Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kai shekarunki fa sai ta fiki komai. Ran Fadila ne ya ɓaci jin an ce Auta za ta fita inta girma, amma ganin suna ciki farin ciki sai ta yi shuru tana murmishi amma ƙasan zuciyarta na ƙara tsanar Auta fiye da da.. Tana isowa ta tsaya a gaban Fadila tana cuno baki ganin yadda suka zuba mata idanu, ta ce" Ku kuma lafiya kun zuba mini idanu rakatau ba wanda ya ce ma sha Allah inma kunga na yi kyau ne?" Da sauri friend ɗin Fadila dake kusa da Auta ya ce" Haba Ƙanwarmu ai ke kuwa ki ka yi kyau matuƙa ma sha Allah sai ina haka ki ka sha ado? Ko kuma kema shagalin birthday za ki yi tare da mu?" Ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya tare da riƙe hannunta yana bin hannun da kallo...

Dariya Auta ta yi ta ce" Tab waye zai zau na shagalin birthday wai? Ba dai ni ba gaskiya ni na yi kwalliya ne dan Mommyna za ta dawo daga inda ta tafi, yanzu ma yunwa ce nake ji shi ya sa nazo Anty Fadila ta zuba mini abinci naci."

Da sauri ya miƙe ya ce" Ki rabu da Fadila dama can dukanki take bare yau da taga tana yin birthday, muje da kaina zan zuba miki abincin kici" Ya faɗa yana janta suka nufi kan darning table. " Sake da baki duk suka bisu da kallo, Mufy ta yi tsaki ta ce" Wallahi Bash ya dai ji kunya wannan zai ke wani likewa, ni har ya sa naji kunya Wallahi." "To ki ka sani ko yana mata haka dan ya hutar da Fadilar" Cewar wata dake gefen Fadila... "E kuma fa haka be to shi kenan ai gara hakan..

Kujera yaja mata ta zau na ita dai sai kallon ikon Allah take, abincin ya zuba mata ya aje a gabanta ya saka cokali ya ɗiba ya nufi bakinta yana murmishi ya ce" Ha Ƙanwata kici abincin ni zan rakaki duk inda za ki tafi."

Ɓata rai Auta ta yi ta ce" Ka aje naci da kaina Malam, nifa ba yarinya ba ce ba girma yanzu da a bani abinci a baki inba Mommy ko Daddy ba' Ta ƙarashe maganar tana amshe cokalin ta yi bismillah ta shiga ci hankali kwance...

Tun ta fara cin abinci ya zuba idanu yana murmishi har ya gama ta miƙe tsaye, ji ta yi ya yi carab da hannunta ta yi saurin juyowa a fusace ta ce" Kai cikani ko in zabga maka mari Wallahi ko an faɗa ma nima ƴar iska ce irinku? To ka fita safgata ka gane" Ta ƙarashe maganar tana wani ƙofa...

Fadila ta daddage ta kawo wata irin ashariya ta kundumawa Auta tana cewa" Ke dalla can banza shashasha dan ma kin samu ya miki magana, duk matan gurin nan ba su dameshi ba ke dan kin samu ya miki magana ma."

Tsaki Auta ta yi ta ce" Can ke ki ka sani mahaukaciya kawai shedaniya marar kamun kai, sai kin haɗu da daidai ke." A fusace Fadila ta miƙe ta iso gurin Auta bata tsaya yin komai ba ta zafga mata wani irin mari mai shiga jiki, gani ta yi Auta ko gizo bata yi ba kuma ba ta yi kukan data saba yi ba, hakan ya sa ta kuma marinta shima bata matsa daga inda take ba..

"Ni ki ka mara? To yau saina rama.

Dariya Fadila ta yi ta sunkuya ta ce" Ga fuska in kin ki r.. Bata ƙarasa ma taji sauka mari wanda ya sa taga taurari, kafin ta dawo an kuma ɗauketa da mari wanda yafi na farko zafi.

A razane ta ɗago ta kalli da take wasa da zoben hannunta, ihu ta kurma ta yi kukan kura ta damƙi Auta ta ce" Ni za ki mara yau sain.. Wutar palon ce ta ɗauke dif, Friend ɗin Fadila ya matso kusa da Auta ya lalibota yana bata haƙuri ya rungume ta da wayo ya soma taɓa ƙirjinta yana cewa ta yi shuru ta rabu da Fadila, wani irin ihu ya kurma ji kake tim....




*Kwana biyu kunjini shuru naje Unguwa ne kuma can ɗin ba network mai kyau, ina godiya a gareku da wanda suka miki magana ta pc da masu kira duk ina muku fatan Alkhairi Ubangiji ya bar ƙauna much love masoya😘🤗🤗*



_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[01/12, 22:59] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_




Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_



_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_

_Ina kuke masu jiran a gama littafin *ABBA NE* to ku garzayo jira ya ƙare an gama sa complete za ku same shi a farashi mai sauƙi akan N500, ga masu buƙatar ku tuntubeni ta WhatsApp number na.👇🏻_

*WhatsApp number +966599791573*


0️⃣6️⃣


Itama Fadilar ihu tasa tana ƙanƙame jikinta, wata irin iska ce ta shiga kaɗawa a palon, tuni kowa ya dunga gwaran kai da na kusa dashi, maimakon su yi addu'a sai suka shiga ihu da kiran juna..

Ɗaya bayan ɗaya ake binsu da gyararren mari a ko wani kunci ai kuwa suka kuma cika palon da ihu, Auta ta miƙe ta nufi inda ta ci abinci, tana isa ta sunkuya ta ɗauko ƴar Teddynta ta rungume tare cewa" Anty Fadila ku kunna mana haske bana ganinku."

"Wani ɗan iskan ne zai kunna miki dan uwarki? Wallahi ki ka sameni da kiran in wuta ta dawo dukan mutuwa zan miki, kina ga.. Bata ƙarasa ba taji saukar wani abu mai shegen nauyi akan bayanta. "Waiyo Daddy na mutu na lalace shi kenan ƙila suminti ya faɗo mini a gadon baya" Ta shiga faɗa tana huci da ƙyar saboda nauyin da aka ɗaura mata yafi ma na buhun sumintin...

Friend Fadila na ƙasa yana ƙoƙarin tashi aka ja shi baya, zane shi aka shiga da bulalar doki. "Waiyo! Fadila tana kuna da Aljannu a gidan nan naku? Shi kenan hannuna ya karye waiyo na shiga uku Mami sun karya mini hannuna" Ya ƙarashe maganar tare da kurma wani zababben ƙara na azaba kana ya baya ya sume...

Fadila ta shiga laliben Friend ɗinta tana kiran shi da" Jon! Jon! Jon! Wai kana ina?" Saukar ruwa mai zafin gaske taji a bayanta hakan ya sa ta saki ƙara tana faɗuwa ƙasa ta shiga birgima, saboda azabar da take ji bata san ta kai gaf da kujerar palo ba ai kuwa ta buga goshinta a jikin ƙafar kujerar, ihun ta kuma sakawa tana jan jiki ta yi baya tare da riƙe goshi tana jin wani lakar zafi wanda bar kan babban ɗan yatsarta ta jishi zafin ba shi da misali..

Girgiza palo ake ana ta yin wata irin dariya mai firgitarwa, tuni wasu suka dinga sakin futsari a jikinsu wasu kuma saboda tsananin firgita har zayo suka saki a jikinsu ba su sani ba, can dai suka ji ɗif shuru babu komai, sai da suka ɗauki kusan minti uku a haka kana suka fara jiyo gudu ana ta zagaye palon, tuni kowa ya soma neman cetan ranshi, wasu a jikin kujera suka maƙale wasu kuma a ƙarƙashin darning table suka liƙe suna zunduma ihu, kowa kiran kowa yake yayinda wannan ƙaran gudu ke funfair gadan-gadan kamar zai hau kansu..

Suna a haka suka ji komai ya dena rawa na palon shuru, harhada kan komai aka shiga su kuma nata ihu har aka gama, wutar palon ce ta dawo haske rau..

Sake da baki kowa yake kallon shi a inda ya zau na, shi ko Jon yana can gefe yashe a sume, Fadila na kusa dashi ta riƙe goshinta da yake mata mugun raɗaɗin azaba, kanta suka yo suna ta kiran sunanta ita da Jon..

Kande ce ta fito daga kitchen hannunta riƙe maggi, ganin Fadila a ƙasa ta nufesu da sauri tana faɗin" Subhanallah Fadila me ya faru dake haka?" Cike da mamaki Fadila ta tsayar da kukan da take ta saki baki tana kallon Kande dake jera mata sannu, kasa daurewa ta yi ta ce" Wai Kande kina nufin duk wannan ta'asar da aka yi a palon nan ba ki ji ba ko me kike nufi da kika fito kina jero mini sannu?" "A a ni gaskiya babu abin da naji ni na ɗauka ma kun fita ne taryar saurayin naki da ki ka ce zai zo daga Abuja zuwa nan Katsina, to amma mene ne ya fasa miki goshi faɗuwa ki ka yi ne?

Tsaki Fadila ta yi amma zuciya cike da mamaki take na abin da Kandan ta faɗa yanzu, to taya za ace duk wannan ɗibar albarka da aka musu amma ta ce wai bata ji komai ba kai anya kuwa ba aljannu ba ne a gidan nan? Fadila ta faɗa a ranta. Tsaki ta kuma ta miƙe da ƙyar ta janyo ruwan da Kande ta kawo ta kwarawa Jon a fuska.

"Innahu Sulaimanu! Ya faɗa a firgice yana zare idanu, shuru ya yi yana binsu da kallo baki buɗe. "Kai dalla can banza ka wani saki baki kama kallonmu ko mun canja kamannin ne ba mu sani" Cewar Mufy tana aiko masa da harara fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye da majina kamar wani ƴar 3 years.. kashewa da dariya ya yi duk da hannun shi dake masa azabar ciwo, da hannu yake nunata yana dariya ya ce" Wai ina ruwan gajala kalli hancinki ya fage kamar an taka makilin a rana, Fadila ki kira mana wanda zai gyara mini hannuna, ina fa jin na goce ne amma dai kuna da Aljannu a gidan nan ko?"

Tashi ta yi da ƙyar suma suka taimaka masa ya tashi suka dawo kan kujera. "Wallahi Fadila da alama kuna da Aljannu a gidan nan, yanzu bari na kira ƴar Maigado ta zo ta koran mana su, haba kalli fa sai tsami wasu suke muje ku yo wanka a ɗakin Fadila wasu kuma ku yi a nan falo" Cewar Mufy tana kallon Fadila..

Fadila ta yi tafi ta ce" Chass ashe ma ke kin san ƴar Maigad? To ki kira mana ita ta zo ko na saka direba ya zo ya kawo mana ita dan Wallahi ba zan dena birthday ɗina ba saboda wata aljana can, kira mana ita yanzu yanzu nake so ta zo ba sai an jima ba.." Ok kawai Mufy ta faɗa tare da danna mata kira, ringing biyu ana uku ta ɗaga tare da yiwa Mufy kirari.

"Yarinya mai tashe mai abin mamaki, gwamnoni naki Ministoti naki.. Wani Farr Mufy ta yi da idanu kana ta ce" Yawwa ƴar Maigado kina jina yanzu ki nakeso ki zo gidan su Ƙawata aljannu ne suka shigo mu su , inaso ki zo ki ci ubansu." "Ba ki da matsala ta hannun dama ta, yanzu za ki ganni na iso kawai kwtance nakeso ki mini. Kwatance Mufy ta mata sannan ta kashe kiran...

Babu jimawa sai ga ƴar Maigado tun daga ɓakin get ta afka turaren hayaƙi tana karkada gashin kaza dake hannunta, Maigadi ya rafka tagumi yana sallallami tare da kallon ƴar Maigado tana yin wasu yaruka da bai san wani kala ba ne. Daret cikin palon ta shigo da jagorancin Mufy ta yada zango a kasan carpet sai sunbatu take..

Fadila ta miƙe ta iso kusa da ƴar Maigado ta sakata a gaba ta soma rattabo mata bayani kamar an jonata. " Ranki ya daɗe ƴar Maigado ki taimaka ki korar mana wannan aljannun dake gidanmu, yanzu haka sai da ta mana dukan tsiya ina so ma ki duba mini Ƙanwata dan na lura da an taɓa ta sai kawai kiga abubuwa suna ta faruwa, ko kuwa dai ɗiyar aljannu ce ba mu sani ba?"


"Kwarai kuwa yarinya wannan ba shakka aljani ya yi cikinta ba mutum ba, maza kira mini ita nan na fitar da aljannun dake jikinta" Cewar ƴar Maigado tana kara zuwa ciyayi a cikin garwashin dake cikin wani ɓakin kasko.. Fadila ta yunkura kenan za ta tashi sai kawai taga Auta a zau ne a ķusanta, zabura ta yi ta fasa ihu tana cewa" Kin gani ko haka take fa kuna zau ne sai dai kiga ta bayyana wallahi aljana ce Auta, ki taimaka kar ta kashemu a gidan nan."

Wani kalar murmishi Auta ta yi ta kalli Ƴar Maigado, ƴar dariya ta yi tana kaɗa kai ta ce" Anty Fadila wannan kuma ita wace ce daga ina ta zo? Ƴar Maigado ta ɗauko wani ruwa a cikin wata tsohuwar langa ta watsawa Auta tana cewa" Tun muna mu kaɗan ku fita daga jikinta kafin na muku hayaƙin Ƴar Mairo mai barkono, bana wasa daku maza ku yi magana na ce." Rintse idanunta Auta ta yi jin wani ruwa mai wari ya kawo mata ziyara, cikin shashshekar kuka ta ce" Allah ya isa muguwa azzaluma mai na miki kike zuba mini ruwa mai wari da tsami? Waye ma ya ba ki izinin shigowa gidanmu?"

Iye! Wato ma ni ce azzaluma ko? Za kuga azzaluma ajin farko yau in baku fita daga yarinyar nan ba, miƙewa ta yi ta zaro wani bulala ta maina mai kauri ta tsaya akan Auta ta ce" Shin za ku fita ko kuwa sai na nuna muku ni a ƙasan gada aka haifeni na kuma gado iyayena da kakannina wajan bayar da maganin irinku? Zan nuna muku alnahin kamata yanzu nan in baku fita ba.."

Auta ta zubawa Ƴar Maigado idanu dan ita dai ta rasa akan wa ake maganar nan, gashi kuma taga ta zo kanta ta tsaya tana mata wasu maganganun banza da wofi, tsaki taja tana ƙoƙarin tashi sai taji an mayar da ita an zaunar...

"Ku ɗaure mata hannu ta baya har ƙafar ma" Cewar Ƴar Maigado.

Kafin sakon biyar tuni sun ɗaurewa Auta hannu da ƙafa sai kuka take tana faɗin" Waiyo Allah Mommy! Wai mai na muku ku sakeni Islamiya zan tafi fa Anty Fadila ki ce su sunceni please and please" Ta faɗa tana zubar da hawaye."

Bash ne ta dubi Ƴar Maigado ya ce" Haba ranki ya daɗe ya za ku ɗaure mata hannu da ƙafa kamar wata mahaukaciya, gaskiya ku since mata jiki ko ma mai za ayi ya kasance tana zau ne za ayi."

Kai fa dama mahaukacin ne ɗan rainin hankali taya za mu yarda a Kunce ta sai kace ba yanzu aka gama lallasa ka ba" Cewar Fadila tana dungure masa kai..

Ƴar Maigado ta ɗaga bulala ta zabgawa Auta a gadon baya. " Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Ta kasheni waiyo Mommy dama Anty Fadila ba ƙaunata kike ba shi ne ki ka kawo mai kasheni har gida me na miki a rayuwar ta duniya da har ki ka zaɓi kisa a kasheni? Anya kina da imani kuwa?" Ta faɗa cikin ƙaraji tana mutsu-mutsu dan ba ƙaramin zafi da azaba taji ba..

Sake ɗagawa ta yi za ta kai mata wani duka aka yi sama da ita aka sakota ƙasa tim!

Bata yi ihu ba sai ta miƙe da ƙyar dan kar su ga kasawarta ta ce" Aljannun nata suna da lafiyar kai yanzu zan musu mai gaba ɗaya, sake nufar Auta ta yi da kanta yake ƙasa tana kuka wiwi har da majina, ɗagawa ta yi za ta sake mata hannun ya tsaya cak, kiciniyar sauke hannun take amma ta kasa, bulalar ce ta yi sama aka shiga zuba mata ita tako ina sai ihu take tana kiran ƴar mairo...

Wani duka aka kawo mata bakinta saiga hakoranta na gaba sun zubo ƙasa, ihu ta kurma ta zabura hannunta a sama ya kasa yin ƙasa ta nufi hanyar fita waje, kafin ta isa aka sauke mata ƙyawawan mari, gashin bayanta ne ya yi wani irin ƙara ƙaƙaratttt!

Ihu suka sa duka falon ai kuwa bulalar nan ta ta shiga zanesu tako ina, Ƴar Maigado ta ci sa'a aka barta ta buɗe ƙofar palon, zaninta a hannu daga ita sai sket na ciki kanta ba ɗan kwali ta fito a 360 tayi wata irin suka sai gata a samar katanga..


Baba Maigadi ya kalleta da sauri ya ce" Ke karfa kiji ciwo ki sauko na buɗe miki ƙofa, wani abin ne yake faruwa a ciki?"

Ƴar Maigado ta watso ƙafafuwanta bayan katangar ta juyo ta kalli Maigadi ta ce" Uwarka ce take faruwa ashe haka gidan nan yake da aljannu." Maigadi zai sake magana Ƴar Maigado ta kurma ihu ganin wata ƙatuwar mage ta yo suna za ta hayo katangar, a firgice ta wuntsila ta faɗo waje timmm! A guje ta bi haya kamar sabuwar kamu yi take tana waiwaye magen nan data biyo.

"Takalmanta a hannu tana tana falfala gudu kamar za ta tashi sama, rigar jikinta granbubu ce tana gudu iska ta cikata, ganin fa da gaske magen nan bata dena binta ba ta zubar da takalman ta dinga ihu tana faɗin" Ihu jama'a taimako! Taimako! Aljana ta biyoni ku tareta kar ta iskoni..

Duk inda ta nufa a guje wanda suke zau ne da sun hangota tana ihun nan za su kwasa a guje su yi gaba....





_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[02/12, 23:18] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_




Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_



_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_

*WhatsApp number. +966599791573*



*بسم الله الرحمن الرحيم*

0️⃣7️⃣

Auta ta kwanta a ƙasa tana birgima dan ba ƙaramin zafin dukan taji ba, miƙewa ta yi daga kwanciyar da ta yi ta kalli su Fadila da suka yi shuru suna kallonta, tsaki taja ta nufi kan darning table ta buɗe babbar kular da Fadila tasa aka haɗawa saurayinta.. "Ke! Dan uwarki karki taɓa mini wannan abincin, duk abincin dake kan darning ɗin sai na wannan kular za kici? Bata kulata ba ta gyara za ma tana huci mai ƙarfi kamar mai ciwon fuka, hannu ta tattare ta saka a ciki ta ciko hannu da dambun kuskus da yaji kayan haɗi yana zuba ƙamshi ta kai bakinta ta kuma danna hannun ta ciwo ta ƙara cusawa a bakinta, da ƙyar take juya abincin dake cikin bakinta sai zare idanu take. Kafin Fadila ta yi taku biyar zuwa gurin Auta tuni ta dinga hannu baka hannu ƙwarya kan kace mai tini babu dambun ta cinye tass. "Kuturun uban can! Auta ke kuwa ki ka cinye abun nan ko kuwa aljannun naki ne suka tayaki? To Alkur'an sai kin rama mini dambu na ko in miki dukan mutuwa dan kakan uwarki. "Karki ƙara zagina malama, dambu kuma na ci sai dai ki farka cikina ki fito dashi in kika takura mini zan sa masoyina ya miki dukan tsiya, banza ke da ko ruwan zafi ba ki taɓa ɗaurawa ba ma" Ta ƙarashe maganar tana cuno baki gaba tare da daura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ƙarewa Fadila kallo..

Tab dijam! Ke yanzu duka nawa kike da har wani sakarai zai kulaki da sunan soyayya? 14 years fa gareki ita ma sai nan da wata biyar za ki cike 14 years ɗin, anya ba aljannun jikinki bane suke da samarin? Hmm aikin banza an yi sadaka da karuwa..

"Amma dai an ta raya sunnar ma'aiki ko? " Cewar Auta tana murmishi mai ɗauke da ma'anoni..

Sake da baki Mufy take kallon Auta sai kuma taja tsaki ta ce" Aminiya ki rabu da wannan ƴar shilar ina mutumci haka zuwa maka da kare, wannan yarinyar in kika biyata ai sai mutumciki ya zube a banza ta take.

"Dama na gama take shi ai" Ya bawa Mufy amsa tana shafa gefen fuskarta..

Riƙe baki Bash ya yi jin yarinya ƙarama na zaro magana kamar wata ƴar shekara 20, Jinjina kai ya yi ya miƙe yana cewa" Fadila ni zan tafi gida a gyara mini hannuna, ina tunanin ki bar birthday ɗin nan sai gobe kawai, kinga shi Al'amin ɗin ya ce sai dare zai shigo Katsina kawai mu bari sai gobe tun da ba a kawo komai ba na birthday." Auta ta mishi kallon uku saura kwata ta miƙe ta wuce sama tana cilla ƴar Teddynta kamar ba ita ba ce yanzu take kuka tana birgima. " Tab Wallahi Fadila aljannun jikin Auta mayunwata ne, diba fa ki ga yadda ta tashi da ƙatotuwar kular abincin, gaskiya bari na wuce gida" Yana gama faɗin haka ya miƙe ya ɗauki key ɗin motar shi ya wuce daga palon.. Suma sauran duk barin gidan suka yi Fadila ta jadadda mu su gobe su fa zo kana suka wuce,cika yi ta yi fam tana nufar sama..


Amra ce ta tafi daga gidansu sanye take da doguwar riga amma tsanyin nata mai rufe ta ba har ƙasa iya kwafrinta ne kawai, shagon wani mai shayi ta nufar tana ɗan wake-wakenta cikin nishaɗi har ya iso gurin. "Yarinya mai za a ba ki ? Cewar mai shayin yana kallon Amra..

"Dama zuwa na yi ka taimaka mana, ba mu da komai ga yunwa da nake ji ka taimaka ka bamu an jima kaɗan zan kawo maka kuɗin ka" Cewar Amra tana matso hawaye..

"Kut! Waye zai baku bashin? Wai anya kuwa kin san Bala mai shayi kuwa? To duk Umguwar nan babu wanda bai sanni ba bana bayar da bashi , ki fice mini a nan ko na mika dukan mutuwa.. "Don Allah kada ka kureni ka bani koda na hamsin ne Innata bata ci komai ba kar ta mutu.

"A fusace Bala mai shayi ya yo kan Amra ta sauke mata mari mai zafi, cikin masifa ya ce" Ni za ki kalla ki ce ba baki bashi dan kin rainani? To ki shiga hankalinki kar in kakkarya miki ƙafa kiji daɗin yin bara akan titi."

Da ƙyar wani mutum ya zo wucewa ya kwaci Amra daga gurin Bala mai shayi, nunata ya yi da hannu ya ce" In na sake ganin ƙafarki a nan wajan gobe saina miki dukan da yafi wannan, banza yar matalauta masu ƙashin tsiya kalleta ko takalmin kirki bata da shi, za ki tafi ne ko saina miki abin da yafi wannan?" Kuka sosai Amra take ta koma gefe tana kallon Bala shayi tana jero masa da saƙon Allah ya isa shi kuma yana aiko mata saƙon zagi, sai da taga mutane sun yi yawa a gurin kana ta miƙe ta tsallaka titi ta nufi inda ta fito...

Kwance take tana sakin murmishi tana juyi ita kaɗai akan gadon, da sauri ta buɗe idanunta sai kuma fashe da kuka ta ce" Haba wallahi ba zan yadda ba ka tafi ka barni, ka dawo mana please" Ta ƙarashe maganar tana komawa buduf ta kwanta tana ci gaba da kukanta. Auta! Auta! Kina ina ɓoyewa kika yi ne wai? Ki zo mu tafi ɗaukan Mommy ta kusa isowa" Sudas ne ki kwalla mata kira yana nufo ɗakinta..

Wani irin tsaki Auta taja tana sake yin miƙa ta kuma cewa" Nidai ka dawo bamu gama magana ba." Buga ƙofar Sudas ya soma har ya gaji ya rabu da ita ya koma ƙasa.

Wani haske ne ya haske fuskarta kana daga bisani ya shige jikinta, kamar ƙiftawa da bismillah bacci ya kwashe ta..

Zau ne suke a cikin wasu furanni masu kyau gefe guda kuma ruwa ne ke ta gudu tsintsaye nata shawayi a saman ruwan, gyara za ma tafi ta dube shi cike da shagwaɓarta mai narka masa da zuciyata ta ce" Shi ne har za ka gudu ko?" Dan murmishi ya saki kawai sai ya kamo hannayenta cikin nuna kulawa ya ce" Afra ai ba zan taɓa guduwa na barki ba har abada ni dake mutu ka raba, ke ko kin mutum ma ba zan auri kowacce mace ba zanke magana da ruhinki." Lumshe idanu ta yi tana jinjina kai alamar gamsuwa da maganar shi, ɗago da idanunta ta yi ta ce" Bobby kasan yau mai Anty Fadila ta mini kuwa?" Tuni annurin fuskar shi ya ɗauke ganin fuskar abar ƙaunar tashi babu annuri, Afra me ta miki maza faɗa miki yau saina rama miki hankalina zai kwanta." Shuru ta yi ta zuba masa idanu ganin yadda nasa idanun suka canja kala, ta riƙe hannunsa tana murmishi ta ce" To ka

1 Comments On ALJANAR GIDANMU
avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment