ba, ita shinkafa da miya take so, tsakar gida ta tafi ta xauna tana share idonta, har wani rawa jikinta yake don yunwa, tashi tayi ta fice gidan gaba daya, ta shiga gidan dake kusa da na kawunta, gidan shigen na kawunta ne, taga wani yaro xaune tsakar gida yana cin tuwo da koren miya, fita tayi da sauri har tana tuntube, gidan dake kusa da wannan ta tura ta ji a kulle, haka na kusa da shi ma, a gida na hudu ta tsaya tana kallon babban gidan don ya fi duk gidan anguwar, tura gate din tayi taji a bude ta shiga tana kallon mai gadin ta gaishesa yace "Wa kike nema?" Ta nuna masa cikin gidan sannan tayi wucewarta, har ta isa balcony kallon karen dake cikin cage a gidan take, ta murda kofa a hankali ta shiga parlorn, tsaye tayi bakin kofar ganin wani matashi da baxai wuce shekara ashirin da shidda ba yana xaune parlorn da plate din abinci a hannunsa idonsa a kan tv, yana kallonta da dan mamaki yace "Wa kike nema" ta kalli abincin hannunsa kamar xata yi kuka a hankali tace "Nobody, I am just hungry" ya buda ido kamar ya ji mugun abu, a hankali tace "Please" ajiye plate din hannunsa yyi yace "Take" ta karaso ciki da sauri ta xauna kan kafarta tana kallon shinkafa da miyar da naman kaza sai coslow dake gefe murya can kasa tace "Thank you" daukan spoon din tayi ta kai abincin baki ta fara ci, ya kafeta da ido irin kallon mamaki, muryar wata dattijuwa taji tace "Who's this?" Ya juya ya kalleta kafin yace komai Khadijah tace "Good afternoon ma.. I am khadijah" matar ta kasa cewa komai, ta kalli yaronta dake xaune kamar yanda shi ma yake kallonta, Khadijah ta dau kazar abincin tana ci tana kallon matar.

*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨






_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻






_Littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne, kindly patronize ur writer and read happily, duk wanda bai ji dadi ba hakan, yyi hakuri plss_






Karasowa parlorn dattijuwar matar tayi har lkcn tana kallon khadijah tace "Where are you coming from?" Khadijah ta dago a hankali tace "Just 3 houses away...." Matar tace "Gidansu Hajiya Salaha kenan?" Khadijah ta gyada kai, matar tayi shiru tana kallonta, can tace "An aiko ki ne?" Ta girgixa kai tace "A'a kawai abinci nake son ci" kallon d'an ta da ke xaune matar tayi, khadijah ta ci gaba da cin abincin gabanta, shi dai bai ce komai ya mike xai bar parlorn, mahaifiyar sa ta bi sa da ido tace "Kaje to Sadiya ta xuba maka wani abincin koh" ya juyo yace "Noo dama it's not as if ina jin yunwa mum, anjima xan ci" daga haka ya wuce ciki, matar ta dinga kallon khadijah dake cin abincin sanyi sanyi, can ita ma ta juya ta bar parlorn, jawo remote khadijah tayi ta kunna TV ta gyara xama tana facing tvn, tana cin abincin amma gaba daya ta ba tv attention dinta, bayan kusan minti talatin taji ance "Wai ke baxa ki gida bane? Ba kin gama cin abincin ba" Ta juyo da sauri ta kallesa sai kuma ta marairaice tace "Plss ina son in gama kallon nan" sakin baki yyi yana kallonta ga plate din abincin ta gama, bai dai ce komai ba ya fita rike da makullin mota, ba a dau lkci da fitarsa ba sai ga yan mata uku sun shigo gidan sanye da kayan islamiyya, tun da suka shigo suke kallonta ita kam ko sanin sun shigo bata yi ba, Muryar matar daxu taji a parlorn tace "Ke baxa a nemeki gida ba" khadijah ta dago da sauri, sai kuma ta bata fuska tace "Anty bana son xuwa gidan" Matar ta buda ido tace "Baki son xuwa kuma?" Shiru ta d'an yi kafin tace "First... They are so dirty and unkept, and I don't like their dishes.... I don't just like the house" matar dake kallonta da mamaki tace "Toh ba gidan ku bane" khadijah ta girgixa kai a hankali tace "Noo uncle dina ne ya kawo ni" matar tace "Maza tashi ki tafi kar ayi ta nemanki kin ji" kallon agogo tayi taga karfe shiddah ta ce "plsss ma... am I always welcome here?" Matar ta d'an yi murmushi tace "Sure" khadijah ta kwashe plate da cups da ta ci abinci tace "Where can I find d kitchen" nuna mata matar tayi ta kai ta fito sannan ta dau ruwan goron da d'an ta ya ajiye tace "In tafi da shi?" Matar ta gyada mata kai, murmushi tayi ta risina tace "Thanks ma" daga haka ta nufi kofar fita matar ta bi ta da ido, tana fita gidan gaba daya ta hango mutane tsaye bakin gate din gidan kawunta, tafiyar minti kusan shidda tayi ta isa gidan, tsaye ta tadda su Hajiya Salaha da yaransu gaba daya ga makota ana ta surutu, Sajida ce ta fara ganinta tace "Lahhh mama kun ganta" sai aka juyo gaba daya ana kallonta, Hajiya Salaha ta isa inda take da sauri ta fixgota tace "Daga ina kike?" Khadijah dake bin kowa da kallo tace "Just few houses away....." Bata rufe baki ba Hajiya Salaha ta sauke mata mari, wani ihu ta fasa tana rike da fuskarta tana jin duniyar na juya mata, tunda take ba a taba kai hannu jikinta ba bare fuskarta sai ranan, iyaka a sa ta tayi kneel down ta daga hannu, har tsadadden bokon da take xuwa a kano ma ba a duka, Hajiya Salaha na huci ta shiga kunduma mata xagi tana cewa "Allah ya isa yawon da kika sa muka dinga yi muna nemanki kamar gantalallu, sai Allah ya saka mana... Kuma bari Alhaji ya dawo wllh xaman ki ya kare gidan nan ya je can ya kai ki gun talakawan dangin uwar ki..." Kuka kawai khadijah take tana rike da fuskarta, hakuri mutanen wajen suka dinga ba Hajiya Salaha suna cewa ai yarinya ce, Hajiya maimuna da ganin Khadijah ya sa ta shiga parlor ta fito da wayar wuta ta nufo ta, wata mata ce tayi saurin janyeta tace "A'a don Allah ki bari Maman Hafsa, ayi mata hakuri" wata mata ma ta rike wayar tana ba Hajiya Maimuna hakuri, Hajiya Salaha tace "Ku bar ta ta ci mata mutunci crook ce wannan yarinyar da ku ke gani haka, wa yasan gidan uban da taje" Matar da ta ja Khadijah ta duka dai dai fuskarta tana kallonta tace "Ina kika je ake ta neman ki yan mata" Khadijah na shessheka tace "I was hungry and I had to....." Kasa ci gaba tayi ta rushe da kuka, Matar ta d'an kwalalo ido tace "Tohhh bata jin Hausa ne?" Hajiya Maimuna tace "Iskancin fa?? Tsabar shakiyanci ne da iyayi da kinibibi ita er mai kudi, toh wai ma ina mai kudin yake yau? Ku ce min yana kabari, toh idan ma xata sauke kai ta yi rayuwa yanda ko wani talaka ke yi ya rage nata, uwar me suka tsinana ma mutane banda tsoron Allah har Alhaji xai daukota ya ajiyeta a gidansa, wai I am hungry... To kafafuwar uwarki xan dafa maki in baki banda abinda aka girka kika ki ci" Hajiya Salaha tace "Ae komai ya xo karshe, ya dawo yasan yanda xai yi da ita, wnn 'ya sai ta kashe aure, taje can inda xa a dinga dafa mata indomie da kwai a bata shayi mai kauri da custard ta sha, mu ba rainon tea da bread muka ma yaranmu ba" daga haka tayi shigewarta ciki, Matar dake rike da Khadijah tace "Ke me yasa kika fita baki sanar masu ba? Komai aka baki kuma bata sai ki ci ba khadijah" Khadijah ta kasa cewa komai sai kuka take, jin kiraye kirayen magrib duk aka fara watsewa ana ma su Hajiya Allah ya kyauta, wasu kuma na tausayin khadijah domin kuwa suna ganin iyayenta basu mata adalchi ba in har abinda su Hajiya ke fada gaskiya ne a kanta, ba a san yanda rayuwa xata kaya ba don haka iyaye ya kamata su dinga koya ma 'ya yansu both the right and left side of life, yau idan an ci na masu kudi gobe a ci na talaka bawan Allah, wannan xai sa yaro yyi adapting a duk situation da xai tsinci kansa. Khadijah ce kadai tsaye tsakar gidan duk sun shige ciki da yaransu, ta share idonta a hankali ta bude kofa xata shiga, a tsawace Hajiya Salaha tace "Ki shigo ki mana me? Maxa koma sai Alhaji ya dawo gidan nan, maxa fita kar in sumar dake annamimiya kawai" juyawa tayi da sauri ta bar wajen bayan ta rufe masu kofa ta nemi wani waje ta xauna ta daura kanta bisa kneels dinta, har aka kira Isha tana wajen ga sauro sai cixonta suke, Kawunta bai dawo gida ba sai wajen karfe goma, bayan ya gama parking xai shigo ciki ya ga kamar mutum a wajen ya haske waya, tana nan yanda take bacci ya dauketa a hakan, da mamaki yace "Ke!!" Firgit ta farka ta mike tsaye da

1 Comments On NOOR AL HAYAT
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls inason novel dinnan cplt

Please Login or Register in order to submit comment