Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri, yace "Me kike a nan" tana kallonsa da idonta da yyi bulu bulu yyi jajir, shatin hannun Hajiya Salaha a gefen fuskarta hankali tace "Aka ce in tsaya a waje" yace "Saboda me?" Tayi shiru bata ce komai ba, shiga gidan yyi ya tarar da su gaba daya da yaransu ana xaune parlor ana kallo ana shewa, duk suka fara cewa "Abba sannu da xuwa..." Bai bi ta kansu ba yace "Me wancan yarinyar take yi a waje?" Hajiya Maimuna ta tabe baki tace "Xaman jiran ka dawo" Hajiya Salaha ta kara da cewa "Tun kafin la'asar ina jin yarinyar can da ka gani ta fita muka dinga bin layi layi muna nemanta da makwabta ba ita ta dawo gidan nan ba sai dab da magrib, duk ta Daga mana hankali daxu gidan nan ba masaka tsinke" yace "Shine xa a bar ta xaune waje cikin sauro a jawo min abinda xai sa in kai ta asibiti?" Hajiya Salaha tace "Toh xan iya mata abinda raina ke raya min Alhaji shi yasa nace tayi ta xama a waje" yace "Toh kada warce ta sake turata waje war haka ko uban me tayi... Na gaya maku" juyawa yyi ya kalli Khadijah dake tsaye ta rakube a fusace yace "Xo nan" karasowa tayi da sauri ya wani hade rai yace "Ina kika je?" Hawaye ya cika idonta ta nuna masa waje da hannunta jikinta na rawa, fixgota yyi ya turata ciki yace "Gobe ki kara, saurayen da suka cije ki ma kadai sun isheki" daga haka ya wuce ciki yana cewa "Sai ku bata abincin idan xata ci idan kuma baxata ci ba ta kwana da yunwa" daki ya wuce, Khadijah ta xauna kasa jikin kujera bata yarda ta hada ido da su Hajiya dake ta 6alla mata harara ba, a wani kwanon da yyi tsatsa aka xuba mata tuwo da miyar kubewar da aka girka, ta jawo abincin a hankali tana kallonsa, miyar ta kai baki ta d'an yamutse fuska, ganin kallonta Hajiya maimuna take tayi saurin saita fuskarta, ta tsura ma TV ido tana kallo kamar yanda duk occupant din parlorn suka yi, ji tayi Hajiya Maimuna tace ma Hafsa taje ta dauke kwanon abincin ta kai kitchen, Khadijah bata damu ba don dama ba yunwa take ji ba, sai waje karfe sha daya da rabi kowa ya tafi makwancinsa ita ma ta kwanta a kan tabarmar da aka nuna mata ta dinga kwanciya a dakinsu Sajida wai katifar baxai dauke su su dukka ba. Bayan kwana biya Khadijah na xaune tsakar gida da yamma tana uban wanke wanken da su Hajiya suka tula mata, su kuma suna ciki da yaransu kasancewar ranar Friday ce bbu islamiyya, yi take kamar baxata yi ba tana turo baki an hanata kallo, wanda a kansa kusan kullum sai ta sha mazga amma ta ki hakura, ita dai tayi kallo, duk ta rame ta kanjale, kana ganinta kasan akwai yunwa sosai da wahala tare da ita, ga rashin sabon aiki, ba laifi yanxu tana d'an wanke plates din su fita sai dai ta kan fi awa biyu kan kwanukan wanke wanken, kayan jikinta kuwa yanda aka san ta shiga rafi tsabar jikewar da yake idan tana wanke wanken, yanxu an ma daina sa ta sharan gaba daya tsabar kawai bata iya ba sai dai wanke wanke da jan ruwa wani lkcn a waje idan bbu wuta, tun ranan da ta fita har yau bata sake fita ba sai dai idan an aiketa gun mai kanti ko kuma xata debi ruwa a er karamar bucket da take dauka, har yau bata sake cin abinci mai dadin gidan da taje ba, abincin gidan kawu daga taliya sai tuwo da shinkafa da wake da mai da yaji, gashi duk bata son su hakan yasa take tare da yunwa sosai, Hafsa ta fito ta jefa mata kudi tace "Khadijah wai Mama tace ki je gun mai kanti ki siyo sabulun wanki da Hypo leda biyu, sai ki siyo maggi mai tauraro na hamsin" Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, tashi tayi bayan Hafsah ta wuce sanin Hajiya na iya lekowa taga ko ta wuce, ta shiga parlor Hajiya Salaha tace "Aiken fa" ta kalli kayan jikinta tace "Mama xan canxa kaya" dakuwa tayi mata tace fita Ki ban guri, shashasha sshe da gangan kike jike kayan wajen wanke wanke kenan kin san abinda ya kamata" juyawa tayi ta fita, ta sake kallon kayan dake a jike tun daga saman gwiwanta har kasa, gate ta nufa kanta sanye da hula don gaba daya Hijabs dinta yaran gidan sun gaje, tafiya ce me nisa xuwa gun mai kanti, tana tafe tana wasa da d'an karamin iccen hannunta, har ta wuce gidan da taje ta ci abinci idonta na kan gate din gidan amma ba daman shiga, tana isa gun mai kanti cikin aiken da aka mata maggi kawai ta tuna, gida ta koma da sauri ta shiga parlor tana kallon Hafsa kamr xata yi kuka tace "Me da me kika ce ma" Hajiya Salaha tayi wani murmushi ta na kallon kishiyarta tace "Me na fada maki" Hajiya Maimuna tace "Kin ji na maki musu? Ko an taba aikenta bata dawo tambayar me aka aiketa ba dama" Hajiya Salaha ta ce "Wllh Ubanki ya cuce rayuwar ki, kishiyar uwarki kuma kiri kiri ta nuna bata son ki tunda har ta sangarta ki haka ta lalata ki saboda ba ita ta haife ki ba, banda haka wannan xabgegiyar budurwa godai godai kullum aka aike ki sai kin dawo wai kin mance, sai shegen turancin iyayi.... ni dai wllh tunda yarinyar nan ta xo gidan nan nake fama da surutu abinda yaran da na haifa ma basu sa ni ba, Allah dai ya isa wllh" Hajiya maimuna ta tabe baki tace "Ke kika ga xa ki iya, ni kinga ina yi? Ai sai dai duka" Kabir ne ya sake nanata ma khadijah Aiken da aka mata ta fita da sauri tana maimaita abinda yace a ranta har ta isa gun mai kantin sannan ta fada masa, yana dariya yace "Ke yar fari ce ko?" Ta wara ido tace "I don't understand" dariya yyi yace "Aa ni ba bature bane, don nema maki saukin kai wa da dawowa idan an aikeki kawai kice a dinga rubuta maki sakon a gida kinji" tace "Ohk then" muryar da taji yana cewa a bashi kati ya sa ta juyawa da sauri, suka hada ido ta washe fararen hakoranta tace "Good evening" daga sama har kasa ya kalleta yace "How you?" Ta langwabar da kai tace "I shud say fine" yana gyada kai yace "Good" karban card din da mai kantin ke mika masa yyi yace "Doguwa dake baki sa Hijab idan xa ki fito" a hankali tace "Bani da Hijab yanxu" bai ce komai ba yana loda card din kafin yace "Toh me yasa kika jika kayan ki" tace "Wanke wanke nake yi tun da rana" yace "Ina ne gidan ku?" Tace "Our home is 3 house's away from u people's" ya kalleta yace "Gidan Alhaji Jibril?" Ta gyada masa kai, yace "Ke yarinyarsa ce" ta girgixa kai a hankali, yace "Yaushe kika xo gidan!" Ta kalli sama kamar me naxari sannan tace "10 days ago" ya gyada kai bai ce komai ba, ta amshi ledan sakonta da canji tana kallonsa kafin tace komai yace "Ya sunanki?" Tace "Khadijah" yace "Good" a hankali tace "Ina son in xo in ci abinci gidan ku amma an hanani, kuma I can't eat the food they are cooking, it's just concoction" a hankali ta karashe maganar, yace "Me yasa aka hana ki?" Tace "Su mama sun ce xa su kashe ni idan na sake xuwa ko ina kuma ina jin tsoro" ya kalleta bai dai ce komai ba, ta matso kusa da shi a hankali tace "Ko xaka dinga kawo min abincin gidan ku da kanka?" Ya buda ido yace "Ina?" Tace "Gidanmu mana, sai in dinga boyewa a backyard ina ci" tana magana ne hawaye cike fararen idonta, jin yyi shiru ta ci gaba tace "I am always hungry...." Ya sauke idonsa daga kanta bai dai ce komai ba.

*Haske writers association*💡

A hankali khadijah dake kallonsa tace "please" ya dago ya kalleta kafin yace "Sai in gan ki a ina in baki abincin?" Shiru ta yi kamar me naxari, can tace "Ohk, ae akwai flowers a kusa da gate din, to ka dinga ajiye min a wajen idan na fito sai in dauka" murmushi yyi yace "Koh?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk" ta kara matsowa gaban sa tace "Promise u will do that plss" yace "I will" ta wara idonta ta hade hannayenta tace "Thank you very much, may Allah reward you, byeee" daga haka ta juya da sauri ta bar wajen ta nufi gida ya bi ta da ido, bbu wanda ya bi ta kanta ta ajiye sakon a kan kujera ta fito ta ci gaba da wanke wankenta Happily, sai kusan karfe biyar ta gama ta shigo ciki, Hajiya Maimuna ta hada ta da uban kayan yaranta ta linke su ta xuba a cupboard, sai kusan magrib ta fito ganin kowa na alwala ita ma taje bakin tap tayi alwala ta dawo tayi sllh, tana rakube jikin kujera aka fara kiran kowa ya je kitchen ya karba abinci, ita ma ta tashi sanin Hajiya Maimuna na iya kunduma mata xagi idan taga bata shigo ba, tuwo ne da miyar karkashi aka yi ranan, ta fito bayan an dungura mata nata tana kallon cikin tuwon, xaunawa tayi ta kai hannu cikin miyar dake turiri ta dangwala ta kai baki, ta kasa hadiyewa ta shiga satan kallon mutanen parlorn trying very hard to keep her face normal, kowa hankalinsa na gun kallon Hausa film da ake yi a TV, ita da yake can gida basa kallon Hausa film ko bin ta kan kallon bata yi ba, sulalewa tayi ta fita waje rike da kwanon tuwon ta ajiye nan verenda ta nufi gate da sauri, a hankali ta durkusa gun flowers din bakin gate tana addu'ar Allah yasa ya ajiye mata abincin, ta bude flower din a hankali tana dubawa ai kuwa ta ga leda fari, ta dauka da sauri ta bude taga takeaway ne da goran five alive, ajiye ledan tayi ta doka uban tsallen murna sannan ta dau ledan har tana tuntube ta shiga cikin gida, backyard ta nufa da sauri ta nemi wani lungu ta xauna ta bude abincin taga jollof rice ne da naman kaza da plantains sai sauce a gefe, Cike da murna ta fara cin abincin tana ci tana gyada kai har da lumshe ido, sauri sauri ta cinye abincin ta bude drink din ta sha kusan rabi sauran ta kasa shanyewa, ta mike ta boye goran drink din sannan ta dau takeaway din ta fita gate ta jefar cikin katon abinda ake xuba shara ta dawo ciki tana goge bakinta, sai da ta tsorata ganin tuwon da ta ajiye ta kauda kai da sauri kamar ta ga mugun abu ta daukesa kamar wani shara tana yamutse fuska ta fita waje, almajiri ta samu ta juye ma sannan ta dawo gidan ta tafi gun tap tana wanke kwanon sajidah ta leko da alamar sai lkcn aka lura bata parlorn, yarinyar ta juya ta koma Khadijah ta bi bayan ta da sauri rike da kwanon da ta wanke, Hajiya salaha tace "Daga ina kike?" Ta nuna mata kwanon tace "Naje wanke wa ne" salati ta saki tana tafe hannu tace "Yanxu abincin kika je kika xubar khadijah?" A tsorace tace "Wllh mama ban xubar ba" Hajiya Maimuna tace "Karya kike, kece xa ki ci tuwon nan har ki cinye?" Ta marairaice tace "Amma ban xubar ba wllh" Hajiya salaha tace "Toh ya kika yi da shi?" A hankali tace "Na ba almajiri" cup Hajiya Maimuna ta dauka ta jefeta da shi tace "Allah ya isa" Khadijah tayi kofa da gudu ta fita ganin Hajiya salaha ta mike, can bakin gate ta tafi ta tsaya a tsorace, yau ma dai kamar jiya kawu ne ya shiga da ita parlor, bayan ya duddungureta yyi gorin iya son ransa sannan ya juya kan iyalansa cike da fada yana nanata masu indai suka janyo ma khadijah malaria sisin sa baxai yi ciwon kai ba sai in su xa su kai ta asibiiti, bbu warce ta tanka sa cikinsu, ya gama bambamin sa ya shiga ciki. Washegari sai da kowa ya tafi makaranta khadijah ta fara wanke wanken kwanukan jiya, kamar xata yi kuka take yi don duk sun bubbushe, tayi kusan awa daya bakin tap din ta bar sauran kwanukan ta shiga ciki, Hajiya tace "Kin gama ne munafuka" ta girgixa kai tace "Na kai halve" koranta tayi taje maxa ta gama, khadijah ta fito tana kallon agogo ta ga karfe tara ya wuce har da rabi, cikin sanda ta nufi gate ta bi anguwar da kallo ta ga ba kowa da yake silent anguwa ce, bude flower tayi dai dai wajen jiya taga farin Leda, ta washe hakora ta dauka da sauri ta shiga ciki, backyard ta nufa tana waige waige kamar munafuka, ta samu inda ta xauna jiya ta xauna ta bude ledan ta fiddo takeaway din, fried potato ne na turawa da uban kwai a ciki, ta lumshe ido tana murmushi, ta fito da wani water bottle karami da ke ledan ta bude tana kallon ciki taga shayi ne yaji madara da Milo, ta wara ido tace "Wowwww" har wani rawa hannunta yake ta kai bakinta tana yi a hankali kar ya konata taji bbu xafi sosai, tun da ta kafa baki bata ajiye ba sai da ta ga bayan shayin, ta ajiye bottle din ta rufe tana lullumshe ido ta dau fork din cikin ledan ta soma cin dankali da kwan, da kyar ta gama cinyewa don ta koshi kuma bata son xubar da abincin, ta tashi a hankali tana leke leke ta fita da gudu ta jefar da takeaway din a bola, ta dawo bakin tap ta wanke bottle din ta sa a Leda ta koma jikin flower ta bude ta ajiye sannan ta shigo ciki ta ci gaba da wanke wanken, bayan ta gama ta shiga ciki Hajiya Maimuna ta nuna mata kunu a cup da aka rufe a walakanci da wani bushashen bread a leda tace "Idan kin ga dama gasu can, don bawa baxae biye ta halin ki ba tunda yana da baya" Khadijah ta girgixa kai ba tare da ta sake kallon direction din kunun ba tace "Ni na koshi mama" sakin baki Hajiya Maimuna tayi can tayi murmushin mugunta tana gyada kai tace "Toh maa sha Allah" xaunawa khadijah tayi a favourite position dinta, daga karshe Hajiya Maimuna ta mike ta wuce ciki, kwanciya khadijah tayi don ji tayi cikinta ya mata nauyi nan da nan kuwa bacci ya dauketa. Yau ma dai da rana shinkafa da mai da yaji aka girka, tana gani suka xubo ma baki da suka yi ita ko oho sai ma wankin socks da panties din yara da aka tula mata bakin tap abinda bata taba ba, sai shafa socks din take tana turo baki gashi ta fara jin yunwa da wajajen karfe uku ne, kalle kalle ta fara yi kafin ta mike kamar mara gaskiya ta fita wajen gate, bude gun flower tayi a hankali taga farin leda sabo, ta wara ido ta dauke ledan taga bbu na bottle din da tasha daxu, ta shiga ciki da sauri ta wuce backyard, snack ne a ledan da roban five alive. Nan da nan ta ci da sauri ta sha drink din sannan ta fita ta xubar da ledan a shara taje ta ci gaba da wankin ta. Sai kusan la'asar bakin suka tafi, Hajiya salaha ta fito ganin wankin da Khadijah tayi, kuka ne kawai bata yi ba, amma har kumfa bakinta yake don fada da xage xage ita dai Khadijah na tsaye jikin bango tana kallonta tana wasa da flower din gown din jikinta, sai da Hajiya salaha ta mayar da gaba daya kayan cikin bucket ta xuba omo xata sake wankewa, Allah ya isa kam Khadijah ta sha sa na barnar omon da tayi mata, daga karshe Hajiya Maimuna ta kirata kamar ta ji shawarar da mai kanti ya ba khadijahr ta dungura mata takarda dauke da abubuwan da xata siyo mata ta bata kudin ta je kanti, Khadijah na isa kantin bayan ta basa takarda ta sa ya bata fallen takarda da Biro, yana mika mata ta xauna shi kuma ya ci gaba da hada mata kayan Aiken da aka yi mata a Leda, rubutu tayi kamar haka "Assalam, I am soo happy you fulfilled ur promise, I am no longer hungry anymore, I love the foods, may Allah reward u abundantly, I like you." Ta tsura ma neat writing dinta mai kyau ido tana murmushi, can ta linke takardar ta mayar ma mai kanti biron sannan ta karbi kayan ta ta wuce da sauri, cikin flowers ta bar takardan yanda xa a gani sannan ta shiga gida, Hajiya Salaha dake ta wanke ta jefa mata kallon tsana tace "Shi yasa fa kayan ki can a kwandon kayan wanki har sun fara tsutsa maga uban da xai wanke maki, ba dai duk kin saye kayan ba" Ita dai bata ce komai ba ta shiga ciki ta kai ma Hajiya Maimuna sakonta. Karfe biyar da rabi yara suka dawo gaba daya, aka xuba ma kowa abinci amma banda ita, ko kallon inda abincin su yake bata yi ba banda kallon da take har kowa ya gama cin abincin ya kai kwanuka waje, Hajiya salaha ta shiga kitchen gun kishiyarta dake girki tace "Maman Hafsa kinsan yarinyar can daxu bata karya ba gashi yanxu ma ko damuwa bata yi tace ina abincin ta ba?" Hajiya Maimuna tace "Wallahi ina lura da ita, ke dai na mu ido, ranan yanke jikinta ta fadi ya kusa xuwa, ni dai baxan roketa ta xo ga abinci ba idan ma ba ta ci ba auki xai ma yaran mu" Hajiya Salaha ta fita tana cewa "Toh ni kinga ina bi ta kanta" Da daddare yau dai macaroni dafaduka aka yi ta manja, Khadijah ta ki xuwa kitchen ta karbi abincin sai kallo take, Tsawa Hajiya Salaha ta mata tace "Toh maxa tashi ki fita ki wanke kwanukan daxu da aka 6ata, ba dai kina xaune kina jiran a kawo maki abinci ba..." Khadijah ta mike ta fita da sauri daga parlorn Hajiya ta bi ta da kallon mamaki don a tunaninta xata shiga kitchen ne, wanke wanken taje ta d'an yi kafin ta fita gate da sauri ta bude flower sai ga wani ledan, tayi murmushi ta dauka ta dawo ciki ta wuce favourite position din da take xama ta bude take away din taga shinkafa ce da miya sai nama kusan yanka biyar ta wara ido cike da jin dadi ta fiddo goron five alive ta ajiye sannan ta fara ci, cikin few minutes ta gama saboda saurin da take ta koshi ba kadan ba don har ta kasa shan drink din gaba daya, ta boye a inda ta saba boyewa sannan taje ta jefar da ledan ta dawo ta ci gaba da wanke wanken tana gyangyadi tsabar koshin da tayi, da kyar ta karasa ta shiga ciki wajen karfe tara tana shiga kuwa isha tayi suna ta kallonta su ji ta ce ina abincinta amma sai ji suka yi tace xata je kwanta daga haka kuma ta tafi tayi kwanciyarta. Haka nan Khadijah ta ci gaba da rayuwa gidan har na kusan wata biyu bbu ranan da ya taba fashin ajiye mata abinci gashi tun haduwar da suka yi a kanti ta bukaci ya dinga ajiye mata abincin basu sake haduwa ba, duk kwana biyu sai ta ajiye masa note din godiya cikin flowers, Bbu abinda ke daure ma Hajiya Maimuna da Hajiya salaha kai irin yanda suka ga Khadijah ke ta kiba tana kyau gashi fa sai ta kai har washegari wani lkcn bata ko bi ta kan abinda suka girka ba, ga uban aikin xa take narka kullum a gidan, ranan dai abun ya ishi Hajiya Maimuna tace "Ni kam yarinyar nan ko dai akwai gun da take xuwa cin abinci ne ba mu sani ba, dubi fa ko bin ta kan abincin gidan nan bata yi ko da an xuba mata sai ta ki ci, gashi lafiya lau sai ma kiba da na ga ta yi kamar" Hajiya Salaha tace "Nima abun na daure min kai kuma kema kinsan bbu inda take xuwa sai gun mai kanti kuma bata dadewa take dawowa gida" Hajiya Maimuna tace "Yanxu dai kawai mu sa ma duk movement dinta ido sosai" Da rana Khadijah na ta xaune parlorn tana jiran su tafi su kwanta taje ta dau abincin ta a flowers, kallon wani Hausa film suke, taga basu da niyyar shiga ciki, ta mike ta dauke few plates dake parlorn duk da tayi wanke wanken safe tace "Mama in je in wanke" Hajiya Salaha tace "Toh sai kin tambaya, ko ba aikin ki bane" fita tayi da sauri don dama abinda take nema kenan, tana ajiye plates din ta fita gate, tuni su Hajiya suka fito suna lekan compound suka ga bbu ita, hakan yasa Hajiya Salaha xata nufi gate Hajiya Maimuna ta rike tace "Jira kamar ga kafafuwanta can a tsaye" ko rufe baki basu yi ba sai gata ta shigo da leda suka yi saurin makalewa da bango, ko lura da su bata yi ba ta wuce inda ta saba xama da sauri, ta bude soyayyen kwai da indomien dake turiri kenan ta ajiye five alive a gefe, sai ga su a kan ta, tsuru tsuru tayi tana kallonsa kamar yanda su ma suka saki baki suna kallon abincin, salati suka saki a tare, Hajiya Maimuna tace "Uban wa ta baki wannan abincin Khadijah" Khadijah da tayi mugun tsorata xata mike ta gudu Hajiya Maimuna ta cafketa tace "Gun ubanwa kika karbo?" Jikinta na rawa tace "Ku yi hakuri" Mari Hajiya Maimuna ta xabga mata tace "Dama shi yasa kika daina bi ta kan girkinmu a gidan nan, karuwanci kika fara ba mu sani ba? To yau sai kin fiddo wanda ke baki abincin nn" cikin kuka tace "Gidansu yana can mama" janta suka yi suka fita ko warce ta yafe dankwalinta a kai ana huci suka ce "Mu je gidan"

Kuka kawai Khadijah take a tsorace tana biye da su Hajiya Maimuna na janta har suka isa kofar gidan, Cikin rawar murya tace "Nan ne gidan...." Hajiya Maimuna ta xaro ido tace "Nan kike xuwa?" Ta girgixa kai da sauri tace "Mama sau daya na xo, mutumin ne ke kawo min abincin ya ajiye cikin flower, ku yi hakuri don Allah" kwankwasa gate Hajiya salaha ta dinga yi da karfi mai gadi ya bude, tace "Ina masu gidan nan" Mai gadin yace "Daga ina?" Bin gefensa tayi a fusace ta shiga tace "Xaka ji da munafurcin ka, ni din ce xaka ce baka taba gani ba" Hajiya Maimuna ta bi bayan ta tana jaye da Khadijah suka isa parlorn gidan suka bude, Hajiya Maimuna ta rafka sallama kamar tashin duniya, Wata yar budurwar ce ta fara fitowa tana kallonsu ta gaishesu, a takaice suka amsa suka tambayi uwarta, ta juya kenan xata je kiranta sai ga ta ta shigo parlor, har ta karaso kallonsu take da mamaki, Hajiya Maimuna ta hade rai tace "Hajiya Amina mun wuni lafiya?" Hajiya Aminar tace "Alhmdllh, in ji lafiya" Hajiya Salaha tace "Ba lafiya ba, ina d'an ki yake?" Da mamaki tace "Da na kuma?" Cike da jaraba Hajiya Salaha tace "Kwarai, ya fito ya gaya mana menene tsakaninsa da yarinyar nan, ya fito yanxun nan" Hajiya Amina tace "Kar ku min hayaniya a gida don Allah, ku gaya min meye ya faru?" Hajiya Maimuna tace "Hayaniya kam dole, don wannan case din sai ya iya kai mu har kotu, tunda batanci yake yi da 'yar mu" bude baki Hajiya Amina tayi tana kallonsu, haka ma 'yar ta... Khadijah dai sai matsar kwalla take jiki

1 Comments On NOOR AL HAYAT
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls inason novel dinnan cplt

Please Login or Register in order to submit comment