Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Auta in ta samu dama.

Daddy ya yi shuru yana nazarin kalaman Auta kana ya ce" OK no problem my dear zan ƙara mata dan farincikin ki." Fadila ta shiga hura hanci ta zabure kamar ƙiftawa da bismillah sai gata a gaban Daddy ta shagwaɓe tare da cewa" Daddy a canza mini mota gaskiya tawa ta samu matsala jiya ma a tsakiyar titi ta lalace, ni a matsayina na ɗiyarka bai kamata ace ina hawa keke napep ba, abin kunya ne ma aga wanda ya fito daga cikin gidan nan ya hau napep." "Karki damu zan saya miki ku je ku huta brothers ɗin ku kusa shigowa. Tsalle ta yi tare da sumbatar Daddy ta koma ta zau na bata ce da friend ɗin nata ba su tafi part ɗinta ba ..

Wani horro film aka kawo a tashar da suke kallo abin da Auta take matuƙar so kenan dan haka ta mayar da hankalinta kacokam akan TV tana murna, Mommy ta koma gefe ta zau na tana harara su Mufy su kuma suna mata kallon uku saura kwata...

Hon suka ji Daddy ya ce" Yawwa ga ma su nan sun iso." Da ihun kiran Mommy da Daddy Sudas da Sauban suka kutso kai cikin palon ba sallama, fito Sudas ya dinga yi ya nufo Mommy, shi kuwa Sauban kamar yadda ya saba eapis ɗinsa a kunne yana bibiyar wakar da yake sauraro,Mommy ta rafka tagumi tana addu'a a zuciyarta har Sudas ya iso gabanta ya kama hannayenta ya mata kiss tare da cewa" Mommy missing you so much. " Harara ta watsa masa sai kuma ta yi murmishi kana ta ce" Welcome back my Son's ya aikin?" Am fine Mommy how are you today? Lafiya ta amsa masa a takaice dan ita ta tsani wannan kwarmaton na dole su sai dai su ma turanci ba za su maka Hausa ba a matsayinsu na 'ya'yan Hausawa, sai dai kawai turanci kamar daga England aka yo ruwan tsirar su...

Bayan an gama murna Kande ta zo ta gyara gurin suka koma kan kujera, tana gamawa ta kawo abinci suka ci ta kwashe komai..

Kowa harkar gabansa yake Daddy na can gefe yana duba wasu takardu, Auta na a gefen shi tana wasa da yar Teddynta tana mata surutu, Mommy na can ɗayan gefen tana kallon wani hira da ake da Malamin addini a BBC a cikin wayarta, Fadila da ƙawayenta tare da yayunta Sudas da Sauban na kallo...

Ɗagowa Daddy ya yi cikin farinciki ya kalli Mommy ya ce" Darling na kara samun riba a company na har ta miliyan goma cikin wata biyar, Auta maza tashi ki ɗauko mini barrow zan rubutawa Kande cak ɗin da kuma naku lis ɗin." Da murna Auta ta miƙe ta nufi ta gaban su Fadila tana cewa" Daddy zan rakaka Dubai sai kawai taji ta yi baya ta faɗi tim.. Bata yi kuka ba ta ɗago kai ta kalli Fadila da take aiko mata da harara, hmm kawai ta faɗa ta wuce ranta a matuƙar ɓace...

Tana tunkaro ɗakin taga kamar an wuce ta gabanta, dariya ta yi kawai ta nufo cikin ɗakin Daddy. Mamaki ne ya kama ta ganin duhu ba alamar haske, bata kawo komai a ranta ba ta miƙa hannu da niyar haska wutar ɗakin. Tun kafin ta kai hannu ɗakin ya gauraye da haske, murmishi ta saki ta nufi inda Daddy yake aje barrow ta ɗauko ɗaya ta juyo idanunta suka kai kan ɗayar ƴar Teddyn ta a kan gadon Daddy..

Ɗaukan Teddy ta yi tana cewa" Baby ashe a nan na barki?" Hasken ɗakin ne ya ragu tare da sautin kuka da muryar yara, dariya Auta ta yi ta ce" Ni ce na aje ki?" Ji ta yi kawai an ce" E". Auta ta miƙe da sauti tana dariya ta ce" Yawwa to yi haƙuri yau zan goyaki a bayana" Ta faɗa tana ɗaukan Teddyn ta wuce zuwa palo. Shuu ta ji wucewar wani abu ta bayanta ta yi saurin juyawa sai taga ba kowa, wucewarta ta yi tana shilla ƴar Teddy har ta sauko ƙasa ta miƙawa Daddy barrow ta zau na.. "Auta ke daga aikin ki sai ki shantake" Cewar Daddy yana ci gaba da rubutunsa." "Daddy ƴar Teddyna na ɗauko har ma ta yi fushi dani tun ɗazu take kuka" Ta faɗa tana rungume Teddy.. Murmishi Mommy ta yi haka ma Daddy...

Sudas ne ya juyo zai yiwa Daddy magana, idanunsa ne ya sauka akan Teddy Auta. Gani ya yi tana zaro masa idanu fuskarta ɗauke da ɓacin rai. Waiyo Daddy tana hararata" Ya faɗa yana maƙalewa a jikin Sauban. . Dariya suka kwasa sai wutar palon ta dauke dif, kowa ya shiga zare idanu. Palon ne ya ɗauki wata irin girgiza tuni kowa ya rungume na kusa tashi duk suka cika palon da ihu, Mommy ta soma addu'a aka yi sama da ita shuu sai gata a ɗakinta aka kullo mata ƙofar.. Auta ta miƙe tana laliban Mommy tana tafiya a duhu sai ta isa gurin su Sudas ta shafa bayan shi cikin wata irin murya ta kwashe da dariya wadda palon gaba ɗaya ya dauki sautin ta.. Futsari Sudas ya saki yana karkarwa take ya maƙale Sauban, ita kuwa Auta dena dariyar ta yi ta dinga tafiya da lalibe har ta iso kusan su Fadila ta soma shafata.

"Waiyo! Fatalwa Daddy kana ina Mo. Bata ƙarasa ba aka yi sama ta isa aka buga a kan kujera ta Ƙwalla ihu, tare da sakin zawo saboda tsananin tsoro. Wani irin kuka-kuka aka dauka kamar na Doki kamar na Jaki hakan ya sa suka karade palon da ihu suna ƙara mannewa da kujera kamar za su shige cikinta.. Wani haske ne ya bayyana a sama duk suka ɗago kai a tunanin su wutar ce ta dawo sai suka yi arba da wani narkaken halitta mai suffar mutane ƙafafuwan shi na Doki hannayen shi irin na biri, fuskar shi ba kyaun gani haƙoransa na gaba manya guda biyu, idanunsa jajaye manya-manya har wani tartsatsin wuta yake..

Sudas ya buga ihu yana cewa" Ihu jama'a ku kawo ɗauki fatalwa a g. Bai ƙarasa ba aka wanka masa mari ya sume a jikin Sauban, shi kansa Sauban ɗin futsari ya saki ya yi sharkaf da futsari haɗi da zufa...




_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[09/12, 00:13] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_




_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_


_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_



بسم الله الرحمن الرحيم


1️⃣1️⃣


"Waiyo Daddy ka taimakeni bayana ciwo yake" Cewar Fadila tana ƙara maƙalewa kujera jikinta na rawa karr³ . Kiyat! Suka ji ƙaran yanka wani abu kamar an yanka zani da ƙarfi, ihun Mufy suka jiyo tana faɗin ta mutu ta lalace a taimaka mata.. Fadila dake gefenta ta soma ja da baya jin wani abu na bin mata hannu, zabura ta yi cikin tsananin firgici da nufin ta sauka akan kujerar. Tinjum! Suka kuma jiyowa kamar an saka wani abu a cikin rijiya mai ruwa sosai..

"Daddy! Daddy ka taimakeni Waiyo ana jana Daddy za su tafi dani ku taimakeni"Fadila ta faɗa a tsorace jinta a cikin ruwa tsundum sai janta ake yi ana yin ƙasa da ita.. Wuta ce ƙarama ta bayyana a palon a inda Fadila take kwance tana neman taimako, a hankali wutar ta dinga nufar Fadila tana wani irin ci bal bal bal kamar wutar gobara, tana isowa kusa da Fadila ta ɓace fat abin da ya ƙara hargitsa su gaba ɗaya kowa ihun ceton rai yake, kaf cikin su ba wanda ya yi tunanin yin addu'a sai ihu da faɗin sun shiga uku. Kafar Fadila aka ja kiiiii zuwa bayan jujera aka haɗa ƙafar da jikin kujera aka buga da ƙarfi ji kake ƙasss! Wani irin ihu Fadila ta kurma saboda tsananin azaba ta saki zawo da futsari a tare , kuka take tana riƙe ƙafar dake jikin kujera an maƙala ta, ja take amma ta kasa fiddawa nan da nan ƙarfinta ya ƙare ta yi lakwas tana mayar da numfashi.

Sudas na jikin Sauban a sume yayinda shi kuma Sauban jikin shi yake rawa haƙoransa sai gamewa suke saboda tsananin firgita da tsoro, da ya juya gefe sai ya ga Mage na ruƙo masa idanuwa sai ya yi saurin rufe idanu, in kuwa ya rufe ƴar Teddyn Auta zaike gani tana neman kai masa cafka sai ya yi saurin buɗe idanunsa. Ji ya yi an tsikara masa wani abu mai kama da allura a wuyan shi ba shiri ya kurma ihu har bai san lokacin da ya zabgawa Sudas mari ba , sake tsikara masa aka yi a kafaɗa ya zabura ya amma ya ƙasa tashi kamar an dasa shi a gurin kasancewar Sudas ya maƙale masa gashi da mugun nauyi kamar buhun suminti babba, gurin ya shafa aikuwa yaji damshi a wajan ga duhu ya kasa ganin ko mene ne, shinshinawa ya yi warin wani abu mai tsami ya daki hancinsa ya yi saurin gogewa a jikin rigarsa, cikin jin zafi da zugin da gurin yake nasa ya ɗaga ɗayan hannun ya laftawa Sudas mari wanda ya yi sanadiyar dawowar numfashinsa daga suma..

"Waiyo Allah! Cewar Sudas yana dafe kuncinsa cike da jin zafin gurin, ɗago kai ta yi ya buɗe idanunsa ya ga duhu ko tafin hannunsa baya gani abin da ya ƙara tsorata shi matuƙa, ɗaga kai ya yi sama duk da baya ganin komai sai duhu ai kuwa ya yi arba da Auta a saman ginin ta yi ringeshe tana kallonsa fuskarta ba alamun wasa, ihu ya kuma kurmawa yana ƙoƙarin komawa jikin Sauban yaji saukar duka a gadon bayan shi, kiran Mommy yake yana ta taimake shi ana ta ci gaba da dukansa, idan ya kira sunan Mommy sai a lafta masa tafi a fuska nan da nan fuskarshi ta kumbura saboda marin da yake sha, tun yana ihu har ya gaji ya dena sai dai na Sauban yaje jiyowa wanda shi kuma ake ta caka masa wani abu kamar allura a duk inda aka samu na jikinsa..

Dariya aka ɗauka a palon zuwa can suka ji sukuwar Dokuna suna ýowa inda suke zau ne, tuni kowa ya dinga ihu ga babu karfin da za su motsa koda ɗan yatsarsu ne hakan ya ƙara firgitasu ba kaɗan ba..

Tun da aka fara abubuwan nan Daddy ya manne a jikin wani lungu wanda yake dauke da kayan game ɗin Auta da sauran kayan kallo, a sauri ya ɗauko wani zobe jikinsa na rawa ya saka a hannunsa yana mayar da numfashi, kamar ƙiftawa da bismillah yana saka ya ɓace fat a gurin.. Mufy ta yi rashe-rashe saboda yadda ta buga ƙugunta a jikin ƙafar kujera, numfashi take mayarwa tana nishi kamar ana zare mata wani ɓangare na jikinta haka take ji, wani irin naushi aka kawowa gefen bakinta ai kuwa ta fasa ihu jikinta ya ɗauki rawa sai futsari ta sume, gashin dokin data yi kitso dashi aka kama tass aka washe kitson gaba ɗaya, wani kalar raɗaɗi take ji kamar kanta baya jikinta ihun ma da take ta kasa sai dai ta dinga nufashin tana kurgumki. Ƙassss! Hannunta ya bada sautin ƙaran nan cikin wani irin amo Mufy ta zabga ihu tana juya kanta tare da jan jiki tana birgima kamar wata macijiya, "Waiyo! Na mutu na lalace a taimakeni zan mutu ban gaji da duniya ba z.. Bata ƙarasa ba taji an yi sama da ita aka shiga yin ƴar wurgiya da ita, tuni cikinta ya kaɗa tana ihun a taimaketa sai kwalalo idanu waje take yi ganinta ita ba sama ba ita ba ƙasa ba tana tsakiya..

Auta dake zau ne akan kujera ta maƙale ƴar Teddynta ta yi shuru idanunta a rufe, gizo masoyin nata ya dinga mata da zarar ta rufe idanunta shi take gani yana ware mata hannaye alamar ta zo gareshi, kamar iska haka aka ɗauki Auta aka yi ɗaki da ita. Daret gado aka yi da ita tare kwantar da ita, hamma ta dinga yi tana miƙa idanunta a rufe ta miƙa hannu ta janyo bargo ta rufa...

Zau ne suke ta yi matashi da cinyar shi hannayen shi na kanta yana shafa lallausan gashin kanta, murmishi ta saki ta ɗago kanta tare da cuno baki gaba tana hararar shi. Ƴar dariya ya yi ya ce" Ya akayi ne shalelena?" Lumshe idanu ta yi sosai sautin muryar shi ta narka mata da zuciya, à hankali ta ce" Bobby miss you"Ta ƙarashe tana masa kukan shagwaɓa. Da sauri ya tasheta ganin zubar hawayenta hankalin shi ya tashi ya shiga tambayarta. "Shalele yi haƙuri kar ki mini asarar hawayenki masu tsada ki taimaka bana son ganin kina ɓacin rai, kwana biyu ina son mu haɗu dake amma aiyuka sun mini yawa shi ya sa ban samu na zo na kula dake ba, ɗago fuskarta ya yi ya zuba mata idanu suna haɗa idanu, wani haske ya fito daga idanunsa ya shiga nata idanun ta yi saurin sauke ajiyar zuciya ta yi baya zata faɗi ya hura mata iska ta buɗe idanu. Idanunta suak kawo ruwa ta kalle shi kamar za ta saka kuka jin yadda take jin son shi na ƙara nunkuwa a zuciyarta ji take kamar ta mayar dashi cikinta saboda yadda take ji har wani rawa jikinta yake yi, numfashi ta kuma saukewa tana ƙara ƙura masa idanu kana ta ce" Bobby!.

Wani shu'umin murmushi ya saki yana binta da kallon ƙauna ya ce" Na'am Shalelena wai yau lafiya kike ta rigima?"

Kuka ta saka masa tana kallonsa.

Dafe kai ya yi yana murmishi ya kuma cewa" Me kike na miki yanzu ki dena kukan nan?"

"Cikina Bobby yana dan mini ciwo bacci kuma nake ji, Bobby kuma zan ci abinci yunwa nake ji..

Ƴar dariya ya yi ya miƙa hannun shi baya sai ga abinci a cikin trey ya bayyana ya miƙo tare da ajewa a tsakiyarsu, nuni ya mata da ga abincin.

Waro idanu ta yi tana kallonsa cikin jin daɗin ganin abin da tafi ƙauna macaroni da naman kifi ga miya a gefe ga ruwa ga lemon juice mai sanyi, wani irin yawu ta hadiye tana buɗewa ta soma ci yau dai ba bismillah ta shiga antayawa cikinta, shi kuwa ya zuba mata idanu yana sakin murmishi har ta gama, da kanshi ya wanke mata hannu ta wanke bakinta. Hamma ta kuma yi ta ce" Bobby bacci"،Ta ƙarashe maganar tana lumshe idanu. Ɗaukan ya yi cak ya miƙe tsaye, taku uku ys yi sai gashi a cikin ɗakinsa wanda ya tsaru gadon ma abin kallo ne , ɗaurata ya yi ya lulluɓeta da bargo shi ma ya haye gadon ya kwanta tare da janyota gareta ya lumshe, shafata yake yana ƙoƙarin cire mata kayan jikinta ta buɗe idanunta, so take ta dakatar dashi amma taji kamar an daure mata duk wata jijiyar jikinta, hannu yakai zai sauke akan ƙirjinta ta waro idanu ta ce" Bobby! Ta faɗa a zabure ya yi saurin rufesu da bargo, ihu ta kurma.

Zabura ta yi ta tashi tana salati jikinta ya yi sharkaf da zufa, Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Me yake faruwa dani? Ta faɗa a bayyane dan ba ƙaramin tsoro ya kama ta ba da zarar ta tuna abin da ta gani a cikin mafarkin nata...

Tashi ta yi taji bayanta na mata mugun ciwo haɗin da jikinta gama ɗaya, mamaki sosai ya rufe Auta tana dingisawa da haka ta shiga banɗaki ta soma yin wanka jin zafi ya hanata sukoni...

Banko ƙofar aka yi lokacin ta fito daga wanka sanye da towel tana goge jikinta, da sauri ta kalli ƙofar taga suak haɗa idanu da Sudas dake mayar da numfashi yana riƙe da hannun shi hawaye shaɓe-shaɓe kwance a fuskar shi, da mamaki ta kalle shi sai kuma ta kwashe da dariya ta zau ne a gaban madubi ta shafa mai, bayan ta gama ta ce" Yaya Sudas wai lafiya na ganka da daren nan kamar an koro ka?"

"Babu lafiya Auta taimaka ki mini ruwan zafi ina jin na ƙarfe" Ya ƙarashe maganar yana yin zaman 'yan bori . Dariya Auta ta kuma yi ta shiga banɗaki ta kawo ruwa a cikin wani bokati, zama ta yi ta ɗauki towel ɗin ta ƙaramin ta dubesa ta ce" Yaya ina Yaya Sauban da su Anty Fadila? Ko kuma bacci suek yi ne?

Jam majina ya yi yana gunjin kuka kamar wani yaro ya ce" Waiyo Allah Auta! Ki dena mini maganar su ki gasa mini dan naji saukin azabar da nake ji." Murmishi ta kuma yi ta ɗauko ta danna masa da karfi, ihu ta kurma yana kwace ƙafar saboda tsananin azaba a gigice ta nufi bakin ƙofa ya rarrafa da sauri zai fita sai kuma ya yi maza ya dawo yana kuka wiwi ya zauna a bakin ƙofar ɗakin yana rufewa. Mamaki sosai ya kama Auta ta isa gareshi tana ce masa lafiya amma ya kasa bata amma, dawowa ta yi ta ɗauki ruwan ta zo gurinsa ta ce" Yaya ka tsaya don Allah a gasa ma targadan naka."

"Wash Anty Afra don Allah ki dena mini da ciwo da hankali za kike yi kar ki ƙarasa ni kin.. Kwashewa ta yi da dariya ta ce" To Yaya yau kuma nice na sawo Anty Afra ba Auta ba?" "E kece ko Mama zan ce miki tun da mun samu an dena mana duka"Ya faɗa yana wani narkewa kamar yaro ɗan shekara 3.. Dariya Auta ta kuma yi ta gyara ta soma gasa masa a hankali, idan taji ya yi shuru sai ta danna masa da karfi ga ruwa akwai zafi sosai, ai kuwa sai ya kurma ihu yana kiranta da Yaya Afra a haka har ruwan ya wuce...

Su Fadila da Abokanta a palo sai da aka gama lallasa su aka gaji kana aka dawo da wutar palon, da ƙyar kowa yake motsawa daga kwanciyar da ya yi, abin da ya ba su mamaki komai na palon tsaf yake duk futsari da zawon da suka yi babu a ƙasa ko akan kujera sai a jikinsu kawai suke jin tsami...

Ana gama salla a Masallaci Mufy dake kwance tana jin ƙafarta da hannunta kamar ba'a jikinta suke ba ta lalibo jakarta ta dannawa Mommynta kira, tana ɗauka ta dinga mata kuka tana bata labarin abin da ya faru da su, abin ya bawa Mommynta mamaki ta turo mata mota aka zo daukanta, da jan jiki ta fito daga palon tana kuka wiwi hannunta har ya kumbura ya yi sintum ya mata nauyi, shi kanshi Direban gidansu da ya ganta sai da ya tsorata, taimako ta nema ya sata a motar na fa ya gara jinjina abin da ya samu Mufy wai yau shi ne take cewa ya taɓa jikinta ya taimaketa ta shiga mota? Sai da ta kuma maganar da muryar kuka kana ya ɗagata cak kamar yarinya ya sakata a mota yaja suka bar gidan..

Haka sauran kowa kira ya yi aka zo aka ɗauke su , labari suke badawa gidan su Big girl Fadila aljannu ne kamar kan tsamiya, wasu sun ce sun yanke ƙawance da Fadila wasu kuma sun ce za su ƙawance amma ba za su zo gidan su ba...

Mommy da kanta ta taimakawa Fadila suka shiga toilet din palo ta gasa mata jiki, ita kanta abin ya firgitata na jiya gadda aka wullata ɗaki aka rufo ƙofar gam...

Daddy sai da ƙarfe 6 na safe ya fito daga wani part dake can jikin ɗakinsa, shi kansa hankalinsa a tashe yake matuƙa, amma sai ya nuna ban ga komai ba a jiya aka ɗauki Fadila da Sudas da Sauban zuwa Asibiti....

"Doctor!Doctor ka taimakeni ga Ƴata na kawo ka duba ta karka tafi gida" Cewar wani tsoho yana binsa kamar zai yi kuka...

A fusace ya juyo ya gagga masa magana ya wuce har da zagi ya shiga mota ya bar Asibitin, dafiya yake ya zo kusa da Masallaci yaji ana kiran Sallar Isha'i ya tsaya ya nufi ciki.. Bayan ya yo tsarki ya zauna zaman alwala, da farko ya fara wanke fuska kana ya shafa ruwa a kai, ya wanke hannu sannan ya wanke ƙafafuwa cikin sauri ya shige masallacin, wani dake kusa dashi ya ce" Kai jama'a yanzu duk yawancin samarin zamanin nan ko alwala ba su iya ba."

Bayan an gama ya fita da sauri ya wuce zuwa gidansa...

A hanya yana kan tafiya ya hango wata Saniya babba a tsakiyar hanya ya kai mata karo ji kake kiiiii!






_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[12/12, 22:59] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_




Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_


_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_


بسم الله الرحمن الرحيم


1️⃣2️⃣


"Subhanallah! Yake faɗa jin an yi sama dashi sosai ya runtse idanu jikinsa na rawa tsoro da firgici sun dabaibaye shi, jin komai ya lafa ya sa shi buɗe idanunsa a hankali har ya gama buɗewa cike da mamaki yake kallon inda yake yana shafa inda aka zaunar dashi, "To waye ya kawoni gida kuma? Ya furta maganar tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki.. Kafin ya yi wani ƙwaƙƙwaran motsi yaji palon ya ɗauki amsakowar wata murya mai amo marar daɗin ji , tuni ya maƙale a jikin bango yana zare idanu tamkar ɓarawon da aka kama a bainannasi jikinsa na ɓari ya soma faɗin" Waiyo Allah na shiga uku! Shuuu yaji an wuce ta gaban shi tamkar wucewar mikiya, ihu ya kurma yana ƙara mannewa a jikin bango tare da rufe fuskar shi. "Buɗe idanunka na ce! Yaji an faɗa a karfi kamar za a fasa masa dodon kunne ya buɗe fuskar ya rufe kunnewan shi kana ya ɗan buɗe idanunsa kaɗan dan yaga waye ya masa magana mai amo irin haka, hango wasu dogayen halittu ya yi masu kama da mutane sai dai ba'a ganin fuskarsu sai dai hannu shi ma hannun irin na biri duk gashi ya yanyame ga facuna masu tsowo da tsini, kwalalo idanu ya yi na ganin wannan halittun wanda shi dai a iya rayuwar shi bai taɓa ji ko a hikaya àn bada labarin irin wannan halittun ba, ɗaya daga cikinsu ya yo gaba hannnun shi ɗauke da jariri ya miƙawa Doctor yana faɗin" Gashi ka duba mini shi bashi da lafiya shi ya sa muka kawo shi." A rikice take kallon jaririn mai kama da gwaggwon biri yana watsu masa harara tare da zaro idanunsa wanda suke jajaye manya-manya babu ƙyan gani. "Maza amshi ka duba shi na ce za mu wuce." Yaji wannan mai ɗauke da jaririn ya kuma faɗa yana matsowa kusa dashi, ai kuwa Doctor ya kurma ihu yana neman inda zai ɓoye kamar zai tsaga bango ya shige ciki sai ƙara mannewa ya yi ya haɗa zufa sharkaf, futsarin da ýake ji tun a hanya ban san lokacin da ya saki futsarin ba yana ƙyarma kamar mai farfaɗiya, ɗauko hannun shi aka yi tare da murdawa ya bada sautin ƙararassss! Wani kalar ƙaran azaba Doctor ya saki yana huci fat! fat! fat! Tamkar numfashinsa na barazanar rabuwa da gangar jikinsa saboda tsananin azaba. Kai! Aka faɗa har sai da ya yi wani kalar zabura yana ja da baya bakinsa na rawa ya soma cewa" N...Ni ..Nifa ba Likita ba ne ku gafarc.. Bai ƙarasa ba jin saukar wani abu mai mugun nauyi akan gadon bayan shi kamar an daura masa buhun sumintin buhu uku da ƙyar yake iya fitar numfashi. Jaririn aka kuma miƙo masa aka ce masa ya duba lafiyarsa bashi da lafiya a wannan karon Doctor kasa magana ya yi saboda nauyin da aka ɗaura masa a baya sosai nauyin ke ratsa masa cikin jikinsa, wani kalar hayaƙi jaririn da ake miƙo masa ya hurawa Doctor nan da nan hayaƙin ya mayar da fuskarsa baƙa kamar an shafa gawayi ko kuma ɓakin panti a fuskar, ihu yake yana neman taimako sai kira sunan mamansa yake har da 'yan'uwansa gabaki ɗaya a wannan lokacin babu sunan

1 Comments On ALJANAR GIDANMU
avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment