Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na sama, ya dago ta yana kallonta yace "Subhanallah" ta fashe da matsanancin kuka ta rikosa tana girgixa kai tana nuna masa kirjinta cikin rawar murya tace "It's hurting....." mikewa yyi da sauri ya shiga ciki ya dauko makullin mota ya dawo, cikin ikon Allah khaleel ya isa wani babban hospital don duk ta rikitasa driving kawai yake, tun da ta rufe ido bayan da suka shiga asibitin bata sake budewa ba sai washegari da safe, yana zaune gefenta ya jinginar da Kansa jikin kujerar da yake xaune, su kadai ne cikin ward din,ta mike xaune da kyar taa kallon ruwan hannunta, jin xuciyarta tayi fayau, sai dai har lkcn tana jin kamar numfashinta na seizing,ta kalli oxygen dake gefenta a dakin, ta mayar da kallonta ga agogo taga takwas ya kusa, cire drip din tayi cike da karfin hali ta sauka kan gadon, kofar da take tunanin na bayi ne ta shiga. Bata dade ba ta fito da alwala, sai kuma taga bbu hijab bare darduma, ta isa kusa da khaleel cikin rashin kuxari tana kallon sa, bacci yake a yanda yake, lkci daya taji tausayinsa sosai wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, durkusawa tayi a hankali ta dafa kujeran cikin sanyin murya tace "Doctor..." Lkci daya ya bude ido yana gyara xamansa, mikewa yyi da sauri ya durkusa gabanta yana kallonta damuwa yace "How you feeling now khadijah?" Murya can kasa tace "Naji sauki, you need rest, ka kwanta saman gado am nt sleepy" hannunta ya kamo yana kallonta xai yi magana daidai nn aka bude kofa wata nurse baturiya ta shigo ward din. Mikewa yyi nurse din ta karaso tana tambayar me yasa ta cire drip din, khadijah ta mike race "I used the restroom" mayar mata da drip din tayi bayanta koma kan gadon, khaleel ya bi ta tare suka fita ward din, tagumi khadijah tayi tana kokarin ganin hawaye bai xubo mata ba, ba a dau lkci ba khaleel ya dawo da mug a rufe ya xauna gefen gadon ya mika mata yace "Gashi ki sha xa a maki allura...." Ta sa hannu ta karba ya bude mata, a hnkli ta kai baki tana sha, ya kafa mata ido, bayan ta sha ta sauke cup din ta karbi murfin ta rufe, yace "Ina ke maki ciwo ynxu?" Ta girgixa masa kai tace "Bbu ko ina, just my chest" yace "Xai daina in sha Allah" nurse din ta dawo rike da tray me dauke da allura da magani, tana kallonta ta gama hadawa ta karaso, mikewa yyi ya fita dakin ya rufo kofar. Tana mta alluran ta bata maganin sannan ta fita bayan ta gwada mata yanda xa ta sha, bayan fitar nurse din khaleel ya shigo rike da table water, ta sha maganin, a hankali tace "I want to go home plss" yace "No sae kin kara samun sauki," ta girgixa masa kai tace "Am feeling better yanxu, bacci nake son inyi" yace "Toh ae sai sun yi discharging dinki koh" bata kuma cewa komai ba ya gyara mata pillow yana kallonta, ba musuta koma ta kwanta a hankali. Sai kusan karfe daya aka yi discharging dinsu ya biya bill din suka bar clinic din, sai da suka yi nisa cikin sanyin murya tace "How much is d bill" bai ce komi ba kuma bai kalleta ba, yayi parking wani eatry, da ido ta bi sa har ya shiga, rike da Leda biyu ya fito ya bude motar ya shiga suka bar wajen. Parking yyi ya juya yana kallonta, ta jinginar da kai da kujeran motar idonta lumshe, a hankali ya dauke kansa, can ya juyo murya can kasa yace "Khadijah" lkci daya ta bude ido, yace "We are home" kalle kalle ta fara yi, ya bude motar ya fita bayan ya dau takeaways din da yyi, ta fito ta rufe motar tana jin jiri na kwasarta, bata yarda ta bar jikin motar ba, kamar yasani kuwa ya xagayo yana kallonta, hannunsa ya mika mata, ta sauke idanuwanta ta mika masa nata hannun, yana rike da ita har suka iso apartment dinta ya kalleta yace "Key?" Shiru tayi kafin tace "A jakata yake" yace "Ina jakar?" Bata iya tace komai ba, ya bude apartment dinsa.

*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻

14.....

Tsayawa yyi yana kallonta ta shiga parlorn sannan shima ya shiga, kan kujera ta nufa ta xauna, ya karaso bayan ya kulle kofar ya ajiye ledan hannunsa kan center table, sannan ya shiga daki, jinginar da kai tayi da kujera tayi xurfi cikin tunanin da take taji yana kiranta, dagowa tayi da sauri ta gansa tsaye gefenta ya rungume hannunsa, a hankali yace "Na hada maki bathing water a bathroom" sunkuyar da kai tayi, ta mike yana gaba ta bi bayansa xuwa dakin, towel ya dauko ya mika mata, ta karba murya can kasa tace "Thank you" ya juya ya fita dakin, da mouth wash na Listerine ta wanke bakinta, tayi wanka da shower gel, sai kusan bayan minti talatin ta fito daga bayin, bayan tayi ta tsayuwa bakin kofar bathroom din tana tunanin fitowa da towel, bbu kowa dakin sai Hijab dinta da ta gani kan gado, mamaki ya kama ta tayi ta kallon Hijab din, karasawa tayi ta dauka ta koma bathroom din, wanke kayan da ta cire tayi sannan ta sa hijab din ta fito da kayan da ta wanke a bucket, xaune ta gansa a parlor yana rike da remote, kallo daya yyi mata ya dauke kai har ta shigo parlorn, yace "Why did u wash, u still under medication" bata ce komi ba, yace "Na bude maki kofar...." Tace "Da gaske?" Yace "Ehh, ki tafi ki shirya" murya can kasa tace "Nagode" sannan ta wuce tana rike da Hijab din. Sai da tayi sllh snn ta wanke masa towel din a bayinta ta fito ta shirya ta tafi shanya kayan da ta wanke da towel din nasa, kwanciya tayi daki bayan ta gama lkci daya bacci ya dauketa. A hankali ta bude ido jin kamar ana tashinta, ta mike da sauri tana kallon sa, yace "I've been knocking and calling since, but.... Taso mu je ki ci abinci" ta girgixa kai tace "Am not hungry bacci nake ji" yace "Noo, baki ci komai ba yau, kuma kinga xa ki sha magani, you have to take something...." Daga haka ya mike yana kallonta, sauka tayi daga kan gadon ta bi sa suka fita parlor, xuba mata abincin yyi ya mika mata ta karba ta fara ci, wayarsa yake ta dannawa har ta ajiye abincin tana yamutsa fuska tace "Na koshi fa" ya kalli abincin sannan ya dau ledan maganin ya ballar mata drugs din ya taso ya mika mata da goran ruwa ta karba, ta sha maganin tana kallon sa yace "Allah ya sauwake" bata iya ta ce komai ba, yace "To ki je ki kwanta, sleep without thought plss" ta gyada masa kai sannan ta tashi ta shiga daki. Bata tashi ba sai kusan biyu da rabi na rana, ta shiga bayi tayi alwala ta fito tayi sllh, tana idarwa ta sake kwanciya. Knocking kofar dakin taji ana yi cikin bacci, ta mike xaune ta sa hijab sannan ta bude kofar, yana tsaye bakin kofar, yace "Have u prayed zuhur?" Ta gyada masa kai, yace "Abinci fa" tace "I am not hungry" ya girgixa kai yace "You are, fito ga abinci na kawo maki sai ki sha magani" daga haka ya juya ya bar wajen, bin sa tayi, yana daga tsaye ya nuna mata abincin kan table, ta karasa ta dauka, tuwon shinkafa ne da miyar vegetable ta gani da ta bude, ta daga kai tana kallon sa, ya daga kafada yace "Yea, a frnd of mine ce ta yi..." Tace "Kai baxa ka ci ba?" Ya girgixa kai da sauri yace "Noo I don't take heavy foods, I don't take swallow" murmushi tayi ta dauke kai, ya shafa kai yace "Sbda ke na karbo" tace "Toh ngd" yace "No thanks" plate taje ta dauko a kitchen ta debi abincin, shi dai har lkcn yana tsaye, ta kallesa a hankali tace "Baxa ka xauna ba" shiru ya d'an yi, sai kuma ya karaso ya xauna kan kujerar dake kallon nata yace "So u care" bata ce komai ba ita dai, a hankali ta dinga cin tuwon, duk lkcn da ta daga kai sai sun hada ido, daga karshe bata sake yrda ta dago ba har ta gama cin tuwon ta dau magani ta sha, sai a snn ta sake kallon sa taga kallonta yake still, hade rai tayi ta dauke kai, yyi murmushi yace "Who is Aliyu?" Kallon sa tayi da sauri, kamar yanda shi ma yake kallonta har lkcn, can ta tsuke fuska tace "Ban gane ba" bai sake cewa komai, bayan kusan minti biyar yace "don't pretend... Is he ur Husband?" xuciyarta na bugawa tace "Nooo" Yana mata wani kallo yace "Ur Ex Husband?" Hade rai tayi sosai cike da masifa tace "Noooo" sai kuma ta mike tana masa wani kallo tace "I know nothing about what u are saying" ya d'an yi murmushi yace "You passed out yesterday at the hospital with the name Aliyu in ur Mouth" shiru tayi tana kallon sa a sanyaye, lkci daya hawaye ya cika idonta, can ta juya ta bar masa parlorn da sauri, kiran ta ya dinga yi har ta shige daki ta xauna kasa ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka, bin ta yyi cikin dakin, ya karaso gabanta ya durkusa a hankali yace "Ohk, I am very sorry Khadijah, may be I shouldn't have say anything about that, but dole xan yi magana, Billah da xan ga Aliyun nan... Sai na sa ya d'an dani abin da kike ji, I guess he broke ur heart kuma yake kokarin dawowa rayuwar ki yanxu saboda may be selfish reason dinsa, he will regret that duk ranan da muka hadu face to face.... I vow!" ita dai bata ce masa komai ba sai kukan da take, duk jikinta yyi mugun sanyi, mikewa yyi ya fita dakin. Har dare khaleel bai shigo ba, tun da tayi magrib take hade abubuwan da tasan xa ta kai gida, don bata jin xata kara kwana a kasar, gaba daya xaman kasar da karatun ya fice mata a kai, hawaye kawai take duk jikinta a sanyaye, Sudais has always wanted her to be a doctor, ta xo ta samu kan ta a bangaren pharmacy, wanda a yanxu bata jin ma xata ci gaba, domin kuwa ta hakura da karatun, may be some other time she wil be d doctor Sudais wants her to be, to ko ta xama likitan ma what is that adding to her life, wanda take son yi dominsa ya tafi ya bar ta a lokacin ta fi bukatarsa a rayuwarta, baxa ta ce ya gujeta ba, but what's the difference? Kusan duk daya.... Ta share hawayen idonta ta fito parlor a sanyaye, tsaye tayi tana kallon Khaleel da shigowarsa knn a hankali ta sauke idonta kasa wasu sabbin hawayen na xubo mata, ya karaso kusa da ita yace "Ina xa ki?" Ta juya masa baya tana kkrin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba, a hankali yace "Khadijah" cikin rawar murya tace "Am going back to Nigeria" ya juyo da ita ya xaunar gefen kujera yana kallonta, ya bar ta tayi kukan me isarta, ta hade kai da gwiwa tana sauke ajiyar xuciya, cikin sanyin murya yace "Tell me about you Khadijah" Ta dago tan kallon sa hawaye na sakko mata, sai dai kuma tayi ma kanta alkawarin bayan Sudais bbu wanda xai ji ita wacece, muryarsa ya dawo da ita tunanin da take, yace "I still don't deserve to know you koh?" Ta sunkuyar da kanta tana goge hawayen dake sakko mata, a ranta kuwa tunani take anya xata iya fadi ma Khaleel ita wacece kuwa, a hankali ta xamo kasa daga xaunen da take kan kujera, ya sakko k'asan shima yana kallon kwayar idanuwanta da suka rine, kife kanta tayi da kujera cikin sanyin murya tace "Ka daina kallona da idon ka" ya d'an yi jim sai kuma yace "Why?" A hankli tace "Bana son irin su" murmushi yayi yace "Da gaske" taki cewa komai, a hankali yace "Toh na daina kallon ki" dagowa tayi suka kara hada ido tayi saurin mayar da kanta jikin kujera, dariya ta basa sai dai bai yi ba ya shafa kansa yana murmushi, murya can kasa yace "Am all ears Khadijah" ta dago kanta tana wasa da dogayen yatsun ta tace "Ohk....." Wayarsa ya da ya fara ring ya ciro aljihunsa, ta kalli screen din kamar yanda shi ma yake kallo, Jawaheer ne jikin screen din... Yyi silencing wayar ya ajiye a hankali, Tsura ma lallausan carpet din da suke xaune kai ido tayi ko kiftawa babu, cikin sanyayyan muryarta tace "I am an only child... I was raised from a very rich home, I was raised by only my Dad don kuwa ina da shekara uku kachal a duniya mahaifiyata ta rasu...." D'an murmushi tayi wasu sabbin hawaye na taruwa idonta tana kallon Khaleel da ya kafeta da nasa idon....

Who is Khadijah?

#Shekaru 6 baya
#6 years earlier
#Flash back....

*Haske Writers Association*💡

Uhm don't know how to announce this, Reason being that... the love, the prayer, the encouragement is 👍🏻 but sai dai ina da na gaba da ni and i heed to their advice always, and babu wanda bai son progression, so?? 🤗 I think this all for the free pages of *Noor-Al-Hayat* sorry to those that I took unaware but don't forget I announced needing patronage in my previous book... you think you love the book, you think love Khaleesat Haiydar.... Then gladly patronize her.... If interested... ping Via Facebook inbox or Via WhatsApp 07087865788, they will be groups available, Thank you.

✨ *Noor-Al-Hayat*✨






_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻





_littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne from this page, kindly patronize ur writer and read happily, duk wanda bai ji dadi ba hakan da nayi yyi hakuri pls_




Shekaru shiddah baya.....


A hankali ta karashe shanye shayin dake hannunnta ba tare da ta bi ta kan soyayyen kwan dake gabanta ba ta ajiye cup ta mike tace "Umma to idan Kawu ya tafi da ni baxan sake dawowa ba?" warce ta kira da Umma dake duke tana goge mata takalmanta masu tsada tana xuba su a wani jaka ta juyo da rinannun idonta tana kallon 'yar yarinyar warce da kadan ta haura shekara sha uku tace "Xa ki dawo Khadijah in sha Allah" Khadijah bata sake cewa komai ba tana dai tsaye, tsadaddun ready made ne jikinta da cover shoe mai kyau sai kyalli yake, da farin hijab karami, kunnuwanta dauke da dankunnen zinari 'yan kanana, Khadijah tace "Toh Umma me yasa ke baxa mu je da ke ba" Umman bata kalleta ba tace "Nima gidanmu xan je Khadijah" Khadijah ta durkusa kusa da ita a hankali tace "Umma ni bana son gidansu Kawu ki tafi da ni gidanku don Allah" Umman bata ce komai ba har ta gama rufe jakar ta daura kan babban jakar dake dauke da kayan Khadijah, jin Umma bata ce komai ba Khadijah ta dau remote xata kunna TV, Umma ta jefa mata wani kallo tace "Xaki fara ko, ni dai na gaya maki kar kije gidan mutane kina masu irin wannan kallon da kike kamar wawuya, kashe TV din nan yanxun nan" Khadijah ta kashe tvn ta koma ta xauna kan kujera, dai dai shigowar kawunta, kuma wan mahaifinta, har ya karaso parlon idonsa na kan soyayyen kwan da Khadijah ta bari a plate, ya dau plate din ya xauna yace "Tsabar almunbazzaranci dubi abinda aka yi ma lafiyayyen kwai, karshen komai ya xo in sha Allah" ita dai Umma bata ce komai ba ta wuce daki don fiddo nata sauran kayan da ya rage a gidan, Kawu ya dinga cin kwan kamar his life depends on it, har dai ya gama daga karshe ya ajiye ya na kallon Khadijah dake ta kallonsa yace "Toh ki tashi ki fita ga adai daita can ki shiga ki jirani a kofar gida" ta xaro ido tace "Kawu ba da mota xa mu je ba" dakuwa ya mata yace "Tashi ki ban waje" mikewa tayi tayi hanyar kofa tana waigosa, shi kuma ya dau katon jakar ya bi bayanta, Umma ta fito da nata kayan waje ta dau plate da cup ta shiga kitchen ta wanke su ta ajiye, ta kuma sake tabbatar da komai a kashe yake sannan ta bi bayansu, Khadijah na tsaye jikin adai daitan Umma ta jawo ta, a hankali tana kallon eyeballs dinta tace "A duk inda kika tsinci kanki ki xamo mai hakuri kin ji Khadijah, nasan ki da shi, komai kuma aka sa ki kiyi, sannan most important of all banda kallon TV don Allah..." Khadijah tayi murmushi da ya bayyana beauty point dinta tace "Umma I can't do without watching tv fah" Umma ta hade rai tace "So u won't heed to what am saying koh?" A hankali ta sauke idonta tace "Am sorry mum" Umma ta ja kumatunta tana murmushin karfin hali tace "That's my girl" a hankali kuma a sanyaye ta kara da cewa "And always pray for daddy, kullum kika yi sallah ki masa addu'ar Allah ya masa rahama" Khadijah ta gyada kai tace "Toh Umma" Umma ta shigar da ita adai daitan tace "Safe trip dear, I will always pray for you" Khadijah ta gyada mata kai trying hard to control her tears, Tuni Umma ma ta juya ta nufi main road da jakarta ba tare da ta bi kan kawu Jibril dake kokarin maka ma gidan kwado ba, Khadijah ta bi stepmother din ta da kallo hawaye na sakko mata, a haka kawu ya shigo adai daitan, yana mata wani kallo yace "Kukan uwar me kike ma mutane" cikin rawar murya tace "Umma ta" Dungurinta yyi yace "Uwar ki ba Ummar ki ba" Khadijah ta sunkuyar da kai, mai adai daitan ya dau hanyar park, hannu Khadijah ta daga ma stepmum dinta ganin sun wuceta, ita ma ta daga mata tana goge hawayen idonta. Tasha mai adai daitan ya kai su, kawu ya sauke kayan Khadijah ya bai ma mai adai daitan kudi sannan ya biya masu kudin mota xuwa katsina, da kyar ya yarda ya biya seat biyu wai xai dauketa a kafa, sai da yan motar suka sa baki, bayan kusan minti goma motar ta cika suka dau hanyar katsina, tunda Khadijah take bata taba shiga motar haya ba, rabonta kuma da katsinan tun tana da shekara bakwai da suka je tare da Abbanta, kai kana ganinta kasan she is restless, matar da ke kusa da ita tace "Yarinya me ya faru?" Kamar xata yi kuka tace "Amai...." Kawu ya kwalalo ido yace "Me?" Tace "Amai" dungurinta yyi yace "Ke yarinya ce xaki ce ma mutane kina jin Amai cikin mota" matar tace "Haba bawan Allah, sai yara ke Amai idan suna tafiya" dakatar da ita yyi yace "Ke... Learn to mind ur business while in public, 'yar ki ko tawa" matar tace "Aa ba yar ka bace wllh, don da yar ka ce baxa ka yi mata abinda kayi mata ba yanxu" Bala'i kawu ya fara kamar mace a motar, ana haka Khadijah ta toshe bakinta jin aman xai taho mata, matar bata bi ta kan kawu ba ta sa driver ya tsaya, ta sauke Khadijah, nan kuwa ta dinga kwara Amai, matar na tsaye kanta, shi ko kawu yana cikin mota sai fada yake yana kumfar baki, kowa ya xuba masa na mujiya bbu wanda yace ci kanka, wani mutumi a motar ya ba matar ruwa ta mika ma Khadijah, ta wanke bakinta da fuska sannan suka dawo cikin motar ana mata sannu, wata mata ta bada leda ta rike a hannu idan ta ji wani aman, har suka isa katsina kawu bai yi shiru ba, Khadijah tayi Amai yyi sau biyar, dunguri kam ta sha sa gun kawu duk da ba a kusa da shi take ba, bbu wanda yace masa ci kanka cikin passenger din motar, a dai dai ta ya samu da xai kai su har gidansa.. Karfe biyu da kusan rabi suka shigo gidan, bungalow ce mai kyau, wanda Abban Khadijah Alhaji Muhd ya mallaka ma yayan nasa a lkcn yana da rai, sai dai ba lallai wanda ke nan lkcn da aka ba Kawu gidan ya yarda Cewar gidan ne a ynxu ba, don yyi mugun tsufa ga dattin bala'i, kuma dudu gidan bai yi shekara shidda ba, Duk matan Alhajin guda biyu suka fito jin shigowar mai gidan nasu suna masa sannu da xuwa, kawu dake kokarin bude jakar kayan Khadijah bayan ya xauna parlor yace "Toh ga ta nan, gida kuma ni da Isiyaka mun rufe an sa a kasuwa, ga ta nan ban san gun warce xata xauna ba cikin ku" Matarsa ta fari Hajiya Salaha tace "Toh ni dai yara sun yi yawa a gu na, ban san dai ko Maimuna ba" warce ta kira da Maimuna tace "Ni kuma sai nace maki yaran basu min yawa ba koh?" Kawu yace "A'a bbu xancen tada jijiyoyin wuya taje dakin ki Maimuna kayanta kuma a kai dakin salaha, shkkn" daga haka ya dinga fiddo da tsadaddun kayan Khadijah, daga shi har matansa bbu mai cewa komai sai kallon ikon Allah suke, Kusan set takwas ya cire ya ajiye gefe yace "Wannan siyar da su xa ayi in sha Allah, domin kuwa baxata xo nan ta dinga saye sayen kaya ba kamar wata er gote ta janyo ayi tunanin shi gareni..." Takalman ma duk ya ware kusan biyar, golds dinta na dankunni da awarwaro kuwa dama suna aljihunsa, Khadijah dake ta tsaye jikin kujera tana waiga ko ina na parlorn da idonta tana neman remote ta kunna TV amma bata gani ba, ganin kawu xai xuba duk kayan da ya ware a wani jaka ta karaso da sauri tace "Kawu ina son wannan takalmin, da shi nake xuwa makaranta" Dungurinta yyi da karfi ya kunduma mata ashar, ta koma baya a tsorace yace "Ki shiga hankalinki da ni fa xan xane ki wllh" xata mike ya fixgota ya cire dankunnin kunnenta, Hajiya Maimuna tace "Toh idan ba fitsara ba ita har xata gaya maka abinda xaka yi" mikewa yyi ya dau jakar yace "Ku shiga da sauran, ni na tafi kasuwa kan yamma yyi" daga haka ya nufi kofa" bayan fitarsa Hajiya salaha ta sake fiddo kayayyakin ta dau kusan kala biyu da panties da kayan bacci, Hajiya Maimuna ma ta jawo jakar ta dau huluna da kaya kala daya da dogon rigar kanti da safunayen hannu da kafa, Hajiya salaha xata sake jawo jakar Hajiya Maimuna ta rike tace "Tsiyace jakar xa ki yi" Hajiya salaha ta jefa mata wani tace "Ke ai arxiki kike karama jakar, abu baxa ayi sa da hankali ba, ita sai ta sa uwar me?" Hajiya Maimuna ta rufe jakar ta tura tana kallon Khadijah dake ta tsaye tana kallonsu tace "Dauka ki kai dakin can dake kusa da wancan kofar, kin wani tsaya ma mutane kememe" Khadijah ta karaso da sauri ta dau jakar ta bi hanyar da Hajiya Maimuna ta nuna mata, kafin ta fito sun dau takalma kala daddaya ta dau jakar takalmin ma ta kai dakin. Uban wanke wanken dake tule gun pampon da aka tanadar don yin wanke wanken Hajiya salaha ta nuna mata taje tayi, a hankali Khadijah tace "Ina jin yinwa" Hajiya salaha tace "Can baki ci abinci bane kafin ki taho, ki je bakin pampon akwai tukunyar taliyar da ta rage ki ci sannan kiyi wanke wanken" Fita khadijah tayi xuwa gun pampon, ta yi kusan minti daya tana kallon taliyar da kudaje ke bi, ta turo baki ta rungume hannayenta, Dawowa parlon tayi kamar xata yi kuka tace "They are flies perching all over the food, ni baxan iya ci ba" sakin baki suka yi gaba daya suna kallonta, can suka kwashe da dariya Hajiya Maimuna tace "Toh baturiyaa jikar mongo park...." Hajiya salaha tace "Kin wuce kin ba mutane waje ko sai na mike.. Ina

1 Comments On NOOR AL HAYAT
avatar
hauwau-8-3

1 year ago

Reply

Pls inason novel dinnan cplt

Please Login or Register in order to submit comment