Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda bai kira ba haka aka dinga gana masa azaba daga an masa wannan in ya soma bada haƙuri sai a kuma canja masa kalar azaba a masa wata daban, wani nauyi aka kai masa a saitin ƙirji sai ga Doctor ya yi can warwas ya sume ai kuwa aka kuma masa wani dukan sai gashi ya farfaɗo yana zabga ihu.. Buɗe idanunsa ya yi yai arba da wani narkeken Jaki baƙi ya tunkaro shi tuni Doctor ya kuma sakin futsari yana zaro idanu ganin Jakin nan na ƙoƙarin isowa gareshi jikinsa na rawa, mari aka sauke masa ya saki ihu cikin wata irin murya aka daka masa tsawa...

"Yiwa mutane shuru mugu azzalumi marar imani. Yaji an furta a tsawace ana ƙara kai masa mari zazzafa mai shiga jiki, jikinsa ne ya bada kululuuu sai zawo haɗe da futsari a karo na barkatai dariya aka ɗauka kana aka soma cewa" Kai har kana da imani ko tausayin da za a tausayawa maka ne? Ko kana taimakon al'ummarka ne a yayinda suke neman taimakonka da har wani zai taimaka maka? Mara mutumci.. Ku yi haƙuri zan gyara halina ba zan sake ƙin taimakawa al'ummata ba kar ku kasheni na muku alƙawarin canja halayena daga yanzu" Ya ƙarashe maganar tare da haɗe hannayensa yana dan ja da baya daga cikim zawon da futsarin da ya yi zaman 'yan bori a cikinsa hatta kayan jikin ya yi sharkaf da ruwn zawon kuɗaje na binsa yooo tamkar an yi sabon yankan rago a mayanka ana feɗe shi." Dariya aka kuma kana yaji ana cewa" ai yadda kake mugu ba wanda zai ji tausayinka dan haka dole ne mu daukarwa bil'adama da 'yan'uwanmu fansar cutarwar da kake musu ba dare ba rana, a matsayinka likita wanda za a sameka da tausayi da jin ƙai na duk wanda ya zo gareka ka duba lafiyarsa, amma sai dai kash sai ka kasance macuci azzalumi mai kwaɗayin abin duniya sai wanda kaga dama kake dubawa, la nuna cewa sai masu kuɗi za ka duba lafiyarsu indai mutum talaka ne ko yana neman taimakon gaggawa bashi da kuɗi a lokacin ya nemi ka taimaka ka dubasa amma sai ka nuna kai sam kuɗi ne a gabanka ba ceton rayukan al'umma ba kamar yadda ka yi ikiri lokacin amsar aikin, asibitin da iya kuɗi kati ake biya kyauta ne komai kai kuma da ka zo duk ka canja komai in an zo sai an biyaka kafin za ka kalli mutane, ka tafka babban kuskure a rayuwarka dan yau ba mai cetonka kamar yadda kaima baka ceton masu neman ka taimaka musu.." Haƙuri ya dinga basu yana ce musu zai gyara su kuma suka zaneshi ta ko'ina ba kakkautawa sai da aka fidda masa haƙurin gaba kana daga bisani aka dinga barbaɗa masa wani ruwa mai yauƙi, duk inda aka zuba masa a jikinsa sai yaji wata irin azaba marar musaltuwa yana ta birgima yana roƙon su masa rai za8 gyara mugayen hakinsa ba zai sake, sai kusan asuba kana komai ya lafa aka bar shi anan warwas a sume..
_________________________

Da sauri-sauri take fitowa zuwa harabar gidan tana kiran Ɗanladi direba ya fito da sauri yana washe haƙora ya ce" Barka da fitowa Autar Hajiya yau ma dai da alama kin makara." Ɗan cuno baki ta yi tana ɓata fuska ta ce" Yo Yaya Ɗanladi Mommy ce yau ta makara bata tasheni da wuri ba ga Anty Fadila komai da Mommy ta mata kamar wata babyn goye yanzu dai muje kar a zaneni kaji." Murmishi ya yi cike da jin daɗin ta kirasa da Yayanta shi ya sa yake matuƙar ƙaunar Auta saboda hankalinta ga kuma girmama na gaba da ita da sanin yakamata motar ya shiga itama ta shiga har ya tada motar ta ce masa ya dakata ta fito da sauri ta gaishe da Baba Maigadi, cike da kulawa ya amsa tare da saka mata albarka kana suka bar gidan. Suna isa inda suka saba haɗuwa da Amra ta fito da sauri tare da wata leda blue ta samu gefe ta aje haɗe da wata takarda akan ledar ta samu wani dutse dan ƙarami ta ɗaura dan kar iska ta ɗauki takarda kana ta juyo da sauri ta wuce mota suka bar wajan, sai da suka kama hanya ta tuna yau fa suna da exam kuma bata karanta komai ba hakan yasa ta rafka tagumi tana tsoron ace bata ci abin da za a musu ba, Ɗanladi ya dubeta ya ce" Auta lafiya dai ki ka yi tagumi?" Ajiyar zuciya ta sauke kana ta ce" Jarabawa garemu kuma ban karanta komai ba." "Karki damu in sha Allah ma za ayi wanda bazai baki wahalar ganewa ba.. Jinjina kai ta yi ta ɗago kanta sai taga sun ƙaraso makarantar, sallama ta masa ta fita. Da sauri ta iso bakin ƙofar ajinsu tana addu'ar ba malamin da take tunani ba ne ya soma koyarwa, tana leƙawa taga shi ɗin ne dai hakan yasa jikinta ya yi sanyi ta nemi izinin shiga ya juyo yana harararta tare da ce mata ta shigo ciki, a ɗarare ta shiga kanta a ƙasa tana karanto kalmar "Lailaha'illa antas subhanaka inni kuntu minan zalimin. Haka ta dinga faɗa har ta ƙaraso kusa da malamin nasu, wani kallo ya watsa mata ya ce" Ƙarfe nawa yanzu?" Jikinta ne ya ɗauki rawa a sanyaye ta ce" Malam Ƙarfe 8:30 ne." "Ok shi ne dan kin raina mutane har kika ƙara 30 minute ko?" Da sauri ta ce" A a Malam ba haka bane ka yi haƙuri Mommyna ce bata tashi da wuri ba bana makara sai yau shima akasi aka samu Malam." "Yiwa mutane shuru kin tsaya dai wani abun a hanya maza fita kafin na zaneki a gurin nan" Ya faɗa yana nuna mata hanyar fita." Sum-sum Auta ta juya da nufi fita sai ta yi kicibus da principal ɗin su a bakin ƙofar sai ta tsaya ta gaishe da shi kana ta raba gefensa za ta fita ya dakatar da ita hakan yasa ta tsaya tana addu'ar Allah ya sa kar a daketa. Principal ya dubi malamin su Auta ya ce" Me ya sa ka ce ta fita daga aji?" Kai tsaye ya ce" Ta yi latti ne ranka ya daɗe." Ɗaure fuska Principal ya yi ya ce" Ka barta ta shiga kasan dai yarinyar bata yin latti dan yau ta yi kuma ta bada uzirinta ai sai ka karɓa ba ka koreta daga aji ba, kasan ma ɗiyar waye ita ɗin da kake daka mata tsawa haka? To karka bari labarin nan yaje kan kunnensa dan za ka yi ta aikinka har abada." Jin kalmar da Principal ya faɗa jiki na rawa ya ce ta dawo ta zau na, godiya Auta ta yiwa Principal cike da jin daɗi ta wuce ta zau na a mazauninta..
_________________________

Amra ce ta bayyana a inda Auta ta aje mata saƙo tana sanye da hijabi har ƙasa fuskarta a sanye da niƙaf, hannu ta miƙa ta dauki ledar haɗi da takardar tana sakin murmishi ta buɗe takardar dan taga saƙon mai ta ƙunsa rubutu ta gani kamar haka:

"Assalam alaikum my Amraty ina fatan kina lafiya ya su Aliyu da Inna? To kice ina gaishesu da kyau ga abinci nan na kawo miki ku buɗe yau na makara shi ya sa ban tsaya mun gaisa ba, sannan in sha Allah na faɗawa Mommy ta biya muku kuɗin makaranta har Islamiya na bata labarinku to ta ce in sha Allah gobe za mu zo ni da ita sai mu ɗaukeku muje a sakaku ke da Aliyu, ina fatan za ki yi farin ciki da hukuncin dana yanke ba tare dana nemi izininki ba naji ta bakinki daga Ƙawarki Auta.. wasu hawaye ne suka zubo daga idanun Amra, a sanyaye ta ce" Saliha baiwar Allah in sha Allah ke ƴar aljanna ce." Juyawa ta yi sai suka haɗa idanu da kama hannun shi suka ɓace daga gurin...

A ɗakinsu suka bayyana Amra ta zau na tare da aje ledar ta dubi Aliyu ta ce" Yanzu za mu samu damar shiga ko'ina na lamuran Auta ta yadda za mu gane waye wannan wanda yake tare da ita." Zama ya yi ya ce" Haka ne Yaya Amra sannan lokaci ya yi da za mu yi maganin duk wanda ya shiga gonarmu kawai ki kira Yaya Amina." Jinjina kai ta yi tare da miƙewa tana zagaya ɗakin wani kalar murmishi ta saki ta juyo ta ce" Zaki ka kwantar da hankalinka ni yanzu burina na gani waye wannan wanda yake ƙoƙarin cutar da ita? Sannan mai meye dalilinsa na bibiyar rayuwarta da wannan mummunar alaƙar?" "To Yaya Amra ki ka sani ko shima abin da aka mana shi aka yi masa shi ya sa ya biyo ta wannan hanyar dan ɗaukar fansa? Girgiza kai ta yi tana binsa da kullo ta ce" Bana tunanin hakan Zaki kawai dai akwai wata a ƙasa kuma koma meye za mu gano shi in sha Allah." Haka suka dinga tattaunawa a tsakanin dan neman mafita game da lamarin..

Washe gari kamar yadda Auta ta yiwa Amra alƙawarin za tazo da Mommy suka zo tare, a daidai inda ta saba tsayuwa Ɗanladi ya yi packing Auta ta fito da sauri tana kiran sunan Amra data juya baya ita da Aliyu Mommy na biye da ita a baya har suka iso gurinsu. Da murna suka rungume juna basu tsaya yin komai ba Auta ta kama hannun Amra suka iso gurin motar ta ce Amra ta shiga kana Aliyu sai Mommy ita kuma a gidan gaba yau harda su glass ta saka kamar wani ƙatuwar mace, tun da suka shigo Amra ta rufe idanunta ta yi shuru shi kuma Aliyu ya harde hannayen shi yana mayar da kallon gefen titi ta ɓangaren Amra.. Suna zuwa makarantar su Auta Mommy ta cike duk wani abin da ake buƙata ta buƙaci a saka su aji ɗaya da Auta aka musu tamabayoyi akan karatun su na baya suka faɗi suna aji 3 ne aka korosu daga makaranta, sosai Auta ta yi farin ciki sai godiya take yiwa Mommynta ta cire kuɗin ta biya kana ta fito Ɗanladi zai mayar da ita taji muryar Amra ta kira sunanta ta juyo ta sauri, a sanyaye Amra ta ƙaraso Mommy ta durƙusa ta ce" Allah ya saka miki da alkhairi Mommy kina da kirki ke da Auta baku da wulaƙanta na ƙasa daku Allah ba zai taɓa bari ku wulaƙanta a idanun duniya ba Mommy, bani da bakin gode miki sai dai na yi ta miki addu'a" Ta ƙarashe maganar tana goge kuntun hawaye." Murmishi Mommy ta yi ta ce" Karki damu ki daukeni tamkar ni na haifeki duk abin da kukeso ki tambayeni zan yi muku shi matuƙar ina da shi." Jinjina kai Amra ta yi Auta ta iso ta jata suka shige aji..

Tun daga ranar alaƙar Amra da Auta ta ƙara ƙarfi dan har gidansu take zuwa tana wuni itama Auta taje nasu gidan, karatu kuwa ko basu duba ba in aka tamabayesu za su amsa daidai abin har ya bai wa yan ajin mamaki sosai duk abin da aka tamahayesu ko tangarda basa yi suke faɗa a daidai, wannan bawan Allah kuma kullum sai ya kira Auta amma bata dauka hakan ya sashi a damuwa har sai da aka yi katari ya gansu tare da Amra ya nemi ta shayo masa kan Auta ko za ta amince da soyayyar shi, amma data sameta da maganar cewa ta yi ita fa sai ta yi shekara 19 ko 20 za ta fara soyayya yanzu a 17 take ta yi ƙarama ta tsaya da namiji, sai da lallami da dubara Amra ta shayo kanta ta amshi soyayyar wannan bawan Allah mai suna Khamis...

Tsaye suke a kusa da gurin shakatawa ita da Khamis tana kumbura baki shi kuma sai lallaminta yake, kallon shi ta yi ta ce" Ruwa nakeso kuma ka mayar dani gida nifa bana son yawo" Ta faɗa tana murguda masa baki." Murmishi ya yi cikin sauri ya miƙe ya ce mata yana zuwa yanzu zai kawo mata ice cream sai su koma gida, Ko ci kanka bata ce ba ta juya baya tana jan tsakin an takura mata. A razane ta juyo jin wani irin ƙara kiiii, da gudu ta nufi wajan da taga mutane sun soma zuwa wajan tana isowa ta kwalla ƙara a matuƙar firgice ta ce" A a Khamiss!




*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*
[14/12, 21:25] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_




Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_


_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_


بسم الله الرحمن الرحيم


1️⃣3️⃣

Mutanen dake gurin kowa salati yake sun kewaye Khamis dake gefen hanya kwance jini nata malala daga bakinsa da hancinsa har ma da gefen fuskarsa, fashewa da kuka Auta ta yi tana kutsa kanta cikin mutanen har ta iso gurin Khamis ta yi zaman 'yan bori tana taɓa hannunsa dake jumke rike da ledar ice cream, kallon mutanen ta yi tana kuka ta ce" Jama'a ku taimakeni ku kira mini Ambulance kar ya rasa ranshi don girman Allah." Wani daga cikin su ne ya yi kiran emergency call na police cikin sa'a aka ɗaga kiran ya yi saurin cewa" Hello taimakon gaggawa mota ta buge wani gashi nan a bakin titi ku yi sauri ku zo." Daga wayar aka tambayesa ina ne Unguwar ya faɗa musu kana ya kashe wayar tare da duban Auta ya ce" Yanzu za su zo." Jinjina masa kai kawai ta yi ta soma laliban jakarta taji bata nan, da sauri ta koma ta ɗauko har tuntube take za ta fadi Allah ya taimaketa bata faɗin ba ta iso cikin azama ta bude jakar hannunta na rawa ta ɗauko wayarta ta dannawa Mommynta kira , sai da ta gama ringing ba'a dauka ba zata kuma kira saiga Ambulance ta iso hakan ya sa ta miƙe tsaye tana kallon motar har suka yi packing suka fito, ɗaukan Khamis suka yi wanda yake tsakanin mutuwa da rayuwa suka sashi a mota. Da sauri Auta ta miƙe ta shiga motar Khamis taja ta bisu a baya hankali a tashe take driving tana kuka har suka iso Asibitin aka shiga dashi emergency room ita kuma ta tsaya a bakin ƙofar tana sharbar kuka. Tana nan zau ne taji wayar Khamis dake hannunta ta ɗauki ringing tabi wayar da kallo jikinta na rawa ganin sunan wanda yake kan screen ɗin wayar, hannunta na rawa ta soma ƙoƙarin ɗaga kiran sai dai kafin ta ɗaga kiran ya katse ta saki baki tana kallon wayar sai ga wani kiran an kuma yi cikin azama ta ɗaga tare da kara wayar a kunnenta ta yi shuru zuciyarta na bugawa hawaye na zarya kan kuncinta. "Hello my Son wai a ina kake haka tunfa ɗazu ake ta jiranka kai kaɗai muke jira ka zo muje kasuwa zaban kayan Afra na birthday ko lokacin bai zo ba ne? Wasu zafafan hawaye suka kuma bin kuncinta ta kai hannu ta goge baki ta buɗe da nufin magana amma ta taji maƙoshinta ya bushe, sake yin magana aka yi daga cikin wayar ciek da mamaki. "My Son wai ba ka jina ne ? A ina kake ka yi maza kazo bana son zuwa kasuwa da Yammaci fa kana jina iye? Wannan karon Auta fashewa da kuka ta yi cikin shashshekar kuka ta ce" Ammi Yaya Khamis n.. Da sauri ta katseta da cewa" Afra lafiya kike kuka?me ya faru da Khamis ɗin ina yake?" "Ammi mota ce ta bugeshi yanzu ma muna Asibiti Ammi ki zo please " Ta ƙarashe maganar cikin raunatacciyar murya.. Salati Ammi ke furtawa ta tambayi a wacce Asibiti ne ta sanar da ita kana ta kashe kiran, zama Auta ta yi zuciyarta na zafi ta rafka tagumi a sanyaye ta ce" Da nasan mota za ta buge da ban ce ina son wani abu ba." Kira ne ya shigo wayarta ganin Mommy ce ke kiran ta yi saurin ɗagawa tana jin muryar Mommy ta sa mata kuka tana cewa" Mommy Yaya Khamis mota ta bugeshi ya zan yi Mommy?" "Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Mommy ta furta da sauri ta ce ta mata kwatance ta yi mata ta kashe kiran..

Kusan a tare Mommy da Ammi duka iso Asibitin Auta na ganin Ammi ta isa gareta tare da faɗawa jikinta tana kuka marar sauti, bubbuga bayanta Ammi ke yi har suka zau na akan kujera ta ɗago ta ita cikin muryar rarrashi ta ce" Afra ki yi shuru mana kalli yadda idanunki suka kumbura. Ba kuka ya kamata ki masa ba addu'a kawai za ki masa." Jinjina kai ta yi ta kallo Mommy dake ɗayab gefenta ta ce" Mommy." Girgiza mata kai Mommy ta yi tana mata nuni da kar ta yi bata sake cewa komai ba Ammi ta kwantar da kanta a kan kafaɗarta. Sai da aka kwashi awa ɗaya a shigar da Khamis emergency kana aka buɗe ƙofar ɗakin, da sauri suka miƙe suna rige-rigen tambayar Doctor ɗin a tare suka ce" Doctor ya jikin nasa?" Kallonsu ya yi yana goge zufar data tsatstsafo masa a goshi kana ya mayar da glass ɗinsa ya ce" Ku biyoni Office." Ammi ta ce su zau na ta taje amma firr Auta ta ce itama zuwa za ta yi hakan ya sa Ammi kama hannunta suka nufi Office ɗin Doctor ita kuma Mommy ta zau na ta rafka tagumi tana jiran fitowarsu sai ga Mahaifin Khamis da Yayan shi sun iso, tambayarta suka yi ta nuna musu inda Ammi ta nufa suka wuce fuskokin su na bayyana tashin hankalin da suke ciki. Sun zau na kenan sai ga su Daddyn Khamis sun shigo suka samu guri suka zau na tare da bada hankalin su ga Doctor dan suji matsalar Khamis, sai da ya gama rubuce-rubucensa kana ya ɗago ya dubi su Ammi ya yi gyaran murya kana ya soma cewa "Gaskiya ɗanku ya naura arziki a yadda aka kawo mana shi ban taɓa tunanin za mu gama aikin nan rai baiyi halinsa ba, amma da yake Ubangiji shi ke yadda yaso da bawansa sai gashi ana gama masa dinki ya soma kiran sunan Afra." Ammi ta yi saurin cewa" Likita yanzu a wani hali yake ciki?" Jinjina kai ya yi kana aje barrow hannunsa ya ce" Am sorry Hajiya gaskiya da yaronku da wahala ya iya taka ƙafarsa, saboda ƙashin kwankwasonsa ya samu matsala mun masa duk wani gwaje-gwaje amma ko wani sakamako haka yake nuna mana ƙashin gurin ya tsage, sannan ya samu karaya a hannunsa na hagu haka ma gefen fuskarsa ya yi babban rauni mun yi masa dinki, alhamdulillahi ƙwaƙwalwar shi bata samu matsalar komai ba inda hali ya kamata ku fitar dashi waje ayi masa aiki, dan gaskiya yana buƙatar aikin gaugawa a kwankwason shi..

Daddyn Khamis ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" To Doctor mun gode in sha Allah yau ɗin nan zan nema mana ticket ko zuwa gobe ne mu sai mu tafi." Doctor ya dubi Daddyn Khamis ciki da tausayi ya ce" Zan haɗaku da wani abokina da yake Ƙasar Paris za ku iya can ko kuma ku tafi Ƙasar Saudiya ina ganin ma nan zaifi." Daddy ya ce" To Saudiyyar ma za tafi mun gode sosai yanzu za mu iya ganinsa?" "E za ku iya ganinsa amma ban da rubutu dayawa. Godiya suka kuma masa kana suka fito zuwa ɗakin, Mommy na ganin su ta tambayesu fatan ba matsala dai, Ammi ta sanar da ita yadda suka yi sosai hankalin Mommy ya tashi suka nufi ɗakin su duka, duk wanda yaga Khamis a wannan lokacin saiya zubar masa da hawaye ko ina na jikinsa an nade da bandeji hancinta an saka masa abin ƙarin numfashi, sai Yamma likis kana Mommy taja Auta shi ma da ƙyar ta yarda tabi Mommy gani take inta tafi za a kirata ace mata ya rasu haka dai suka tafi tana sharar hawayen tausayin masoyin nata..
_____

Ko da suka je gida ɗakinta ta nufa ta faɗa kan gado ta ci gaba da kuka zuciya na mata zafi da raɗaɗin ganinsa a wannan yanayin, bata taɓa jin ƙaunar Khamis ba irin ta yau ji take kamar ta koma Asibitin ta ƙara ganinsa ajiyar zuciya ta sauke ta tashi zau ne tare da zama a tsakiyar gado, can ta miƙe ta lalibo wayarta ta shiga duba number da Amra ta bata ta danna kira har ta yi ringing ba a ɗauka ba ta kuma kira nan ma haka, sake kira ta yi a karo na uku tana ringing har ta cire rai za a ɗauka sai ance hello. Baki na rawa ta ce" Amra kina jina?" "E ina jinki lafiya dai naji muryarki a haka?" Kuka ta sa mata ta shiga bata labarin abin da ya faru, salati Amra ke yi daga cikin wayar itama na tayata kukan ta ce mata gobe su haɗu za ta zo taga jikin nasa haka dai ta yi ta kwantar mata da hankali sai da ta tabbatar ta daina kukan kana suka yi sallama. Idanunta ne suka soma rufewa hakan ya sa ta jefar da wayar ta koma ta faɗa kan gadon tare da lumshe idanunta.

"Afra! Taji an kira sunanta a saitin kunnenta hakan yasa ta ɗan buɗe cikinta ne ya soma murda mata ta sa hannu ta riƙe cikin, wasa wasa ciwon cikin ta dinga karuwa tun tana kan gado har bata san lokacin data faɗo daga gadon ba tana murkususu tare da yin salati, tun daga ɓakin gado take birgima har takai jikin ƙofar ɗakin tana juyi tana wash cikinta haka ta dinga birgima a tsakar ɗakin har wani wahalallan bacci ta yi gaba ita..

Zau ne yake a jikin wata bishiya cikin shiga ta alfarma gefensa tana zau ne ta kauda kanta gefe, juyo da fuskarta ya yi cikin kulawa ya ce" Afra na wai duk fushin ne haka?" Bata yarda ta haɗa idanu da shi ba hakan ya tabbatar masa bata huce ba, shu'umin murmushi ya yi tare ta hura mata iska a gefen wuyanta . Da sauri ta juyo tana saɓa baki kamar mai shirin yin kuka ta ce" Bobby! Ɗan murmishi ya saki kana ya ce" Afra na kwana biyu ban ganki ba ke ko kewata ma ba ki yi ba ma." "Na yi mana Bobby" Ta bashi amsa tana shafa cikinta tare da ɗauko hannunsa ta ɗaura akan cikin nata tana murmishi. "Tashi muje mu kaɗai ake jira kowa ya hallara" Ya ƙarashe maganar yana miƙar da ita. Cike da farin ciki take binsa har suka isa ɓakin ƙofar wani ɗaki ƙarami ƙofar ɗakin bata fi yaro dan shekara biyar ya wuce ba, hakan yasa ta kallesa za ta yi magana ya ɗaura mata hannu a bakinta ta yi shuru ya kama hannunta suka kutsa kai ta ƙofar, kamar kiftawa da bismillah ta taga sun wuce ta ƙofar sai gasu a wani tamfatsetsan ɗaki. Baki da hanci t saki tana kallon gurin taga dai ba kowa hakan yasa ta ce" Bobby ka ce mu ake jira kuma naga bà kowa ina suke masu jiran namu? Hannu ya kai ya rufe mata idanu ta yi murmishi kawai bata ce komai ba, wani haske ne ya fito daga idanunsa ya zagaye suka wajan sai wasu dabbobi sun bayyana cike da gurin, duk dabbar da ya kalla sai ta rikide ta dawo suffar mutum. Buɗe mata idanun ya yi ta kalli gurin taga ya cika taf kowa ita yake kallo, baƙi ɗaga za ta yi magana taji an yi sama da ita da ƙarfi ta ce" A a Bobbyyyy!

A firgice ta farka tana salati jikinta sai rawa yake, al'ajabi da tsoro sun hanata motsawa zuciyarta na bugawa da ƙarfi sai zufa ke karyo mata ta ko'ina ta sauke ajiyar zuciya kana ta yi ta maza ta miƙe da ƙyar tana riƙe bayanta dake mata ciwo, cike da mamakin mafarkin nata ta ce"

1 Comments On ALJANAR GIDANMU
avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment