Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarinyarta sannan ya bata wayarta, tace "Bata sa number ba ai yaya" ya hade rai yace "Xan tura maki ta WhatsApp" rasa abinda xata ce masa tayi, ganin yanda ya hade rai tace "Toh baxa ka ba mai cab din kudi ba" yace "Bani da" yar dariya tayi tace "Kai ya khaleel ba ma haka da kai fa, kayi hakuri kar in tafi kana fushi da ni" Khadijah da ko kallonsa bata yi ba ta daga ma fatima hannu tace "Toh Allah ya tsare hanya Maman baby" daga haka ta juya da sauri ta koma ciki don bata son ta ci gaba da jin kayan takaici, tana shiga bedroom ta wuce direct ta dinga fiddo kayan da ta harhada, taje dauko na karshen taji an bude kofar parlor, still tayi na yan sakwanni sai kuma ta juya da sauri ta fito xuciyarta na bugawa.


*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻

6......

*Nigeria*

Ajiye fork da knife din hannunsa yyi ya tura abincin gabansa lkci daya ya fuzar da iska ya dau tissue yana goge bakinsa ya mike ya bar dinning din, mum dinsa dake xaune parlor ta bi sa da wani kallo tace "Barin abincin kayi sbda xancen da nake maka Aliyu?" Kallonta yyi da sauri yace "Noo, not at all Mum, xan je sallama da Granny ne coz am leaving as early as possible tomorrow" daga haka ya dau makullin motarsa da ya ajiye kan Center table ya nufi kofa yace "Sae na dawo mum" tagumi mahaifiyar tasa tayi ta bi sa da kallo cike da damuwa har ya fita, ya fuzar da iska bayan ya shiga motarsa ya jinginar da kai jikin kujera hade da lumshe ido yace "Ba ta taba barin in ci abinci in koshi Mum, always with a particular complain" ya bude ido a hankali snn ya tada motar yyi horn mai gadi ya bude gate ya fita rai ba dadi, bai yi minti goma yana tafiya a Independent way ba wata 206 dake gabansa ya taka wani burki da har sai da ya kusa bugesa ba dan shi ma yyi saurin preventing hakan ba, wanda hakan kuma ya janyo motar dake bayan tasa motar ta buge sa, Kilan rudewa ya sa me 206 din ya juye kan steering wanda hakan yasa ya buge motar gefensa shi ma da karfi, everything just happened all of a sudden, lumshe ido Aliyu yyi ya bude yana kiran Allah a xuciyarsa bayan komai yyi still kamar ba ayi ba, sai a sannan ya lura da wani bike ne ya shigo ma mai 206 din yyi kkrin avoiding da ya janyo faruwan slight accident din, Aliyu ne ya fara fitowa daga motarsa daga nn kuma kowa ma ya fara fitowa, ya nufi 206 din da har driver din ya fito da sauri ya bude back seat, kukan yara ke tashi a motar, jin hakan Aliyu ya karasa da sauri gun motar, identical twins ne bayan motar da baxa su wuce shekaru biyar ba, Aliyu ya fiddo su duk biyun daga motar yana kallon yaran dake sanye da uniform din makaranta ya durkusa a hankali yace "Hey boys are you okay??" Dayan kadai ne ya gyada masa kai a tsorace, dayan kuwa banda kuka babu abinda yake yana kiran Anty, kallon yaran kawai Aliyu yake ko kiftawa bbu, muryar mutanen da ke tsaye gun kowa na fadin albarkacin bakinsa yasa shi mikewa a hankali yana shafa kansu yace "Sorry Boys, Allah ya tsare gaba" Wani mutumi ne ya dinga tambayarsu inda ke masu ciwo duk suka girgixa kai, Aliyu ya daga kai jin abinda mutumin da ke gefensa ke ce masa yana kallonsa, "Allah dai ya kiyaye gaba ka tafi da yaranka gida kawai, Allah kyauta na gaba" cewar mutumin kenan, wani mutumi ma ya sake fadin makamancin hkn, murmushi yyi yace "No, ni ban san su ba" mutumin karshe da yyi magana ya kalli yaran sannan Aliyu, kada kai yyi yace "Ikon Allah...." bude bayan motar Aliyu yyi ya shigar da yaran yana kallon Drivern yace "Ka ajiye su gida, Allah ya kiyaye gaba" godiya Drivern yyi ma mutanen wajen ya shiga motar ya tada ya hau kan titi ya bar wajen. Aliyu ya koma gun motarsa ya shiga har lkcn cute twins din na ransa, bai kuma damu da kallon da wasu suka bi sa da shi ba. A waje yyi parking ya shiga gidan grandmum dinsa da sallama bayan sun gaisa da masu gadi, wata budurwa ce da baxata wuce shekaru ashirin da daya ba kwance kan kujera dake parlon tana danna waya, sau daya ya kalleta bai sake kallon inda take ba ya wuce dakin grannynsu da suke kira da yaya, sllh ya sameta tana yi ya kalli agogo sanin Magrib bai yi ba, ya tabe baki ya dawo parlon ya xauna ko sallan me take, ba a dau lkci ba ta biyosa tace "Mijin ka xo kenan" ya gaisheta ta amsa da fara'a tana tambayarsa ya hanya, yace "Alhmdllh" ta kalli budurwar dake kan kujera tace "Ke koh Salmah kun gaisa da yayan naki" yarinyar ta gyada mata kai idonta a kan waya, ya kalleta fuskarsa daure yace "Uban wa kika gaida?" Ba ta ko kallesa ba tace "Yaya ni ki ce ya daina xagi na plss" Mikewa grandmum din tasu tayi tace "A'a ni dai gaskiya ba a gidana ba yau, ku je can gidan iyayen ku ba ruwana, kai kuma naga ai ba dole bane sai an gaisheka, ke kuma sa'an ki ne shi din da baxa ki gaishesa ba" mikewa yyi ya nufi kofa, kakar ta bi bayan sa da sauri tana cewa "Ina kuma xaka Aliyu" bai juyo ba yace "Sallama dama na xo maki gobe xan wuce Uk...." da sauri take bin sa ganin yaki tsayawa tace "Toh baxa ka tsaya ba ina ma magana" yace "Mu yi waya" bata fasa bin sa ba tana cewa "Da kai fa nake Aliyu..." juyowa yyi yace "Don Allah yayah ki rabu da ni dama sallama na xo maki kuma gashi na maki dai ko" rike ha6a tayi tace "Yo ni me ya sha min kai da sallamar ka da rashin sa, magana ce dai baxan fasa maka ba tunda ba tsoronka nake ba, baka kuma isa inji tsoron ka ba, kum maganar dai da baka so ce xan maka wato maganar aure, Aliyu sa'annin ka daga me d'an shekara biyar sai mai d'an shekara shidda kai har bakwai akwai, yanxu kai baxa kayi ma kanka fada ba kasan inda ke maka ciwo d'an nan, ga mahaifin ka ya xuba ma na mujiya ya kyaleka ya fita lamarin ka, me kake son mayar da rayuwar ka ne, idan ma lafiya ce baka da ba sai ka mana bayani ba ko ni in kai ka asibiti amma ka mayar da mu shashashai...." tsaye yake yana saurarenta sai dai bai juyo ba har ta kai karshe sannan ya juyo yana kallonta yace "Allah kawo lkci yayah" daga haka yyi ficewarsa daga gidan, ya jima xaune mota ya kasa barin anguwar, ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido a hankali ya bude cikin sanyin murya yace "Can I ever get her? Then Where?" Lkci daya idonsa ya kada ya hade kansa da steering, ya fi minti goma a haka kafin yyi karfin halin dagowa ya tada motar ya bar gun jikinsa a sanyaye, yana hawa independent way yaran daxu suka fado masa, ya d'an yi murmushi loving to see them once more and their parents. Bai yarda ya wuce gida ba a lkcn kawai ya wuce gidan abokinsa kuma amininsa Farouq, ganin Magrib tayi sai da ya fara shiga masallacin dake anguwar don gabatar da magrib bayan yayi alwala, ana idarwa kuma suka fito tare da Farouq, gaisawa suka yi Farouq yace "D'an rashin kirki kace min xaka dawo ranan kasa Madam tayi serving har da kai amma kaki dawowa, ina ta xuba ido, I called kuma you refused picking saboda kasan baka da gaskiya koh" Aliyu ya shafa kansa yana murmushi yace "Na ma mance me ya hanani dawowa wllh" har suka shiga gida mitan xancen Farouq yake, suka karasa har parlor, Boys din Farouq suka taho da gudu don gaida abokin dad din nasu, Aliyu ya rungumesu yana tambayar su ya school suka ce masa "Alhmdllh" Wara ido yayi yace "Toh ban ga "Baby Fiddausi ba" Ahmad yace "She's upstairs with mum" yace "Alryt maxa ku je ku ce masu Ina gaishesu" Ahmad me shekara shidda da kaninsa takwaran Aliyu suka wuce daki da sauri. Farouq dake ta kallon Aliyu yyi kasa da murya yace "Doctor...." Kallonsa Aliyu yyi da sauri, Farouq yace "I don't knw, may be am nt worth ur best..." Aliyu ya d'an bude ido yace "Ban gane ba Umar" Farouq ya girgixa kai yace "Kullum tambayata why did you prefer living as a bachelor ka ki bani answer, what's ur problem Aliyu, am I not worth knowing ur problem, I would love seeing ur kids Frnd duk clique dinmu kai kadae ne Bachelor har ynxu, tell me why... I beg you..." Kallonsa kawai Aliyu yake can yyi murmushin karfin hali ya kauda kai yace "Xan yi Farouq, lkci ne kawai" a d'an fusace farouq yace "Na gaji da jin haka Ali.. For good six years this is always ur reply, kudin gashi kana da su Alhmdllh, yan matan gasu kawo maka hari suke ta ko ina.... Toh meye kuma yayi saura??" Aliyu dai bai ce komai ba sai danna wayarsa da ya fiddo yake, farouq na masa wani kallo yace "Ko Iman din dai kake jira har yanxu, I mean aljanar nan taka..." Aliyu ya dago da sauri hade da yin murmushin da ya fiddo da ainahin kyansa na fillo ya karyar da kai yace "Yeah" tsaki farouq ya ja yana girgixa kai cike da takaici, Aliyu ya dafe shoulder dinsa a hankali yace "Look frnd, wllh ba aljana bace mutum ce kamar ka, ka bar ce mata aljana" Farouq yace "Toh wai ni abinda ban gane ba a nan shine ita ta san ka?" Aliyu ya sauke manyan idanuwansa daga kallon abokin nasa a hankali yace "Yea may be tasan ni, may be kuma bata san ni ba" Wani dariya Farouq yyi har da kyakyatawa yace "Wllh baka da hankali Haiydar, wato bata ma san ka ba?" Murmushi kawai Aliyu yyi yana shafa cute beard dinsa bai dai ce komai ba, Farouq yace "To what if tayi aure? Ko kuma tana da aure?" Murmushin fuskar Aliyu ya bace lkci daya ya mike a fusace yace "Billah sai ya saketa ko ma waye shi... Na rantse da sarkin dake busa min numfashi xan iya kashe ko ma waye ya aureta" sakin baki Farouq yyi da mamaki yana kallonsa, yana kikkiffta ido yace "Aliyu are you alright kuwa, wani irin rantsuwa da threat ne haka, anya kana right sense din ka kuwa" Ko kallonsa Aliyu bai yi ba ya nufi kofa, Farouq ya mike da sauri ya rikosa yace "Habaa, Toh Allah baka hakuri, let eat plss, In sha Allah ma Iman bata yi aure ba duk da ni dai billahil azim ban yarda ba aljana bace" yana magana ne yana satan kallon Aliyu da har lkcn fuskarsa ke daure, da kyar dai ya samu ya lallabasa ya dawo ya xauna, Aliyu ya lumshe ido yace "In kaji wacece Iman din nan xa kayi mamaki Umar" Farouq yace "Toh don Allah ka gaya min wacece" A takaice Aliyu yace "Noo baka santa ba, bata sanka ba, kilan ni kadai na santa" dariya sosai Farouq yyi yace "Ko da yake gogan ma bai san ko ta san shi ba balle ni, wllh you look confused Aliyu, Allah ya yaye maka wannan bala'i" Aliyu ya kallesa yace "Plss xancen Iman da muke ya tsaya iya nan kar ko da wasa wataran kaje can gida kana cewa Iman" Farouq yace "Why, ko sun santa?" Aliyu ya girgixa kai yace "A'a kawai dai kar ka sa a daukeni mahaukaci ne" Farouq ya jingina kai yana murmushi yace "Hauka kam ka jima da fara sa ai frnd"

*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨


_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻

7.....

Matar farouq ta sakko suka gaisa da Aliyu tayi serving dinsu abinci ta koma daki, farouq na lura da abokin nasa dake cin abincin a hankali, yayi breaking silence din after a while yace "Toh tun yaushe kasan Iman din nan ni dai ka ban labari frnd" Aliyu ya dago yana kallon sa, murmushi yyi ya ajiye spoon din hannunsa yace "Tun tana shekara sha hudu..." Farouq ya wara ido yace "Kace yanxu ta girma kam" Aliyu ya d'an bude ido yace "Uhn" Farouq yace "Kuma yaushe rabon da ka ganta a mafarkin naka" wani kallo Aliyu ya watsa masa yace "Ce maka nayi a mafarki na santa?" Farouq yace "Au, nayi xaton a mafarki ne ai" tsaki Aliyu yyi ya mike yace "Da gaske ka ma mayar da ni mahaukaci wllh" farouq yyi dariya sosai, Aliyu ya dau makullinsa yace "Am full frnd, gobe xan tafi UK in sha Allah" Farouq yace "UK? Ba last month ka dawo ba?" Aliyu yace "Yeah ina da aiki can, beside na fi jin ddin can wllh, ba takura..." Kofa ya nufa farouq ya mike ya bi bayansa, har gun mota ya rakasa Aliyu ya shiga ya tada motar yace "Toh sai na dawo frnd, a kulan min da boys dina" Farouq yace "Toh Allah ya tsare, ya sa ka taho mana da tsarabar mata ko da baturiya ce wllh don na gaji da ganin ka ba aure" d'an murmushi Aliyu yyi yace "Toh Abba...." farouq yace "Allah kuwa, Abban ma da ya gaji ya xuba maka ido ynxu, ni wllh da ma kawai su yi taking dinka unaware kana dawowa sai dai kaji ai an sa ranan ku da Hanan, ga mace har mace tana son ka amma kayi ta mata jan aji kana jiran Iman Aljanar ka, ni wllh ko Salmah ce a hadaku, ka kuma san gwara Hanan sau dubu kan salmah..." Aliyu bai ce komai ba don har ya 6ata masa rai, ya ja motarsa kawai ya bar gun Farouq na dariya.

Tunda Khadijah ta shiga daki ta sa key bata sake lekowa parlor ba kusan awa daya da rabi kenan, ita dai ta ga abinda ya isheta.... Khaleel taji kanwarsa ta kirasa da ko wa?? Kwafa tayi ta juya xuwa daya side din gadon da take kwance, kallon agogo tayi a hankali ta jawo wayarta dake gefenta ta gama dialing number ta kai kunne, Muryar Nanny taji, bayan sun gaisa tace "Umma fa?" Nanny tace "Umma na tare da bakuwa...." Tace "Toh xan kira xuwa anjima...." Nannyn tace "Ga su Sudais...." Khadijah ta d'an buda ido tace "Boy... how you?" Shiru tayi tana apprehending abinda twins din ke gaya mata a waya duk jikinta yyi sanyi sosai, Shuraim yace "Hello... Are you there Anty?" Ta lumshe ido ta bude cikin sanyin murya nace "Yea soldiers, hope ba ku ji ciwo ba" Shuraim yace "Not at all aunt, we where just freaked out, and an Uncle consoled us right there and made sure we where fyn, he was kind aunt...." Tace "That nyc of him, But did you both prayed?" Duk suka ce "We did..." Tace "Good, you make prayer ur daily routine before leaving home and when coming back, clear?" Suka ce "In sha Allah aunt" tace "Hand the phone over to Nanny..." ba musu suka kai ma Nannynsu wayar, ba su dau lkci suna magana ba tayi mata sallama ta ajiye wayar duk da ta so magana da Umma, har lkcn hankalinta ya kasa kwanciya, mikewa xaune tayi a hankali, she can't imagine loosing the boys, she just can't..... Tunanin hakan yasa hawaye ya cika idonta ta rike kai tana jin dama ta gansu kusa da ita a yanxu, ita kanta bata san wani irin soyayyan yaran bane ya dirar mata all of a sudden tun daga shekaru biyun da suka wuce, unlike before, kamar yanda bata son mutuwarta until her God is please with her haka bata son su, bata son su kusa da ita but now.... Reverse is d case, Allah yasan yanxu bata da kamarsu a duniyar nan gaba daya, she just love them, she know she love dem dearly... Ji tayi kamar xata yi xaxxabi ta koma ta kwanta, nan bacci ya dauketa, ba ita ta farka ba sai kusan magrib, bayan ta idar da sllh ta bude kofar dakin a hankali tana lekan parlor, bbu kowa parlorn kamar yanda ta yi tunani, ta karasa ciki a sanyaye a ranta tace ae da ka xauna ka jira ni, ta isa gun main door ta sa makulli tana kallon tray din abincin da ta kai ma fatima daxu, toh ko shi ya kawo ya ajiye daxun, ta bude plate din dake a rufe taga da sauran Irish din, da alamar fatima bata ci da yawa ba, ta dau tray din ta wuce kitchen, disposing din abincin tayi, duk da muryarsa da ta ji a baya bata leka ba har ta gama abinda xata yi ta bar kitchen din, Mis cals din Vanessa ta samu a wayarta, ta mayar da kiran bayan sun gaisa Vanessa tace yau ma tana ta jiranta, murmushi tayi tace "Sorry love, I had a visitor today, an unexpected one..." Vanessa tace "Alryt then, good nyt" daga haka Khadijah ta katse wayar ta ajiye, Daren ranan bata samu bacci me tsawo ba, don da tayi xata farka, karfe uku tana ta xaune har lkcn ta kasa baccin bayan ta idar da sallah, tashi tayi ta wuce kitchen don diban ruwan Lipton ta sha ko xata iya karatu, kamar ance ta daga kai suka yi ido hudu da shi xaune da uban textbooks a gaban sa yana sanye da siririn farin glass, ta cikin glass din yake kallonta, a hankali ta sauke idonta ta gama abinda xata yi ta kashe wutan kitchen din ta wuce. Har gari ya waye idonta biyu kamar warce ta sha wani abu, Shayi kadai ta iya sha da safe bayan ta shirya ta bar gidan misalin karfe bakwai da rabi don wucewa makaranta, throughout ranan bata da walwala a makarantar ma, bayan la'asar tare da Vanessa suka taho gidanta kamar yanda ta bukaci su je, suna gama cin abinci khadijah ta tafi tayi wanka ta bar Vanessa parlor tana kallo, bayan ta gama shiryawa ta dau waya ta shiga kiran Umma, a hankali ta gaisheta, bayan yan sakwanni tace "Umma yaushe su Sudais xa su yi Mid term break?" Umma tace "Mid term... gobe ne ai...." Ta d'an yi shiru sannan kamar me tsoron magana tace "Toh, dama Umma don Allah da sai su taho gu na da Nanny suyi hutun a nan plss" Umma tace "Saboda rashin hankali" shiru ta yi bata ce komai ba, Umma tace "Shi hutun kwana hudun ne xa su kwashi jiki su tafi UK" Khadijah ta girgixa kai tace "Toh shkkn Umma kiyi hakuri" Umma ta katse wayar ta, misalin karfe shidda suna xaune waje da Vanessa suna duba wani material na karatu khaleel ya bude kofa ya fito, 3 qtr da singlet ne jikinsa, tun da ta kallesa sau daya ta mayar da kanta kasa bata sake daga kai ba, taji Vanessa tace "Good evening" cikin cool voice dinsa yace "How you?" Tace "Am great" ya saci kallon khadijah sai kuma ya juya ya koma ciki, Vanessa tace "Ur neighbor?" Khadijah tace "Yeah" Vanessa ta wara cat like eyes dinta tace "He is damn cute, a Nigerian also?" Khadijah ta nuna mata kofar flat dinsa tace "You can ask him" Vanessa tayi dariya tace "Sure I can" suna nan xaune har kusan goman dare, Khadijah ta san ba don suna wajen ba da yanxu ya fito, sai taji dadin hakan ko ba komai dai sun hanasa xama wajen, a ranta tace ba don ba don ba ma a nan xata kwana a xaune, sha daya saura suka tattara takardunsu suka wuce ciki, ae kam ko minti takwas ba su yi da shiga gida ba taji fitarsa, Missed calls din Umma ta gani har biyu a phone nata dake daki, ta shiga kiranta bayan tayi shirin kwanciya, Umma tace "Kin yi bacci ne" ta girgixa kai tace "Yanxu xan yi Umma" Umma tace "Tunda ganin yaran kike son yi gobe xa su bi train xuwa Abj su yi boarding plane...." Khadijah ta d'an xaro ido tace "A'a Umma hutun ba yawa ai" Umma tace "Ai kinsan da ba shi da yawa kika ce su taho, so keep shut" shiru ta yi bata iya tace komai ba har Umma ta katse wayar, har ranta taji dadin abinda Umma tace, tayi murmushi ta kwanta hade da lumshe ido.

"Sir ga mu Airport din..." Dago kai Aliyu yyi da sauri daga danne dannen wayar da yake yi, ya kada kai yace "Alryt Bilyamin thank you" daga haka ya bude motar ya fita yana rike da karamin travelling bag dinsa, in 2 hrs and a halve har sun shigo Abj daga kd, ko don yayi gudu ne, "Amin nagode" amsar da ya ba Bilyamin kenan dake masa Allah ya kiyaye hanya ya bar gun ya nufi hanyar shiga cikin airport din, yana jin wayarsa na ring a aljihunsa amma sanin warce ke kiransa yaki fiddo wayar. Aliyu na kokarin ajiye karamar jakarsa sama bayan an shiga jirgi ya ji an taba sa, juyowa yyi da sauri, lkci daya ya wara dara daran idonsa ya durkusa yana kallon Little Shuraim dake masa murmushi yace "Waow handsome we met again" Shuraim yace "Sure!" Aliyu ya juya ko xai ga any of his parent ganin babu yace "So how you?" washe hakora shuraim yyi yace "Am fyn Uncle, and you?" Aliyu ya shafa kansa yana murmushi yace "Same sweetheart... Where is ur twin" nuna masa Sudais dake kusa da Nanny tana bude masa cake dinsa a leda yyi, Aliyu ya dinga kallon matar kafin yace "Is.... that your mum?" Shuraim ya girgixa kai yace "Noo she's our Nanny, we left mum at home, we r going to meet aunt in UK in sha Allah" Aliyu ya gyada kai yana mamakin sharpness din yaron don da ganin sa baxai wuce shekara biyar ba, ya kamo hannunsa yace "That's nyc my boy, am also heading there, What's ur name?" "I am Shuraim Muhd" Cewar Sudais yana wara masa ido, Aliyu yace "Waow, ur twin name?" Shuraim yace "Sudais Muhd" Aliyu yyi patting shoulder dinsa yace "That's my boy" mikewa yyi ji da yyi ana announcing ayi fastening din seat belt, Tuni Nanny ta taho tafiya da Shuraim, kafin Aliyu yace komai yaron ya daga masa hannu yace "C ya uncle, well' meet later, may be in UK...." daga haka ya bi Nannynsa Aliyu ya bi sa da kallo yana murmushi, xaunawa yyi seat dinsa, Baturiyar dake wajen tana murmushi tace "You've got a lovely son" Aliyu ya kalleta da sauri,
Sannan ya kalli Shuraim sai kuma yace "Ohhh thanks very much" har jirgi ya tashi Aliyu bai daina juyawa yana kallon cute twins din ba har ya lura sun yi bacci few hours later. Da yamma suka sauka Uk, Aliyu ya mike ganin Twins din duk bacci suke ya nufi Nannynsu da ke kokarin tada su gaba daya, yace "Bari in taimaka maki da guda daya Madam" bai jira cewarta ba ya dau Sudais don ya fi kusa da shi, ya rungumesa yana rike da jakarsa ya nufi kofar fita jirgi, Nanny ta bi bayansa da sauri tana rike da Shuraim da har ya tashi, sai da ya jira suka dau luggage dinsu sannan ya samar masu taxi... tuni Sudais ya bude ido yana kallon Aliyu ya wani tsuke fuska, Aliyu ya sakar masa murmushi yana kallonsa a hankali yace "How you Prince?" Sudais bai amsa ba sai ma kokarin sauka da ya fara yi daga jikinsa, hakan yasa Aliyu ya sauke sa yana kallonsa murmushin dake fuskarsa yyi fading a hankali, Shuraim dake rike da Nanny da ke kkrin saka jakar kayansu cikin booth din taxi yace "Uncle are we going the same way?" Aliyu ya kallesa sannan ya girgixa masa kai yana

1 Comments On NOOR AL HAYAT
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls inason novel dinnan cplt

Please Login or Register in order to submit comment