Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu ta bar gidan duk jikinta a sanyaye, da Khadijah ta dawo ta kyallara ido taga ba umma ta dinga ihu tana kuka a gidan tana cewa a kai ta gun ta, Bakin yakumbo a leko ta dauko muciya tace "Kin ga wannan abun hannu na? To wllh da shi xan fasa maki kai idan kika ci gaba da tona min asiri a anguwa, kaji min katuwar banxa, maxa ki tafi tare da Fauxiyya ku siyo min ice da xan yi tuyan awara anjima" Jikin khadijah na bari suka fita, matan gidan dake ta kallon ikon Allah suka ce "Yo ke kulu da kike jiran fauxiyya ta kara wayo ki kai ta aikatu kina samun kudi don me baxa ki kai wnn budurwar da aka kawo maki ba? Ai wannan da ganinta bbu aikin da baxata iya ba har wanki" Yakumbo tayi shiru tana kallonsu.

Ko da suka dawo gidan firewood kwara biyu kadai khadijah ta riko a hannu, fauziyya kuma ta rike ya kusa shidda, daga matan gidan har Yakumbo sakin baki suka yi suna kallon Khadijah da ta ajiye tana haki, yakumbo tace "Meye wannan din kika dauko?" Da kyar khadijah tace "Firewood, it's too heavy, and it's pricking me all over" a fusace Yakumbo tace "Kin ma uwar ki Amina turanci ba ni ba, kuma ke kadai xaki koma ki kwaso duk wanda ga rage fauziyya baxa ta je ba tunda ba ki da mutunci" korata Yakumbo tayi ta fita ta na share hawayen dake sakko mata, mai firewood din ganin yanda take hawaye kuma kana ganinta kasan baxata iya dauka ba ta dauko wani rabanta ta xuba mata su a ciki ta daura mata a kai tace "Kina kai wa ki dawo min da roba na kin ji" a hankali khadijah tace "Toh nagode" A haka ta isa gida tayi ta tsayuwa da roba a kai wai bbu ke sauke mata inji Yakumbo, daga karshe ladi ta kike ta sauke mata tana cewa "Idan ka xa ki kama jiki ki kama jiki ki daina ma mutane kamar mara laka a jiki" Khadijah dai bata ce komai ba, bayan ta juye iccen tace ma yakumbo xata mayar da roban, ko kallonta yakumbo bata yi ba ta juya ta fita kai ma mai iccen robar ta. Yakumbo ce tsaye tsakar gida bayan kwana uku da xuwan su Umma, tafi minti talatin banda kumfar baki da masifa bbu abinda take, ga matan gidan da yaransu a xaune babu mai bata hakuri sai ma xugata da suke, khadijah kuma na tsaye bakin xaure duk tayi wani duhu ta rame sosai, idonta duk ya kumbura don kuka ga shatin bulala a jikinta, Ladi tace "Yo da kinsan haka ne tun farko kema ai baxa ki fara daukarta ba, meye amfanin yaron da baxa ka amfana da shi ba sai shegen son jiki da iyayi, ai kadan ma kika mata da kin hada kin fasa shegen bakin turancin da take xagin mutane da shi a gidan nan" Yakumbo na huci tace "Ai Amina ta cuce ni, ta yaudare ni... Tasan haka shegiyar yar take xata kawo min ita tun farko, gode gode da yarinya bata iya komai ba wanke wanke duk ta jika kayan jikinta tayi awa da awanni a bakin kwararo, shara duk a gantale, gyaran daki gwara ka da fauziyya mai shekara biyar, aike sai kayi yyi sau uku, har yau ta kasa iya hura icce, girki dama ba a maganar sa, wa ennan yan mitsimitsi yaran idan na sa ta tayi masu wanka ta shaka masu sabulu a hanci ko a ido, ni dama tun farko abinda ya sa na karbeta na yi xatan xan amfana da ita ne, banda haka me xai kai ni kowa na ta kansa a rayuwar nan gashi gobe ko jibi xa a xo a fitar mana da kaya har ynxu ban kama wani gidan ba, ni wllh wllh da nasan gidan Amina sai in yi kudin mota in mayar da ita ta bani kudi na don baxan iya kayan tsiya ba, dama can Aminar ma ba wani kyautata min take ba uba ne kadai ya hada mu" Salamatu tace "Ai irin yaran nan kyansu aikatu wllh, a can xa a horasu su ladabtu...." Katse ta yakumbo tayi tace "Yar da har yanxu bata iya shara ba xan kai aikatau, ai koramu xa ayi daga ni har ita" Ladi tace "Yo ke nuna masu xa ki yi bbu abinda bata iya ba ai, a can xa su gyara mata xama ta iya komai, mutanen da basu san darajar d'an Adam ba, ai tuni wahalar da xa su dinga mata xai sa ta xage a nan kuma xata koyi komai, wannan d'an abincin da kike bata ma take kin ci take yawo da yunwa can nema xata yi ta rasa, hakan xai ladabtar da ita wllh" Yakumbo ta ja kujerar tsugunno ta xauna tace "Kai amma fa kun kawo shawara, amma...." Sai kuma tayi shiru ta kalli khadijah dake kallonsu, tsawa tayi mata ta ce "Fita ki ban waje kije gun mai kanti da hamsin di ta dake gunsa ki amso min barkonu" juyawa khadijah tayi da sauri ta fita gidan, Yakumbo ta mayar da dubanta gun su Ladi tace "Toh Amina fa? Kunsan baxa ta yarda ba" dariya Ladi tayi tace "Ka ji ki, sai ki gaya mata, barin ma yanxu tashi xa ku yi Ku bar anguwar, shawara a nan shine kada ki kuskura ki gaya ma ko inda kika koma a anguwar nan, kawai cewa xa ki yi ba ki ma samu gidan ba gidan wata yar uwarki xa ki kafin ki samu, ke kuwa kije shanono abun ki ki kama ko daki daya ne bbu wanda yasan inda kike, dama ba waya gare ki ba, har ki tara kudin da xa ki tara da yarinyar daga nan idan ma mayar da ita gun Aminan xa ki yi sai ki ja mata kunne ki mayar da ita" Yakumbo tayi murmushi tace "Dadina da ku akwai shawara mai ma'ana, amma fa har da kudin da xan sa yarinyar a makarantar gwamnati ta bani, yanxu haka ma da kudin xan je kama haya a shanonon, dubu hamsin kuma jari xan ja na su omo da sabulu ina siyarwa, ita can na kai ta gun aiki ana biyanta dubu uku misali, kun ga ni ban ma kai da nisa ba...." Ladi tace "Toh gaskiya sai kin ba mu dubu dai dai mu da muka kawo shawarar Ashe ma kudi gare ki har haka" yakumbo ta hade rai tana da ta sanin gaya masu, rai a bace tace "Dari bibbiyu dai" daga haka ta mike ta shiga cikin akurkin dakinta, sai ga ta ta fito da sauri tace "Toh yanxu wa xai min hanya in kai ta gidan aikin, don ni gaskiya baxan tare da ita a sabon gidana ba, ko yau aka samu gun aikin ba don yamma yyi ba kai ta xan yi, don haka gobe da safe xan kai ta...." Ladi tace "Akwai wata kawata Habiba dillaliyarsu ce, xan baki lambarta... Ko kuma ki sa katin dari a wayata mu kirata, in sha Allah nasan baxata rasa inda xata kai maki ita ba" hakan ko aka yi Yakumbo ta sa kati ladi ta kira Habiba, suka ci sa'a number ya shiga, bayan ladi ta gaisa da kawartata tace "Bibalo dama wata yarinya ce da ake son kai ta gidan aiki to shine muke son ki yi taimako" Bibalo tace "Kai yanxu haka Ina hanyar dawowa daga kauye na mayar da wasu yara, amma gobe da safe xa ki gan ni duk da bani da wa enda ke son masu aiki yanxu, amma nasan kawata Abu baxata rasa ba don ta ma fi ni sanin gidajen manya" daga haka suka yi sallama ladi ta katse wayar tana kallon Yakumbo don ba sai ta mata bayani ba tunda a handsfree tasa ita ma ta ji komai, Yakumbo tace "Toh Allah ya sa a dace, ni wllh ko dubu biyu ma xa a dinga biyanta na yarda" tagumi tayi tace "Allah gani gare ka, kasa a karbi yarinyar nan ni kuluwa" Washegari da safe kuwa sai ga Bibalo tare da kawarta da ta fada Abu, Yakumbo dake ta washe hakora ta gaishesu suka amsa aka xaxxauna kan tabarma ladi ma ta fito akurkin ta tana masu sannu da xuwa, bayan sun gaisa Bibalo tace "Toh kinga ni bni da inda xan kai ta amma Abu tace kawarta ta taba hadata da wata Hajiya mai neman mai aiki, da xata dinga share share da goge goge sannan wanke wanke, akwai ma wata babbar mai aiki dake girki a gidan, to Abu taje gidan ya fi sau uku ba a bude mata gate, yanxu ma gwada sa'a xa ayi kuje har da ke kika wajen, idan sun dauketa to, idan kuma sun ce A'a sai ki jira har a bukaci mai aiki a wani gidan sai in kai ta" Yakumbo tace "A'a mu je kawai mu gwada sa'ar mu" Bibalo tace "Toh ki sallame ni ni xan wuce" Yakumbo ta hade rai tace "In sallame ki? Me kika min da xan sallame ki" Bibalo ta bude baki tace "Au haka ma xa ki ce, shi kudin motar da nayi da kuma bata lokacina da na yi na xo nan tare da kawata har xa ki ce min me na maki" mikewa Yakumbo tayi rai a bace ta shiga ciki ta fito da dari biyu tana cewa "Ko daukar yarinya ba ayi ba xaki wani ce in sallame ki idan ba hadama ba" dungura mata dari biyun tayi a gabanta rai a bace, Bibalo ta dauka ta mike tace "Ya fi babu ai" daga haka ta yi ma Ladi sallama da Abu tayi ficewarta, Abu tace "Toh inji kinsan mu dubu daya ce sallamar mu?" Yakumbo ta hade rai tace "Idan an dauki yarinya ba" Abu tace "Toh gwara da kika san haka don ni baxan tsaya cacar baki ba, yanxu Ina yarinyar take?" Yakumbo ta nuna mata khadijah dake ta fama da wanke wanke, kwalalo ido tayi tace "Warcen da ta fi minti ashirin tana d'an wanke wanken can, tun shigowar mu fa take wanke wanken kamar ayi kamar baxa ayi ba" yakumbo ta marairaice tace "Haka take Abu, akwai iya aiki amma ba sauri ne kawai, amma tana xuwa can nasan xa su gyara mata xama ta xama mai hanxari" Abu ta tabe baki tace "Toh unguwar da nisa, don can Gra ne, kuma wllh gidan babban mutane ne, ni dai Allah ya sa su dauketa, yanxu sai ki tashi ku shirya ta hada kayanta ina jiran ku mu kama hanya" Yakumbo ta mike da sauri ta shiga ciki tana cewa "Toh bamu minti biyar kacal" tana shiga dakin ta kwalo ma khadijah kira, khadijah ta mike ta shiga da sauri. Yakumbo ta jawota tayi kasa da murya tace "Dijangala ta mai gari, ba auren talaka ba" tana washe hakora ta fadi haka, ita dai khadijah kallon ta kawai take, Yakumbo tace "Kinsan inda xa mu yanxu kuwa?" Girgixa kai khadijah tayi, Yakumbo tace "Gidan da xa a dinga biyanki kudi mai yawa in tara maki in sa ki a boko, kai har in maki aure ma" khadijah tayi shiru bata ce komai ba, yakumbo ta marairaice tace "Don haka muna xuwa kice kin iya aikin komai, sai ki bada himma idan an saki aiki ki yi da sauri da sauri, sannan don Allah Idan mun je gidan khadijah kar ki masu wannan yaran naki na turanci kin ji koh? Kawai Hausa xa ki masu, idan kuma baki san Kalmar da xa ki fada da hausa ba sai kiyi shiru abun ki ba sai kin yi turancin ba" yanxu maxa canxa kayan Ki bari in tusa maki wa encan a jaka tunda basu samu wanki ba idan kin je can ko ba ki iya wankin ba ki tsoma su a ruwa ki xuba omo ki shanya" daga haka Yakumbo ta shiga tusa kayanta a wani karamin Ghana must go, don har ta siyar da jakar da Umma ta kawo mata kayanta ciki, karfe tara da kusan rabi su yakumbo suka bar gidan tare da Abu bayan ta yi ma yan gidan sallama suka dinga yi mata Allah ya bada sa'a, tana rike da hannun khadijah suka isa bakin titi, Abu tace "Amma kinsan ke xa ki biya kudin abun hawa dai koh?" Yakumbo ta tsuke fuska tace "A kan me?" Abu tace "A'a mayar da wukar ae dai naga ba xuwan kai na xan yi ba gidan don hka idan kinsan gidan ke sai ki kai ta, yakumbo ta rikota da sauri tace "Naji, mu je ya na iya, daga yau ai babu wanda xai xo yace in biya masa kudin napep dai koh?" Ko tanka ta Abu bata yi ba ta shiga napep din da ta tsayar, Yakumbo ta shiga ta daura khadijah a cinya. Tafiya ce mai nisa kamar yanda Abu tace masu, tun da suka bar hayi dama Yakumbo ke addu'ar Allah ya sa a dau khadijah gidan aikin idan ba haka ba asirinta ya tonu don ta sa rai da kudin da xa a dinga biyan khadijah, tun da suka shigo anguwan Yakumbo ta saki baki kamar yawu xai dalalo tana kallon gidaje na alfarma, Abu ta dinga nuna ma Mai napep din inda xai bai, har suka iso wani cool silent anguwa mai cike da shuke shuke a ko wani gate, ga bakin kwalta a shimfide daga farkon layin har inda yakumbo ke tunani karshe ne, bakin wani gate Abu ta sa mai napep din ya tsaya, yakumbo ta wage baki tana kallon jibgegen gidan da aka yi ma ginin xamani kamar ta sure ta gudu, gidan ya hadu ne kawai don ita a ganinta duk ya fi sauran gidajen dake layin haduwa, suka sauka sai kuma Yakumbo aka tsuke fuska da ta tuna kudi xata bada yanxu, ta dungura ma mai napep din kudin da yace lkci daya kuma tana hararan Abu, Abu da ko lura da ita bata yi ba tace "Toh Allah ka bamu sa'a don kwanaki da na xo haka na sha xamana bakin gate rana yayi maganina ban samu shiga gidan ba... Yakumbo tace "Yana da kyau mutum ya dinga fadin alkhairi ko yayi shiru, yanxu me ya kawo wannan xancen, in sha Allahu ma sai mun shiga don haka ki mana shiru" daga haka Yakumbo bta kwankwasa gate din a hankali kamar me tsoron kada ya fashe don ita fa gani take kamar glass ne a kauyancinta, ta kwankwasa ya kai sau hudu kafin wani da alamar mai gadi ne ya bude yana kallonsu, Yakumbo ta durkusa har kasa ta gaishesa, yace "Wa ku ke nema?" Yakumbo ta mike tace "Matar gidan muke nema ce mana tayi mu samo mata mai aiki yarinya karama, to cikin ikon Allah gashi mun samo mai haxaka, shine muke hadaka da Allah yaro ka bar mu mu shiga, mu gabatar mata da aiken da ta mana" ya girgixa kai yace "Ai akwai mai aiki yanxu haka a gidan don haka ban ji xa a bukaci warce xa ku kawo" Bakin yakumbo ya fara rawa tace "Wllh xa su bukata dubeta fa kaga bbu abinda bata iya ba, sannan Hajiyar da kanta ta sa mu ko daxu mun yi waya da ita tace sai mun xo, haba yarona ka duba tsufana mana gashi daga hayin rigasa muke wllh" Mai gadin yace "Toh yanxu ma ku kirata idan tace ku shiga toh shkkn" daga yakumbo har Abu aka hadiye yawu da kyar don babu mai waya cikinsu, Yakumbo tayi karfin halin cewa "Wallahi wallahi na mance wayar a gida kaji rantsuwar musulmi" Abu ta saki baki jin rantsuwar da Yakumbo tayi alhalin taji Bibalo tace bata da waya.


Taku har kullum Hauwa Bello Jiddah (Khaleesat Haiydar) 📚✍🏻

Thanks once more for patronizing my book fans... For those still wanting to buy the complete document it's just 300 Via transfer 👉🏻 3276052019 Hauwa Jiddah Bello, fcmb.

07087865788.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On NOOR AL HAYAT
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls inason novel dinnan cplt

Please Login or Register in order to submit comment