Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

What a f**k... I will get you" Da gudu ta koma daki kamar ya biyota din nan, ita kadai tasan irin tsoratan da tayi. Gaba daya ta kasa bacci har kusan karfe daya gashi ko wanka bata yi ba balle ta sauya kaya xuwa na bacci, duk kamshin turarensa ya cika ta tun rikon da ya mata, ko ta ya ta juya kamshin kawai take ji, a hankali ta tashi kamar mara laka ta cire kayan jikinta ta shiga toilet, wanka tayi ta fito ta xura rigar bacci ta kwanta bayan ta feshe jikinta da turarrukan ta, sai a sannan bacci ya dauketa. Sai kusan karfe bakwai ta tashi washegari ta mike da sauri ta shiga toilet tana salati ganin ynda ta makara, karfe takwas da rabi ta fito shirye cikin doguwar rigar kanti kamar ko da yaushe, blue ne rigar mai stones baki, sai white veil da ta daura kanta, takalminta ma fari ne haka karamar jakar hannunta sai handouts dake hannun, kana ganinta kasan a tsorace take, ta rufe kofarta da sauri ta nufi gate dai dai nan suka kusa cin karo xai shigo, sosai gabanta ya fadi ta juya kamar kiftawar ido har ta bar bakin gate din, can gun da aka tanada domin parking space a gefen apartment dinta ta nufa sannan ta juyo tayi iya kkrin ganin ta boye tsoron fuskarta tana kallonsa tayi kicin kicin da fuska, lkci daya ta karasa kofarta ta ga ya nufo wajen, tsabar rikicewa ta kasa bude jaka ta ciro makulli sae rawa hannunta yake, ta fashe da kuka ganin ya kusa wajenta tace "Am begging you stay away from me plss, I don't know you.... Stay outta my way" har ya karaso gun bata iya ta motsa ba, kawai ta durkushe kasa ta rufe ido, jin ya bude kofar sa ta dago da sauri, suka hada ido yace "I only have ur time at night" daga haka ya shiga ciki ya rufe kofarsa ta mike a sanyaye tana kallon kofar, da sauri ta fice compound din gabanta na faduwa. Suna gama lectures ranan tace da Vanessa a gidanta xata yi spending night din, don haka tare suka wuce gidan Vanessa dake Round church street, Vanessa tayi masu girki suka ci bayan Khadijah tayi sallah, karfe shidda saurayin Vanessa ya xo gidan Khadijah ta shiga bedroom ta bar masu parlorn, har ta fara bacci Vanessa ta tada ta wai Richard xae kai su shopping, duk yanda Khadijah taki amincewa aje da ita sai da Vanessa tayi convincing dinta suka fita tare, turarurruka kawai ta deba a mall din, sun yi kusan minti sha biyar kafin Vanessa ta gama siyayyar da xata yi suka bar mall din, gun siyar da ice cream suka tafi daga nan, Suna tsaye cikin Aromi ba a kai ga siyar masu cold stone ice cream din da xa su siya ba kamar ance ta juya suka yi ido hudu da neighbor dinta, xaune yake da wata kyakkyawar baturiya da baxata wuce ashirin ba ga kayan ciye ciye a gabansu yarinyar na rike da hannunsa cikin nata, tun daga sama har kasa yake kallon khadijah, ta hade rai tayi saurin dauke kai ta amshi ledan ice cream din da Vanessa ke mika mata, Richard ya siya masu har da pizza ya biya bills din, tuni ta yi hanyar fita Vanessa na biye da ita, ta d'an saci kallonsa taga kallonta yake yana wani murmushi ta jefa masa harara suka fita wajen, motar Richard suka shiga ya mayar da su gida. A gidan Vanessa tayi weekend din gaba daya, ranan lahadi ta shirya ta koma gida ba don ranta ya so ba, duk da a xuciyarta dama niyyar dawowa ta kwaso kadan daga kayanta ta dawo gidan Vanessa tayi, tunda taxi ya ajiye ta gabanta ke faduwa kamar mai tausayin kasa ta dinga tafiya tana waige waige duk da bata ga motarsa ba hankalinta ya ki kwanciya, tana kkrin bude kofa taji an bude nasa kofar a gigice ta sakko kasa dai dai lkcn da yarinyar da ta gani a eatry ranan ta fito daga parlornsa, yarinyar tace "Hello, seems I frightened you" banxa Khadijah tayi mata da farko can kuma tace "Never mind" daga haka ta shige apartment dinta bayan ta bude, bin parlorn ta dinga yi da kallo ganin ya d'an yi k'ura, kawai tayi deciding ta gyara ko ina kafin ta bar gidan, ta tsaftace ko ina ta goge, sannan tayi wanka ta canxa kaya ta fito parlor, kitchen ta shiga jin tana jin yunwa, cikin mintuna kalilan ta hada ruwan jollof din cous cous da yaji nama ta dawo parlor ta kwanta, har bacci ya dauketa ta farka da sauri don ko cous cous din bata xuba ba, ta dawo parlor bayan tayi hakan bacci ya sake saceta, cikin bacci ta dinga jin k'auri, ta shi da sauri ta nufi kitchen din, turus tayi komai nata ya tsaya ganin wanda ke tsaye bakin gas, wani ihu tayi ta juya cikin rikicewa xata fita ya fixgota, ya matse ta jikinsa ya rufe bakinta, kasa kwakkwaran motsi tayi ta kuma kasa freeing kanta, hawaye ya cika idonta taji kafafuwarta sun kasa daukarta, yana mata wani kallo cikin husky voice nasa yace "Kin gama gudun kin dawo?" Xaro ido tayi tana kallonsa da mugun mamaki, bai damu da hakan ba yace "All this while kina gidan boy Friend din ki right?" Takaici ya rufe ta dake tace "Yess" yyi wani murmushi yace "Kina me?" Tace "Abinda kke kawo yan mata suke yi a flat din ka...." Ko rufe baki bata yi ba ya hade bakinsa da nata, ta rude ta dinga kokuwa da shi amma ko gezau, don kansa ya saketa yana kallonta da lumsassun idonsa yana murmushin rainin hankali yace "Haka kenan" ta fashe da kukan takaici ta durkushe a wajen xuciyarta na tafarfasa, yace "Next time ba sai kinje gidan saurayin ki ba, you need it... Ki sameni a flat dina kawai" daga haka ya nufi kofa, sai kuma ya juyo yace "Mind you, I hate smell of burnt foods" yana kai wa nan ya fita gidan gaba daya cike da kasaita, ta mike da sauri ta na kallon kofar don a tunaninta ta rufe da ta shigo.


*Haske Writers association*💡



*Haske Writers Association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻

4......

Ta fi minti biyar a tsaye duk jikinta a mace, tunani daya ya xo xuciyarta a lokacin and that is ta bar apartment din ta koma gun Vanessa da xama gaba daya har ta samu wani gidan, ta juya ta kalli gas din kitchen din taga ya kashe, kamar mara laka ta fito parlor ta karasa kofa ta sa key, xaunawa tayi parlor har lkcn tana ganin abun kamar a mafarki, ita fa yanxu bata ga namijin da ya isa ya takura ma rayuwarta, ba ayi namijin nan ba ko waye shi kuwa, tunanin hakan yasa ta yi murmushin takaici hade da jan tsaki ta mike ta wuce daki, nan ma dai xaunawa tayi gefen gado ta kasa daina mamaki, kiss kuma? how dare him kiss her? Haka nan kawai yayi kissing dinta kuma ta kyalesa, hawaye ne ya cika idonta tuna hakan da tayi, ca tayi masa ita gantalalliya ce? Ko kuma xaman kanta take a k'asar? ta xamo kasa ta jinginar da kanta da gado xuciyarta na kuna, to yanxu wa xata kai ma kukanta a kasar nan, nobody in particular, Vanessa won't take this as anything ko ta gaya mata ma dariya xata mata, Yusuf?? ji tayi ranta yyi wani mugun baci da ta tuna yaren da yyi mata, wai a hakan shi bahaushe ne ko kuwa Hausa kawai ya ji, abinda ta kasa ganewa kenan, ta kuma jan tsaki a xuciyarta tace ai sai dai kawai ya ji Hausan don in har dai shi Afuno ne he is nothing but a disgrace to Hausa and Hausa land as a whole, infact ta ma san ba bahaushe bane.... har kusan goma tana xaune kamar mara abun yi, xuciyarta dai ya kasa dawowa dai dai, ta Dade ranta bai baci ba irin na yau, can dai ta kuma jan tsaki for the countless time tace "Sai nayi maganinka kafin in bar gidan nan in sha Allah, you can't just put ur filthy mouth in mine and go scot free...." daga haka ta mike ta shiga bathroom, wanka ta yi ta dauro alwala ta fito ta yi shafe shafenta ta xura doguwar Riga ta tada sallahn Isha, ko da ta idar ta shafe addu'o'in da tayi ta jawo wayarta don sau biyu ana kira tana sallan, Vanessa ce ke kiranta, ta shiga kiranta baya, Vanessa na dagawa tace "Hey love, you are still nt yet back" Khadijah ta kalli agogo a hankali tace "It's late Vanessa, I will come over tomorrow" daga haka Vanessa tayi mata sai da safe ta katse wayar, sai a sannan taji ta fara jin yunwa, ta mike ta fita xuwa kitchen don duba girkinta na daxu, tsaye tayi ta kasa kunne jin kamar muryar mace a kitchen dinsa da yake ko ina was very silent, a hankali ta karasa jikin window ta kafa kunne, nan ko ta kara tabbatar da hakan, muryar mace take ji, ta rike ha6a da mamaki k'ana ta kyabe baki ta dau plate ta debi abincin da xata diba ta fita kitchen din, tana gama ci ta tafi daki ta hada gaba daya kayan sawanta a jaka biyu, tana shirin kwanciya wayarta yyi kara, ta dauka tana kallon screen din sannan ta xauna gefen gado ta daga kiran hade da sallama, a hankali tace "lafiya lau Umma ya gida" Daga daya bangaren warce ta kira da Umma tace "Alhmdllh, na ma yi tunanin kin kwanta, ya karatun" tace "Alhmdllh Umma, yanxu xan kwanta" Umma tace "Toh Allah ba mu alkhairi, a dai dinga kula sosai kinji" cikin sanyin murya tace "Toh Umma" daga haka suka yi sallama ta katse wayar, kwanciya tayi hade da rufe duk jikinta da duvet har lkcn ranta ba dadi. Tun da ta idar da sallan asuba bata koma ba kasancewar da safe take da lectures, ta yi wanka ta wanke bathroom dinta sannan ta fito xuwa kitchen don tsaftace sa shi ma, wanke duk utensils da ta 6ata jiya tayi sannan ta hada bin din gaba daya a kwandon da aka tanadar don haka, Hijab ta koma ta xura kan yar rigar jikinta ta dawo kitchen din ta bude kofar ciki ta fita don disposing sharan dustbin, still tayi ganinsa a wajen, ya ajiye weight din hannunsa tana ganin haka ta juya da gudu ta koma kitchen ta rufe kofar da makulli hannunta na rawa, tsaye yayi jikin window din kitchen dinta yace "Ga Beast ko monster koh?" Ko kallonsa bata yi ba, ta kashe fitilar kitchen din ta fita parlor ta yi banging kofar da karfi ta rufe. Yayi wani murmushi yana share xufar forehead dinsa, Komawar da ba ta yi kitchen din ba kenan har ta gama shirin makaranta, Abaya ne baki da mayafinsa sanye jikinta, duk da yunwar da take ji haka nan ta dau jakarta ta nufi kofa, a hankali ta murda makullin ta bude ta leka waje sannan ta fito tana karanto addu'a a xuciyarta, ta gama rufe kofar kenan, wata baturiya da baxata wuceta ba ta fito daga apartment dinsa, ba karamin faduwa gabanta yyi ba don a tunaninta shine, 'yar riga ce iya cibi da wando jikin baturiyar sai yar karamar jaka da litattafai a hannunta, Khadijah bata sake kallonta ba har ta sauka d'an stairs din dake wajen, taji yarinyar tace "Good morning" yi tayi kamar bata ji ta ba tayi wucewarta, taji yarinyar na cewa "Is she having difficulty in hearing?" sai a sannan Khadijah ta gane shi ma ya fito kenan, hakan yasa ta kara saurinta, taji yace "I think so" tuni ta fice daga gidan ta tsayar da cab ta hau ta gaya masa inda xa ta, ya ja cab din, a xuciyarta tace In sha Allah ma this is the end, ba lallai ma ta kwana gidan ba yau, don tana dawowa makaranta dama fiddo kayan ta xata yi ta yi wucewarta gidan Vanessa, but she promise before leaving xata koya masa lesson xata gwada masa cewar ba ko wace mace ce sha sha sha kamar sa ba, abinda ta lura da xaman k'asar shine gwara a hadaka da bature waje daya sau dubu a kan wanda ku ka fito k'asa daya. Xaune Khadijah take tare da Vanessa da wata course mate dinsu Angela, sai wata Maryam 'yar Nigeria kamar ta amma kuma a nan UK aka haifeta, ko kadan Khadijah bata yarda sun saba da Maryam ba, hasalima gaisuwan kirki bai hadasu, ita kanta Maryam bata sake da ita ba, amma kilan hakan na da nasaba da cewar ba course daya suke ba, duk da haka dama can yarinyar bata ma Khadijah ba, ba wai tana da wani aibu bane ko wani abu, kawai she just don't like her ta rasa dalili kuma, don so tari ma idan ta ganta sai taji faduwar gaba, sannan ganin ta na tuno mata da wani abu da ba ta son tunawa a rayuwarta gaba daya, yanxun ma su kadai suke hirar su, ita dai tana ta danna wayarta kanta a sunkuye, duk ta kagu Vanessa ta tashi su tafi, dama can Angela ba kawarta bace, don she is too lousy to be kept as friend, d'an gaisuwar da suke ma da ita ta dalilin course dinsu daya ne, gajiya tayi daga karshe ta mike ganin Vanessa bata da niyyar tashi da halshan turanci tace mata xata je can gidanta ta dau kayan da xata dauka sai su hadu a can gida, Wato gidan Vanessa din, Vanessa tace to sai sun hadu, daga haka ta fara tafiya, Angela tace "See yahh tomorrow Pretty" sunan da wasu ke kiranta da shi kenan a makarantar, Juyawa Khadijah tayi ta kirkiri murmushi tace "Sure" daga haka tayi wucewarta Maryam ta bi ta da kallo. Karfe biyu da yan mintuna ta isa gida, ta fito ta ba mai cab kudinsa, a hankali take jin faduwar gaba har ta shiga ciki tana kallon parking lot ta ga bbu motarsa, ajiyar xuciya ta sauke ta nufi flat dinta da sauri don ta yi abinda ya kawota ta bar gidan, da d'an mamaki take kallon farar matar dake tsaye b'akin apartment dinsa matar na rike da wata kyakkyawar yarinya kamar ta, lkci daya kuma tana kuma danna wayar hannunta, Khadijah bata sake kallonta ba ta shiga kokarin bude apartment dinta, a hankali matar tace "Hi" sai a sannan ta juyo ta kalli matar, ita dai matar ga ta kamar fulani kamar kuma balarabiya, idanuwanta kuma kamar na neighbor dinta, Khadijah ta dauke kai tace "Hello" matar tace "Plss Dr Ayman, will he be back anytime soon?" Khadijah ta mata wani kallo a takaice tace "I don't knw" Matar tace "Really? And I have being Calling but I can't reach him" Khadijah da har ta bude kofar ta tace "Hard luck" daga haka ta shiga ciki sai kuma ta juyo suka hada ido da cute babyn hannun matar, kasa rufe kofar tayi a hankali tace "Or you go come back, may be later" matar tace "Am from a far place, and he knws I will be here" Khadijah ta rasa abinda xata ce, can dai ta dauke kai ta juya ba don ranta ya so ba kuma don tausayin babyn hannun matar tace "If it's ohk... u can come in and wait him" daga haka ta shiga parlor matar tace "Alryt Thank you" ta shigo parlorn ta xauna, Khadijah ta bude fridge ta kawo mata ruwa da lemo ta ajiye mata, matar ta d'an yi murmushi tace "I am fatima Ayman" kallonta Khadijah tayi na yan sakwanni kafin tace "Am Khadijah Muhd" Matar da ta kira kanta da fatima tace "Ohh that's nyc, from which country?" Khadijah tace "Nigeria" d'an buda ido fatima tayi tace "Tribe" Khadijah tace "Hausa Fulani" Fatima tace "Waow ashe Hausa ce ke sister" Khadijah ta kalleta tayi murmushi tace "Ehh" Fatima tace "Allah sarki, amma naji dadin haduwa da 'yar uwata daga Nigeria, na xo nan last 3 weeks but kamar baki nan" Khadijah tace "Eh naje gida ne" Fatima tace "Maa sha Allah, tare da mai gidana muke ya xo wani aiki a nan shine nace ya ajiye ni kawai mu gaisa da yayana tunda yau xa mu koma, kuma fa na sanar da shi yayan nawa xan xo amma dubi yanda ya shanya ni a waje" murmushi kawai Khadijah tayi ta amshi babyn hannun ta tana kallonta tace "Ya sunanta?" Fatima tace "Iman...." Lkci daya murmushin dake fuskar Khadijah yyi fading jikinta yayi sanyi......

*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨






_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻






5.....

Fatima da bata lura da yanayin da Khadijah ta shiga ba tace "But ina jin kilan ya shiga schl ne, kinsan PhD din nan sai hankali, yanxu ma idan Abban Iman ya kira dole sai dai mu wuce kawai tunda ban san lkcn da xai dawo ba" Khadijah dai bata ce komai ba ta mike a hankali ta kwantar da babyn da uwarta ta kira da Iman, ta kirki murmushi tace "Bari in shiga kitchen" daga haka ta kunna masu kayan kallo ta wuce cikin kitchen, kauda damuwar da ya so dirar mata a rai tayi, ta jingina da kitchen cabinet tana tunanin light abinda xata girka masu da baxae dau lkci ba, can dai ta fiddo Irish ta shiga ferewa, cikin minti ashirin ta gama hadadden porridge din Irish da yaji kayan hadi da hanta da nama, tuni kamshin dahuwar abincin ya kauraye ko ina na gidan, fitowa parlor ta yi fatima dake xaune tana danna wayar hannunta tace "Sannu da aiki" Murmushi Khadijah tayi tace "Thank you, hope ba ku yi fushi ba na bar ku ku kadai" Fatima tace "Ayya ba komai ke da kike aiki" Khadija ta koma kitchen tayi serving abinci a plate tasa fork ta daura kan tray da glass cup na ruwa a gefe ta fito parlorn tun kan ta ajiye fatima tace "Toh fah, ni fa a koshe nake khadijah, wlh am nt hungry bamu dade da cin abinci ba" Khadijah ta d'an canxa fuska tace "Saboda ke fa nayi girkin" fatima tace "Ayya, to ban san xai ko anjima ba amma yanxu gaskiya a koshe nake kiyi hakuri" dai dai nan aka bude kofar parlorn duk suka kalli direction din, tsaye yyi bakin kofar kamar me examining din wani abu, Khadijah da xuciyarta ya kusa shigewa cikinta tayi saurin kauda kanta gabanta na faduwa, mikewa fatima tayi da fara'a da farko sai kuma ta hade rai tace "Yaya ai da sai ka ce min kar in xo baka nan, ka wani shanya ni a waje ina ta jiran ka," karsowa yyi cikin parlorn da takalmansa ba tare da ya kalleta ba bare ya tanka ta, fatima ta xaro ido tace "Ana fa sallah yaya.... Ka cire takalmin" Bai ce komai ba ya duka yana kallon Iman dake kwance saman kujera, sai a snn yyi murmushin da ya bayyana light dimples dinsa yace "She's.... growing" daga haka ya dau babyn ya manna mata kiss a cheeks dinta ya juya ya nufi kofa yana cewa "Wayata na silent I don't knw u were calling," Fatima tace "Uhn ai shikenan, ya karatun" bai tanka ta ba har ya fita, kallon Khadijah tayi tace "Nagode sosai Khadijah Allah ya saka da alkhairi" Khadijah ta kirkiri murmushin karfin hali tace "Welcm" fatima ta dau jakarta da abun daukan babynta tace "Bari in je mu gaisa" daga haka ta juya ta nufi kofa Khadijah tace "Toh abincin fa?" Fatima ta yi yar dariya tace "Toh shkkn bari dai in je da shi" dawowa tayi ta duka xata dauka ganin kayan hannunta khadijah tace "Let me help" fatima tace "Toh nagode" khadijah ta duka ta dau abincin, sai kuma tayi still tunawa da tayi hakan na nufin parlornsa xata shiga kenan?? Tuni fatima ta isa kofa, a hankali ta bi bayanta a sanyaye ba don ta so ba, fatima ta bude kofar yayan nata ta shiga da sallama, b'akin cover shoe dinsa na ajiye bakin kofa wato ita ya raina xai shigo mata parlor da takalmi, xaune suka gansa kan daya daga kujerun parlon yana rike da Iman dake 6a66aka masa dariya, kallo daya Khadijah tayi ma hadadden parlon nasa tayi saurin sunkuyar da kai gabanta na faduwa, fatima da har ta xauna tace "Ina yini yayana" yace "Ya kike" tace "Alhmdllh ya karatun" karasowa Khadijah tayi ta ajiye abincin hannunta ba tare da ta dago kai ba, ya kafeta da ido, kamar ta sani kuwa ta ki kallon inda yake, fatima tace "Yaya neighbor dinka tana da kirki sosai, ka taya ni yi mata godiya" yace "Koh?" Kallonsa fatima tayi ta kasa cewa komai jin kalan tambayar da ya jefo mata, sannan tafi kowa sanin halin wan nata, hakan yasa kawai ta bude jakarta tana murmushi tace "Guess what yaya...." Ya kalli jakar bai ce komai ba dai, Envelope ta dauka ta mika masa tana yar dariya tace "3 days ago su Ummu suka ba Abban Iman ya taho da shi" Karba yyi yace "Meye a ciki?" Ta buda ido tace "Invitation card din ku mana...." Mayar mata yyi yace "So?" Tace "Aa cewa aka yi in kawo maka" yace "To mayar" Fatima tayi murmushi tace "Ko dai Jawahir din ta tura maka ne" Ya hade rai yana kallonta sai kuma ya juya yare xuwa larabci, tuni khadijah ta nufi kofa dai dai lkcn da aka bude kofar, wata black American mai kyau ta shigo parlorn tana sanye da wasu damammun kaya, ta daga masu hannu gaba daya da murmushinta tace "Hi" daga haka ta nufi bedroom, lkci daya mood din fatima ya canxa ta bi yarinyar da kallo, shi kam ya dauke kai, Khadijah ta saci kallonsa suka hada ido, tabe baki tayi ta dauke kai ta juya ta bude kofar ta fice abin ta a ranta tace Allah wadaran naka ya lalace, ko kunya bai ji ba, Tana komawa apartment dinta ta shiga gyare gyaren ko ina na gidan, duk wani abu da tasan xai iya samun matsala a fridge duk ta tattara su gu daya don tafiya da su gidan Vanessa, kafin la'asar ta gama komai tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta shirya cikin kananun kaya ta daura kimono a kai ta yafa gyale a kanta xata fito parlor aka danna bell, karasawa tayi ta tsaya bakin kofar tace "Who's there?" Muryar fatima taji tace "Ni ce Khadijah, dama nace in maki sallama xan wuce" Khadijah ta bude kofar tace "Ayya, har xa ku tafi" fatima ta kirkiri murmushi duk da Change din mood dinta tace "Wllh kuwa, Abban iman na jiran mu" Khadijah tace "Toh shkkn, Allah ya tsare hanya, ya kai ku gida lafiya" Fatima tace "Ameen ngd, tnx once more for the hospitality" murmushi kawai Khadijah tayi, aka bude kofa sai gashi ya fito rike da Iman, Fatima ta kallesa da kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "Ya Khaleel da gaske baxa ka kai mu ba mu hau taxin kawai" a takaice yace "Ehh" ta langwabar da kai tace "Toh shkkn" majestically yyi wucewarsa waje, Khadijah ta bi sa da ido, fatima da ta bi sa da kallon ita ma tayi murmushi tace "Kinga da gaske taxi xai tsayar mana maimako ya ajiye mu da motarsa daga na gaya masa gaskiya...." Khadijah tayi murmushi bata dai ce komai ba, Fatima tace "Toh muje wayana na gun sa sai ki sa min digit din ki mu dinga xumunci" Khadijah ta bi bayan ta ba don ta so ba, ko da suka isa har ya tsayar da mai cab yana jiran kanwar tasa, fatima tace "Yaya idan ma fushi kake da ni kayi hakuri pls" ya kalleta bbu yabo bbu fallasa yace "Not at all, shiga ki tafi inda xa ki" tace "To bani wayar Khadijah ta sa min digit dinta" yayi kamar bai ji ba ya bude back seat yace "Shiga malama" fatima ta shiga ya mika mata

1 Comments On NOOR AL HAYAT
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls inason novel dinnan cplt

Please Login or Register in order to submit comment