Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[24/11, 21:24] Maman Nusaiba: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU🧟‍♀️*_



Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum(Maman Nusaiba)_

_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_

Daga marubuciyar:
Amir da Amira.
Aljanar Jarumai.
Hafsat.
Ƙaddara ce.
Tani da Manu.
Rayuwar ma'aurata.
Sumayya baiwar Allah.
Abba ne.
And new book.
Aljanar gidanmu.

Ya Ubangiji yadda ka bani damar ɗaura Alƙalamina ka kuma bani dama da ikon sarrafa tunanina da baiwar da ka mini, ina addu'a ka bani ikon ɗauke shi lafiya, ya rabbi ka bani ikon rubuta abin da zai amfani Al'ummar Annabi Muhammad (S.a.w) Habibi ɗan gatan Allah shugaban duniya da ƙiyama. Allah ka ƙara mana lafiya da wadatar zuci ka hanemu ga aikata saɓo....


*WhatsApp number +966599791573*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

0️⃣1️⃣

Tsaye take a gefen babban titi tana rusar kuka, gefenta wata tsohuwa ce kwance tana rawar sanyi bakinta na haɗewa da labbanta saboda yadda jikin nata yake rawa sosai. Juyowa yarinyar ta yi za ta yi magana sai ta fasa ta mayar da hankalinta ga wata mota da take mata oda, tsayuwa ta yi tana Ƙifƙifta idanu tana jiran taga wanda zai fito daga motar...

Babbar motar ce fara sol ta yi parking a gaf da ita, direban dake a set ɗinta ya buɗe murfin motar ya fito fuskar shi na nuna fushi, yana zuwa bai tsaya yin komai ba ya kife yarinyar da mari ya kuma ƙara mata wani a ɗayan kuncin..

"Ke uban wa ya ce ki zo kan hanya ki tsaya? Dan uwarki ana magana kin wani tsare da manyan idanunki kamar wata maiya, to ki shiga hankalinki so kike ki ɓata mini suna a gari na ƙare rayuwata a gidan yari ko me?"

Shuru yarinyar ta yi ta zuba masa idanunta wanda ya ciko tam da kwalla, sosai taji zafin marin da ya mata hakan ya sa hawayen idanunta suka shiga zubowa jikinta nawa, da sauri ta sunkuyar da kanta tana goge kwallar data zubo mata tare da lumshe idanun nata, sai da ta jima kafin ta ɗago kai za ta yi magana taga ana ƙoƙarin buɗe motar daga set ɗin baya ta yi shuru tana kallon ƙofar..

Wani babban mutum ne ya fito tare da wata ƴar yarinya mai kimanin shekaru 13 tana riƙe da ƴar Teddynta, idanunta ne ya sauka akan yarinyar da taga an mara ta yi saurin sakin hannun mahafinta ta isa gurin yarinyar ta tsaya, a sanyaye takai hannu ta shafa gefen fuskarta da shatin yatsun direbansu yake kwanta tar.. "Ki yi haƙuri zan rama miki marin da ya miki kinji." Yarinyar ta faɗa ta ƙara da cewa" Ya sunanki?"

Ajiyar zuciya yarinyar ta sauke ta buɗe idanunta akanta sannan ta ce" Na gode sunana Amra."

Murmushi Yarinyar ta yi ta kamo hannun Amra da yake ɓace da taɓo ga dauɗa data kwanta amma bata ji kyamarta ba ta riƙe hannun nata tana shafawa ta ce" Sunanki mai daɗi ni kuma sunana Afra amma ana ce mini Auta dan ni ce Auta a gidanmu, kuma z.. Bata ƙarasa maganar da take son yi ba mahaifin nata ya iso gurin tare da fisge hannun Auta daga na Amra ya ce" Auta me ya sa bakya ji ne? Yanzu wannan ƙazamar yarinyar kike taɓawa ko ba ki ga yadda take da datti ba? Kalle ta fa sai wari take."

Amra ta kawar da kanta gefe ta durƙusa a gaban shi ta ce" Ranka ya daɗe ka taimaka mana kaga Mamata can a kwance bata da lafiya bamu da gurin kwana ko abinci da ƙyar muke samu muci, ka taimaka mana na kaita Asibiti" Ta faɗa tana riƙe ƙafafunsa."

Cikin azama ya buge ta ta yi baya ta faɗi. "Ƴar matsiyata ni za ki taɓawa jiki ɗan uwarki kinga na miki kama da matsiyatan mutane irin ki? To ba zan taimaka ba ɗin ko an faɗa miki kuɗin a banza nake samun su da zan ke yiwa kowa hidima kamar ban san ciwon kaina ba? Ke kuma ki fice mu tafi gida" Ya faɗa yana damƙar hannun Auta da ta yi tsaye baki buɗe tana kallon Mahaifin nata.."

"Waiyo Allah! Daddy don girman Allah ka taimaka mata kalli fa yadda Mamanta ke rawar sanyi, haba Daddy me ya sa ba za ka taimaka mata ba kuma har kake dukanta? Ni dai ka barni na tashe ta sai mu tafi" Auta ta faɗa tana mintsinin hannun Daddy da yake ƙoƙarin janyeta daga gurin..

"Ke ba ki da hankali za ki taɓa jikinta? Wannan fa tsami take ki rabu da ita mu tafi gida" Cewar Daddy yana ƙoƙarin janta.. Fir Auta ta kafe ta ce ba fa inda za taje sai ta tashi Amra dake ƙasa a yashe, haushi ne ya kama Daddy ya ɗauke cak ya sata a cikin mota yana ta masifa. Da sauri Auta ta buɗe schoolbag ɗinta ta fito da biskota gida uku da kuɗi ta dubi Daddy ta ce" To ka bari na bata wannan tun da ba za ka taimaketa ba." Dafe kai Daddy ya yi bai kuma ce mata komai, ganin haka ya sa Auta ta balle murfin motar ta fito da gudu-gudu ta iso inda ta bar Amra zuwa lokacin ta tashi tana kusa da Mamanta tana rusar kuka. "Amra! Ta kira sunanta da ɗan ƙarfi ganin hankalinta baya inda take. Juyowa ta yi tana kallon Auta bata amsa ba sai binta da kallo da take.. Murmishi Auta ta yi ta miƙa mata kayan hannunta ta ce" Ki yi haƙuri da abin da suka miki Amra Allah zai saka miki ga wannan kici wannan kuɗin kuma ki kai Maman naki Asibiti kinji" Ta faɗa da muryar tausayi."

Itama Amra murmishin ta yi ta miƙa hannu ta amsa sannan ta ce" Na gode Auta kina da kirki ba zan manta dake ba a rayuwata." Jinjina kai Auta ta yi ta ciro zoben dake hannunta mai kyau ta kalli Amra ta ce" Bani hannunki nasa miki zobe ina so ki za ma Ƙawata." Ba muso ta miƙa mata hannunta wanda ƙuraje ƙanana suka fito a yatsotsin nata wasu har sun yi ruwa kuɗa nata bin hannun. Cikin tausayawa Auta ta kalli hannun ta ce" To ki riƙe karki saka tun da naga ƙuraje sun fito miki ki sayi magani kisha sai su mutum zan ke sawa direba ya biyo nan dani dan nake ganinki." Jinjina kai Amra ta yi tana zubar da hawaye da ƙyar ta ce" Na gode Ƙawata." Ba komai Auta ta ce kana ta miƙe ta mata bye bye sannan ta koma cikin motar direba yaja suka bar gurin....

Sai da taga tafiyar su sannan ta miƙe da ƙyar tana dafe kwankwasonta da yake mata zafi. "Wash Inna ƙila ƙashin kwankwasona ya karye" Ta faɗa tana buɗe kwalin buskotar..

Ɗago da kan Inna ta yi tana jera mata sannu ta tashe ta, kafaɗarta ta shiga ta taimaka mata ta miƙe. Napep ta tsayar ta ce masa ya kaisu kyamis mafi kusa, kallon Amra mai Napep ɗin ya yi yana done hanci, tsaki yaja yana ce mata taya zai dauketa tana tsami salon ta kashe masa kasuwar shi ga mota da mutane biyu.. Kuka Amra tasa ta durƙusa ta ce" Ka taimaka ka kaimu kaga Innata bata da lafiya magani zan sayo mana ko nawa kake so zan baka ina da kuɗi."

Wani kallo ya kwatsa mata ya yi gaba abin shi..

Kuka sosai take tana riƙe da Inna sai neman faɗuwa suke, sai da ta gaji da tsayuwa sannan ta samu wani ya daukesu ya kaisu kyamis....

Tun da suka bar gurin Auta ta murtuke fuska tana kumbura baki, shi ko Daddy ko a jikin shi sai ma faɗa da yake mata akan biskotanta da ta bai wa Amra....


Suna zuwa gida Auta ta fito a guje ta nufi ciki tana kuka..

Kicibus ta yi da Fadila da ƙawayenta biyu sunsha kwalliya suna wani ɗage kai..

"Ke dalla can jaka daga gidan uban wa kike yanzu?

Auta ta tsayar da kukan da take ta ɗago kai tana saba baki ta ce" Anty Daddy ne."

"Kuma dan Daddy ne ya sakaki kuka sai ki shigo mana afujajan kamar wadda ta gudo daga Dawanau? Nifa kin sani bana son iskanci za ki wuce ko saina bangajeki daga hanyar? Ta faɗa tana nuna mata hanya..

Wani kukan Auta ta kuma sakawa tana sakin schoolbag ɗinta a ƙasa ta kuma ƙarawa kukanta sauti.. Tass tass ƙaran marin ya daki dodon kunnen Direba da yake ƙoƙarin shugowa da ƴar Teddyn Auta. Waro idanu ya yi yana ja da baya jikin shi na rawa..

"Kai kuma munafiki uban me ka shigo yi cikin palonmu? Cewar Fadila tana jefa masa gorar ruwan da tasha rabi ta bar rabi..

Kuka Auta ta Ƙwalla tana riƙe kuncinta cikin jin zafin marin ta sunkuya ta ɗauki schoolbag ɗinta tare da nufar hanyar cikin palon, har ta kusa kaiwa palo ta dawo ta isa gurin direba ta amshi ƴar Teddynta, kallon Fadila ta yi ta ce" Muguwa azzaluma Allah ya isa ban yafe miki sai na faɗawa Daddy" Tana faɗin haka ta kwasa a guje ta shiga ciki."

Kanbu! Ni ki ka cewa muguwa? Zan dawo na haɗu dake yau zan ga mai rabamu dake a gidan nan, ba dai Mommy bata nan ba zan yi maganinki" Cewar Fadila tana girgiza jiki ta yi gaba suka bi bayanta.. Tana zuwa saitin mai gadi ta ce" Kai kuma Ɗanladi sai na sa Daddy ya koreka daga aiki tun da in na ce ka wanke mini mota ba za ka yi ba ko?

Haƙuri ya shiga bata amma taki ko kallon shi ta shige mota ita da ƙawayenta, kiɗa suka konna kana taja suka bar gidan a guje kamar za su tashi sama...

Misalin ƙarfe 11pm na dare Daddy na zau ne yana duba wata jarida, Fadila dake gefe ta kunna kallo ta kawo MBC2 tana kallon wani American film ana ta nuno wasu masoya suna rungume da juna, Auta dake kan stamp ta rafka tagumi tana kallonsu...

Da fito ya sanyo kai cikin palon, shi kuma na bayan shi ya shigo yana waka da turanci kiɗa na tashi a cikin wayarsa..

"Oh my god! Daddy yaushe ka shigo gari ne ba ka faɗa mana ba?" Cewar Sudas yana miƙawa Daddy hannu.

Dariya Daddy ya yi ya ce" My Son's ai dama surprise na muku daga ina haka?"

Wani juyi Sauban ya yi tare da yin rawa ya iso gaban Daddy ya bashi hannu suka tafa, kallon su Auta ta yi sai kuma ta yi saurin saukowa tana murna ta nufo su. Tana zuwa saitin Fadila tasa ƙafa ta taɗeta ta faɗi tim a ƙasa. Sudas ya yi saurin juyowa ya ce" Kai Auta bi a hankali mana har kina faɗuwa."

Kallon Fadila Auta ta yi bata ce komai ba ta miƙe ta isa gurin Sudas ya ɗaurata akan cinyar shi ya yi yana shafa guiwar hannunta da take mata zafi...

" Sannu Auta Mommy bata dawo ba?" Cewar Sauban yana danna wayar shi...

Bata cewa kowa komai ba har suka gama surutun su suka rabu da ita...

Miƙewa Fadila ta yi ta wuce ɗakinta, Auta ma ta miƙe ta nufi ɗakinta. Tana hawa kan stap taga ƴar Teddynta tasa hannu ta ɗauketa ta wuce ɗakinta...

Tana shiga ta faɗa kan gado sharar hawaye...

Ƴar Teddynta ta rungume tana ci gaba da kuka har bacci ya kwashe ta..

Bata fi minti goma da soam bacci ta farka, saukowa ta yi daga kan gadon riƙe da ƴar Teddynta ta buɗe ƙofa ta fita..

Ɗakin Fadila ta nufa tana mutsitsika idanu, tana isa ta shiga buga ƙofar da ƙarfi tana faɗin" Anty Fadila ki buɗe mini ƙofa."

Cikin bacci Fadila taji ƙaran buga ƙofar ta miƙe, a fusace ta nufi ƙofar ranta na tafasa, tana buɗewa ta faɗo ɗakin ta takure a guri ɗaya..

Galala ta saki baki tana kallonta, wani ɓakin ciki ne ya rufe Fadila ta janyo cazar wayarta ta soma tsula mata tana faɗin" Dan uwarki uban me za ki mini a ɗaki ni z.. Bata ƙarasa ba taji an yi caraf da hannunta an zafga mata wani gigitaccen mari wanda ya yi sanadiyar ɗaukewar jinta da ganinta na wani dakikun...




_*Maman Nusaiba ce*_
[25/11, 19:47] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_



Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_

_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_


*Littafin Aljanar gidanmu na kuɗi ne only N300*

_WhatsApp number. +966599791573_

بسم الله الرحمن الرحيم

0️⃣2️⃣


Baya Fadila ta yi tana murza idanu dan tabbatarwa da abin da taji, bata yi aune ba taji ta jikin miro ta buga hannunta. "Kan uban can! Ta faɗa da ƙarfi tana yarfa hannunta da yake mata azabar zafi. Ɗago da idanunta ta yi ranta a matuƙar ɓace ta kai kallonta bakin ƙofar, Auta dake rakube jikin bangon ɗakin ta ƙara rungume ƴar Teddynta tana kuka marar sauti.. A fusace Fadila ta iso gaban Auta ta watsa mata wani irin kallon wulaƙanci sannan ta ce" Ke! A zabure Auta ta ɗago idanunta ta ɗaura su akan Fadila jikinta na rawa, ja da baya Fadila ta yi tana waro idanu ta ce" Uban me ya kawo ki ɗakina da daren nan? Ko kin fara hauka bayan ɓakin halin da ki ka kwaso na Mommy? Ni ki ka mara Auta? Za ki yi magana ko sai na ɗauki wannan kwalbar na fasa kanki da shi?" Ta faɗa tana nuna mata kwalbar...

Baki na rawa Auta ta soma faɗin" Anty Fadila yunwa nakeji banci komai ba ga Mommy bata dawo ba, muje ki dafa mini indomie please " Ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka tare da riƙe cikinta."

"Mutumelesy! Yanzu saboda kina jin yunwa ne ki ka shigo mini ɗaki, to wai ma waye ya mareni iye? Ta kuma faɗa tana son ɗamko Auta..

Nima ban sani ba Anty" Cewar Auta tana ɗago Teddynta. Tsananin mamaki da tsoro ne suka cika zuciyar Fadila har bata san lokacin data miƙe tsaye ba tana riƙe baki. "Wai da gaske kina nufin ke kaɗai ki ka shigo ɗakin nan? Tabbas nasan tsayinki ba zai kai nawa ba har ki iya marina, to amma waye ya mareni ko dai mafarki na yi? Ta faɗa tana kallon Auta da itama ita ɗin take kallo tana cuno baki gaba.

"Ni dai banga an mareki ba kawai dai naga kin yi baya" Cewar Auta tana haɗe rai ta kuma cewa" Abincin nakeso Anty ki dafa mini yunwa nakej."

"Tsuww ashe ma mafarki ne na yi dama bacci ne a idanuna na tashi, ke kuma daga yau in ki ka sake shigo mini ɗaki a irin wannan lokacin sai na murde wannan bakin naki na rashin kunya" Ta faɗa tana ƙoƙarin kai hannu ta kama bakin Auta, ji ta yi an huta mata iska a kunne ta yi saurin juyowa taga wayam, tsaki taja. " Kinga bari naje ko apple ne na ɗauko miki kin san dai ko ruwan shayi ban iya dafawa ba a gidan, gashi har kin sa ina jin tsoro alhalin ba abin da ya tsoratar dani...

Ita dai Auta kallon Fadila take har ta gama zazzaginta da rankwashinta ta fita zuwa kitchen..

Tana saukowa palo an kashe wutar falon, kasancewar wayarta na a hannunta sai ta haske da hasken wayar har ta isa kicthen ɗin, wutar kitchen ɗin ta kunna tana kai dubanta fridge. "Ihu ta kwalla ta mannewa da jikin bango tana cewa" Waiyo! Mage me ya kawo mage kitchen kuma? Juyowa ta yi tana kallon kan kukagas, tukwane guda uku ne akan kukagas ɗin sai tafasa suke, cikin Fadila ne ya bada kuuuuuu zufa ta shiga keto mata ta ko ina har bata san lokacin data saki futsari ba a jikinta..

Runtse idanu ta yi tana murza su dan ta tabbatar da abin da take gani, tana buɗewa ta yi saurin isowa gurin tukwanan, abincin ta gani a cikin ɗayar tukunyar farar shinkafa ce har ta yi fiyaya ta yi tsami, ɗayar tukunyar ita kuma farfesun kayan cikine suma sun yi tsami kuɗaje ne yamama a cikin farfesun wasu sun mutu wasu suna ta yawo a ciki, ɗayar kuma taliya ce an yi jalop ɗinta nama ne manya manya a cikin taliyar kamar yanzu aka zuba su a tukunyar sai kannin jini taliyar take..

Ja da baya Fadila ta yi tana mayar da numfashi taji an shafa mata baya. Waiyo! Daddy na mutu na lalace" Ta faɗa tana takurewa a jikin bango..

"Anty ba ki gama ba har yanzu" Taji muryar Auta daga bakin ƙofar kitchen ɗin..

Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Fadila ta sauke, a sanyaye ta ce" Ashe ma Auta ce." Kallonta ta yi sake da baki ganin kayan da yake jikinta. "Auta yaushe ki ka canja kaya kuma?

Kallon kayan nata Auta ta yi ta dawo da kallonta kan Fadila ta yi dariya cikin nishaɗi ta ce" Anty yau kuwa lafiya kike? Dama ɗazu fa ki ka ce mini wai an mareki kalli jikinki ruwan mene ne ya jika miki kaya?"

Tsaki taja tana ƙoƙarin miƙewa Auta ta yi saurin isa gurin tukwanan tana murna ta ce" Anty Fadila ki bari ga abinci ma Kande bata ɗauke ba shi zanci, dama can ke ba iya girki ki ka yi ba sai jin
music kamar shedaniya."
"Kut ni kike faɗawa magana dan uwarki dan ma kin samu na zo zan haɗa miki abincin? To kin yi da shegiya zan yi maganinki in ki ka sake ƴar wahala" Ta faɗa tana ƙarasa miƙewa." Bata kula ta ba ta isa kan tukunyar taliya ta zuba kaɗan ta dauko gishiri ta ƙara tana jujjuya taliyar tana cewa" Anty zo muci abinci macaroni da naman kifi nasan kina son irin wannan haɗin" Ta ƙarashe maganar tana kai loma..

Shiii! Fadika ta faɗa tana rufe baki ganin Auta ta kai taliyar bakinta sai yafki take kamar an zuba miya. "Ke! Ba ki da hankali taliyar mai yafki za kici tana tsami?

Tsayawa Auta ta yi tana kallon abinci cike da mamaki, ita dai macaroni take ci da naman kifi da ɗuminta amma sai ta ce mata wai taliya mai yafƙi da tsami, harara ta watsa mata tana turo baki ta ce" Ni dai ba ruwanki dani tun da yau kin samu ciwon hauka, haka kawai ina cin abinci sai ki ce wai yana yafƙi da tsami? Ki rabu dani yunwa nakeji." Saboda mamaki Fadila kasa cewa komai ta yi sai binta da kallo take kamar an kafeta a gurin..

Kamar wadda ta yi sati bata ci abinci ba haka Auta shiga cin abincin, kafin ta cinye wani ta kai wani, tana gamawa ta miƙe ta wanke hannu a inda ake wanke-wanke ta dawo palo ta zau na akan kujera...

Da ƙyar Faɗi taja jiki ta bar kitchen ɗin cike da mamakin Auta wai yau ita Auta ke faɗawa magana? Yarinyar da bata yarda su haɗa idanu . Juyowa ta yi sai taga ba kowa a palon TV kuma kunne yana ta aiki, tsoro ne ya shigeta ta yi saurin yin sama ta nufi ɗakinta da gudu gudu, har ta kusa isa sai ta fasa ta iso ƙofar ɗakin Auta a hankali ta tura ƙofar jikinta na rawa...

Waro idanu ta yi tana murzawa ta kuma buɗe su tarr bakinta buɗe take kallon Auta dake kan Sallaya ta kai sujjada tana faɗin" Subha rabbiyal a'ala..

"Kan buhun uban can! Ta faɗa tana ɗaura hannunta kan hannun ƙofar ɗakin.

Auta na gama yin tahiya ta salamce ta ɗaga hannayenta sama ta soma faɗin" Ya Ubangiji ka shirya Daddy da Anty Fadila da Yaya Sudas da Yaya Sauban da ma dukkan wanda suka kauce hanya, ya Allah ka dawo mini da Mommyna lafiya ka tsare mini ita a duk inda ta nufa, Allah ka ƙara mata lafiya mai amfani, Allah ka aurar da Anty Fadila mu huta da jin kaɗe-kaɗe a gidanmu" Tana kaiwa nan ta karanto Fatiha ta shafa tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya...

"Iye! Auta ni kike cewa na yi aure ku huta dani ko? Ba shakka mandiya sannu Hajiya uwar Daddy , kuma yaushe ma ki ka shigo ɗaki har ki ka yi alwala ki ka yi salla? Ba a palo na baroki ba kina zau ne za ki kunne TV?" Fadila ta ƙarashe maganar zuciyarta na harbawa da sauri-sauri kamar za ta faso ƙirjinta ta fito saboda tsananin tsoro da tashi hankali, yanzu ji take tsoronta ya ƙara lumkuwa akan na ɗazu..

Sake da baki Auta ke kallon Fadila dan ita a iya saninta ta kwanta a kan gado bata tashi ba in ba yanzu ba data farka dan ta gabatar da sallar daren data saba yi, miƙewa ta yi ta cire hijabinta ta aje a gefe ta dawo bakin gado ta zau na, addu'a ta yi ta shafa a jikinta kana ta gyara ta kwanta sai a lokacin ta kai dubanta ga Fadila da ta yi tsaye tana zare idanu...

"Da alama dai yau Anty kin Sha kodin ko wiwi, ina ha dai ko jimawar can kin kalli film ɗin abin tsoro shi ya sa ki ka kasa bacci har kike gani kamar ina miki gizo, to ni yaushe ma na fita har naje palo na kunna kallo a cikin wannan talatainin daren? Ko kuma kin zo ki zalinceni kamar yadda ki ka saba ne?" Tana gama faɗin haka ta juya ta ɗauko ƴar Teddynta ta rungume tana shafa kanta kamar ta rungume mutum. "Baby gobe Daddy zai kaimu kasuwa zan sayo miki blanket mai laushi saboda da sanyi ya kusa zuwa" Ta faɗa tana ƙara rungume ƴar Teddyn..

Fadila

1 Comments On ALJANAR GIDANMU
avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment